You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cike da rashin daraja da rashin tarbiyya.

Abubbuwa a tsakanina da Babangida sun faffaru a wajen rawarnan sosai da sosai. Ga sigari bazan iya

tuna kara nawa na sha ba.

Hannuna Babangida yaja muka fice daga cikin club din zuwa dogon falon da zai sadamu da Wakunan

zangon ba™in.

"Wani Waki ya tura muka shiga anan muka tadda abokanshi. Mustapha, Gaddafi, Hannafi, sai Sani wanda"

shi Allah yayi mishi rasuwa.

Ko wanne budurwarshi tana gefenshi anata hira da cin nama da shaye_shayen sigari.

"""Mazaje wannan mai zafin fa?"""

Cewar Mustapha har yana zaro harshe yana lashewa

KafaWarshi Babangida ya buga.

"""Kai dan abu ta kazanka. Wannan ba irinsu Karina bace. Dubeta fa da kyau ai kai da ganin kasan zata"

bada wuta.

"Baby muje daga ciki"""

"Jana yayi zuwa cikin uwarWakin, su kuma abokanshi da ΄an matansu suna falo."

Gadon a mugun yamutse yake halamar anyi abubuwa akai dayawa.

Haka Babangida ya haye gadonnan tare da mi™o mun hannayenshi.

Wannan daren shine dare mafi muni a rayuwata dare mai Wauke da tarihin da abadan ban isa manceshi

ba.

Amman a ranar sai nake jin daren ya kasance darane na musamman a cikin sauran dararen dana saba

kasancewa da mazan bariki.

Babangida yakai iyakar ma™urar kaiwa. Amman fa bai wuce Khalid ba sai dai suyi kunnen doki.

Sai dai yafi Khalid iya lallaSa mace har mace ta dinga jin tafi kowa kyau da kayan atata ( Khadija maidoki).

Bayan komai ya lafa munje munyo wanka tare mun fito Babangida ya zaunar dani bisa cinyarshi cikin

™asa da murya da narke idanu yace.

"""Sabuwa ina sonki. Lokaci guda kikai zabari da zuchiyata. Amman ina da kishi yaya zaki yi wajen ganin kin"

"kiyaye motsawar kishina, hauka nake yi sosai in naga yarinyata da wani namijin. Sannan ina da naci naga kinyi daidai da irin halittata. Yaya zamu yi?"""

Cikin kissa nace.

"So kake nayi watsi da duk samarina in ri™eka kai kaWai wai tilo?"" Na ™arashe maganar ina murmushi na"

ciki irin wanda ba'a buWe baki sai dai aga halamunshi a kumatu.

"Kai ya Waga mun halamun ""E"" har yana sake gyara mun zamana a jikinshi da kyau."

"""Abinda nake so kenan"""

"Amman kana ganin baka so kanka da yawa ba. Sannan daga ganin sarkin fawa sai miya tayi za™i?"""

Cakulkuli ya shiga yi mun. Nan nahau dariya da shure_shure shi kuma dama musamman yayi hakanne da

manufar ya sake afkamun a karo na biyu. Ilai kuwa hakanne ya faru.

Kafin mu fito falo sai da Babangida yayi duk wani daWin bakin da kuka sani harna amince zan killace kaina

dominshi shi kaWai tare da al™awarin zamu dinga haWuwa babu fashi. Sannan zai dinga bani kuWi duk satin Allah.

"A falonnan muka kwana dukkanmu da abokan Babangida, wasu dai sukan tafi Waki daga baya su fito."

"Sai washegari da safe Babangida ya kawo ni har ™ofar gida a motar Abokinsu Sani. Da ragowar kazata, da"

"lemuka, ya ™irgi dubu goma ya bani."

KuWin da ya bani na mugun raina sosai. Amman yadda tasirin sonshi ya yaWu a zuchiyata lokaci guda

harma ya shafe tarihin wanzuwar Khalid a rayuwata yasa nake jin zan iya bashi kaina kyauta bama sai ya biyani ba.

Godiya nayi mishi na shige gida.

