You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Asabe"

"To Mommy" ta fad'a sannan ta tashi ta fita.

Tare da Asaben suka dawo,ta kalleta tace "ki tafi da wannan yarinyar d'akinki ku zauna tare zata rik'a tayaki aiki"

"Bak'uwa muka samu kenan,sannu da zuwa"

Kai kawai Janan ta d'aga.

Juyawa tayi ta sake tambayar Adnan jikin Jalal da k'yar ya rik'a amsa mata.

Har zasu fita tayi saurin cewa "af baki fad'a min sunanki ba"

"Indo" kawai sunan yazo mata a baki kuma ta furtashi"

"Okay" Mommy tace.


Dan kar Mommy ta gane shiyasa shima Adnan yayi saurin tashi yayi sama.
Anan yaci karo da Jalal wanda yana lab'e duk yaji komai.

"Adnan wallahi bana son Janan ta wahala bana son na ganta a wahale"

Dafa kafad'arsa yayi yace "Jalal tunda tak'i yarda tazo a Janan ya zamuyi wannan itace hanya mafi sauk'i da zata dawo kusa da kai"

Ranar babu wanda ya runtsa a cikin su ukun,Adnan,Janan,Jalal.
Raihan kuwa ji tayi kamar ta kashe kanta saboda kishi,ta kuma d'aukarwa kanta alk'awarin bazata bar Janan ta huta ba sai ta ta wahalar da ita da aiki.

Adnan kuwa ji yake soyayyar Janan tamkar sabuwa,amma sai dai bakin alk'alami ya bushe.

Janan kam bayan ta kwantar da Abba k'arami a katifar ta kwanta ta hau aikin tunani da kuka.

Babban abinda yake bata mamaki shine wai ashe dama Salman shine Adnan wanda Jalal ya bata labari,mutumin da har yau babu wanda ta tab'a yiwa soyayyar da tayi masa,amma yau ita ya nuna bai gane ba saboda kawai rayuwa ta juya mata baya,dama ashe zuwan da yayi Kaduna guduwa yayi daga gidansu,to meye alak'arsa da inna? tunda ko lokacin data mutu bata ga wasu masu kud'i sunzo ta'aziyya ba.
Da wannan tunanin ta kwana a ranta.

Har saida tayi sallar Asuba sannan ta samu bacci mai nauyi ya kwasheta dama Abba k'arami ba mai yawan kuka bane.

Kamar daga sama taji ana d'an bubbuga k'afarta ta bud'e ido a hankali sannan ta d'an murjesu da hannunta,tashi tayi zaune tana kallon Asabe.
"Ba harara ta zakiyi ba,ki tashi bakwai har tayi kije kid'an goge falon zanje in had'a break fast ni kuma"

Murmushi Janan tayi tace "wallahi ba harararki nake ba idona ne a juye haka"

Murmushi itama Asabe tayi sannan tace "k'warai kuwa ga alama"

Girgiza kai kawai Janan tayi dan ta san bata yarda ba.

Kallon Abba k'arami tayi wanda har a lokacin bacci yake.

"Zan iya barin shi anan?"

"Eh idan har kinsan bazai tashi ba"

"Bara kawai na goyashi"

Goyashi tayi ta shiga toilet ta d'auraye fuskarta sannan ta fito ta d'an tsane fuskarta suka tafi.

A farfajiyar gidan ma sun tarar maza masu aiki sunata share share da bawa flowers ruwa kai tsaye suka nufi part d'in gidan.

Hawaye duk sun taru a idon Janan dan rayuwar gidansu ta tuna da taga kowa na aikinsa.

Suna shiga babban falo suka tarar da Adnan kwance kan kujera idonshi a rufe.
Sai da gaban Janan ya fad'i sosai ta rik'a Allah-Allah su wuce ba tare daya farka ba.

Suna zuwa daf dashi kawai sukaji yace "Asabe kun fito"

Duk suka kalleshi kuma har lokacin idon nashi a rufe yake.

