You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


A haka sauran 'yan sandan suka kamasu suka shigar dasu mota.

Shi kuma ya tsugunna a gabanta ya k'ura mata ido,tayi saurin sauke k'wayar idonta k'asa.

"Ai na fad'a miki nan gurin akwai had'ari kika k'i yarda"

'Dago idanunta tayi tana kallonshi tana tunanin waye shi yaushe ya fad'a mata hakan.

"Nine mai napep d'in daya kayo ki nan d'azu"

Ta d'an zare ido cike da tsoro mai had'e da mamaki.

Murmushi yayi yace "ni d'an sanda ne mai rik'e da muk'amin _dsp_ kullum da dare misalin k'arfe tara na kan zama d'an adaidaita saboda shine hanya mafi sauk'i da nake kama masu laifi.

"lokacin Dana kawo ki nan hankalina yak'i kwanciya musamman dana ganki da ciki,kai tsaye na nufi gida na sanarwa mamana sai tace in dawo inga halin da kike ciki idan har da taimako to in taimaka miki,a lokacin na tafi gida na nayi wanka na saka uniform sannan na kira yarana muka taho sai gashi na tarar dake a wannan hali"

Shiru tayi bata ce komai ba,ya sake fad'in "ki tashi muje gida ki kwanta da safe sai a kawo ki tasha"

Tayi saurin girgiza kai tace "a'a nagode ka barshi kawai"

"Umarnin mamana ne dan Allah karki musa wallahi mu ba macuta bane"

Da k'yar ya lallab'eta suka tafi gidan.

Suna shiga falo Maman nashi ta rufe littafin hannunta tana fad'in "da fatan dai komai lafiya Namijin"

Murmushi yayi yana fad'in "Alhamdulillah Mammy gata na kawo ta ta kwana anan Kausar sai ta kwana a d'akinki ko"

"Eh Yaya"

Da sauri 'yan matan suka taso suka rik'eta.

Jidda tace "sannunki ya sunanki?"

Bata amsa ba sai da ta gaida Mammy sannan ta zauna a k'asa.

"Ki tashi ki zauna kan kujera" laila ta fad'a.

Kausar tace "dan Allah ki zauna"

Sai da Mammy ta saka baki sannan ta zauna dan duk a d'arare take.

Kusan minti talatin suna hira amma ita bayan gaisuwa da gabatar da sunanta babu abinda ta sake cewa.

Ja'afar ne ya tashi ya k'arasa gaban Mammy ya durk'usa yace "Mammy zan wuce gida ki samin albarka"

Kanshi ta dafa tace "Allah ya albarkaci rayuwarka ya baka sa'a a duk inda kake ya kare min kai Namijin duniya"

"Ameen Mammyna nagode"

Ya tashi zai wuce sukayi masa sallama tare da fad'in ya gaida Aunty farha(matarshi).

Rayuwar tasu sai tayi matuk'ar burge Janan.

_*Washe gari*_

Ta gama shirinta tsaf suka bata kaya ta saka amma tak'i karb'a ta mayar da nata.

Mammy tace "da munsan bazaki karb'i wasu ba da an wanke miki"

"Babu komai hakan ma nagode"

"Da fatan zaki rik'e zamunci dan yanzu mun zama d'aya"

"Insha Allah"

"Idan kin haihu ki sanar damu wlh zamuzo har katsina"

"Da iznin Allah"

"Zan rubuta miki numbers d'inmu a paper tunda kince wayarki ta fad'i a mota kuma an kira a kashe" kausar tayi maganar

"Okay ba damuwa nagode"

Suka rubuta mata ta karb'a a lokacin ta haddace number Jidda dan itace babu wahala,da zumar tana fita ta yaga takardar kawai.

A falo suka tarar da Ja'afar a zaune ya hard'e k'afa ransa a b'ace.

"Lafiya kuwa?" Mammy ta tambayeshi.

