You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ita ba,ba kuma sau d'aya ba.

"Allah ya isa,Allah ya tona muku asiri ya wulak'anta ku tsinannu"

Shine abinda Umma ta fad'a cikin matsanancin kuka.

Wani k'aton k'arfe d'aya daga cikin su ya d'akko sannan yace "mu kike fad'a wa haka?" A k'afa ya doka mata k'arfen sannan ya sake d'agawa yayi mata fashin kwakwa aka,wani mahaukacin k'ara tayi ta zube anan cikin jini"

Da sauri suka fita dan sanarwa ogansu sun gama.

Ummi kwance cikin jini haka Umma ma.


"Ku sakasu a mota ku watsar dasu a bakin titi sannan a darennan a samo min wadda zan kwana da ita"

"Yallab'ai ina zamu zamu mace a darennan in ba karuwa ba?kuma kace kafi son nutsatstsu"

'Dago kai kawai yayi ya kalleshi.
A tsorace yace "sorry yallab'ai"

Da sauri suka shiga suka fito dasu ba tare da sun tsaya duba ko suna da rai ko sun mutu ba.

Har zasu fita gaba d'aya yace "Faisal ka dawo mu jirasu dan naga fuskarka na nuna alamun tsoro kamar yau ne ka fara"

"Abokina amma duk abinda muke babu wacce ta tab'a bani tausayi kamar yarinyar nan dubeta kamar gawa fa"

"Itama uwar tata da kuka buga gata kamar gawar"

"Bazaka fahimta ba Ayuba wallahi yarinyar mun wahalar da ita da alama yarince d'anya"

"To sai me? Ban tab'a jin dad'in mace ba kamar yarinyar nan dan dai idan nayi amfani da mace bana kuma yi sannan bana ajje mata a gidana da wallahi dadirona zata zama"

Shiru kawai Faisal d'in yayi ya tuno yadda take ihu da ranta lokacin da suka cin mata.

Kai ya dafe tare da sunkuyar dashi.


**********

Likitan na tsaye jikin gadon da Ummi ke kwance har lokacin bleeding take,bedsheet d'in da aka rufeta a jik'e jigif.

Doctor ya juyo ya kalli d'aya daga cikin 'yan sanda uku da ke tsaye yace "Muna samun case sosai na fyad'e amma bamu tab'a samun irin wannan ba"

"Kamar ya kenan?" 'Dan sandan yayi tambayar.

Ajiyar zuciya doctor yayi sannan yace "ba mutum d'aya bane yayi amfani da ita sannan anyi amfani da ita kusan sau goma a lokaci d'aya"

Da sauri d'an sandan ya rufe ido tare da yin salati.

Doctor ya cigaba da fad'in "ya kama ta ku 'yan sanda kuyi hob'b'asa dan ganin an kauda yawan fyad'e a k'asar nan,dubi yarinyar nan tamkar gawa,har yanzu mun rasa yadda zamu tsayar da zubar jinin nata dole sai an had'a da aiki,itama waccan matar tana zan an kasa d'aura k'afar,k'ashin gurin yayi daga-daga, kanta kuma sai aske gashin aka yi sannan aka mata d'inki da alamu tazo ceton yarinyar ne su kuma suka amfani da wani abu mai k'arfi suka k'wad'a mata a k'afa da kanta,ya kama ta kuyi bincike sosai a kama wannan mutane marasa imani"


"Muna ta binciken akan hakan,saboda har yanzu an kasa samun kowa nasu,a bakin hanya wani bawon Allah ya gansu shine aka sanar damu,ga 'yan jarida na k'ok'arin d'aga mana hankali shiyasa muka zo nan dan bana son 'yan jarida su shigo cikin abinnan zasu k'ara b'ata mana suna wajen al'umma"

"Zamuyi k'ok'ari wajen ganin sun samu lafiya"

Hannu ya mik'a masa suka sakeyin musabaha sannan doctor ya fita.

Matsawa yayi jikin gadon ya sake kallonta ya girgiza kai sannan ya juya zai fita tayi saurin rik'o hannunsa.

