You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dakatar dasu,bayan ta gaidasu ta zauna tace "Mameey na kira number Janan tun d'azu bata shiga ba,shine nazo naga ko lafiya saboda tace zamuyi magana idan ta koma gida"

"To kinga tunda kuka fita bata dawo ba muma sai kira muke wayarta a kashe" Mameey tayi maganar

"Tun yaushe kuka rabu" muryarta na d'an rawa alamun rashin gaskiya ta d'an dake ta kalli Fahad tace "tun wajen 6:15pm da yake yau sai 6:00pm muka gama lectures "

"To Mameey maybe ta tsaya a wani gun tunda yanzu 6:30pm mu d'an jira mu gani"

"To amma meyasa ta kashe wayar bayan ta san za'a nemeta?" Fahad ya sake jefowa Raihan tambaya.

'Dak'ar ta lalubo kalmar "eh tace min Aliyu nata kiranta gashi muna lecture shine tace bara ta kashe idan mun fito sai ta kirashi to maybe ta manta bata kunna ba.

" kiji wani shashanci irin na Janan"
"Mu dai jira mu gani".


*********

Tana kwance taji alamun an bud'e k'ofa idonta a rufe take karanto addu'ar da duk tazo bakinta.

"ba dai bacci kikayi ba ga babana yazo" jin muryarshi ne yasa tayi saurin bud'e ido tare da mik'ewa zaune.

Manyan ledoji guda biyu a hannunsa ya dire mata "na san kina jin yunwa"

Wani sabon kukan ne yazo mata,ta had'e hannunta tana fad'in "kayi hak'uri dan Allah karka cutar dani ka maidani gidanmu na san ana ta nemana"

"Zan mayar dake amma sai kinci abinci sannan kinmin abinda ya kawoki"

"Karka cuceni dan Allah"

"Na miki kama da macuta?"

Bata bashi amsa ba kawai kallonshi take yana bud'e ledojin,takeaway ya fitar ya bud'eshi, lafiyayyan shinkafane da coslow a gefe,sai d'ayan ledar da wani yogurt,lemuka,shawarma,pizza da kaji.

Kallonta yayi yace "bismillah"
Kai ta girgiza tace "na k'oshi"
"Baki son tafiya gida kenan?"

"Idan naci zaka kaini gidanmu?"

Har tausayi ta bashi amma bai nuna mata ba kawai dai ya amsa mata da "eh"

Gefe ya zauna yana kallonta tana ta cin abinci.

Ta d'an ci da yawa sannan tace masa ta k'oshi.

"Okay" ya fad'a yana danna waya,gani tayi ya kara a kunne gabanta ya cigaba da fad'uwa,sai ji tayi yace "Hello Mom ga surukar taki ku gaisa"

Bai jira komai ba kawai ya manna mata wayar a kunne da sauri ta rik'e tanaji ana ta hello amma ta kasa magana,meyasa zai mata haka,kallonshi tayi taga ya had'e hannunsa alamar dan Allah tayi magana.

"Salamu alaikum" ta fad'a a sanyaye.

Daga d'ayan b'angaren taji wata daddad'ar murya tace "wa alaiki salam 'yata ya kike"
"Lafiya lau, ina yini ya gida?"
"Lafiya k'alau 'yata" shiru ne ya biyo baya sannan taji tace "yace min a poly kike ko?"
"Eh"
"Wane course kike karanta?"
"Business Administration"
"Okay ba course d'inku d'aya ba kenan?"
"Eh"
"To Allah ya taimaka,da fatan dai yana maida hankali dan nasan Yarima akwai rashin ji"
"Bayayi,yana karatu sosai" ta fad'a tana kallonsa.

"Ki kula dai 'yata banda shiririta banda biyewa abokan banza"
"Insha Allah"
"Madallah yaushe zaki kawo mana ziyara?"

