You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a zuciyarta sannan ta dake tace "kina nufin ke ba mutum bace?"

"K'warai kuwa"

"Amma abinci da ruwan wanka da kayan dake jikina nida jariri na ya akai kika samu?"

"Na saka yarana sun je gidan wani babban mutum anan garin matarshi ma ta haihu yau ake suna shine aka d'akko wannan kayan na jikinki dana jikinsa,tuwo kuwa da kunu da ruwa a gidan wata maijego na d'ebo da kaina"

"Ya sunan mutumin?"

"Ba damuwarki bane kedai kiyi abinda ya dameki"

Cikin dakiya da zafin rai Janan ta nuna ta da yatsa tace "kada ki kuskura ki sake bibiyata,kuma yanzu zan cire kayan in ajje ki mayar inda kika d'akko banaso,sannan gidannan ba naki bane saboda mutum ne ya gina meyasa baza kuje can daji kuyi gininku ku zauna inda ba mutane ba, babu inda aka ce aljani ya rab'i mutum,dan haka bana son taimakonki akaina ko d'aya ki fita a rayuwata idan ba haka ba zan k'ona ki da ayar Allah"

Murmushi tayi tace "yarinya nayi miki ne saboda tausayi"

"Ba'ason taimako kada ki kuma"

Dariya ta b'ab'b'aka tace "kanki ake ji 'yar nan,zan tafi bazaki sake ganina ba dan naga jininmu baizo d'aya ba bazamu had'a hanya dake ba"

"Nafi k'arfinki addu'ata data iyayena tana tasiri a koda yaushe"

Da sauri Janan ta cirewa jaririn kaya,tayi sauri taja nata da aka shanya ta sab'i jaririn ta shiga can ciki ta cire ta maida nata.

Tana fitowa taga babu alamar tsohuwar nan.

Da k'arfi ta furta "ga kayannan na ajje dan bazamu saka kayan da ba mallakinmu ba"

Nad'e jaririn ta tayi a cikin d'ankwalinta ta rumgumeshi tana kuka.

Gaba d'aya a tsorace take dan haka ta tattara komai nata a viva ta tafi ta bar kangon tana tunanin Jarumta irin tata da har takewa aljana tsawa.

Wajen dandazon wasu almajirai ta nufa,dan gani take nan sai yafi mata dad'i.

A nan Allah ya had'a ta da wata mata Asabe wadda ta tausaya mata har tayi mata alk'awarin idan ta warware zata nema mata aiki a gidan da take aiki.

Kulum matar idan taje aiki sai ta ragowa Janan abinci da zata ci saboda shayar da d'anta.

A nan inda suke kwana kangone mai d'aki biyu amma duk an musu rufin langa-langa haka dandazon almajiran nan ke kwana a cinkushe,Janan kuma ta dawo tsakar gida ta rufe jaririn ruf ta kwanta dan ita bata son zafin nan ga wari.

Sam bata fita ko ina dan ita a ganinta bara asara ce ga duk mutumin da bayada wata nakasa.

Ranar da d'anta ya cika kwana bakwai a duniya ta rungume yaron tana kuka tace "nayi maka hud'uba da sunan mahaifina Hashim sannan zan rik'a kiranka da Abba k'arami,dan Allah ina son kayo halin Abbana kaji"

"Haba Jannat ya zaki zo ki rungume yaro kina kuka"

Ta d'ago kai ta kalli matar tace "mama kukan da nake na tausayin yaron ne"

"Karki damu ai Allah yana ji kuma yana kallon halin da kuke ciki"

"Hakane"

"Zan tafi gurin aiki dan Allah ku kula da kanku kinji"

"Insha Allah".


*******

Yau watan Janan biyar a gidan nan kuma Abba k'arami shima watansa biyar a duniya dan har ya fara zama,yaro fari kyakykyawa sak kamannin Janan ya d'ebo hatta rashin k'ibar.

