You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ban sansu ba.

"""Akwai wani sabon labarine?'"

"E akwai barister"""

"Nan na zaiyana mishi yadda muka yi da Babangida jiya. Da labarin da su Adama suka kawo mun yanzu"""

"""Da kyau waWannan maganganun suna da matu™ar amfani zamu adanasu da akwai gaSar da zamu"

"sokota. Yanzu muje an soma shiga kotu"""

"Wucewa yayi ya barni, ni kuma na koma wajensu Adama."

"""Mu jenku Sabuwa anata shiga mu muna tsaye"""

Inji Adama kenan. Sai da su Babangida suka wuce mu kafin muka bi bayansu zuwa cikin kotun.

Kotu dai a mugun cike take yau ma™il cikin ™an™anin lokaci kotun ta cika har babu wajen zama dole wasu

"suka tsaya daga waje, ciki harda Hamida da Amaryar Babangida ³ar Shuwa kam ita da uwarta summa"

riga mu shiga kunnenta naWe da audiga. Da halama ba shari'armu kaWai za'ayi ba. Dan duk inda na waiga sai inga bansan mutanen ba dan sun fimu yawa sosai.

"Karfe goma dot al™ali ya shigo ta wata karamar kofa. Duk muka zabura muka tashi, bamu zauna ba har"

"saida al™ali ya zauna kana."""

Mai karanta ™arane ya mi™e da takadda a hannunshi ya soma jawabi kamar haka.

""", Ayau ashirin da biyu ga watan maris ne zamu saurari ™ara mai lamba Wari da shittin. ˜arar da Halima ta"

"shigar tana tuhumar mijinta Baballe da handame mata kuWaWen gadonta tare da siyar mata da gidanta data gada."""

"Ashe ba shari'armu za'a soma ba. Kai kawai na girgiza maza da yawa son zuchiyoyinsu kawai suka sani."""

Al™ali ya Wago kai yace.

"""Lauyan Halima in yana kusa ya gabatar da kanshi."""

Wani lauyane ya mi™e tare da cewa.

"""Cike da girmawa ya mai Shari'a sunana Barrister Buhari Ladan nine lauyan wacce ta yi kara wato Halima."

Nagode ya mai Shari'a.

Yana zama wani lauya ya mi™e shima yace

"""Sunana barrister Ibrahim Abubakar nine lauyan wanda ake ™ara wato Baballe. Nagode mai Shari'a."""

Al™ali yace.

"""Ko lauyan wacce take ™ara yana da shimfiWa da zai ma kotu?"""

A zabure da zafin nama ya tashi.

"""My lord Halima matar Baballe ce suna da yara huWu tare dukka mata. Mahaifinta ya rasune shekarar"

biyu da suka wuce ya rasu ya barma yaranshi su Halima kadarori da ruwan dukiya.

Jin™ai irin na mace akan mijinta da Halima ta nuna ma Baballe shine. Da aka raba aka bata gadonta na

gida da ruwan kuWi miliyon bakwai. Kuskuren da tayi saita dam™ama Baballe miliyan biyar a hannunshi

tace ya ja jari dasu. Kasancewar yana taya abokinshi saida motoci saita bashi shawarar me zai hana ya dinga bin abokin nashi zuwa kwatano suna Wakko mota tare tuwaris.

Akan wannan dalilin Halima ta ba Baballle kuWinta kuma ba kyauta ba da sharaWin zasu dinga raba duk

wata riba da aka samu harya gama biyanta kuWinta.

"My lord kuWinta basu fito ba, a tsakaninta da Baballe babu mutuntawa daga karshe da kuWinta yayi"

"aurenshi ya kama ™atotin gida ya saka amaryarshi, ya sai motar zagaya gari da'ita. Ita Halima da yaranta ya barsu a ™unci."

Hakan baiyi mishi ba kuma kwatsam Halima na zaune da yamma a gidanta ranar talata biyar ga wannan

watan. Sai taga Baballe da dillalai masu duba gida.

Data tambayeshi lafiya saiya kada baki yace da'ita ya saida gidan harya amshe kuWinshi dan haka shi ya

saketa ta tattare kayanta ta bar gidan.