Shiru ta d'anyi kafin tace "duk lokacin da kuke so"
"Ai mu ko yaushe ma muna son ganinki dan mun dad'e muna son ya fito da mata shida d'an uwansa sunk'i amma kimin alk'awarin da weekend zaki ziyarce mu next week"


Jikinta a sanyaye tace "insha Allahu"
"Mungode,af na manta baki fad'a min sunanki ba kuma shima bai fad'a min ba"

"Sunana Janan"
"Suna mai dad'i Allah ya inganta rayuwarki"
"Ameen" ta fad'a tare da saurin mik'a masa wayar.

"Hello Mom hankalinki na san ya kwanta yanzu"

Bata ji abinda tace ba sai maganarshi da taji ya sake fad'in "Mom ai a fili ma haka take"

"Mom insha Allahu"

"Shima akwai lokaci da iznin Allah"

"To ba damuwa,bye bye" ya katse wayar,ita kam jikinta sai karkarwa yake.

"Saura babana" ya fad'a yana murmushi.

"Dan Allah kayi hak'uri ka rufamin asiri"
"Dama ai a rufe yake,kina nufin baki son ganinshi da sanin nasa"

"Dan Allah kayi hak'uri ka maida ni gidanmu"


"Amma da sharad'i?"

A tsorace ta kalleshi tace "sharad'i kuma wanne?"