Durk'usawa tayi tace "eh yallab'ai ina kwana"

"Lafiya k'alau ya kuka wayi gari?"

"Lafiya k'alau" juyowa tayi ta kalli Janan tayi mata signing kan ta gaidashi,kamar baza tayi ba sai kuma tace "ina kwana" bud'e idonta nashi yayi ya saukar da k'wayarr idonshi akan tata,tayi saurin sauke idonta k'asa.

Murmushi yayi yace "ya baby?"
"K'alau" ta amsa a tak'aice.

"Amma yallab'ai Allah yasa dai lafiya na ganka a falo a wannan lokacin?"

"Eh lafiya k'alau"

Tashi tayi suka wuce sai da sukaje kitchen ta kalli Janan cikin b'acin rai tace "ke yarinya wallahi bazaki ja min tashin hankali da salalon tsiya ba,ki kalleni ki gani kin san dai nayi jika dake ko?har ni na durk'usa amma ke ki gaidashi a tsaye,dan ma su ba mutane bane masu fad'a to ki kiyaye ni"

Ruwa ta had'a mata a d'an k'aramin bucket amma sai fad'a take,ta mik'a mata ruwan da towel tace "kije ki goge goge idan kin gama kiyi mopping saura kiyi masa hauka kinsan yana falon dai".

Karb'a kawai tayi ba tare da tace komai ba ta wuce.

Tana zuwa falon ta dire bucket d'in, sai a lokacin hawaye suka samu damar zubowa daga idanuwanta.

Center table ta fara goge wa tana yi tana share hawayen idanunta.

Adnan tashi yayi zaune yana shirin tambayarta dalilin kukan kawai yaji ance "lafiya na ganka a falo yanzu?"

A d'an tsorace ya juya ya kalli Mommy yace "eh lafiya lau na fita ne dana dawo kawai nayi branching anan"

"Fita kuma da sassafen nan"

Shiru yayi Allah ya taimakeshi Janan ta k'atse mata tambayar da gaida ta da tayi.

Cikin sakin fuska ta amsa sannan ta kalleshi tace "muje ka koma d'aki ban son zamanka anan"

_ko Mommy ta fuskanci wani abu ne?_ ya tambayi zuciyarsa lokacin da ta fara tafiya.
Da sauri ya tashi kawai ya bi bayanta,sai daya juyo ya kalli Janan yaga har lokacin kuka take.


*_10:00am_*

Suna zaune su hud'u akan dinning Asabe da Janan na cigaba da jera musu kayan abinci.

Jalal kawai sunkuyar da kai k'asa yayi dan bazai iya jurar ganin Janan a wannan hali ba.

Tsam Adnan ya tashi yana shirin tafiya Mommy tace "ina kuma zaka"

"Mommy bana jindad'i kawai a kawo nawa d'aki"

"Ikon Allah" ta fad'a tana kallon bayansa dan har ya wuce.

Raihan tayi saurin kallon Janan tace "ke indo d'ebar masa komai da komai kikai masa"

"To" kawai tace ba tare data kalleta ba.

Jalal kuwa kallon Raihan kawai yake cike da mamakin yadda ta murje ido tana bawa Janan command.

A k'aton tire ta had'a komai bata san ina bane d'akin amma da bala'in Raihan sai da ta nuna mata, ita a dole sai ta bak'anta mata.

Ajje tire d'in tayi ta fara knocking, sai da taji yace ta shigo sannan ta d'auki tire d'in ta shiga.

Ganin itace yasa yayi saurin tashi zaune.

Bata ce komai ba kawai ta ajje kan d'an table d'in ta juya zata fita yayi saurin cewa "ya akai Janan d'ita ta canza lokaci d'aya ta zama tamkar mara gata?"

Cak ta tsaya,lokacin da taji mugun bugun zuciya.

Kasa bada amsar da tayi ne yasa ya taso ya dawo gabanta.

