You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*********

Yana tsaye jikin wardrobe d'inta ita kuma tana zaune gefen gado ta had'e ranta kanta na k'asa ta k'i d'ago shi.

Jalal yayi ajiyar zuciya ya sake cewa "amma ya kamata ki saurareni Janan nazo tun d'azu ina magana tamkar da iska nake"

'Dago kanta tayi ta kalleshi tana hura hanci tana fad'in "bana son jin kalamanka mara dad'i Jalal,mene amfanin bani hak'uri bayan kai d'in za'a aura min"

Sai kuma ta fashe da kuka sannan ta cigaba da fad'in "Adnan nake so shine Salman d'ina bana sonka ban tab'a sonka ba kuma bazan tab'a sonka ba,ko da ka aureni gangar Jikina ka aura amma zuciyata na gurin Adnan"

"Janan ni kike fad'awa haka?baki jin ko kunyar idona"

Mik'ewa tayi tsaye tana fad'in "idan tsoho baiji kunyar hawa jaki ba to jaki bazaiji kunyar yada shi ba"

'Daga hannu yayi cikin zafin rai zai mare ta sai kuma ya tsaya.

"Ka mareni mana ai ga kumatun nawa,ba yau ka fara marina ba ai bazanji komai ba dan ka d'ora daga inda ka tsaya,kuma wannan shine banbancin Adnan da kai saboda shi mai tausayi da kare mutuncin 'ya mace ne"

Idanunsa tuni suka sauya kala suka koma launin ja.

"Ka cuceni saboda da ka barni da ban ga Adnan ba bare har ya tado min tsohuwar soyayya data kwanta a zuciyata, nayi dana sanin sanin ka a rayuwata ka cuceni Jalal"

Ya bud'e baki zaiyi magana aka turo k'ofar.

Dukkansu suka maida kallonsu ga k'ofar.
Abba k'arami ne ya shigo hannunsa rik'e da Balloon.

Gurin Jalal ya fara zuwa yanan fad'in "daddy me aka yi wa Ammi?"

Muryarsa a can k'asa yace "bata da lafiya Prince"

"Abbana zo nan" ta kira yaron.

Komawa yayi gurinta ta rungumeshi tana goge hawaye tana shafa kanshi tana fad'in "Abbana wannan ba daddynka bane Uncle ne kada ka sake kiranshi daddy saboda kai baka da uba"

"Janan......."

"Dakata Jalal dole in sanarwa d'ana matsayinka a gurinshi saboda idan ka haifi naka zai fara ganin banbanci duk da dai ba lallai in haihu da maci amana ba"

"Ya isheki haka Janan na gaji da jin munanan kalamanki"

Mtsww "idan baka son ji ka fita daga d'akina bana son ganinka"

Ta k'ara rungume Abba k'arami tana kuka.

Da sauri ya fita ya shiga mota ya bar gidan ma gaba d'aya.

*********

Da sauri ya d'auki takardu zai fita ta tsayar dashi "Muhasin ka tsaya kayi min bayani wai dagaske ne ko kuwa dai kana fad'a dan ka kwantar min da hankali?"

Ya juyo ya kalleta yace "Momma wallahi da gaske nake,da kunne na naji labarin abinda yasa ma na gane itace saboda ta bamu labarinta,kuma na kira shi mutumin ya tabbatar min da Janan tana gidansu a Abuja,har ya bani address d'in gidansu dan yayi tunanin ko nasan wani abu daga mutanen da ake nema"

Wasu siraran hawayene suka sauka a kuncinta na murna.
Cikin farin ciki ta goge hawayen tana fad'in "idan kuwa har hakane bamu ga ta zama ba,gobe da sassafe zamu tafi Abuja kayi mana booking na jirgi sai mu tafi tare da Humaira"

"Momma nima ina son zuwa naga Janan"

"Zainab mijinki ba lallai ya yarda ba shima Muhasin ba zuwa zaiyi ba saboda ba zai tafi ya bar matarshi ba daga yin Aure"

