You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaiyi hawaye.

"Ka daina fad'ar haka Aliyu"

"Dole ne na fad'a saboda muna cikin had'ari sosai,muna da banbanci dake sosai gashi umma ta sakoni a gaba"

"Bamu da wani banbanci saboda dukkanmu mutane ne kuma munzo daga Adamu da hauwa'u"

"Janan kenan! Meyasa kike b'oye abubuwan da suka zama gaskiya,na tabbatar ba Wanda yake son tarayya ta dake har k'awayenki taya ya zamu samu damar zama abu d'aya"

Shiru tayi tana kallonsa kawai.

"Kinyi shiru?"
"Eh bani da abin cewa"
"Kamarya?"

"Aliyu ban san taya zan maka yadda zaka fahimta ba,ni a ganina indai har muna son junanmu ai babu ruwanmu da k'iyayyar mutane"

"Kin tabbatar?"

Kai ta d'aga alamar eh.
Murmushi yayi tare da cewa "indai har kin yarda da hakan inason ki fad'awa Abba cewar ni kike so kuma zan turo magabatana cikin satin nan,sannan ina son duk runtsi karki yarda a rabaki da masoyinki a karo na 2"

Mik'ewa yayi tsaye ya had'e hannayensa tare da fad'in "ina son a yau ki jajirce ki nunawa mahaifanki nine masoyinki wanda kika zab'a a matsayin mijin aure"

Gabanta yayi mummunar fad'uwa a zuciyarta take fad'in _taya zan furtawa Abba wannan kalmar?lallai na d'ebo dala ba gammo tabbas za'ayi wani d'an k'aramin yak'i a gidan nan_

"Idan kina son mutum karki ji kunyar bayyana soyayyarshi ga kowa" ta tsinkayi muryar Aliyu na fad'ar haka.

Shiru tayi dan ji take gaba d'aya tamkar babu jini a jikinta,Aliyu ya sake fad'in "zan tafi ina sauraren wayarki da daddare akan duk yadda kukayi da Abba"

Barin gurin yayi ba tare daya jira amsarta ba,tafi minti talatin tana zaune ta kasa ko motsawa sai da taji wayarta na ringing sannan ta duba,ganin Abba ne yasa ta firgita har ta mik'e tsaye.

Jikinta na tsuma ta d'aga kiran
"Kome kike ki dawo gida yanzun nan"

"Abb......." Bata ma k'arasa fad'a ba taji ya katse.

Hannu ta d'ora aka tare da fad'in "na shiga uku ba dai Aliyu yaje gida ya fad'a ba"

A sanyaye ta lalubo number baita tace yazo ya d'auketa,gashi a lokacin ana musu lecture gashi suna da wata ma 2-4 amma babu dama dole ta bi umarnin Abba"


Driver na yin parking tayi saurin fita ta doshi hanyar main parlor d'insu.

Tunda ta hango Abba a tsaye ya hard'e hannu a gefe ga Fahad da Mameey zaune kan kujera sunyi shiru ta san tabbas akwai matsala.

Jikinta a sanyaye ta k'arasa gabanshi ba tare da ta kalleshi ba tana neman ta tsugunna kawai taji ya sakar mata wawan mari.

Tsawon dak'ik'a goma tana rik'e da kuncinta ta d'an duk'a kamar mai shirin yin ruku'u.

'Dago kai tayi ta kalleshi cike da mamaki bata san dalilin marin ba.

"Ni zaki nuna wa aikina Janan?"

Shiru tayi bata ce komai ba,ya cigaba da fad'in "har ni zaki aiko Fahad ya ce min hukuncin da nayi wa Fauziyya yayi tsauri?kuma uban waya baki damar zuwa police station keda k'annen Aliyu"

Sai a lokacin sautin kukanta ya fito,ta d'ago kai ta kalleshi idonta a fek'e tace "Abba wannan dalilai biyun sune zasu Saka ka mareni"

"Ni kike fad'awa haka Janan?" Yayo kanta Mameey tayi saurin tasowa ta tare ta.