Rayuwa ta fara canza mata,Mama asabe ta fara wulak'anta dayi mata gori.

Da yammacin ranar tana zaune a tsakar gidan tana shayar da Abba k'arami,tunanin data saba kawai take dan bata zama ba tayi ba,ji tayi kawai an watso mata kaya a jiki tayi saurin juyawa dan hatta Abba k'arami sai daya tsorata.

'Dago kai tayi ta kalleta bata ma yi magana ba Asabe tace "ga wanki nan zanje gidan aiki kafin in dawo ki wanke dan bazan rik'a ciyar dake a banza ba"

Fita tayi tana ta 'yan maganganu.

Janan kuwa tashi tayi ta goya d'anta dan ita ma yau fita zatayi neman aiki ta gaji da gori da wulak'anci ga kwana cikin dandazon almajirai.

A k'ofar wani babban store ta tsaya tana tunanin ko ta shiga taji in zata samu koda aikin zubar da datti ne.

Ta shiga cikin farfajiyar store d'in kai tsaye ta nufi inda k'ofar shiga take tana ta tunanin yadda rayuwarta take a baya in sunzo store.

Hawaye ya taho mata amma bai samu damar zubowa ba dan wanda ta gani yana k'ok'arin fitowa daga ciki shine yasa numfashinta ya fara neman d'aukewa.





_*Fans wane wannan?*_
_oyaa naji daga gareku?👂ko zaku canki abinda ke zuciyata._








_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safna luv```


_'Groups ina jindad'in comments d'inku.Nagode da yabo,da kuma k'aunar da kuke nuna min....much luv😍😘_




34

Kallon kallo suka tsaya yi dan shima mamaki yake da ya ganta a wannan yanayi.

Juyawa tayi da sauri da niyyar barin gurin yayi saurin cewa "Janan".

" ka santa ne?" Abbas ya tambayeshi.

"Janan d'ina ce fa"

Gabanta ya cigaba da fad'uwa tana tafiya zani na hard'e ta,yayi saurin shan gabanta.

"Janan ki tsaya"

Cikin dakiya ta kalleshi tace "wacece Janan?Malam ka bani guri in wuce"

"Karki raina min hankali Janan kina son kice bazan iya gane ki bane?"

Wasu zafafan hawaye suka fito daga idonta ta sake juyawa zata tafi ya rik'o hijabinta "karki min haka Janan na san kece"

Fuskarta sharkaf da hawaye tace "ba Janan bace dan Allah karka tara min mutane"

Ta fuzge hijabinta da sauri da sauri ta wuce ta cigaba da tafiya.

Shi kuma kawai yaji zuciyarsa tayi rauni,ya sunkuya jikin motar dake kusa dashi yana hawaye an kai gab'ar da bazai iya rik'esu ba.

"Jalal kuka fa akan waccan k'azamar yarinyar?"

Ya d'ago kansa idanunnan sunyi jajir yace "waccan da kake gani ada bazaka nuna mata komai ba,kaidai kaji tsoron rayuwa kawai abokina"

"To ai naga kana mata magana tana wani zuk'ewa"

"Muyi sauri muje karta b'acewa ganina"

Yayi sauri ya tafi ya bud'e mota zai shiga Abbas yayi saurin cewa,mu had'u a gida kawai danni ban gama siyayya ba"

"Okay ga key"

"A'a zan kira sai a kawomin motana"

"No amshi kawai sai ka taho da kayan duka" yayi sauri saka masa a pocket sannan ya wuce Abbas kuma ya koma ciki.

Yana fita ya hangota a can gefe tana share hawaye.

Da sauri ya k'arasa gurin,tana ganinsa ta k'ara rikicewa tana neman hanyar da zata bi.

