You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gane ina d'auke da cuta mai karya garkuwar d'an adam shiyasa a lokacin na nemi number Abba na fad'a masa cewar bazan sake dawowa ba yace miki na mutu saboda bazan iya aurenki da cutar nan ba,na kuma godewa Allah daya sa ban Aure ki tun a lokacin ba dana cutar dake"

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un,ina zan saka rayuwa ta Salman to meye alak'arka da Iya?" Tayi maganar tana hawaye.

"Iya ita na fara had'uwa da ita ta taimakeni dan zuwa na garin kaduna bani da gurin kwana ita ta jani a jikinta kuma ta sanar dani an kashe kowa nata ita 'yar gudun hijira ce,gidannan ma taimaka mata dashi akai,haka na za me mata d'a har lokacin data koma ga Allah"

"Wa iyazubillah" ta fad'a tana kuka sosai.

"Dan Allah ki rage kuka Janan so kike ki rasa idanunki ki daina gani"

"Wallahi gwanda na daina gani dana zauna ina ganin wannan masifun ji nake kamar na kashe kaina na huta"

"Janan na miki alk'awarin zan nemo miki su Mameey in har suna raye a duniya sannan zan nemo wanda sukayi ginin nan a kaf fad'in duniyar nan in har suna raye ko mutum d'aya in aka samu alhamdulillah"

"Nima na maka alk'awarin bani da wani miji kamarka"

Gaba d'aya ya zare idanunshi tare da fad'in "haba Janan ni ba azzalumi bane bazan iya aurenki da ciwo a jikina ba,kuma ko babu ciwo bazan iya aurenki ba saboda naga yadda Jalal ke sonki kamar ranshi bazai tab'a cutarki ba"

"Na san haka Jalal na sona amma ni kai nake so kuma kai zan Aura"

"Kamar yadda na rik'e alk'awarin ki nak'i fad'awa Mommy kece Janan nima kimin alk'awarin ba wanda zaki fad'awa kece wadda mukayi soyayya ki ajje wannan a tarihinki bazan tab'a aurenki ba har abada,,da Jalal kika fi dacewa"

Da sauri ya tashi zai fita cikin kuka tace "kai nake so zan zauna da kai a duk halin da kake ciki kuma zan zauna da kai ko wane ciwo ne a jikinka sai dai in guduna kake saboda yanzu bani da wani gata"

Cak ya tsaya sannan ya juyo ya kalleta "ko me kika zama a rayuwa bazan tab'a gudarki ba saboda kece macen dana fara gani naji inaso har cikin zuciyata"

"Dan Allah ka fad'a min kana so na kace kana sona Salman"

Sai daya d'anyi shiru sannan yace "ina sonki har gobe amma babu zancen Aure ga macen da k'anina ke so,uwa uba bazan aureki ba bayan ina d'auke da cutar HIV"


Kuka ne yaci k'arfinta har ta kasa mayar masa da amsa.

"Jalal na sonki yadda bakya zato kuma zai rik'eki fiye dani,ki manta da cewa mun tab'a soyayya ki d'auke ni a matsayin yayan mijin da zaki aura" yayi sauri ya fice.

Ta k'ara rusa kuka tana bubbuga kanta da hannayenta.










