You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a ranka"

Ya kalleshi lokacin tarin ya lafa yace "Fahad bazan iya cirewa ba,kaima na ja maka matsala a gurin aikinka sun k'wace mana komai hatta kud'in dake account d'in mu sun karb'a duk wani kadararmu sun karb'e wannan wace irin shari'a ce?wane irin bahagon hukuncine,da kayan sawa kad'ai aka barmu Fahad" kuka sosai Abba yake suma suna kuka.

Turo k'ofar da aka yi ne yasa duka suka kalli wajen.

A fusace Fahad ya taso yana fad'in "me kazo kayi mana anan?"

Murmushi yayi yana fad'in "kwantar da hankalinka ba zama ya kawo ni ba"

Zai k'ara magana Abba yayi saurin d'aga masa hannu alamar yayi shiru.

Taku biyu Aliyu yayi ya k'arasa jikin gadon "sannu ko" yayi dariya 'yar kad'an sannan ya juya ya kalli Mameey.

"Kin gani ko haka Allah yake ikonsa,yau gani nine mai arzik'in,duk wani abinda kuke tak'ama dashi babu,kin san me?zuwa nayi na baku sadaka dan a samu a sayi magani kuma 'yarki zan mayar da ita k'ask'antacciyar baiwa a gidana"

" 'karya kake matsiyaci wallahi har yanzu bakayi arzik'in da zaka wulak'antamu ba" Fauziyya ta fad'a a fusace.

"Hahahahh keee! Har kin samu kanki kenan? 'Yar iska mai bin maza"

Hannu ta d'aga zata wankeshi da mari yayi saurin rik'ewa "kul! Karki kuskura ki fara" ya wurgar da hannunta gefe sannan ya juya ya sake kallon Mameey ya fiddo bandir na dubu ya wurga mata yace "ayi kud'in magani"

Wani damk'a da Fahad ya kai masa ne yaja kaurewar fad'a tsakaninsu,da sauri Mameey ta fara k'ok'arin rabasu Aliyu ya kai mata duka a fuska ta dad'i,da gudu Fauziyya ta fita neman taimako,Abba ya tashi shima jiri ya d'ebeshi ya fad'i.

Da k'yar wasu likitoci suka shigo suka raba fad'an,Aka kama Mameey aka bata gado itama.

Abba kuwa aka Saka mashi oxygen saboda numfashinsa baya fita da kyau.

Aliyu na shigowa gida ya rufe Janan da duka,ta fito k'ofar gida da gudu ya biyota yana duka,mutane na rik'eshi yana fad'in a sakeshi ya illatata.

Mutanen gurin kuwa sukace a k'yaleshi ai matarsa ce,ita kuwa da gudu ta fad'a gidan Asabe,yana neman shigowa tayi saurin maida k'ofar ta rufe tare da zubewa k'asa.
Sai a lokacin taji zugi a k'afarta dan har ta manta da ciwon saboda wawan dukan da yayi mata,gannin jini a k'afarta ne yasa ta k'walla ihu a take ta sume a gurin,a haka Asabe tazo ta ganta.

******
Tana farfad'owa ta ganta a kwance kan gadon Asabe.

Asabe na mata fifita Zuhra na gefenta tayi tagumi.

"Inna Asabe kinga ta bud'e idanunta"

Kallon ta tayi tana hamdala,da sauri ta tashi ta kawo mata ruwa.

Bata ma karb'a ba illa kuka da take tayi dan ta gama tsinkewa da lamarin.

Ganin kukan yayi yawa ne yasa Zuhra ta fara magana rai a b'ace.
"Wai ke Janan hawayenki baya k'arewa ne?akan me zaki zauna Haidar yana neman kashe ki?"

Bata iya cewa komai ba sai kukanta daya k'aru.

Asabe tayi Ajiyar zuciya tace "ni wallahi na rasa rashin tausayi irin na mahaifiyarsa ita take zugashi"

"Wallahi na auri Aliyu ita bata isa ta saka ya dokeni na kasa ramawa a kanta ba,duk uwar mijin data kasa rik'e mutumci ta sai ka hau ka taka,ke Janan wallahi dole ki dokasu a kotu a raba aurenku ki huta"

Sai a lokacin ta fara magana tana fad'in "idan na kai Aliyu kotu ya sakeni ina zan koma?babana ya koreni in aka raba mana aure da Aliyu bani da inda zani"

"Baki da dangi ne?"