Kallonta yayi sannan yace "Momma ai nine jagoran tafiyar"

"Kwana hud'u da yin aurenka sannan kace zaka tafi Abuja"

"Momma komai kamawa take ina son zuwa,dan haka zan mana booking jirgi ni dake da Humaira"

"Yaya Muhasin dan Allah dani nima"

"Ki kira mijinki ki tambayeshi idan ya yarda to"

Ai a gabansu ta kira shi tayi masa bayani tace saboda yanzu za'ayi booking ma in ya barta aikuwa ya amsa mata yace ba matsala tun da da Momma ne.

Murna da farin cikin da suke ciki bazai musaltu ba.

Muktar na dawowa yace shima zaije,Momma tace sunyi yawa ya hak'ura sai wani jik'on.

*********

An karramasu a gidansu Jalal sosai duk da basu san ko su waye ba,a falon bak'i aka saukesu.

Mommy ta fito sun gaisa sannan tace "sai dai ban shaidaku ba"

Momma tayi murmushi tace "ni ce marik'iyar Janan,dan tamkar 'ya take a gurina tun b'atanta shekara biyu da watanni bamu sake jin d'uriyarta ba sai yanzu"

Mommy ta d'anyi shiru sannan tace amma Janan bata tab'a sanar dani tana da wata uwar rik'o ba"

"Karki damu in dai ta ganmu zata gane mu"

"Okay bara na kira muku ita" tashi tayi ta fita.

Zainab ta kalli Momma tace "ko me Janan ta haifa?na san har ya girma"

"Koma meye ai zaki gani,uwar surutu" Muhasin yayi maganar.

Murmushi tayi Humaira ma tayi saurin cewa "ni kawai so nake naga yadda Janan ta koma"

Murmushi Momma tayi tace "na san Janan na cikin kwanciyar hankali tunda gidan manya take zaune"

Suna zaune Mommy ta shigo Janan d'in na bayanta.

Tana ganin Momma ta ruga da gudu ta rungumeta tana fad'in "Momma dama kece,ashe zan sake ganinku a rayuwata" Sai kuma ta fashe da kuka.

Momma ma kuka ta fara yi,sukayi ta kuka a haka Jalal da Adnan suka shigo.

Zazzaunawa sukayi ta cigaba da goge hawaye sannan ta kalli Muhasin tace "Yaya Muhasin ina yini ya hanya?"

"Oh sai yanzu ma kika ganni ko?"

"Yi hak'uri Yaya"

Tashi tayi ta koma kusa da Zainab da Humaira tace "Humaira ya karatu?"

"Alhamdulillahi shine kika gudu ko?"

Murmushi tayi mai had'e da hawaye sannan tace "gashi yanzu na dawo"

"Mun nemo ki dai"

Murmushi duk sukayi.

Adnan yace "ko kaine wanda mukayi Waya?"

Muhasin yace "kwarai kuwa nine"

"Ina cikin ki Janan?" Gabanta ya fad'i ta fara Allah-Allah kar su ce cikin Aliyu ne dan su kad'ai suka san gaskiyar lamarin.

"Na haihu har ya kusa shekara biyu,bacci yake bara na d'akko shi"

"A'a ki barshi ai muna garinnan har gobe zamu ganshi idan ya tashi"

"A'a Momma na san ya tashi ma"

Tayi sauri ta hau sama.

Tana zuwa ta tarar dashi yana ta wasanshi.

Yana ganinta da gudu ya rungumeta.

'Daukarshi tayi ta shiga toilet ta sake yi masa brush sannan ta fito ta canza masa kaya ta fesheshi da turaruka suka nufi k'asa.

Dukkansu sunyi mamakin ganin wai wannan d'an Janan ne.

Ga yana da son mutane dan haka wannan ya d'aukeshi wannan ya d'auka duk suka rik'a santin kyawunsa duk da yana fuzgen kama da Janan d'in.