_Sadeey S Adam_✍

🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_πŸ‘„



```Dedicated to Mrs Xerks & Safnah luv```





_*Safeenah Safnah ina kika shiga ne?😭abin kamar wasa babu ke babu labarinki,ya Allah kasa kina cikin k'oshin lafiya a duk inda kike,Allah kasa ina da rabon k'ara jinki a rayuwataπŸ™*_




41

Yana fitowa falo ya tarar Raihan d'in janye da trolley idanunta duk sun kunbura saboda kuka.

Mommy ta kalleshi tace "ina Janan d'in"

"Itama kukan take" ya bata amsa murya a dashe.

"Bara naje gurin Janan, Jalal ka tabbatar Raihan ta bar gidannan yanzu"

Da sauri ta wuce ta haye sama.


_2days later_

Tana zaune a falo tana d'an wasa da Abba k'arami.

Har lokacin bata gama sakewa da gidan.

Jalal ne ya fito hannunsa dauke da wata k'atuwar tidy ya zo ya ajjeta gaban Abba k'arami.
"Prince ga abin wasa kanaso"

Hannu yasa yana dukan tidyn yana gwalan-gwalantunsa na yara.

"Meyasa kika zaune ke kad'ai?"

"Babu komai na gaji da zaman d'akin shiyasa na fito nan"

"Oh ko nazo mu fita yawo?"

Murmushi tayi tace "a'a"

Shiru ya d'an biyo baya sannan tace "yawwa Jalal dan Allah ina son magana da kai"

"Ina saurarenki"

"Jalal dan Allah ka dawo da Raihan ka bawa mommy hak'uri"

Hmmm "Janan kenan banyi niyyar sakin Raihan ba amma abinda mommy ta fad'a ya b'atan rai sannan ni a halin yanzu bani da burin auren ko wace mace bayan ke,zan rayu nida ke da prince da sauran 'ya'yan da zamu haifa amma ban da wata mace"

"Kana nufin ka mayar da Raihan bazawara haba Jalal"

"Ita ta mayar da kanta ki daina ganin laifina Janan"

Shiru tayi kawai bata sake cewa komai ba.
A zuciyarta tana fad'in _zan yi k'ok'arin kwantar da hankalinka Jalal ka dawo da Raihan,amma ni kam bazan iya auren wani ba bayan ina ganin Salman_


Shima ranshi ya b'aci shiyasa yayi shirun.

"Soyayya ake in koma ko kuma hira ake in k'araso"

Duk kansu suka dubi Adnan da yake maganar.

Jalal ne yace "hira ake bros"

"In shigo kenan" ya fad'a yana tahowa.

Wata harara Janan ta dalla masa duk da harara garke take amma still ya gane harararshi take.

Murmushi kawai yake dan shi lamarin nata har ya fara bashi dariya.

'Daukar Abba k'arami yayi ya cilla sama sannan ya cab'e shi,shi kuma sai dariya yake.

"Abbana akwai fara'a" ya fad'a lokacin da ya zauna.

Jalal ne yace "bros kaji wai rok'ona take in mayar da Raihan"

"Wace ce ma Raihan? Oh wai wannan yarinyar cab ai mun gama da babinta"

"To kinji ko,aimu duk abinda mommy bata so muma ba sonshi muke ba"

Bata basu amsa ba kawai dai ta cigaba da wasa da yatsun hannunta.

"Yawwa na saka a bincika mana wannan masu ginin wanda suka gina gidan commissioner saboda haka a ko yaushe zamu iya tafiya nijar ka zama cikin shiri" Adnan ya fad'a yana kallon Jalal.

Ita kuwa a zuciyarta ta cigaba da fad'in Allah yasa a samesu cikin sauk'i.

"Maganar su Mameey fa?" Jalal ya tambaya.

"Duk tare na bada cigiyan,jiya tun safe nake yawo har gidajen radio na Kaduna da gidan tv duk naje"

"Allah ya bayyana su"

"Ameen"

Da sauri Janan ta tashi ta fita dan ji tayi hawaye na k'ok'arin zubo mata.

********

A kwana a tashi yau Janan shekararta d'aya da wasa hud'u a gidansu Jalal, Asabe ta sakko sosai take girmama Janan musamman da taga yadda 'yan gidan ke k'aunarta,ita kuwa Janan tana son Asabe ta kanje ta zauna suyi hira ma sosai,tuni ta yaye Abba k'arami tun yana wata sha shidda dan yanzu wata biyu da yaye shi magana kuwa sai kace d'an shekara uku bakinshi rau-rau musamman in yana tare da Jalal ko Adnan.

Yana cewa Adnan Abba yana cewa Jalal daddy kamar yadda suka koya masa.

Yau gidan yayi katari da manyan bak'ine Raihan da besty.

Raihan suna zaune a falon Mommy shi kuma Besty yana falon bak'i tare da Adnan dan lokacin Jalal yana gurin aiki Adnan kuma ya samu hutu ne.

Bayan sun gaisa da Mommy ne ta koma bedroom tana shirin fita unguwa.

Raihan ta rik'o hannun Janan tace "ni fa mamaki nake wai wannan balaraben yaron ke kika haifa"

Murmushi Janan tayi tace "to mamakin nlme,ance muna kama haskene kawai nashi yayi yawa ni kuma nayi duhu kinga kuwa ai kowa ya gani ya san nawane ko ta kamannima"

