You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄


```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```




17

"Raihan ce masa ya shigo"

Da sauri ta fita.

"Mameey in har kina sona zaki yadda cewa wannan Salman d'ina ne ba k'arya nake ba" kuka ne ya sake kubce mata.

Fahad ne ya shigo da alama ma daga office yake.
Turus ya tsaya tare da fad'in "lafiya?ita kuma wannan me aka mata?"

"Wai wani ta gani kamar Salman shine ta dage wai shine" Fauziyya ta bashi amsa

Tsaki yayi a daidai lokacin Yarima suka shigo tare da Raihan.

Ita kanta Mameey da ta ganshi sai da ganshi tayi tunanin Salman d'in ne dan bata tab'a tsayawa ta kalleshi sosai ba bare ta gane wani banbanci tsakaninsu.

"Bismilla zauna"

Zama yayi kan kujera,itama Mameey ta zauna Janan kuwa k'in zama tayi Mameey ta rik'e hannunta sosai.

"Dan Allah ka daure ka fad'a mana gaskiya kaine Salman kuma kasanmu?" Mameey tayi masa tambayar.

Kallon Mameey yayi yana murmushi ya girgiza kai "yace wallahi ban tab'a amfani da wani suna bayan Yarima,Saraki,da kuma Jalal,gaskiya bani bane Salman saboda ban sanku ba sai yanzu"

"Karka yaudari kanka dan Allah ka fad'a musu kaine Salman"

Kallonta yake cike da mamaki.

"Janan wallahi zan miki dukan da zaki kasa tashi meyasa kika zamo matsalar gidannan ko dan kinga ana k'yaleki,idan Salman ne gidan ubanwa zaki kai Aliyu kuma?ko kina tunanin mu k'ananan mutane ne"

"Ka k'yaleta kawai,amma kina wannan abin kike tunanin zaki iya zaman aure?kina gidan Aliyu zaki rik'a gigicewa akan mutumin daya rasu har kina suma?kina tunanin idan mu mun d'auka mijinki zai d'auki wannan shashancin?"

Maganganu ta fara akan ita ko me za'ayi wannan Salman d'inta ne,sai da Aliyu ya bata mari sannan ta nutsu tayi shiru tana shashshek'ar kuka.

Jalal jin marin yayi tamkar a fuskarsa,Janan kuwa tana rik'e da kuncinta dan a yanzu kam kuncinta har ya saba da mari.

Da k'yar Mameey ta sulhunta abin,kuma suka yarda cewar kamannine kawai amma ba Salman bane har ita Janan d'in ta yarda saboda Salman da Jalal suna da babanci sosai sannan ta san Mahaifiyar Salman kuma ta san ta rasu tun kafin a rabasu da Salman sannan wadda Jalal ya nuna musu a waya bama sa kama sam da Maman salman kawai ta yarda kamannine suka kusan zuwa d'aya.

Mameey ta mata nasiha sosai akan ta sakawa zuciyarta salama.

A b'angaren su Jalal kuwa bayan sun tafi yake tambayar Raihan shin waye Salman d'in nan.

"Shine Saurayin da ta fara yin soyayya dashi, tana Ss3 lokacin,ban sanshi ba nima saboda a poly na had'u da Janan amma lubna itace childhood friend d'inta tare sukayi tun primary har secondary a yadda lubna ta bani labarin Salman tace duk wanda ya zauna dashi dole ya so shi mutum ne mai son jama'a da kuma karamci,daga shi sai mahaifiyarsa suke rayuwa a garinnan dan koda aka tambayi danginsa yace basu da kowa kawai daga shi sai ita,talaka ne sosai ko abinci wani lokacin wahala yake musu amma Janan babu wanda takeso bayan shi,bayan rasuwar mahaifiyarsa sai ya shirya auren Janan shi kuma Abba yace ba zai bawa d'iyarsa auren mutumin da baya da asali ba,gashi baya da ko sana'ar da zai rik'e masa 'ya,Janan tace ita tana sonshi a haka Abba fur yak'i yarda ya hana,haka sukayi baran baran da Salman,tun daga lokacin bata sake sakashi a idonta ba,tayi jinya kamar bazata rayu ba dan lokacin ta gama makaranta har ta samu admission a jami'a amma bata samu taje ba saboda ciwo, shine dalilin da yasa ta rasa gurbin karatu a Jami'a sai ta samu admission a poly kuma lokacin ne Abba yazo mata da labarin Salman yana lagos kuma ya rasu a can sakamokan fad'awa ruwa da yayi,wannan shine tak'aitaccen labarin Salman"

