You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Janan ya sakata washe baki tare da fad'in "wai kece kuwa a gidan nan ko mafarki nake"

"Ni ce mana" itama tayi murmushi

"Bismillah shigo"
Ta fad'a tare da d'akko tabarma ta shinfid'a tabarmar a inuwa.

Zama tayi tare da sauke ajiyar zuciya,kallon gidan take tana tuno yadda tayi rayuwa a cikinsa dan ko wancan zuwan bata tsaya tayiwa gidan kallon sosai ba.

Ruwa mai sanyi Zuhra ta kawo mata tare da fad'in "ga ruwa kisha dan na san kinsha rana"

"Wallahi kuwa ya kuke ya gida ya jikin Aliyu"

"Da sauk'i sosai d'azu ma ya fita yace zaije cikin garin kinsan ya fara neman Admission"

"Allah sarki Allah ya taimaka"

"Ameen"

"Amma Zuhra ina kud'in da aka bashi na fili naga gidan nan sai k'ara rub'ewa yake"

"Eh kin san da yake fili ya saya ya fara gini zamu koma cikin kaduna shiyasa koda wannan ginin ya zube ya saka kara idan mun tashi zai zuba 'yan haya a ciki"

"Maganar sana'a fa ya kamata ace ya fara business saboda kar ya fara tara 'ya'ya abin yayi masa yawa"

Ajiyar zuciya Zuhra tayi sannan tace "haihuwa dai gashinan shiru har yanzu munje har asibiti ance lafiya ta k'alau amma danginsa sun kasa yarda da hakan saboda shi ya tab'a haihuwa" ta rik'o hannun Janan tace "Janan dan Allah ki kawo masa yaronsa ya d'an kwana biyu a gurinmu wallahi ya damu akan rashinsa"

Murmushin k'arfin hali tayi sannan tace "karku damu ni yanzu na manta abinda suka min saboda na dad'e da yafe musu kuma insha Allahu zan kawo masa yaronsa ya gani kuma zan tallafa muku a duk inda kuka gaza,sannan zan taya ki da addu'a kema Allah ya kawo zuri'a d'ayyiba"

"Ameen mungode Janan in har kin tafi Aliyu bai zo ba lallai yau zai bani goro kafin in fad'a masa wannan babban albishir"

Murmushi Janan ta sake yi.

"Yawwa Janan ina neman wata alfarma kuma"

"Ina jinki"

"Dan Allah ku maida aurenki da Aliyu"

A d'an tsorace ta kalleta tace "ki rufan asiri Zuhra"

"Dan Allah Janan"

Idonta ta fara murjewa tana k'ok'arin maida hawayenta amma duk da haka sai daya zubo.

"Zuhra na riga na cuci rayuwata nayiwa rayuwata babbar illa ta yadda bani da damar zab'ar duk mijin da yayi min,Zuhra taya zan auri mijinki bayan inada wannan cuta kina so in goga muku ku mutu ta sanadina,ni kaina a yanzu naga illar abinda na aikata kuma Allah ya nuna min kuskurena wanda nayi haka domin shi ya rasu babu rayuwar da muka mora ni dashi a duniyarnan,na yarda cewar duk abinda kake so bashi kake samu ba da wuya ka samu abinda kake so duka sannan na yarda taurin kai,rashin jin maganar iyaye su suka kawo tangard'a a rayuwata ina hango future na ashe duk gaibu nake gani gashi zan k'arashe a haka ina ribar abubuwan dana aikata?wannan ba tausayi bane ganganci ne wanda nake fatan mutane da dama zasu d'au darasi a kaina hakan zai zamo izna ga sauran mata masu taurin kai"

Shiru Zuhra tayi na tsawon lokuta tana kallon Janan na zubda hawaye,har sai da tayi mai isarta sannan ta sake cewa "ina dana sanin kuskure na farko na rashin jin maganar mahaifina da nayi,duk a tunanina tsana ce ashe soyayya ce ashe ya hango min abinda ni ban hango ba gashi ya barni a duniyar ina ganin rayuwa iri-iri"

"Sai hak'uri Janan ki bar kukan nan Allah yajik'ansa da rahma ke kuma ya dafa miki"

"Amin Zuhra"

Ruwan ta d'iba a hannu ta matsa ta wanke fuskarta dashi sannan tace "ni zan tafi,amma banji muryar Asabe ba ko bata nan?"