Da sauri ya juyo ya kalleta.
Muryarta a sark'e tace "ka.....kkk..kace...Jan...Jannn.....Janan tat..ta yafe min"

"Janan?" Ya maimaita sunan.

Kai ta d'aga cikin jinjiki da hawaye tace eh.

"A ina kike?ina Janan d'in?su waye suka miki wannan abin"

"Kad......"
Kakarewa tayi idonta ya fara kakkafewa da k'yar ta iya yin salati daga nan bata kuma yin motsi ba ta rufe idonta hawaye suka zubo.

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un" ya furta lokacin daya tab'a tsintsiyar hannunta yaji ta daina aiki,yakai hannunsa jikin hancinta yaji babu numfashi.

"Kirawo doctor" ya fad'a da k'arfi.

"Okay sir"

Su duka suka fita suka dawo da doctor.

Sun rufe gurin sun gama duk wani gwaje-gwajensu sannan suka janye abin.

Ganin an rufeta ruf ne yasa ya tabbatar da ta rasu.

"Ya kamata a nemo 'yan uwanta su d'auki gawarta kuyi wani k'ok'arin"

Fita yayi ya bar shi tsaye yana zulumi.















_Sadeey S Adam_โœ
๐Ÿ๐Ÿ๐Ÿ
*DIREBAN GIDANMU*
๐Ÿ๐Ÿ๐Ÿ



_*by SaNaz deeyah*_๐Ÿ‘„




```Dedicated 2 Miss Xerks & Safnah luv```


*_Ke ta daban ce Miss Xerks_*



_Groups d'in da suke bibiyan novel d'ina nagode sosai._



```Na baki kyautan shafin nan Zahrah Mansur```



_Godiya ta musamman da fatan alkhairi ga_
*TASKAR SANAZ*
&
*DIREBAN GIDANMU FANS*



47

Tunani ya rik'ayi wane gari ne kad da bai gane ba.

Yafi minti 50 a tsaye cak yana tunanin wane gari take son fad'a.

"Kad.....Kaduna" yana fad'a d'aya daga cikin yaransa ya shigo d'akin.

"Yallab'ai a gefen zanin waccan matar aka samo wannan wayar"

Da sauri ya karb'a ya kunna.

Number farko ya fara d'auka a wayarshi sannan ya duba dialpad yaga duk dialed numbers d'in ciki sunan Aliyu ne.

Da sauri ya kira ya kara a kunne.

Ringing biyu tayi Aliyu ya d'aga.

Jin abinda ya faru ba k'aramin d'aga masa hankali yayi ba.

Babu shiri suka taho Kano dashi da baba Isa da baba Idi.

Awa guda da rabi ta kawosu kano asibitin doctor warshu dake 'yankaba saboda mahaukacin gudun da yayi bana wasa bane.

Ganin gawar Ummi da yanayin da Umma ke ciki unconscious ba k'aramin sake d'aga masa hankali yayi ba.

Kuka sosai yake kamar k'aramin yaro yake fad'in "ban san ya akai na koresu ba,ban san meyasa nace su bar gidan ba"

Jiri daya d'ebeshi anan ya zube,da k'yar shima aka samo kansa ya farfad'o.

Sai da 'yan sanda sukayi cike-cike akan case d'in sannan suka bada gawar Ummi aka kuma tafi da Umma dan su ba mazauna kano bane dole su tafi can su cigaba da jinyarta.

Anan ne 'yan jarida suka samu damar yin cincirindo akai.

Hatta Ja'afar bai tsira ba duk yadda yaso zamewa amma sai da suka samu damar cin masa.

Anan ne ya d'auki alk'awarin kamo duk wanda yake da ruwa da tsaki a wannan aika-aikar.

Yana shiga falon ya zube a k'asa.

"Namijin lafiya?"

Ajiyar zuciya yayi yace "Mammy case d'in yarinyar nan"

"Eh ina jinka an gano mutanen da sukayi aika aikar?"