Ajiyar zuciya yayi yace "Allah sarki Allah yaji k'ansa da rahma"

"Ameen"

"Waye Aliyu kuma?"

Murmushi tayi tace "Aliyu shine wanda zata aura"

"d'an gidan waye?ko ince a ina yake?"

"Ba d'an gidan kowa bane,shima dai talaka ne kamar Salman amma shi yana da asali"

"A ina suka had'u?"
"Direban gidansu ne kafin su fara shirin aure"

"Direba kuma"
"Eh,a dalilin lubna ta aibanta shi shine ita kuma tace sai ta aureshi,shima still Abba bayaso amma Mameey tace sai ta aureshi saboda Janan d'in ta shiga damuwa"

"Lallai Janan tana da tausayi,wannan wane irin so ne"

"Nima na kasa gane shi,Janan idan tana soyayya gani take zata iya bada ranta saboda shi"

Jikinsa yayi sanyi a zuciyarsa yace _lallai mommy tayi rashin suruka tagari,ya zanyi in fitar da kaina daga k'aryar da nayi ma mommy?_

A fili kuwa ya sake murmushin k'arfin hali yace "yaushe ne zamu sha bikin Janan?"

"Next week ne"

"Sure?" Ya fad'a a d'an firgice.

"Wallahi next week ne bikin"

"Allah ya nuna mana" ya fad'a a sanyaye.

"Ameen" ta amsa tana murmushi dan ta gama gano loggarsa.


********

To! hausawa dai sunce _rana bata k'arya.....,sai dai uwar d'iya taji kunya_

A yaune dai aka d'aura auren Aliyu da Janan.

Ba sai na bada labarin irin occasions d'in da akayi ba kunsan dai d'iyar masu kud'i ce kuma 'yar gatan Mameey.

Gaskiya taga gata sosai a gurin Mameey,Fahad da Fauziyya.

Jalal ma ba'a barshi a baya ba dan ya kashe mak'udan kud'i sosai a wata dinner da yayi organizing,sai dai har aka k'are bikin yana ta tunanin me zai cewa Mommy game da Janan.

Ranar da za'a kaita furucin da Abba yayi ya tsaya mata a rai sosai.

"To na wullar da k'wallon mangoro na huta da k'uda,bazan miki baki ba,amma kinsan yawancin talaka bai san halacci ba,to dai tunda kin zab'i haka gaki ga auren daga yanzu na zame hannuna daga kanki duk abinda yaje ya dawo karki nemeni kije can ki k'arata,kirki dawo min gida komai zai faru"

Wannan itace kalamin Abba na k'arshe daya yi mata kuma ya tsaya mata,dan hatta Mameey a lokacin sai da jikinta yayi sanyi,Fauziyya kuwa kuka ta rik'ayi.
****
Gidanta masha Allah yayi kyau sosai,plat building ne kuma safe content, bedrooms uku falo biyu,kitchen store sai kuma resting room inda aka Saka mata tuntu da show glass.

Tana zaune akan gado bayan kowa ya fita shi kuma Aliyu yaje rufo gidan,ta yaye mayafin fuskarta ta d'aga hannayenta sama tace "Allah na gode maka daka ciki min burina"

Tana nan zaune taji ya turo k'ofa,cike da murmushi ta d'ago kai,ganin ranshi a b'ace ne yasa ta mak'ale dariyarta a leb'e.

"Lafiya naga ranka a b'ace bayan yau ranar farin cikinmu ce"

Ya kalli akwatunan da aka kawota dasu kusan guda 15 yace "ki shirya kayan sawarki da abubuwan da zaki buk'ata a akwati biyu gobe zamuyi tafiya"

Da mamaki tace "tafiya kuma daga yin aurenmu yau?ko honey moon ne ai sai ka bari a d'anyi sati biyu saboda mutane zasu zazzo"

"Karki ce ban gaya miki ba,zuwa sha d'aya na safe zamu tafi ki shirya" juyawa yayi ya fita ta bishi da sauri,d'ayan d'akin ya shiga ya rufe.

Tun tana bugawa har ta gaji ta daina ta koma d'akin ta bud'e akwatunan tana zab'ar kayayyaki masu kyau dan tana tunanin honey moon zasuje kuma bata so a raina ta,sai data shirya kayan sawa akwati biyu sannan ta shirya kayan shafe shafe da turaruka a akwati d'aya,akwatuna uku ta cika dam da k'yar ta zuge.

Ta kwanta tana zulumin ko waye ya b'atawa Aliyu rai.



_*Washe gari*_