Akan wannan rashin adalcin da Baballe yayi ma Halima ta shigar dashi ™ara sabida ™ila ya amta da

hukuma.

"Ina neman wannan kotu mai alfarma data dubi halima ta kwato mata hakkinta. Nagode mai Shari'a """

"Kai na girgiza ina kwatanta girman wautar da Halima tayi. Ko da yake bana kira hakan da wauta ba, ita a"

"tunaninta shine mijinta shine makwafin ubanta a wannan lokacin, kuma dashi kaWai ta amince shi yasa"

ta dan™a mishi ragamar dukiyar tata. Shi kuma ya tata mata wannan rashin mutuncin.

Muryar alkaline ya katse mun tunanina.

"""Lauya mai kare wanda ake ™ara yana da abun cewa ne?"""

"""Ya mai girma mai Shari'a ina da ja akan dukkan abinda lauyan wacce tayi ™ara ya faWa a matsayin"

"shinfiWa. Sannan ya kamata ya iya harshenshi wajen tabbatar da laifi akan wanda ake tuhuma, domin zargine ba tabbas"""

Al™ali yace.

"""Barister Buhari Ladan a kiyaye jingina laifi kai tsaye ba tare da an tabbatar ba."""

Lauyan wanda ake ™ara yace.

"""My lord Halima matar Baballe bata ba Baballe ko sisin kwabonta ba. Asalima shi da kanshi ya ro™i ta"

taimaka mishi da jari ta™i. Kowa yasan Baballe mutum ne tsayayye ba mai macacciyar zuchiya ba. Babu ko sisin kwabon Halima a hannunshi. Batun gida da take ikrarin ya siyar ya saketa. Ya mai girma mai Shari'a itace ta siyar da abinta sabida kishin auren da mijinta yayi wai itama sai an kama mata hayar tabkeken gida kamar yadda ya kamama Amarya. A wannan gaSarne ya saketa kuma Allah ya baka yawan

rai yanzu haka a cikin kotunnan ya dawo da matarshi.

"Nagode my lord """

Halima dai sai share hawayenta take a kusa da juna muke inaji tana sambatu masu zafi da raWaWi.

"""Bayan sauraren ™ara da wannan kotu tayi, da shimfiWa da lauyoyin Sangare biyu suka yi."

Wannan kotu ta Wage ™ararnan zuwa ashirin da biyu ga wata na gaba. Tana bu™atar lauyoyi na

Sangarorin da su kawo hujjojinsu masu ™arfi domin kotu taci gaba da saurarensu. Sai ™ara na gaba

"kuma"""

Mai karanto ™ara da ake kiranshi da turanci ko mene nadai kasa haWe turanci amman ai kun ganeshi ko?

Saiya mi™e yace.

"""Sai ™ara mai lamba Wari da sittin da Waya wacce Sabuwa ta maka mijinta mai suna Babangida a kotu bisa"

tana neman ya saketa sakamakon kasa cika hakkokinta na Aure.'

Al™ali yayi rubutu yayi rubutu kana yace.

"""Zamu je hutu na rabin awa in mun dawo saimu saurari ™aran."""

"Wannan guduma ya buga, yabi ta ™ofar baya ya fice."

"Nan take kotu ta Wauki hayaniya ³an uwan Halima suka shiga tsinema Baballe, da wannan muka"

"runtuma zuwa wajen kotu. A wajenne muka tarar da Baba Malam, da su Rakiya da Maigogul suna zazzaune."

Gefe guda na zauna nayi tagumi. Baba Malam ne shi da Barister Ahmad Ahmad suka karaso inda nake.

Gaishe da Baba Malam nayi da girmamawa ya amsa kamar kullum.

"""Sabuwa kar ki karaya naga halamun mutuwar jiki a tattare dake. Zan baki duk gudunmawar data dace."

Dangane da shirin da Babangida da gyatumarshi suke yi bazai yi tasiri ba da izinin Allah. Akan son

zuchiyoyinsu da cimma manufofinsu kawai suke.