"Mammy na gaji da halin farha daga bata labari shikenan ta d'aga hankalinta wallahi ko runtsawa bata barni nayi ba"

"Ka kai Janan tasha ka dawo sai muyi maganar"

Tashi yayi ya fita suka bishi.

Suna cikin tafiya tace masa "dan Allah kayi hak'uri ka daina kai matarka k'ara gurin iyayenka saboda zaka ja mata k'iyayya a gurinsu"

"Da kinsan irin laifukan da take min ina k'yaleta da baki ce haka ba,sai kace ba ita ta rik'a nace min ba har na aureta"

Murmushi tayi mai had'e da hawaye tace "wannan shine abinda kullum mijina yake fad'a wanda ban d'auka son da nake masa zai zama k'iyayya ba dan Allah ka sassauta ranka akan matarka"

Ganin hawaye a fuskarta yasa yace "shikenan na d'auki shawararki na daina insha Allahu"

Har tasha ya kaita ya biya kud'in mota sannan ya mik'o mata 5k yace tayi tsaraba tace a'a da k'yar sai da mutane suka saka baki ta karb'a tayi godiya"

Sai da har motarsu ta tashi sannan ya juya ya tafi.

Yana komawa gida ya tarar dasu a zaune sunyi zuru-zuru.

"Ya naganku wani iri" Ja'afar ya tambaya bayan ya zauna.

"Wallahi duk kewar baiwar Allah nan nake da alama akwai damuwa a tattare da ita dan kausar tace data tashi tsakar dare ma ta ganta a zaune tayi tagumi"

"Nima na fuskanci tana da damuwa Mammy amma kinga bazai yuwu mu tambayeta ba bayan taimakon gurin kwana muka mata amma wallahi a raina ta kwana"

"Yaya ka duba fa ka ganta 'yar k'arama da ciki anya kuwa ba cikin shege tayi ba shine ta gudu daga gidan iyayenta?" Laila tayi maganar.

"Gaskiya nima ina tunanin haka" Jidda ma ta fad'a.

"Tace min tana da miji amma tana shan wahala a gurinsa"

"Kai ban yarda ba,Namijin dan Allah kabi bayanta ka binciko mana ko wacece ita idan na mu taimaka ne saimu taimaka"

"Insha Allah zanyi bincike akanta dan nima ina tausayinta,Mammy jiyafa daga bawa Farha labari shikenan ta rik'a cimin mutumci wai son Janan d'in nake matar da take da ciki"

"To idan ma ka sota sai me ni wallahi yarinyar ta shiga raina ai tafi Farha"

"Wallahi tana da kirki da shiga rai" Laila tayi maganar.

"Ku dai tayani addu'a Allah yasa na nemota cikin sauk'i"

"Ameen" duk suka amsa.

*******

Kwananta biyu a katsina cikin ```filin Samji``` tana neman gidan Malam lado amma kowa bai sani ba.

A rariya take kwana dan bata san kowa ba.

Kud'in gurinta kuwa duk ya k'are saboda zarya adaidaita ga abinci ga ruwa ga magani data siya.

A rana ta uku Allah ya bata ikon zuwa gidan,wani bawan Allah ya taimaka ya rakata har k'ofar gidan.

Gidane na jar k'asa da dannin kara amma kuma family house ne irin na k'auye dai da suke.

Cikin sallama ta shiga b'angaren farko da ta gani.

Bayan sun gaisa ne tace musu "dama ance min nan ne gidan Malam lado"

"Eh nan ne nine babban d'ansa, duk iyalansa anan suke"

"Yawwa Alhamdulillah dama gurinsa nazo"

Kallon juna sukayi da matar cike da mamaki ya kalleta sannan yace "ai Malam ya rasu shekaru uku da suka wuce"

Jikinta a sanyaye tace "Allah sarki Allah yaji k'ansa ya masa rahama"

"Ameen dan son annabi" suka amsa

Ta d'anyi shiru sannan tace "dama nima mahaifina ne da zai rasu yace in nemi gidan Malam lado zai min kwatancen gidan wani alto sarkin gini wanda yake a k'asar Nijar"

"Allah sarki Allah ya gafarta masa"

"Ameen" ta amsa.