³ar Shuwa tana hangoni ta she™o a guje tazo ta rungumeni. Zuchiyata cike fal da farin ciki da mararin

kamuwa da sabuwar soyayyar da tasa nake jin ni nama fi ko wacce mace sa'a a duniyarnan.

Šaki muka shige muna dariyar iskanci.

Muna jiyo Rakiya nata zaginmu ko mu kula.

"""Bani labari dan ALLAH. Naga gayen da kuka fita tare ai. Naga gayen yayi har yafi Khalid kyau"""

"Ai bama iyakar kyau ba yafi Khalid komai da komai kuWi kawai Khalid zai nuna mishi"""

Dariyar da Yar Shuwa take yi sai ta dena. Nasan halinta sarai da shegen son kuWi.

"""Ai ni duk haWuwar saurayi in baida awalaja to Wallahi bazan saurareshi ba. Ni bana soyayyar wahala"

"kinga kuWi? To sun fiye mun komai ke akan kuWi sai mu raba gari dake"""

Dariya muka yi dukkanmu harda tafawa.

Labarta mata abinda ya faru na shiga yi ina yi ina farin ciki.

"""Kar dai ki za™e kinsan dai bariki babu amana. Ni ina mamaki da kike wani faWawa soyayya lokaci guda."

Kin ganni nan inje inyi abinda zanyi a bani kuWina a wuce wajen shi kawai na sani. Kinsan dai in ba tsautsayi ba babu yadda za'ayi kiyi saurayi a club ya Waukeki ku kwana tare ya biyaki har kiyi tunanin zai

"aureki sai dai in asiri zaki sa Maigogul yayi mishi"""

Dariya muka tuntsire dashi. Soma shigowar ΄an matan Wakin namu masu kwanan gida yasa muka

sassauta hirarmu. Ko wacce data zauna saita baje ™unshin namanta.

Rakiya ce ta shigo tayi tsaye.

"""Ko wacce ta kawo Wari uku kuWin wuta dan sunce yau babu Waga ™afa in bamu biya ba sai yanke wa."

Ke kuma Lolo har jikin naki yayi ™warin da bama jeka ka dawo ba harda kwana sai kin je kin jawo mana

"masifa tukunna ko? To ki dai tuna da maganar likita. Ni wallahi da aurenku kuka yi da zai fi muku da wannan tambaWar."""

Ni dai Wari biyar na zaro na mi™a mata ina ™un™unni. Haka kowa ya mi™a mata duk taba kowa canji.

"""Ko Wari uku ce ku bani zan sai sabulu in Wan wanke kayana"""

Nan fa wannan tace ita bata da kuWi wannan tace hidimar anko ce a gabanta. Sai ni na mi™a ma Rakiya

Wari biyun databani canji.

"Sai naji tausayinta sosai wallahi, uwa kenan duk lalacewarta uwa ce dai, Wari biyar na kuma zara na bata."

"Sai washe bakinta take yi, ta samun albarka babu iyaka."

Haka wunin ranar ya kasance mun gwanin daWi da farin ciki. Tun yamma Babangida ya karSo motar

abokinshi ya zo ya Waukeni muka tafi zaga gari kawai. Muna tafe muna hirarmu ta soyayya. Haka wannan ranar ma ban kwana a gida ba wani Wakin abokinshi dake bayan layinsu ya kaini abokin bayanan yayi tafiya.

Bayan komai ya lafa daf magriba Babangida yayi wanka a banWakin dake Wakin ya fito a gaggauce. A

lokacin ina kwance ina kallo a TV babu komai wallahi a jikina.

"""Baby zanje masallaci in yi Sallah. Amman bazan shigo ba sai ™arfe tara. Zan je gidanmu akwai makaranta"

"da nake koyar da maza bayan sallar isha. Makarantar ta mahaifinmu ne muna taimaka mishi ne. Dana sallami Walibai zan dawo dame zan shigo miki?"""

Idanu na buWe harda baki.

"""Me kake koyar musu, yanzu nan kai malami ne wai?"""

Tsugunnawa yayi yana dariya yace.

"""Kin Wauka wasane ko? Allah da gaske nake yi mahaifina Malami ne haka mahaifiyata malama ce."