*Ku biyo ni*✍









_Sadeey S Adam_
[9/29, 8:15 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄


```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```







15

Kallonta shima yake yana shafa fuska yace "ya naga jikinki na shaking tun kafin na fad'a miki"

Bata ce komai ba idonta yana gefe amma tsoronta k'ara dad'uwa yake.

"Idan na kaiki gida zaki gabatar dani gabansu mom da dad d'inki na gaidasu?"

A tsorace ta kalleshi,idonta duk ya firfito,ta marairaice tace "zan kaika gobe amma yanzu dare yayi za'a min fad'a"

"Okay ba damuwa kin dai yi alk'awari ko?"

Kai ta d'aga alamar eh
"Yawwa muje"


A mota suna tafiya ko wanne yayi shiru,ita tana tunanin k'aryar da zata yiwa su Mameey shi kuma yana tunanin yadda zasu k'arke da Mom.

"Kin san me?" Muryarsa ta daki dodon kunnenta,a tsorace tace "a'a" dan a matuk'ar tsorace take dashi.

"Zan fad'a miki dalilin daya saka na yiwa mahaifiyata k'arya dake dan karkiyi tunanin ko sonki nake u are not my type dan babu auren siririyar mace haka kamar ke,sirantarki tayi yawa tausayi ma kike bani dan ba zama ki iya zaman aure ba,zakiyi ragonta da yawa bazaki tab'a jurar ayyukan da matan aure ke sha ba"

"Na yiwa Mom k'aryane saboda hankalinta ya kwanta,dan tun lokacin da dad ya rasu take damunmu akan muyi aure amma aure baya gabanmu ma,kin san dalili?"

Bata bashi amsa ba,bama ta kallonshi,ya san tana jinshi murmushi yayi a zuciyarshi yace _kina da aji sosai_ a fili kuwa ya cigaba da fad'in
"Mu biyu ne a gurin iyayenmu duk kanmu maza ne, yayana Adnan sai ni yarima Jalal,na samo sunan yarima daga gurin kakana wato mahaifin Mom wanda ya kasance shine sarkin bauchi"

"Shine ya fara kirana da sunan kasancewata ina da k'asaita da isa da nuna izza tun ina k'arami,hakan ne yasa wasu mutanen suke kirana da saraki yayinda kakana Sarki Abdurrahman ke kirana da yarima"

"A lokacin zan iya cewa rabin rayuwata a bauchi nake yayinda iyayena suke zaune a Abuja,na samu tsangwama wajen 'ya'yan sarki dan gani suke duk cikin jikokinshi yafi sona,dan ko yana fada ina gefensa"

"Hakan ne yaja cece kace har abin yana son tab'a zumuncinmu dan haka Daddy yace a dawo dani Abuja kawai"

"Babana shine minista na kud'i a birnin tarayya ta Abuja C.B.N,muna da arzik'i sosai kuma mun samu gata fiya da tunaninki"

"Ni da Adnan dukanmu a U.S mukayi degree d'inmu bayan mun kammala muka dawo d'auke da kyakkyawan sakamako"

"Kwatsam bayan dawowarmu da wata uku sai daddy yace yayima Adnan mata d'iyar abokinsa mai suna bilkis"

"Kasancewarshi mutum ne mai hak'uri sai ya amince ba tare daya musawa daddy ba,ita kuma Mom tace bazai aureta ba saboda yarinyar bata da tarbiyya"

"Fad'a ne ya kaure tsakanin Daddy da Mommy wanda har abin ya haddasa gaba tsakaninsu"

Ajiyar zuciyar da tayi ne yasa yayi saurin katse maganar ya kalleta "ya dai"
"Bakomai" ta bashi amsa,a zuciyarta tace _present abinda yake faruwa a gidanmu_.

Shi kuma ya cigaba da fad'in "Adnan dai ya cigaba da bawa Mom hak'uri akan insha Allah idan ya aureta zata canza hali,Mom tace sam bata yarda ba"

"Haka dai kin san namiji yafi k'arfi a fannin 'ya'ya Mommy dai bata so haka akayi auren Adnan da bilkis ya koma kano da zama saboda a can ya samu aiki a wani katafaren company na motoci dan yace shi yafi so ya gina kansa da kansa,ni kuma daddy ya sama min aiki anan C.B.N amma ko a lokacin bani da niyyar aure barni dai da wulak'anta duk macen da tace tana sona dan dama na gaya miki inada izza gashi bana jin magana,kuma dama ni da Adnan Allah bai d'ora mana biye-biyen 'yan mata ba"