Shiru ne ya biyo baya,ganin basu sake magana ba yasa ta sake cewa "idan da wanda ya sanshi dan Allah a kwatanta min"

"Wallahi bamu sani ba da yake yana aiki da yawa da mutanen Nijar amma mu da yake munfi k'arfi a kasuwa ba harkar gini ba"

"Yanzu duk gidannan babu Wanda ya sanshi"

"Eh to muje in tambayi sauran"

Tare sukaje aka tambaya babu wanda ya gane shi hatta mak'ota da yake mu'amula dashi sunce kawai dai sunsan yana zuwa amma basu san inda yake ba tun bayan rasuwar Malam lado bai sake zuwa ba.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un na shiga uku ni Janan ya zanyi Abba kayi hak'uri kana ji wai babu wanda ya sanshi"

Zama tayi a k'asa tana rusa kuka tana fad'in ta shiga uku.

Hak'uri sukayi ta bata ta tashi kawai ta tafi dan bata son ganin gidan Malam lado ma.

Tafiya kawai take tana magana tamkar zautacciya.

"Anan zan k'arasa rayuwata to ina zanje duk inda naje ma ba karb'ata za'ai ba Mameey ta gujeni zama zanyi har Allah yayi ikonsa a kaina Aliyu kuwa na san yaci bulus kawai"

Tana tafiya tana ta zantuttuka a haka har ta fita daga unguwar ta fara shiga jeji gidajen unguwar ba yawa sai kango a can k'arshe.










