You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Downloaded From https://tknovels.com.ng ÿþIDAN KAYA YA GAJI....

GAMMO MA YA GAJI

LITTAFI NA BIYU

BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ˜AMSHI

LABARI MAI DAŠIN SAURARE

*Abinda ya faru shine*

*Jiya da daddare da misalin ™arfe bakwai na dare wata lamba ta kirani cikin ikon Allah na Wauka sabida

ban fiye Waga waya ba nafi gane a turo mun sa™on karta* *kwana.*

*Sai tace dani*

"*""³ata dan ALLAH hutun da kika ce zaki yi na* *tsawon kwana goma yayi yawa ki daure zuwa monday in"

"dai da hali kici gaba da rubutun dan* *ALLAH. In ina karanta littafinki ina samun nishaWi sosai. ³ata Ubangiji Allah ya huwace miki baiwar tsara rubutu da fikrar hausa sosai. Ni tsohuwar ma'aikaciyar jarida ce, nafi shekara talatin ina karance karancen littattafan hausa irin nasu Ado gidan dabino, Balaraba Ramat, Anty Bilki funtua* *Amman ³ata salon rubutunki ya bambamta da na ragowar marubuta."

"Hausarki, sunayen jarumai, da* *yadda kike amfani da daWaWWun kalaman hausa, bugu da ™ari sunayen"

"littattafanki sunfi komai burgewa.""*"

*Mun yi maganganu da'ita sosai na yaba na kuma yi mata godiya dattijuwace sosai.*

*Na yi mata al™awarin monday zanci gaba da posting da izinin Allah.*

*Maigidana daya dawo* *masallaci na bashi labari sai ya umarceni da yau lahadi in soma posting Win

kawai.*

*Mamana gashi na* *soma posting sabida girman soyayyar da kika nuna mun*

*Masoyana a duk inda suke da bazarsu nake taka rawa. In babu ku babu BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI

B4B GIDAN ˜AMSHI.*

001

SABUWA:.

Hannu na saka zan amshi ledar da Khalid yake mi™o mun ina murmushin cusa haushi. Ban aune ba naji

an warce ledar tare da tunkuWeni gefe naje na faWi na dauje hannuna.

Babangida ashe ya fito a mota da gudu kamar mayunwacin zaki.

"""Dan ubanki waye wannan, wanne kwarto fasi™in ma™iyin Allah da manzonsa ne wannan. Au ashe"

"Sabuwa har yanzu baki dena bin maza ba da gasken dai duk fitar da kike yi maza kike bi?"""

"Da sauri na mi™e ga mutane har sun soma taruwa"""

"""Malam koma me kake tunani bai kamata ka shiga Waga murya a hanya haka ba. Matarka ce fa, ya zaka"

"tunkudeta haka"""

Karku daWa kar ku raga iyakar abinda Khalid ya faWa kenan Babangida ya kucuneshi ya soma cunkusa

mishi manyan ashariyar da kamar a bakin tasha aka haifeshi yana yi yana jijjiga Khalid idanunshi kamar gauta.

"Ka sake shi Babangida, zanma baya"""""""

"Hannu yasa ya zabga mun mari, ya sake marina bakina ya fashe."

Ya sake Waga hannu kenan Khalid ya ri™e hannun gam jikinshi na rawa yace.

"""Kar ka sake dukanta in kai baka san darajarta ba ni nan nasan darajarta. Baby ashe Wan balaja'u kike"

"aure ban sani ba, madoki wanda baisan darajarki ba?"""

"Habawa Khalid bai rufe baki ba Babangida ya runtumashi da ™asa, dambe ya kaure kica_kica jama'a suka"

haWu kamar ya™i mata sai tittiWowa suke yi sada gidajensu.

Da kyar aka raba faWannan Babangida ya shiga labartama jama'ar da suka taru.

"""Matatace fa kwarto ya kawota har gida, har yana mata siyayya fa, saina kasheki Sabuwa wallahi, shima"

sai ya mutu. Mutuwa nima zanyi uban kowa ya huta. Yana faWan haka ya cabke wuyana ina kakari yana

dukana. Da ™yar aka SanSare Babangida a jikina. Duk ya fasa mun wuyana.