"Ki matsa yau in kawo k'arshen rawar kan Janan"

"Abba kayi hak'uri na fad'i hakane saboda ciki d'aya muka fito da Fauziyya,Aliyu kuwa shine ..........."

Sai kuma tayi shiru tana shashshek'ar kuka.

"Aliyu uban meye fad'amin"

"Ka gafarceni Abba,Aliyu shine wanda nake son na aura kuma cikin wata d'aya me zuwa"

Jikinta ya fara karkarwa tun kafin hukuncin da Abba zai mata yazo.

Code ya ciro ya fara tsula mata,kuka sosai take amma taurin kai ya saka tak'i tashi daga gurin(Juliet ko ince laila majnoon).

Cikin zafin rai ta rik'e wayar tace "ka barni haka Abba ka bari in kashe kaina da kaina.

Mamaki ya sashi ya tsaya ya daina dukan nata.

Cikin kuka ta cigaba da fad'in " Ka gafarceni Abba"

"Janan kin haukacene?" Mameey tayi tambayar a razane

A galabaice ta kalli Mameey tace "Mameey wallahi son gaskiya nake masa kada kusa ya rasa ransa kamar yadda Salman ya mutu a dalilina,zaku rasa ni idan har kuka hanani auren zab'ina a karo na biyu"

Fahad ya taso ya rik'eta yana jijjigata "Janan ki dawo hayyacinki"

"Fahad maza kirawo Family doctor" Abba ya fad'a.

Kallon Abba ta sake yi tace "karka zama sanadi Abba"

Kamar jira ake ta gama fad'a ta langwab'e kanta wanda suka kasa gano shin a raye take ko kuwa ta mutu.






_Sadeey S Adam_✍
[9/29, 8:15 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_πŸ‘„



Dis page goes 2 Hawwy Garba(Ambaby),tnx 4 d luv n support,am glad 2 hav u as bst sista,a sista 4rm another mother❀words can never express how mch i luv u...i jst mean it.....tnx u 4 everything😍😍



12

_Bayan wasu mintuna_

Tana kwance akan gadonta tana baccin wahala,rabin jikinta a kan cinyar Mameey yake haka hannunta ma Mameey ta rik'eshi gam.

Abba na zaune a gefensu yana kallonta ransa duk a b'ace shi dai Allah ya jarabceshi da 'ya mai taurin kai.

Gyaran murya yayi ya kalli Mameey yace "wace irin yarinya ce Allah ya bani wadda take da taurin kai,Janan ta san bazan aurar da ita ba yanzu to akan me zata bi ta damu kanta?sannan Sanin kanta ne bata dace da irin mazan nan ba"

Cike da mamaki Mameey take kallonsa,ya cigaba da fad'in "ko zanyiwa Janan aure ai bazan tab'a aura mata wanda baya da albashin da zai rik'e kanshi bare iyalinsa ba"

"Kamarya?me kake nufi?Janan baiwace wadda Allah yayi maka dan ka gane illar abinda kake,ka kasa gane mutum bashi yake yiwa kansa arzik'i ba,dan haka a wannan karon zan jajirce a matsayina na Uwa dan ganin na aurawa Janan zab'inta tunda bashi da wani gurb'ataccen hali"

"Wallahi baki isa ba,ni nake da ikon zab'a musu mijin daya dace dasu,kuma bazan tab'a aurawa Janan wannan yaron Aliyu ba kamar yadda ban aura mata Salman ba"

"Idan har da ranmu kuwa kaine mad'aurin auren Janan da Aliyu bata da uba daya wuce kai sannan a wannan karon dole ka barta ta Auri Aliyu dan bazaka saka rayuwar 'ya'yana ta salwanta ba gashi kana so ka sabauta min Fauziyya duk ba kaine silar komai ba" ta k'arasa maganar cikin fad'a.