"Shekarar Adnan da bilkis biyu da yin aure Allah ya basu haihuwa suka samu d'a namiji suka saka masa sunana Jalal suna kiransa da Prince"

"Shekarar yaron hud'u a duniya ya rasu sanadin rashin lafiyar da yayi tayi ba'a san dalili ba,sunje har turai amma abin ba sauk'i har dai Allah yayi ikonshi akan yaron,ni kaina sai dana sha kuka sosai kasancewar mun shak'u da shi sosai bare su iyayensa da suka haifeshi"

"Ko shekara d'aya prince baiyi da rasuwa ba itama bilkis ta fara rashin lafiya dsame irin wadda prince yayi,babu yadda ba'ayi ba akan suje asibiti tak'i,ta kuma k'i yarda doctor yazo gida ya duba ya,mamanta ta goya mata baya akan zasuyi magani a gida,shima mahaifinta ya zama tamkar mijin tace yace tunda sunce a barta a gidan to a barta"

"Watanta biyu tana jinya ta rame sosai tamkar k'warangwal,a cikin wata na uku tace ga garinku"

"Idan kinga yadda Adnan ya rame ya damu sai kin tausaya masa"

"Bayan 'yan watanni da rasuwarta daddy yace ya yanke shawarar bashi k'anwarta"

"Adnan ya hangi irin rayuwar da sukayi da Bilkis kusan kullum cikin fad'a suke zaman hak'uri yayi da ita,ga k'anwar tata ta fita bud'e ido da fitsara ga gantali kamar bilkis d'in dan haka yace wa daddy ya barshi a wannan karon ya zab'i zab'insa"

"Nan ma rigima ce ta sake kacamewa a gidanmu Mommy harda tattare kayanta tace wallahi indai ya auri hajar to sai ta bar gidan kuma sai dai ya canza uwa"

"Kwana biyu da faruwar abin muka tarar yayi wasik'a ya ajje akan shifa a wannan karon zai tafi nemo soyayyar gaskiya dan haka idan yayi musu laifi su yafe masa"

"Hankalin Mommy ya tashi sosai daddy kuwa yace duk wanda yasa akayi cigiyar Adnan bai yafe masa ba"

"Haka muka zauna cike da jimami,ni dai a cikin Abuja babu inda ban duba ba haka a kano ma na tattabayi abokansa cikin sigar da bazasu fahimci guduwa yayi ba,gidansa kuwa da naje a kulle da alama ya sallami maigadinsa ma"

"Kwatsam daddy yazo mana da labarin zai bawa hajar ni ma'ana zai had'a mu aure,na kuwa bud'e idona nace babu wanda zai min auren dole idan na shirya aure zanyi amma ni zan zab'o mata da kaina"


"Dagani har Mom abin mamaki yake bamu,mun rasa wace irin aminta ce tsakanin Daddy da Alh.Ibrahim baban su bilkis"

"Ganin dai ba yarda zanyi in auri hajar ba yasa ya hak'ura,banyi auren ba itama batayi ba,tsawon shekara uku sannan Adnan ya dawo,ganinsa ba k'aramin d'aga mana hankali yayi ba yadda muka ganshi ya rame ya d'anyi duhu ga gashi buzu-buzu ko ina a fuskarsa idan baka sanshi ba zaka gane shi ba"

"Mun tsorata sosai ganin yanayinsa amma kuma munyi murna da dawowarsa,daddy da kanshi yayi waya akazo aka aske masa gashin akai masa gyaran fuska"

"Kwananshi biyu da dawowa ya bamu labarin irin soyayyar da yayi da wata yarinya har suna shirin yin aure komai ya ruguje,da irin wulak'anci da k'alubalen daya fuskanta bayan tafiyarsa,babu wanda bai masa hawaye ba,a lokacin daddy yayi alk'awarin bazai sake yunk'urin yi masa auren dole ba ya yarda ya fito da duk wadda yake so saboda nima ya gaji da zamana a haka duk da lokacin shekarana 29 a duniya shi kuma yana da 33 amma bamu da jikin girman da za'ace mun kai haka"

"Adnan yace shi ya hak'ura da soyayya k'ila baya da farin jinin wannan"

"Haka farin ciki ya cigaba da wakana a gidanmu kamar ada kafin ayi auren Adnan"

"Watansa shidda da dawowa ya fara rashin lafiya yau ciwo gobe waraka,a k'arshe wani mugun gudawa ya rik'ayi ba tsayawa,da k'yar ya samu abin ya lafa"

"Wata rana bani mantawa muna zaune da yamma a main parlor da Mommy muna hira sai gashi ya shigo tamkar an hankad'o shi"