"A guje na faWa motar Khalid, ana in fito naki fitowa Babangida kamar zai haukace haka yake ji. A guje ya"

gangara.

"""Malam ja motarka ka bar wajennan dutse yaje Wakkowa zai ragargaje maka mota"""

"Da sauri Khalid ya buWe motar ya shigo, yana ma motar key muka hango Babangida da ™aton dutse a"

"hannunshi, habawa a guje muka hau titi har muka kusan kaWe wata baiwar Allah mai ciki, dutsen da Babangida ya harbo ya fashe ma Khalid gilashin bayan motarshi.taratsatsatsa"

Gudu muke yi Babangida na binmu a mota.

"Ka kaini gida Khalid, na gama auren Babangida na gama zama dashi kenan har abada."""

"""Amman babu matsala Baby jini ne yake zuba a bakin ki da hannunki fa muje asibiti"""

Idanu na lumshe na waiga Babangida na biye damu a mota.

"A_a ka kaini gida kaga biyo mu yake yi, in kuka kuma haWuwa zai iya maka komai"""

˜wafa yayi yace

"""Rabu dashi bai isa yayi miki komai ba, ni kuma daidai nake dashi. In yana jin shi tataccen Wan iskane ni"

"ubanshi ne a iskanci"""

Idanuna na runtse ina kuka mai ciwo yarana kawai nake tunowa kada wannan labarin tozarcin ya iskesu

shin Yaya zasu ji musamman Mardiyya da Aminu?

"Ajjiyar zuchiya nayi dana tuna ™arshen zamana da Babangida ne wa'adin ya cika, wannan abinda ya faru"

"kaWai na cancanci ya sakeni, dama banje inda naje domin a kwato mun hakkina ba."

"Ban buWe idanuna ba sai a ™ofar gidanmu, Khalid na tsayawa Babangida ya fito a mota da kanshi ya buWe"

motar ya fincikoni yana neman dukana. Jikinshi yana rawa.

"Dira nayi a wuyanshi na shiga dukanshi tako ta ina, haukacewa nayi duk inda na samu naushi nake yi,"

idona ma a rufe yake.

"Ashe an cika a layi anata tsogumi, Rakiya da Adama ne suka Sanbareni a jikin Babangida. Wanda a tsaye"

"kawai yake jikinshi na rawa, idanunshi na hawaye."

"""Kayi hakuri dan Allah Babangida. Rashin hankali ke damunta ne shi yasa"""

Murmushin takaici yayi kawai idanunshi sun ri™ide yace.

"""Kamata nayi da wani Wan iskanta fa ya kawota har gida. Dake baku bata tarbiyyar arziki ba shi ya"

kawota gida. Ni zata daka harta zubarma da jini? Kuma ku wani fito kuna bani ha™uri wallahi saina

kasheta.

Sabuwa amman wallahi sai kinyi Wan da kace ba'a haifeki ba. Komai yazo ™arshe kurun™us shi kanshi mai

"Waure miki bayan yau dai zai sallama zamana dake yazo ™arshe"""

To se me IDAN KAYA YA GAJI GAMMO MA YA GAJI.

Tuni nabi hanyar nemo ma kaina mafita.

"Me za'ayi da aurenka auren ™addara wawa jahili da™i™i kawai"""

Ina faWin haka na shige cikin gida ina kukan fitar rai. Duk wannan bidirin Hamida fa tana tsaye ake yinshi

abun yafi ™arfin tunaninta ne.

Rakiya da Adama ya suka ™are oho ga mata duk an fito kallo sai ri™e baki suke yi.

"""Ke Lolo wai dama dake akeyi ne, eh ya naga jini a jikinki yana gudana ne wanne Wan abu ta kazanne?"""

Cewar Gaza da bansan ya fito daga firzin ba.

Babangida ne ya dokeni ya tara mun mutane a unguwarmu da ™yar na iso gida Gaza kaje ka ramamun

"wallahi bazan Yadda ba"""

Mi™ewa yayi tare da neman hanyar waje tar da cewa.

"""Kutumar dumadu lahira ga ba™o"""

"Maigogul ne ya taso a guje ya bishi, ni kuma na zube a tabarma ina kuka kaina kamar zai fita."