"Amma Janan bayan tafiyarki ina kika nufa,na rik'a nemanki Janan kullum na tunaki sai nayi kuka,da naga an shekara sai nayi tunanin kin had'u da su Mameey ne" Momma tayi maganar tana sake goge hawayen da suka zubo mata.

Labari ta basu tiryan-tiryan tun da ta fara Adnan ya kafeta da ido dan yanzu Janan har tsoro take bashi.

Momma,Zee,Humaira hawaye sosai suke musamman Momma fuskarta tayi Jajir.

Ganin Janan na kuka ne yasa Abba k'arami shima ya rud'e ya fara kuka.

Mommy ta karb'eshi tana fad'in "kun tsorata yarona"

Rarrashinsa ta hau yi yak'i dainawa sai da Jalal ya karb'eshi ya sab'a a kafad'a yana jijjigashi.

"Momma" Janan ta matso gabanta sannan ta sake cewa "Momma wannan fa shine Salman d'in da nake ta fad'a muku"

"Oh shine Salman"
"Eh"
"Allah sarki da rabon zaku sake had'uwa kenan"

Murmushi tayi.
"To Allah tabbatar da Alkhairi naji dad'i da kika ganshi ko dan alk'awarin Iya da kuka d'aukar mata"

Jalal ji yayi zuciyarshi na harbawa.
_Janan kenan sam bata tunawa dani bare har ta bawa wasu labarina,lallai na yarda bata sona._

Adnan kuwa duk wani nauyi yake ji rayuwarshi a Kaduna ta dawo tamkar sabuwa.

"Saura sati d'aya bikinta da k'aninsa Jalal"

"A'a to Salman d'in fa?"

Murmushi Mommy tayi tace "ai da yake Allah ya k'addara sai abu ya faru bayan rabuwar Janan da Salman sai kuma suka had'u da Jalal"

Anan Mommy ta basu labari sannan ta k'ara da cewa shine yace ai duk d'aya ne ya barwa k'anin nasa"

"Allah sarki,Allah ya zab'a maka mafi alkhairi"

"Ameen"

"Amma Janan zaki bimu ki kwana biyu ko?"

Murmushin k'arfin hali tayi dan ta tsani a had'a ta da Jalal ranta duk ya b'aci.

"Zata zo bayan biki insha Allahu dan ina mata shiri ne"

"Laaa zata min k'wacen 'ya,nima ai shirin zan mata" Momma ta fad'a tana dariya.

"To aini anan har na biya kud'i an fara" Mommy ma tayi maganar tana dariya.

"To shikenan sai a bamu d'an Amana mu tafi dashi yayi sati in zamu zo biki sai mu taho dashi"

"Wannan kuje an baku amma zaku sha damu akan tatsuniya"

"Indai tatsuniya ce yazo gidanta"

Duk sukayi dariya.

Su Momma a gidan suka kwana,Humaira da Zainab d'akin Mommy,Momma ta kwana a d'akin Janan amma sai da suka raba dare suna hira anan ne Janan ta fad'awa Momma dalilin hanata Adnan da aka yi ta kuma gaya mata k'udirinta.

"Abinda Mommy tayi shine daidai Janan,Jalal ya miki halacci duk da dai Adnan kike so to amma Jalal shi yafi cancanta da zama mijinki koda Salman lafiyarsa lau"


"Hawaye ta fara tana fad'in " Momma dan Allah ki tafi dani ki auran Yaya Muhasin wallahi bana k'aunar Jalal dan shi ya rabani da Adnan"

Rungumeta tayi tana fad'in "wallahi yana sonki tun da mukazo yake d'awainiya damu,Janan karki nemi saka wa kanki ciwon da Allah bai saka miki ba"

Cikin kuka ta sake fad'in "alk'awarin dana d'aukarwa Iya fa"

"Wanna kuma ai k'addara ce tasa bazaki aureshi ba,Jalal yana k'aunarki kiyi amfani da damarki sai nan gaba zaki gane cewa mun miki gata"

"Wallahi Momma Adnan ma yana sona kawai dan dai ciwon nasa"

"To kin gani ki d'auki k'addara kamar yadda ya d'auka"

Kuka tayi tayi Momma na rarrashinta.