"Duk kanmu muka mik'e a tsorace dan a ranar ya koma kano da asuba sai gashi da yamma ya dawo ai dole mu tsorata"

"Takardu ya mik'a wa mommy yana kuka yana fad'in Mommy bilkis ta cuceni,tun Mom bata bud'e ba take fad'in lafiya meya faru"

"Ya goge hawaye da zuffa yana fad'in ashe HIV gareta shiyasa tak'i yarda muje asibiti lokacin da bata da lafiya kuma cutar ce ta kashe prince shiyasa bata tab'a yarda mukai prince asibiti tare sai dai taje da Mommynta,ko lokacin da za'a kaishi waje k'in yarda tayi muje tare sai Hajar na yiwa visa sukaje tare,sai yanzu ina bincike can k'asan kayanta cikin wata atamfa na gansu"

"Duk kanmu muka dafe kai muna salati,Mommy kuwa kuka take sosai tana fad'in dama sai da nace bana son auren nan saboda na san duk Kansu basu da tarbiyya"

"Zama mukayi zugum tamkar muna zaman makoki sai kusan k'arfe 11 daddy ya dawo yana ganinmu ya san da matsala"

"Mommy tana kuka tayi masa bayani tare da bashi takardun,shima salati yake tayi,a take ya kirawo family doctor d'insu aka masa test sannan doctor yace da safe zai dawo da result"

"Babu abinda Adnan yake sai kuka tamkar yaro ranar haka ya zama,sai k'ara fad'i yake wallahi ban tab'a mu'amala da wata mace bayan bilkis"

"Ranar kwana mukayi a zaune muna bawa Adnan hak'uri tare da bashi k'arfin gwiwa"

"Da safe da k'yar muka samu mukayi break fast dan Mommy ma saida daddy ya matsa mata,k'arfe 11 na safe doctor Hafiz ya dawo da sakamako ya nuna cewar shima Adnan yana d'auke da cutar tsawon shekarun nan,a take daddy ya suma,haka Mommy ma,shi kuwa babu abinda yake sai addu'a da hawaye yayinda nima nake hawayen"

"Da k'yar aka samu suka tashi,kwana uku da faruwar abin daddy ya rasu saboda tsananin damuwa zuciyarshi ta buga,dan gani yake kamar shine sila,dan koda ya sanar wa da mahaifin bilkis sai suka k'aryata mommynta har da zage zage wai sunwa matar dake cikin kabari sharri"

A dai-dai lokacin yazo k'ofar gidan.

Tsayawa tayi tak'i fita.
"Ya kika tsaya kije sai da safe" a lokacin ya lura fuskarta sharkaf da hawaye.

"Na san duk wanda yaji labarin Adnan dole ya tausaya masa,wai a hakan ma ba komai nake fad'a miki ba dan ban baki labarin wahalar daya sha lokacin daya bar gida yaje yayi soyayya da wata mara imani" ya fad'a shima yana goge hawaye.

"Ka k'arasa min labarin dan Allah"

"Ki bari sai da safe idan mun had'u a skul kinga yanzu 8 ta gota bana son a miki fad'a"

"Karka damu na san abinda zan ce masu"

"Kin tabbatar ba matsala?"
Kai ta d'aga masa.

Parking yayi a can gefe kar securities d'in su masa magana.


Ya cigaba da fad'in "Ran daddy ya b'aci sosai ganin ya yarda da abokin nasa amma ya ha'incesa,sukayi baran-baran aikuwa tun a k'ofar gidansu bilkis d'in ya fad'i daga nan akayi asibiti dashi kwana biyu a asibiti ya rasu kuma har ya rasu yana fad'in Adnan ka yafe min nayi tunanin gata na maka ashe cutar da kai nayi,duk da Adnan yana fad'in ya yafe masa bai masa komai ba k'addara ce amma still baya awa biyu bai sake Neman yafiyar Adnan ba,kwananshi biyu a asibitin ya rasu"

"Karkiso kiga tashin hankalin da Mommy ta shiga tamkar itama bazata rayu ba,d'umbin mutanen da sukayi rakiyar gawar daddy kabari bazan ce ga adadinsu ba dan kinsan nace maki ministan kud'ine ga kuma d'imbin masoya saboda daddy mutum ne na mutane,ya samu shaida mai kyau haka akayi ta zuwa daga garuruwa daban daban harda turawa da sukayi aiki a Turkish suma sukazo ta'aziyyar daddy,har wata guda muna karb'ar ta'aziyya kuma har a lokacin Mommy ba lafiya,shi Adnan ma ya fara sakin jiki"