"Taje can rugarsu jibi nake tunanin zata dawo"

"Ki mik'a gaisuwata idan tazo" ta fad'a tare da d'akko 10k ta ajje kan tabarmar "ga wannan ki k'ara ba yawa"

"Haba Janan harda hidima"

"Bakomai"

Har k'ofar gida ta rakata sukayi sallama tana ta godiya Janan ta tafi.

Napep d'in da ta samu shima drop ta d'auka tace ya kaita wani private hospital a cikin kaduna, A-Rashee Hospital.

Bata wani dad'e kasancewar private hospital ne,nan da nan ta yanki kati bata sha wuya ba wajen ganin likita.

Tayi masa bayani akan cewar tayi missing duka maganin nata,ya tambayeta sunayensu ta sanar masa.

"Dole sai an sake yi miki sabon test tunda ba wancan asibitin bane,zamu ga matakin da kike sannan mu d'ora ki kan magani"

"Amma doctor ai na fad'a maka sunan maganin duka bana son sayen magani a chemist shiyasa na zo nan d'in nayi tunanin kawai zaka rubuta inje pharmacy in saya"

"Ina kika tab'a ganin anyi haka?dole za'ayi test ba wani dad'ewa bane baifi 2hrs ba kije ki karb'o result ki kawo min,yanzu bari na had'a ku da wata nurse d'in kuje"

"To babu damuwa"

_3 hours later_

Da sallama ta tura k'ofar office d'in ta shiga.

"Har kin dawo"

"Eh ga result d'in" ta mik'a masa sannan ta zauna.

Ya karb'a ya fara karantawa,hannu yasa ya gyara glass d'in fuskarshi,yayinda ni kuma nasa ido na duba naga ya dace na tsaya a nan na d'an huta😁.