Hannunsa biyu ya had'e ya tsaya gabanta yace "dan Allah karki min haka Janan,babu irin neman da ban miki ba lokacin da naji labarinki raina ya b'aci saboda su Raihan basu fad'a min da wuri ba"

Kallonshi tayi har zatayi magana sai kuma ta fasa,gefenshi tabi ta wuce kawai taji ya rik'e hannunta cikin zafin rai ta d'aga d'ayan hannun ta saukeshi a fuskarsa.

"Janan" ya sake furtawa cike da mamaki.

Itama ta tsorata sosai da abinda ta aikata dan ta kasa kauda idon nata akan hannunta.

Ganin mutane sun fara taruwa suna tambayar ko lafiya ya saka ta sakin wani kukan a fili.

Kallon wani mutum tayi tana kuka tace "Malam kayi min tsakani dashi dan Allah tun d'azu yake bina yana cewa ya sanni ni ban san shi ba,kuma ni matar aurece taya zai rik'a bina? akan me?tun da nace ban sanshi ba meyasa bazai k'yakeni ba"

Ai kuwa aka yi kansa caaa ana ta fad'a masa maganganu amma ya kasa cewa komai har lokacin hannunsa na kan kuncinsa.

Ita kanta sai take jin zafin yadda mutane suke aibunta Jalal.

Juyawa tayi da sauri ta tsallaka titi,shi kuma kawai yaji bazai iya bari ta kub'uce masa ba bayan dama nemanta yake.

Da sauri ya bar gurin da niyyar binta,ai kuwa yana hawa titin kafin ya tsallaka motar ta taho kansa ji kake k'iiii.
Mutane duka aka hau salati,jin haka ne yasa tayi saurin juyowa.

Ganin Jalal cikin jini ba k'aramin d'aga mata hankali yayi ba.

Da sauri ta dawo,yayi daidai da fitowar matashiyar budurwar da ta kad'aishi da kuma Abbas.

"Jalal na shiga uku dan Allah karka rasa ranka a dalilina"

Jin haka yasa mutane aka fara zaginta ana binta da muggayen kalamai musamman da aka ga yanayin talauci a tattare da ita.

Abbas kuwa jin abin da ya faru ne yasa ya figi hijabinta dan harya yaga mata amma sai da ya direta a gefen titin.
"Kada ki sake rab'arsa ke ba ajinsa bace sam amma a haka har kike wulak'antashi kina nuna baki sanshi ba"

Kuka sosai take tana ji tana gani aka saka Jalal a motar wannan matar aka tafi,Abbas ma ya shiga mota ya bi bayansu.

Ganin mutane sun dawo kanta ya saka ta saurin barin gurin dan wasu har sun fara dungure mata kai.

Da k'yar ta iya kai kanta gidan da suke zaune,dan ta zama tamkar mahaukaciya tana tafiya tana hawaye.

Tun a tsakar gida ta fara cin karo da b'acin rai.
"To tambad'ad'd'iya daga ina?kin san bazan ciyar dake ba shiyasa kika tafi neman arzik'i da jikinki,to sai dai hakan in ba haka ba wazai d'auke ki aiki dubeki a k'azance haka"

Janan ta kalli mama Asabe sannan ta kalli kanta taga sam babu had'i tsakaninsu duk da tana cikin wahala bata barin kayanta kina yaronta da k'azanta.

Cikin b'acin rai tace "dan Allah ya isa haka,ina ganin girmanki tun da har ban ce zanci abincinki ba ai saiki k'yaleni ki barni inji da abinda yake damuna"

"An k'i a k'yaleki d'in,kuma daga yau ki daina ganin girman nawa kinji,kuma dole in fad'a miki duniyarnan cud'eni in cud'eka ce wanki da kika barmin nayi kayana abinci kuwa kin rasa"

Bata sake tanka mata ba,ta tsince goyon bayanta dan har yayi bacci ta kwantar dashi kan cinyarta zuciyarta a cunkushe da damuwa.

Da yamma kuwa kasa jurewa tayi taje asibiti kusan guda biyar amma bata sameshi ba,haka ta dawo gida da tarin yunwa da gajiya a tartare da ita,bata da ko taro bare ta sayi abu taci haka ranar ta kwana da yunwa da tunani.