"Ina fa,yarinyar ta rasu har 'yan uwanta sunzo sun d'auki gawar da waccan matar itama ashe mahaifiyarta ce,har suka tafi bata san inda kanta yake ba"

"Wa iyazubillah ya Allah ka tona asirin wannan shaid'anun mutane"

"Ameen Mamyna nima nayi alk'awarin kamo duk wanda keda hannu a wannan ta'asar,ina neman k'arin addu'a Mammy"

"Allah ya baka iko ya shigar maka gaba a duk wani al'amuranka Namijin duniya"

"Ameen Mammyna,kuma kinsan abinda ya tsaya min a rai,yarinyar kafin ta rasu tace min wai ince Janan ta yafe mata"

Janan kuma?"

"Haka tace"

"To ko Janan d'in da muke nema wannan yarinyar da ta kwana a nan?"

"Nima shine abinda ya tsaye min a rai"

"To amma ai ita wannan Janan d'in 'yar katsina ce su kuma wad'annan kace kaduna ne"

"Hakane kuma ba ita kad'ai bace mai sunan,ina ma zanga Janan d'in da take nufi in rok'ar mata gafara wallahi na tausaya mata sosai da k'yar ta iya fad'ar sunan"


"Wallahi ni kuma sai na tuno da Janan d'in da tazo nan inajin yanzu har d'anta ya girma kusan shekara uku fa kenan"

"Wallahi nima ita na tuno Mammy"

"Kuma tace zata neme mu amma shiru"

"K'ila ta manta damu ne gashi mu muna ta tunota"

"To Allah yasa tana cikin k'oshin lafiya a duk inda take"

"Ameen,Mammy ina yarannan naji gidan shiru"

"Sunje gidanka wai su taya Auntynsu hira tunda ka fita tun safe"

"Okay".




A b'angaren su Aliyu kafin suje gida tuni an fad'awa 'yan uwa da abokan arzik'i.

Dan haka cikin gidan da waje tuni ya cika da mutanen k'auye dana birni da yake yanzu ya zama mai kud'i ganin manyan motoci a gurin ba matsala bane.

Anyi mata wanka sannan aka yi sallah aka d'auke ta zuwa gidanta na gaskiya.

Har a lokacin Umma bata dawo hayyacinta.

Likitoci har hud'une a kanta a rana,sannan sunyi zarya a gidan daga safe zuwa dare har sau biyar duk dan ganin an samo kan Umma.

Likitan gargajiya ne yayi mata dorin k'afar ya sanar musu cewa nan da wata guda zai dawo a sin ce.

Zuhra kam hawaye yak'i tsayawa a idonta dan ko shakka batayi itace sila,duk da tana ganin alhakin Janan ne ya fara bibiyarsu,tunaninta d'aya ina zata ga Ummi bayan ta rasu,so take kawai ta rok'i gafararta duk da ta san ba wani abu ta aikata mata ba illa tsamgwamar da take kallon abin a matsayin ramawa Janan.

Idan ta zauna bata tunanin komai sai irin rayuwarsu a k'auye ita da Ummi k'awayene sosai kafin ta auri Aliyu,hakan ba k'aramin kuka yake saka ta ba.

Kwanan Ummi biyu da rasuwa Umma ta dawo hayyacinta.

Kuka sosai tasha kamar ranta zai fita da taji labarin Ummin ta rasu,Aliyu kuwa gafara yayi ta rok'arta,a ranar ta rantse yafi sau a k'irga kan cewa idan har ya cigaba da zama da Zuhra sai ta tsine masa,a haka ya lallab'ata yace tayi hak'uri ayi sadaka saboda mutane.

Shi kansa yana jin mutuwar Ummi har cikin ransa,yadda suka tashi da son juna,sannan tun suna fama da talauci yake mata alk'awarin inganta karatunta,sai gashi yana yin aure komai ya dagule,Ummi ta tambayeshi abubuwa da yawa yak'i yi mata bayan yana da halin yi d'in kuma Ummi nada hak'k'i a kansa,tana da burin yin karatu da kuma driving amma har ta mutu bai cika mata wannan burin ba,kullum tayi maganar ma ranta saiya b'aci.

