You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiga ba"

Shiru tayi shi kuma yayi tafiyarsa.
*
Suna zaune a falon gidansu Lubna.

Ta sunkuyaar da kanta kawai tana kuka dan da taji maganar Janan sai tayi hawaye.

"Ki daina kukan ya isa haka"

'Dago kai tayi ta kalleshi tace "wallahi tun sanda na ganka da Janan na san kunyi mugun dacewa amma yadda Janan ta d'auki son Aliyu ta lik'awa zuciyarta shiyasa kawai na kasa furtawa,mun maka laifi amma kayi hak'uri"

"Bakomai fatana Allah ya dawo mana dasu lafiya"

"Ameen" ta amsa tana goge hawayen fuskarta.

********

_*Bayan wata guda*_

Suna tsaye jikin mota,Muhasin na gefe tare da doctor yana masa bayani akan magungunan da za'a saya.

Jikinta duk yayi sanyi saboda sam bata k'aunar k'ara had'uwa da Aliyu.

Momma ta gane hakan,dan haka ta janyo hannunta tace "karki damu Janan ki rik'a kwantar da hankalinki kinji"

Kai kawai ta d'aga,Muhasin ya dawo ya shiga motar suka tafi.

Sai da suka fara zuwa k'aton chemists suka siya magungunan sannan momma tace Janan tayi musu kwatancen gidan.

Har k'ofar gidan sukaje a bud'e ma k'ofar take dan haka suka kutsa kai suka shiga.

A k'ofar Babban falo sukayi knocking, sun d'an juma kafin a bud'e k'ofar.

Ummi ce ta fito tana kallon su a shek'e.

Kamar bazata matsa ba sai kuma kawai ta matsa tace "Ku shigo"

Bayan sun zazzauna ita kuma Ummi ta haye sama.

Sai jin muryar Umma sukayi tana fad'in "uban me ta dawo yi gidannan?"

Duk Kansu suka kalli gurin.
Tana gaba Aliyu da Ummi na biye da ita.

"Tashi ki fita matsiyaciya" ta fara fuzgar Janan.
Momma tayi saurin cewa "baiwar Allah dakata mana"

Juyowa tayi tana fad'in "ke kuma a suwa"

"Dakata iya haka kada ki yarda kici mutuncin uwata ba tare da kinsan matsayinmu ba"

Sai kuma tayi shiru,shi kuma ya kalli Aliyu ya cigaba da fad'in "dama munzo mu sanar da kai matarka na d'auke da cikinka ba wani abu muke buk'ata ba kawai ina son kasan akwai jininka ko nan gaba"

"Karya kuke wallahi, mu zakuyi wa d'anmu sharri"

Ta juya ta kalli Aliyu tace "ko gaskiya ne?"

Jikinsa a sanyaye ya girgiza kai.
"Naga kayi sanyi?" Umma ta k'ara tuhumarshi.

_idan ban k'aryata hakan ba tabbas komai zai iya faruwa._

Cikin d'aga murya yace "a gidan ubanwa zaki d'ebo cikin shege ki lik'a min"

Janan da tun lokacin da aka fara maganar ta sunkuyar da kanta tana kuka sai a lokacin ta d'agoshi ta kalli Aliyu
"Kaji tsoron Allah ka fad'i gaskiya karka shegantamin d'a Aliyu dan Allah ka fitar dani daga zargi"

"Dalla rufamin baki tanan kika b'ullo kuma?to wallahi ranki zaiyi mummunan b'aci idan har kika cigaba da kiran shegen cikinki a matsayin nawa danni ban tab'a had'a shimfid'a dake ba"

Muhasin ya kalleshi yace "ka yarda muje kotu kuyi li'ani?"

"Muyi mana wayake tsoro" ya mayar cikin b'acin rai.

Momma kuwa sai doka salati take tana hawaye.