"Okay ai ga fili ga mai doki kisa in aura mata Aliyu mutumin da yayi yunk'urin lalata 'yar uwarta"

"In har da ranka zaka ga aurensu kuma kaine waliyinta,sannan ka daina alak'anta yaron nan da abinda bai aikata ba dan Fauziyya ta fad'i gaskiyar komai"

Haka Abba da Mameey sukayi Baran baran, Fahad daya dawo haka yayi ta bin kowa yana bashi hak'uri amma abin yaci tura.

Haka ya hak'ura ya zubawa sarautar Allah ido,gidansu daya kasance kullum cikin nishad'i yau gashi shiru tamkar anyi rasuwa.

***********

Yana ta aikin yiwa d'akinsa fenti da sauran 'yan gyare-gyare,Nura da Nazifi Wanda suka kasance aminansa suna aikin zagaye b'angaren nashi da jar k'asa.

Ummi ce ta k'araso gurin tace "Yaya kazo inji umma"

Hannu ya saka ya yarfe zuffar goshinsa sannan yace "kice ina zuwa"

Tafiya tayi,shima ya d'ebi ruwa ya wanke hannunsa sannan ya k'arasa gurin umma.

"Umma gani" yana fad'a yana k'ok'arin zama

"Sannu da aiki Aliyu"
"Yawwa umma"

Shiru ta d'anyi kafin tace "Aliyu kun gama magana da yarinyar?"

"Eh umma amma jiya na kirata dan jin yadda sukayi da mahaifinta naji wayarta a kashe na san k'ila ta samu matsala ne daga shi dan dama na san hakan zata faru"

"Kana ganin babu matsala?"
"Da yardar Allah umma"
"Toh Allah ya ida nufi"
"Ameen Umma,ina son a had'a komai kafin azo biki,inason na had'a mata lefe ma"

"Lefe kuma?"
Umma ta fad'a tana masa kallon Mara hankali.

"Ina son in had'a akwati guda in kai mata,a matsayin lefe ina son mahaifinta ya fara ganin b'acin rai tun kafin bikin,zan saka k'ananun atamfa guda hud'u,man shafawa 1 makilin da brush,sai reborn biyu hijabi da mayafi d'aya sai takalmin roba da sark'a da d'ankunne d'aya d'aya shikenan fa"

"To ba damuwa Allah taimaka" ta fad'a ba dan ranta yaso ba.

*******

Tana zaune akan gadonta idonta na kallon silin yayinda hawaye ke bin kuncinta.

Mameey ce ta turo k'ofar ta shigo cikin sallama.
A hankali ta amsa mata sallamar idonta ya koma kan Mameey.

'Karasowa kusa da ita tayi ta dafa ta "Janan bazaki bar kukan nan ba,tun jiya kike abu d'aya"

Kamo hannun Mameey tayi ta rik'e,gwiwowinta a k'asa tana kuka take fad'in "Mameey ki taimakeni ban san ya zanyi ba wallahi Mameey tausayin talaka da yanda mutane ke wulak'anta su yasa na fara son Aliyu,ban tab'a tunanin zan so shi haka da yawa ba dan Allah ki tayani da addu'a Mameey ina ganin tamkar na haukace ne"

Rungumeta tayi tana rarrashinta tare da alk'awarin yau za'a bata damar tace wa Aliyu ya turo magabatanshi.

'Dago kai tayi ta kalleta tace "Mameey taya ya?Abba bazai tab'a yarda ba"

"Abba shima ai yana da manya ko?na sanarwa su Alhaji babba kuma yanzu haka ya kira shi yace yaje yana son ganinsa a wannan karon bazan bari rayuwarki ta shiga had'ari ba"

Hannu tasa tana goge mata hawayen tana fad'in "tashi muje falo"

Ita dai jikinta a sanyaye yake haka Mameey ta kama hannunta suka fita.

Suna zaune Mameey ta kunna tv suna kallo saboda ya d'ebe mata kewa ta saki jikinta.