_idan da Janan ce bazata aikata haka a gareni ba,Janan na da tausayi da tawakkali,lokaci yayi da zan nemi Janan da yarona in rungumi kayana dan na san ta haihu yanzu gashi har yanzu shi kad'ai ne d'ana gudan jini na._

Abinda ya ayyana kenan dan yayi imani Janan bazata saka ya aikata wa 'yan uwansa da sukayi wahala tare haka ba.

Kewar Janan yaji sosai tare da alk'awarin neman gafararta,sannan yayi alk'awarin zai faranta mata yadda bazata sake yin b'acin rai ko kad'an ba.

'Kudirin da yake ransa shine ana Shafa makoki zai fara neman matarsa da tilon d'ansa

Shi har yanzu ya kasa samo amsar abubuwan daya rik'a yiwa su Umma a wannan gidan.

Su Ja'afar sun zo sun k'ara tattambayar ta abubuwa game da mutanen da suka musu wannan abin ta kuma bada amsar iya abinda ta sani,sun masu ta'aziyyar Ummi sannan sun k'ara da cewa zasu rik'a zuwa akai-akai saboda bincike.


***********

Wayar hannunta ta zame ta fad'i k'asa "lafiya?"

"Ya Fahad ne ya kira ni" ta fad'a muryarta a raunane.

"Meya faru ne?ko mutumin ne yace ba zai zo ba?"

Girgiza kai tayi alamar a'a.

Fauziyya tayi saurin cewa "To mene?kin d'aga mana hankali fa"

"Wai Ummi ce ta rasu yau uku yanzu yake jin labarin a radio anyi magana da Aliyu ma yace in yazo zai mana bayani"

"Wace Ummi?"

" 'kanwar Aliyu mana"

"To mu ina ruwanmu abinda ya kaimu shi zamuyi yau hatta azzulumin alk'alin daya yanke hukunci sai yaji kunya"

Kallonta Janan tayi tace "haba Yaya Fauzah mutuwa fa"

Cikin fad'a Fauziyya ta sake fad'in "mu da Abba ya rasu a cikinsu waya tausaya mana"

Kallon Mameey Janan tayi tace "Mameey ki saka baki a d'aga tafiyar nan zuwa wani satin"

"Shikenan Janan a barshi hakan"

"Mameey ki rabu da Janan wallahi na lura tausayinsu take kuma wannan tausayin yana nuna cewa har yanzu kina son wannan makirin Aliyun"

Kallonta kawai Janan tayi rai a b'ace dan batayi tunanin maganar zata fito daga bakin Fauzah ba.

Tashi tayi da sauri ta shige cikin d'akin ta fashe da kuka.

Mameey ta kalli Fauziyya tace "Janan ta fiki gaskiya,mu ai bai kamata mu nuna halin k'aranta ba,mutuwa da ban ce dan haka dole mu d'aga musu k'afa,ki kirawo Fahad ki ce ya sanar musu sai wani satin"

Wayarta ta d'aga ta kirashi ta fad'a masa sak'on Mameey yace dama tun d'azu ya sanar dashi cewar a d'aga saboda rasuwar.


Katse wayar tayi tace "Mameey kinji Janan can na kuka sai kace na zagi Abba ko ke"

"Ah to sai kije can ki rarrasheta tunda dama ke kika tab'ota"

Tashi tayi da sauri ta shiga d'akin ta tarar da Janan d'in kwance tana kuka da haki.

"Sis kiyi hak'uri ni ban fad'a dan na b'ata miki ba"

"Amma meyasa kika fad'a?"

"Naga alamun haka ne"

Murmushi tayi mai had'e da hawaye sannan tace "kin san kukan me nake?"

Da mamaki Fauziyya tace "a'a sai kin fad'a"

Tashi tayi zaune tare da tank'washe k'afarta ta sake yin murmushi ta cije leb'e tace "ina kukan rashin Jalal da Adnan"

"Kamarya"

"Maganar da kikayi d'azu ita ta canza wa zuciyata shawara"

Shiru kawai Fauziyya tayi tana kallonta ita kuma ta cigaba da fad'in.