"Ya naga kina hawaye Janan?amsa ya kama ta ki bani"

Hannu ta d'aga masa tare da fad'in "ka fitar da sunan Janan a bakinka ka d'aukeni a matsayin indo 'yar aiki ka daina kirana da Janan"

Tsayawa yayi yana kallonta kawai,ta cigaba da shashshek'ar kuka tana fad'in "ka cuce ni Salman ka cuci soyayyarmu ka gujeni lokacin da nake buk'atarka a kusa dani,sai da rayuwa ta dawo mara amfani sannan na ganka,meyasa kayi min haka?zuciyata bazata tab'a yafe maka ba"

"Janan"
"Ya isa haka ka barni in fita kawai kar mutanen gidannan su fuskanci wani abu"

Tana k'ok'arin fita yayi saurin tare k'ofa idonsa yayi jajir saboda tashin hankali "Janan dole yau in sanarwa kowa abinda ke tsakanina dake duk da na san bazan iya aurenki ba saboda cutar dake tattare dani amma zan yi k'ok'arin samo miki farin ciki ta hanyar had'aki da Jalal dan na san zai kasance mai sonki kuma jigo a gareki"


Idanuwanta gaba d'aya sun fito waje saboda tsananin tashi hankali.

Bata san lokacin dana dafe kanta ba ta zunduma salati tare da rugawa a guje,shima a kid'ime ya bita,steps bibbiyu ta rik'a had'awa tana zuwa falo ta zube sumammiya,Abba k'arami kuwa ya k'walla k'ara gami da kukan rud'ewa yadda ya bugu sosai.

Su Jalal dake kan dinning duk suka mik'e.......