"Muna dasu amma kinsan dangi na yanzu ba wani zumunci ake ba babu wanda zai saurareni bamu had'uwa sai in har wata sabga ta had'a da kamar wuya yanzu in tunkaresu da matsala ta su karb'a"

"To gaskiya kije ayi miki tsakani dasu a kotu ina dalili,dubi yadda kika koma fa,wanda ya dad'e bai ganki ba bazai shaidaki ba".

**********

Ganin yadda yake neman sark'ewa yasa Mameey ta tashi da sauri zata fita kiran likita.

Hijabinta ya rik'e yace " karki kira kowa"

"Meyasa?" Ta tambaya tana kuka.

"Saboda mutuwa zanyi" ya fad'a yana murmushi sannan ya saka hannu a aljihun wondonsa ya d'akko takarda ya mik'a mata.

"Ki bawa Janan wannan,ki fad'awa Fahad da Fauziyya na yafe musu suma su yafe min,sannan dan Allah karki raba kan 'ya'yana duk runtsi duk wahala ki zauna dasu ki k'ara musu darasi akan zaman duniya"

"Yallab'ai dan Allah ka daina fad'ar haka,ita mutuwa ko wanda yake lafiya k'alau tana d'auka"

"Baki san irin azabar da nake ji ba ni kad'ai na san yadda nake ji"

Ranar dai haka Abba ya rik'a shan azaba bai ma san wake kansa ba,k'arfe 11 na dare Allah yayi masa rasuwa.
_(wayyo Allah tashin hankali wanda ba'a sa masa rana,karkuso kuga yadda Mameey ta rik'a suma tamkar itama bazata rayu ba)._

Kafin safiya dubban mutane sun jin labarin mutuwar Alh Hashim,wasu suna Allah wadarai da hukuncin da aka masa a kotu wanda yayi sanadiyyar mutuwarsa wasu kuma suna cewa alhakin Aliyu ne.

A gidan mak'ocinsa aka yi masa sutura, wanda yake side d'insa, Alhaji Ibrahim yana aiki a wani babban kamfanin saida motoci mutum ne mai karamci,side d'aya ya warewa su Mameey suka zauna zaman makoki tunda gidansu an k'wace musu.

Kwana biyu da rasuwar Abba Mameey tace su tafi su bar garin bata son zama duk da ana ta zuwa ta'aziyya ta dai fad'awa matan gidan ta wakiltasu su karb'i ta'aziyyar Abba.

Babu yadda Alh Ibrahim baiyi ba akan su zauna amma tace a'a duk da dai bata jindad'i kuma bama ta san ina zasu nufa ba.

Haka suka had'a duk kayansu na amfani suka tari taxi da sassafe suka tafi suna mai yiwa iyalan Alh Ibrahim godiya akan karamci da suka musu,sannan ta bawa haj kaltume uwar gidan takardar da Abba ya bada tace idan Janan tazo a bata a kuma bata hak'uri akan abinda ya faru.

Duk wannan abin da ake daga Janan har Aliyu babu wanda ya san wainar da ake toyawa dan a kwanaki biyun babu inda ya fita.

Janan kuwa dama daga d'aki sai band'aki saboda k'afarta ba lafiya bakuma ta jindad'i a kwanaki biyun nan.

Ranar da Aliyu ya fita ganin gidan yana son ya tsara yadda zasu zauna a ranar yaga mutane a k'ofar gidan mak'ocin Abba,koda ya tambaya sai aka ce masa Alh Hashim ne ya rasu yau kwana uku kenan kuma iyalansa sun bar garin.

Bai samu damar shiga gidan ba saboda yadda yaga mutane na masa gani-gani,babu shiri ya dawo k'auyen gaba d'aya jikinsa ya mutu duk da yana ganin hak'k'insu ya kashe Abba ya bi Hafsa da baba.

A tsakar gida ya tarar da Umma tana ta fito da kaya tana sakawa a bakko.

"Ya akai? ka kawo mai motar da zamu tafin?"

"Umma a bari sai gobe kinga yanzu yamma ta kusa"

"To a wane dalili kasan tafiyar ba yau ba kasa muke ta had'a kaya tun safe,to wallahi baka isa ba"

"Umma naga bama su kwashe komai ba,kayan d'aki da sauransu"

"Tunda kaga sun bari ai namu ne an hutar da kai siyan wasu"

Ganin ranta ya b'aci sosai yasa yace "to Ku shirya bayan sallar magriba zamu tafi"

"Allah ya kaimu" ta fad'a tana cigaba da had'a kayan.