_Sadeey S Adamโœ_
๐Ÿ๐Ÿ๐Ÿ
*DIREBAN GIDANMU*
๐Ÿ๐Ÿ๐Ÿ



_*by SaNaz deeyah*_๐Ÿ‘„



```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```



_*Ummi kina burgeni,d way yadda kike magana akan novel d'in nan na kanyi dariya ko ina cikin fushi๐Ÿ˜ƒUmmin Aliyu๐Ÿคฃtnx 4 d support*_



32

A dai dai kangon ta tsaya ta kalli ciki taga babu alamar datti.

Shiga tayi ta lek'a ko ina taga babu alamar 'yan shaye shaye na zuwa gurin.

'Dankwalinta ta cire ta zauna wasu hawayen na zuba a kuncinta.

_Ashe ma 70k d'in da nake tattali har ita sai da akaje banki aka karb'e,Allah ka saka min bazan tab'a yafe wannan zaluncin ba._


_Washe gari_

Bata farka ba sai da taji rana a tsakiyar kanta da yake kangon ba rufi.

Tashi tayi tana murza ido bacci har yanzu bai isheta ba ga uwar yunwa da takeji.

'Dan kwalinta ta d'ora sannan ta fito waje,unguwar tamkar babu mutane.

Zaninta ta kunce ta fiddo 2k d'in data rage mata ta fara tunanin me zata saya kafin wani lokacin.

Gari da suga ta tuno dan suna sha a gidan Aliyu duk da dole ce tasa take sha har yanzu bata saba ba.

Haka tayi ta tafiya a k'asa da k'yar ta samu wani guri ta sayi kofin roba da plate da cokali da buta da dai d'an tsince tsincen da zata buk'ata sai ta sayi gari rabin kwano da suga kwata.

Bayan ta dawo ta tsaya a wata borehole tayi pumping na ruwa a jerrycan(keg) ta tafi dashi.

Ta fara shan garin kawai taji anyi sallama a kangon
Gabanta yayi mummunar fad'uwa da k'yar ta iya amsa sallamar.

Farar dattijuwa ce,gashin girarta ma fari sol ne,fatarta duk ta yak'une saboda tsufa.

Kallonta Janan take har lokacin data samu guri ta zauna.

"Sannu baba"

"Yawwa 'yata sannu,ke kuwa meya kawoki kika zo kika zauna a kangonnan ga tsohon ciki?"

Murmushi tayi mai d'auke da hawaye tace "karki damu Iya nan ma ina jindad'in zama tunda a rufe yake"

"Ina rufuwa bayan sama a bud'e yake ga damuna tana shirin zuwa"

"Karki damu Iya"

"Yarinya ke kuwa meyasa kikayi cikin shege da k'uruciyarki?"

Jin haka ne yasa tayi saurin mik'ewa tsaye ta kalli tsohuwar tace "idan cin mutumci ya kawoki nan ki gaggauta fita,to waima ina ruwanki dani da har kike kiran cikina shege instead of ki tambayi ina mijina,bana son kowa ya sake shigo min rayuwa ki fita ki bani guri"

Tsohuwar ta tashi tana zare ido tana fad'in "ni kike fad'awa haka yarinya?"

"Na fad'a d'in idan har bakija girmanki ba tabbas zanbi ta kanshi in take"

"Shikenan kije zaki gani"

Cikin tsiwa Janan tace "Alkhairi zan gani insha Allahu"

Tsohuwar na fita ta zube ta fara kuka tana fad'in "ka cuceni Aliyu Allah kayi min sakayya".

Haka rayuwarta ta cigaba da tafiya a wannan kango take kwana,tun abinci baya gagararta har yazo yanayi.

Sai ta kwana ta yini bata ci ba,wani lokacin sai dai ta shiga daji ta ciro ganye taci saboda yunwa.

Ta zama k'azamar k'arfi da yaji dan a sati sau d'aya take wanka shima sai dare take d'ora hijabin jikinta tayi sannan idan da hali ta wanke kayanta kafin asuba sun bushe sai ta saka.

Idan har baka santa sosai ba bazaka tab'a gane ita bace.

Tayi bak'i ta rame idanunta sun sake yin zuru-zuru.

Wani lokacin idan ta rasa abinci har restaurant take zuwa wanda suka ci suka rage ayi wawa ita da almajirai.

Idan kuwa taga biredi an yarda lalatacce zata d'auka ta gyara taci.

Rayuwar Janan gaba d'aya ta zama abin tausayi.

Yauma kamar kullum tana zaune da yamma a kangon lokacin anyi ruwa yayi mata dukan tsiya.