_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyah*_👄



```Dedicated to Mrs Xerks & Safnah luv```



39

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" shine abinda Mommy da Jalal ke ambata.

A kid'ime Adnan ya k'araso gurin,d'ago kai Jalal yayi yana masa kallon tuhuma,da sauri Mommy ta kunce mata goyon ta rungume Abba k'arami.

"Mommy ya za'ayi?mu kaita asibiti" Jalal ya fad'a a rud'e.

"A'a kirawo doctor kawai"


*_2 hours later_*

A hankali ta bud'e idanunta ta kalli silin kawai hawaye na zuba ta gefen idanunta.

Mommy ta dawo gabanta "Sannu kinji"

Kallonta kawai tayi sannan ta kalli Abba k'arami dake hannunta yana ta wasa da hannunsa.

Hannu tasa ta dafe goshinta tare da lumshe idanunta.

"Adnan muje zanyi magana da kai"

Gabanshi ya fad'i sosai amma ya daure yace "babu damuwa mommy"

Suna fita Jalal yayi saurin dawowa gefenta "Janan me aka miki wanda har yasa ki gigicewa haka?"

Kafeshi da ido kawai tayi bata ce komai ba.

"Kiyi min magana dan Allah"

"Ba Janan bace" shine abinda ta fad'a tare da d'auke idonta daga kallonshi.

"Dole cikin biyu ki zab'i d'aya,ko mommy ta san wace ke ko kuma mu samar miki gida ki cigaba da zama a ciki"

"Zan zauna a matsayin 'yar aiki idan har ka canza wannan matsayin zaka nemeni ka rasa Jalal"

"Meyasa Janan" ya fad'a yana goge k'walla ita kuwa bata iya bashi amsa ba.


"Ka fad'a min matsayin yarinyar nan a gurin ka ma'ana wacece ita?"

Kallonta yayi a d'an tsorace yace "mommy ban gane me kike nufi ba?"

"Ka san me nake nufi Adnan tunda da hausa na tambayeka"

"Mommy ni dai kawai ta bani labarin rayuwarta shiyasa naji tausayinta na taimaka mata"

" 'Kila ma k'arya ta shimfid'a maka ka hau ka zauna,amma har kake cewa kana jin tausayinta to ba zai yuwu ba tana fad'uwa mana a gida da yaro dubi yaronnan abin tausayi yanzu idan ya tashi yaga uwarshi a haka ai mu kanmu bazamu ji dad'i ba"

"Mommy dan Allah ki barta anan ko dan yaron nan nata muji tausayinta pls"

"Idan kuma matsala ta faru ban san kowa nata ba me kake tunani?"

"Ba abinda zai faru da yardar Allah"

" to shikenan Allah ya shige mana gaba"

"Ameen mommy"


Adnan kuwa ya samu Jalal ya fad'a masa cewar sai sun d'an ja baya da Janan saboda Mommy ta fara fahimtar wani abu.

Haka Janan ta cigaba da gudanar da aikinta a gidan su Jalal dan har ta fara sabawa da wahala gashi sam basa shiri da Asabe,Asabe ta takura mata sosai musamman idan Abba k'arami na kuka duk da ba mai yawan kuka bane amma in yana yi Asabe ta rik'a masifa tamkar zata daki Janan.


Kullun Abba k'arami yana hannun Adnan saboda shine baya zuwa office yana ta neman transfer zuwa wani garin anan nigeria dan Mommy tace babu inda zai koma, Mommy kuwa ta kan d'aukeshi itama idan ta fito falo,gashi sun tsaftace shi sosai.

Ita dai Janan har a lokacin tana tattare da jin haushin abinda Adnan yayi mata dan gani take shine silar fad'awarta tarkon Aliyu.

Raihan kuwa kamar yadda ta kudurta haka ta rik'a wahalar da Janan bata bari ko kad'an ta huta,da zarar Jalal ya bar gida to lokacin wahalarta ya fara kenan tun da shi Adnan baya shiga b'angarensu

Wasa-wasa yau satin Janan uku a gidansu Jalal.

Raihan d'in ce zaune akan sofa tana shan lemo tana latsa waya, Janan na zaune tana goge kayan Raihan d'in da ta wanke.

"Hello lubna"
Jin Raihan tace haka ne yasa Janan tayi saurin kallonta,itama kallonta tayi tace "Dalla malama ki cigaba da gugar munafuka kawai"

Ranta ba k'aramin b'aci yayi ba amma ta daure ta cije ta cigaba da gugar tana satar kallon Raihan.

"Ke Raihan wa kike zagi haka"

"Ke dai bari k'awata kin san 'yan aikin yanzu akwai gulma"

"Hmm Raihan kenan to ya gida ya kike?"

"Lafiya lau Lubna ya amarci kuna can Spain dai ko"

"Ke dai bari har na fara zuwa skul"

"Dan Allah fa,ni Jalal yace min sai na haihu"

"Haba?ba dai kin kusa haihuwa ba?"

"A'a fa kinji ki wane haihuwa bayan da muka had'u kin ganni sak'ayau"

"Ah to na sani ne, kusan wata 8 rabona dake fa tun bikina"

"Ke babu komai sai 'yan hanji"

Daga b'angaren Lubna kuwa dariya tayi tace "wallahi ni kuwa kin ganni nan wata uku kenan"

"Dan Allah fa"

"Wallahi kinga kuwa yadda besty ke ririta ni da k'yar yake bari na tafi skul"

"Amma na miki murna Lubna Allah ya saka mu a danshinku"

"Ameen,k'ila in kin tashi ki haifo mana twins ko triple"

"Rufamin asiri Lubna ina zan iya d'ayan ma ya isa"

Dariya tayi kawai.

"Amma in kin haihu zakizo ko?"

"Eh yace da nayi 2months da haihuwa zamuzo ganin gida"

"Woww Allah ya kaimu,amma zaki k'araso Abuja ko"