*******

A hankali ya bud'e idonsa ya kalli matashiyar budurwar sannan ya kalli Abbas dake d'ayan gefen ya rik'o hannunsa yace "Abbas ina take?karkace min ka barta ta tafi ba tare da na san inda take ba"

Ran Abbas a b'ace yace "Haba Jalal wannan 'yar ficiciyar yarinyar wata k'azama da ita zaka wani damu,babu abinda zata nunawa matarka"

Hawaye suka biyo gefen fuskarshi ya sake furta "baki min adalci ba Janan meyasa zaki min haka?meyasa kika zab'i haka Janan?"

Tsaban b'acin rai Abbas yayi banza ya k'yaleshi.

Najwa ta matso kusa dashi tace "ka sassauta zuciyarka pls,likita yace karka fiya magana"

"Wace wannan?" Ya tambayi Abbas.

"Itace wadda ta kad'eka"

Ya had'e girarshi yace "oh itane tayi min tsakani da Janan,to me take kuma anan?"

"Haba Yarima Kaine fa ka kawo kanka taya zata muku tsakani,karfa k'azamar yarinyar nan ta haukata ka"

Kuka Najwa ta fara tana fad'in "ni ba da gangan na kad'e kaba dan Allah kayi mini kyakykyawan zato.

Dukkansu sai ta basu tausayi Abbas yayi ta rarrashinta.

A rannar mamanta da babanta suka zo suka dubashi.


Daga gidan su Abbas ake kawo masa abinci kuma Abbas shiya cigaba da kula dashi.


_*4 Days later*_

Suna zaune su biyu suna hira,Abbas ya kalleshi yace " Abokina ya kama ta a sanarwa da Mommy ko Adnan ko Raihan amma yaushe har aka sin ce d'orin nan har ka koma gida"

"Baza'a fad'a musu ba Abbas,saboda hankalinsu zai tashi kuma zasu ce a mayar dani asibitin can in cigaba da jinya ni kuma banason barin garin nan ba tare dana ga Janan ba"

"Allah ya sawwak'e"

"Amma ka duba ko ina kuwa?nifa ina tunanin in har ka karad'e garin nan zaka ganta,da ace ban samu gocewar k'ashi a k'afa ba da babu abinda zai hanani nemanta duk ciwon dake jikina"

"Najwa ta kirani a waya da safe" Abbas ya kawar da maganar Janan.

"Okay"

"Kasan me?"

"Sai ka fad'a"

"Ina tunanin yarinyar nan sonka take"

"Wa kenan?"

"Najwa mana ta damu da rashin lafiyarnan taka sosai,har fa a lecture hall ta kirani tana tambayana ya jikinka"

"Ai dole ta damu tun da ita ta kad'eni"

Abbas ya d'anyi tsoki yace "kai ana nuna maka hanya kana kaucewa"

"Hanyar ce batayi min ba abokina"

*******

A gajiya ta juya ta fita daga emergency bayan ta k'asa samunshi a karo na ba adadi.

Ta fidda ran zata ga Jalal,ga kukan Abba k'arami har cikin ranta ta rasa meke damunsa,ga ita kanta ta galabaita dan tun safe take yawan nemanshi a asibiti yafi a k'irga bata samu ba,ga tafiyar k'asa ga tazara tsakani asibiti da asibiti.

Tana fitowa taga Abbas ya fito daga motarsa.

Ta manta sunanshi amma ta gane shi.

Da sauri ta k'arasa gurinsa ta d'an russuna tace "ina yini"

Kallon sama da k'asa yayi mata dan ya ganeta sarai amma sam yak'i nunawa.

"Dan Allah dama........." Bai bari ta k'arasa ba ya mik'a mata dubu d'aya "gashi karki tsaya kina min magiya"

Kallon kud'in tayi sannan ta kalleshi kawai taji hawaye dan a ganinta ya wulak'anta ta.