Sadeey✍🏻
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁


_*by SaNaz deeyahπŸ‘„*_



```Dedicated 2 Miss Xerks & Safnah luv```

_Fans kuyi hak'uri kwana biyu na zama lazy a typing, yanzu ma sis Xerks ce da sis Zahra suka sakoni gaba._



_wannan shafin sadaukarwa ce gareki sis Zahra Darma,nagode da kulawarki a gareni_


59

Ajjewa yayi ya kalleta yace "wane likita ne ya dubaki har ya sanar dake kina da cutar HIV?"

"Wani family doctor d'inmu ne"

"Ko zan iya sanin sunanshi da asibitin da yake?"

"Likita lafiya kuwa?"

Glass d'in idonsa ya cire ya sake kallonta yace "result d'in da ya fito ya tabbatar mana da cewar bakya d'auke da wannan cutar amma gashi har kina shan maganin masu ciwon"

Idonta gaba d'aya yayo waje ta kalleshi galala tace "dan Allah doctor kar kayi yawo da hankalina,ni da kaina na sawa kaina ciwon fa"

Kallonta yayi sosai sannan yace "kina da hankali kuwa?"

"Inda bani da hankali zanzo nan ne, taya ciwo na jikina kusan shekara sannan kazo ka k'aryata bayan da kaina na sawa kaina cutar nan"

"Ai ni ban san mahaukaciya bace ke da bazan yarda ki shigo nan ba,fitar min daga office ko kuma na saka a fitar da ke"

Ganin yadda ransa ya b'aci ne yasa ta figi jakarta ta fita tana fad'in har ma kace bani da ciwo bayan ina da tabbacinsa"

Ranta a b'ace ta tari Napep ya kaita hotel ta kama d'aki.

Kan gadon ta zauna ta dafe goshinta da hannu sai kuka,wai ace tana garin Kaduna amma zaman gidansu ya gagareta ga abinda ya faru a asibiti.

Kuka mai isarta tayi sannan ta tashi tayi sallahr la'asar da Magriba,bayan ta shafa addu'a ta janyo wayarta ta kunna aikuwa kira ya shigo wayar.

Tsaki tayi kamar bazata d'aga har ta katse wani ya sake shigowa sannan ta d'aga.

"Inajinka" shine abinda ta fad'a kawai.

Daga d'ayan b'angaren Jalal yace "inason ki dawo ki kashe wutar da kika hura a gidan nan,Mommy bata min magana babu abinda ke shiga tsakanina da ita sai hantara"

"Wannan kuma damuwarka ce,kuma kai kaso hakan"

"Janan kin san kuwa da wa kike magana,wallahi karki saka na huce a kanki"

"To sai me? Ka huce akan nawa mana,kawai ina ji da matsalolina kana janyo min naka ina dalili" da sauri ta katse wayar tayi wurgi da ita gefe.

_Washe gari_

Tun safe ta shirya zuwa wani asibitin Babban abinda ya bata mamaki shine abinda wancan result d'in ya bayar shi wannan ya bata ma'ana bata kamu da wannan cuta ta HIV ba,sai da taje asibiti na uku da taga result d'inta ya sake bada Negative sannan ta zauna tayiwa likitan bayani dalla-dalla.

Kallonta yayi sosai sannan yayi dariya yace "shekarata 1 a asibiti nan ban tab'a had'uwa da patient mai abin dariya kamarki ba"

Kallon shi tayi cike da mamaki dan ita kam ta san tun shigowarta batayi dariya ba,hasalima ranta a b'ace.

"Wannan shine asibiti na uku da nazo amma dukkanku kuna min kallon mahaukaciya bayan da hankali na"

Dariya ya sake yi sannan yace "taya ya zan tabbatar da hakan?"

Table d'insa ta buga da k'arfi ta mik'e tsaye tare da fad'in "kar ka yarda mana ina ruwan wani"

Cikin jin zafin dariyar da yake mata tace "kuma kamar yadda kasa na zubda hawaye na kirana mahaukaci da kayi kaima saika zubda da yarda Allah" Jakarta ta d'auka ta fita da sauri.

Wani tunani yazo masa dan haka yayi saurin fita yabi bayanta.

Shigarta napep yayi daidai da fitowarsa.

Hancin motarsa ya saita yabi napep d'in da ta shiga.

Harta sauka a bakin gate d'in hotel d'in amma bata san yana binta ba.

**********

Yana zama a kan kujera ya sake sakin wani murmushin.

Salima ta zaune gefensa tare da fad'in "Rabon da naga kayi dariya har na manta"

Wani murmushi ya sake saki sannan yace "kin ci abinci kuwa?"

Ganin yana cikin farin ciki bata son ta katse masa yasa tace "eh naci"

"Kin tabbatar?"

Kai ta d'aga lokacin da cikinta ya sake yin kukan yunwa.

"Yaya meya sakaka farin ciki yau?"

Labari ya bata sannan ya sake fashewa da dariya.

Kallonsa kawai take dan ita bata ga abin dariya ba a maganar.

Kanta a k'asa ta nisa a tunani,har yayi mata magana bata ma san yana yi ba.

Iska ya hura mata a kunne tayi saurin d'ago kai ta kalleshi idonta cike da hawaye.
"Lafiya?me kuma ya faru"

Kanta ta d'ora a kafad'arsa tace "Yaya Allah yasa dai baka kamu da sonta ba"

"Meyasa kika ce haka?"