Yayyena duk malamai ne muna taimakawa mahaifinmu makarantar tashi ce.

"Yanzu dakin Sulle bayan layinnan zaki hango gidanmu da tarin tulin almajirai"""

Kai kawai na jinjina ina mamakin Wan malam ya™i halin Malam.

"To yayi. In zaka shigo ka tawo mun da fanta mai sanyi da balangu mai ruwa_ruwannan asa yaji sosai """

"Hakan kuwa akayi da Babangida ya tashi tawowa yazo mun da sa™ona, kusan raba dare muka yi muna"

"aikin assha aikin dana sani aikin saSama Ubangiji, aikin zubar da mutunci."

Ranar bamu je club ba a wannan Wakin muka kwana da safe bayan nayi wanka na shirya inaso zan tafi

gida Babangida ya jawoni na faWo jikinshi.

"""Amman fa kince mun ba daWewa zaki yi ba, kar kisa inta jiranki a zaune anan. Duk da inaso zanje gida in"

samu in gaishe da mahaifiyata.

"To ni yaushe zaka kaini in gaisheta to?"""

Dariya muka yi dukkanmu nasan a raina Babangida ba aurena zaiyi ba morar ™uruciyata kawai yake so

yayi. Duk da yayi mun rantsuwar aure zamu yi.

Hakan baisa nayi ma kaina faWa ba saima sake dulmiya a kogin sanshi da nake yi a ko da yaushe. Ko dana

koma gida kayana na Wiba kala bakwai na dawo wannan Wakin abokin Babangida a ciki muka ci gaba da rayuwa tamkar mata da miji. Ina komawa gida duk bayan kwana biyu inje in kwana sai in kuma dawowa.

Munyi rayuwa irinta a'uzubillah ni da Babangida.

Gaga gaga rayuwa taita shurawa soyayya mai karfi muke ma juna ni da Babangida. Babu irin soyayyar da

"baya nuna mun. Duk da bai kai rabin Khalid kuWi ba amman Babangida komai shi yake yi mun, ga lokacinshi da nake samu a ko da yaushe, ko ina zamu muna tare a manne da juna. Sanadiyyar Babangida idanuna ya kuma buWewa a yawon dare da yawon zuwa club shima, sabida Babangida kullum sai ya je club. Ko yaya saurayi ya kulani Babangida zai cukumeshi sai inda ™arfinshi ya ™are, ba wuya ya fasa"

"kwalba, faWa dai akaina yayi da yawa, ya jima samari rauni da yawa."

Ta Sangaren gidanmu kuma Maigogul ya koma sana'arshi ta kawalci. Gaza ya fito daga gidan yari

Magazin kuma ya bar gari sakamakon wata Sarna daya aikata. Uzairu zuchiyata kuwa baya Wakkowa kowa magana shi dai a barshi da lalata yaran mutane da kalaman soyayya kawai.

Kwatsam wata ranar asabar na tashi da zazzaSi mai zafin gaske ko tashi bana iyayi sai an taimaka mun.

Ga wani irin ciwon mara da nake ji tamkar bayana zai dare ya fashe.

"""Sabuwa ki kira Babangida a waya ko zai kai ki asibiti mana naga jikin naki kuma tsanani yake yi"""

Cewar ³ar Shuwa kenan. Rakiya dake zaune tana shan tea da wainar ™wai tace.

"""Ato gara ta kirashi dai su je asibiti ina jiye miki in dai cikine dake wallahi kin shiga uku"""

Bata rufe bakinta ba Maigogul ya faWo Wakin da sauri.

"""Rakiya kaddai ciki Lolo ta kuma kwasowa? To wallahi a wannan karon watan barinki gidannan ne ya"

"tsaya kinsan Allah duk wanda yayi miki ciki sai kin aureshi na gaji da wannan masifar"""

"""Ka sassauta murya haba. Ba cikin bane gargaWi dai nake yi mata da jan kunne. Ka adana faWan naka"

tukunna in akaje akace cikinne sai kayi wacce zaka yi.