Janan ta mik'e tsaye cikin kuka tace "ba sai anyi ba saboda bani da tabbas amma ni na san cikinka ne,amma ka sani ko wata rana kada ka nemi d'anka, ka k'addara baka da d'a dani"

"Dama ai babu,dalla ki fita bana son ganinki"

Da sauri ta wuce ta fita,Momma ta sake kallonsu kawai ta fashe da kuka tace "Allah ya saka miki Janan"

Muhasin kuwa kasa cewa komai yayi saboda yadda zuciyarsa ke tafasa komai zai Iya faruwa.

A farfajiyar gidan jiri ya d'auki Janan ta zube.






*_Masoya sai kun yi min hak'uri dan kwana biyun nan ina busy, kuyi manage da wannan_*









_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_πŸ‘„



```Dedicates 2 Mrs Xerks & Safnah luv```

*_Kwana biyu kunjini shiru,wlh 'yata da cousin d'ina aka kwantar a asibiti_*
_muna barar addu'arku_


_Wannan Shafin sadaukarwa ne gareku masoyana😍na san kun matsu nayi typing._



30

Da sauri Muhasin ya k'arasa ya d'agata yayi waje Momma na biye dashi.

Ganin idon Aliyu duk abinda ya faru, ji yayi kamar ya shak'e Muhasin saboda tsananin kishin Janan da yake.

**********

Ta d'an goge guntun hawayenta bayan ta ji irin tarbar da iyalan Momma suka mata.

"Ba wai shawararku nake nema ba,na gabatar da ita ne a matsayin 'yata a gareku dan karku sakata a wani matsayi na daban daga yau matsayinku d'aya da ita a gidannan" Momma ta fad'a rai a b'ace.

"Wallahi ba'a isa a kawo mana wata haka kurum ace ta zama 'yar uwarmu" Zainab ta fad'a tare da tashi ta wuce ta bar falon.

Muktar ma tashi yayi yana gunguni ya bi bayan Zainab.

Momma cikin b'acin rai ta kalli Humaira tace "kema rashin kunyar zaki min?"

Itama Humaira ranta a b'ace take kallon Momma tana fad'in "taya zaki d'akko mutum kawai kice wai zata zauna a gidan nan"

"To gidanku ne ko gidana?"

Babban d'anta Umar yayi saurin cewa "gidanmu ne Momma saboda muke da gadon gidannan"

Baki kawai ta saki tana kallonsa cike da mamaki.

Haka rayuwar gidan Momma take duk kanin 'ya'yanta sun rainata Muhasin ne kad'ai ya fita zakka a cikinsu hakan ya samo asalina ga irin gatan da tayi musu fiya da misali.

Umar shine babba,yana da mata da 'ya'ya biyu kuma a cikin gidan part d'insa yake.
Muhasin shine na biyu baiyi aure ba amma dai yana shirin yi,sai Muktar saurayi yana l3,Zainab tana l1 sai Humaira itace Auta tana Ss1.

Mahaifinsu ya dad'e da rasuwa tun Humaira na 'yar shekara 3 a duniya Momma itace gatansu babu abinda suke nema su rasa daga gareta tun mahaifinsu na da rai yakan ce mata wannan ba gata bane tana lalatasu ne kawai,amma sam bata yarda.

********

Momma na zaune a gefen gadon ta zuba uban tagumi,Janan na gefenta tana mamakin yadda akayi yaranta har suka rainata haka.

Zamewa tayi k'asa ta durk'ushe gaban Momma tace
"Ina neman alfarma a gareki"

'Dago ido tayi ta kalleta tare da janyota tana fad'in "haba Janan taya zaki tsugunna har k'asa dan kina neman alfarma"

Hawayen daya so zubo mata ne tayi saurin mak'aleshi tace "bakomai! Dan Allah ina so ki barni in tafi saboda ki samu zaman lafiya keda yaranki"

"Karki damu Janan ko ki tafi ko karki tafi haka halinsu yake ba fasawa zasuyi ba"

"Amma........"
"Ya isa Janan pls karki damu kinji"

Haka Momma ta jata ta nuna mata d'akin da zata zauna.
'Daki ne daya tsaru da duk wani kaya na bedroom sai toilet a gefe.