K'arfe tara ta fito daga wanka ta zauna ta d'auki tsawon minti talatin tana makeup.

Ta shirya cikin wani tsadadden swiss lace Ash da touch d'in red.

Fitowa tayi falo ta bud'e fridge ta d'akko yoghurt ta zuba a glass cup tana sha.

_to ina Aliyu ya fita haka tun safe,wai me aka yi masa ne ko kajin nan a alibidi bamu ci ba bamuyi nafilfili ba dan yiwa Allah godiya akan cikar burinmu,ko dai yana da damuwa ne?._

Ta furta a zuciyarta wanda babu mai bata amsa.

Wajen k'arfe goma ta d'anyi bak'i suma bata wani sansu ba 'yan unguwane kuma basu dad'e ba suka tafi.

Raihan da lubna ma sunzo dan sai kusan 12 bayan sunyi mata girki suka bar gidan,yara da mutane anata shishshigowa.

Sai kusan k'arfe uku ya dawo lokacin ma Akwai wata mata da tazo,a gurguje suka gaisa ya shige ciki.

"Bara na tafi tunda maigidan ya dawo"

"Da kin zauna muna hirarmu bama dad'ewa zaiyi ba yanzu zai fita"

"A'a na dawo wani lokacin tunda bamu da nisa gidana ne a opposite naki"

"To ba damuwa nagode nima insha Allah zan shigo"

Haka sukayi sallama ta tafi.

Da sauri Janan ta bishi ciki.

A tsaya ta ganshi yana zagaye a d'akin.

"Lafiya Aliyu?dan Allah ka fad'a min damuwarka"

Ransa a b'ace yace "ina kayanki da kika had'a?"

"Suna d'akin can" fita yayi,da sauri ta bishi.

"Naga akwati uku"

"Eh kayan nawa bazasu ci akwati biyu ba"

"Ba damuwa d'akko gyalenki"

Ta sauri ta bud'e closet d'in ta janyo red veil ta yafa,ta d'auki jaka ta saka takalmi.

Ya trolley biyu ita kuma taja d'ayar,har zasu fita daga falon tace "oh Akwai abinci fa da yawa kaima naka na kan dinning"

"Karki damu muje kawai"

Suna tafi taga wata mota golf duk taji jiki da alama ta haya ce.

"Malam habu a tayani saka kayan a baya"

Suka saka ta shiga ta zauna zuciyarta cike da wasiwasi,kawai sai ganinsu tayi a k'auyen su Aliyu kuma k'ofar gidansu.

Batace komai ba ganin ransa a b'ace yake.

Bayan an gama shiga da akwatunan ya kalleta yace "muje mana"

Ta shiga ciki da sallamarta.

"Ga d'akin nata can karka kawo mana tsiya nan" taji Umma dake tsaye a tsakar gida ta fad'a.

Cak Janan ta tsaya zuciyarta cike da mamaki.

"Kika tsaya kina kallonmu kamar mayya ko ba'ayi miki bayanin cewar ga d'akinki can ba" Ummi tayi naganar.

Kallonsu kawai Janan take tana ganin abin tamkar a mafarki.

Ta gabanta Aliyu ya dawo ya kalleta ido cikin ido "ke ba magana ake miki ba,ga d'akin ki nan anan zaki cigaba da rayuwa"

Sai a lokacin tace "ban gane ba bayan Mameey ta baka gida sannan ta baka jari taya zaka dawo dani nan kace in zauna bazan iya ba wallahi"

"Oh dama ta bani ne dan Ku dawo kuna goranta min?to bari kiji gida dai ita ta bani amma a halin yanzu bata da iko akanshi kuma kinaji kina gani za'a auri wata a kaita gidan ta cigaba da rayuwa a ciki ke kuma kina gidan nan babu abinda kika isa kiyi"

"Aliyu" ta fad'a da mamaki

"Eh Aliyu ba direban gidanku da kika wulak'anta lokacin yana k'ark'ashinku,ki k'arasa mana"

"Aliyu ko dai auren manufa kayi dani?"

Dariya yayi yana tafa hannu yace "karki shiga wasiwasi na aureki dan in rama sharrin da ubanki yayi min"

Jin yadda ya fad'i sunan mahaifinta gatse-gatse yasa ta harzuk'a cikin d'aga murya tace "kada ka nemi ka zagi Abba kuma bazan zauna a wannan kangon gidan naku ba sai ka bani takarda ta in koma gida saboda ina da gata dama tsiyar ka auri talaka kenan saboda baku da halac....................." Mari ya wanke ta dashi wanda yayi sanadiyyar katse maganartata.












_Sadeey S Adam_✍
[9/29, 8:16 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄




```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```



18

Tana zaune tana kuka tana k'arewa d'akin kallo, babu abinda ke cikin d'akin daga tabarma da bakko a gefe sai akwatunanta.

Har lokacin kuka take tana fad'in "na cuci kaine dana k'i bin shawararka Abba"

Jakarta ta janyo ta bud'e ta d'auki wayarta ta fara neman number Mameey,kawai ji tayi an fuzge wayar d'ago kai tayi kawai taga Umma ce.

Da sauri ta mik'e tsaye tana kallonta ido cikin ido.

"Ubanwa zaki kirawo da wayar?".

Shiru tayi bata ce komai ba,da mamakinta taji ta wanketa da mari.
" nace ubanwa zaki kirawo da wayar,munafuka kin tsareni da ido kina neman cinyeni"

Babu abinda Janan take sai kuka,wannan wace irin jarrabar rayuwace,tana tunanin tayi aure ta huta ashe ba haka bane.

Fita Umma tayi ta barta tana kuka tamkar yarinya.


Kusan magriba sai ga Aliyun ya shigo da wata katifa number 1, da kanshi ya ajjeta ya shinfid'a bedsheet ya ajje pillows sannan ya d'auki labulen k'ofa tare dana taga ya saka,sai a lokacin ta gane katifan tace extra da Mameey ta siyo bedsheet da labulayen tasan duk nata ne,ta tabbata anan zata zauna.

Sai daya gama tas yana shirin fita tayi saurin shan gabansa.

"Aliyu ban cancanci haka a gurinka ba ka tausaya min dan Allah, idan ma wani abu maihaifina yayi maka ka yafe masa karka manta Allah yana son mai yafiya"

Har ta gama maganar idonshi a kanta bai d'auke ba,kusan minti biyu sannan ya fara k'ok'arin bin gefenta ya wuce.