"Zan koma gidan Aliyu"

'Dan zabura Fauziyya tayi ta matsa gefe.

"Kina da hankali kuwa Janan?"

"Ai banyi kama da tab'ab'b'u ba ras nake"

"Ban yarda ba akwai matsala a k'wak'walwarki"

"Babu komai Yaya Fauzah ina son yin amfani da dama ta ne kafin in mutu,na yanke shawarar komawa gidan Aliyu in goga masa cutar dake jikina ba tare daya fargaba har sai lokaci ya k'ure ma'ana lokacin da cutar zata bayyana a jikinsa babu zancen shan magani,a lokacin zan sanarwa da d'ansa irin illar da yayiwa rayuwa ta daga nan zan daina shan maganin nima in mutu saboda na san lokacin na rasa Adnan"

'Daga hannu tayi ta wanke ta da mari a daidai lokacin Mameey ta shigo.

"Me nake gani Fauziyya?"

Tashi tayi da sauri ta rungume Mameey ta rusa kuka.

Janan ma sauke kanta tayi k'asa tana mamaki karo na farko Fauzah ta mareta.

"Meyasa Janan bata mutu ba ta dawo garemu?muna zaman lafiya Mameey Janan na neman tarwatsa d'an farin cikin da muka samu"

"Ki daina fad'ar haka Fauziyya"

"Mameey kinji mugayen kalaman da take fad'a kuwa?"

"Banji ba amma kema bai kamata kice haka"

"Zan tafi zanyi nisa daku bazan kuma dawowa ba tunda ba k'aunata kuke ba har fatan mutuwa kuke min"

Kuka sosai take.

Mameey ta rungumota tana kuka,fauziyya kuwa duk jikinta yayi sanyi ta rasa dalilin daya sa tayi furucin nan.

Alk'awari tayi zata bawa Janan d'in hak'uri idan ta huce dan ta san yanzu bazata saurareta ba.