"Ni dai ina jiyo ihu daga waje, Hauwa ma da gudu ta fita tana salati."

"Wani yanayi na shiga wanda nake shiga in ™unci yaimun yawa nafi awa uku bansan meke faruwa ba,"

"kaina sai jujjuyawa yake yi, ga maganganu a kaina ina ji can kuma saina dawo hayyacina."

"""Sabuwa sannu. Rakiya kinga ta samu kanta Alhamdulillah"""

Cewar Maigogul dake bakin gadon da nake kwance.

"""Sannu Lolo, daure ki tashi ki watsa ruwa Rakiya ko Adama su kaiki gidanki. Kinga uban mijinki ma yanzu"

"yabar gidanan"""

Da ™yar na buWe bakina nace.

"Narantse da Allah bazan koma gidan Babangida ba sai dai sama da ™asa ta haWe"""

"""Babu inda zata je. In akayi wasa fa sai in ™arashe Babangidan uban kowa ma ya huta. Ya sabida rashin"

"sanin darajar kai Dattijo kana ganin yadda ya cire imani yaima yarinya duka ace kuma ta wani koma. Babu inda zata je in dai ni Gaza ina numfashi. Uban mijinta ai bashi yake aurenta ba, bafa sonta yake yi ba. Wallahi domin rufin asirinsune kawai yake lallaSa Lolo nine ubanta daga yau"""

Maigogul yace.

"""To duka ai ka rama mata saranshi fa kayi Gaza. Kuma ai kana ji yace fa da wani namijin ya ganta."

"Tsinannen halinsu ashe bata dena ba. Dole ya doketa ai, kana gani uban mijin ya biyo bayanta yadda muka yi dashi data farka za'a mayar da'ita"""

"""A_a Maigogul ni ina ganin a dakata da batun komennan har komai ya lafa tukunna. Duba da irin saran"

"da Gaza yayi ma Babangida """

"Cewar Rakiya, ina dai jinsu da masu cewa in koma da masu cewa in bari ™ura ta lafa duk dai, basu san"

hukuncin dana Wauka bane amman in tayi wari zasu ji a lokacin nayi musu bayani.

Babangida:.

Yana tafe a mota jini na Wibanshi Hamida tana gefe tana salati.

"""Abban Usama kabi komai a hankali ka gode ma Allah daya tuna asirinta. Ohh ace mace da aurenta tana"

"bi kwararo kwararo bin maza, mu muna zaune zata kwaso mana cuta. Babu mamaki ma infection Win dake damun mu duka gidan ita taje ta Webo mana"""

Idanu ya lumshe ™wa™walwarshi na hasko mishi hoton Khalid da Sabuwa data shige motarshi.

Babu shiri ya tsaida motar a gefen titi yana haki.

Malama Babba sai kiran wayarshi take yi.

"""Kada ki Wauki wayar Wauko wayarki ki kira mun Mustapha ki bani shi"""

Ya ™arashe maganar tare da cije leSenshi na ™asa.

"KafaWarshi sai jini take yi, ga saran da Gaza yayi mishi ya shiga sosai har wajen ya soma kumbura."

Hamida ta mi™o mishi wayarta Mustapha nata

"""Hello Hello"""

"""Mustapha kazo ka kaini asibiti dan Allah"""

Nan yaima Mustapha kwatanceN inda suke ba'a jima ba sai gashi acaSa ya saukeshi. Ganin yadda jini ya

"Sata kayan Babangida da motar ma da yake ciki saiya tashi hankalinshi. Sai da Mustapha ya kira wani kofur abokinsu ne ya shige musu gaba a asibiti kafin aka karSi Babangida, a lokacin jini ya Webeshi ko"

gani bayayi ga zuchiyarshi kamar ana soyawa dan ™una a sume akayi cikin Waki dashi.

"""Wai meya faru hakane, rikici ne ya haWasu da wani kome?"""

Hamida ta kwashe labari tsab ta labartama Mustapha. Hankalinshi yaji ya tashi ainun yasan yadda

"Babangida yake da matu™ar kishi wannan dambarwa yanzu aka soma, shi kuma wannan farka ko a ina"

yake sai sun nemoshi.

