You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wanda duk hayarsu yayi akan dubu d'ari-d'ari.

Bayan an d'aura Aure ya tafi gidansu Amal d'in,anyi hotuna sosai itama ta sha shaddarta dark blue kamar tashi sunyi kyau sosai.

Duk da bata da lafiya amma ta daure ta fito anyi komai.

Sun keb'e yake sanar da ita bazai samu damar a tafi dashi U.S ba inda za'a mata magani saboda zasu tafi Egypt kai Adnan.

Abbu ta fad'awa suka masa fatan samun sauk'i na d'an uwanshi,sannan suka sanar dashi babu komai idan ya warke itama lokacin ta dawo sai ayi biki.

Sai bayan la'asar ya bar gidan su Amal yayi mata alk'awarin zai dawo da dare saboda friends d'in ta sunce suna son ganinsa.


Tana zaune a d'akin ita kad'ai tayi tagumi yayi sallama ya shiga.

Ciki-ciki ta amsa sallamar.

" ya jikin Adnan d'in?ina Mommy? "

Banza tayi dashi kamar ma bata san dashi a d'akin ba.

"Magana fa nake miki kin yi min shiru Janan"

Nan ma bata ce komai ba,tsam ta tashi ta fita ta bar d'akin.

Zama yayi kan kujerar da ta tashi yana mamakin yadda tayi ignoring d'insa.

Mommy ce ta shigo tana masa kallon mamaki tace "ka fito kamar wani Ango"

Murmushi yayi yace "bikin wannan abokin nawa Saif da nake fad'a miki to yau aka yi d'aurin Aure"

"Shine kuma ko ka gayyacemu?"

"To ai naga babu lafiya nima dole ce tasa naje"

"Daddy....." Abba k'arami ya fad'a tare da rungumeshi.

"Ya kake? Yanzu baka samun damar wasa ko tatsuniyar Mommy ko"

Kai ya d'aga alamar eh.

"Daddy ka sayo min chocolate"

"Ka jishi ko d'azu fa aka sayo masa ya shanyeta yanzu ma rigima yayi wai sai mun fita waje shine muka fita"

"Ai kuwa ga hak'oran sun fara yin bak'i alamun shan zak'i ai idan wannan suka fita wasu suka fito bazan yarda kana yawan shan zak'i ba kar hak'oranka su lalace"

"Daddy meya samu Ammi?" Abba k'arami ya sake tambaya.

"Yawwa Mommy wai me aka yi mata ne nima fa dana shiga k'in kulani tayi inata magana ni kad'ai"

"Wallahi nima na rasa gane kanta tun safe"

"Bara na fita na sameta"

"Yawwa maybe kai ta fad'a maka meke damunta.

A can bayan Amenity d'in ya hangota zaune tana kallon guri d'aya.

Yana zuwa ya tsaya gabanta tayi sauri ta tashi zata bar gurin yace " meye haka Janan?koma mena miki laifinki ne hankalina ya tashi kuma kinsan abinda zanyi ba haramun bane amma kika kicincine"

Tsoki taja ba tare data kalleshi ba bare ya samu damar ta bashi amsa.

"Tsoki kika min Janan"

A harzuk'e ta kalleshi tace "nayi tsokin meye na biyoni nan ina ruwanka da shiga sabgata kada ka kuma shiga ba ruwanka da lamurana ina zuciyar taka ko karen ya lasheta"

"Ban sani ba amma zaki iya zuwa ki tambaya"

"Wa zan tambaya?"

Tab'e baki yayi sannan yace "wanda kike kallo a matsayin kare"

Hannu ta d'aga zata mareshi sai kuma ta tsaya.
Nunashi da yatsa tayi tace "babu ruwanka dani,wallahi sa'arka d'aya ka girmeni kuma ina ganin girmanka amma da sai na sauke yatsuna a fuskarka"

Dariya sosai yayi yace "kin cini wasa fa,lallai yarinyar nan to da wane tsayi zaki mareni dubeki fa kamar sandar suluka,kinga malama ni dai ki daina had'e mun fuska bana so"

Mtsww "aikin banza" ta fad'a tare da wuce wa ciki.