"Hakane amma har yanzu mamaki nake,dan har yanzu baki da wani k'iba ko dogon tsayin da za'ace kin haifi yaron nan sai naga kamar bazaki iya haihuwa ba"

"To yanzu ai kinga na haihun ko ke da kuka tsafe kikayi k'iba kuka haifo Affan har ya kusa shekara bakizo ba ai sai ki fad'an sirrin ko"

Dariya tayi tace "wallahi kuwa na zama wata uwar mata ko?"

"Eh mana"

"nima ba son kibar nake ba amma dai bana son irin ramarki Janan"

Hmmm "dan ma baki ganni lokacin ina garari ba,wai a hakan na yi k'iba"

"Cab an kwashe k'ibar an bawa Abba k'arami"

Ta d'anyi 'yar dariya tace "ke dai bari"

"Kin san me?"

"Sai kin fad'a"

"Raihan fa tayi aure"

Ta d'an tsorata sannan tace "dan Allah a ina?"

"Wallahi a Zaria ai babansu cewa yayi bazai yarda ta masa zawarci a gida ba tana gama idda ya had'ata da abokinsa itace ta uku"

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un"

"Meye na salati sai kace an miki rasuwa?"

Ta d'an goge hawaye tace "naso ta cigaba da rayuwa da Jalal saboda tana sonshi sosai"

"Ke dalla ai Jalal naki ne wallahi dan yana matuk'ar k'aunarki"

"Ni kuwa Salman nake so"

Lubna ta d'an zare ido tace "ke Janan,ada ba"

"Har gobe wallahi"

Hmmm "lallai Janan karki zama mai butulci,wallahi da ace babu Jalal kika sake had'uwa da Salman nima zan ce ki aure shi amma ni tun da kika ce min Salman d'an uwan Jalal ne hankalina ya tashi na san za'a rina,gaskiya karki zama mai butulci Janan"

"Babu zancen butulci amma ba zan iya auren Jalal ba saboda bana son shi ni ai dama ban tab'a cewa ina son Jalal ba"

"Janan"
"Lubna"
"Karki yiwa Jalal haka dan Allah, ya sadaukar da rayuwarshi saboda ke amma kice kina son yayansa ya kike tunanin zaiji?"

Ajiyar zuciya tayi sannan tace "ni bana tuna komai sai girman so,kuma Salman nake yiwa shi"

Haka dai sukayi ta musu duk yadda Lubna taso fahimtar da Janan amma ta kasa.

Da zasu tafi ma a bakin mota Lubna ta sake fad'in "ki zama mai adalci Janan kada kisa yayi biyu babu ba wan ba k'anin"

Bata ce komai ba haka tayi sallama suka tafi da alk'awarin zata zo Kaduna kafin su koma.

Mommy lokacin bata nan da suka zo ta fita unguwa nan gidan mak'otansu anyi haihuwa ta fita barka ita da Abba k'arami dan haka gidan ya rage saura su biyu Asabe ma na d'akinta.

Suna shiga falo Adnan ya fara sauri yana son shigewa aikuwa tace "oh har guduna ma kake"

Juyowa yayi sannan ya dawo baya sai dayazo daf da ita yace "karki zama mara halacci kamar yadda Lubna ta fad'a"

"Rashin halaccin me nayi?"

"Idan har kika guji Jalal"

Shiru tayi tana kallonsa kawai.

Shi kuma ya cigaba da fad'in "Jalal d'an uwana ne ciki d'aya muka fito dashi dole in so abinda yake so kuma idan har kika gujeshi kin zama butulu,shekara da shekaru bai tab'a furta so ga kowa ba amma ke daya furta miki kina neman gudunsa"

"Ni ban gujeshi ba kuma in har na k'i aurenka ban yiwa kaima adalci ba saboda kai nake so"

"Idan har kika k'i amincewa da Jalal tabbas keda shi za kuyi biyu babu, ki rasani ki rasashi shi kuma ya rasa ki gashi ya rasa Raihan"

"Kana k'ina ne kawai saboda yanzu na zama k'ask'antacciya ga kuma d'a,kana son ka rama abinda Abba ya maka tun da nima a yanzu talaka ce"

"Bance haka ba Janan amma kinsan........"

"Kayi shiru kawai na san baka sona saboda wannan dalilan"

"Ina sonki Janan ban tab'a jin ranar da babu sonki a zuciya ta ba amma ba zan tab'a aurenki bayan ina da wannan cutar wannan shine kad'ai halaccin da zan miki,idan na aure ki da HIV a jikina ban miki adalci ba"

"Kaine mutumin dana fara so a rayuwata dan haka nima wallahi saina Shafa ma kaina cutar HIV tunda a kanta kake guduna,idan mun zama d'aya sai ka aureni,amma na san duk wanda zan aura bayan kai gangar jikinsa zan aura ba shi b........."


Turo k'ofar da aka yi ne ya saka tayi saurin juyawa a kid'ime,shima Adnan ya tsorata ainun.








*_Fans wane ya shigo?JALAL ko MOMMY?_*













_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁




_*by SaNaz deeyah*_πŸ‘„