_2hrs later_

Janan na kitchen tana had'a musu fruit salad taji k'arar motocin su Abba da alama ya dawo.

'Kirjinta sai buguwa yake dauriyace ta saka kawai ta cigaba da abinda take.

Kamar daga sama taji muryar Abba yana fad'in "ina Janan d'in".

Da sauri ta ajje wuk'ar hannunta ta koma falon a tsorace.

"Kin zab'i d'a namiji akan ni mahaifinki ko?kin zab'i aure akan karatunki ko?to ga Aliyu nan zan aura miki shi"

"A'a dakata Alh karka mata baki mana,idan har baka sanya alkhairi ba to kaja bakinka kayi shiru"

"Kin kaini k'ara gurin Alhaji babba kin sa ammin dole akan abinda banyi niyya ba to wallahi duk sai kun fuskanci hukunci daga gurina"

Da sauri ya haye sama shida guards nashi guda biyu.

Hawaye ne ya fara sauka daga fuskar Janan,ta kalli Mameey tace "Mameey kawai na hak'ura"

"A'a Janan ki k'yaleshi zai sakko"


Suna nan zaune a falon ya fito,da sauri Janan ta sauke kanta k'asa dan wani mugun tsoro ne ya ziyarceta.

Zama yayi kan kujerar dake gefenta,tayi saurin sulalewa k'asa ta zauna.

"Ki ce masa ya turo iyayenshi gobe,ke kuma ki shirya wani satin zan d'aura aurenki dashi kuma zaki bar min gida a ranar da aka d'aura aurenki,sannan na janye hannuna daga komai naki mijinki ne keda iko dake idan yaga dama ki cigaba da karatu idan baiga dama ba kanki,idan yaga dama ku zauna a daji ma ba gidan k'asa ba wannan ba damuwa ta bace abu d'aya zan sake nanata miki duk abinda ya biyo baya karki nemeni matuk'ar bazaki canza ra'ayi ba"

Da sauri ta d'ago kai ta kalleshi hawaye gaba d'aya ya wanke fuskarta.
Kafin tayi magana taji Mameey tayi saurin fad'in "sai kuma aka yi sa'a mamanta 'yar kasuwa ce kuma tana da arzik'i dai-dai gwargwado dan haka zan basu gidana dana gama ginawa su zauna,dama nayi shine ina son in bawa Fahad shi kyauta amma na barwa mijin Janan halak malak,ni dai fatana ka d'aura aurensu amma bance ka bada komai ba zan zamto Uwa da uba a gareta zan share mata hawayenta kuma duk abinda ya taso zan mata shi"

"Da kin kyauta" ya fad'a tare da tashi ya koma sama.

Janan ta matso ta rungume Mameey ta cigaba da kuka.

"Karki damu ki share hawayenki ki kira Aliyun ki fad'a masa ya turo iyayenshi gobe sannan ni zan bashi jari ya fara Sana'a mai kyau wacce zata rik'eku kuma zan bashi takardun gidan yayi signing na bashi ku zauna ku rayu a ciki,ko babu komai Aliyu ya ceci rayuwar fauziyya dan da yanzu ta shiga gurb'atacciyar rayuwa"

"Mameey Allah ya biyaki da gidan aljanna" ta fad'a tana goge hawaye.






_Sadeey S Adam_✍
[9/29, 8:15 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁



_by SaNaz deeyah_πŸ‘„




```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```



*_wannan shafin nakune kyauta Ummi,Asma'ul husna,Aunty Ramlat,Rabi'atu Adam,Zulaihat.......godia da soyayyarku ga ni da novels d'ina gaba d'aya ina yinku sosai_*



*_Mrs Xerks ban san da wani kalamin zan miki godia ba sai dai in k'ara godewa Allah daya bani mai sona da zuciya d'aya,fatana Allah ya barmu tareπŸ™_*



13

****
Cike da murna yazo ya sanarwa da Umma yadda sukayi da Janan.

Farin ciki ya rufe ta sosai har da goge k'wallah,lallai ta yarda Allah maji k'an bawa ne.

"Kaje k'auyen ka sanarwa su baffa idi da baffa mu'azu sai su shirya suje gobe a had'a harda sadakinta"

"To Umma"
"Yanzu zakaje fa kar lokaci ya k'ure naga kamar kana shirin fita wani wajen"

"Eh dama zanje gidan su Zuhra ance baffanta yana nemana,so daga can sai in wuce k'auyen su baba idin"

"A'a bana son ayi sanya ka dai fara zuwa k'auyen tunda su Malam Zakar muna tare idan ka dawo sai kaje"

"To umma"

Haka kuwa aka yi sai da yaje k'auyen ya sanar musu komai sannan ya bada dubu 11 a matsayin sadakinta dan baya da ko sisi.

Yana dawowa ya sauka a gidansu Zuhra,yaci sa'a kuwa Malam d'in yana zaure da samari biyu yana musu d'orin karatu.

Ya gaidashi ya samu gefe ya zauna,Malam ya bawa samarin umarnin su d'an bashi guri ya gana da shi Aliyun,tashi sukayi cikin girmamawa suka yiwa Malam sallama suka fita.

"Aliyu bismillah"
Tashi yayi ya dawo kusa da Malam.

"To dama magana ce nake ji jite-jite cewar wai zakayi aure cikin watan nan shine nakeson jin gaskiyar lamarin"

"Hakane Malam amma............"
"Ya isa haka" Malam ya tari numfashin sa tare da fad'in "karkace komai ai shi aure nufi ne na ubangiji fatana dai Allah ya tabbatar da alkhairi"

"Ameen Malam" ya fad'a jikinshi a sanyaye.

"Kajeka ba komai zan sake nemanka"

Babu k'warin gwiwa ya koma gida,Umma da ta ga yanayinsa ta tsorata sosai tunaninta ko wata matsalarce,sai daya bata labari sannan hankalinta ya kwanta ta kuma tausasashi akan indai tana raye sai ya auri Zuhra.

Da dare haka ya shirya ya nufi gidan su Zuhran, koda ya aika tazo ma bata sauya a yadda ya saba ganinta ba da kuma yadda suka saba hirarsu hakan yasa hankalinshi ya kwanta sosai.

*********

Tana kwance a kan gado tana ta juyi tunani babu wanda batayi ba,Raihan ce ta turo k'ofar ta shigo.

"Cab lallai yarinyar nan a kwance kike ma"

"Raihan"

"Dalla ki tashi meya hanaki shiga skul?wlh test zamuyi k'arfe 2 kinsan yanzu ma muka gama lecture barrister Sanusi yace mu yago paper mu rubuta test,na samu na miki amma kinsan ta statistics dole kizo kiyi dan kin fini iya calculation"

"Raihan anya kuwa zan iya nutsuwa inyi?"

"Saboda me?"
"Saboda ina cikin cakwakiya,ko kinsan wani satin bikina"

Mtsww "dalla malama bana son wasa"

"Wallahi dagaske nake"
Labarin yadda sukayi da Abba da Mameey ta fad'a mata sannan ta k'ara da cewa"a tsorace nake Raihan,gani na nake tamkar mahaukaciya,saboda Aliyu na rufe idona na kasa janyewa Abba fushi yake dani"

Raihan ta dafa ta tace "ki daure ki hak'ura tunda kinga Abba baya so Janan ni kaina wallahi bana son tarayyarki da Aliyu"