"Saboda na san bazaka iya aurenta ba sai an rabaku kamar yadda aka rabaka da duk sauran 'yan matanka,ta hanyar yi maka sharri kala-kala,Yaya dan Allah ka daina yin abinda zaisa daddy yasa a kulleka a cell ni kuma ayi ta gana min azaba"

Ajiyar zuciya yayi yace "Salima na kusa shekara arba'in a duniya amma bani da mata,ban tab'a Aure ba,ke kanki shekarunki sun kai ace kina da 'ya koda d'aya ce amma abu yaci tura,na rasa wane irin laifi Umma tayiwa daddy wanda har ta mutu ya kasa yafe mata"

"Babu,ba wani laifi da tayi masa,Umma Jamila ce ta hanata sakat haka muma,babu damar ka kawo mata sai anyi abinda yasa ta tsaneka aka fasa auren,an rigada an asirce daddy"

"Kada ki sake saka wannan a ranki Salima,kawai ki cigaba da yiwa daddy Addu'a Allah yasa ya daina yi mana wannan tsangwamar"

"Ameen Yaya"

Key ya mik'a mata yace "kije bayan motana ki d'akko ledar da nayi mana takeaway na abincin da zamuci"

Cikin murna ta amsa ta fita dan dama yunwa take ji.

**
Kwana biyu yana tarar Janan a k'ofar wannan hotel d'in amma sam tak'i ta saurareshi,ya rok'e alfarmar ta bashi ko phone number ta ne idan bata son ta tsaya dashi a waje amma sam yak'i saima wulak'anci da yake sha.

Yau ma haka yasha rok'onta daga k'arshe ma had'ashi tayi da securities d'in gurin suka wulak'anta shi sukayi masa tas,dan duk kallon d'an bariki suke masa.

Gidan Abbas ya wuce ransa a b'ace.

Maigadi da gudu ya shiga kiran Abbas dan yadda yaga idon Hisham a juye yasan ba lafiya.

"Hisham" Abbas ya kira sunansa sannan ya ja hannunsa zuwa falon sa.

"Mimi ku tashi kuje gurin Amminku ta kunna maku game" Abbas ya yima yaranshi wayo dan su bar falon.

Cikin murna suka tashi sukayi bedroom d'in mamansu.

"Me kuma ya faru? Yanayinka ya sauya Hisham"

"Abbas aure nake son yi kuma a cikin sati biyu masu zuwa,zanje na auro karuwa dan na san itace kad'ai zata iya aurena ko wane irin hali akace ina dashi"

"Kasan me kake fad'a kuwa?"

"Abbas na gaji,aure nake son yi,idan banyi aure ba zan iya mutuwa,yanzu haka mara ta ji nake kamar zata b'alle azaba nake ji,kuma sanin kanka ne bazan iya zina ba,bazan iya sab'awa ubangijina"

Dafashi yayi yace "wacece ita? A ina take?su waye iyayenta?nayi maka alk'awarin zan yi iya bakin k'ok'arina wajen ganin ka aureta dan na san kaga watane shiyasa kayi wannan furucin"

"Bazaka iya ba,ka san halin mahaifina da kuma Umma Jamila"

"Babu abinda zasu iya kasa a ranka komai da yake faruwa da kai k'addara ce daga Allah bawai su ba"

"Abbas bani da wani farin ciki da kwanciyar hankali,na rasa gatana na rasa farin ciki na, matan dana kai gida da niyyar aure Umma Jamila da 'ya'yanta suka ruguza abin sun kai goma ko ince sunfi goma"

"Wannan ita tana k'in saurarena na san kuwa baza ta tab'a aurena ba na san ana fad'ar halina zata gujeni,ban san ya akai na kamu da sonta ba,ni dai kawai naji ina son ta "

"Ai ba halinka ake fad'a ba,da halinka ake fad'a babu matar da zata k'ika kawai ana kusheka ne dan a k'untata maka"

"Abbas ina gab da fara zina kamar yadda na kasa na daina shaye-shaye" ya mik'e tsaye idonsa ya cika da hawaye.

"Karka aikata zina,kuma karka auri karuwa,dan manzon Allah S.A.W yace β€œku nemawa 'ya'yanku mace tagari” ka fad'a min yarinyar da kake so zan yi iya bakin k'ok'arina"

"Ban san a ina take ba amma na san sunanta dan tazo asibiti akan wani case" zama yayi ya bashi labarin komai duk yadda sukayi da ita.

Gaban Abbas ya fad'i ya sake k'urawa Hisham ido.

_Janan d'in dana sani ce,kenan dama bata da cutar HIV,yarinyar da Jalal ya mato akanta,to ta wane hanya zan b'ullowa lamarin? Dan na tabbatar in Jalal ya san bata da cutar tabbas zai aureta dan yana matuk'ar k'aunarta,ga Najwa ta sakoni a gaba itama._

Hisham ne ya tab'o shi yayi saurin d'ago kai ya kalleshi fuskarsa d'auke da tashin hankali.

"Ko ka santa ne?"

"Eh to na tab'a jin sunan amma ban Sani ba ko ita d'in ce"

Ajiyar zuciya Hisham yayi sannan yace "Abbas ka taimakeni dan Allah"

"Karka damu zan yi iya bakin k'ok'arina"

Sallama sukayi ya rakashi har mota.

Sai daya sha maganin da yake sha sannan yaja motar ya tafi.

A buge ya shiga falon,Umma Jamila da 'ya'yanta suna zaune suna kallo,ta d'ago kai a razane tace "me zan gani?giya ka sake sha Hisham"

Yana tangad'i ya ke takowa zuwa falon,Salima da ta fito daga kitchen ta saki plate d'in hannunta ya fashe a k'asa,jikinta na rawa take kallonsa dan ta san dalilin shan giyar.
🍁🍁🍁
*DIREBAN GIDANMU*
🍁🍁🍁


*_by SaNaz deeyahπŸ‘„_*