Binta yayi da ido gace "ai dole ma in k'i zama da matata a gidan Mommy saboda kin koya zafin zuciya karki rik'a juye mana shi"

Da dare kamar yadda yayi alk'awari yaje gidansu Amal bayan yayi wanka ya saka k'ananun kaya, a babban falon bak'i aka musu masauk'i shida ita da friends nata da Saif daya rakoshi aka yi ta hira,friends d'in ta sukayi ta ce mata 'yar baiwa dan tayi dace da kamilin miji".

Kusan k'arfe goma ya ankare ya nufi asibiti.

Yana tura k'ofar idonshi yakai kan hotonsa da Amal na yau yana yawo kan screen d'in wayar Janan daga gani turo mata aka yi ko kuma an d'ora a social media ta gani.

'Dago kai tayi ta kalleshi sannan ta kashe hasken wayar ta kauda kai.

"Mommy tace idan kazo sun tafi saboda Abba k'arami ya dameta su tafi"

Bakinsa ya kasa cewa komai zama yayi kusan minti uku sannan yace "ina son magana dake Janan"

Ko kallonshi batayi ba.

"Ko bazaki kalleni ba dan Allah ki saurareni"

Nan ma shirun tayi.

"Dan Allah kar Mommy taji zancen nayi au............" Tayi saurin tarar numfashinsa da fad'in "abu na 'yan uwa ni cikon benci ina ruwana,Jalal idan kaga dama ka Aure duk matan garinnan bai shafe ni ba"

"Kiyi hak'uri ko ranarma wlh raina ne a b'ace"

Banza tayi ta rabu dashi yayi ta rok'onta har ya tashi ya tafi bata sake cewa komai ba.

Bin k'ofar tayi da harara bayan ya fita tamkar tana kallonta.