*_Washe gari_*

Da sassafe su Zainab suka shigo aka kafa sabuwar hira.

Anan ne suka fad'a mata Zainab d'in tayi aure watanta shidda,Muhasin kuma kwana biyar tayi musu murna tace "saura Humaira da Muktar"

"Kai aini yarinya ce l1 fa nake" duk sukayi dariya.

Momma tace "dama aike yarinya ce tsahon k'afa kikayi,Muktar ma anyi baiko"

Sai Janan taji tana son ta bisu Yola,Momma tace tayi hak'uri sai bayan bikin.


Haka ta shirya kayan Abba k'arami tsaf,k'arfe sha biyu suka bi jirgi suka tafi.

Duk kewarsu ta rufeta ga rashin Abba k'arami taji kewar d'anta sosai.

Da yamma tana kwance akan gado tana tunanin maganganun da sukayi da Momma akan Auren Jalal.

Wasu hawaye ne suka sauka a fuskarta a fili ta furta "ku yafe min Mommy da Momma wallahi Adnan nake so"

Da sauri ta tashi ta bud'e drawer jikin mirror ta d'akko razor ta bud'e ta kalleta tayi murmushi mai d'auke da hawaye "yau da darasinki zanyi amfani Umma,na san zafin razor a farko, ana biyu kuwa bazata min zafi ba"

Ta goge hawaye ta cije leb'enta tace "Jalal bana sonka kar kuma kasa in soka dan kawai ka taimakeni,kowa yana ganin kamar idan na gujeka nayi rashin halacci,to wai shin ina ruwan soyayya da halacci,kawai tana son wanda take so ne,dan haka tunda ank'i aura min zab'ina saboda ciwon jikinsa na san in muka zama d'aya zasu auran shi,yau zanwa tumk'ar hanci"

Da sauri ta fita tana goge hawaye.