Ni jin suna ta wannan tababar ma sai naji tuni na nemi ciwon ma na rasa. Babu shiri nace.

"Nifa ba ciki bane dani, shikenan ba dama mutum yayi ciwo sai ace cikine?."""

Da™uwa Maigogul yayo mun ina zumSure baki na mi™e zaune na jawo jug din tea mai kaurin da Yar

Shuwa ta haWa mana zamu yi kumallo na soma sha. Ita kuma Rakiya ™auyensu ma zata tafi yau zata je

bikin Tsahare ita da Labbai.

Tana gama karyawa suka kama hanya har tasha muka rakasu muna dawowa muka tadda Babangida a

™ofar gida yana jirana.

"""Kaga Babangida soyayya daWi wato kaji mutuniyar taka shiru shine ka biyota ko?"""

Cewar ³ar Shuwa data zauna a dakalin da Babangida yake zaune. Shi kuma gabaki Waya hankalinshi

yanaa kaina.

Zama nayi daf dashi ina ™akaro murmushi dan bana wani jin daWin jikina.

"""³ar Shuwa meke damunta ne naga jikinta babu ™wari?"""

Yayi mata tambayar yana ™ara kallona cike da kulawar da take sake dulmiyani a soyayyar Babangida.

"""To yau dai da ciwon mara ta tashi mai tsanani. Abinda ya kashe mata jiki kenan. Da harma zamu kiraka"

"ko zaka kaita asibiti a duba lafiyarta sai kuma ta warke"""

Kai ya girgiza tare da cewa.

"""Sannu Babbar yarinya. Ko asibitin zamu je? Nama kira wayarki a kashe, ke da baki da lafiya to ina kuka"

"je harda kwalliya haka?"""

Sai lokacin nayi magana.

"Ba sai munje asibitin ba jikinma da sau™i. Rakiya ce tayi tafiya shine muka kaita tasha"""

"""Wacece kuma Rakiya?"""

Ya faWa tare da kafeni da idanu. Ni kuma cikin rashin damuwa nace.

Babarmu ce.

Baice dani komai ba sai cewa yayi.

"""Ni dama nazo in Waukeki ne mu fita"""

Idanuna na lumshe nima ina jin kewarshi sosai.

"To ai sai muje a shirye nake. Waya da jakata kawai zan Wakko"""

Nan na shige cikin gida na bar ³ar Shuwa tana yi mishi hira.

Qamriyya na hango Maigogul na tsine mata albarka har yana neman dukanta. Bakina a taSe na shige

Wakinmu ina tsaki. Lokacin ΄an matan Wakinmu duk sun dawo wasu na baje suna karyawa wasu na ramuwar baccin da basu samu yinshi jiya ba. Wajen jakar kayana na nufa banko kula kowa ba. Doguwar rigar materiyar na Wakko na sake kayan jikina nice harda sake kwalliya da janbaki. Jakata na zara nayi

ficewata ina fitowa muka wuce da Babangida ³ar Shuwa kuma ta koma cikin gida abinta.

"Haka dai lamura sukaita tafiya, kasala da nauyin jiki nata ™aruwanmun. Tafe_tafe har wata huWu"

"dukkannin wani sauyi a lokacin ya bayyana a tattare dani ni kaina naga nayi ™iba na sake yin kyau, ga"

wani irin haske bau dana sake.

Amman ban kawo komai ba duk da bana jinin al'ada dan yakan yi mun haka in nasha maganin zubar da

"ciki sai in yi wata shida al'adata bata zo ba, ko wata huWun A wannan karon ma saina Wauka hakannen."

Wata Ranar litinin na dawo daga wajen Babangida da safe mun kwana a club.

Rakiya dasu Adama duk suna tsakar gida har Maigogul yau ya tashi da gyaran fuska yana kan turmi da

madubi a hannu.

Idanu Hauwa ta ™ura ma cikina daya taso sai ta saki salati harda sakin bokitin hannunta.

"""Maigogul yarinyarnan Lolo wlh cikine da'ita ga ciki har ya bayyana."""

Ras naji gabana ya tattake ya faWi. Rakiya tace.