"Eh mana me zai hana"

"Sai kinzo har kinga Janan ma"

Janan tayi saurin kallonta,itama Lubna ta d'anyi shiru kafin tace.

"Janan d'ita dai?"

"Ita dai wadda kika sani amaryar Aliyu"

"Kina nufin Janan dama tana Abuja?"

"Eh yanzun dai tana Abuja tana aiki a gidana kinganta yanzu ma guga take min"

Da yake handsfree ta saka Janan d'in najin yadda Lubna ke jira salati.

"Yanzu Raihan kina so kice Janan ta zama ''yar aiki a gidanki duk yadda muke da ita"

"Yadda kike da ita dai,nifa zan iya komai akan Jalal wallahi ko uwarshi ce take neman rabamu to zanyi k'ok'arin rabata dashi kafin ta rabamu"

Maganar Lubna da alamun kuka take fad'in "shiyasa kuka zab'arwa Janan aiki a gidanki kuma Jalal yana kallo,Lubna kin san Janan bazata tab'a auren Jalal ba tun da taga kina aurenshi"

"Zuciya bata da k'ashi,kuma Jalal baya so amma haka tace ita bata son kowa ya san itace zatayi aikin kawai dan ta samu gurin zama"

"Amma Raihan baki yi halacci ba"

"Wannan shine Babban halacci tun da bance Janan bazata zo gidana ba,da yaronta haka muka ganta cikin k'azanta muka d'akkota muka mayar da ita mutum"

"Dan Allah Raihan bawa Janan wayar muyi magana"

"Ki fad'a tana jinki"

"Janan! Janan!!"

Kuka kawai Janan take tana cigaba da gugar.

"Karki yarda k'azamin hawayenki ya d'iga a kayana" ta fad'a tana kallon Janan sannan tace "Lubna kinga bafa zatayi magana ba"

Cikin kuka Lubna tace "dan Allah Raihan zan aiko miki kud'i kiyiwa Janan visa ta taho Spain dan Allah kimin taimakon nan"

"Kin san dai Umma bata son tarayyarku da Janan ko"

"Yanzu a k'ark'ashin mijina nake kuma ni in har Besty zai auri Janan mu zauna mu biyu zan jidad'i wallahi"

"To gaskiya kinyi k'ok'ari, kinga ki samu wani yayi mata ni bazan iya ba"

Ta katse wayar kawai.

Lubna nata kira amma tak'i d'agawa.

"Janan ki goge hawayen nan ki cigaba da gugar karki k'ona min kaya"

Goge hawayen tayi duk da bai daina zuba ba ta cigaba da gugar kawai.

Ta kusa gamawa Mommy ta shigo da Abba k'arami a hannunta.

Cikin girmamawa Raihan ta mik'e tsaye "Mommy naga kamar fita zakiyi ko"

"Eh wallahi zan d'anje unguwane"

Da sauri Janan ta kashe socket ta tashi tana shirin karb'ar Abba k'arami,Mommy tace "barshi indo dashi zan tafi"

Raihan taji wani bak'in ciki sosai,Mommy ta kallesu tace sai na dawo.

"A dawo lafiya" suka fad'a.


**********

Rayuwar Umma da Ummi abin tausayi dan yanzu komai ya koma hannun Zuhra basu da iko sai nata.

Aliyu kuwa gaba d'aya ya zama mijin tace dan sai abinda Zuhra tace akeyi a gidan

Ita bata bin boka amma mamanta tazo ta hura mata wuta akan sai taje,ganin bazata je bane yasa ita Maman tayi komai da kanta.
Zuhra kuwa gani take ai kawai isa da iya kissa ne yake jan Aliyu.

Yauma Umma da Ummin na zaune a falo suna tattatunawa akan matsalar gidan.

Zuhra ce ta fito zata wuce amma sai da ta jefa haibaici "tsab'ar k'wawa da maita irin ta kura ina ita ina cin rub'eb'b'en nama kuma guntu maimakon abar sauran namun daji suma su warwasa".

" hmmm" kawai Ummi tace dan ta san bata isa tayi magana ba.

Umma ce ta fashe da kuka ta fara fad'in "Allah ya isa ban yafe ba kin mayar da d'ana bawon ki kin k'wace duk wani kadarorinshi kin maida su naki ke kike juya komai,mun tsamo ki daga rana mun maidaki inuwa amma kina neman tura mu rana"

Shewa tayi sannan ta tafa hannu tace "oh Allah sarki Janan ita kuma ko tace me?ita bayan an rabata da tukiyar ta sai da aka rabata da ahalinta,banga laifina ba dan wannan shi ake kira da sata ta saci sata"

"Zuhra wai kin manta mu ne kike mana irin wannan furucin?"

"Janan ce da Umma uwar Aliyu mana" Zuhra ta fad'a.


_Dare_
*_10:30pm_*

Yana jingine da jikin gado ya tallabo wuyansa da hannayensa duka.

Zuhra na tsaye jikin mirrow sai da ta gama feshe jikinta da turare sannan ta juyo ta kalleshi tana murmushi tace "yau ma tunanin kishiyar tawa kake ko"

" 'Dago kai yayi ya kalleta ita ma ta d'aga mai gira sannan ta dawo gabanshi ta zauna.

" Aliyu lokacin yayi da zaka fara neman Janan tun da kana k'aunarta"

Murmushi ya d'anyi sannan yace "bana k'aunar kowa sama dake Zuhriyya"

Itama murmushin tayi sannan tace "na san kana k'aunar Janan nima kuma ina k'aunar ta dawo garemu"

"Ki daina min zancen Janan kin san ba so nake ba ko?"

"To kayi hak'uri amma maganarta dole ce"

Juyawa yayi ya kwanta kawai,tayi murmushi tana kallon shi dan ta san yana son Janan d'in dan babu yadda zaiyi ne.







_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁




_*by SaNaz deeyah*_👄