"Meyasa?" Ta fad'a cike da mamaki

"Wallahi kawai zuciyata bata kwanta dashi ba"

"Ina sonshi Raihan dan Allah kiso abinda nake so,wallahi bazan iya rabuwa da Aliyu ba ban san wane so nake masa ba amma a cikin jinina nake jin son Aliyu"

Ajiyar zuciya tayi tace "Allah ya tabbatar mana da alkhairi,ina Yaya Fauzah ne?"

Shiru ta d'anyi sannan tace "taje Abuja gidan kawu"

"Ah ah amma ai ba Hutu sukayi ba"

"Eh an turata research shine ta zauna a can amma tace min zata dawo upper week"

"Okay Allah ya kaimu,shirya mu tafi skul"

A gurguje ta shirya suka fita,sai da ta biya ta b'angaren Mameey tayi mata sallama sannan suka wuce driver ya kaisu.

Bayan sun fito daga test ne Raihan take bawa Lubna labari lokacin suna tafiya zasuje department suyi submitting wani file na Lubnan.

Dariya sosai Lubna keyi tana fad'in "ita fa wannan k'awar tawa so take ta rigani yin aure,ita a dole sai tayi gasa dani gashi ta k'wacemin kyakykyawan saurayina"


Janan ta d'an doketa a baya tace "to shikenan na fasa aurenshi kinga sai mu auri besty mu biyu"

"Cab wlh ban yarda ba kowacce ta rik'e nata" ta fad'a tana yarfa hannu fuskarta d'auke da annashuwa.

Ita dai Raihan sam bata so dan gani take Janan bata dace da Aliyu ba,tafi dacewa da gidan hutu yadda take haka kamar a hure ta,ta san bazata iya jurar wahala ba.

"Kunji wayata na ringing ban ma sani ba muna ta surutu" Janan ta fad'a tana bud'e jaka zata lalubota,suna tafiyar wayar nata ringing ga jakar duk ta baza kayan make-up tana ta lalube sunzo dab da shiga kawai taji tayi karo da mutum,da sauri ta d'ago kai suka had'a ido.

_A karo na biyu kenan._
Ya fad'a a zuciyarsa sannan ya sake kallonta yace "ke! Baki da hankali ne?karo na biyu kenan kina bugeni"

"Dan Allah kayi hak'uri Yarima" Raihan ta fad'a.

Ya kalli Raihan yace "Kece bakinta?ita bara iya bada hak'uri bane"

"Amma duk d'aya ne kayi hak'uri mana" Lubna ta sake fad'a

"Wallahi sai ta bani hak'uri da kanta"

Kallonshi kawai Janan take cike da mamaki,shi d'an gidan uban waye da zata bashi hak'uri bayan a wancan karon hak'urin nata baiyi tasiri ba,ji tayi abin daya faru ya dawo mata sabo.

"Bazan bada hak'uri ba,shi d'an gidan waye?wlh bai isa ba na bashi hak'uri idan yana tak'amar shi d'an wani ne nima haka,kawai bana son fitina shiyasa a wancan karon ma ban d'auki mataki a kansa ba"

Raihan tayi saurin rufe baki cike da tsoron abinda zai biyo baya.

Matsowa yayi dab da ita yace "kina son sani?"

Tsaki tayi ta matsa tare da bin gefenshi zata wuce ya fizgo hannunta ya dawo da ita "yau zaki san waye babana"

"A'uzubillah! Dalla Malam sakarni" ta fad'a cikin tsiwa

Dariya yayi ya sake fad'in "dole yau kisan babana" ya fizgeta yana tafiya su Raihan suna bashi hak'uri baibi takansu ba,ita kuwa sai fuzgewa take amma yak'i sakinta,abin mamaki duk mutanen dake gurin aka rasa wanda zai dakatar dashi.

Bayan motarshi ya bud'e ya watsata ya rufe sannan ya shiga yaja.

Raihan ta dafe kai tace "mun shiga uku lubna"

A rud'e lubna tace "bara na kirawo number Mameey na fad'a mata a sanarwa da Abba"

