You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaman ya k'are haka"

Cak ya tsaya kusan minti biyu sannan ya fice kawai.

Kan kujera ta fad'a tana kuka "dole ka soni babu wanda zaka so a duniya sama dani ni ce mace ta farko da ka fara so a duniya wallahi baka tsaneni ba Jalal" kuka dirza ita kad'ai tana jin fitarsu ta tashi ta koma bedroom ta kwanta kanta na mata wani matsanancin ciwo.

A b'angaren su Mameey kuwa kai tsaye tace ya kaita wannan hotel d'in.

Yayi mamaki sosai har yake tambaya me zatayi a can kasancewar bata fiya zuwa hotel ba sai da wani k'wak'k'waran dalili.
"Kai da kai kake driving ai zaka gani ko me zanyi a can d'in"

Shiru yayi da yaji kamar tayi maganar da fad'a-fad'a.

Suna k'ofar room d'in Mameey tayi knocking shi dai Jalal kanshi a d'aure yake dan haka da ido kawai yake bin Mommy,shiru ba'a bud'e ba ta sakeyin knocking.

"Am coming" daga ciki akayi maganar.

Muryar da Jalal yaji ta hautsinasa jin muryar yayi kamar gizau,tana bud'ewa sukayi ido hud'u dashi.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" ta fad'a tare da rufe fuska taja da baya.

Kallonta yayi tun daga sama har k'asa,wandone a jikinta irin skin tight d'in nan bai je k'asa sosai ba,sai rigarta body hug kuma aimless ce kanta babu d'ankwali ta saki kalabar attach d'in har gadon bayanta wasu kuma sun zubo gaba.

"Baby keda waye anan"

Matashin da ya fito daga toilet yake maganar,daga shi sai boxer da d'an k'aramin towel yana goge ruwan jikinshi,ya matsa Mommy tayi saurin rik'e shi tace "Karka yi masa komai Jalal da bata kawo kanta ba da babu yadda za'ai ya kawo ta da k'arfi"

Kuka Amal ta fara ta tsugunna tace "dan Jalal kayi hak'uri na tuba wallahi bazan k'ara ba"

Kallon Mommy yayi idanuwansa cike da kwalla yace "Mommy ki sanar dani cewar abinda idona ke gani mafarki ne ba gaskiya ba"

"Jalal gaskiya ne wannan shine abinda nake so ka gane game da yarinyar nan ka kasa gane wa,kwanaki ma ina shiga falonta namiji na fitowa daga bedroom d'inta na rufa mata asirine saboda ciwon 'ya mace na 'ya mace ne shiyasa na nemi ka sake ta kak'i"

Saurayin nata da yake tsaye tuni ya gane Jalal dan haka shima a kunyace ya fara zura rigarshi.

Hannun Amal Jalal ya fuzga yayi waje da ita Mommy nayi masa magana kan ya tsaya ta saka hijabinta amma ina.

Bayan mota ya watsata ya rufe,Mommy na shiga yaja motar da k'arfi.

Yana driving yana hawaye har suka isa gida.

Mommy sauka tayi ta wuce part d'in ta shima ya wuce part d'insa,Janan najin shigowarsu ta sama d'akinta key.

Amal tana tsaye ta kasa d'aga k'afarta ta shiga gidan dan tabbas ta san zamanta a gidannan ya k'are.

"Meyasa?shed'an baka min Adalci ba,meyasa da nayi Aure ban bar yin wannan gurb'atacciyar rayuwar ba?"

Zama tayi a gefe tana kukan nadama daidai lokacin ya fito,mik'ewa tayi tsaye hawaye sharkaf a fuskarta ta fara kallon takardar hannunsa.

Girgiza kai ta fara tana fad'in "ba halina bane dan Allah ka bari inyi maka bayani"

Wurgi yayi da takardar yace "babu bayaninki da zan saurara zamana dake ya k'are,na sake ki saki uku Amal"

"Na shiga uku dan Allah kayi hak'uri Jalal karka ruguza min rayuwa"

"Amal 1hour na baki ki tartare komai naki ki bar gidana bana k'aunar ganinki kada kisa inyi abinda zuciyata ke assasamin"

Wucewa yayi ya koma ciki,cikin kuka ta shiga ta had'a kaya a trolley ta tafi.