Tana zaune jikin ginin bayan an gama ruwan a fili ta furta " idan banyi mantuwa ba watan haihuwana ya kama,yanzu idan na haihu me zan sawa jaririna a jikinsa?bani da komai sai reza dana sayo gudun ta b'aci bansan tayaya ake yanke cibi ba kar in kashemu fa"

Wata zuciyartata tace _to ya zakiyi Janan mutuwarku itace jindad'in ki tunda kinga mak'otanki ma k'yamatarki suke harda wadda kikaje gidanta ta watsa miki kwata._

"Zan haihu a nan in mutu anan k'ila ma har sai gawarmu ta fara wari sannan a san mun mutu"

Ta cigaba da goge hawayen da kullum kuma ko yaushe sai ta zubar.

*********

A firgice ya tashi tare da fad'in "inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" ya dafe kai.

Raihan dake jikin mirrow tana makeup tayi saurin ajje form d'in powder ta k'araso gabanshi ta zauna gefen gadon.
"Yarima lafiya"

Shiru kawai yayi yana kallonta,ganin hankalinsa a tashene yasa ta sake fad'ar
"Pls ka fad'a min meke damunka?"

"Mafarki nayi Janan na cikin mawuyacin hali,mafarkin ya mutuk'ar tsorata ni"

Wani abu taji yazo ya tokare mata mak'oshi,ranta a b'ace tace "amma kasan mafarki ba gaskiya bane ko?"

"Hakane amma dole inje inyi sadaka"

Da sauri ya tashi ya fice ta bishi da ido.

"Lallaima guy d'in nan ya rainamin hankali satinmu biyu da Aure har ya fara min zancen wata Janan to wlh dole in yiwa tubk'ar hanci"

Maganarsu da Lubna ce ta fad'o mata a ranar da aka d'aura aurenta da Jalal.

_Raihan idan Janan ta dawo taga kin auri Jalal bazata ji dad'i ba_

_kamarya?Janan ai tayi nisa bazata dawo ba._

_oh haka kike fata?_

_ni bance ba amma ai Janan bata tab'a cewa tana son Jalal ba saboda lokacin da suka fara mutumci dashi ai batayi Aure ba kuma maganar so bata shiga tsakaninsu ba har tayi Aure, ko ta fad'a miki tana son shi?_

_bata fad'a ba amma ai mun sani ko? kuma duk wanda yaga yadda Jalal suke da Janan ai yasan suna son junansu kawai dai sun kasa furtawa ne,sannan Jalal ya fito fili ya fad'a lokacin da Janan ta bar garinnan kin san kuwa bazai tab'a manta Janan ba kuma ba zai tab'a daina Sonta ba._

_matar mutum kabarinsa Allah yayi ni zan aureshi ba ita ba dan Allah bana son irin haka Lubna._

_Allah ya baku zaman lafiya ya huci zuciyarki._

_Ameen_

Ta ja tsoki lokacin data tuna maganar.

"Allah ka k'ara nisanta Janan da ganin Jalal,ba dan na tsaneta ba sai dan kishin da nake akan Yarima Jalal"


Tashi tayi ta fita main parlor ba tare data k'arasa kwalliyar ba.

A zaune ta tarar da Adnan da Mommy suna kallon ball.

"Barka da hutawa Yaya" ta fad'a lokacin data zauna a gefen Mommy tana fad'in "Mommy sannu da hutawa"

"Yawwa 'yata" Mommy ta fad'a cikin jindad'i yau gata ga matar muskilin d'anta Jalal,abinda ta dad'e tana mafarki,dan da gani take kamar Jalal baya da rabon Aure a duniya.

Cikin fara'a Adnan yace "Matar k'anina ya gidan?da fatan babu wata matsala ko?"

"Babu Yaya" ta fad'a cikin k'arfin hali.

Ranar kuwa da fad'a suka k'are da Jalal dan daya dawo tayi masa maganar kada ya sake kawo mata maganar wata Janan tunda itace matarsa ba Janan ba.

Shi kuma yace bazai daina ba,haka tayi zuciya ta bar masa d'akin ta koma falonta ta kwana instead of ta shiga wani bedroom d'in tunda ba d'aya bane amma saboda ta san zai damu shiyasa tayi haka.

Haka rayuwarsu ta cigaba da tafiya gwanin sha'awa amma fa duk lokacin da yayi mata zancen Janan zasu kwasheta,wani lokacin ma idan yana son yin aiki dan karta takura masa sai ya fara maganar Janan.
Shi abin har mamaki take bashi wai Raihan bata son a ambaci Janan.

Adnan kuwa shima a cikin Abuja ya cigaba da aiki a wani babban kamfani.

*********

Turo k'ofar yayi da k'arfi har saida ta tsorata ta saki kayan da take ninkewa.