"A'a lubna hakan zai zama matsala kinsan dai su waye iyayensa shima,ki dai bari muga yadda Allah zaiyi,idan Mameey ta kirani ko ke sai muce bamu gama lecture bane,idan dare yayi muce mun san ta tafi gida amma bamusan inda ta tsaya ba,kar mu jawa kanmu da iyayenmu tashin hankali Janan k'awarmu ce amma kinsan matsayin ba d'aya bane"

"To Allah ya tsareta daga sharrinsa"

"Ameen"

A b'angaren su Janan kuwa sai k'ok'arin bud'e k'ofa take ta kasa,cikin zafin rai tace "ina zaka kaini?"
"Zan kaiki kiga waye ubana"
"Wallahi zan yi ihu in fasa glass in tara maka jama'a idan baka tsaya na fita ba"

Dariya sosai yayi harda buga sitiyari ya kalleta yace "kinga sai ince mahaukaciya na d'akko"

Ganin dai da gaske yake sai ta fara masa magiya tana rok'on ya k'yaleta,bai sake ce mata komai ba har suka isa wata unguwa haka wajen garine dan ba gidaje sosai,abin ya bata tsoro sosai lokacin da suka isa k'ofar wani katafaren gate,horn yayi akayi sauri aka bud'e gate d'in masu gadi biyun nan da suke bakin gate bata ga alamar wasu mutanen bayan su ba.

Akwai tazara sosai tsakanin gate d'in da manya-manyan ginin na gidan har part uku duka bene ne.

Fitowa yayi ya bud'e k'ofar tana shirin fitowa taji ya sake fizgota ya nufi d'aya daga cikin part d'in.

Remote ya danna k'ofar ta bud'e ya jata suka shiga k'ofar ta maida kanta ta rufu.

A katafaren falon wanda yayi matuk'ar bata tsoro ya hankad'ata k'asa,ya sunkuyo tare da rik'e hab'arta "kina son sanin waye ubana ko"

"Dan Allah karka cutar dani kaji tsoron Allah"

Murmushi yayi wanda har suka bayyana hak'oransa,tashi yayi tare da fad'in "yanzu kika san Allah?"

Jikin wani d'in glass drawer yaje ya bud'e ya d'akko Shisha,gabanta ya sake fad'uwa zuciyarta ta tsinke lokacin da taga ya janyo center table ya ajjeta akai yana zuk'a yana furzar da hayak'in.
"Ko zaki sha?" Ya fad'a yana turo mata.

Girgiza kai kawai take lokaci guda hawaye na zuba a idonta.

Sai daya sha ta ishesa sannan ya tashi ya kalleta yace "ki gama kukan ki goge hawayenki ki Shafa hoda ki gyara lipstick d'in kan lips d'inki sannan uban nawa yazo ki ganshi ko"

"Dan Allah kayi hak'uri karka ruguza rayuwata"

Dariya ya sake yi sannan ya d'auki jakarta ya fiddo wayarta ya danna Switch "ah kinga missed calls,bara na kashe kar a damemu" ya kashe wayar ya zura a pocket d'inshi.

Ganin yayi hanyar fita yasa ta rusa uban ihu,da sauri ya juyo yace "zaki lalata muryarki fa dan wallahi babu wanda yake jinki daga Allah sai ni,in zaki shekara kina kuka da ihu babu wanda zai sani idan ba ya shigo ba,dan haka ki sassauta ranki kar ubana yazo yaji muryarki a dashe,kid'an goga lipstick d'in dan babu alamar kin shafa duk kin goge shi da hawayenki" da sauri ya fita ta taso da gudu zata bishi k'ofar ta rufe.

Zubewa tayi a gurin ta cigaba da kukan da babu mai jinta.








_Sadeey S Adam_
[9/29, 8:15 AM] Aishat A Muha'd: 🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁




_*by SaNaz deeyah*_πŸ‘„



_Ayshat A Muh'd wannan shafinki ne ke da masoyanki❣ ki d'au rabi ki raba musu sauran😊,Allah ya bar zumuncin dake tsakaninmu AmeenπŸ™_





14