_ba yawa dai😊😊_





_Sadeey S Adam✍_
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁


_by SaNaz deeyahπŸ‘„_



```Dedicated 2 Miss Xerks & Safnah luv```


_Assalamu Alaikum masoyana makarantana ina mai baku hak'uri jinkiri da nayi wajen posting wannan novel d'in,hakan ya samo asaline ga 'yan gyare-gyare da nayi da kuma 'yan bincike akan abinda ya dace na saka a ciki_


_Pls kuyi min afuwa,ku 'kaddara Amal tayi istibura'i kamin ayi aurensu da Jalal kuma still anyi abin ba tare da sanin Mommy ko wani dangi nashi sannan Amal an tafi da ita india while su kuma sun taho Egypt da Adnan, 1 mnth da zuwansu Egypt._

_TASKAR SANAZ saboda ku na canzawa labarin akala dan na san bazaku wani ji dad'insa ba in har ban canza daga yadda nace ba._



55

Tana zaune a d'akin daya kasance natane tun zuwansu Egypt.
Ta lank'washe k'afarta bisa gado ta zurfafa a cikin tunani.

Har ya turo k'ofar ya shigo bata sani ba,ya tsaya a kanta kusan minti d'aya yana nazari kan wane tunani take haka.

Murmushi yayi sannan ya tafa hannunsa,tayi saurin d'ago kai ta kalleshi sannan taja tsiki tare da jan gyale ta rufe jikinta.

Ransa a b'ace yace "kin san babu abinda na tsana a duniya sama da tsoki?"

Wani tsokin ta sake sannan tace "idan ka tsani haka sai kayi nesa dashi mana"

"Kamar ya kenan?"

"Ina nufin ka daina min magana ka fita a harkata ni ba danginka bace babu wata dangantaka data had'amu ni matar yayanka ce ba taka ba dan haka lokaci yayi da zaka dawo da tunaninka Jalal"

"Kin san kuwa me kike fad'a Janan"

Mugun kallo ta masa cikin b'acin rai ta sake fad'in "amma kasan ai ba'a tab'a min gwajin k'wak'walwa ba ko"

Hannunsa ya dunk'ule ya d'ora a fuska tare da furzar da iska mai zafi,ji yayi kamar ana soya zuciyarsa.

"Yau ni kike bud'e baki kike fad'awa duk abinda kika ga dama?"

"Na fad'a,dan Allah Jalal ka fita a rayuwata ina dalili meke damunka?menayi maka?ka barni inji da abinda ke damuna mana"

Juyar da kai yayi cikin b'acin rai.

Ajiyar zuciya yayi yace "shikenan insha Allah zan nisanta dake zan fita a rayuwarki kamar yadda kika buk'ata,amma ki sani ina miki komai saboda Adnan da kuma Mameey domin na d'auketa tamkar Mommyna bayan nan babu wani abu a zuciyata"

Juyawa yayi ya fita da sauri,tabi k'ofar da ido tanajin wani zafi a zuciyarta.

A tsaye ya tarar da Mommy yayi saurin k'arasawa gabanta
"Mommy......." Hawayen da suka zubo daga idonsa ne yasa ya kasa cewa komai.

"Jalal kayi hak'uri" shine abinda ta fad'a cike da tausayinsa dan ta san tabbas abinda ya sashi kuka ba k'arami bane musamman da taga ya fito daga b/room d'in Janan.

Hannu tasa tana goge masa hawayen a daidai lokacin Janan ta fito.

Turus tayi ta tsaya zuciyarta cike da tsoro da fargaba.

Ganin ta fito ne yasa Jalal saurin fita daga falon.

Saddad da kai tayi k'asa idonta a soye yake ta kasa yin kuka sai na zuci.

Mommy ta tako har inda take ta dafa kafad'arta tace "ki sawa zuciyarki salama,ki cire damuwa a ranki"

Ba tace komai ba har Mommy ta janye hannunta a kafad'arta sannan ta koma ciki da gudu.

Kan gado ta fad'a ta fashe da matsanancin kuka.
"Wayyo Allah na na shiga uku Allah ka d'ora min wannan ciwo na paralysis nima in zama kamar mijina dan in daina sanin abubuwan da suke faruwa a duniya ma,Aliyu ka cuceni tunda na aureka har yau na kasa samun zaman lafiya wannan wace irin rayuwace ne".