Tayi saurin sake tarar gabanshi,aikuwa ya saka hannu ya buge ta,fad'uwa tayi har k'asa cikin jin azaba da rad'ad'in ciwo,sunkuyawa yayi daidai saitinta ya d'an jona hannunsa akan hancinsa saboda idon ta a rufe yake.

"Oh ashe kina da numfashi,dan bana son ki mutu bakiga yadda zan k'ask'antar da mahaifinki ba"

Tashi yayi ya fice kawai,tana nan kwance kanta na sarawa tana d'an jin hayaniya sama-sama Umma na ta zaginta.

Tafi awa a kwance a gurin sai da taji an fara kiran sallar magrib sannan ta tashi jikinta na rawa alamar zazzab'i na son rufeta.

Tsakar gida ta fita da niyyar tayi alwallah,buta ta hango ajiye jikin randunan ruwa,ta nufi gurin ta d'auki guda d'aya tana shirin ta bud'e randar ta d'ebi ruwa caraf taji an rik'e hannunta.

'Dagowa tayi dan ganin ko waye.
"Bazaki d'iba ba tunda bake kike mana jigilar d'aibo ruwa ko siyan ruwa ba"

Mamaki take yadda Ummi take gaya mata magana kai tsaye,ta tuno lokacin da taje gidansu tana kuka an rufe mata d'an uwa a cell.

"Mamaki kike ko?to bari kiji wannan somun tab'i ne idan har kina raye sai kinga yadda ubanki zai rik'a bara a kasuwa yan.............." Mari Janan ta wanketa dashi cikin jin zafin cin mutumci da take neman yi mata.

A zafafe Ummi ta d'aga hannu zata rama Janan tayi saurin rik'e hannu ta wullar gefe tare da shak'o wuyanta ta matse ta jikin bango.

Wani ihun azaba da kururuwa Ummi tayi wanda ya saka Umma fitowa daga d'aki a guje.

"Ke kashe ta zakiyi?"

"Rai ba a hannuna yake ba amma ina mata gargad'ine"

Ummi sai k'ok'arin k'wace kanta take amma ta kasa,Umma sai dukan Janan take tana fuzgarta amma tak'i sakin Ummi har ta kai mak'ociyarsu ta lek'o ta katanga da yake bata da tsayi,ganin tak'i sakinta ne yasa mak'ociyar ta zari hijabi ta fito,Aliyu da Nura ta tarar kan taya suna shan rake ta fad'a masu abinda ke faruwa da sauri suka shigo gidan.

"Ke sakarta"

Jin muryar Aliyu ne ya saka ta tayi saurin sakin wuyan Ummi ta juyo zata masa magana kawai Umma ta fara kuka wai za'a kashe mata 'ya,aikuwa Aliyu ya harzuk'a ya fara dukan Janan ta ko ina,da k'yar Nura ya k'wace ta yana fad'in "ai sai ka kasheta wannan irin duka meyayi zafi Aliyu"

"Kai baka ga ba itama kisan take son yi"

Janan na tsugunne tana kuka,jikin mak'ociyar kuwa yayi sanyi dan batayi tunanin haka ba,daga kawo amarya yau.
Sumsum ta fice ta bar gidan.

Aliyu ya kalli Ummi yace "meya had'aku?"

Bata b'oye masa komai ba ta dad'i abinda ya faru.

"To ai ba k'arya kikayi da kanta sai taga hakan indai tana raye,yarinyar da aka gina da haram"

Kallon shi kawai take wai yau Aliyu ne ke fad'a mata bak'ak'en maganganu marasa dad'in ji.

Nura ne yace "haba Aliyu bai dace kana fad'ar haka ba kaifa musulmine kuma Janan matarka ce"

Umma tayi caraf ta amsa da "a'a ba matarshi bace saboda nina saka ya aure ta dan mu rama sharrin da ubanta ya mana,sannan yanaji yana gani Aliyu zai sakar masa ita saki uku kuwa"

Aliyun ma cewa yayi "me zanyi da wannan yarinyar kallarta kamar tsinke ai bata cikin jerin matan da zanso dan bana mata kallon mace ma,kai nifa a gidansu ma nafi tsanarta ita da mahaifinta"

Da sauri Nura ya jashi yana fad'in mu bar nan dan naga alama ranka a b'ace yake zaka iya fad'ar komai ma.