```Dedicated to Mrs Xerks & Safnah luv```





40

Yau misalin k'arfe hud'u da rabi Mommy na zaune a falo ita da 'ya'yan nata da Raihan duk kansu sun mayar da hankalinsu akan wani program da ake gabatarwa a Arewa24, Janan ce ta shigo tana sab'e da Abba k'arami a kafad'arta.

Dukkansu su ukun hankalinsu ya koma kanta.

'Karasowa tayi gaban Mommy ta durk'usa tace "Asabe tace kina kirana"

"Eh dama coconut juice nake son a had'a mana,kin iya?"

"Eh na iya"

"Yawwa kije kitchen na ajje komai a fridge, kawo Abba na rik'e miki shi"

Murmushi tayi tace "nagode" sannan ta mik'a mata ta tashi.

Har ta d'anyi taku kamar biyar sai Mommy tayi saurin cewa "Yawwa Janan ki d'anyi da yawa saboda ku"

Tun kafin ta kai k'arshe Janan d'in ta tsaya cak tamkar wacce aka zarewa laka.

Jalal,Adnan da Raihan kuwa sunyi mugun d'imaucewa.

Mommy ta mik'e tsaye tana fad'in "ya naga kin kasa tafiya kina mamaki sunanki na gaskiya daya fito daga bakina?"

Jalal yayi saurin mik'ewa tsaye zaiyi magana mommy ta d'aga masa hannu "dakata Yarima ka zauna karka fad'i dan naga ka tsorata "

Adnan ne yayi saurin cewa "Mommy abin ne ya bamu mamaki kin kirata da sunan da ba nata ba,ita fa sunanta Aysha indo"

"Gaskiyane Adnan, saboda kai ka haifeni bani na haifeka ba dole ka nemi yi min wayo"

Kallon Jalal tayi wanda har lokacin ya kasa zama tace "ka saki jikinka Jalal yau dai ga Janan d'in da kake ta yi min k'arya da ita,kun d'auka duk abinda kuke bana lura,ni dama tun da tazo jikina ya bani,dan naso in gane muryarta amma na manta ina na san muryar"

Ta kalli bayan Janan wanda har lokacin ta kasa motsa ko d'an yatsan ta,murmushi tayi sannan ta taka har gaban Janan d'in ta kalleta taga yadda hawaye ya wanke mata fuska sai kawai itama taji hawayen.