************

Gyara zama tayi tace "amma meyasa bazaka fad'a min ba?"

"Mommy kiyi hak'uri wallahi bana son ki hanani komawa 9ja"

"Ka fad'a min meye had'aka da Janan?"

Murmushin k'arfin hali yayi yace "kai Mommy me kika gani?ni kam me zai had'a ni da ita"

"Kuna b'oye min abinda dole wata rana in sani,na lura gaba d'aya satinnan baku magana kwata-kwata itama na tambayeta tace babu komai"

"Babu komai Mommy da da akwai ko ban fad'a ba ita zata fad'a ai"

"Amma da can bakace zakaje 9ja sai yanzu"

"Am sorry Mommy bazan dad'e zan dawo an kirani a office kuma dole naje amma bazan wuce 5wks ba insha Allahu"

"Shikenan Allah yasa,karka manta kana sauka ka kiramu"

"Insha Allah zan biya in duba Adnan kamun in wuce (asibitin ba'a zaman jinya su sukeyi da Kansu,sai dai kaje kaga patient d'inka shima na Adnan basu fiya shiga ciki ba sai dai ta glass su hango shi wani lokacin kuma ana bari a shiga)".

Haka yayi mata sallama ya tafi Janan bata ma san anayi ba.

Kwana biyu shiru bata ganshi ba ko zasuje asibiti babu shi shiyasa ta yanke shawarar tambayar Mommy inda yake.

Ta kuwa shaida mata ya koma 9ja an kirashi a office,duk sai Janan taji babu dad'i dan ta zargi kanta sosai.

_A month later_

Tun bayan tafiyar Jalal bai sake nemanta ba duk da ta san yana waya da Mommy dan wata rana ma a gabanta zai kira amma bai tab'a kiranta ba,tana kiransa Sam baya picking daga baya ma kullum ta kira sai taga number busy hakan ya tabbatar mata da cewa yayi blocking d'in ta dan haka ta goge number sa a wayarta ranta duk babu dad'i.

Haka aka cigaba da jinyar Adnan jikinsa da sauk'i sosai yanzu har bud'e ido yake kuma yana gane mutane sai dai bakinsa har yanzu baya magana.

Wata ranar Alhamis sun dawo daga asibiti ta shiga d'akin ta kira Yaya Fahad suna waya Mommy ta shigo cikin fara'a,da sauri Janan kuwa ta katse wayar.

"Albishirinki"

"Goro" ta fad'a tana murmushi itama.

"Amma fa goron Fari Sol nake so"

"Angama Mommy" ta fad'a

"Adnan ya fara magana kuma side d'in damansa yana motsawa"

Ai tun kafin ta gama fad'a Janan ta mik'e tsaye cikin farin ciki ta rungume Mommy .

"Alhamdulillah Allah na gode ma",ta fad'a tana hawayen murna.

" ki shirya muje dan yanzu suka yi min waya yana son ganin mu"

Cikin murna ta fad'a toilet lokacin Mommy ta fita,cikin saurin ta gama shirinta ta kalli agogo lokacin ya buga k'arfe 12am.

Fitowa tayi ta samu Mommy a falo suka fita,suka shiga taxi zuwa asibitin.

Gown ta atamfa ce a jikinta amma har hard'eta take saboda sauri.

Har d'akin aka jagorancesu.

Yana kwance idonsa na kallon k'ofar shima shigowarsu kawai yake jira.

Murmushi yayi lokakacin da suka shiga.

Da sauri ta rik'o hannunsa tare da d'ora kanta akan k'irjinsa ta fashe da kuka.

"Janan" ya kira sunanta a hankali tare da runtse idonsa shima hawayenne suka zubo masa.

Mommy ce ta shigo d'akin da sauri ta k'arasa jikin gadon tare da shafa kansa.

Janan ta d'ago kai tana goge hawayen ta.

Cikin dubara suka tadashi zaune tare da jinginar dashi.

Hira suka yi sosai bakinsa ya d'an karkace amma still yana d'an yin magana.

Mommy tashi tayi ta tafi gida dan ta barsu su yi hira cikin sakewa.

Kan gadon Janan ta hau ta k'ura masa ido shima kuwa ya kafeta da nashi idon,kusan minti biyu babu wanda ya janye idonsa daga kallon da sukewa junansu,lumshe ido tayi tare da d'aga hannayenta sama tace "Allah nagode maka daka bawa mijina lafiya,ya Allah ka k'ara masa lafiya"