"""Bani kiga wayoyin nashi in ri™e mishi. Su Baba Malam sun san me ake ciki kuwa?"""

Wayoyin ta mi™a mishi.

"""Wannan ba™ar wayar Maman Mardiyya ce lokacin da abin ya faru ta faWi shine na take ta."

Banyi tunanin su Malama Babba sun san halin da ake ciki ba yana da kyau a sanar musu. Yau munga

"tozarci da abun kunya. Babu kunya ta kule motarshi shi kuma yaja suna shirin guduwa"""

Kai kawai Mustapha yake ta jinjinawa. Kiran Malama Babba ne ya sake shigowa wayar a karo na barkatai.

Mustapha ya Wauka tare da karawa a kunne kana yayi sallama.

"""Muryar Mustapha kamar nake ji. An kashe mun Babangidan ko? Wallahi sun jawowa kansu bala'i dan"

"bazan yarda ba."""

"""A_a bai mutu ba Malama ki kwantar da hankalinki muna asibiti yanzu dai aka shiga dashi, saran dai ya"

shiga sosai.

"""Shikenan gamu nan zuwa asibitin hankalin kowa a tashe yake"""

GIDAN SU B HOUSE

Sauke wayar Malama Babba tayi a kunnenta.

"""Malam kaji wai suna asibiti da Mustapha abokinshi. Sai muje ko? Ka kira Wawo yazo ya kaimu"""

Jim Baba malam yayi tare da dena rubutun da yake yi a allo yace.

"""Ki je ki kira Ramadana yazo mu je, Wawo yana wajen aiki ai ba sai an rabo shi da wajen aikin ba. Allah"

"dai ya kyauta tsuntsun dai da yaja ruwa shi ruwa kan doka, kuma duk wanda yasai rariya yasan zata zub da ruwa"""

Kuka Malama Babba ta kuma fashewa dashi tace.

"""Anya malam kana ™aunar Babangida kuwa?"""

Girgiza kai yayi yace.

"""Ko kaWan. Da ana canja Wa da tuni na canja Babangida daga tsatsona. Kaf haulata babu mai muguwar"

"Wabi'ar Babangida."""

Shigewa ciki tayi tana kuka. Baba Malam kuma ya shiga tunano baya

Sallamar wani bawan Allah mai saye da surt ce ta katse tunanin Malam Baba.

"""Ameen wa'alaikas Salam. Bawan Allah daga ina?"""

"""Daga kotu al™ali Muhammad Muhammad ya rubuto sammaci yace in kawo gidannan. Surukarka"

Sabuwa ce ta shigar da ™aran Wanka Babangida kacigari. Wannan sammacinne ranar zaman kotun yana jiki Malam zaku gani.

"Sai a daure a halarci kotu kuma dan Allah a tabbatar takaddar taje hannunshi."""

Salati Malama Babba ta saki wacce fitowarta kenan Ramadan na ri™e da hannunta.

"""To Shikenan wannan takadda in sha Allah zata je hannunshi, kuma da zaran lokaci yayi zai zo, da kaina"

"zan kawo shi"""

Hannu Baba Malam ya saka ya karSi takaddar. Ya juyo ya zuba ma Malama Babba da Malama ™arama

"idanu, can ya dubi Ramadan yace."

"""Kayi musu jagora kuje asibiti. Akwai inda zani yanzu daga can zan biyo"""

Malama ™arama na son magana amman tana tsoro dan Malam kaifi Waya ne.

Dole haka suka wuce asibiti shi kuma ya nufi gidansu Sabuwa a karo na biyu.

"Sallama yayi a bakin ™ofar gidan dan ya rasa yaro Wan aike"""

SABUWA:.

"Fitowata daga wanka kenan, Rahama da su layuza duk sun zo, gasu Sadiya anata mayar da zance. Na jiyo"

sallama tabbas Muryar Baba malan ne. Maigogul ne ya fito daga Wakin Hauwa.

"""Yauwa Lolo ki daure ki shirya in mayar dake."