Shi kuma ya wuce kewayensa.

A zaune ya tarar da ita tayi uban tagumi da duka hannunta biyu.

Tunda ya aureta bata tab'a bashi tausayi kamar yau ba,yana so ya fad'a mata rasuwar Abba amma ya kasa saboda da ciwo ace mahaifinta an kaishi har kuma kwana uku bata ganshi ba bataji labarin rasuwarsa ba.
_the same abinda ya faru dani_ ya fad'a a zuciyarsa.

"Ki shirya zamu bar garin nan mu koma Kaduna yau"

Gabanta yayi mummunan fad'uwa idonta ya ciko da hawaye tace "kana nufin gidanmu?ina su Abba suka koma?"

"Ba cewa nayi kimin tambaya ba umarni ne na baki" ya fad'a a dake,dan ji yake kamar yayi mata kuka.

Sauri yayi ya fita ya bar mata d'akin.

Ana yin sallah kuwa ya shigo yace su fito ,haka ta janyo trolley d'inta tana d'angasa k'afarta, fad'uwar gabanta ya tsananta.

A k'ofar gida ta had'u da Asabe "saura ki yada zumunci Amarya"

"Insha Allah zan rik'a ziyartarki bazan tab'a mantawa dake a rayuwata ba"

"Ki yawaita addu'a duk inda kike kuma a duk inda kika tsinci kanki karki manta addu'a"

"Insha Allah"

Wasu magunguna ta mik'o mata k'ulli biyu tace "wannan mai maik'on kina shafawa a ciwon,shi kuma na garin maganin na duk wani ciwo ne,ki kula da kanki,Allah ya kiyaye hanya ya kuma tsare ki"

"Ameen nagode sosai" ta fad'a ta d'aure maganin a zanenta

"Karki damu" Asabe ta fad'a cikin damuwa.

Duk abinda sukeyi Aliyu yana tsaye jikin motar yana kallon ta.

Su Umma da Ummi na fitowa tayi saurin zuwa ta shiga motar suka tafi.

A motar ma babu abinda Umma keyi sai habaici da zagin Janan tamkar wata sa'arta,ita kuwa tayi shiru tama rasa me yake mata dad'i.

Tun daga nesa ta hango canopy taji gabanta yayi mummunan fad'uwa duk da ba a k'ofar gidansu bane.

A zuciyarta tace _to ko mamansu bilkisu ta rasu ne dama ba cikakkiyar lafiyane da ita ba._

Suna tsayawa a k'ofar gate d'in gidan ta kasa fitowa,wai gidansu ne ya zama mallakin Aliyu,gani take tamkar a mafarki.

"To ki fito mana 'yar dad'i mota" Ummi tayi maganar tana yatsina fuska.

Jikinta a sanyaye ta fito tana k'ara kallon rumfunan da aka kafa a k'ofar gidan Alh Ibrahim.

Hasken lights d'in daya cika layin ne yasa Baita ya hangota, da sauri ya taso ya taho,lokacin ana sauke kayansu a mota.

Yana zuwa gabanta ya fashe da kuka.

Ita duk a tunaninta ko korar Abba daga gidan ne ya sakashi kuka dan haka tace "Baita pls ka bar kukan nan"

Cikin kuka yace "Janan wallahi ban san Abba ya rasu ba sai yau d'innan bamuyi adalci ba amma kuma ba laifinmu bane office aka ce dole sai mun koma"

Tunda ya fara maganar Janan ta saki baki tana kallonshi bata ma fahimtar me yake fad'a sosai.

Aliyu sadda kai k'asa kawai yayi yayinda Umma da Ummi ke mamaki.

"Wa.....wan...wane Abba?" Ta fad'a bakinta na karkarwa.

Jin haka ne ya sakashi yin shiru dan tunda yaji haka ya san bata san mutuwar ba.

Wuyan rigarsa ta shak'a tace "Abbana?wallahi k'arya kake yana raye bai mutu ba"

Dariya tayi irin ta zautattun nan sannan ta sake shi ta b'ata rai,sai kuma ta ruga da gudu ta fad'a gidan Alh Ibrahim d'in ta manta ma da ciwon k'afarta.