"""Yau ba™ar hassadar taki akan Lolo kuma ta sauka. To ta Allah ba taki ba. Sabida Qamriyya tayo cikin"

"shege za'ai mata auren dole shine kike son yima Lolo sharri? Ke dai Hauwa anyi jar mitsiyaciya kunga Mata da shegen hassada. Lolo dai tayi muku fintinkau wallahi nan gani kuma nan bari"""

A zabure Maigogul ya mi™e.

"""Ke Rakiya yafa isheki haka. Kinsan Allah a wannan karon babu sani babu sabo. Bana neman wata"

"magana ki duba mun Lolo cikinne da gaske ko kuwa?"""

Rakiya zata yi magana Maigogul ya dan™aro ashariya ya dan™ara mata tare da doka ™afarshi yana kumfar

baki.

Allah dai ya taimaka Rakiya bata yi yin™urin ramawa ba ta nufo ni ni dai jikina har rawa yake yi dan

"kaWuwa. Latsa cikina tayi ta dubeni muka haWa idanu, ta sake latsawa."

"Maigogul da Hauwa, da su Sadiya kowa yayi shiru yana jiran abinda Rakiya zata ce."

Jikinta a mugun mace tace.

MRS BUKHARI

"[8/14, 7:22 AM] +234 802 205 9556: IDAN KAYA YA GAJI...."

GAMMO MA YA GAJI

LITTAFI NA UKU

SHAFI NA BIYU 2

BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ˜AMSHI

https://chat.whatsapp.com/JmCasXpUuuT0J6dfLTWFNk?mode=ac_t

.

18066696785.

Hussaina Bello

HAJIYA KAYAN KITCHEN KIKE SO MASU SAU˜I DA KYAU. KO KUMA SARIN KAYAN KITCHEN KIKE SO KI

SOMA KIN RASA INA ZAKI SAMU AKAN FARASHIN DA KEMA ZAKI SAMU ALKHAIRI?

H@H AVAILABLE WHOLESALE AND RETAIL DUNIYA NE

MAZA TUNTUE HUSSSAINA BELLO KAI TSAYE A LAMBAR WAYARTA.

KO KUMA SHIGA CIKIN ZAURENTA DOMIN KASHE ˜WAR˜WATAR IDANU

"""shikenan Lolo yanzu duk jan hankalinki da nake yi saida kika sake yadda wani shegen ya durka miki wani"

"cikin. Kin mance da jar wahalar da kika sha, da gargaWin da likita ya bayar akan ki, ke da kamar ba ma zaki rayu ba."

"Ai shikenan, ke kuma Hauwa hankalinki ya kwanta, kai kuma me son ji Lolo to cikine da'ita sai kayi"

"abinda zaka yi akai."""

Tana faWan haka tayi shigewarta Waki. Tana kutuntuma zagi. Maigogul ya daWe a tsaye yana nazari kamar

ma bazai ce komai ba. Hauwa kuwa sai shewa take yi tana faWin.

"""Bana dai ΄ar so za'a wuce gidan miji tunda ita ba sai tayi ciki sau uku da namiji Waya yanzu duk cikin"

"daya shiga dole a haifeshi. Uhm lallai nagode Allah da yasa a Wakin Rakiya za'a soma kafa tarihin Wan kuka, Maigogul da Rakiya za'a sha raino. Mai arzikin dai da ake nema ake fata ba'a samu ba Alhamdulillah. Yadda yaranmu aka cusa su kema dole a cusa ki."""

Da ido maigogul yake ta bin Hauwa abun al'ajabi baice uffan ba.

"Waya Maigogul ya zaro a ajjihunshi ya danna kira, jim kaWan aka Wauki wayar."

"""Cicib kazo ka same ni a asibiti zaka raka ni wani wajen daga asibitin"""

Iyakar abinda ya faWa kenan ya kashe wayarshi.