```Dedicated 2 Miss Xerks & Safnah luv```



60

"Yaya" ta fad'a da k'arfi tare da k'arasawa gabansa.

"Meyasa kayi haka bayan kayi min alk'awarin ka daina,meyasa zaka je kasha"

Yana sunkuye a gurin yayi goho baya ma kallon inda take.

"Wallahi ba a gidan nan ba,bazai yuwu ba ana kwatance damu" Umma Jamila ta fad'a tare da fita da sauri.

Khalila dake tsaye zura masa ido tayi ita da Khairat dan sun kasa cewa komai ma.

Tare da Daddy Umma Jamila ta fito,lokacin ya sunkuya tamkar wanda yayi sujjada.

"Me zan gani Hisham,me na fad'a maka game da wannan shaye-shayen naka?"

'Dago juyayyun idanunsa yayi ya kalli daddy yayi magana cikin maye "daddy ka barni nayi Aure,Aure nake so"

Duk kansu kallon mamaki suka bishi dashi.

Ruma da ta turo k'ofa ta shigo,anan ta tsaya tana salati.

Kallon daddy tayi tace "wa ma zai aauri wannan mashayin?ai duk mace ta gari bazata aureshi ba"

Wata damk'a zai kai mata tayi saurin gocewa ta ruga kusa da Umma Jamila..

Daddy juyawa yayi zuwa d'akinsa yayinda duk kowa ya tarwatse ya barshi shida Salima.

Kuka ta durk'ushe tana yi tare da fad'in "ka karya alk'awari baka min adalci ba"

Da k'yar ta samu ta kaishi d'akinsa tasa ya kwanta kan gado sannan ta fito da sauri ta shiga d'akin ta ta d'auki mayafi tana kuka ta fita.

Har k'ofar gidan Abbas Napep ya direta,ta shiga da kukanta,maigadi ma kallon ta ya tsaya yi dan ya san ba lafiya ba.

A falo ta tarar da Fatima yaranta,tana ganin yanayin ta aikuwa da sauri ta tashi ta tura su Mimi d'akin su tace suyi wasa.