"Oh tun da kin raina shikenan" ya mayar da kud'in aljihunsa.

Jikinta a sanyaye tace "dama Jalal nake nema,nasha wahala tun safe nake nemansa naje asibiti yafi a k'irga ban sameshi ba"

"Wane Jalal?"

"Wanda na ganku ranar tare dan Allah ka taimaka min"

"Bazan taimaka ba,b'ace min da gani"

"Dan Allah"

"Wallahi zan miki d'an banzan duka a gurin nan nace miki ban san wani Jalal ba kin zo wata k'azama dake kina min magana"

Wuce wa yayi ya shige ciki ita kuwa a gurin ta tsaya tana kuka.

"Yarinya juya in fad'a miki inda yake"

A tsorace ta juya ta kalli dattijuwar tare da saurin matsawa nesa da ita jikinta na kyarma.








_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```




35

"Meya dawo dake kuma?"
Ta fad'a a d'an tsorace.

"Wanda kike nema yana ciki,Amenity room3 cikin main male ward"

Ta bud'e baki zatayi magana taga babu matar.

Jikinta a sanyaye tace "kina son in yarda dake ne saboda in fara tunanin kin san komai,da Allah na dogara ba dake ba"

Jikinta ba k'wari ta cigaba da tafiya cikin asabitin.

Kusan mintinta biyu a tsaye a k'ofar d'akin kafin ta murd'a k'ofar ta shiga.

Yana kwance yana duba waya yaji an turo k'ofar.

Da sauri ya mik'e zaune ganinta a cikin d'akin ba k'aramin mamaki yaji ba.
Farin cikin dake zuciyarshi bazai musaltu ba.

"Janan"
"Jalal" ta kira sunanshi itama,a dai dai lokacin wasu zafafan hawaye suka sauka a kuncinta.

"Ki zauna ga kujera" a hankali ta k'arasa kan kujerar ta zauna tare da fad'in "ya jikinka?"

"Da sauk'i"
Kukan Abba k'arami ya saka ta mik'ewa ta fara jijjigashi.

Jalal kawai kallonta yake cike da tausayi.

Wai 'yar k'arama da ita amma tana wahala da yaro,wani ma sai yace ajiya aka bata.

Mamaki yake yadda gaba d'aya ta canza ta zama 'yar k'auye futuk,ya kalli takalmin k'afarta shima silifas ne green yasha d'inki da bak'in zare.

Wani hawayene ya sauka a fuskarsa ba tare daya shirya ba.

Sauke goyon tayi ta mayar kafad'a tana jijjigashi amma kamar k'ara cewa take yayi kuka.

Duk tabi ta rud'e gashi bata son ta shayar dashi a gaban Jalal kunya take ji,kuma ta san ma ba wani abu zai samu ba tunda itama ba k'oshi tayi ba.

Ganin ta rud'e ne yasa Jalal mik'a hannu ya d'auki yaron yana jijjigashi.

"Ke uban wa ya baki damar shigowa nan?"

Abbas ya fad'a,Najwa ma tsayawa tayi tana k'arewa Janan kallo cike da k'yank'yaninta.

"Zo ki fice" Abbas ya fad'a a tsawace yana nuna mata hanya.

Jikinta gaba d'aya rawa yake tama rasa me zatayi,Jalal kawai tsayawa yayi yana kallonsa cike da mamaki wai a gabansa yake ciwa Janan mutumci bayan ya fad'a masa matsayinta a gurin shi

"Rik'e shi Janan" Jalal d'in ya fad'a yana mik'a mata Abba k'arami da har lokacin yake callara kuka.

"Malama kiyi sauri ki fita ba b'ata lokaci nace ki tsaya yi ba kin damemu da kukan yaro"

Ta karb'i d'anta daga hannun Jalal tana zubda hawaye.

Baice komai ba ya sakko daga kan gadon yana d'angasa k'afa cike da jin zafin ciwo.