```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```




_*Wannan shafin sadaukarwace ga duk wani masoyin littafin nan*_😘😍
_#TARENE#🀝❀_



42

Adnan rud'ewa yayi ya kasa cewa komai dan yana ganin yanayin fuskar Jalal ya san tabbas yaji komai.

Dariya Jalal yayi wadda iyakarta leb'e sannan yace "kuyi hak'uri na muku katsaladan na shigo kuna magana na katse ku"

Yayi saurin wuce wa side d'insa duk suka bishi da ido.

Janan ta goge hawayen idanunta ta kalli Adnan tace "Jalal yana da damar da zai zab'i macen da duk yake so amma kai baka da dama, hakan ne yasa zan jajirce dan ganin na samo maka farin cikin rayuwa,ina son na ganka da d'anka na kanka Salman"

"Me?ke! Janan ko dai kin fara samun matsalar kwakwalwa?"

"Koma me zaka ce kace amma ka sani ba zan auri Jalal ba kai nake so Allah ya sani ban tab'a son wani kamarka ba"

"Karki saka raina ya b'aci a kanki bana son samun matsala dake Janan na san Mommy tana ta shirye-shiryen aurenku da Jalal,ki duba irin d'awainiyar da yayi miki amma kawai rana d'aya kice baki son shi"

"Bana son Jalal kai nake so idan har naga ana shirin aura min wani ba kai ba to tabbas zan bar muku gida"

"Ba sai kin bari ba Janan"
Kawai suka jiyo muryarsa.

'Daga ido tayi tana kallonsa Adnan kuma ya juya gareshi.

"Jalal ka fahimceni dan Allah karka saka zargi a zuciyarka" Adnan yayi maganar.

Murmushin karfin hali ya sake yi sannan yace "babu zargi a ciki sai gaskiya,idan har kaine Salman d'in da ake fad'i kuma itace wadda kaje kayi soyayya da ita a Kaduna to tabbas tana matuk'ar k'aunarka dan Raihan ta bani labari,bros kai take so bani ba dan haka zata auri zab'in zuciyarta ba zab'in wata zuciyar ba"


"Bata da wani zab'i da ya wuce kai Jalal" Adnan ya fad'a yana kallonsa.

Tun kafin Jalal d'in yayi magana tayi saurin cewa "ni ban tab'a cewa ina son Jalal ba kai nake so kawai kana guduna ne saboda bani da gata"

"To kaji ta fad'a da bakinta,bata sona kai take so nine nake son ta,nayi kuskuren sonta da nayi,dan Allah bros ka nuna mata ita d'in mai gata ce,ka aureta kawai"

"Abinda ba zai yuwu ba"

Kukanta ne ya fara fitowa fili dan haka tayi saurin to she baki da hannu ta wuce d'akinta da gudu.

Shima Jalal hawayen idon nashi ya goge yace "Adnan kaine zab'in zuciyarta"

"Ka daina fad'ar haka Yarima dan Allah, wai taya zan auri lafiyayyar mace bayan ina da ciwo"

"Tace zata sakawa kanta idan har baka saka mata ba ina tausayin Janan bana so ta cutu ka daure bros"

"Na san fad'a take kawai ka daina wannan furucin Jalal"

Hmmm "na san halin Janan wallahi zata iya aikatawa,karka damu na san yadda zan sanarwa Mommy"

"Karka kuskura ka fad'awa Mommy zancen nan,bazai yuwu in auri Janan ba"

"Saboda me bayan da kunnena naji kace kaima kana sonta,kana k'inta a yanzu saboda kawai ina sonta,to ni na bar maka bros"

"Yarima......."
"Dan Allah ka bar maganar nan Adnan"

Da sauri Jalal d'in ya wuce ya bar Adnan a tsaye shi kad'ai.