"Watan Mommy biyar sannan ta warware sosai a lokacin kuwa duk magana ta yad'u a Abuja cewar Adnan yana da HIV shiya gogawa matarsa ma da d'ansa har yayi ajalinsu,kiji sharri fa,kinsan muna da arzik'i dole baza muyi wahalar kwatance ba,abin mamaki sai ga abin a YouTube an d'ora wai shin zargin da akewa d'an gidan marigayi Alh.Abdullah ministan kud'i gaskiya ne?,wallahi da kaina na sa akaje aka kamo wanda ya bugo abin da wanda ya d'ora sannan naje har gidan tv n da aka fara yad'a abin na wulak'antasu na kuma ce suyi abinda ya ke gabansu"

"Da abin yayiwa Adnan yawa yacewa Mommy zaije k'aro karatu a lokacin tak'i yarda tace sai yayi aure yace tayaya zaiyi aure da cutar HIV a jikinsa nasiha sosai ta masa tace ai suna auren masu cutar suma kuma harsu samu zuri'a dan haka dole ya nemo ya aura,k'in yarda yayi yace shi gaskiya zai tafi karatu har sai maganganu sun lafa,itama ganin ya damu yasa tace masa ta yarda yaje"

"Tunda Adnan ya bar k'asar take ta damuna akan nima nayi aure ina ce mata zanyi insha Allah, cikin ikon Allah kuwa na nemi admission a skul d'inku saboda ina sha'awar samun kwalin diploma na kumayi sa'a na samu shine dalilin zuwana Kaduna dan ban tab'ayin sati a kaduna ba sai dana fara karatun nan naga mommy ta matsa shiyasa lokacin da kika min tsaurin ido na samu damar da zan kwantar mata da hankali dan ko baki je ba at least ta yarda ina da shirin aure amma a zahirin gaskiya bani da niyya dan na tsorata da halin da Adnan ya shiga mata biyu sun wahalar mana dashi d'aya zab'insa d'aya zab'in daddy shiyasa bana sha'awar aure ko kad'an kuma na tsani duk wata mace mai iyeyi shiyasa nake jin haushinki tun had'uwarmu ta farko dake naga kina da rawar kai"

Ajiyar zuciya Janan tayi tare da goge wani hawayen "Allah yajik'an daddy yayi masa rahma"
"Ameen"
"Yanzu kuma ina Adnan?"
"Adnan shekararsa biyu a span yace min baya jin dawowa anan kusa sannan ya sanar mana yana karb'ar magani a can kuma yana cikin k'oshin lafiya,dan wani lokacin ma video call muke,shiyasa hankalin Mommy ya d'an kwanta amma a Nigeria mu kad'ai muke waya dashi ni da Mom dan mun d'aukar masa alk'awarin babu wanda zamu bawa number shi"

"Allah sarki,Allah ya saka masa"

"Ameen janan"

"To ya bayanin iyayen Hajar da ita kanta?"

"Hmmm suna nan a Abuja amma babu abinda ke had'amu sai kallon banza idan mun had'u,ya kamata ki shiga gida Janan tara ta wuce"

"To sai da safe"
"Allah ya nuna mana" ya fad'a yana mik'o mata wayarta,jikinta a sanyaye ta karb'a ta fita.

A falo ta tarar dasu Mameey, jikinta duk yayi sanyi ta sugunna tace "na san na muku laifi kuyi hak'uri"

"Daga gidan ubanwa kike?" Fahad ya jefo mata tambayar

"Gidan su Raihan" ta fad'a kai tsaye.

Daddy ya kalli Mameey cikin mamaki sannan ya dawo da kallonsa kan Janan yace "yaushe kika zama karuwa Janan?"

A firgice ta d'ago kai ta kalleshi tace "Abba karuwa fa"

Mameey tace"Idan ba haka bane meyasa kikayi k'arya bayan yanzu Raihan ta bar gidan nan itama nemanki tazo tun kafin magrib baki dawo ba,yaushe kika zama mak'aryaciya Janan?"

Jikinta a sanyaye ta sadda kai dan bata da abin cewa.

"Ki fad'a min gidan ubanwa kika je?" Fahad ya sake tambayarta.

Shiru kawai tayi kanta a k'ansa.

Matsawa kusa da ita yayi ya d'auketa da mari.
"Gidan ubanwa kika je?"

Da hannu ya fara dukanta tana kuka amma bata bashi amsa ba.

"Fahad k'yaleta haka"

"Abba barni in hukuntata tun kafin ta b'atawa gidanmu suna"

"Ka k'yaleta ai ta kusa barin gidan mu huta" Abba ya fad'a.

Da sauri ta tashi ta ruga d'akinta tana kukan k'unci.







_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄




```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```




16

Kulle d'akin tayi da key tasha kukanta ta k'oshi,sannan ta tashi ta nufi toilet tayi alwallah,har zata tada sallah ta tuna wayarta a kashe take,tayi saurin kunnawa da niyyar tana idarwa ta kirawo Aliyu.

Tana tada sallah kuwa wayar ta fara ringing, kafin ta idar an mata missed calls ya kai goma.

Bayan tayi addu'oi ta duba wayar taga duk missed calls d'in Aliyu ne,da sauri ta kirashi,har ta kusa katsewa sannan ya d'aga.

"Assalamu alaikum,Allah ya huci zuciyarka"

Ajiyar zuciya yayi sannan ya amsa sallamar yace "nayi tunanin ko laifi nayi"

"Bakayi laifi ba ni ce nayi maka laifi ina neman afuwa"

"Karki damu ai bakyayin laifi a gurina na yafewa matata" wani dad'ine ya mamaye zuciyarta sai taji har ta manta da abinda Fahad ya mata suka sha waya sosai har yake sanar mata ranar asabar za'a kawo lefe kuma yana son ta rubuta I.v zai shigo skul gobe ya karb'a.

"A'a Aliyu karka damu Mameey ta d'auki nauyin komai"

"A'a abin yayi yawa,d'azu da mukazo ta bani mukullin gidan da zamu zauna can tudun wada yake,sannan ta karb'i account numberta tace zata turomin kud'in da zanyi business d'in da zan rik'e ki,Janan Mameey na sonki sosai kuma Mameey tayi min gata da ban san da kalamin da zan gode mata ba"

Wasu hawayene suka sauka a idonta najin dad'i.
"Karka damu Aliyu ai yiwa kaine"

Haka suka gama hirarsu sukayi sallama cikin kewarshi ta kashe waya.

Labarin da Jalal ya bata ne ya dawo mata a rai.

Ta zauna ta zuba uban tagumi tana tunanin dama akwai azzaluman mata haka a duniya,tausayi ne ya rufeta gaskiya akwai babbar sakayya a lahira.

********

*12:30pm*

Kamar a mafarki taji ana ta knocking k'ofarta.

A hankali ta bud'e ido ta kalli agogo,hamma tayi tare da salati sannan ta sakko a hankali zuwa bakin k'ofar.

"Waye"
"Ni ce"
Jin muryar ne ya saka tayi saurin bud'e k'ofar ta kalleta.

Rungume juna suke cike da murna sai kuma fauziyya ta fara kuka.

Zama sukayi suna ta maganganu akan matsalar gidan nasu, anan Janan ta fad'a mata maganar aurensu da Aliyu.

Tayi mata murna sosai dan ji take dama itace dan matsalolin gidan ta fara gajiya dasu.

A haka suka tsara komai na game da shirin bikin.

"Zan fita skul karfe 2 fa"

"Ki shirya na rakaki saboda na dade ban fita ba,daga can sai mu wuce muyi shopping ko?"

"Okay ba damuwa bara na shiga wanka"

"Nima bara na shirya ko"

"Okay"

**********

Fauziyya taji dad'in yadda taga Janan na mayar da hankali sosai a karatun ta,yadda take yawan amsa tambaya a lecture hall.