*_Comments d'inku kawai zan saurara dan jin ra'ayoyinku readers._*











_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_👄




```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```





44

Kai tsaye d'akin Adnan ta nufa.

Tana tura k'ofar ta tarar dashi zaune akan sofa ya d'ora hab'arsa akan gwiwarsa.
Idanunsa akan plazma dake manne jikin bango amma a zahiri ba kallon yake ba.

Shigowarta yasa shi juyo kai ya kalleta.

Wasu zafafan hawaye ne suka sauka a fuskarta ta kalleshi tace "Adnan alk'awarin Iya dan Allah ka zamo mai halacci da adalci"

"Wannan ne iya adalcin da zan miki Janan,wannan shine zai nuna wa duniya cewa ina son ki kuma bana fatan cutar dake daga ke har Jalal,wallahi da kinsan irin son da Jalal yake miki da baki nuna masa k'iyayya ba"

Cikin kuka tace "kenan kai baka sona Adnan?"

"Ina son ki mana amma Jalal shi yafi cancanta da ke"

"Oh kenan idan da babu ciwo bazaka Aure ni ba saboda Jalal?duk irin son dana nuna maka?"

"Da babu ciwo a jikina babu abinda zai hanani aurenki Janan"

"Shikenan zan wa tufk'ar hanci yanzu"

Kafin yayi magana ta kai razor nan ta yankin hannunsa.

Yaji azabar zafi,amma a fusace ya rik'o hannunta dan karta aikata abinda take shirin aikatawa,aikuwa ta bank'are hannun cikin zafin nama ta yanke razor a cikinta.

Wanin azababben k'ara ta k'walla hakan bai hanashi d'aga hannu ya wanketa da mari ba.

Hawaye gaba d'aya ya wanke mata fuska hannunta rik'e da kuncinta wani jiri-jiri take ji.

Shima hannun nasa ya rik'e yana hawaye ya kasa tab'uka komai.
"Kin cuci rayuwarki Janan" ya fad'a a can k'asan mak'oshinsa.

A haka Jalal da Mommy suka shigo.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" Mommy ta fad'a tare rik'o Janan d'in da take k'ok'arin sumewa,jini gaba d'aya ya wanke mata gaban rigarta.

Jalal ya tsaya cak ya kasa motsawa wasu hawaye ne kawai ke fita daga idanunsa.

Mommy ta juyo a rikice tace Jalal muje asibiti.

Jikinsa a sanyaye ya juya zai fita tayi saurin cewa "Jalal bazan iya d'aukanta ba"

A sanyaye ya juyo ya d'auketa a sume kamar gawa ya fita.

Mommy ta kalli Adnan tace "tashi mu tafi ga yadda jini ke zuba a hannunka"

'Dago ido yayi ya kalleta yana hawaye yace "Mommy zan wanke da spirit ku kaita kawai"

"Haba Adnan idan kai baka san ciwon kanka ba ni na sani"

"Mommy kunyar had'a ido da Jalal nake"

"Adnan ka bar maganar nan ka tashi muje kawai,wai baka san ciwon kanka bane"

Jikinta a sanyaye ya bita.

Har zata shiga baya Jalal yayi saurin cewa "Mommy dan Allah kiyi driving wallahi bani da wani k'arfin da zan iya yi"

Tausayinsa sosai taji ta karb'i key d'in maigadi ya bud'e gate d'in aikuwa a guje taja motar.

_*Asibiti*_

Suna zaune a office d'in likitan yana sake musu bayani.

Jalal kanshi a k'asa yake ya dafe goshinsa da hannu.

Adnan na tsaye rik'e da hannunsa da yasha bandage.

"Ya akai har hakan ta faru?"
Likita ya nemi k'arin bayani.

Adnan ne ya fara yi masa bayanin yadda abin ya faru,tunda ya fara magana Jalal d'in ya kafeshi da ido har ya gama.

Shi kanshi likitan salati yayi tare da girgiza kai.

"Doctor yanzu shikenan itama ta kamu da cutar?mun zo nan ne saboda kaine family doctor namu na san bazaka tab'a yi mana k'arya ba" Mommy tayi tambayar.

Gyara zama yayi yace "to yanzu dai duk test d'in da muka mata babu wanda ya nuna mana cewa tana da cutar a jikinta amma babu makawa ta kamu da ciwon tunda a lokacin ta yankeshi ta kuma yanki kanta,da ace razor tayi 15minutes sannan ta yanka kanta to babu wani abinda zai faru,sai dai bazamu tab'a tabbatarwa ba har sai nan da wata uku lokacin ne idan munyi test in dai ta kamu da ciwon zamu gani dan haka zamu d'orata akan magani kafin lokacin"

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" shine abinda Jalal yake ta nanatawa yana goge hawayen dake zuba a fuskarsa.

"Doctor ai magana ta k'are tunda har kayi bayani,sai dai kawai nan da wata uku mu dawo a d'orata akan magunguna na masu ciwon"