Sai data gama kukanta har ta gaji sannan ta duba agogonta taga k'arfe 3:45pm,da sauri ta mik'e tsaye tana goge guntun hawayenta ga yunwa ga shi ko azzahar batayi ba.

Kallon k'ofofin falon tayi daban-daban ga wani k'aton dinning area a gefe sai bene side biyu.

_to waye babanshi da har zai mallaki wannan kud'in?shin waye shi?duk yadda akai shi d'an gidan shugaban k'asa ne,to amma ai na san 'ya'yan shugaban k'asa,to d'an waye???_
Gabanta ya yanke ya fad'i lokacin da wata zuciyar ke ce mata _masu garkuwa da mutane ne_

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un wayyo Mameey Ku cece ni" wani sabon kuka ta rushe dashi lokaci guda ta nufi k'ofar da zuciyarta ta raya mata.

Tana turawa taga wani falon ne amma bai kai wancan girma ba,kallon falon kawai take tana jinjina irin dukiyar da aka kashe wajen k'awata shi,wasu k'ofofin ta sake gani kai tsaye ta nufi wadda take facing d'inta.

Tana tura k'ofar ta tsaya cak zuciyarta cike da tsoro.

Yadda taga k'ayatuwar d'akin ko bedroom d'in Mameey daya fi ko wanne kyau a gidansu bai kaishi ba,baza ta iya fasalta kyawun d'akin ba.

A hankali take tafiya tana k'ara kallon d'akin k'ofofi biyu ta sake gani a ciki wanda ta tabbatar d'aya daga ciki toilet ne.

Tana tura ta side d'in dama taga d'an k'aramin d'akina ga qur'ani guda uku a mazauninsu,sai sallaya guda d'aya mai matuk'ar kyau a shinfid'e kan lafiyayyan carpet daga gefe kuma d'an k'aramin fridge ne.

Janyo k'ofar tayi ta rufe sannan ta nufi ta left hand side d'inta,tana turawa taga toilet ne makeke shi Kansa abin kallo ya zame mata duk da tana cikin tashin hankali.

Alwallah tayi ta nufi wancan d'akin da taga sallaya ta shiga tayi sallah sannan ta janyo Qur'an ta fara karantawa tana kuka,can ta duba agogon hannunta taga k'arfe biyar har da minti sha tara "na shiga uku,na san su Mameey suna ta nemana,me bawan Allah nan yake nufi dani?ko dai da gaske kawoni yayi ya yanka kamar yadda zuciyata ke fad'a"

Tashi tayi ta koma falon ta zauna,idonta ya k'ank'ance fuskarta tayi jajir saboda kuka.

Har ta gaji da kukan ta daina kawai ta zubawa sarautar Allah ido.

Ganin duhu ya d'an farayi ta k'ara tsorata ta tashi tana d'an zagaye ga yunwa na neman halaka ta,kamar daga sama taga haske ya bayyana a gidan,nepa ce ko generator oho!.

'Dakin ta koma tayi sallar Magrib ta duba fridge d'in babu komai a ciki sai ruwa.

"Wayyo Mameey zan mutu" ta fad'a tare da sulalewa k'asa ta lumshe idonta kawai tana jiran Allah yayi ikonsa a kanta,gani tayi d'akin harya fara juya mata rabonda taci abinci tun jiya da rana.


*********

Mameey na zaune akan kujera tana kad'a k'afa.

Kallon Fahad tayi tace "wai har yanzu bata d'auki wayar ba?"

"Ai a kashe ma wayar take tun d'azu"

"Wannan wane irin shashanci ne ta san zamu nemeta saboda yau akayi za'a zo ayi magana,gashi mutanen har suka tafi babu ita,ina Aliyu ya tafi?"

"Ya hak'ura ya tafi shima tun d'azu"

"Janan bata da kirki"

"Mameey ki barni da ita wlh sai na b'ata mata,gidan wa zataje ta kai dare haka gashi har magriba tayi"

Sallamar Raihan ce ta

Please Login or Register in order to submit comment