Fitowa tayi ta kama hannun Salima ta zaunar da ita kan kujera.
"Lafiya Salima?meya faru?me akayi miki?"

Cikin kuka tace "ina Yaya Abbas?"

"Abbas ya fita"

"To bara na tafi kawai"

"A'a Salima wannan yanayin naki bazan barki ki tafi ke d'aya ba,me ya had'oki da Hisham ya b'ata miki rai ko?"

"Aunty Fatima dan Allah wacece ita?wacece yarinyar da Yaya yake so ki fad'a min inda take dan Allah"

Ganin yadda ta rud'e yasa Fatima tace "Wai mene?kin rud'a ni Salima ki fad'a min abinda ke faruwa ina Hisham d'in?"

Ganin tana kuka sosai tak'i nemo nutsuwarta yasa ta kira number Abbas tace yazo ga Salima tazo tana kuka.

A nashi b'angaren yana wani park ya zauna yana ta nazari akan yadda zai samu Janan ya sanar mata cewar abokinsa na sonta,ya riga ya d'aukawa Hisham alk'awari amma shi sam Janan bata masa ba.

Jin wayar Fatima ne ya sashi saurin tashi ya nufi motarsa.
Yana shiga kiran Jalal ya shigo wayar tashi,gabansa ya fad'i sosai amma ya daure ya d'aga.

"Kayi wuyar gani kamar kud'i" daga can b'angaren Jalal yayi maganar.

"Ba haka bane abokina ka san yanayin aikin nawa"

"Da anyi magana sai kace yanayin aiki kamar a kanka aka fara aikin bank,kana Kaduna amma bazaka iya fidda rana d'aya kazo mu gaisa ba,so kake nima sai kaji matata ta haihu sannan ka d'ebo su Fatima ku taho"

"A'a Jalal ba haka bane amma zan zo karka damu"

"Babu wata damuwa nima gobe ina nan tafe zuwa Kaduna"

"Me zakayi ne?"

"Zanzo gidansu Janan,saboda ta kunna min wuta tak'i dawowa"

"Kamarya kenan?ban gane abinda kake nufi ba"

Labarin komai ya bashi,yayi dariya yace "Janan tana garinnan yau ma na ganta a hotel"

"Hotel kuma?"

"Eh mana ai yanzu a wani hotel take zama dan bata gidansu gaskiya,gaskiya kayi sa'a abokina da Allah yasa baka auri yarinyar nan ba dan ba k'aramar tantiriya bace shiyasa sam bana son tarayyarka da ita"
'Dif Jalal ya katse wayar.
Dariya Abbas yayi sannan yaja motarsa zuwa gida.

Ganin Salima a zauna ta zuba uban tagumi ya sa jikinsa yin sanyi

"Lafiya?Fatima me ya sameta na ga idon nata jajir alamun taci kuka"

Ajiyar zuciya tayi sannan tace "wacece yarinyar da Hisham yake so?ina ne gidansu"

"Oh wai Janan?a Green Palace take zaune fa bama musan iyayenta ba"

Zama yayi kan kujera tare da fad'in "ina ganin kamar Hisham ya hak'ura mu fara neman maganin da zai karya sihirin da aka yiwa Daddy sannan yayi aure itama Salima tayi amma na tabbatar babu yadda za'ayi a gidansu a yarda ni kaina bazanso ya auri karuwa ba"

Salima ta d'ago jajayen idonta tace "kana nufin yarinyar da Yaya yake so karuwa ce?"

"Zaman kanta take yi a hotel,mecece idan ba karuwa ba"

Kuka ta fashe dashi tace "Yaya Abbas koda karuwa ce yayi jahadi idan ya aureta ai ni dai inaso in ganta in rok'eta ta auri Yayana"

"Salima ki kwantar da hankalinki komai zai daidaita"

"A'a ni kam dan darajar annabi Muhammad (S.A.W) ka kaini in ganta"

"Kin shirya karb'ar ko wane irin wulak'anci?"