"Meyasa kika bari rayuwarki ta koma haka bayan da gatanki?"

Shiru babu magana sai shashshek'ar kukanta "Janan kin san bazan tab'a cutar dake ba ko?kuma tun lokacin da Jalal ya kira muka gaisa naji kin shiga raina,bazan tab'a cutarki ba Janan meyasa kika min haka?yanzu ba dan wata k'awarki Lubna ba da haka rayuwarki zata k'are Janan"

"Lubna" Jalal ya fad'a cike da mamaki.

Mommy ta kalleshi tace "eh tun da kai ka zama mace kana da rauni,ka kasa fad'awa mahaifiyarka gaskiya to ita Lubnar da ta damu da damuwar Janan ai ta kira ta kuma sanar da ni komai"

Raihan sai a lokacin ta mik'e dan ta tsorata sosai da maganar Mommy.

Hannun Janan d'in Mommy taja sannan Janan ta motsa.

Janta tayi har cikin d'akinta ta zaunar da ita gefen gado.

Sai lokacin Abba k'arami ya fara kuka yana mik'a hannu alamar ta d'aukeshi.


Kallonshi kawai take dan jikin nata babu wani k'warin da zata iya karb'arsa.

Mommy ta mik'a mata shi tace "ki bashi yasha k'ila yunwa yakeji"

Karb'arshi tayi kawai ta rungume sai kuma ta fashe da kuka mai tsanani.

Jalal,Adnan,Raihan da sauri suka shigo d'akin.

Raihan d'in ce ta k'arasa gabanta tana fad'in "Janan kiyi hak'uri ki sassauta zuciyarki tun ranar da muka had'u nake son gyara rayuwarki amma kika ce ke a dole sai dai kizo gidannan a 'yar aiki"

Ko kallon ta bata yi ba sai da tasha kukanta ta k'oshi sannan ta fara goge hawayenta.

"Adnan ku fita zamuyi magana"

"Mommy duk abinda ya shafi Janan ya shafemu dan Allah ki barmu kawai"
Jalal ya fad'a ranshi a cunkushe.

Adnan kuwa hawaye yake hannunsa rik'e da hankici idanunsa sun koma tamkar gauta.

"Shikenan" Mommy ta fad'a sannan ta k'ara dafa Janan tace "ki fad'a min labarinki Janan"

Ta d'ago harara garken idanunta ta kalli Mommy ta d'anyi shiru sannan ta fara basu labarin rayuwarta.
Wani gurin sai ta tsaya tayi kuka sosai sannan ta cigaba.

Bata b'oye komai ba a tarihin rayuwarta tun ranar da ta fara soyayya da Aliyu har zuwa yanzu,amma ta b'oye musu cewar Abba k'arami d'an Aliyu ne.

Kawai sai gani sukayi Mommy ta rushe da kuka.

Ganin haka ne yasa Jalal ya koma gefenta ya rungumota shima yana hawaye.

Sai da tayi kuka sosai sannan ta goge hawayen ta ta shafa kan Abba k'arami ta mik'a hannu ta d'auke shi.

"Janan kina nufin wannan yaron aljanna ce tayi masa wankan farko a duniya"

"Nima ita tayi min wankan jego na farko a duniya ta kawo min kunu da abinci ta bani zam-zam da dabino"

"Ikon Allah kenan"

Kallon Jalal tayi tace "yanzu kai har ka biyewa Janan dan tace idan baka yarda tazo a 'yar aiki zata gudu,kai kuma Adnan kaima ka biye musu"

"Mommy wallahi gani nake kamar da gasken zata gudu shiyasa"

"To ai yanzu Lubna ta kirani ta fad'a min komai tun had'uwarku da Janan har rabuwarku kamar yadda Janan d'in ta fad'a yanzu,yarinyar tana kuka tana bani labari tace min bata k'asar tana Spain amma zatazo ta tafi da Janan d'in,nace mata ta bar Janan a hannuna babu abinda zai faru da yardar Allah"

"Mommy munyi kuskure kiyi hak'uri" Adnan ya fad'a.