"""Ke Lolo ki shirya dan ubanki zamu je asibiti daga asibiti kema kinsan sauran zancan. Ke kuma Hauwa ki"

kaimun ruwan wanka yanzunnan in watsa mitsiyaciya mai neman maganar tsiya yau dai in baki bi Rakiya

"a sannu ba tana iya danda™aki"""

Šakin Rakiya fuu ya shige. Hauwa kuma ta juye mishi ruwan wankan tana ta wa™en baka.

"""Lolo kije ki shirya kafin ya fito. Ki dena Waga ma kanki hankali cikin shege ba kan ki barau ba kuma ba"

zaki zama ™arau ba.

"Wanne irin cikin shege ne ba'ai a gidannan ba?"""

Cewar Adama. Labbai tace.

"""Kuma ba'a Wakko shirin denawa ba. Shima Maigogul faWan gan_gan kawai yake yi. Kuna zuwa aka bashi"

"kuWi shikenan fa zancan ya ™are duk da naki lamarin ya dakeshi ya sha bambam da namu"""

Ni dai zama nayi a cikin ΄an uwana nayi shiru babu uhm banu uhm_uhm.

A wannan ranar Rakiya da Maigogul ba karamin rikici suka yi ba. Tun suna yi a daki har suka fito tsakar

gida Rakiya na cukume da wuyan Maigogul. Da dai yaga Rakiya na neman ta kwashe mai ™afafu ta zuba shi da ™asa ai sai dambe ya kaure Rakiya na Kururuwa. Abun kunya matan ma™otane da Malam Habu ma™ocinmu mutumin Labbai suka raba wannan rikicin. Kuma akaimun terere akan nayi cikin shege ne. Ni

kam a lokacin ko a jikina dam bamu san wata kunya ba.

Har Maigogul ya fito wanka ya shirya su Labbai nata godona akan in shirya nima na™i fur.

"""Taso muje Lolo asibiti a tabbatar mun cikin ne in shine kuma wata nawa"""

Carab Hauwa tace.

"""Wannan cikin zai iya kaiwa wata biyar ko huWu"""

BuWar bakin Maigogul yace.

"""To da shike ke kika yi mata ko? Hauwa ki kiyayi Rakiya a gidannan yau."""

Rakiya ce ta fito mayafinta a kafaWa.

"""O_o batta tayi ai duniya ce. ³a΄a gasu nan jibge a Wakinta. Lolo kuma ita ta siyo mun abinda Hauwa ta"

"samu nasara a kaina. Sana'ar kayi nayi na ta fiye mun wannan kaddararren gida, da ™addararren miji, da ™addararriyar jar makirar kishiya wallahi dukkanku bakwa gabana"""

Tana kaiwa nan ta wuce.

"""Ke Adama tawo muje ki raka mu ayi komai a gabanki."""

Tasowa Adama tayi muka rankaya asibiti. Muna kan bin layi Cicib ya ™araso yana rausaya mu uku muka

shiga Wakin Adama aka barta a waje.

"""Ku kuje daga waje Baba inna gama dubata zan kiraku"""

Wannan likita ta faWa ranta a Waure.

Haka su Maigogul suka fita.

Likita ta gama aune aunenta ta tabbatarma da su Maigogul cikine na wata huWu babu sati Waya a jikina.

"""Lolo ina fatan kinsan wanda yayi miki cikinnan, sannan kinsan gidanshi ina nufin gidan da matarshi da"

"yaranshi suke ko?"""

Maigogul ne yayi mun wannan tambayar cikin dakewa da kakkafeni da idanu.

"Saurayine bashi da aure. E nasan gidan amman"".."

Dakatar dani yayi da hannunshi.

"""Wuce ki kaimu gidansu tunda dai kinssn gidan. Saurayine, magidancine, talaka ne, ko mai kuWi wannan"

"kuma ke ta shafa"""

"""A_a Maigogul me zai hana shi yaron a kirashi tukunna ya sameka in yaso in yayi musu sai a dangana da"

"gidan iyayen nashi. Kaduba abubbuwan da suka faffaru a baya. Sannan Lolo kes Winta ya bambamta ita dai babu halin zubar da ciki ya kamata a nemeshi ayi magana ta nutsuwa dashi, in aurenta zaiyi sai ya aureta su rufama juna asiri"""

Maigogul ya dubi Adama data gama magana ya dubi Cicib dake tsaye yana gyara mayafinshi. Nima ya

kalleni tsab.