"Ameen matata" ya fad'a yana murmushi,itama murmushin take mai had'e da hawaye.

"Ina Jalal?"

"Ya koma Nigeria amma Mommy har ta kira ta fad'a masa tun kafin mu k'araso nan"

"Allah sarki bros Allah ya saka masa da alkhairi"

"Ameen"

Shiru ya d'an biyo baya sannan yace "Janan bakya jin bacci?"

Murmushi tayi ta sauke k'wayar idonta tace "ai ji nake kamar ba'a tab'a halittar bacci a idanuna ba farin ciki nake yau Adnan d'ina Salman d'in Iya ya tashi har yana magana"

Hmmm "Allah sarki Iya Allah yayi mata rahama"

"Ameen"

"Kina ziyartar Aliyu kuwa?"

Ta d'an b'ata rai tace "ni kam ina ruwana da wani Aliyu, rabona dashi tun ranar da mukaje tare da kai"

"Meyasa?"

Kallon mamaki tayi masa sannan tace "babu wata alak'a tsakanina dashi kud'in gidansu an kai masa sannan Yaya Fahad ya bashi shawarar yaja jari dashi kaga kuwa babu sauran abinda ya rage tsakanina da Aliyu"

"Akwai"
Ta d'an zare ido sannan ta girgiza kai tace "babu komai tsakanina dashi pls ka bar yi min maganarsa"

"Dole nayi maganarsa saboda akwai sauran abu biyu ko uku tsakaninku"

Shiru tayi ta dafe goshinta da hannunta.

Shi kuma ya cigaba da fad'in "Abba k'arami shine abu na farko sannan na biyu Janan dan Allah ki yafe musu kodan darajar wad'anda suka rasu Umma da Ummi kenan"

Hawaye ne suka sauka a idonta ta kalleshi tace "Abba kuma daya rasa ransa a dalilinsu,haba Adnan"

"Janan dole ki zama mai yafiya saboda ko wane d'an Adam yana da zunubi kema idan kika yafe za'a yafe miki,ki rage kafiya da taurin kai dan Allah idan kun koma Nigeria ki furtawa Aliyu kin yafe masa kinji"

Kuka sosai take tak'i ce masa komai ma.

"Janan" ya sake kiran sunanta.
Bata amsa ba bata kuma d'ago kai ta kalleshi ba.

"Kina sona?" Da sauri ta kalleshi ta d'aga kai tare da fashewa da wani sabon kukan.

"To kiyi shiru kiji abinda zan sanar miki dan Allah"

Hawayen ta fara gogewa tana sheshshek'ar kuka.

"In har kina sona to bazan sake furta miki cewar ki yafewa su Aliyu ba ko dan Ummi dana d'aukarwa alk'awarin zan nemar mata yafiya a gurinki idan baki yafe mata ba da wane ido zan kalleta a lahira?na karya alk'awari kuma kin san Allah zai hukuntani akan hakan?to in kina sona zaki yafe musu"

"Shikenan na yafe musu"

"Naji dad'in hakan,kuma ki furta hakan a gaban Aliyu kuma kina kai masa d'ansa yana gani akai akai pls"

"To"

"Sannan....." Sai kuma yayi shiru

"Meya faru?"

"Bana son hankalinki ya tashi"

Ajiyar zuciya tayi sannan tace "ka fad'a min pls"

"Tausayinki nake Janan"

"Tausayina kuma a na me?"

"Kin aikata kuskure Janan dan Allah na rok'ek'i karki kuma"

"Ka sakani a duhu na kasa gane me kake nufi wane kuskure na aikata"

"Cutar HIV da kika sakawa kanki Janan kin saka ne saboda ni gashi ba zaki rayu dani ba"

A d'an tsorace ta kalleshi tare da fad'in "ban gane me kake nufi ba,meyasa zaka rik'a yin wannan furucin"

Hawaye ya zubo a idonta ta saka hannu tana sharewa shima ya d'aga hannunsa mai aikin ya janye nata yana fad'in "bazan kuma cewa haka ba kiyi huk'uri kinji"

Kai ta d'aga alamar to.

"Meyasa Jalal ya koma 9ja"

"Aiki aka kirasa a office"

"Idan yazo kice masa ya yafe min kuma ina gaidashi sosai"