_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah*_πŸ‘„


```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```



*_'Kawata Amarya Khadija,a gaskiya abinda kika zo min dashi yau bazan iya musulta farin cikin danaji ba,har na cire ran zan samu saboda yadda nasha nema na rasa,ashe abin yana ranki har sai da kika samomin,zazzafar k'auna ce wannan,na yarda ke mai k'auna ta ce,fatana Allah ya saka miki da gidan aljanna ya biya miki dukkanin buk'atunki ya k'ara dank'on k'auna tsakaninki da maigidanki,ya k'ara dank'on zumunci tsakaninmu._*
```Nagode matuk'a```



26

A babban falon gidan ta tsaya tana zazzare ido tana kallon mutanen dake zaune.

A hankali ta fara ganin ko ina yana juya mata,cikin kuka ta furta "Mameey kina ina?ki fito ki fad'a min gaskiya Abba na san bai mutu ba" sai kuma ta rik'e gashinta ta sulale k'asa.

Salati aka hau yi,haj Mariya tayi saurin zuwa suka kamata aka yi d'akin bilkisu da ita.


*_Few minutes ago_*

Idanunta ta bud'e gaba d'aya tana kallon mutanen dake kanta.

Wani k'ara data k'walla sai daya gigitasu dukansu.

Ta mik'e tana neman ta ruga sukayi saurin rik'e ta,wani fizgewa da tayi Alh Ibrahim shi kad'ai ya iya rik'eta gam,aka kira likita yayi mata allurar bacci.

Idonta k'yar akan likitan har bacci ya d'auketa.

Kallon Alh Ibrahim yayi yace "tana neman rasa tunaninta fa ya kamata ana kwantar mata hankali"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,ya Allah ka bamu ikon ceto rayuwar yarinyar nan"

"Ameen" haj Mariya ta fad'a cikin damuwa.

Sallama sukayi da doctor ya rubuta wasu magungunan da zata samu relief sai kuma na ciwon k'afar tata,sannan yace zaizo washe gari ya cire mata bandajin goshin nata.

*******

"Wai meke damunka Aliyu?naga duk kabi ka shiga damuwa akan waccan banzar yarinyar"

Ajiyar zuciya yayi yace "Umma wallahi ina mamakin rasuwar mahaifin Janan"

Mtsssw taja tsaki cikin b'acin rai tace "to ko shine Alh Rabe iya abinda zakayi kenan,mutumin daya kashe maka mahaifi da mata har ka ji tausayinsa,ai yanzu lokaci ne daya kamata ace muna farin ciki"

Shi dai bai ce komai ba illa kanshi kawai daya dafe "ina son dama kazo ka nunnuna mana abubuwan da bamu Sani ba,sannan kana sane da cewar wani satin za'a d'aura aurenku da Zuhra ko?"

Baice komai ba kawai tashi yayi yana fad'in "muje na nuna muku" ta lura dashi sarai akan damuwar daya sakama kanshi amma sai ta shareshi kawai.

*******

Janan sai da tayi sati guda tana hauka-hauka sannan Allah ya bata sauk'in abin.

Yanzu ma tana zaune kamar ko yaushe tana ta kuka ,Bilkisu na gefenta tana bata hak'uri.

Haj Mariya ce tayi sallama ta shigo "Janan kukan ne har yanzu"

Zama tayi kusa da ita ta dafa kafad'arta tace "Janan Abbanki addu'a yake buk'ata ba kuka ba,ki Sani wannan kukan da kike yi kina saka masa rad'ad'i ne"

Cikin kuka tace "ina kukan takaicine,nabi son zuciya nayi abinda mahaifina baya so Ashe ajalinsa na janyo masa,ina dana sanin k'in bin maganarsa da nayi gashi har ya rasu bai bud'i baki yace Janan na yafe miki ba,sannan su Mameey sun tafi ban san ina suka shiga ba,taya bazan yi kuka ba,ku barni inyi dan Allah"

"Kiyi hak'uri Janan haka Allah ya k'addara"

"Ban san k'addarar mutuwar Abba da rashin su Mam.........." Da sauri Bilkisu ta rufe mata baki tana fad'in "kina addu'a Janan"

Jiki a sanyaye haj Mariya ta mik'a mata takardar tace "gashi inji Mameey tace Abba ne yace a baki"

Karb'ar takardar tayi ta kwanta ta cigaba da kuka,su kuma suka tashi suka fita dan ta samu damar karantawa a nutse.