Mommy ta fad'a a sanyaye dan ita kanta dauriya take.

"Karki damu hajiya,zasuyi rayuwarsu kamar yadda kowa keyi tunda haka ta zab'a,amma fa sai dai bazata shayar da yaron ba sai dai da madara karki damu komai Jarabawa ce daga Allah"

"Na Janan sakaci ne da rashin jin magana" Jalal ya fad'a sannan ya tashi ya fita.

'Dakin da aka kwantar da Janan ya shiga.

Idanunta a rufe suke,bedsheet rufe da jikinta har zuwa wuyanta.

Jikin gadon yaje ya tsaya yace "ban tab'a tunanin tsanar da kike min ta kai haka ba Janan,har ki sakawa kanki cutar HIV saboda kawai karki aureni,ni dai na san son da nayi miki so ne na gaskiya na so ki tsakani da Allah da kuma zuciya d'aya,bana bak'in cikin auren Adnan da zakiyi amma ina bak'in cikin abu biyu ciwon da kika sakawa kanki da kuma rashin ki da nayi a rayuwa"

Ya d'an tsaya yana goge hawaye sannan yace "zan nisanta dake Janan saboda bana son in fara tsanarki kamar yadda kika tsaneni"

Juyawa yayi zai fita yaji tayi magana.
Da sauri ya juya ya kalleta.

Idanunta a rufe suke amma still hawaye na zuba.

"Jalal wallahi ban tsaneka ba,kawai bana sha'awar kasancewa matar wani in ba Adnan ba,shi nake so shina fara so a rayuwata,kayi hak'uri Jalal"

Fita kawai yayi da sauri ya bar d'akin.

Satinsu guda suna jinyar Janan, Adnan sam baya zuwa saboda haushinta kawai yake.

***********

"Lallai samu guri kenan,waye ya bawa wannan tsofaffin damar shigowa falona?"

'Dago kai Umma tayi ta kalleta tace "Zuhra kin san kuwa suwa ne wannan?"

"Koma su wane bai dameni ba kawai a fitar min daga falo bana son tarkace"

Cikin b'acin rai baba Isa ya tashi ya kalleta yace "idan ubanki ne zaki fad'a masa haka?"

"A'a dakata baba,ina ganin girmanka kada ka sake sako mahaifina"

Juyawa yayi ya kalli Umma wadda tayi tsumu-tsumu yace "wannan itace surukar taki dana sani ko kuwa musaya ne?"

"Itace wallahi ai yanzu ta gagari kowa a gidannan sam bata ganin girmana"

"Lallai kuwa dole muyiwa tumk'ar hanci,idan Aliyu ya dawo lallai kice ina nemansa" baba Idi da tunda ta fara rashin mutumcin ta baiyi magana ba sai lokacin.

"Ni fa ban sa daku ba ya kamata ku rufamin bakin nan naku da yayi dumu dumu da goro"

"Iyeee lallai na yarda Alhakin yarinyar nan ke binki Isa wuce mu tafi"

Ransa a b'ace suka wuce Zuhra ta bisu da fad'in "Umma ta gaida Assha"

"Lallai Baki da mutumci Zuhra kuma idan kikace dani zaki ja tabbas zaki zubda hawaye"


Dariya tayi ta tafa hannu tace "ahayye ayi mu gani mana idan sabulu zai daina kumfa,ai ga fili ga mai doki"

Wucewa tayi ta barta a tsaye.

Hawaye suka sauka a idon Umma a fili ta furta "lallai nayi sakaci dana har Aliyu ya saki Janan ashe dama Zuhra bata da mutumci"

'Daga hannu tayi tana fad'in "Allah ka kawo mana sassauci,ga dukiya sai k'ara hab'aka take amma babu kwanciyar hankali ina dalili"

**********

Suna zaune su duka a bedroom d'in Janan,Mommy ta kalli Jalal da Adnan tace "dan Allah ina neman alfarma a gurinku"

Duk sunyi shiru basu ce komai ba ta cigaba da fad'in "koda wasa kada ku bayyana cewa Janan nada wannan cuta dan Allah saboda mutane da kuma yaronta mu rufawa kanmu asiri"

Ta kalli Janan tace "ko Asabe ban yarda kin fad'awa ba ki rufe sirrinki"

"Mommy insha Allahu babu wanda zai ji wannan maganar daga bakina" Jalal yayi maganar.

Adnan kuwa ya kasa cewa komai,tausayin d'an uwan nasa kawai yake.

Idon Janan a k'asa duk kunyarsu ta hanata kallonsu.

Bakinta na rawa tace "dan Allah Mommy kiyi min izni in koma Yola gurin Momma"

Kallonta ta sakeyi tace "Janan babu inda zaki je har sai bayan bikinki kamar yadda na fad'a,karkiji nauyina ni tamkar mahaifiya ce a gareki"

Kallon Jalal tayi tace "Mai martaba yana nemanku nayi masa bayanin da Adnan za'a had'asu tun jiya mukayi waya yace abar bikin nan da wata d'aya zai samu sauran 'yan uwa yayi musu biyani a fara shirye-shirye sannan yace yana son ganinku dan haka Ku shirya a wannan week d'in kuje"

"Insha Allah" Jalal ya amsa.


_3 weeks later_