"Meyasa kake magana kamar wanda yake bada wasiyya kana karya min zuciya"

Murmushi yayi yace "kin san me?"

Kallon shi kawai take ba tare da tace komai ba.

"Soyayyar mu na tuna tun lokacin Iya" ya fad'a dan ya kaucar da waccan maganar.

Dariya sosai tayi tace "kaji ka ko"

"Eh mana ina jin kamar na dawo da baya"

"A'a..." Tayi saurin fad'a tare da cewa "ni kuma inajin kamar na janyo future,na k'agu ka warke mu koma gida mu k'ara gina soyayyarmu cikin aminci da yarda juna ina sonka sosai so mara misaltuwa"

"Nima ina matuk'ar k'aunar ki wanda na san ko kwatansa baki min"

"Wallahi zan iya bada rai na dan kai ka rayu bazan tab'a iya musulta son da nake maka ba"

"Allah ya had'ani dake a gidan aljannah"

"Amin mijina"

Da likitoci sukazo dubashi ta fita,sunfi awa sannan suka fito,tana ganin fitarsu ta koma.

Ganin idonshi tayi a rufe ta k'arasa kan kujera ta zauna.

"Allah ya baka lafiya"
"Ameen" taji ya amsa.

"Oh nayi tunanin bacci kake"

"Sun yi min allurar da duk ta kashe min jiki, zafi nake ji a cikin k'asusuwana,Janan anya ba allurar mutuwa suka min ba"

"Dama akwai allurar mutuwa?"

Shiru yayi yana cije leb'e
"Bara na kira su"
"A'a karki damu fad'i kawai nake bana jin komai fa"
"Ban yarda ba"

Da saurinta ta tashi ta fita tayi musu bayani aikuwa suka hau ta da masifa ta tashi ta dawo ta zauna kusa dashi tare da rik'o hannunsa ta sumbata.

Bud'e ido yayi ya kalleta tayi masa murmushi tare da cewa "ya jikin".

"Naji sauk'i kuma jikin ya fara saki"

"Sannu"


Kai ya d'aga ita kuwa ta kwanta kan k'irjinsa tace "kasan me?"

"Sai kin fad'a"
"Gaskiya za'a sallamemu sai a cigaba da treating d'inka a gida"

"Nima nafi son haka na gani da zaman asibiti"

"Amma idan ka warke zamuje honey moon ko?"

"Eh ai dole ma da yardar Allah zamuje k'asashe uku"

"Zaka zab'a mana"

"Na baki zab'in"

"To Spanish zamu fara zuwa"

"Saboda Lubna ko"

"Ni dai bance ba kawai nafi son muje can"

"Kedai ki fad'i gaskiya"

"To shikenan na baka zab'i"

Dariya yayi,haka suka cigaba da hirarsu har bacci ya kwasheta.

Har gari ya waye bata san meke faruwa ba.

A hankali ta bud'e ido lokacin da taga likitoci birjik a kanta.
Rik'e hannunta da taji anyi ne ya saka ta bude ido.


"Ya aka yi kina bacci baki san ya mutu ba baki kuma kirawo mu ba"
A tsorace ta kalli Adnan wadda alamu ya nuna mata cewa bacci yake,ta sake kallon likitan tare da cewa "ban gane ba gashinan bacci yake"

Hannunsa ta rik'e ta jishi a sake,ta kama tsintsiyar hannunsa taji bata aiki.

Idanunta tuni sun kad'e sunyi jajir.

"Ke kika kashe mijinki saboda bama yarda a zauna amma har kika kwana anan bayan bama so ayi masa hayaniya"

"Wallahi k'arya kuke kun kashe min mijina dama allurar mutuwa kuka masa da gaske, bazan yarda ba sai nayi shari'a daku"

A daidai lokacin Mommy ta shigo cikin kuka ta rungume gawar Adnan.

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un dan Allah kar kayi min haka Adnan, Adnan ka tashi dan Allah"

Kuka sosai take lokacin da Mommy ta kama hannunsu tana tofa addu'a sannan ta raba ta dashi a hankali.

Anan janan ta sulale tana kuka.

Fitar da akace suyi ne tana tashi ta kafawa gawar Adnan ido har lokacin bata gaskata mutuwar tashi ba.

'Kirjinta ta dafe ta sulalewa a gurin ko motsi bata kuma ba.

***********



_Sadeey S Adam_✍🏻
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyahπŸ‘„*_