"Lafiya Aliyu?" Ta fad'a tana kallon sa

"Ashe dama baki da mutumci Zuhra?"

"Ni ce bani da Mutumci Aliyu?shin ance maka ni karuwa ce ko an tab'a kamani da wani?"

"Ba'ace ba amma su Umma sunce miki cous cous da miya suke so kin tashi kin dafa jollof d'in macaroni"

Ajje zanin hannunta tayi tace "Aliyu gani nayi kafi son macaroni kuma kai nake Aure ba Umma ba,sannan kitchen ai a bud'e yake meyasa bazasu dafa abinda suke so ba ai ban hanasu ba"

" k'arya kike 'yar matsiyata wadda bata gaji arzik'i ba,kuma dole ki dafa abinda nake so a gidannan"

Fuska ta rufe ta fara kukan k'arya tana fad'in "na gaji da abinda mahaifiyarka take min Aliyu,kullum idan baka nan sai ta zageni wani lokacin harda mari wai tafi son ka zauna daga kai sai ita sai Ummi a gidannan,ni kawai ka sakeni tunda hakane"

A rud'e ya fara bata hak'uri Umma ta saki baki tana kallon su ta ma kasa cewa komai.

Juyowa yayi ya kalli Umma yace "Umma tunda abin hakane kuna dafa abinda kuke so itama tana dafa nata"

"Aliyu ni kake fad'awa haka?kasan kuwa irin rashin mutumcin da yarinyar nan take min?amma kana bin bayanta?"

"To Umma ya zanyi in ba haka ba?"

"Eh lallai ka kyauta zakazo har d'akina ka sameni"

Ta fita fuuuu.

Aliyu ya kalli Zuhra yace "kiyi hak'uri na miki fahimtar baibai"

"Karka damu mijina amma ka fad'a mata bai kamata tana shigo mana d'aki haka ba saboda zata iya tadda mu a wani halin a matsayinta na surukata ai bai dace ba"

"Hakane kiyi hak'uri,itama bara naje na bata hak'uri"

Bata ce komai ba kawai ta bishi da ido.

A zuciyarta tace _Alhaki kwikwiyo ne,ni ba Janan bace,kuma yadda kika raba Janan da Aliyu haka zan rabaki dashi,dan dole a canza muku gida ki barni da mijina in wala_.


********

Bud'e idonta tayi taji garin tsit babu ko motsi daya wuce na saurayen gurin,sai kuma taurari dake baje a sama da kuma hasken farin wata.

Ji tayi cikin nata yana k'ara murd'awa,tun tana salati har ta soma k'ara tana kuka.

Babu sarki sai Allah haka tayi ta murk'usu a gurin tanajin motsin cikinta yana yowa k'asa yana komawa.

Hannunta ta dafe da bango d'ayan ta rik'e cikin,sosai take kuka da salati,nishi babu abinda bata yi.

Kusan awa d'aya sannan taji ruwa na fitowa daga gun,ta kalla sosai amma bata gane mene ba.

"Mameey kina ina kizo dan Allah kizo ki taimakeni zan mutu,wayyo na shiga uku na lalace"

A galabaice take fad'in maganganu.

Kusan awa biyu tana ta shan azaba babu alamar haihuwa,tun tana magana har bakin ya daina magana sai maganar zuci kuma,hawayen idanunta sun daina zuba sam.

Ita kad'ai ta san tsananin azabar da take ji.

Can tayi wani yunk'uri ta k'walla uban ihu tayi wani bahagon nishi ai kuwa kukan jariri ya karad'e ko ina.

A galabaice take amma hakan bai hana ta d'auki reza ba tare da tasan ya ake yanke cibi ba kawai ta saita inda ya mata ta yanke.

Jaririn ya k'ara zunduma kuka,tayi sauri d'aukar ruwa a kofi ta tsiyaya a hannu ta fara bashi kenan taji ko ina na juya mata.

Wasu hawaye masu zafi suka sauka a kuncinta.

"Allah ka raya min koma mene na haifa Allah ka bashi ikon tausayi da jink'ai kasa ya k'ato min hak'k'in......."

Bata k'arasa ba ta fara kakari,tayi saurin rik'e k'irjinta,cikin seconds da basu wuce biyar ba har anyi angama.

Anan ta zube babu motsi mini faca-faca ko ina, jariri kuwa sai callara kuka yake cikin jini abin tausayi.







_โœNa ajje alk'alamina dan in huta saboda nima tausayin ya saka hannuna yin sanyi._







_Sadeey S Adam_โœ
๐Ÿ๐Ÿ๐Ÿ
*DIREBAN GIDANMU*
๐Ÿ๐Ÿ๐Ÿ


*_by SaNaz deeyah_*๐Ÿ‘„