Kai na gyaWa nace.

"Allah ya bamu nasara Nagode sosai Baba Malam"""

Maigogul ya karaso wajen a hargitse.

"""Lolo inaso zanyi magana dake ta ™arshe kafin ayi zaman kotunnan. Gara da Allah yasa kuka fito'"

"Magana zanyi, muka haWa idanu da Baba Malam ya girgiza mun kai halamar kada in musa mishi."

"Jiki ba laka na mi™e nabi bayanshi har zuwa wajensu Rakiya da Hauwa, dasu Adama."

"""Lolo ashe ba zaki ji maganarmu ba kin dage sai kin tozarta uban ΄a΄anki ke akan daidai kike ne. Wanne"

irin iskancine baki tata a gabanmu ba. Kin dace kin auri malami Wan gidan malamai a kab ΄an uwanki babu wacce baki fita dace ba. Ki duba irin mazan da suke aure daga ΄an iska sai ΄an abu ta kazan uba.

"Adama zawarci, Labbai zawarci, ™annenku duk zawarci Salaha, da A'isha, da Rahama ne fa kaWai suke"

zaman Aure. A Wakin Hauwa kuwa Layuza ce kaWai sai Qamriyya da aka kawo sadakinta za'ayi bikin.

"Dame kike so inji Lolo. So kike ki tozarta kanki ba wani abun ba. In Dai baki janye wannan Shari'ar ba, ki"

"sani ko Babangida ya sakeki ba zaki zauna mun a gida ba saidai ki kama haya kamar yadda su Adama akace sun kama haya suna shirin tarewa. ni dai na faWa miki"""

Tunda maigogul ya soma maganarshi nayi ™uri ina kallon waje guda. Rakiya itama ta kama taita

ragargazata da yi mun tone tonen abubbuwan da bana ko ™aunar tunosu ma.

"""Lolo kiyi ma kanki faWa ato. Duk wuyar gidan Babangida kinsan yafi gidan ubanki. Ba'a rageki da ci da"

"sha ba, suturarnan kina dasu yaranki suna karatunsu."

Duk abinda kika samu mu shi muka rasa muka zauna har saida aka koremu muka ha™ura. Yaranmu duk

"sun kama irin layinmu na bin maza baka isa ka hanasu ba sabida babu abinci, babu sutura yaya zasu yi suyi rayuwarma.'"

Inji Adama kenan. Ina tsaye nayi shiru har lokacin shiga kotu yayi. Bance musu kuci kanku ba har suka

gama. Kai kawai nasa na wuce cikin kotu ko gani banayi sosai sabida jiri.

"Kotu ta cika da dangina dana Babangida, harma da ΄an kallo waWanda ba'a fiye rasasu a kotu ba."

"""Lauyoyin Sangare biyu su gabatar da kansu."

Barister Ahmad Ahmad ne ya tashi ya gabatar da kanshi. Kafin lauyan Babangida ya mi™e.

"""Sunana barrister Abubakar Shagari nine lauyan wanda ake ™ara tare dani akwai abokiiyar aikina wanda"

"tare zamu yi aiki. Nagode my lord."""

Yana zama abun mamaki sai wata lauya mace ta mi™e.

"""Sunana barrister Asabe madaki. Nagode my lord."""

Kai na gyaWa wato su Babangida a shirye suke lauyoyi har biyu? Allah ya bamu lafiya.

"""Ko lauyan wacce tayi ™ara yana da shimfiWar da zaima kotu?"""

Gabana ya faWi ras. Barister Ahmad Ahmad ya mi™e yace.

"""My lord Sabuwa ta shigar da ™aran mijinta Babangida ne a bisa dalilai masu yawa kamar haka."

Na farko Babangida baya ciyar da Sabuwa da ΄a΄anta.

Na biyu baya biya ma yaranshi kuWin makaranta.

"Hatta da sutura baya musu, bai damu da lafiyarsu ba."

Uwa uba ya jingine Sabuwa tsawon lokaci baya sauke hakkin daya rataya a kanshi na mu'amalar Aure.