Koda taje gida bata basu takardar ba sai kawai tace ya sake ta amma yak'i fad'a mata dalilin sa.

Kai tsaye Ummu ta k'aryata ta yayinda Abbu ke fad'in shine yaga duhu kuma sai Allah ya saka mata domin ya wulak'antata saki uku lokaci guda.

Ita kuwa ganin abin take tamkar a mafarki koda ta nutsu ta daina kukan ta kira Sarah ta fad'a mata aikuwa tace gatanan zuwa da safe.

Kusan k'arfe goma kuwa tazo "k'awata lafiya na ganki haka kamar wadda ta shekara tana ciwo"

"Sarah an sakeni saki uku"

"Me?kinga k'awata bana son wasa wane irin saki ana zaune k'alau"

"Wallahi dagaske nake miki"

Fashewa tayi da dariya tana rik'e ciki, ran Amal gaba d'aya ya b'aci.
"Sarah meye hakan?nifa bana son rashin mutumci idan da kin san dariya zakizo kina yi min ai da baki zo ba"

Dafata tayi tana dariya tace "bazaki gane ba kawata wallahi naji dadin haka ne,saboda abinda kikayi min,ni ce nasa Janan ta rik'a bibiyarki dan taga halin da kike ciki tun ranar aurenki ta san wacece ke,domin na sanar mata da komai tun lokacin suna Egypt"

"Ban gane ba Sarah?"

Tashi tayi tsaye tace "yawwa bara na ganar dake,kin manta abinda kika yi min?kika rabani da Khalid ana gab da bikinmu shiyasa nima nace sai na rama,kinga kema yanzu kin bar mijin naki sai mu zauna mu d'ora daga inda muka tsaya"

Kuka Amal ta fashe dashi tace "amma kin cuceni Sarah,Allah ya isa tsakanina dake"

"Allah ya Isar mana baki d'aya ke har kin manta abubuwan da kika min amma da yake ke sakarai ce har kika cigaba da fad'a min sirrinki ta hakan ne na gano bakin zaren,na barki lafiya ina miki murnar saki"
Ta figi Jakarta ta wuce.

"Wayyo Allah na cuci kaina meyasa nayi haka?"

Kuka sosai tayi mai cike da nadama.

***********

Kallon agogo ta sake yi taga k'arfe 02:30pm.
Duk gidan ta jishi wani iri,babu Mommy tun asuba ta tafi Lagos sai kiranta tayi a waya ta sanar mata cewa ta tafi dan bata son Jalal ya kawo mata wata magana,tace sai ta huce zata dawo gashi Jalal tun daya dawo jiya har yanzu bata ga fitowarsa daga d'aki ba.

Baki ta tab'e tare da fad'in "shi ya sani"

Tashi tayi ta shiga d'aki ta kwanta tana son bacci ya d'auketa amma inaa

Kusan k'arfe biyar na yamma ta tashi ta nad'e daddumar da tayi sallah sannan ta k'ara fita falo ta zauna.

Tana k'ok'arin kunna TV taji tarinsa daya bayyane ko ina a gidan.

"Lafiya?" Tayi maganar a fili.

Tashi tayi da sauri ta nufi bedroom d'insa.

Tana bud'ewa ta ganshi yana dafa bango yana k'ok'arin fitowa hannunsa rik'e da k'irjinsa.

Da sauri ta k'arasa gabansa ta rik'esa "Jalal meya same ka?"

Kallonta kawai yake idanunsa sun fara juyewa suna lumshewa.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Jalal lafiya?"

Da k'yar ta kamashi ta mayar dashi kan gadon.

Fita tayi da sauri tana hawaye taje ta d'akko waya ta kira doctor.

Dawowa tayi d'akin har lokacin yana tari sama-sama.
Zama tayi akan side drawer ta dafe goshinta tana hawaye.

Jin ya ruk'o hannunta yasa ta juyo ta kalleshi.
Yatsun hannunsa ya zura cikin nata ya rik'esu sosai.

Kallon shi tayi idanunsa a lumshe suke a hankali ta saki ajiyar zuciya.

Cikin minti talatin doctor yazo,k'ok'arin cire hannunta tayi daga nashi amma yak'i saki.
Doctor yana ta tsokanarsa.