Cicib yace.

"""Yarinya tazo da hanzari. Yanzu Maigogul abi a hankali din. Ita Lolo ta kirashi ta sanar dashi mu muna"

"nemanshi zuwa da daddare ™arfe takwas. Barsu su yi tafiyarsu kasan na baro ba™i ."""

Sai da naga su Maigogul sun Sace kafin na sauke ajjiyar zuchiya mai ™arfi.

Muna cikin abun hawa Adama taga nayi shiru ina tubkewa ina warwarewa.

"""Ke Lolo da mun koma gida sai ki kira shi saurayin naki ki sanar mishi halin da ake ciki. Amman ina ganin"

zaifi kyau ki sanar mishi cewar ana nemanshi a gidanku. Duk da dai nasan babu al™awarin aure a

tsakaninku. To yaya zamu yi a haka muka tsinci rayuwarmu.

Maigogul da kanshi yaita ingizamu zuwa shiga duniya sabida kyan da Allah ya huwace mana. Gashi duk

kyanmu ya zama kyan Wan maciji.

Ajjiyar zuchiya na sauke duk abinda ta faWa babu gyara a cikinshi

Amman Adama kai tsaye sai inga kamar in nace mishi ana nemanshi ba tare dana sanar dashi dalilin

"neman ba. Ba lallai bane yazo, amman in yaji akwai ajjiyarshi a jikina zai iya zuwa ko dan tsoron tonuwar asirinshi tunda gidansu gidan malamai ne."""

"""Toh hakane kam kince wani abun kuma. Shikenan ki sanar mishi yayi ™o™ari yazo in ba haka ba sai yayi"

"dana sanin saninki a rayuwar baki Waya dan wallahi Maigogul suka je gidansu za'ayi Wauki babu daWine."""

Haka mukaita tattauna matsalolin kanmu da kanmu har abun hawa ya saukemu a kofar layinmu.

Gidan ko da muka shiga Hauwa ce kaWai a gidan sai ΄ar Shuwa dake ta shafa hoda halamun fita zata yi

ita mahaifiyarta ta sama mata miji wani Wan uwanta zata aura harma magana tayi zurfi yazo ya ganta sau

"biyu kuma ya yaba, itama ³ar Shuwa tayi na,am dashi. Yanzunma shine yace zai zo daga Maiduguri bai"

wuci kwalliyar tarbarshi akeyi ba dan a Wakin Rakiya suke zancan.

A tsakar gida Adama tayi zamanta mu biyu ne a Wakin.

"""Sabuwa anya kuwa cikin dake jikinki kuwa na Babangida ne? Ni sai nake ganin kamar na wannan Alhajin"

da yazo Jamus ya haWaki dashi ne. Ko dai kin mance ne? Gashi shi ba'asan ma a ina yake ba. Ko dai a

"hakan kike so ki ™a™abama Babangida? Kinsan dai mitsiyacine baida wani kuWi ke rayuwarsu Layuza bata zame miki abun duba ba, yama kika yi sake ciki ya shiga ne? """

Ras gabana ya faWi nama rasa ni kam mai zance dan shab na mance da batun Alhajin da Jamus ya haWani

"dashi, kuma cikin yayi daidai da lokacin da muka haWu. To amman Yaya zanyi? Tunda dai wannan Alhajin"

ni bansan inda zanma sameshi ba. Shi kanshi Jamus in wu™a za'a saka mishi baisan inda yake ba kuma

"baida lambarshi, duk da dai babu tabbacin cikin nashi ne gaskiya."

To ³ar Shuwa yaya zanyi ni dake kaWai muka san wannan ™ullin inaso mu haWu mu binneshi a

tsakankaninmu. Dole Babangida zan li™ama cikinnan. Tunda bamu da tabbacin ba nashi bane tunda

"shima ai muna tare dashi a lokacin."""

Shigowar Adama tare da Rahama da tazo yanzu tana tafe raSe_raSe da yara yasa dole muka rufe shafin

nan aka buWe sabon shafi.