"Janan jirani mu tafi"

Juyowa tayi ta kalleshi tace "baka da lafiya Jalal ka zauna dan Allah karka damu dani ni yanzu rayuwata bata da wani amfani"

"Yanzu dan na koreta shine zaka bita Yarima?"

"Eh saboda ka gane muhimmancin ta a wurina"

"Jalal pls ka dawo ka zauna shikenan itama mun yarda ta zauna" Najwa ta fad'a

"Wallahi bazamu zauna ba,abinda kayiwa Janan kawai hannunka mai sanda ne,kana so kace Jalal na gaji da ciyar da kai da kuma biyan kud'in magani shine abinda yasa ka ciwa Janan mutumci"

"Subhanallah! Karka fassara ni baibai Jalal"

"Abbas wallahi bazan zauna ba,zan canza asibiti a cigaba da kula dani"

"Jalal pls kayi hak'uri" Najwa ta sake fad'a

Har zai yi magana sai kuma ya kalli Janan yace "Janan mu tafi"

Ganin Jalal da gaske yake yasa Abbas kiran daddynsa.

Yayi masa bayani daddy yace a bawa Jalal.

Hak'uri daddy ya bashi sannan ya koma ya zauna tare da karb'ar Abba k'arami.

Abbas ya kalli Najwa yace "muje waje mu bar masoya su shak'ata"
Ranshi a b'ace yayi maganar ya fita.

Najwa ta mik'e ta tsaya tana kallonsu itama ran nata ya b'aci ta bi bayan Abbas.

Tana fita Jalal yayi murmushi kawai sannan ya mayar da kallon shi ga Janan da har lokacin kanta a k'asa.

"Ya sunan babyn?" Kanta a k'asa tana murza yatsun hannunta tace "sunan Abba ne amma ina kiranshi da Abba k'arami"

"Ni kuma zan rik'a kiranshi da Prince"

Ta d'anyi murmushi.

"Wai da gaske ke kika haifi yaron nan Janan?"

Tambayar sai tazo mata a bazata gaba d'aya taji nauyin tambayar.

'Dago ido tayi ta kalli Abba k'arami sannan ta kalli Jalal ta d'aga kai kawai.

"Yaushe kika haifeshi?a ina?meyasa kuka bar Kaduna?ina su Mameey?taya ya idanunki suka juye haka?"

Ta d'anyi shiru na 'yan mintuna kafin tace "wannan tambayoyin sun min yawa wanne zan amsa?"

"Duka nake buk'atar amsar pls"

Ajiyar zuciya tayi tace "Na haifi yaron nan wata biyar da suka wuce a cikin garinnan,mun bar Kaduna saboda babu amfanin zama a garin da aka ci mana fuska,Mameey kuma ban san ina suke ba tun lokacin da Abba ya rasu suka bar Kaduna ni kuma ban san rasuwar Abba ba har sai ranar da yayi uku shiyasa ban san tafiyar su Mameey ba ban kuma san inda suke ba shekara d'aya da wata hudu kenan,idanuna kuma tsabar kukane yasa suka koma haka"

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un,yanzu a gidanwa kike zaune a katsina?"

Kuka ta fara hakan ne yasa ya gane ba a gidan kowa take ba.

Abba k'arami kukan ya fara tsalawa Jalal duk yabi ya tud'e yana bawa Janan hak'uri yana kuma jijjiga Abba k'arami.

Sai da taci kuka ta k'oshi sannan ta mik'a hannu ta karb'i Abba k'aramin ta rufeshi da hijabi tana shayar dashi aikuwa d'if kakeji babu kukan yaron.

Kallonta kawai Jalal ya cigaba dayi yana ganin abin kamar a mafarki wai 'yar k'aramar Janan tana shayarwa,shi sam ya raina girmanta a tunaninsa ma bata isa Aure ba bare haihuwa.