A cikin gidannan babu uwar abinda zaki tsinta. Zawarawan gidan ma neman makafa suke yi balle ke da

"mijinki yake da rufin asirinshi, mu kanmu dake fa muka dogara. Ni dai na faWa miki wallahi Allah sai kin koma"""

"Fu ya fice, nima na shiga Wakinmu a hankali, zancan ake dai ta tattaunawa, kowa yana da damar faWin"

albarkacin bakinshi da duk abinda yake so yace.

Mai Rakiya ta mi™o mun mai gurguwa babu ko murfi duk datti cikinshi.

"Kaya kawai na zura, goduwar rigar kanti da Sadiya ta ajjiye mun."

"""Rakiya ke da Lolo kuzo, ku zo da tabarma"""

"Gabana ya yanke ya faWi, Rakiya tayi saurin mi™ewa ta fice, Adama ta bi bayanta da tabarma, ni ko sai da"

Maigogul ya le™o yai mun dakuwa.

"""Ungo nan. Kaga ne mun ´ar nema zaki fito ne ko saina shigo nayi miki Sarin makauniya""?"

Bakina a ture na suri mayafin rigar jikina na fita. Dukkansu suna kan taburma ni suke jira. A hankali na isa

na nemi waje gefen Adama na zauna kaina a ™asa.

Gyaran murya Baba malam yayi yace.

"""A kwanakin baya Sabuwa tazo mini da batun in amince Babangida ya saketa, na rarrasheta na bata"

"ha™uri ta koma gida. To a wannan karon nasan tabbas rigima ce ta kaure a tsakaninsu, rigimar da ta lafa shekaru fin goma. Yanzu haka ga takadda daga kotu an turo mana Sabuwa ta maka Babangida a kotu, shine nazo inji ba'asin musabbabin abinda ya haWa rikicin, da dalilin yin ™arar"""

"Nan dukkansu suka shiga sallallami, Maigogul kuwa yin™urawa yayi ya kawo mun wani wawan dukan da"

zafinshi ya jima yana ratsa tsokokin jikina.

"""Zauna Maigogul abi komai a hankali Sabuwa fa tana da gaskiyarta."

"""Wacce gaskiya malam bata da hankaline da zata maka mijinta a kotu dan ubanta, dame ya rageta ba dai"

"hakuri akeyi ba. Da ba'a ha™urinnan ai da itama fa ba zata zo duniyar ba"""

Maiduguri ne yake magana duk a daburce da halama lamarin ya doke su sosai. Rakiya dai sai tafa

hannayenta take yi kaina na ™asa ina Wigar hawaye. Gaza daga can gefe yana ma Rahine wanka yace.

"""Kaga ³ar gari. Wallahi baki taSa burgeni irin yau ba"""

"""A_a ai mata uzuri shekaru goma sha ba kwana goma bane ba. Nasan abubbuwa da dama da ku baku"

sanshi ba dangane da tafiyar aurensu.

"Amman menene dalilin rikicin?"""

Maigogul ne ya zage ya labarta mishi yadda abun yake.

Idanu ya runtse ba tare da yaso jin gaskiyane ko ba gaskiya bane. Yace

"""Batun shigar da ™aran akan menene shi kuma Sabuwa?"""

A mugun sanyaye nace.

"Saki nake nema Malam Baba kayi ha™uri"""

"Da sauri ya Waga mun hannunshi akan in yi shiru, mu™ut na haWiye maganata."

"""Sabuwa zan miki tambayoyi ki amsa mun su ki daure ki kuma dena kuka."""

Ina shesshe™an kukan ba™in ciki da tsagwaron tantagaryar nadama na gyaWa mishi kaina.

"""Kin shirya rabuwa da Babangida kin tabbatar, sannan kin shirya zawarci da kaucema kuskure da kauce"

"hanyar da akabi a baya, sannan Sabuwa ki sani Shari'a zata iya baki ´a´anki, to in bata baki su ba kin shirya ha™uri, sannan zaki karSi duk halin tagaiyara ko tozarci da ™as™ancin da zaki gansu a ciki? Dan daga ranar da kika rabu da Babangida daga lokacin duk tallafin da nake yi zai ™are, hatta Islamiyya sai an"

"biya musu zasu je balle boko da ba tawa bace. Hatta ubansu yabar sake shigo mun gidana. Sabuwa!"""