"""Lolo kiyi ™o™arin kiran saurayinki tun yanzu ni dai na faWa miki"""

Kafinma ta haWiye yawo kiran Babangida ya shigo wayata. Šanewa nayi ™uryar katifar Rakiya.

Allah ya taimaki mai martaba sarki a cikin zuchiyata. Koda yaushe zuchiyata da gangar jikina cike suke da

"kewarka. Dama ko baka kirani ba daman ni zan kira akwai abinda ya taso ne"""

"""To bari in gama sauraren sarauniyar dake da babbar fada a zuchiyata. Lokacina naki ne ke nake saurare"""

Kai tsaye nace dashi.

"Cikine dani, kuma kasan cikinka ne tunda bana kula kowa. Shine Maigogul yace kazo yana so ya ganka"

"zaku yi maga.."""

˜it Babangida ya kashe wayarshi. Da mamaki na zare wayar a kunnena da gaske katsewa yayi?

Sake kira nayi sai ga wayarshi a kashe abun almara. A karon farko dana taSa jin wayar Babangida a kashe

kenan.

"Hmm bariki kenan alalan gero kunun wake, ni Babangida yake so yaima akuyanci? Ashe baisan wacece"

Sabuwa ba labarin Sabuwa yake ji? Ni da na zauna a kango na kwana na tashi a cikin ru™a™™un shegu. Na

"taka duk ubanda naso. Naba Babangida kwana biyu matsawar bai neme ni ba kuma bai zo ba zan nuna mishi nawa kalan barikin"""

"³ar Shuwa ce ta duro gadon, na kalleta kawai ina harare_harare, gasu Adama sai mayar da zancan cikin"

"suke yi."""

Labartama yar Shuwa nayi tare sa Waurawa da cewa.

Wallahi saina kuikuyama Babangida rashin dajarar da sai yayi dana sanin shiga bariki. Waini Lolo yau ni

"namijin bariki zai nuna ma bariki ni da tsabar yagewan idanuna dayan ya haWe da Wayan."""

Dariya muka saka harda tafiwa.

"""Tabb ustaz ya taro mach Win da bazai iya bugawa ba. Da yasan waye Sabuwa da Maigogul wallahi bazai"

"kashe wayar ba, kuma bazai ™i amsa wannan gayyatar girman da babuma wanda ya taSa samu ba."""

Da daddare sai ™aryar Babangida yayi tafiya zuwa jibi zai dawo nayi musu.

"""To naji jibin kaWai kike dashi wallahi. Ko ya dawo ko kar ya dawo zamu je gidansu dan asan da ajjiyarshi"

"a jikinki tunda haihuwar cikin za'ayo dole ™anwar na™i."""

Da haka muka rabu dasu ina cike ni kuma da mamakin Akuyancin Babangida.

Duk sanda zan kira wayarshi a kashe take har Allah ya kawo mu kwana biyun wa'adin sharaWin da

Maigogul ya gindaya.

"""To Lolo taso muje rana bata ™arya. Cicib yana waje yana jiranmu"""

"Riga da wandone a jikina a haka na mi™e na warware gyalen dake Waure a kaina na yafa, wu™a na soke a"

™un™uruna muka fito. Har munzo bakin ™ofar gida Rakiya ta tawo da sauri.

"""Maigogul wai yanzu in kunje me zaka cema mahaifan yarannan?*"

KafaWa ya Waga tare da cewa.

"""Me kuwa zan faWa musu daya wuce abinda ya faru. Ke kinga mu sai mun dawo"""

Haka suka sakani a gaba abun hawanmu har kofar gidansu Babangida. Ai kuwa almajirai cike da

makaranta anata karatu. Ga wani farin dattijo mai cike da kamala da haiba. Yanayinshi kaWai ya tabbatar da yana da managartan halaye Albasa ce kawai batai halin ruwa ba.

Wallahi ko ku kuka ga mahaifin Babangida sai kunji inama wani Wan uwanku ne.

"Ga gidannan. Inaga wannan shine mahaifin

Please Login or Register in order to submit comment