Kallonta ya sake yi yace "karki yarda ki tab'a musu ruwa idan kina buk'ata kije ki d'ebo naki na fad'a miki".

Ficewa su kayi suka bar gidan Umma da Ummi ma suka shige d'aki aka barta ita kad'ai a tsugunne.

Wani sabon kukanne ya sake kubce mata,sai da tayi mai isarta a gurin,tana gani suka fito suka d'ebi ruwa sukayi alwallah suka koma d'aki.

Ganin gari ya fara duhu ga sauro yana cizonta abinda bata saba ba kenan,ta tashi tana 'yan soshe soshen hannunta inda sauro ya cicciza.

'Daki ta shiga ta janyo jakarta,kud'in ciki ta fiddo duka dubu had'u ne dan sauran ta bada anyi mata depositing a banki.

Dubu d'aya ta d'auka ta mayar da sauran ta d'auki mayafinta ta fice.

Bata san inda shago yake ba wanda zata sayi ko pure water ne tayi alwallah.

Tafiya kawai take tana d'an waiwaye-waiwaye ta san tayi nisa da gidan amma babu alamun shago.

Wasu 'yan mata ta hango suna tafiya da sauri ta k'arasa gurinsu.

" sannunku"
"Yawwa sannu" suka fad'a suna kallonta.

"Dan Allah ina zan samu d'an shop d'in da zan sayi pure water"

Kallon juna sukayi,sukayi dariya,d'ayar tace "ai garin nan shago d'aya ne sai kuma masu saida abubuwa akan d'an tebur,kuma idan zaki karad'e k'auyen nan kaf bazaki samu pure water ba sai kinje can bakin titi gidan mai to anan zaki samu kuma dai yanzu kinga dare ne ga da d'an tazara tsakaninmu da titi"

"Hala ke bak'uwa ce?" d'ayar ta fad'a.

"Eh bak'uwa ce"

"To ke bazaki iya shan ruwan mu ba?,ai ruwanmu yana da kyau kuma kinga da kinsan hakane da kin taho da guzurin ruwanki"

'Dayar ta sake fad'in "to gidan da kika zo ba maza ne da baza'a karb'a a siyo miki ba"

Shiru tayi bata ce komai ba,tana tsoron tace musu alwallah take son yi dan bata son tona asirin kanta.

"Naja nifa ban yarda da wannan ba"

"Kai lallai ku d'in nan me kuka tsaya yi anan?"
Budurwar da ta k'araso gurince ke fad'ar haka.

"Kinga wata ce wai tana neman inda ake sai da pure water kuma wai bak'uwa ce amma ace babu wanda zai karb'a a gidan da tazo ya siyo mata shine muke mamaki"

"Toooh" ta fad'a cike da mamaki ta haska fuskarta da touch light, ido Janan ta rufe saboda yadda hasken ya haskesu.

"Kai Janan" ta fad'a.
Ita kuwa jin an ambaci sunanta ya sata saurin bud'e ido.

Bata gane ko wace ba saboda ta kashe fitilar.

"Baki ganeni ba?"
"Eh" ta fad'a a sanyaye.

"Zuhra ce wadda muka zo gidanku ni da Ummi"

Ji tayi gabanta ya fad'i,dan ta tuno ko wacece.

"Kin Santa ne?"
'Yan matan suka tambaya.