Tana zaune a falo ita kad'ai ta zabga uban tagumi,rashin kulata da Jalal keyi abin na d'aga mata hankali,gashi ko magana tayi masa sama-sama yake amsawa.
Adnan ya sakko daga steps fuskarsa d'auke da fara'a ya k'araso kusa da ita.

"Ya dai naga kin zabga tagumi?"

'Dagowa tayi ta kalleshi idanunta d'auke da hawaye.

"Kinji matsalarki fa wannan hawayen na mene ni na fito ina murna"


"kin san me?an samu wanda suka yi ginin nan shiyasa na fito kuma yanzu muka rabu da Jalal ya fito yace gurinki zaizo"

Tun kafin ya gama maganar ta mik'e tsaye tare da fad'in "da gaske ko wasa Adnan?"

"Wallahi dagaske nake"

"Adnan suna ina yanzu"

" 'Daya daga cikinsu yana kano cikin wata unguwa Kuntau yayi min kwatancen gidan ma"

"Allah na godema" ta fad'a tana hawaye.

Da sauri suka nufi d'akin Mommy aka sanar mata.

A take Adnan ya sake kiranshi sukayi waya da Mommy tayi masa godiya sosai tace insha Allahu gobe Suna kan hanya.

Jalal ma daya dawo yaji labarin ba k'aramin farin ciki yayi ba.


_Washe gari_

Tun k'arfe takwas suka shirya suka nufi kano.

K'arfe 1 a kano ta musu,kasancewar Adnan yayi zaman kano unguwar bata musu wuyar samu ba.

Bayan sun huta ne mutumin mai suna Sule ya sake yi musu bayanin komai,ya sanar dasu cewa jibi ma ogan nasu zai zo dan baya nijar d'inma yana chadi amma da yaji labarin ne yace insha Allahu yana nan tafe.

"Babu damar muje kadunar yau?in har kai ka gane gurin da aka safe bishiyar" Jalal yayi maganar

Murmushi yayi yace "a'a ai shi ogan namu zanan gidan yana gurinsa da yadda ya zana tun kan a gina da kuma bayan an gina komai dai shi zai nuna saboda muma bamu muka sare ba wasu aka kira mu gini kawai mukayi kuma shekarun da yasa ba lallai na gane gun ba"

"Ba damuwa Allah yasa mu dace" Mommy ta fad'a.

"Ameen"

Sai kusan la'asar sannan suka fito zasu tafi,ya fito shi da matarsa da 'ya'yansa suka rakasu har mota,Jalal nata musu godiya.

A daidai makaranta kuntau shagunan dake gefe nan taga Fahad zaune kan benci kamar a mafarki.

"Inna lillahi......" Ta fad'a a tsorace.

"Lafiya Janan?" Suka tambayeta

"Jalal dan Allah kayi parking"

"Meya faru?"

"Dan k'aunarka da annabi (SAW) ka tsaya"

Da sauri yayi parking d'in,ta fita da gudu suka fito suka biyota.

Bata kula da mazan dake tsaye da Wanda ke zaune a gurin ba da k'arfi tace "Yaya Fahad kai d'in ne dagaske?"

A dai dai lokacin su Mommy suka k'araso.

Kana ganin Fahad kasan yana cikin wahala da talauci.

Kallonta ya tsaya yi kamar bai santa ba.

Juyawa tayi ta kalli Mommy tace "Yayana ne fa" wasu hawayen suka sauka a idonta.

Mutane aka hau magana k'asa k'asa.

"Taya ban sanki ba zaki zo kina neman tara min mutane?"

Baki ta saki tana kallon sa.

"Kaine Fahad nima na shaidaka" Jalal ya fad'a yana kallonsa.

"Tabbas Fahad ne dan kamanninsa basu canza ba" Adnan ma ya fad'a.

Kallon Adnan da Jalal da Janan yake duk ya rud'e dan abin mamaki yake bashi.
_dama Salman bai mutu ba meya had'asu su suka tare?._ shine abinda zuciyarsa ke furtawa.

Janan ta sake fashewa da kuka tana fad'in "wane laifin nayi muku Yaya Fahad me nayi muku kuka tsaneni kuka gujeni"

"Dalla malama b'ace min da gani a ina kika sanni" ya fad'a ba dan ransa yaso ba,sai dan yana ganin ita ce silar shiga damuwarsu.

'Daga yatsa tayi ta nuna shi cikin karaji tace "Kaine na ratse kaine Yaya Fahad me nayi muku kuk........" Bata k'arasa ba ta zube k'asa sumammiya.

A gigice Jalal da Adnan suka sunkuya zasu rik'ota Fahad yayi saurin tallabota yana kuka yace "Janan ki tashi muna sonki dole ce yasa muka gujeki,dan Allah Janan ki tashi"

"Muje asibiti mana"
Adnan ya fad'a a rud'e.

"A'a gidanmu babu nisa muje can kawai mamanmu tana nan" ta sauri ya saka ta a kafad'a ya wuce suka bishi.









_Wai! Cab! ya Mameey zataji idan taga Janan?,dan ma a sume za'a kai mata ita._


_Ku biyoni dai cikin wannan littafi_📝











_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁




*_by SaNaz deeyah_*👄