```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```



*_WASI'KA BU'DA'D'DIYA GAREKU MASOYANA MAKARANTANA._*
*_Gareku masoyana,ina son ku tsaya kuyi tunani akan Aliyu._*

*_Mahaifin Janan yayi abu cikin rashin sani._*
*_shima Aliyu yayi abu cikin rashin sani._*
*_Aliyu ya fara ramuwa ne ta kan Janan saboda sai abin yafi sosa zuciyar mahaifinta,sannan in baku manta ba Aliyu fa bai tab'a son Janan ba sai da mahaifinta ya rasu,in baku manta ba ya aureta ne saboda ya rama abinda aka masa._*
*_sannan duk wanda ya karanta novel d'ina HUZNUL HAYAT yasan Janan bata ga komai ba akan yadda Rabi'at taci wahalar rayuwa kuma ta mutu a wahala,wlh ni kaina akwai page d'in da idan nayi typing nazo yin editing sai nayi hawaye,kuma kirkirarren labari ne amma ina ganinsa tamkar gaske._*
*_ina son readers su gane cewa wahalar da Janan take sha akan abu biyu ne,na farko k'in jin maganar mahaifinta wanda har yace ya zame hannunsa a kanta(wasu zasu d'auki wannan a k'aramin abu amma babban abu ne),kusan irin abinda ya faru da Sumayya ta littafin MENE AIBUNA,ina son readers su gane cewa su fa iyaye ko yaya sukayi furuci na b'acin rai akan 'ya'yansu wlh musiba ne har gwamma ka lallab'asu a hankali,na biyu kuma son zuciyarta ne yaja mata._*
*_Sannan ni har yanzu fa banga wahalar da Janan kesha ba๐Ÿ˜‚karkuce SaNaz muguwa ce amma kunsan rayuwa babu yadda bata zuwarma mutum._*
*_saboda kar ayi gaba inji an fara SaNaz d'in nan.............๐Ÿคฃtun yanzu ya kama ta ko wacce tayi nazari kafin muje pages na gaba ace bana kyautawa._*



33

_Tafiya take a hankali cikin dajin cikin yanayi mai dad'i da take ji._
_Daji ne mai cike da fulawowi masu kyau da burgewa,farin gida ta hango kyakykyawan gaske,murmushi tayi cikin zumud'i ta k'arasa k'ofar gidan ta saka k'afarta zata shiga kawai taga mutum ya fito sanye da fararen kaya, ta kalleshi tace Abba dama Kaine a wannan babban gida?,murmushi yayi yace eh Jannat,Abba amma ni ina shan wahala kai gaka a cikin jindad'i,Jannat ki koma ki rik'e d'anki ki raineshi har ya girma amma karki yarda ki nuna masa Aliyu ne ubansa ki zauna dashi a matsayin wanda bashi da uba duk runtsi,koma Janan koma ga d'anki._

A firgice ta bud'e idonta,hadarin daya had'u sosai take kalla,ta juya k'wayar idonta ta kalli kangon.
_Abbana ina fatan kana kwance cikin kabarinka cikin jindad'i kamar yadda na gani a mafarkina,ya Allah ka sa haka ameen_ ta furta a zuciyarta.

Sai lokacin tunanin ya dawo mata a hankali ta tashi zaune ta kalli gabanta.

Jaririn na kwance idonsa a bud'e sai mamular leb'ensa yake yana numfashi sama-sama,jini kuwa wani har ya bushe wani kuma yana nan.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta furta lokacin da ta kai hannu ta d'auki jaririn nata.

"Bawan Allah" ta sake furtawa tana hawaye.