"Shikenan ya wuce a kiyaye gaba,yanzu zamuje a siyawa Janan kayan sawa da komai amma kafin nan ina son Jalal ka saki Raihan yanzun nan zan kuma saka bikinka da Janan da zarar ta yaye d'anta"

Duk kansu sun kad'u da jin maganar.

Raihan ta durk'ushe k'asa cikin matsanancin kuka ta fara magana "mommy ki rufa min asiri dan Allah, wallahi idan kika rabani da Jalal kamar kin rabani da farin ciki ne"

Janan ta durk'usa a gaban Mommy itama cikin kuka tace "kiyi hak'uri dan Allah wannan hukuncin yayi tsauri,Raihan k'awata ce bazan so na auri mijinta ba sannan na janye batun aure a yanzu kam bani da wannan burin"

Rik'o hannun Janan Raihan tayi tace "hakane Janan kowa ya san muna son junanmu ni dake"

Mommy bata ce masu komai ba ta sake kallon Jalal tace "ka saki Raihan nace ko baka ji ne"

"Mommy kiyi hak'uri,ina son Raihan,kuma ina son Janan duk kansu zan iya zama dasu"

"Jalal ba iyawarka nake nema ba kawai so nake ka cika umarnina" ta fad'a ranta a b'ace.

"Mommy dan Allah kiyi hak'uri tun da yace duk yana sonsu kuma zai iya" Adnan ya fad'a

"Shikenan" ta fad'a sannan ta tashi.

Kawai sai suka ga ta janyo trolley ta bud'e closet tana d'ibar kaya tana zubawa.

"Mommy lafiya?"

"Zan bar maku gidan tun da bani da wani iko akanku"

Shima Jalal hawaye ya fara yana fad'in "Mommy ban san dalilinki ba kin sa ni a duhu Mommy"

"Amma bazan tab'a cutarka ba ko?jiya fa da kunnena naji wayarta da k'awarta,ita kanta Janan ai tayi hak'urin zama da Raihan kawai saboda Jalal ta rik'a wulak'anta ta kamar bata san darajar mutum ba"

Sai kuma ta hau kuka tana basu labarin duk abubuwan da taji,da irin aikin da Janan kewa Raihan bayan ta san k'awarta ce"
Sannan ta k'ara da fad'in "banyi wa Raihan lab'e ba dan ban tab'a yiwa wani ba amma kawai danaji tace ko uwarshi shiyasa na tsaya"

Raihan kuka sosai take tana bada hak'uri amma ina ran Jalal ya b'aci haka ya figeta har falo.
Mommy ta d'auki Abba k'arami ta bishi,, d'akin ya rage daga Janan a tsugunne tana kuka sai Adnan dake zaune gefen gado yana goge hawaye.
Tashi yayi ya durk'usa gabanta yace "Janan ki yafe min dan Allah wallahi akwai dalilin daya sa nak'i dawowa gareki"

'Daga hannu tayi ba tare da ta kalleshi ba,alamu tayi masa na yayi shiru kawai.

"Janan ki fuskance ni dan Allah"

"Babu wata fuskanta da zan maka, kayi min k'aryar suna da asali sannan ka gujeni,wallahi kaine silar duk wata masifa dana fad'a da ba ka gujeni ba da haka baza ta faru dani ba,ban tab'a yiwa wani namiji irin son dana yi maka ba"

"Na san nayi kuskure dana gujeki amma ki sani nayi haka ne dan in bi umarnin Abba da yace in bar garin saboda ki manta dani dan yace bai shirya aurar dake ba,kuma ko an tashi aurenki bazai bawa talaka mara asali ba,na dawo gidanmu da niyyar in kin kai lokacin da Abba zai bada aurenki zanje masa da nawa asalin,watana shidda da dawowa na

Please Login or Register in order to submit comment