Sai dai duk ranar da yaji sha'awarta yazo ya nemeta ta hanyar ™arfi.

Babangida yasha ya doki Sabuwa ya hakke mata tamkar namijin da ke ma yarinya fyaWe.

Daga baya ma ya ajjiyeta a gefe ta fita daga jerin matanshi a zahiri saidai a baWini matarshi ce.

Cin mutunci da cin zarafin iyayenta babu wanda bayayi mata.

Da wannan ne Sabuwa taga cutuwar tayi yawa take ro™on wannan kotu mai alfarma data kwato mata

hakkinta.

Sannan ko a musulunci Babangida bai sauke hakkin da Allah ya rataya mishi akan iyalinshi ba. Ba'a aure

"babu abubuwannan dana lissafo. Nagode my lord"""

Wasu siraran hawayene suka shiga aikin yawo a kumatukana.

Barister Asabe madaki ce ta mi™e.

"""My lord duk abubbuwan da lauyan Sabuwa ya faWa zamu iya kiranshi a ™age. Sabida Babangida yana"

ciyar da Sabuwa yana shayar da'ita kuma yara suna zuwa makatanta. A yanzu haka ma suna makaranta.

Ya mai Shari'a Babangida yana neman hakkinshi a wajen Sabuwa sakamakon bin maza da take yi da

aurenshi. Malama Sabuwa har a hotel take kwana da maza da aure a kanta.

Akwai sanda Babangida ya kamata ita da Khalid wanda ya kasance tsohon saurayin ita Sabuwa ne tun

tana budurwa.

Sabuwa a titi tayi dambe da mijinta Babangida sabida kawai ya kama Khalid da dambe.

Wanta kuma ya sari Babangida a kafaWa shi da sabuwa suka haWu sukaita dukanshi.

"A ta dalilin wannan saida Babangida yayi fin sati uku a asibiti, ga rauni a kafaWarshi ga karaya duk a"

hannu Waya.

"Ya mai girma mai Shari'a Babangida yana neman a fitar mishi da hakkinshi."""

Zama tayi.

Ni kuwa sai haWiyar zuchiya nake yi zufa na keto mun.

Barister Ahmad Ahmad ne yace.

"""My lord ina da ja. Lauyan wanda ake ™ara kwatakwata ya sauka akan layin shari'ar da muke yi ."

In tuhumarta Babangida yake son yi ™ara zai shigar shima domin a kwato mishi hakkinshi.

"Yanzu muna magana ne akan Sabuwa da ta kawo karan Babangida da tana son ya saketa"""

"""Ina da ja ya mai Shari'a """

Cewar baristar Abubakar Ibrahim daya mi™e.

Al™ali ya bashi damar yin Magana

"""My lord Batister Asabe madaki tana kan layin shati'a ta yiwu sabida halin rashin kamun kai da bin"

"mazan banza ne yasa Babangida ya watsar da lamarin Sabuwa. Tunda yasan tana bin maza taya zaici gaba da Waukar Wawainiyarsu. Ya mai girma mai Shari'a wannan shari'ar tana da girma muna bu™atar a bamu lokaci domin gudanar da binciken daya kamata a tsanake. Sannan a duba wanda ake tuhuma bashi da cikakkiyar lafiya kullum yana zuruftun zuwa asibiti wankin ciwone, asalima kwananshi uku da aka"

"sallamoshi daga asibiti. Muna bu™atar lokaci mai tsawo. Nagode my lord """

"Bayan al™ali yayi rubutu, yayi rubutu saiya Wago yace."

"""Ko lauyan wacce take ™ara yana da ™orafi?"""

Mi™ewa yayi yace.

"""E akwai ya mai girma mai Shari'a. Muna ro™on wannan kotu mai alfarma da kada taja wannan shari'ar"

domin Sabuwa tana cikin damuwa sosai. Sannan mara lafiya tunda yana iya zuwa asibiti zai iya halartar

"zaman kotu. ˜orafina kenan nagode my lord"""

Tunda lauyoyin Babangida suka soma magana nake tsiyayar hawaye babu ™a™™autawa. Zuchiyata har

tsalle take yi mun tsabar bugawa. Dana waiga na kalli ΄an uwan Babangida matan da Malama Babba saina ga suna cike da farin ciki. ³an uwanshi maza kuma girgiza kai kawai mafi akasarinsu suke yi.