"Eh na Santa mana itace matar Aliyu fa"

"Kut wallahi da na san itace da bazan tsaya bama"

"Haba Hassana meye hakan" Zuhra ta fad'a

Wadda ta kira da Hassana ta sake fad'in "Matar Aliyu fa kikace Aliyun daya ci amanarki ya auro wannan saboda 'yar masu kud'i ce"

Zuhra tace "Kiji ki sai kace bakya zuwa islamiyya shi fa aure nufine na Allah"

"Uhmm naga alama,Hassana dalla taho mu tafi" d'ayar ta fad'a, wucewa sukayi,Zuhra ta girgirza kai tace "Allah ya shiryeki Naja"

Kallon Janan tayi tace "meyasa shi Aliyu bai karb'a ya siyo miki ruwan ba,saboda dare yayi kuma da d'an nisa tsakanin mu da gidan mai duk da na san baza'a samu bama sai gobe in Allah ya kaimu"

Shiru ta d'anyi kafin tace "dan Allah idan ba damuwa ki taimaka min da ruwan alwallah ko magriba banyi ba"

Da mamaki Zuhra tace "subhanallah ba ruwa a gidan?"

"Eh" kawai tace.

Ran Zuhra ya b'aci dan ta san ko babu ruwa ai Aliyu zai fita ya nemo.

_Auren Manufa,lallai ashe abinda Ummi ta fad'a min gaskiya ne,Aliyu zai auri Janan saboda yayi ramuwar gayya,dama Aliyu zai iyayin haka?ni nayi tunanin da suka fad'an haka saboda zuciyata tayi sanyi ne ashe da gaske ne,ilmin Aliyu bai masa amfani ba,ita Janan meye laifinta?mace mai tausayi ga rashin k'yamar talaka._

Haka ta rik'a tunanin har suka isa gidansu.

Buta ta bata ta nuna mata band'aki, ta shiga tayi tsarki sannan ta fito tayi alwallah.

Bayan ta iddar da sallah tana addu'oi Zuhra taje ta zuba mata abinci ta kawo mata da ruwa a Kofi.

Tashi Janan tayi ta nad'e sallayar tace "bara na tafi kar Aliyu ya dawo ban koma ba,nagode"

"A'a kici abinci kafin ki tafi"

"Bana jin yunwa nagode"

"Hajiya kinga wai bazata ci abinci ba"
Zuhra ta fad'a da k'arfi.

Hajiya dake tsakar gida tace "A'a Jana kici abinci ai kuma kunayin irinsa a birni dambu ne,idan bakici ba sai muyi tunanin ko k'yank'yaninmu kike"

Murmushin jindad'i Janan tayi ta janyo abinci Zuhra na dariya tana fad'in "kinji hajiya wai Jana take ce miki"

Itama Janan d'in dariya take lokacin da taji hajiya na cewa "ina jinku kuna gulmata" sai taji ina ma ace Umma ce Hajiya Zuhra kuma Ummi,dan taji dad'in yadda basu nuna mata kishi ba.

Kad'an taci abincin ta tashi,Zuhra ta kira k'ananta Zainab da Isa,ta d'orawa isan jarkar ruwa ta ok tace ya bi Janan da ita,Zainab ta rakasu.

Tayi musu sallama tana godiya suka tafi.

A hanya ma sai hira suke kamar dama ta sansu,Zainab na fad'in "Aunty zanzo in rik'a tayaki aiki"

"Nima Aunty zan rik'a miki aike in za'a sayo miki abu"

Cike da farin ciki suka k'arasa gidan.

Tana yin sallama ta tarar da su duka ukun Zaune kan tabarma suna hira sun kunna fitilar k'wai.

"Yaya Ali ina yini,Umma ina yini"
Duk suka gaidasu

"Ah yau tsohuwa Abu ce a gidan da Isa"

"Eh"
"To sannunku" yadda taga suna binta da kallon yasa ta gama shan jinin jikinta.

A kewayansu ta kama da k'yar suka sauke ruwan.

Sukayi mata sallama suka tafi.

"Tab lallai yarinyar nan 'yar rainin hankali ce Yaya,to a ina ta san gidansu Zuhra" Ummi ta fad'a.