Haka rayuwar Janan ta cigaba da tafiya a gidan,Sam bata jin dad'in zama da 'yan gidan idan ba Muhasin da Momma ba.

Haka ta daure ta cigaba da renon cikinta cikin k'unci da b'acin rai.

*_6 Months later_*

Tana zaune akan kujera tana danna remote tana neman canza tasha kawai taji an warce remote d'in.

Da sauri ta d'ago kai ta kalleta tace "lafiya?"

"Oh tambayata kikeyi ma,bak'ar munafuka kawai"

A hankali ta mik'e tsaye saboda cikin jikinta ya fara tsufa.

Kallon Zainab tayi tace "ya isheki haka dan na gaji da rashin mutumcin da kuke min"

"Da kin gaji da kin bar gidanmu saboda ba k'aunarki muke ba kuma ba k'aunar ganinki a gidanmu muke yi ba"

"To ai ba ku kuka kawoni gidan ba dan haka baku isa ku kureni ba babu yacce kuka iya dani"

"Oh keda kanki kike fad'ar haka?"

Da sauri ta juya ta kalli wanda yayi maganar.

Taku kad'an ya k'araso dashi gurinta,wani mari daya zabga mata yasa ta tsungunna har k'asa hannunta rik'e da kuncinta.

Umar ya ja hannunta ya d'agata yace "ki gaggauta barin gidan nan tunda bana ubanki bane ko dan kinga ban d'auki mataki akanki ba 'yar matsiyaci kawai"

Kallonshi tayi lokaci guda idanunta suka koma jajir,a gigice ta juya ta d'auki glass cup d'in dake kan center table ta fasa sannan ta nufo inda Umar yake gadan gadan zata caka masa.

Zainab ta d'ora hannu aka ta k'walla ihu,shi kansa Umar kawai d'ora hannu yayi aka ya runtse idanunsa.

"Janan!" Ya kira sunan a gigice,itama a gigice ta juya ta kalli Muhasin.

Da sauri ya k'arasa gurin ya rik'e kwalbar a hankali.
"Karki aikata kisan kai Janan"
Sakar masa tayi kawai ta durk'ushe a gurin ta rusa kuka.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,Abba kana k'ark'ashin k'asa ana zagar min kai,Abba koda baka nan bazan yarda sunanka ya wulak'anta ba"

Kuka take sosai a fili,duk kansu sai da jikinsu yayi sanyi musamman shi Umar duk sai yaji ya kunyata.

Muhasin ya durk'usa gabanta yana fad'in "dan Allah kiyi hak'uri Janan ya isa haka"

Girgiza kai take tana kallonsa tace "bansan me nayiwa Mameey ba da har zasu tafi su barni tsawon watannin nan a koda yaushe ina nemansu amma basu nemana,ko dai na tafka babban zunubi shiyasa Allah yake jarabtata da wannan abubuwan"

"Yau zan bar gidan nan zan bar muku gida in tafi can wani gurin in k'arasa rayuwata,zan dogara da Allah da kuma kaina,bazan k'ara zama k'ark'ashin inuwar wani ba bare har a zagar min Abbana,komai iyayena suka min bazan tab'a yarda su wulak'anta ba"

Jin haka yasa Muhasin ya d'aga waya ya kira Momma yace ta dawo gida ba lafiya.

Zainab da Umar kuwa sai sukaji tamkar maganar da Janan ta fad'a dasu take.

_yarinyar k'arama har ta san ta d'auki mataki akan dan an zagi iyayenta zagin ma ba wani na azo a gani ba,mu kuma da muke kallon idon Momma muci mata mutunci fa?matar da tayi d'awainiya damu tun muna ciki dole mu gyara halayenmu_ Umar ya fad'a a zuciyarshi.

Zainab ma a zuciyarta tace _Ashe haka soyayyar iyaye take?insha Allah daga yau na daina yima Momma rashin kunya._


Suna nan a falon sunyi cirko-cirko a haka Momma tazo ta same su.

Zainab ta ruga gurinta ta rungumeta sai kuma ta fashe da kuka.

Jikin Momma gaba d'aya yayi sanyi,yaushe rabonda Zainab tayi hugging d'inta,tabbas ba lafiya ba.

Kallon Muhasin tayi tace masa "Ina Janan?"

Jikinsa a sanyaye yace "tana d'akinta"