Sai da tayi kuka sosai ta samu nutsuwa sannan ta ware takardar ta fara karantawa.

_Zuwa gareki 'Yata Jannah._
_Na san bazaki riski wannan takarda ba har sai na koma ga Allah, lokacin da zaki karanta na san zaki karantane kina mai zubda hawaye tare da nadamar k'untata min da kika yi na auren wanda ba zab'ina ba._

_Janan duk da na san bakya jin magana amma ban d'auki abinda kika yi a komai ba sai k'addara kuma babu yadda muka iya da hukuncin Allah._

_Janan ina mutuk'ar son ki ban tab'a jin sonki ya ragu a raina ba,ku uku Allah ya bani dan haka nafi son Ku fiye da komai a rayuwata,duk ranar da nayi muku wani abu kukaji haushi a ranar bana runtsawa saboda yadda nake jinku a raina yafi k'arfin wasa amma ina dannewa ne saboda in muku tarbiyya mai kyau bana son na sangartaku_.

_ko da kikaga ina korarki idan kinzo gida dan in hukuntaki akan laifin da kika yi ne,daga ke har Mameeyn naki na san baku tab'a hango abinda na hango muku ba,ba wai ina k'yamar talaka ba a'a ina gudun irin cin mutumci nasu da zarar ka mayar dasu inuwa,bance ko wane talaka haka yake ba,ban kuma ce daga yanzu Ku rik'a k'yamar talaka ba,a'a ina son kuyi bincike sosai akan duk abinda kuka saka a gaba._

_Sannan ina son sanar dake cewar Salman bai mutu ba,nace miki ya mutu ne saboda in fitar dake daga damuwar da kika shiga kuma in mantar dake shi,tabbas Salman mutumin kirki ne Janan, dan ko dana rabaku dashi bai tab'a min koda kuwa kallon banza ba har ya bar garinnan,na hanaki aurenshi ne saboda baya da asali Janan amma ki Sani Aliyu yayi min babbar illa,sannan ni ban san inda dukiyarshi take a gidana ba saboda ban san inda aka sare bishiyar da yake fad'a ba,gadonku yana hannunsa idan har ya cinye muku Allah bazai barshi ba,sannan ki k'ara sanar masa ina nan ina jiran ranar da zamu tsaya ni dashi a mana hisabi dan ban yafe masa ba._

_Ina son ki nemi gidan wani Malam Lado a cikin katsina yake a wata unguwar_ ```filin samji``` _yake kice masa yayi miki kwatancen gidan wani wanda ake kira da Alto sarkin gini a cikin garin Nijar ban san wane gari bane,in kikaje mutumin ko bai biyoki ba zai fad'a miki inda bishiyar da suka sare take don shine da yaransa sukayi aikin gidan duka,ban fad'awa kowa ba koda a kotu domin na san shari'ar ha'inci aka yi ban fad'awa kosu Fahad ba ke na zab'a na kuma fad'a miki kije ki farauto muku 'yancinku ki amso muku dukiyarku Janan kena wakilta dan haka tafiya ta kamaki da zarar kinga sak'on nan karki zauna_.

_daga k'arshe ina muku fatan Alkhairi a sauran rayuwarku,ina fatan zaku cigaba da rayuwa cikin jindad'i da amincin Allah, na yafe miki duniya da lahira nima ki yafe min 'yata._

Kuka har sark'e mata ya rik'a yi,tanayi ta magana tana fad'in "baka min komai ba Abba na yafe maka Abba"

Kasancewar gidan babbane suma basu jiyo kukanta har tayi ta gama ta kwanta lamo tanayin kukan zuci.

Shigowar Alh Ibrahim ce yasa ta d'ago kanta tana hawaye.

" 'yata kukan ya isa haka,mahaifinki kowa ya shaida shi mutumin kirki ne,har aka kaishi makwancinsa mutane suna kukan rashin adali,yana kwance cikin jindad'i amma ke kina d'aga masa hankali,kina son ya rik'a jin azaba da rad'ad'in kukan da kike masa"
Ta girgiza kai tana goge hawayen wani na k'ara zubowa.

"Abu d'aya zaki masa wanda zaiji dad'i ya kuma san ya haihu shine addu'a karkiyi wasa da yi masa addu'a kinji" ta d'aga kai alamar to.

Haka ya cigaba da mata nasiha cikin rarrashi.