_Sadeey S Adam_โœ
๐Ÿ๐Ÿ๐Ÿ
*DIREBAN GIDANMU*
๐Ÿ๐Ÿ๐Ÿ



_*by SaNaz deeyah*_๐Ÿ‘„



```Dedicated 2 Miss Xerks & Safnah luv```



_~kowa ma ya san ke tawa ce,wollah ko bakiyi na ni ina yinki sosai my Aunty๐Ÿ˜˜~_




*_Zuwa ga makaranta wannan littafin,naji k'orafe k'orafenku amma ina mai tabbatar muku cewa har na gama novel d'in nan bazanyi abinda bazai gamsar daku ba,karku duba dad'in novel d'in nan sosai kawai ku duba fad'akarwarsa,na tabbatar abubuwan da suke faruwa a yanzu akwaisu a littafin nan kuma in har akwai abinda ya zama akasin haka ko kuma kuna ganin babu fad'akarwa dan Allah ina son comments ya isa gareni kai tsaye babu wani b'oye-b'oye._*



48

Kanta na cikin gwiwarta har lokacin da Fahad ya gama basu labarin rasuwar Ummi abinda ya faru, amma Janan bata d'ago kai ba.

"Wannan fa meya sameta?"

"Ita da Fauziyya ne"

Kallon Fauziyya yayi yace "me kika ma autarmu mun samota da k'yar kina neman b'ata mata rai"

"Yaya nifa wasa nake mata,amma wallahi ka jawa autar nan kunne bata jin magana taurin kai ne da ita har yanzu"

"Ai a gurinki ta koya"

Ya dafa kan Janan yace "kiyi hak'uri Janan ki rabu da ita kinji"

Kai kawai ta gyad'a daidai lokacin wayarta ta fara ringing.

'Dan juyar da kai tayi sannan ta goge hawayen idonta ta d'aga wayar.

"Salamu alaikum"

Daga d'ayan b'angaren Momma ta amsa da "wa alaiki salam Janan ya kike ya gida?"

"Lafiya k'alau Momma ya su Zainab da Humaira"

"Zainab k'alau suke suna gaidaki,wato kinga mama shine kika guji Momma ko?"

Murmushi tayi tamkar Momma na gabanta tace "a'a ai zan koma insha Allahu"

"Ai tace da kanta zata zo ta d'auke ki jibi"

"To Momma"

"Kina wace unguwa a kano?"

"Kuntau ne daidai layin makaranta"

"Okay muna nan tafe yau d'in nan"

"Yau Momma, eh mana ai tun jiya muna Abuja yanzu mun taho kano ni da Muhasin"

"To Allah ya kawo ku lafiya"

"Ameen Janan ki gaida mamanki kafin mu k'araso"

"To"

Katse wayar tai batayi niyyar fad'awa su Mameey ba saboda yadda ranta ke a b'ace.

Amma da Mameey ta tambayeta kawai sai ta fad'a.

Babu shiri suka d'aura girki,Fahad ne ya fita ya sayo k'ank'ara Fauziyya ta had'a zob'o mai dad'i.

Duk abinnan da ake har lokacin bata saki ranta ba.

Duk da suna cikin aikin Fauziyya ta bata hak'uri tare da cewa haushi taji shiyasa tayi furucin.

Ita kuwa ta kudurta a ranta babu wanda zai hanata komawa gidan Aliyu ko dan ta hukuntashi akan abinda ya masu.

Kusan k'arfe hud'u su Momma suka k'araso.

Hankalinta sosai ya tashi ganin Abba k'arami a hannun Muhasin tamkar gawa.

Da sauri ta kai hannu zata karb'eshi suka had'a ido da Mameey ta fasa.

Iso aka masu bayan sun gaisa Momma ta kalli Janan wadda damuwarta ta fito k'arara.

"Kinga Abba ko?"

"Meya sameshi?" Ta fad'a da sanyi murya.

"Figar ruwa da ciwon hak'ark'ari wallahi banyi niyyar dawo dashi ba amma shekaranjiya ya d'aga mana hankali sosai ya rik'a mimmik'ewa daya dawo hayyacinsa ya fara kuka yana kiran Ammi da daddy shiyasa nace bari kawai mu kawoshi saboda gudun tsautsayi,muna shiga cikin Abuja ya mimmik'e mana ba shiri mukayi asibiti ina kiran Mommy kuma tace kina kawo shiyasa ban d'aga musu hankalina na k'i fad'a musu muna Abuja a asibiti muka kwana nasa suka sallamemu dan kiga d'anki"

Mameey ce ta karb'eshi.

Janan tayi k'arfin hali sosai ta danne hawayen dake k'ok'arin zubo mata.

"Mameey ai bamuga ta zama ba mu tashi mu kaishi asibiti bari na kira Sagir na sanar masa"

Da k'yar su Momma suka ci abinci sannan suka tafi Asibitin AKTH a motar dasu Momma sukazo da ita.