Ya kirani da murya ta gaske.

Bakina na rawa na amsa.

"""Kin shirya ma duk waWannan lissafin da nayi miki, da waWanda tunanina bai kawo su ba?"""

Rakiya tace.

"""Babu ma Kotun da za'a shiga Malam dan Allah maganar nan a barta Sabuwa dai ba ita ta haifo kanta ba,"

ni da Adama da daddare zamu rakata gidanta. Sannan shima Babangida a bashi ha™uri da abinda ya

"shiga tsakaninsu da Gaza. Shaye_shayenshi yayi bata faWa mishi gaskiya ba ko maigogul?"""

Ta tambayi Maigogul dake hararata. Da sauri yace.

"""Sosai ma. Kaga muma fa in yayo shaye_shayenshi ya dibga sai yazo yace uwar tashi zai zane, ko kaji ma"

"ya kirata da matarshi. Ayi ha™uri """

Malam Baba yace.

"""Assha Allah ya kyauta. Ai Maigogul duk wannan fa ba damuwa bace, addinin Musulunci addinine mai"

"sau™i, nima da kaina ina sulhunta aure, wasu ma in abun ya™i sai in turasu kotu daga ™arshe kaga an rabu."

"Sabuwa ki amsa mun tambayoyina duk kin karSa?"""

"E Baba malam na karSa babu damuwa"""

Idanunshi ya runtse tare da ri™e kanshi yayi shiru kamar ruwa ya cinyeshi.

Sautin Wura ashar na Maigogul kawai kake ji a wajen sai zagina yake yi yana mangareni. Gaza kuma ya

taso shima ya tsaya akan Maigogul sunata faWi in faWa.

"""Maigogul dan Allah kabi komai a hankali duk wannan bashi bane. Ke Sabuwa da daddare ki shirya"

"Rakiya da Adama su mayar dake Wakin ki, kije ki zauna har aga menene sakamakon ™arshen shari'a. Ki"

"sani da aure a kanki shi wannan bawan Allah kar ki sake haWuwa dashi, aji tsoron Allah Sabuwa"""

"Da sauri na Wago jin ya ambaci in koma Wakina, magana nake son in yi amma nauyi da kwarjininshi yasa"

dole na sunne kaina ™asa ina hawaye.

"""Ji mana kai Dattijo bafa eh zata wani koma ba in faWa maka gaskiya"""

Baba Malam ya dubi Gaza yace.

"""Abi komai a hankali Sabuwa ta koma Wakinta har sai an gama Shari'a"""

Mi™ewa yayi yai mana sallama ya fita.

Dawa Allah ya haWa su Maigogul in bada ni ba.

"Nan wannan yace wannan, wannan yace wancan akaita zagina tare da aibantani. Har Sadiya tana duban"

tsabaragen idanuna tana cewa dama in Babangida ya sake ni ita ya aureta duk bala'i zata zauna. Gaza shima ya saka tijara shi yana bayana.

ASIBITI:.

Isowar su Malama Babba ke da wuya aka fito da Babangida daga Wakin ™aramar tiyatar da akayi mishi a

"hannunshi, a gadon marasa lafiya aka wuce dashi zuwa ward Win maza."

"Malama Babba sai sharce hawaye take yi, a kaf yaranta Babangida shine mafi soyuwa a gareta, inda zaSi"

"za'a bata na ta zaSa sauran yaranta duka, ko Babangida shi Waya tilo, to da shi zata Wauka."

"Ba wai dan ya fisu biyayya ba, sai dan irin yadda yake da shiga ran duk wanda yake tare dashi."

Baba Malam yana mutuwar son Babangida da yabon ™wazonshi a baya kafin Sabuwa ta shigo

rayuwarshi.

"""Ku daure mu jira daga waje yana bu™atar hutu, sannan kai inason ganinka a office Wina."""

Cewar Dr A_A NAFAŠA kenan tana kallon Mustapha dake waya da Wawo. Da sauri ya kashe wayar .