Dubana na mayar kan Baba Malam wanda na kasa fuskantar a cikin irin yanayin da yake.

Ta Sangarensu Maigogul sai naga tamkar sunfi su Malama Babba ma farin ciki. Su Adama kuwa ko wacce

ranta a Sace yake da dukkan halama suna tayani jin zafin abinda ke faruwane.

"""Bayan sauraren ™ara da wannan kotu mai alfarma tayi wannan kotu ta Wage wannan ™ara izuwa Waya ga"

watan Mayu. La'akari da shi Babangida da ake tuhuma bashi da ishasshiyar lafiya. Kotu ta bashi dama yaje yayi jinya kafin ya dawo aci gaba da sauraren wannan shari'ar. Sannan tuhumar da Babangida yake ma Sabuwa bai shafi shari'ar da muke yi ba. In hakan suke so sai ya shigar da sabon ™orafi. A zama nabiyi

"lauyoyin Sangare biyun zamu basu damar soma gabatar da hujjojinsu."""

Ya kwaWa gudumar kotu duk aka mi™e.

Ni kam saida Adama ta tallafamun kafin na iya tashi. Bana ko ganin gabana Adamace ta zame mun

garkuwa.

Da muka fito harabar kotun lauyana da Baba Malam ne suka tareni.

"""Sabuwa ki kwantar da hankalinki ki dena Waga ma kanki hankali. Ko wata nawa aka saka na sake zaman"

kotu zaizo ne. Kuma duk yadda azzaluman lauyoyi suka kai da iya sharri dole za'a kai ™arshen wannan

shari'ar dole. Barister Ahmad zai nemo wani lauyan suma su zama su biyu. Shari'a yanzune za'a soma.

Adama ki daure tunda naji labarin mutuwar aurenki kije ki zauna da Sabuwa ko dan Webe mata kewa.

"Ramadan anjima zan aikoshi da kuWin cefane da kayan abinci ya kawo muku."""

"Godiya nayi mishi kawai Sama da Uzairu zuchiyata ne suka ™araso inda muke tsaye, su Maigogul kuwa"

suna keSe da Babangida.

"""Lolo wannan tonon sililin har ina, kinji fa abinda lauyan mijinki yake cewa a kotu. Wai hotel_hotel kike"

zuwa mu'amala da mazan banza. Wai shine nace wai dama baku watsar da rayuwar da kuka gudanar a baya ba. In da anji talaucine ya sakaku kaucewa yanzu da kike gidan aure kuma me yasa kika kauce?

Adama kinsan Allah nakai zuchiyata nesa ne da muna fitowa zan cukume Babangida ayi wacce za'ayi.

Allah yasa Gaza bayanan yana canma a kulle me yau da anyi batacciya.'

Adama tace.

"""Sama duk fa abinda yake faruwa Sabuwa fa akan daidai take. Abinda kaji lauya ya faWa sharrine. Ina"

"Khalid tsohon saurayin Lolo?"""

Ta tambayeshi Uzairu zuchiyata yace.

"""Wannan baban nacin zaki ce mun"""

Adama tayi dariya tace.

"""Shifa. To a asibitin da ita Lolo take kai yaranta yake ranar taje asibiti saiya ganta ya rago mata hanya ya"

kawota gida. A bakin titi a cikin mota fa ya gansu shine yayi mata wannan sharrin. Dake shima Wan iskane shi yasa tunaninshi ya tafi can.

Mu faWama kanmu gaskiya Babangida fa taceccen Wan duniya ne fa. Maigogul da Rakiya suma kuWi suke

"yima. Mu bi bayan ΄ar uwarmu kawai Sama"""

Kai Sama ya girgiza yace.