Ganin ya kafeta da ido ne yasa tayi saurin cire Abba k'arami,aikuwa ya fara tsala mata kuka.

Jalal ya d'anyi gyaran murya yace "bai k'oshi ba idan kunyata kike bara na fita"

Har ya tashi,cikin kunya tace "a'a Jalal babu damuwa ba sai ka fita ba"

Tayi saurin maidashi cikin hijabin ta gyara zamanta.

"Meyasa kike jin kunyata yanzu?"

Shiru tayi batace komai ba.

"Dan Allah in tambayeki Janan?"

"Allah yasa na Sani" ta fad'a kanta a k'asa.

"Sanin kin sani ne yasa zan tambayeki,amma ki bani amsa tsakaninki da Allah"

"Ina jinka"

"Da kika haifi yaron nan waye ya d'auki d'awainiyyar yi masa ragon suna"

Hmmm "babu kowa hasalima ni kad'ai na haifeshi kuma nike tare dashi har zuwa wannan lokaci"

Da mamaki yace "ke kad'ai fa Janan tayaya zaki haihu ba d'an taimako?"

"Gashi kuwa na haihun kuma muna lafiya,sai dai shi da nake tunanin kamar bashi da lafiya"

"Janan wannan ganganci ne taya zaki haihu ba mataimaki" aikuwa yayi ta fad'ansa har ya gaji ya bari.
Sannan yayi alk'awarin yana warkewa zai sayi rago ya bada a yanka na suna sannan a rarrabawa mutane.

"Aliyu bai nemi d'anshi bane?"

Gabanta ya dad'i sai ta tuno mafarkin Abba da tayi,idanunta taf da hawaye tace "d'an nan nawa da kake gani bashi da uba,dan ban san waye mahaifinsa ba"

"Me kike nufi Janan?,Aliyu ne mijinki fa"
"Na samu cikin nan bayan rabuwata da Aliyu"

"Janan meyasa?" Ya fad'a yana zubda hawaye.
Itama kuka take tana fad'in "k'addarar rayuwa Jalal,ni kuma haka Allah ya tsara k'addarata a haka"

"Babu k'addara a cikin shege ban yarda da wannan k'addarar ba,dan Allah ki fita a d'akin nan ki fice bana son ganinki a gabana"

Cikin matsanancin kuka ta mik'e tsaya tana kallon shi.

"Fita ga hanya" ya nuna mata k'ofa.

Tana shashshek'ar kuka tana tafiya jikinta sai b'ari yake,har ta kai bakin k'ofa yace "kin cuceni kin cuci son da nake miki Janan"

Ta d'an tsaya kad'an sai kuma ta wuce da sauri tana kukan.

_2 Minutes later_

Abbas da Najwa suka shigo d'akin.

Najwa ce ta k'arasa gefen gadon tace "Sannu Allah yasa dai bata b'ata maka rai ba naga ta fita tana kuka"

Baima samu damar bata amsa ba gudun kar ya fad'i abinda ba daidaiba dan ransa a b'ace yake.

"Wai Jalal meya had'aku ne,tana fita fa ta fad'i k'asa,mutane duk an rurrufeta naje nace su k'yaleta iskanci ne"

Ai bai jira Abbas ya k'arasa maganar ba ya take k'afar ya fita da sauri..
Suma da sauri suka rufa masa baya.

Yana fita ya ganta zube a k'asa ana ta jijjigata tak'i tashi,Abba k'arami yana hannunta wata mata ta danne masa goshi gefen kunnenshi da tsumma.

Baima tsaya tambayar meya sameta ba ya sab'eta key d'in motarsa na aljihu ya fito dashi ya bud'e ya saka Janan a bayan mota sannan ya dawo ya karb'i Abba k'arami wanda gaba d'aya fuskanshi a wanke take da jini.

Salati kawai yake tayi lokacin daya figi motarsa ya bar asibitin zuwa wani.

Da taimakon Nurses aka shigar da Janan da Abba k'arami cikin emergency.