Kallon Zainab tayi da har lokacin bata daina kuka ba tace "meya faru?lafiya?"

'Dago idanunta tayi da suke zubda hawaye tace "ki yafe min Momma na tuba bazan sake musu dake ba,bazan sake yin abinda bakyaso ba"

Kallon Umar da Muhasin tayi Wanda sun kasa zama ma.

Janyo hannun Zainab tayi suka k'arasa kan kujera suka zauna.

"Muhasin ka fad'a min meke faruwa?ka kirani a waya ina gurin aiki ka d'agamin hankali"

Umar ne yayi saurin durk'usawa k'asa yace "Momma ki yafe mana laifukan da muka miki,hak'ik'a yau abinda Janan tayi ya mutuk'ar d'aga mana hankali,ace babba dani na ajje yara amma bana daraja tawa mahaifiyar?idan yarana suka girma taya zasu daraja ni?"

Kallon mamaki kawai Momma take binsu dashi,shi kansa Muhasin mamaki yake.

"Shin mafarki nake ko gaskiya" Momma ta furta cikin raunanniyar murya.

"Momma ba mafarki kike ba,mune a zahiri muke neman yafiyarki" Zainab ta fad'a

Kallon Muhasin tayi tace "ka fad'a min gaskiya meke faruwa?"

Zama yayi a k'asa ya bata labarin duk abinda ya faru.

Da sauri ta tashi ta nufi d'akin Janan suka rufa mata baya.

Tana tura k'ofar ta hango Janan d'in kwance a tsakiyar gado ta saka hannayenta ta rufe fuska.

Har kan gadon Momma ta hau ta cire hannun nata daga fuska.

A hankali ta bud'e idanunta hawaye har lokacin bai daina zuba a cikin su ba.

Da sauri ta tashi zaune bakinta na rawa tace "bana gani"

"Bakya gani kamar ya?" Momma tayi tambayar tana d'an jijjigata.

"Na shiga uku dan Allah ku taimakeni wallahi bana ganinku bana ganin komai sai duhu"

Muhasin yayi saurin hayowa kan gadon yace "kin ganmu fa ki k'ara kallonmu sosai"

Idonta a kan Momma yake saidai bata iya ganin komai.

"Shikenan bazan cika ma Abba burinsa ba bazan sake ganin Mameey da 'yan uwana ba,bazan ga Salman ba bazan ga abinda zan Haifa ba,ya Allah ka yafe min idan wani laifin nayi kake hukuntani da haka"

Wasa-wasa har farfajiyar gidan suka fito da ita amma bata gani.

Lokacin ma Humaira ta dawo daga skul abin ya bata mamaki ta kama hannun Janan har wajen rumfa tace "kin gane a inda muke"

Girgiza kai tayi alamar a'a.

A gurin ta sunkuya ta cigaba da hawaye Momma ta rungumeta tana kuka itama.

Dukkanin iyalan Momma hatta matar Umar da tafi kowa wulak'anta Janan sai da tayi mata hawaye lokacin da Momma na basu labarin rayuwarta.

_Asibiti_

Tana kwance a kan gadon asibiti idanunta nannad'e da bandage bama zasu gane bacci take ko idonta biyu ba.

Muktar ya goge hawayen idonsa yace "Momma bana son baiwar Allah nan ta mutu ban nemi gafarar ta ba,wallahi mun azabtar da ita sosai a cikin gidannan musamman idan kun tafi wajen aiki keda Muhasin, amma bata tab'a ko nunawa ba bare ta fad'a muku,hatta Yaya Umar haka zaisa taje gidanshi tayiwa matarsa duk wani aikin gida"

Humaira ta kalli Momma tace "Allah ya sani ta girmeni amma ni babu abinda yake had'ani da ita sai gori da hantara,wallahi har lemo na tab'a watsa mata lokacin da friends d'ina suka zo itama ta fito falo"

Zainab kuwa kanta a k'asa tana hawaye dan ta san ita nata yafi na kowa bama zata iya magana ba.

Momma tasa hannu ta goge hawayenta tare da kallon Janan cikin tsananin tausayinta.

Muhasin ya kalli inda Janan ke kwance yace "Wallahi Momma har yanzu abinda likita ya fad'a na kasa gaskata haka,wai dama da gaske kuka yana janyo makanta"