"""Wallahi hakane wai duk basu suka SalSanta rayuwarmu ba, sun haifemu sun watsar damu muna gantali"

a titi ba. Ai shi yasa ni aure ma zanyi ciniki harya faWa Lolo muje gidan naki sai mu tattauna acan ance

"kun sake gida ana muku gyara a wancan gidan naku."" Duk wannan bayanin da yake yi zaku ce faWa akeyi yanayi yana ihu da wauware hannaye."

Šunguma muka yi dukkanmu muka nufi gidana.

"A bakin titi wajen samun abun hawa muka tarar da su Sa'a suna tsaye kome suke jira ohon musu, sai"

wani kallon ™yama suke yi mana sabida dattin da Sama yayi. Niko a raina ina faWin ai kallon ™yamar auroni ya kusan zuwa ™arshe tare da Malama zamu zama zaurawa.

"Muna tsaye motar da zata Webesu ta fito suka shige,motarsu Baba Malam na binsu, sai ta su Malama"

"Babba, sai ta samarin gidan."

Mu kuma muna dai tsaye duk abin hawan da muka tare sai suce banan zasu yi ba. Daga ™arshe sai hawa

muka yi muka rage tafiyar muka sake shiga wani abun hawan.

Su Rakiya tun muna neman abun hawa suka zo suka wuce mu a mota Maigogul ke tu™in motar wata

haWaWWiyar mota ko kallonmu shi kan baiyi ba ga kiWa ya sakar musu Rakiya mandiya tana gaban mota.

Da sallama muka shiga gida.

MRS BUKHARI

IDAN KAYA YA GAJI...

GAMMO MA YA GAJI

LITTAFI NA BIYU

SHAFI NA TARA

BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ˜AMSHI

Assalamualaikum brkanku d warhaka hmmmm Wani kaya sai amale tohhh mata masu capacity matan

kwarai ga ramlex Mai kayan daa kayan buje akwae

Package na uwargida

Package na amarya

Package na mejego

Tsimi baure

Tsimi magarya

Hadin tattabara

Hadin kaxa

Hadin ciccibi

Gumban Madara

Gumban ridi

Gumban waken soya

Karin dandano

Xuman matsi

Manta uwa

Hadin mallaka

Hadin bita xaixai

Hadin tsuguno hmmmmm gareku mata akwae adashen gata duk sati 2k hadi Mai kyau xaayi muku duk

Mai bukata ga no 07069722234 ko 07044503983 snnn dn Neman Karin bayani ku tuntubi wnnn layukan



BABANGIDA:.

Yana bayan motar Mustapha a zaune idanunshi a rufe tun daga cikin kotun har suka fito motarsu ta

nausa titi bai buWe idanunshi ba.

Yana jin su Bashiru suna jinjina rashin mutuncin Sabuwa.

"""Ai ni wallahi Mustapha mamaki Sabuwa ta bani ban taSa tunanin da gaske take yi za'ayi zaman"

"kotunnan ba. Bura uba ni matata ta kaini kotu akan saki wallahi ko da bakin iyaye a kaina saina saketa. Babangida matsala Waya ce tasa bazai taSa iya sakin Sabuwa ba matsalar Malama Babba. Amman da dan bakin Baba Malam ne kaWai wallahi da tuni an saki mitsiyaciya ta kama gabanta muga wanne kamilinne zai fito ya aureta. Yarinyar da aka taimakama ji iyayenta fa da ΄an uwanta, ni naga uban harda mota"

"yazo arowa yayi amman dai ko? Kai amman Baban Sabuwa ya mugun iya wanka. """

Gabaki Waya suka fashe da dariya Mustapha yace.

"""Bashiru wallahi kai Wan iska ne. In ba arowa ba a ina zai samu Jeep ce fa ina yaga kuWin mallakar"

"wannan motar.? Ko da yake kawalai wallahi ™asar a hannunsu take"""

Wayar Babangida sai kuka take yi ya™i buWe idanunshi ji yake tamkar inya buWe idanunshi kanshi zai faWo.

Bashiru dake kusa dashi ne ya Wauki wayar ya kara a kunnenshi ganin wacce take kiran wayar.