Mafarkin da tayi ne take sake tunawa tare da k'ank'ame jaririn data Haifa.

"Sannu yarinya" taji an fad'a.

Da sauri ta d'ago kai ta kalleta,wannan dattijuwarce dai gefenta 'yammata biyu d'aya na rik'e da bokiti da ruwan zafi da robar wanka d'ayar kuma na rik'e da ganyen carbi da wani bokitin cike da ruwa shima.

Mamaki kawai take to taya ma akai ta san ta haihu da har tazo?.
Me ma ya sake kawota bayan sunyi Baran-baran.

"Karki damu zan miki abu dan Allah ne amma ba dan halinki ba"

Ita dai Janan binta kawai take da ido dan bata da ta cewa tana buk'atar taimako a halin yanzu.

Matar ce ta gyara ta ita da jaririn su kuma 'yammatan su suka gyara inda ta haihun.

Ta bata wasu kayan ta saka sannan ta wanke mata nata duk da dai sun k'od'e amma har yanzu da k'warinsu.

'Yan Matan ne suka dawo d'auke da kwanuka.

Tsohuwar ta amsa tace "to kuje zan taho"

Zama tayi ta saka Janan a gaba sai da taci tuwon nan.

Tuwon shinkafane da lafiyayyar miyar kuka taji kifi da man shanu da yajin daddawa.

Sai da ta cinye tas sannan ta kora da kunun kanwa mai zafin gaske wanda da k'yar take sha saboda zafi.

Shima tasha kusan rabin kwano saboda tsohuwar tace sai ta sha sannan zata samu ta shayar da jaririn.

Tana gamawa ta mik'o mata dabino guda d'aya da zam-zam "ki tauna dabinon ki bashi,sai ki d'isa masa ruwan zam-zam d'in"

Kamar yadda ta umarceta haka tayi,dattijuwar tayi murmushi tace "anjima kad'an ruwan mama zai kawo sai ki fara shayar da d'anki ni zan tafi"

Har ta juya ta fara tafiya Janan tayi saurin cewa "nagode Allah ya saka da alkhairi"

Da sauri dattijuwar ta dawo ta zauna tana dariya.
"Naji dad'i da kika fara godemin bani na gode miki ba,yau zan fad'a miki ko wacece ni"

Kallonta kawai Janan take ba tare da ta k'ara cewa komai ba.

Dattijuwar ta cigaba da fad'in "nan inda kike zaune gidana ne ni da iyalina anan muke zaune,babu mahaluk'in daya tab'a tunanin zama anan saboda da yawan maza sunsha zuwa nan da niyyar yin lalata zan sa a halaka min su saboda bani da tausayi,kin san meyasa bani dashi?"

Kai Janan ta girgiza alamar a'a.

"Saboda ina zaman-zamana a cikin gari gidana Babban gidane amma akazo aka min fin k'arfi aka rugaza min gida wasu 'ya'yan nawa sun mutu sanadin haka shiyasa na d'auki alk'awarin duk wanda ya zauna a kangon nan zan halaka shi,munyi tafiya ni da yarana kwatsam muna dawowa na ganki shiyasa nazo nayi miki magana ki tashi bai kamata ki zauna anan ba,abinda yasa na biki cikin lallama saboda naga kina da ciki amma ba dan haka ba saina halaka ki a take a gurin"

"Tun bayan tafiya ta nake neman hanyoyin da zan halaka ki amma saboda k'arfin addu'ar dake bakinki ko da yaushe,kullum dake muke kwana anan amma na kasa tab'uka komai a kanki,ta guri d'aya na samu nasara dana hana kowa ya taimakeki,na saka k'yamata tsakaninki da 'yan unguwarnan"

Gaban Janan yayi mummunar fad'uwa dan a lokacin idan da za'a tsagata baza'a samu jini a jikinta ba.

Addu'oi ta karanta

Please Login or Register in order to submit comment