"Gaskiya ne yawan kuka yana sa makanta"

"Ya Allah ya bata lafiya ya raba ta da wannan azababben ciwo"

Duk kansu sukace "ameen".

**********

Mommy ta kalli d'an nata cikin jindad'i tace "tunda har Allah yasa ka dawo gida bazaka sake komawa ka barni ba"

Yayi murmushi ya d'an shafa kansa yace "Mommy ga yarima a kusa dake"

"Shima da yaga ka gujeni sai ya gudu Kaduna"

Jalal yayi murmushi har sai da hak'oransa suka bayyana,ya kalli Adnan yace "ina fa zuwa duk k'arshen sati kuma nama kusa gama karatun"

"Kai yarima duk karatun da kayi bai isa ba?"

"Wlh a gurin aiki aka buk'aci mu kawo diploma certificate dole na tafi nayi"

"Eh hakane dole kayi tunda ance Ku kawo"

Mommy tayi dariya tace "oh ka dawo kenan shine zaka fara shigar masa ni bani da dangi ko"

"A'a Mommy mu mun isa muce haka"

"Kunyi yawa ma gashi tun yanzu har ka fara nuna min wariya"

Dariya yayi tare da fad'in afuwan Mommy"

"Nak'i yawon"

Dukkansu suka saka dariya cikin farin ciki da annashuwa.

"Ya bayanin aure Adnan?"
Mommy ta watso masa tambayar.

Kallon Jalal yayi suka had'a ido sannan ya dawo da kallon sa gurin Mommy.

Shiru yayi baice komai ba,itama ta kafeshi da idanu kawai.

"Kayi min shiru kana kallona,Jalal ya fito da mata kai muke jira sannan a saka rana gaba d'aya"

"Mommy ni kuma?"
"Eh mana ai na fad'a maka tun kana can"

"Mommy kiyi hak'uri ban shirya yin wani auren ba a halin yanzu babu macen da take burgeni bare har na aureta"

"Ni fa na saka maka doka Adnan" ta fad'a rai a b'ace

"Kiyi hak'uri kawai Mommy" yana neman barin gurin Jalal yayi saurin rik'eshi.

Ita kuwa ranta a b'ace ta tashi tayi side d'inta.

Jalal ya maido kallonshi ga Adnan yace "meyasa kayi haka Adnan?"

Murmushi yayi mai had'e da k'walla yace "bazan iya yi mata k'arya ba Yarima nafiso na fito fili na fad'i gaskiya dan bana son sake tsoma kaina a wata masifar"

"Adnan wannan ciwo da kake dashi bazai hanaka yin Aure ba ka rayu da matarka harma ku samu zuri'a"

"Wane Aure kenan?auren wadda take da cuta irin tawa bashine kwanciyar hankalina ba,nafiso na rayu da Mommy harna mutu a gabanta"

"Ka daina zancen mutuwa haba Adnan bafa kai kad'ai ne keda wannan larurar ba"

"Amma kaina na sani ko saboda bilkis ta zalunceni bazan sake aure ba,zan cigaba da bawa Mommy hak'uri akan hakan"

"Shikenan Allah yasa haka shine mafi alkhairi"

"Ameen nagode da fahimtata da kayi,ya sunan surukar tawa?"

"Raihan a poly take karatu"

"Okay amma dai idan ka aureta zaka bari ta cigaba da karatu ko?"

"Eh sosai ma kasan ni d'in d'an boko ne"

Dariya Adnan yayi tare da fad'in "yaushe aka saka bikin?"

"Su baffa sunje sun kai komai har lefe kai kawai ake jira Mommy tana son a had'a da naka"

"Oh kenan su can basu matsa ba"

"Eh baffa yace zai musu waya ya sanar dasu date d'in,naji dai Mommy tace bazai wuce 1 month ba tunda nace mata anan gida zan zauna dan har an gyara part d'ina da naka"

"Gidanka fa"

"Zan zuba 'yan haya kanaji Mommy na complain wai bamu son zama a gurinta"

"Hakan ma yayi Allah ya sanya alkhairi"

"Ameen bros"

"Tashi muje ka rakani rarrashin sweet Mom kaga tayi fushi dani"

Dukkansu suka saka dariya.








_Sadeey S Adam_✍
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁



_*by SaNaz deeyah*_πŸ‘„