********

Da sallama ta tura k'ofar d'akin ta shiga.
"Dama Umma tace kina nan kina kuka" Raihan ta fad'a lokacin da ta k'araso jikin gadon ta zauna.

Wasu sabbin hawaye ne suka fito daga fuskar Lubna ta saka hannu ta goge sannan ta fara magana.
"Dole duk ranar dana tuno Janan nayi kuma,ke! na san Janan bazata tab'a gogewa a zuciyata ba"

"Hakane Lubna wallahi ni kaina ina jin Janan a cikin jinina lokacin guda na shak'u da ita yanzu haka Ummina fad'a take min akan meyasa ban kawota suka cigaba da zama a gidanmu tunda Akwai extra rooms"

Lubna na hawaye tace "nifa saboda Janan daddy ya hanani fita ko ina dan kar inje gidansu,wallahi ina dana sanin barin Janan tayi soyayya da Aliyu,Ashe ba alkhairi bane shiyasa har mukayi fad'a da ita a kanshi,tunda yarinta muke tare da Janan tare mukayi primary, secondary skul sannan muna tare a high institution ma amma ace rana d'aya na barta ta barni,saboda Janan bata da lafiya nak'i cigaba da karatu har sai data warke muka fara poly tare amma ace yau an rabamu mahaifina ya mana tsakani da ita" kuka sosai take Raihan ta rumgumeta tana rarrashi.

Turo k'ofar da aka yi ne yasa Raihan ta juya tace "kinga Umma kukan take"

"Aini har na gaji da kukan Lubna ki rarrasheta dai ke k'ila taji maganarki"
Fita tayi taja musu k'ofar.

"Lubna dan Allah ki bar kukan nan"

"Dole inyi kuka Raihan,Abba ya rasu ban je musu gaisuwa ba gashi ance sun bar garin ya zanyi"

Hmmm "hak'uri mana Allah ya Sani ba da gangan mukayi ba,nima ban san rasuwar Abba ba sai jiya kuma yau ina zuwa na tarar wai Aliyu ne a gidan,dana fito na tambayi wani a waje sai yace sun bar garin kuma bai san inda suka koma ba"

"Kinji fa,gaskiya Aliyu azzalumine Raihan wallahi sai yanzu na k'ara dana sanin k'in fad'awa Jalal da mukayi na san da yayi wani taimako"

"Hakane gaskiya bamu kyauta ba,jiya ma munyi waya dashi ya tambayeni tana zuwa skul nace masa eh ni ban san ta ina zan fara masa bayani ba,amma yace min sai upper week zai shigo Kaduna"

"Idan ya shigo kawai mu sanar dashi dan k'aryar ba inda zata kaimu"

"Yawwa credentials d'in Janan komai da komai yana hannunki ko?"

"Eh"

"Ki bani in na shiga skul gobe zanje in mata deferring dan bana son ta rasa karatunta"

"Amma Raihan meyasa bazaki bari muga yadda Allah zaiyi ba ko zata dawo"

Hmmm "Lubna mun kusa fara exam yaushe kike tunanin zata iya covering bayan tana cikin damuwa koda ta dawo d'in ma kawai ki bani wannan itace hanya mafi sauk'i"

Tashi tayi a sanyaye ta d'akko mata ta bata,sukayi sallama ta tafi.

********

Yana kwance yana juyi akan makeken gadon Abba wanda a yanzu ya zama mallakinsa.

Hankalinsa gaba d'aya a tashe yake,yau satinsa biyu kenan bai saka Janan a idonsa ba,bai tab'a tunanin ta shiga ransa ba sai yanzu da bata gabanshi, da kuwa gani yake kawai ya tsaneta baya son ganinta amma yanzu babu abinda yake son gani sama da ita.

Yaje gidan Alh Ibrahim har sau biyu amma ko farfajiyar gidan maigadi ya hanashi shiga bare ya samu ganin Janan.

Shi unguwarma ta ishesa babu wanda yake mu'amala dashi kowa ya tsaneshi,ko a masallaci mutane basa musabaha dashi.

Kodan ansan shi ada *Direban* gidan ne shiyasa suke masa gani-gani.

_ni kuwa komai zai faru ba zan bar gidan gadonmu ba saboda anan na girma,in basuyi mu'amala dani ba wasu zasuyi._ ya fad'a a zuciyarsa.