```Dedicated 2 Miss Xerks & Safnah luv```


_Makaranta littafin NAGA RAYUWA dan Allah kuyi min afuwa zakuji shiru babu posting, so akwai dalilin dayasa zan dan tsaya da posting dan haka ayi min afuwa._


56

***********

"Mommy taya zan samu visa a yau nazo Egypt" ya fad'a cikin kuka shima

'Kara manna wayar tayi a kunnenta muryarta a dashe tace "haba Jalal muma ai ba zama zamuyi ba,nan da kwana d'aya ko biyu zamu taho da gawarshi anan za'ayi masa sutura,ka dai sanar da 'yan uwa da abokan arzik'i"

"Innalillahi wa inna'ilaihi raji'un yanzu shikenan na rasa shi dagaske Adnan baya numfashi"

Katse wayar tayi dan karya k'ara karya mata zuciya,a lokacin kuma Janan ta farka daga dogon summan da tayi.

"Wayyo Allah na shiga uku meyasa Adnan zai mutu a lokacin da nake buk'atar mu rayu tare,ina zansa rayuwata ya zanyi"

Runtse ido kawai Mommy tayi dan ita kanta tana jin mutuwar Adnan sosai.

Da sauri Janan ta tashi zata fita Mommy ta rik'ota "ina zaki Janan?"

"Mommy zanje gurin Adnan wallahi ban gaskata ba"

"Wanda ya mutu bazai tab'a dawowa ba,Janan kiyi masa addu'a"

'Dora hannu tayi aka ta k'walla k'ara,Mommy ta rik'eta sosai lokacin ta k'ara birkicewa tana fizgewa.

Ranar haka ta zama tamkar mahaukaciya,har susucewa ta rik'ayi kuka sosai take kamar zata amayar da zuciyarta.

Ranar kuwa Mommy tayi receiving calls da messages da yawa anata mata ta'aziyya.

'Yan gidansu kuwa da suka kira Mommy bata fad'a musu halin da Janan ke ciki ba.

Jalal kuwa duk bayan awa sai ya sake kiran Mommy dan har yanzu bai gaskata rasuwar Adnan ba.

***********

"Momma wallahi ji nake kamar nayiwa Janan kuka,yarinyar nan taga jarrabar rayuwa"

"Wallahi Yaya nima tausayi take bani,gashi a sanadin matsalolin rayuwar nan har idanunta fa sun juye,tabo na har abada" Zainab ta fad'a itama tana kallon Muhasin.

"Mijinta na farko shiya fara ruguza rayuwarta"

"Inji wa?" Sai lokacin Momma tayi magana.

"Momma hakane ai dan shine........"
"Ya isa haka kema har dake Humaira,ku k'addara kawai wannan itace k'addararta Allah ya kub'utar da ita da shiga wata matsalar shi kuma Allah yajik'ansa"

"Ameen" duk suka amsa.

"Yaushe zamuje Abuja?"

"Sai sun dawo Jalal yace zai kiramu"

"Allah sarki Adnan Allah ya masa rahama" Muhasin ya fad'a,duk suka amsa da Ameen.

***********

Yawo yake kawai a tsakiyar d'akinsa idanunsa gaba d'aya sunyi jajir.

Saif dake zaune gefen gado ya taso tare da dafa kafad'arsa.
"Jalal kayi addu'a mana"

Kallon shi yayi da idanunsa da suka gama komawa jajaye yace "ina yi amma na san bazaka tab'a fahimtar irin tarin damuwar dake damuna har na rasa wane tunanin zanyi,wallahi Saif har yanzu na kasa gaskata cewa Adnan ya mutu gani nake kamar mafarkin nake wanda har yanzu ban farka ba"

"Ba mafarki bane,mutuwa ai gaskiya ce kai kanka ka sani ina so ka nutsu kayi masa addu'a domin wanda ya mutu ya mutu baya tab'a dawowa.

Da bango ya jingina ya d'aga kanshi sama yace " Allah sarki Adnan Ashe duk ciwon nan da kake bazaka tab'a tashi ba,Allah ubangiji yasa mutuwa ta zama hutu a gareka ya yafe maka dukkanin kura-kurenka"

"Ameen"

_2 days later_

Ya dad'e a airport yana nan zaune su Saif sukazo tare da wasu friends d'in nashi.

Ana gaf da jirgin zai sauka sai ga wasu daga cikin danginsu manyan iyaye.

Aikuwa jirgin na sauka akayi cincirindo gurinsu,duk Kansu maza ne shiyasa ba'ayi 'yan koke-koke ba,Jalal kuwa Mommy ya rungume yana hawaye,itama da ka ganta ka san tasha kuka ta k'oshi.