```Dedicated 2 Mrs Xerks & Safnah luv ```



```Sadiya Mrs Xerks d'ita ni kad'aiπŸ˜†.
kin zama tamkar 'yar uwa a gareni,u alwayx luv me nd nvr hurt me.```
_Kin zamo jinin jikina😍_


_wannan shafin nakine Zarah Darma,nagode da kulawarki a gareni😍_



31

Satinta guda bata ganin komai.

Har sai da aka yi mata aikin ido sannan aka d'orata kan magani.

Yau ma kamar kullum k'arfe 7:00am Zainab suka shigo ita da Humaira,Humaira na sanye da uniform d'inta dama sai tazo take wucewa skul.

Bayan sun gaida Momma suka zauna a gefen gadon Humaira ta kalli Janan tace "Aunty sannu ya jikin?"

Murmushi Janan tayi ta kalleta tace "da sauk'i"

"Momma naga kamar tana harararmu" Zainab tayi maganar.

Momma ta d'anyi murmushi sannan tace "Zainab idonta ne ya koma haka,harara garke(kallon ruduwa) idan tana kallon ki zakiyi tunanin gefe take kallo,idan tana kallon gefe kuma zakiyi tunanin ke take kallo ko kuma wani lokacin idan tana kallonki zakiyi tunanin harararki take"

"Momma shikenan idanunta ya koma haka?"

"Eh mana"

Kallonta Zainab tayi tace mata "sannu Janan Allah ya k'ara lafiya"

"Ameen Zee" ta amsa tana murmushi.

Sun dad'e suna hira har su Muhasin suka zo za'a mayarda Zainab gida itama ta shirya Humaira kuma a kaita skul.

Zasu fita kenan Janan tace "yawwa Humaira dan Allah ki sanmin takarda da biro mana"

"Okay" ta bud'e skul bag ta d'akko note buk da pen ta mik'a mata.

"Ki barshi a gurinki idan na dawo na karb'a.

" to nagode sosai "
Murmushi tayi tace "karki damu".

_5hrs later_

" Janan! Janan!! To ina ta fita kuma"

Bud'e toilet tayi taga babu kowa,ta fita har farfajiyar asibitin bata ganta ba sai tayi tunanin ko ta gaji da zaman guri d'aya shiyasa ta fita ta d'an zagaya.

Zama tayi ta cigaba da duba magangunan sannan ta sake gyara gadon.

Kusan awa d'aya da rabi Janan d'in bata dawo ba dan haka ta tashi da sauri ta sake fita tana dubawa.

K'walla ce ta taru a k'asan idanunta ta fara fad'in "Janan dan Allah karki gudu ki barmu,ina sonki Janan kin shiga ranmu da yawa"

Waya ta d'akko ta kira Muhasin ta sanar dashi duk abinda ke faruwa.

Cikin minti talatin ya iso asabitin
"Momma wai ya akai ta fita baki sani ba?"

"Wallahi naje karb'o sauran magunguna a pharmacy kafin in dawo naga babu kowa"

"Mu tambayi masu gadi ko sun ganta tunda asibitin ba wani girma ne dashi ba kuma gate d'in shiga shine na fit.............."
Bai k'arasa maganar ba ya hango 'yar takarda a gefen gadon ta d'ora biron da littafin a gefe.

Da sauri ya k'arasa ya d'auki takardar ya ware ta ya fara karantawa a fili.