Ummi ce ta turo k'ofar cikin sallama ta shigo ta zauna.

"Lafiya?" Ya fad'a yana kallon ta.

"Yaushe zan koma makaranta kuma Umma tace zaka koya mana mota tunda akwai motoci"

"Bazan koya miki ba yarinya tun kafin ki waye har kinsan k'arya" ya fad'a rai a b'ace.

Tashi tayi tana turje-turje ta fita.

Sai gata sun dawo da Umma.
"To mara kunya naji sak'onka"

Tashi yayi zaune yace "Umma wane k'aryar taje ta fad'a miki"

"Maganar koya mota dole ne a koya mata itama"

"Umma....."

"Rufamin baki kabi Umarnina kawai"

Knocking suka ji ana tayi dan haka duka sukayo waje dan sunsan babu wanda zai nemesu to waye haka?.

Yana bud'e k'ofar idonsa ya dira akan nata,gabanshi har fad'uwa yayi yadda yaga idanun nata kamar sun juye.

"Ohh kece kika dawo" Umma ta fad'a tana k'ok'arin fitowa.

Bata ma kalleta ba kawai tace "ba dawo wa nayi ba nazo karb'ar takardata ne"

"Ina nufin ka sake ni Aliyu" ta fad'a idanunta a cikin nasa.

"Kinzo a dai-dai gab'ar daya dace,dama saki ai ko baki nema ba zai miki shi dan haka na baka damar ka sake ta saki uku a take anan"

Ya kasa d'auke idonsa akan Janan sannan ya kasa magana.

"Ka saketa nace"

"Umma bazan iya ba,idan na saki Janan ina ganin babu adalci a lamarin"

"K'arya kake Aliyu" Janan ta fad'a tana nuna shi da yatsa tana k'ara fad'in "dole ka sake ni wallahi kai baka isa kayi min illa ba kuma in cigaba da zama da kai,har yaushe kasan adalci ai baka da adalci kai azzalumi ne" ta k'arasa maganar tana kuka.

Umma ta kalleshi cike da mamaki tace "ince ka saketa amma kana ce min bazaka iya ba"

"Kiyi hak'uri Umma bazan iya sakinta ba"

Sakin baki Ummi tayi tana mamakin yayan nata,Umma kuwa k'ara fad'i take wallahi sai ya saki Janan yana fad'in bazai iya ba.

Cikin matsanancin kuka tace "kayi shari'a da mahaifina kaci galaba to ka sani a wannan karon ni zanci galaba zamu tsaya gaban alk'ali da kai dole ne ka sake ni, ka jira sammaci daga kotu"

Da sauri ta juya ta tafi tana cigaba da kukan tare da k'udiri da yawa a kanta.






_Sadeey S Adam✍_
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁


_*SaNaz deeyah*_πŸ‘„




```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```


_*Zuwa ga readers naji k'orafe-k'orefenku game da Aliyu da Abba,ina son ku gane cewa a halin yanzu is hardly ayi shari'ar gaskiya,wani yana da gaskiya ake danne masa hak'k'i sannan shaidun Aliyu sun shaida mahaifinsa yana da d'unbin dukiya uwa uwa uba gonaki ,da filayensa wanda duk takardun sun salwanta a gidan tunda ba'a san inda suke ba wannan shine dalilin daya saka aka bawa Aliyu dukiyar Abba wanda k'ilama yafi Abba dukiya cox kunsan 'yan k'auye akwai hana kai a tara dukiya,ina son duk wanda ke karanta labarin ya karanta a nutse karku rikice pleaseπŸ‘*_

_Godiya mai tarin yawa tare da fatan alkhairi gareku masoyana._


27

Tana fita Umma ta kalleshi tace "wallahi idan baka bita ka sake ta ba ban yafe maka ba,kawai muna zaman lafiya a nemi maidamu kotu"

Shiru kawai yayi baice komai ba.
"Zaka saketa ko saina tsine maka"

"Umma........"
"Ka saketa nace"

Jikinsa a sanyaye ya fita,a tsaye ya ganta jikin gate d'in tana goge hawaye.

Shima hawayen yaji suna k'ok'arin zubo masa yayi saurin dakewa yace "ba sai na wahalar dake ba wajen zuwa kotu, kije na sakeki saki d'aya"

Kallon shi tayi wasu hawayen na zuba a idonta tace "dama ka k'ara biyu dan na gama zama da

Please Login or Register in order to submit comment