Kan kujera ya zube dan ji yayi k'afafunsa ba zasu d'aukeshi ba ga azabebben ciwon kan daya fara ji.


Janan kuwa tana zuwa d'akinta ta zube a gado tana kuka mai tsanani ita tana tausayin Jalal amma bazata iya auren shi ba bayan tana ganin Salman.


Ta b'angaren Jalal kuwa yana shiga d'akin nasa ya zauna kan sofa tare da dafe kai.

_ni da Adnan duk munyi Aure mun rabu da matanmu,cikin ikon Allah sai gashi mun fara son mace d'aya ni dashi,wannan k'addararmu ce._
Ya fad'a a zuciyarsa tare da goge hawaye.

Wata zuciyarce take ce masa _kai baka sha wahalar da Adnan ya sha ba,saboda kai ka fito da wadda kake so shi kuma auren dole aka masa kuma aka aura masa macen da ta zama sanadin cutarsa._

Ajiyar zuciya yayi wasu hawayen suka sake sauka a fuskarsa.
A fili ya furta "sadaukarwa ba abu bane mai sauk'i amma dole ne in barwa Adnan Janan,duk da na san ba zan manta Janan ba bazan tab'a daina sonta ba amma zanyi k'ok'arin manta cewa nayi soyayya da Janan tunda bata sona bazan so b'acin ranta ba ina son farin cikin Janan da Adnan"

Haka yayi ta surutanshi shi kad'ai yana hawaye.

Kafin Mommy ta dawo tuni suka manta komai,duk da dai taso ta gane Jalal amma still ya nuna babu komai harma suka zauna suna hira a falo Janan kuwa tuni baccin wahala ya kwasheta.


_*Dare*_

Lokacin da Mommy da Asabe suka gama jera komai a dining Asabe take tambayar Mommy shiru tun d'azu bata ga Janan ba.

Mommy tayi murmushi tace "ai ta fito nace mata ta komai dan naga kamar bata jindad'i"

"Oh ni dai ince yau babu abokiyar hira tun bayan tafiyar bak'inta,Abba kuwa dama sai dai yazo ya isheni da surutu mara ma'ana ko kuma yace inyi masa tatsuniya"

"Abba sarkin son tatsuniya"

Haka suka cigaba da 'yar hira daga bisani Asabe tayi musu sallama ta nufi d'akinta lokacin Jalal da Adnan sun fito.

Bayan sun zazzauna Mommy ta kalli Abba tace "je ka kira Ammi kaji"

Da gudu ya haya sama ya nufi d'akin Janan.

"Ammi! Ammi!! Ammi" ya shiga da gudu tana kwance kan gado ya fid'a jikinta yace "Mommy tace kizo abinci"

Rungumoshi tayi tana goge hawaye tace "kai kaci abincin Abba?"

Girgiza kai yayi yana fad'in "Mommy tace kizo"

Kallonshi tayi ta shafa kansa sannan tace "kace wa Mommy na k'oshi kaji,sai ka zauna Mommy ta baka ka ci sannan ka dawo na maka tatsuniya ai kana so ko?"

'Daga kai yayi yana murna sannan ya ruga ya fita.

Wasu hawayen taji sun sauka a kuncinta a fili ta furta "ina kunyar had'a ido da Jalal"

Tana kwance tana hawaye taji maganar Mommy a kanta.

Da sauri ta tashi zaune tare da sauke k'wayar idonta k'asa.

"Dama na san Akwai abinda ke damunki"

Shiru tayi kawai ta cigaba da hawayen.


"Me suka yi miki?"
Girgiza kai tayi alamar ba komai.

Zama Mommy tayi sannan tace "Janan nifa tamkar mahaifiyace a gareki karki b'oye min damuwarki"

"Bani da lafiya ne"

"Meya sameki?"
"Zazzab'i"

Ta d'an tab'a jikinta taji kuwa da zafi.

"Sannu,amma shine zaki b'oye min,bara na kira doctor a waya yazo ya dubaki"

Tashi tayi ta fita ita kuma Janan ta kwanta sai kuma ta fashe da kuka.



*_Few minutes ago_*
Tana kwance an saka mata drip,Mommy na zaune gefenta sai Jalal dake tsaye ya jingina da bango,Abba k'arami na jikinta yayi bacci ma,Adnan kuwa dama tuni ya fita.