```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```






45

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un,Janan nake gani"

"Itace Mameey" ya fad'a lokacin daya shimfid'eta akan carpet d'in tsakar d'akin,ya shiga ciki da sauri ya d'akko fulo.

Mameey tsire Jalal da Adnan tayi da ido a d'an tsorace tace "dama baka mutu ba Salman?to ina kuka had'u da Jalal na kuma ganku da Janan ina kuka samo min Janan a sume?"

"Mameey a d'ebo musu ruwa tukunnan" Fahad ya fad'a.

"A'a mungode a k'oshe ma muke"

Jalal ya goge hawayensa daya ga yadda suke a wahale kamar basu ba.

Adnan kuwa zuciyarshi zafi take kukan zuci kawai yake.

A hankali Janan d'in ta bud'e idanunta ta dire su a fuskar Mameey aikuwa ta fashe da matsanancin kuka.

Mameey ta taso tazo kusa da ita ta zauna,da sauri Janan ta matsa gefe.

"Janan guduna kike?" Ta fad'a tana zubda hawaye.

"Mameey gudunki nake saboda baku k'auna ta kuma,kuka gujeni kuka sani a k'unci da matsananci hali kuka k'i waiwayata bare ku ga halin da nake ciki"

Da sauri Mameey ta k'ara matsawa kusa da ita ta rungumeta suka k'ara fashewa da kuka.

"Ban gujeki ba Janan taya zan gujeki wallahi bana k'aunar ganin Aliyu shiyasa na tafi"

"Amma Mameey aka rasa wanda zai sanar dani mutuwar mahaifina har sai da yayi kwana uku,shima ba dan nazo Kaduna ba da bazan sani ba"

"Janan muna cikin tashin hankali wa zai iya zuwa bak'in k'auyen nan?ina zamu je gidan mak'iyanmu gashi baki da waya,kiyi hak'uri Janan wallahi na tsani Aliyu"

"Mameey na fiki tsanar Aliyu saboda yayi min babbar illa ya cutar dani ya cutar da innocent Abba wallahi ban tab'a ganin azzalumin mutum kamar Aliyu ba"

'Daga

Please Login or Register in order to submit comment