"Ka gani tana neman tozartamu bazaka d'auki mataki ba Aliyu" Umma ta fad'a.

Janan kuwa najin abinda suke fad'a hakan ne ya sata mak'alewa a bango jikinta sai rawa yake.

Shi kuwa a zafafe ya tashi ya nufi kewayen nasu.










_Sadeey S Adam_✍
[9/29, 8:16 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁


*_by SaNaz deeyah_*👄



```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```


19

Tana ganin ya shigo ta runtse ido tana jirin me zai biyo baya.

Mari har sau biyu ya sauke mata a fuska sannan ya saka k'afa ya hankad'ata zuwa cikin d'akin sannan ya rufe k'ofar yayi mata duka tamkar ya samu jaka.

*02:30am*
Tana zaune jikin bango tana hawaye tare da soshe-soshe dan sauro ne birjik a d'akin ita kuma abinda bata saba bane,ga jikinta ciwo yake saboda dukan da tasha.

Gogan yana kwance kan katifar sai bacci yake abinsa da alama ya saba da cizon sauron ta fad'a a zuciyar.

Kallonshi kawai take tana mamakin yadda yake da mugunta haka,wai Aliyu mutumin da yake tamkar baya magana ashe gadar zare yayi mata.

Lokaci guda taji sabon zazzab'i na shirin sauka a jikinta ga masifaffan ciwon kai da take fama dashi.

Wasu hawaye na takaici ta sake gogewa tana fad'in ko me Abba yayi ma Aliyu bai kamata ya masu wannan sakayyar ba saboda farkon zuwanshi gidanmu Abba yana sonshi sosai.

Kwanciya tayi a k'asa kan tabarma inda ya umarceta da ta kwanta dan bazasu had'a makwanci ba,mayafinta ta janyo ta rufe jikinta duk da ba dad'in kwanciyar taji ba,amma a hakan bata san sanda bacci b'arawo ya sace ta ba.

*04:15am*

Kamar a mafarki yaji ana ta kyalkyala amai,yayi saurin bud'e ido ya haska tabarmarta yaga bata nan,hakan ne ya tabbatar mai da itace take amai.

Murmushi yayi ya juya kwanciyar a fili ya furta "yanzu kika fara zazzab'i dan a cikin abinda zan miki wannan somun tab'i ne sai naga kin fara aman jini sannan zan tabbatar da cewa na rama, lokacin ne zan fara murnar na cika burina"

Ganin tak'i daina aman ga dare ne gashi wata k'ila ma mak'ota na jinta.

Ya taso ransa a b'ace ya fito ya hasketa
"Oh a k'ofar d'aki kike min amai dan k'azanta?to wallahi ki tabbatar kin samu k'asa kin kwashe sannan ki saka ruwa a gurin banza k'azamar
yarinya kawai"

Bata tanka masa ba yayi ta bala'i har ya gaji ya koma ciki.

Ita ko Janan da k'yar ta samu aman ya tsaya,a daddafe ta zuba ruwa ta wanke gurin da bibbiyu take ganin komai.

Shigowa d'akin tayi ta zube masa anan tana fad'in "Aliyu bani da lafiya dan Allah ka taimakeni da ko panadol ne"

Dariya yayi a fili irin ta marasa imanin nan yace " 'yar gidan mommy da daddy ai nayi tunanin zaki ce na kaiki asibiti ko na kirawo family doctor ashe kin sakko"

"To bari kiji anan k'auyen babu inda zaki samu wani panadol ki bari gari ya waye sai kije dawa ki sassak'o ki dafa kiyi turare ko ki jik'a ki sha,wannan shine maganinmu kuma babu bawanki da zai yo miki sannan ina kara jaddada miki duk sanda kika sake d'ibar k'afa kikaje gidansu Zuhra wallahi duka ne hukuncinki dan bazaki kashe min aure ba

Please Login or Register in order to submit comment