Bayan doctor ya gama rubuce-rubucensa ya mik'awa Mommy takardar yace "ga wannan takardar sauran maganin da za'a saya ne,sannan a daina barin ta tana yawan damuwa saboda jininta ya fara hawa"

"Insha Allahu mungode doctor"

"Okay babu damuwa"

Bayan tafiyar likita Mommy ta sab'i Abba k'arami tace "bara na kaishi na kwantar sannan nayi sallar isha'i ka zauna wajenta kafin in dawo"

"Okay ba damuwa Mommy"

Bayan fitar ta ne ya kalli Janan d'in yace "dan Allah ki cire damuwa a zuciyarki haba Janan"

"Jalal kenan tun ranar da Aliyu ya aureni har yau ban sake ganin farin ciki ba,ina son d'an uwanka amma na san kai da sauran mutane zaku kalli abin a matsayin butulci saboda kana sona kuma ka fito ka fad'a"

Ji yayi zuciyarshi ta harba,sai da ya karanto inna lillahi wa inna ilaihi raji'un a zuciyarshi sannan yace "karki damu dani da Adnan duk d'aya ne kuma tunda shi kike so baki da wata matsala,Janan ko wani kike so wallahi zan tayaki so kawai saboda ina son farin cikinki bare d'an uwana Adnan, kuma na san irin son da kike masa tunda an bani labari"

"Adnan baya sona saboda kai da kuma cutar jikinshi,yana ganin kamar baiyi ma kanshi adalci ba idan har ya aureni ni kuma wlh ko wace irin cuta gareshi zan zauna dashi a haka,Jalal dan Allah ka tayani cika burin raina"

Wani irin tartsatsi yake ji a zuciyarsa amma ya daure ya sake cewa "in Allah ya yarda baki da wani miji daya wuce Adnan ki cire damuwa"

"Adnan har ya fara guduna fa"

"Ba gudunki yake ba shima baya jindad'in jikin nasa"

Shiru tayi na d'an wani lokaci kafin tace "Allah ya bashi lafiya"

"Lafiya ta k'alau karka d'auramin ciwo yarima"

Juyowa yayi ya kalleshi sannan ya k'araso ransa a b'ace yace "tabbas gudunki nake saboda na gaji da maganganunki marasa amfani,idan mafarki kike ki farka wannan Adnan ne ba Salman ba,kuma ni ba butulu bane bazan tab'a aurenki ba wallahi idan har kika bari Mommy taji maganar nan ranki zaiyi mummunan b'aci"

Kuka sosai ta fara ganin haka ne yasa Jalal ya fara fad'a yana fad'in kar yaja ciwon ya k'aru.

"Ya k'aru mana sai me,akan me zata rik'a kawo min shirme,idan kinsan wannan maganganun zaki rik'a min kada ki sake min magana a gidannan bani ba ke"

Da sauri ya fice ya bar d'akin,aikuwa ta rik'a kuka tana shashshek'a tamkar k'aramar yarinya.

Sai rarrashinta yake amma ko kad'an tak'i ta rage ko sautin kukan.

Ganin haka ne yasa yaje ya kira Mommy, koda ta tambayi ba'asi sai yace bai san dalilin kukan ba.

Da k'yar Mommy ta shawo kanta,sai wajen k'arfe d'aya ta samu bacci sannan suma suka bar d'akin.

Duk sautin kukan nata a kunnen Adnan yake sauka yana jin kamar ana watsa masa garwashi a k'irjinsa,wai Janan d'insa dayaso yin rayuwa ta din din din da ita,Janan d'in da ta so shi ba dan wani abu nasa ba,Janan d'in data yarda ta d'auki cutar HIV saboda shi amma yau ita yaje yana fad'awa magana.
"Anya na yiwa kaina da Janan Adalci kuwa?" Ya fad'a a fili.

Zuciyarshi ta bashi amsa da _wannan shine adalcin da zakawa Jalal,kuma shine halacci,hakan kad'ai ne zaisa Janan ta cire sonka a zuciyarta._

Haka zuciyarsa tayi ta yawo da hankalinsa,sai yaji kamar yaje ya bata hak'uri sai kuma yaji ina bazai yuwu ba.

A haka har ya daina jin sautin kukanta.

Hakan ne ya bashi damar tashi yayo alwallah ya fara jera nafiloli har zuwa Asuba.