Sai a lokacin yaji wani azabar zugi a k'afarshi tamkar an cire masa ita.

Zama yayi kan kujerar ya rik'e k'afa yana cije leb'e.
A nan ya fad'i ya suma daidai shigowar Abbas da Najwa cikin gurin.


*********

"Kaiii na shiga uku wai shin Umma aurenki nake?ko dai zamu fara raba kwana ne tsakaninmu naga kina neman mayar dani kishiyarki kin hanani na sake a gidan mijina wai shin meke damun rayuwarki?"

"Umma kike cewa haka"
Ummi ta fada tare da taso wa gadan gadan kan Zuhra.

Umma tayi saurin cewa "barta Ummi karki yi fad'a"

"Ai da kin barta mun goga k'ashi dan ta tabbatar da ruwa ba sa'an gwando bane"

"Ai kin yi kad'an ke baki isa kice zakiyi wa Umma rashin kunya in kyaleki ba.

Tafa hannu tayi tana dariya sannan ta kama hab'a tace " oh Allah mai iko kaji masu Umma mu kuma da muka fad'o daga sama sai muyi kuka"

Shiru sukayi mata ta sake fad'in yau zaku bar gidannan sai inga nida Uwar taki wa yafi matsayi a gurin Aliyun"
A zafafe Ummi ta taso ta damk'i wuyan Zuhra,aikuwa Zuhra ta sakar mata mari har sau biyu a kumatu d'aya.

Ganin hakane yasa Umma ta taso suka had'u ita da Ummi suka fara dukan Zuhra harda waya,a haka Allah ya fad'o da Aliyu cikin gidan.

"Subhanallah,meke faruwa haka ya fad'a tare da zuwa ya fara fincike Umma yana bata hak'uri sannan yayiwa Ummi tsawa ta nutsu.

Wannan karon kuwa su biyun suka hau masa kuka,Zuhra da Umma"

Umma na fad'in wallahi saiya saki Zuhra,ita kuma Zuhra na fad'in sai ya canza mata gida bazata iya wannan abu ba,kullum baya gida suna cikin dukanta.

Hannunta yaja sukayi upstairs.
Umma ta tsaya galala tana kallon sa wato bama zai bata hak'uri ba kawai yaja matarsa suka wuce.

Ummi ta tab'e baki tace "Umma kin gani fa,da Janan ce hankalinmu a kwance,bata da wani tashin hankali ko fad'a amma ki duba ki gani Zuhra fa so take ta rabamu da yaya gaba d'aya"

"Ki barni da matsiyaciyar yarinyar nan wai har ta kai Aliyu yana tsallake magana ta ba shakka yarinyar nan asiri ta masa"

"Umma wallahi idan muka zauna kwad'o zai mana k'afa"

"To ya kike so nayi Ummi,da wanne zanji?"

Murgud'a baki tayi tace "ah muma muyi asirin to waye bai iya ba,daga k'auyen da ta fito muma fa daga nan muke"

"Amma ai bamu kai dad'ewarta ba saboda iyayenta anan suka girma haka ita ma"

"Umma gidan boka fa ba sai wanda ya san gari ba wanda bai san gari bama sai kiga yafi d'an gari sanin malamai"

"Ummi bazan yi asiri ba,kin san dai shirka ne ko,bana son aikata zunubi ina gudun shiga wuta"

"Umma zunubi kuwa ai mun gama aikata shi saboda ko iya goggo Zahila da Janan da iyayenta aka tsaya ai kin aikata babban zunubi,kuma wancan zuwan waye ya nuna miki gidan bokan sai wannan kawai saboda a dawo da hankalin Yaya Aliyu shine kike tsoron zunubi?"

" kaji shak'iyiyar yarinya?uban me na yiwa Zaliha bayan cutar da Zahila tayi min na sanadin mutuwar Malam,wallahi Ummi idan kika

Please Login or Register in order to submit comment