_Momma da Yaya Muhasin nagode sosai da karamcin da kuka nuna min,Momma kiyi hak'uri zanyi kewarki da yawa amma babu yadda na iya zama bai kamani ba,zan tafi farautar hak'inmu sannan zan rik'e kaina iya wuya iya dad'i bazan k'ara zama inuwar da ba tawa ba,Yaya Muhasin ina maka fatan samun mace tagari a rayuwarka,ina fatan zaku kasance cikin yi min fatan alkhairi a koda yaushe nima zan cigaba da yi muku,dan Allah karku nemeni dan bazaku ganni ba tunda ba b'ata nayi ba,ina fatan Allah ya k'ara had'a fuskokinmu da alkhairi ameen._

"Shikenan! Ashe dama abinda zata rubuta kenan shiyasa ta karb'i paper a hannun Humaira" Momma ta fad'a lokacin da hawaye suka sauka a idonta.

"Allah sarki Janan Allah ya kare mana ke a duk inda kika shiga a fad'in duniyarnan"
Muhasin ya furta

Momma sunkuyawa tayi kan gado tana kuka na tausayin Janan "yarinya k'arama da batafi shekara 17 a duniya ba" ta furta tana hawaye.

"Momma nayi miki alk'awarin duk sanda Janan ta dawo kona ganta bata da wani miji kamar ni koda kuwa da matana a lokacin"

"Nagode Muhasin kaima kayi k'ok'ari ai,saboda sanadin Janan 'ya'yana sun shiryu ina son zama da Janan"

*********
Janan ta sadda kanta tana hawaye lokacin da motarsu ta tashi daga Yola zuwa kano.

Kusan awa d'aya suna tafiya amma bata d'ago kai ba.

Matar dake gefenta ta dafa kafad'arta tace "baiwar Allah meyayi zafi haka tun d'azu kina kuka ko gajiya bakyayi ga da alamu tsohon ciki ne dake"

'Dago kai tayi ta kalli matar tace "karki damu da kukan da nake saboda mutane da dama irinki sun rarrasheni amma nak'i dainawa,hawaye ne ya jawo k'wayar idona ta canza daga lafiya zuwa akasinta,idona ya koma harara garke duk a sanadin kuka,kuka ya fiye min dad'i fiye da komai a rayuwa"

Ai kuwa wannan furucin nata yaja mata cece kuce a cikin mota kowa na fad'in albarkacin bakinsa.

Duk tana jinsu amma bata ce komai ba har sai da wani yayi maganar da tayi mata zafi sosai.
"Aikuwa ya kamata a kaiki gwajin k'wak'walwa domin mara hankali da tunanin ne kad'ai zaice kuka nada dad'i"

Bata ko kalli inda yake ba cikin muryar kuka tace "hakane bani da hankali saboda ko kaine aka yiwa abinda aka min zaka haukace,idan na haihu d'ana ya girma wa zan nuna masa a matsayin mahaifi?bayan ban tab'a aikata alfasha ba kuma da aure na samu cikin amma ina ji ina gani mahaifinsa yace ba d'anshi bane kawai saboda son zuciya da rud'in duniya,ka gaya min idan nayi kuskure da nace kuka yafiye min komai"

Nan ma hayaniya aka fara ana ta zaginsa,wasu na cewa insha Allahu zaiga sakayya wasu na cewa Allah yasa karya k'ara haihuwa a rayuwarsa kuma idan yazo neman d'ansa karta bashi.

Ita dai kukanta take bata k'ara saurarar kowa a cikin su ba.

Matar ta d'ago kanta ta d'ora kan cinyarta tana jijjiga ta.