Kusan awa guda sannan aka gama processing aka basu gado a emergency kafin suyi scanning aga abinda ke damun nasa.

Sai a lokacin su Momma sukayi musu sallama da alk'awarin insha Allahu zasu dawo.

Suna zaune duk sunyi jigum lokaci-lokaci Janan na goge hawaye.

Fauziyya ta shafo kansa tace "Gaskiya mai sunan Abba ya girma Allah ya baka lafiya"

"Ameen dai,aini jira nake ya warke in masu tsiya daga shi har uwar tasa da ta zauna tanawa d'an fari kuka"

Mameey ta kalli Fahad tace "sai tak'i kuka kai ka mata nak'udar ko kai ka haifa mata, kai dai da ka zauna kak'i Aure ai ka ta ganin 'ya'yan k'annenka"

"Mameey abin harda gori"

"Eh in kaji haushi ka kawo min matar da zaka aura"

"Aikuwa tana nan tafe"

"Nima ina nan ina jiranta"

Ita dai Janan idonta yana kan d'anta dake kwance da uban oxygen a hanci ga drip a hannu.

'K'arfe shidda security ya shiga yana cewa dan Allah a fita lokaci yayi.

Janan ta kalli Mameey tace "su fa nan basa d'agin k'afa da lokaci yayi suke cewa a fita,kuma mutum d'aya ne ke jinya"

Mameey tace "To yanzu abinda za'ai ku tafi gida inya so sai na zauna dashi"

"A'a ni meye amfani na Mameey kawai zan zauna,Sai na sanar da Sagir baya da matsala yanzun ma aikine ya rik'eshi an bashi wanki da yawa shiyasa bai zo ba"

"Haba Fauziyya sai kace na zama uwar banza,da 'ya da mijinki ki taho jinya"

"To Mameey ai komai kamawa take,inda little Janan ce ba lafiya ai dole ya barni na zauna"

Janan tayi narai-narai da ido tace "Mameey dan Allah ku barni nayi jinyarshi"

Yadda tayi maganar Mameey taji tausayinta sosai, aikuwa tace to shikenan ta zauna.

Sai da suka suyo mata duk abinda take buk'ata sannan suka tafi..

Wajen k'arfe 8 wani nurse yazo ya bata takarda ta kai lab da safe za'a karb'o jini.

Hankalinta ya tashi sosai yanzu har k'arin jini za'a masa.

Kasa jurewa tayi ta tambayi nurse d'in meke damunsa.

"Bazamu gane ba har sai likitoci sunzo sun gani anyi scanning bana son fad'a miki abinda ba shikenan ba"

"To jinin siya zanyi ne ko d'auka za'ayi?"

"Eh duk wanda kuke so ai sai gobe za'a saka masa da safe to wannan takardar ta group d'insa ce in kije lab zasu ce ki saya ko ki kawo wanda za'a d'auka a jikinsa"

Jinjina kai tayi tana fad'in "Allah ya bashi lafiya"

"Ameen, yanzu ki kira mamansa ta zauna sai kije ki karb'o ke"

Ta d'anyi murmushi duk da a cikin damuwa take tace "ni ce mamanshi ai,kuma 'yan gidanmu sun tafi tun d'azu ban san ya za'ayi ba"

Kallonta ya sake yi yace "dagaske kece mamanshi"

"Nayi k'ank'anta ko"

"Gaskiya kam koni ban yarda ba sai yanzu na d'an ga kamannin naku,nayi tunanin k'aninki ne"

Murmushi ta sake yi kawai.

"Amma ya akai suka tafi da wuri haka har babansa"

"Babansa baya k'asar so sai mamanmu su kuma da 6 tayi akace lokaci yayi kawai sai suka tafi"

"Ai dama d'an tsayawa zasuyi a waje in an gama fita sai su dawo saboda irin haka,da ace babansa na nan da da dad'i"

"To yanzu ya zanyi?ko goyashi zanyi naje"

"Da oxygen taya zaki goyashi?jininsa dai yanzu 19% dole kayi k'ok'arin zuwa lab a san abinyi,bara kawai naje na kai miki"

"To nagode sosai Allah ya saka da alkhairi"

"Ameen".

Bayan ya dawo ya sanar da ita za'a zo a saka masa jinin da safe.

" oh siya akai?"

"Eh saboda ai babu lokaci tunda da safe ake buk'ata"

"To nawa ne kud'in?"

"Ki barshi kawai k'anwata na biya ga takardar,ai mamakinki ya sani biyan kud'in nan"

"Mamakin me?"

"Da kika ce yaronki ne wannan"

"Ba abin mamaki bane"

Haka yayi ta janta da hira har ya cire drip d'in ya jona wani yace da taga ya k'are ta fad'awa duk wani nurse da ta gani.