"Akan Yayana zan iya komai,na san yanzu idan na koma gida sai naci duka shi kam ina tsammanin tuni Daddy yasa a jefashi cell"

"Ya sha giya kenan"

"Eh a buge ya shigo gida"

"Lallai kam dole kiso ganin Janan,zan kaiki amma ban san d'akin da ta kama ba,za dai mu tambaya amma ni bazan shiga ba gaskiya zan juya in tafi idan kun gama sasantawa sai ki hau Napep ki koma gida"

"Na yarda Yaya Abbas nagode"

Da sauri ta tashi ta fita tun kafin ma ya tashi.

"Fatima ya kalla yace " sai mun dawo"

"Allah ya bada sa'a"
Ta fad'a a sanyaye.

***********

Ta dad'e sosai a reception kafin ta samo number d'akin Janan,dan sai da ta basu kud'i sannan suka bincika mata.

Kai tsaye ta nufi d'akin,a bakin k'ofar ta tsaya tana knocking, jin ance "waye"yasa gabanta ya fad'i.
Wani tunanin ne ya fad'o mata tayi saurin cewa " room service "

A hankali Janan ta sakko daga kan gado taje ta bud'e.

"Lafiya?" Ta fad'a

'Dago kai Salima tayi ta kalleta sannan ta sauke ajiyar zuciya.
"Kece Janan?"

"Eh nice menene?" Tayi maganar a d'an rud'e.

"Idan babu damuwa mu shiga ciki zan miki wata muhimmiyar magana"

"Bismillah" ta fad'a tare da nuna mata ciki ba tare da ta san ko wace ba.

Shiga tayi sannan Janan ta shiga ta rufe da key.

Zama tayi gefen gadon,Janan kuwa ta tsaya jikin wardrobe.

"Sunana Salima Isyaku ina zama anan bayan government House layin dake jikin AP"

"Allah sarki"

Shiru ya d'an biyu baya,Salima ta rasa ta ina zata fara fad'a mata maganar .

"Amm...idan ba damuwa ki zauna pls maganar ba ta tsaya bace"

"Okay" Janan ta fad'a lokacin da taja kujera ta zauna.

Ajiyar zuciya Salima ta sauke sannan ta fara bata labarinsu.

*LABARINSU*

Sunan mahaifinmu Alh Isyaku Abubakar shi cikakken makiyayine a wani k'auye anan k'ark'ashin jahar Kaduna.

Mahaifinmu ya gado kiwo ne tun iyaye da kakanninsa,amma sai dai har a lokacin bai ajje komai ba,dan haka yakan amshi shanuwai na mutane kullum ya tafi kiwo dasu anan yake samun abincin da zaici.

A k'auyensu babanmu anyi ittifak'in cewa babu wanda ya kai mahaifinsa talauci dan koda ya mutu bai ajje musu komai ba.

Hakane yasa duk inda yaje neman aure ba'a bashi saboda ana ganin shi kanshi dak'yar yake samun abinci bare ace yana da iyali,hakane tasa mahaifinmu ya dad'e baiyi Aure ba,dan har abokansa wasu ma suna da 'ya'ya.

Akwai lokacin daya tab'a soyayya da wata,dan ita tace duk halin da yake ciki zata aureshi saboda shi d'in take so ba kud'i ba,amma fur iyayenta suka k'i yarda,abokansa sunyi iya yinsu ganin ya samu shima yayi aure amma abin yaci tura,a haka har ya daina batun Aure ya mayar da hankalinsa ga kiwonsa,duk abinda ya samu nashi ne shi da mamansa dan yanzu ita kad'ai ta rage masa a duniya,kullum cikin kuka take da addu'a Allah yasa d'anta ya samu nashi rabon,shi kad'ai ne d'a d'aya tilo a gurinta dan bayan ta haifeshi bata sake haihuwa ba,kishiyarta kuwa tun bayan rasuwar mijin nasu ta tattara ta koma rugarsu dan dama ba anan take ba aurene ya kawota.