Magunguna ya rubuta sannan ya bashi wasu ya tafi.

Da sauri Janan ta tashi ta bawa Asabe tace taje chemist ta sayo.

Dawowa tayi ta shiga toilet ta had'a masa ruwan wanka.

Fitowa tayi ta zauna gefensa tace "kayi wanka sai kaci abinci na had'a maka ruwan.

Kai kawai ya gyad'a ita ta taimaka masa yayi wanka sannan ta shiryashi.

Tea ta had'a masa mai kauri ta bashi yasha ya kwanta.

Ya samu kulawa sosai a gurin Janan cikin kwana biyu ya warware.

Aikuwa ranar ta juye masa dan tun safe da yace mata zaije office tayi mishi adawo lafiya.

Kusan k'arfe uku ya dawo tana zaune a falo tana kallon film tun bayan amsa sallama bata k'ara ce masa komai ba.

Zama yayi kan kujera ya d'an kalleta yace "wallahi na gaji sosai"

Tashi tayi tsaye ta kalleshi ta tab'e baki ta wuce.

Bedroom d'in ta taje ta zauna ta saka hannunta a hab'arta,tana zaune kuwa ya shigo,da sauri ta tashi zata fita yayi saurin cewa "idan kina k'aunar Annabi Muhammad (S.A.W) ki tsaya"
Cak ta tsaya ba tare da ta juyo ba.

Takawa yayi har gabanta yace "meya faru?menayi miki?waye yazo ya zugaki lokaci d'aya haka?"

"Har kana tunanin akwai wanda zai zugani?Jalal kai fa ka fad'a cewa ka tsaneni to mene amfanin sakar maka fuska,darajar rashin lafiya ce tasa na kula da kai har tsawon kwana2"

Zata tafi ya rik'o hannunta tare da juyo da ita suna facing juna.
"Kece fa,kece wannan macen wadda na fara so a rayuwata na soki so mara misaltuwa duk macen dana so bayan ke ban mata son da nayi miki ba,Janan karki sake guduna dan Allah ki tausayawa zuciyata a wannan karon"

Hawaye ne kawai ke fita daga idanunta "Jalal bana son ka yaudari zuciya ta me zakahi dani nice fa wannan mai cutar k'anjamau"

"Munyi waya da Mommy d'azu na bata hak'uri nace kuma ta tayani baki,anan ta sanar min cewa baki da wannan cutar kuma har ta turo min result din ta waya,Ina sonki Janan babu yaudara a maganata"

"Inaso kiyi min alk'awarin zama dani har abada,muna sonki daga ni har Mommy na san a wannan karon nayi zab'in da Mommy tafi so kuma nasan bazan tab'a dana sanin kasancewa dake a matsayin mata"

Jikinsa ya rungumota ta lafe tana kuka mai cike da farin ciki.

Da sauri ta nufi d'akin ta ta d'akko wrist watch d'in ta d'ora masa,sumbatar hannun yayi yana wani murmushi mai cike da bayyanar farin cikinsa.



*ALHAMDULILLAH* _godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki mai kowa mai komai daya bani ikon kammala muku wannan littafin,kuskuren dake ciki Allah ya yafe min._

_Ina fata zaku min uzuri akan wasu abubuwa da kuke ganin kamar ya dace in saka kuma ban saka ba._

_Zakuga na datse labarin Hisham,naso sakashi a littafin sai wasu suka kawo min k'orafin zanja littafin ne, so zan cigaba da labarin HISHAM mai taken 'KADDARATA labarin Hisham labarin gaske ne,ma'ana true life story,ban san yaushe zan fara ba,zan iyayi a ko yaushe ma daganan zuwa ko wane lokaci so karkuyi ta zura ido kuji shiru._

_Ina mik'a sak'on godiya ga dukkan masoya littafin nan nagode sosai kuma ina muku fatan alkhairi._

_Ina jajen rashin SAFEENAH TALBA(SAFNAH) Allah yasa kina nan lafiya keda babynki cikin kwanciyar hankali a duk inda kuke._🙏



_Sak'on kai tsaye game da littafinnan, kai tsaye ga wannan number_ _07035111671_








_Sadeey S Adam_✍🏻

Downloaded From https://tknovels.com.ng


Please Login or Register in order to submit comment