Kuka da sukaji yana fitowa ne duk yasa suka juya suna kallonta a daidai lokacin da aka fito da gawar Adnan lullub'e da likkafani.

Fahad data hango yasa ta k'arasa gurinsa da gudu ta rungume ta fashe da wani kukan.

Babu wanda bai tausaya mata a gurin ba.

Fuskarta ta haye sosai da k'yar kake gane Janan ce,idanunta babu alamar farar k'waya dan ta zama jajir.

Jikinta gaba d'aya yayi jajir idanunta sun shige sun k'ara juyewa Sosai fatun idon sun kumbura suntum.

"Janan ya isa haka kiyi masa addu'a ita yake buk'ata a yanzu"

Bayan kukan nan babu abinda yake iya fita daga fuskarta bakinta ya kasa furta ko kalma d'aya.

Suna shiga gida aka fara 'yan koke-koke 'yan uwa da abokan arzik'i.

Janan kuwa na ganin Mameey ta bud'e wani shafin kukan,Fauziyya ma kukan take sosai,Abba k'arami yazo gabanta yana jijjigata ganin bama ta kallesa ba yasa shi fashewa da kuka.

"Janan dan Allah kiyiwa mijinki addu'a ba kuka ba"

"Rayuwata ta gama lalacewa babu wanda zai kuma sona Mameey bazan iya rayuwa babu Adnan ba nima mutuwa zanyi"

"Innalillahi wa inna'ilaihi raji'un,Janan dan Allah kiyi shiru kinji kiyiwa Adnan addu'a"

"Na shiga uku" ta fad'a cikin matsanancin kuka.


An gama k'ara shirya shi akace a kira mahaifiyarsa da matarsa su sake yi masa addu'a.

Dukkansu lokacin da suka zauna gaban gawar kuka suke Janan na na fili Mommy na na zuci.

Addu'o'i sosai suka masa sannan aka d'auki gawar za'a fita da ita Janan tayi saurin rik'e makarar "dan Allah ka tashi ka tashi kada a binne ka da rai Adnan dan Allah ka tashi ni na san suma kayi ba mutuwa ba"

Kuka take ana janyeta tana cewa ita bata yarda Adnan d'inta ya rasu ba.

_2days later_

Tana kwance kan ciyar Mameey tana hawaye wanda hakan ya zamar mata jiki.

'Yammata biyu ne sukayi sallama suka shigo.

Gaisawa sukayi tare da yi musu gaisuwa.

Shiru suka d'anyi sannan suka ce "Janan d'in bata nan ne?"

"Ga tanan kwance Janan tashi bak'inki ne"

Idanunta da suka gama rinewa ta d'ago tana kallon su.

Yarinyar ta k'urawa ido dan bazata mance kamanninta ba.

"Ya hak'uri"
"Alhmdlh"
"Allah yajik'ansa ya masa rahama,nima sai jiya Jalal ya fada min,Ummu na muku gaisuwa Abbu ma yace ayi muku ta'aziyya yana can farfajiyar gidan"

"Mungode Allah ya bada lada" ta fad'a lokacin da wasu hawayen suka sauka a idanunta.

Kusan awarsu guda sannan suka fita.

Babu jimawa sai ga Raihan,da kuka ta shigo d'akin ta rungume Janan.

Kuka suka cigaba dayi Raihan na fad'in "Janan ki yafeni ban san Adnan yayi jinya ba sai jiya naji rasuwar a radio,dan Allah kiyi hak'uri Allah ya masa rahama yasa mutuwa ta zamo hutu a gagareshi"

Kuka kawai Janan take Raihan ma kukan take.

Lubna kuwa bata samu tazo ba da yake sun koma can amma tana ta kira a waya tace tana kan hanya.

_5 days later_

Yau ne sadakar 7 ta Adnan gidan ya cika mak'il da Jama'a kuma har

Please Login or Register in order to submit comment