"""Malama kuje ku zauna a waje Ramadan ya zauna dashi zanje ganin Dr yanzu"""

"""A_a ni kam bazan iya fita daga Wakinnan ba ™arama kije ki zauna a waje Sa'a da su Kudidi suna hanyarsu"

"suma"""

"Da Malama ™arama da Mustapha da Dr tare suka fita, Malama ™arama ta nemi waje ta zauna Mustapha"

"yabi bayan Dr A_A NAFAŠA zuwa office Winta, a hanya suka hadu da Wawo dasu Sa'a. Wawo yabi bayan su Mustapha, su Sa'a kuma suka wuce zuwa wajen su Malama Babba."

"""To Alhamdulillah mun yi mishi tiyata a hannun nashi, anci sa'a karaya Waya aka samu a hannun, kuma"

anyi gaggawar kawo shi asibiti baku ce na hausa zaku yi ba. Jininshi yayi matu™ar hawa ainun yana cikin damuwa a zahirin gaskiya. Amman dangane da tiyatar mun yita cikin nasara. Amman ya kamata aWauki mataki akan duk wanda ke da sa hannu akan wannan saran. Gaskiya hannun yaso ya kutsure mishi tun

"daga tushe, kuma ™wararrene yayi saran da ™warewa a kan gaSa ya sareshi"""

Ajjiyar zuchiya Wawo ya jawo tare da saukewa a hankali kana yace.

"""Mungode sosai Dr. Wannan faWa kuma rikicin cikin gidane, amman za'ayi ma tubkar hanci in sha Allah."

"Yanzu dai babu wani abu ko Dr?"""

Bayan ta gama rubutu akan fail Win Babangida tace.

"""˜warai babu wani abu a yanzu, zamu rikeshi har zuwa hannun ya soma sau™i gudun famawa. Kuna iya"

"tafiya"""

Godiya suka yi mata suka fito. A hanya Wawo ya tsayar da Mustapha yace.

"""Mustapha kasan waye Alhaji Abubakar Baban Bola?"""

Kai Mustapha ya gyaWa yace.

"""Tabbas na san shi, suna harkar kasuwanci sosai da Babangida, kusan zan iya cewa oganshi ne. A lokacin"

da Babangida zai siyo injinan ni™a ™arafai ta hannunshi ya samu hanya ya haWashi da ´an Chinan da ya

"sai injin Win a hannunsu."""

Hannu Wawo ya zura a aljihu yace.

"""Biri yayi kama da mutum akwai danshin gaskiya a maganganun Alhaji Abubakar Baban Bola tabbas."

"Amman duk da dai maganganunshi akwai Waurewar kai a ciki, amman dai zamu bashi ha™uri ya bari har"

"Babangida ya farfaWo inji ta bakinshi"""

Mustapha yace.

"""Wani abunne ya faru a tsakaninsu?"""

"""O_o o_o yafi ™arfin a tsaya daga tsaye ana maganar amman akwai gagarumar matsala babba in dai"

abinda Alhaji Abubakar Baban Bola ya faWi ya zama gaskiya.

"Muje maza mu same su"""

Da sauri_sauri suke tafiya har suka iso ward Win. Wayar Babangida kuwa tunda ya kwanta Ramatu ke

"rangaWa mishi kira bata nan tana Sokoto, kuma wai tayi sare_saren kaya shi yasa take kiranshi ya tura mata kuWi kimanin dubu Wari biyu da hamsin. Da taga ya™i daga wayar ne sai tayi mishi sa™o Mustapha"

ya girgiza kai kawai tare da yin ™uri yana kallon waje guda.

Shima kanshi a cikin matsalolin matan gida da tulin ´an matan daya tara a waje yake. Yanzu haka lokacin

da Babangida ya kirashi yana asibiti yakai budurwarshi anyi mata allurar zubar da ciki. Dole a asibitin ya

barota ita da ™awarta.

Shigowar wayar Sumy ne ya dawo dashi daga tunanin daya shige mai zurfi.

Matsawa yayi nesa dasu sa'a da tun zuwansu suke ta mayar da zance ya Waga wayar Sumy.

Ya kuka ji labarin?

Yanzu ne muka soma shigowa asalin gundarin littafin nagode sosai da wannan soyayya da kuke nuna ma

wannan labarin.