Kwasam wata rana mahaifina yaje kiwo yaci karo da wasu takardu an yarda anyi kamar watsi dasu,sai kuma wata 'yar k'aramar wallet,ganin sahun tayar mota ne ya saka shi tunanin ko mai motar ne ya watsar dasu.

Kasancewar mahaifinmu baiyi karatun boko ba yasa ya tattaro komai ya dawo cikin gari.

Gurin abokinsa Datti yaje shi da yake yayi karatu har matakin secondary ya bashi takardun ya duba.

Kinsan dai karatu na k'auye ba wani ilmi bane ingantacce to sai ya kasa fahimtar komai baya ga suna sai kuma cikin wallet d'in akwai suna da address d'in mamallakinta to iya abinda ya gane kenan.

Ya sanarwa da mahaifina wannan takardun makaranta ne da kuma I.D card watak'ila mai su ya yarda ne kuma idan babu su bazaka karb'i certificate d'insa ba.

Ganin address d'in na Kaduna ne yasa yace dashi ko zai rakashi suje su tamk'awa maishi tunda a jikin I.D d'in akwai photo da kuma Address.

A haka suka saka ranar tafiya nan da kwana hudu dan sai sati-sati garin ake samun motar da zata kaika direct cikin birnin Kaduna, in ba ranar ba sai dai ka hau Babur ya kaika wani k'auyen kahau mota ko kahau keke in kana dashi dan Babur ma yana wahalar samu.

Daya koma gidan ya sanar wa mahaifiyasa sannan ya mik'a mata takardun ta ajje masa in zasu tafi zai karb'a.

Ranar da zasu tafi kuwa ya tattaro kud'in daya tara yace mata zai tafi dasu idan ya samu wani abu ya sayo ya fara saidawa saboda sana'ar kiwo tayi masa kad'an da zai tara kud'in aure da ita.

Goggonsa(mamansa) har da 'yar k'wallarta ta tausayin yaronta.

Haka suka kama hanya shi da Datti suka nufo garinnan,da kud'in yayi kud'in mota dan daga k'auyen zuwa Kaduna akwai 'yar tazara bare shi k'auyen da ba a bakin titi bane.

Wata shawara ce ta fad'owa babanmu ya kalli Datti yace,kawai mu tambaya sunan mutumin da kuma sunan unguwar saboda kasan wani zai iya cewa ya sanshi ya karb'e takardun saboda son zuciya.

Kayi dubara Isyaku abinda za'ai kawai mu samu abin hawa ya kaimu unguwar sannan daga nan mu tambaya sunan mutumin ko.

Hakan sukayi bayan sun tambayi sunan mutumin sai ya nuna musu gidan.

Sunsha bak'ar wahala kafin su samu su shiga,dan masu gadi sam hanasu sukayi.

Suna nan tsaye suna tayi sai ga wani saurayi ya fito daga cikin gidan,gaidashi sukayi sannan suka masa bayani suka masa tare da nuna masa takardun aikuwa cikin murna ya jasu har falon gidan.

Aunty warakar Kawu tazo kinga wasu ne suka zo gidan tare da takardun.

Su duka dake zaune a falon duk suka mik'e cike da al'ajabi.

An karramasu sunci sunsha sannan aka musu iso zuwa falonshi.

Bayan sun gaisa suka mik'a masa takardu,yayi godiya sosai har ya sanar musu cewa darajar takardun nan itace gatan duk iyalan nasa,bai fad'a masu na mene ba amma sun tabbatar ba na makaranta bane.

Maihaifinmu ya bashi labarin yadda ya samu takardun da yaje kiwo.

Ya fad'a musu cewar yaje super market kafin ya fito ya

Please Login or Register in order to submit comment