Sun sha tafiya mai nisa har saida taga kamar baza suje kano ba saboda bata tab'a yin tafiya mai nisan haka a mota ba,ko yola da sukaje da Momma a motar gidane bataji wahala sosai ba,yanzu kuwa ga tsohon ciki.

Kusan k'arfe goma na dare suka sauka a kano.

Daga ita sai hijabin jikinta ta sauka ta d'an matsa daga gefe can.

Matar tazo ta tsaya kusa da ita tace "bara mijina yazo sai mu rage miki hanya ko"

Ta kalleta tana murmushin k'arfin hali tace "karki damu zan hau napep sauri nake"

"Dan Allah ki bani number ki muna gaisawa"

Ta sake yin murmushi tace "bani da waya"

"Toooo! Ai kuwa ina son muna gaisawa kawai naji ina tausayinki,dan Allah ki bani address d'inki tunda kince baki da waya"

"Eh to ki bani naki in Allah yayi da rabon zamu sake gaisawa sai na nemeki"

Da sauri ta bud'e jaka ta d'akko compliment card ta mik'a mata.

"Idan ba damuwa ki haskamin in gani"

Ba musu matar ta kunna torch light d'in wayarta ta haska card d'in.

"Okay na gani gashi"
"a'a to ki rik'e mana"
"A'a na rik'eshi a brain d'ina idan na karb'a zan iya yardawa"

"Dan Allah idan kin samu lokaci ki ziyarceni,sunana Hajara kefa?"

"Sunana Janan Baku da damuwa zan ziyarceki insha Allah"

"Nagode Janan"
"Nima nagode"

Napep ta tara ta hau tana d'aga mata hannu.

"Hajiya ina muka nifa?" Mai napep yayi tambayar.

"Tasha zaka kaini inda zan hau motar katsina"

"To ai dare yayi hajiya ki bari sai da safe saboda motar dare bata da dad'i ga mace musamman ke dana ganki da tsohon ciki"

"Okay ka kaini tashar sai in kwana a can saboda ina son zuwa katsina kafin fitowar rana"

"Hajiya ki fad'i dai unguwar da zan kaiki ki kwana tasha ai dandalin 'yan shaye-shayene akwai had'ari ko baki da 'yan'uwa anan?"

"Nan nace ka kaini Malam ba fa kyauta zaka kaini ba kudinka zan baka"

"Allah ya huci zuciyarki ban san abin zai b'ata miki rai ba"

Shiru tayi bata sake ce masa komai ba,ya kaita har tasha ta sinto kudi a gefen zaninta ta bashi.

Tana shiga kuwa da warin taba ta fara arba,wani amai ne ya taho mata tayi saurin toshe baki da hanci ta wuce.

Can baya inda ba mutane taje ta shimfid'a d'ankwalinta ta kwanta ta cigaba da kuka k'asa k'asa.

Kusan awarta biyu a gun taji ana fad'in "babaaa ga mutanenmu anan"

Da sauri ta tashi zaune tana kallon su duk sun tsaya mata a ka.

"Ke taso nan"

Bakinta na rawa tace "dan Allah kuyi hak'uri"

"Ai ke zamu bawa hak'uri dan baza muga kayanmu mu k'yale ba"

"Duk wanda ya tab'ata sai ya bak'unci lahira"

Duk suka juya suka kalleshi,ganin mutumin ne yasa suka fara k'ok'arin guduwa, ya nuna su da bindiga yace "Wanda kuma ya k'ara motsawa saina fasa k'wak'walwarsa"

Hannu suka d'aga suna fad'in "yallab'ai ayi hak'uri wannan fa yawa ne ko mun shiga cell zamu fito"

Please Login or Register in order to submit comment