Uzairu zuchiyata yana mi™o sa™on gaisuwarshi ga duk masoyanshi.

Sabuwa ma tace tana godiya da uzirin da kuke ta yi mata. Tana bibiyar duk wani sharhi.Ina godiya sosai

sai Allah ya kaimu gobe.

MRS BUKHARI

IDAN KAYA YA GAJI....

GAMMO MA YA GAJI

BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ˜AMSHI

LITTAFI NA BIYU

SHAFI NA 2

INA GODIYA A GAREKU DUKKAN ŠAUKACIN MASOYANA.

INA MI˜A SA˜ON TA'AZIYYATA ZUWA GA IYALAN TSOHON SHUGABAN ˜ASA BABA BUHARI.

ALLAH YA BA IYALANSHI HA˜URIN RASHIN SHI. ALLAH YAYI MISHI RAHAMA.

"""Honey ya inata kiranka baka Waukar wayata ne?"""

Sumy ta furta a hankali cikin salon debe hankali.

Mustapha yace

"""Ke ³ar balaja'u ba"

"Honey yana kwance a asibiti babu yadda yake ´ar wahala kike wani kashe wayar"""

"A kidime Sumy ta tambayi dalilin, Mustapha ya fyeWe mata biri har wutsiya ya Waura da cewa."

"""Wayarshi na hannuna, kuma a ko da yaushe wayar zata iya komawa hannun mahaifiyarshi dan haka sai"

"ki tsagaita da kirashi kar kije ki kira mishi ruwa. Kinsan gidansu malamai ne gaba da bayansu dan Allah a kiyaye Sumy na sanki baki da mutunci"""

"Suka dan tattauna fisha haka, kafin sukai sallama daga ™arshe Mustapha ya dawo mazauninshi."

"Isowar Baba Malam yasa su Sa'a yin shiru, yana isowa ³ar Shuwa na isowa kamar tare suke, harda"

mahaifiyarta suka tawo.

Tare da Baba Malam aka rakasu Šakin da Babangida yake ciki.

"Malama Babba da Hamida suna zaune duk sunyi tagumi, shi kuma mai jinya yana kwance yana bacci"

"numfashinshi na fita a hankali a hankali, ga kafaWarshi Waure da bandeji, ga kuma inda akai mishi gyaran karaya a tsintsiyar hannun nashi ga karaya ga ciwo."

"Baba Malam ya ™urama fuskar Babangida idanu, me yake tunawa sai Allah sai shi da yake tunawa."

"""Yanzu Malam Sabuwa ce har zata Wauki Babangida ta maka a kotu sabida rashin ta'ido, duk halacci da"

"fifikon da kake bata a cikin surukanka da abinda zata saka ma da Šanka kenan, sannan a kamata da wani ™ato da aurenta dake ta kwashe kayanta daga gaban ma'aiki shine da abinda zata saka mana kenan? Ko da yake ita dama karuwa bata da al™awari. Wannan ciwon da suka jima Wana wallahi bazan yadda ba."""

"""Ke Saratu ya isheki haka nace. Lafiyanki kuwa, ya matar Wanki zaki dinga kiranta da karuwa a gaban"

"abokan zamanta?"""

"Shiru Malama Babba tayi ta sauke kanta. Fin shekaru ashirin rabon da taji Malam ya datsa sunanta, sai"

gashi akan Sabuwa yayi.

"""Allah ya bashi lafiya ni zan koma gida tunda dai Wan gatane ga dangi da matanshi baibaye dashi"""

"""Haba Malam ya zaka ce haka. Yaya akeso in yi da raina dan ALLAH?"""

Idanunshi ya kafa mata babu shiri ta yi shiru.

"""Ina nufin harke, su Sa'a ma kowa ta tafi gidan mijinta. Ramadan ya zauna dashi, matanshi ma zuwa dare"

"su kama hanya su koma gida umarnine Ramadan kaWai zai zauna"""

Yana dasa aya ya fice.

Dole ™anwar na™i Malama Babba ta mi™e tabi bayan Malam tana sharce ™walla.

Su kuma Hamida da ³ar Shuwa aka barsu zuchiya fal tunanuka ko wacce da abinda take

Please Login or Register in order to submit comment