_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_πŸ‘„





```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv```





_Sai kun rik'a min uzuri kwana biyunnan banjin dad'i ,yau inada lafiya gobe bani da ita,addu'arku ce jindad'i na nagode da masu min addu'a koda yaushe😍_


43

Kwananta uku a kwance amma idan yaje dubata ko kallonshi bata yi.

Duk da hakan bata masa dad'i amma yana ganin haka shine mafi a'ala.

Yau suna zaune su biyu a falo suna hira Jalal yace "Mommy dama ina son magana dake"

"Ina saurarenka"

"Mommy game da Janan ne"

"Meya faru da Janan d'in?"

"Mommy ashe itace wadda Adnan yayi soyayya da ita a Kaduna tsawon shekara uku,mahaifinta yak'i aura mata shi saboda baya da asali itace wadda yazo yana bamu labari"

Cikin mamaki Mommy tace "kai ya akai kasan wannan?"

"Tun lokacin da suka had'u sun gane juna amma suka b'oyewa kowa yanzu kuma tace ita idan bata aureshi ba ta hak'ura da aure a duniya"

"Amma Jalal kai kenan dama bata sonka ko me?,yau nake shirin in aika gombe fa,ina son saka bikinka da ita wata d'aya"

"Mommy tafi son Adnan domin shine ta fara so kuma rabasu akayi,shi Adnan d'in ne yace baya son kiji dan bazai aureta ba"

"To dama taya ya zai aureta bayan yana da ciwo a jikinsa,bazai yuwu ba"

"Mommy tace wallahi idan bai aureta ba zata gogama kanta cutar ni ina ganin da tayi haka gwanda ai auren tunda ta san yana da ciwon tace zata zauna dashi"

"Wannan babbar magana ce,kirawo min Adnan da Janan a waya"

"To Mommy"

'Daga waya yayi ya kirasu duka sukace gasunan zuwa.

Janan ce ta fara zuwa saboda ita tana gidan.

Ta taho hannunta rik'e dana Abba k'arami,ta samu guri gefe ta zauna shi kuma Abba k'arami ya nufi gurin Jalal ya d'aukeshi ya rungume.

"Oh yau gurin daddy ko ba gurin Mommy ba"

"Mommy zaki min tatsuniya" ya fad'a yana dariya.

"Nak'i bazanyi ba"

Ya d'aga kai ya kalli Jalal yace "daddy zaka min tatsuniya ko?"

"Eh mana zan maka wadda tafi ta Mommy dad'i"

Dira yayi yana ta tsalle-tsalle a haka har Adnan ya shigo.

Zama yayi ya tank'washe k'afa yana fad'in "Allah yasa dai lafiya"

Ita dai Janan har lokacin kanta yana k'asa.

Mommy ta gyara zama tace "naji wasu maganganu ne shiyasa na tara ku dan jin gaskiyar lamarin"

Duk kansu shiru sukayi.

Mommy ta kallesu tace "ya kukayi shiru,Janan, Adnan ku nake saurare"

"Mommy duk abinda kikaji hakane"
Labari ya bata na duk abubuwan da suka faru sannan ya k'ara da fad'in "Mommy itace ta kasa fuskanta"

Kallon Janan tayi tace " 'yata zo nan"

Sai a lokacin ta d'ago,idonta duk ya cicciko da hawaye.

Tashi tayi jikinta a sanyaye ta koma gefen Mommy ta zauna.
Dafata Mommy tayi sannan tace "Janan kiyi hak'uri,kinsan bazan zama uwar banza ba,kinada lafiya bazaki auri Adnan ba,karki cuci kanki kiyi yunk'urin daurawa kanki ciwon da Allah bai jarrabeki dashi ba shi kanshi Adnan da k'addarar ta hau kanshi ji yake da da hali da ya raba kanshi da ita,kina son Adnan amma Allah ya k'addara bazai kasance mijinki ba,wallahi ina da yak'inin duk abinda kike nema daga Adnan zaki samu daga Jalal domin duk 'ya'yana ne na san halinsu kiyi hak'uri ku d'auki k'addara"


Hawaye sosai yake zuba daga idon Janan shikenan da gaske an haramta mata auren Adnan.

Kallon Jalal tayi tace "bikinku sati biyu na mayar,sai ka fara shirye-shirye"

Adnan ji yayi zuciyarshi na harbawa da sauri saboda tsananin tausayin Janan dashi kanshi ya k'udurta a ransa ana yin bikin zai bar k'asar.



Please Login or Register in order to submit comment