Bayan sun fito Raihan tace "Janan mu zagaya da Yaya Fauzah taga skul d'in"

"To" ta amsa

"Ke ni baki bani labarin yarima ba naje har gida jiya fa baki dawo ba"

Hmmmm "ke dai bari kawai"

"Ban labarin yadda kukayi dashi jiya?"

Ganin bayan shi tayi daga can nesa a zaune kan kujera.
Jikinta kawai ya bata cewar shine.

Da sauri ta k'arasa ta barsu Fauzah da Raihan anan.

Tana isa taga shine kuwa "jalal"
Da sauri ya d'ago kai da alama yana cike da damuwa a lokacin.

"Ah ah Janan kin shigo kenan"

"Eh ya kake?"

"Lafiya lau"

Sai a lokacin su Fauzah suka k'araso cike da mamaki Raihan ke kallon Janan bakinta d'auke da tambayoyi da yawa,Fauzah na kallonsa a tsorace tace "Salman dama kana raye?"

"Salman kuma" Janan ta fad'a tana kallon Fauzah

"To waye?"

"Sunanshi Jalal"

"Wallahi yana kama da Salman sosai nayi tunanin shine ma"

Kallonshi Janan tayi sosai sai a lokacin taga yayi mata kama da Salman sai dai shi Salman ruwan tarwad'a ne (chocolate color) Jalal kuwa fari ne sol.

Hawaye ne suka sauka a idonta shima cikin mamaki yake fad'in "Waye Salman?"

Da gudu ta juya ta bar gurin,Fauzah nata kiranta amma tak'i ko juyowa,Raihan haka ta bita kamar mahaukaciya da taga gudun Janan ba mai k'arewa bane sai kawai ta dawo a rikice.

"Dan Allah mu bita a mota nifa ina ganin Janan ta fita a hayyacinta"

"Wlh banzo da motana ba kawomu akayi"

"Muje a mota na" Yarima ya fad'a cikin sauri suka wuce.

Parking space na gurin suka k'arasa da shida Fauziyya suka shiga gaba Raihan na baya.

A bakin main gate da suka tambayi securities d'in da wanda ke gurin akace an ganta ta hau napep a gigice anyi tunanin ma ko wani abu ya faru da ita.

"Mu tafi gidan" Fauzah ta fad'a a kid'ime.

Baita ta kalla tace "Janan ta dawo kuwa?"

"Eh"

"Okay a bud'e gate ina masu gadin?"da kanta ta danna horn suka bud'e ya shiga da gudu.

Fauzah da Raihan suka shiga ciki suna rige rige.

A Babban falo suka tarar da ita a kwance tamkar gawa,idonta a bud'e amma hawaye na zuba ta gefe,ba ta ko motsa idon dan ta tsayar dashi cak a kan cilin kanta na bisa cinyar Mameey.

"meya sameta ne?a waje ta fad'i sai zuwa aka yi aka shigo ta ita"

Fauzah ta zauna kusa da Mameey ta dafa Janan tace "Mameey daga naga wani mai kamar Salman shikenan ta rikice kuma already ta sanshi fa dan ita taje gurinshi"

Da sauri Janan ta tashi zaune idonta sharkaf da hawaye tace "wallahi shine, Salman d'ina ne"

"Janan kin haukace ne ko kin tab'a ganin wanda ya mutu ya dawo?" Mameey ta fad'a tana jijjiga ta.

"Mameey wannan fa sunanshi yarima" Raihan ta fad'a

"Waye shi?"

"A skul d'inmu yake tare muka zo dashi nan gidan ma yana waje"

"Wallahi Salman d'ina ne Allah ya dawo min dashi"

Da sauri take k'ok'arin fita,Mameey ta rik'eta.






*kuyi hak'uri masoyana wallahi kwana biyu ne na zama busy babu time d'in typing.Da masoya littafin _A dalilin so_ duk kuyi hak'uri,ku dai yi manage da wannan.*









_Sadeey S Adam_✍
[9/29, 8:15 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*


Please Login or Register in order to submit comment