A daren ta kira Mommy ta sanar da ita,aikuwa tace suna nan tafe gobe.

_Washe gari_

'Karfe takwas Sagir ya kawo Fauziyya a lifan suka kawo mata breakfast.

Sun d'an tab'a hira kad'an sannan suka tafi kasancewar ba lokacin visiting bane kuma nurses da doctors sun fara round.

Bath wash ta masa sannan ta d'akko kayan da aka kawo nasa ta saka masa riga mara nauyi da pampers.

Likitoci hud'u ne tsaye suna ta magana akan yanayin ciwon nasa suna kuma duddubashi tare da yi mata tambayoyi.

Bayan sun yi rubutu a file d'in sun fita d'ayar ta dawo.

"Kamar na sanki ko"

Janan ta d'ago kai ta kalleta tana tunanin inda ta santa.

"Yes na san ki mana Janan ko?"

Kai ta d'aga alamar eh.

"Kin manta ni hala?"

"Gaskiya na kasa tuna inda na sanki"

"Mun shiga mota d'aya nida ke daga yola zuwa nan kano,Hajar ce wadda ta baki compliment card d'in ta"

"Oh eh hakane na gane ki"

"Kinma manta ni shiyasa baki nemeni ba"

"Kiyi hak'uri ba haka bane"

"To yane! Ba dai cikin jikin ki bane wannan har d'anmu ya girma"

"Shine fa"

"Masha Allah karki damu insha Allahu zai samu sauk'i,naji dad'in k'ara had'uwa dake"

Murmushi kawai tayi,sai kuma hira ta b'arke tsakaninsu har Janan ta d'an fara manta damuwarta.

Mameey da Fahad duk sun kira sun duba shi sannan suka ce da yamma zasuzo lokacin visiting amma Fauziyya da wuri zata zo saboda lunch.

Hajar ita ta raka ta tayi har scanning kasancewar Hajar likita ce bata sha wahala ba,sai da sukayi scanning har kala uku.

Sai da ta tabbatar anyi scanning d'in sannan suka koma ta tafi sai bayan kwana uku result zai fito.

Da zata tafi gidama tazo ta mata sallama tace da yamma zata dawo dubiya ta musamman.

Godiya sosai Janan ta mata ta tafi.


*************

Suna zaune ita da Mommy da Adnan sai Fauziyya da bata dad'e da zuwa ba.

"Ni fa rashin lafiyar nan ta bani mamaki lokacin d'aya fa"

"To ya za'ayi haka Allah yake lamarinsa"

"Mommy kawai zan mana visa mu tafi ko India ne sai yafi"

"Ka bari dai muga abinda Allah zaiyi"

"Mommy ki duba kiga Abba fa kamar baya da rai,wannan jinin na biyu kenan ake k'ara masa ni gaskiya gwanda aje can India tunda suna da k'wararrun likitoci"

"Adnan ka kwantar da hankalin ka mana kabi ka rud'e"

"Ai dole ne dubi itama Janan yadda ta koma a rana d'aya dole in damu da damuwarsu Mommy"

Kallon shi kawai Fauzah take tana jindad'in yadda suka damu da Janan.

Wani b'angare na zuciyarta yace _gaskiya Janan bata da hankali da har ta kasa gane masoyinta har tana ik'rarin zata komawa Aliyu,ita kuwa duk ranar da Janan ta koma gidan Aliyu tabbas zasu raba jaha da ita._

Salamar Hajar ce ta katse mata tunanin suma ta katse musu maganar da suke.

Duka su biyun suka mik'e tsaye Mommy da Adnan.

Itama Janan cike da mamaki ta bisu da kallo yadda taga Hajar ta tsaya cak ta kasa k'arasowa ya tabbatar mata akwai abinda ke faruwa.

"Meya kawo ki nan?" Adnan ya fad'a cikin b'acin rai.

Yatsina fuska tayi tace "kai zan tambaya dalilin zuwanka nan"

"Karki raina min hankali mana"

Janan ce tayi saurin tashi tace "Adnan itace wadda ta taimakamin fa,ta taimakeni har sau biyu a ray............"

"Dalla rufamin bakinki,ki rasa wa zai taimaka miki sai wannan matsiyaciyar mara kunya da tarbiyya"

Daga Janan har Fauzah sun tsorata da yadda ya had'e rai yana fad'a.

"Kada ka sake jifana da magana,akwai wanda ya kaika rashin tarbiyya,Alhamdulillai gidanmu babu gadon HIV naga mun........" Bata k'arasa ba ya sakar mana wawan mari har

Please Login or Register in order to submit comment