"""Wallahi da baka Wauki wayarnan ba da kaji mummunan labari. Ina son ganinka da gaggawa wallahi awa"

Waya na baka in ba haka ba narantse da Allah ubanka zai kiraka ya sanar maka Wanka ya koma gidan kakanninshi. Lallai Babangida kaci abinci ka kuma yi wasa da tunanina. Allah Waya kenan sai ka yi dana

"sanin sanin Sumy a rayuwarka."""

Wayar a hands free take duk abokan Babangida suna ji. Babu shiri Babangida ya buWe idanunshi tare da

warce wayar.

"""Sumy ganinan zuwa yanzu kiyi ha™uri """

˜it ta kashe waya

"""Hmm bariki kenan. Ku da ba dan bariki ba Sumy ta isa ta faWa mun magana haka? Mustapha dan Allah"

"juya akalar motarnan zuwa gidan Sumy kasanta muguwar mahaukaciyace saita aikata abinda ta ambata."""

Mustapha yace.

"""Amman ya zaka yi da zaman meeting da za'ayi a gidanku kuma a kanka?"""

"Yama mance shaf amman ya zaiyi dole yaje ya soma kashe wutar da Sumy take son sake kunno mishi."""

"""Kai dai muje kawai ai ba zama zamu yi ba"""

Bashiru ya harareshi yace.

"""Kai da wa? Wallah ba zamu shiga ba sai dai kai kaWai ka shiga. Kaima da munji shiru sai mun kawo maka"

"Wauki mun kira motar ΄an kwana_kwana (fire service) """

"Dariya suka fashe dashi, shi kuma ya koma ya jingina bayanshi a kujerar motar."

Har suka isa ™ofar gidan suna surutu.

Wani yaron gidanne yace.

"""Laa ga baban Amiru ya dawo daga tafiya"""

Yana faWin haka ya ruga a guje. Babangida a karon farko daya soma nadamar ajjiye farka daya soma

kenan a rayuwarshi.

Mazan dake ™ofar gidan ya gaisar sunata kiranshi Baban Amiru.

"""HaWari kayi ashe Baban Amiru?"""

"Wani ya tambayeshi, kafin ya bashi amsa Amiru fito da tafiyarshi irin ta yara ya rugungune ™afafun"

ubanshi.

"""Wallahi kuwa Malam Hamza haWarin mota nayi"""

Nan suka shiga jajanta mishi dai. Hannun Amiru yaja suka shiga da sallama cikin gidan.

Matan gidan duk suna tsakar gida suna aikace_aikace.

Sannu kawai yayi musu ya shige ciki.

Sumy tana tsaye tana jijjiga dan bala'i da masifa hancinta har hunhuna yake yi.

"""Kai ka Wauka wasa nake yi Babangida, tsawon shekaru nawa ka ajjiyeni ka hana kowa ya raSeni, ka"

hanani kula kowa sai yanzu inji labarin ka cikace mata huWu?

"Wallahi Allah saika saki mace Waya dan samamun gurbi a gidanka, wallahi Allah saina rayu dakai rayuwa"

irinta sunnah ko kuma inje har gidanku in fallasa asirin ka in zaiyanama mahaifinka irin tsawon zamanin da muke tare da Irin duk abinda muka aikata kuma in bashi Amiru ya kiraka ya baka Wanka tunda tonon

"asirin kafi so. ³ar balaja'uce ni cikakka. Har bidiyonka saina fitar wallahi"""

Zama yayi babu shiri a kujera yana ta aikin kallonta tace wannan tace wancan.

"""Wata Waya tak na baka muyi aure a gama komai shine magana. Ko ayi haka ko kuma duniya ta sanka"""

"""Amman kinsan ko zan aureki sai kin koma gaban iyayenki kinyi istibiraWi na wata uku kafin muyi aure ko?"

"Kuma ki sani duk matar da zan saka itama dole sai tayi wata uku na idda kafin ta fita a sahun jerin matana, ko nayi saki in dai na mutu kafin ta gama idda dole za'ace matana huWu kuma zataci gado. To"

kinga batun muyi aure a wata Waya bai taso ba.

Sannan ke me yasa bakya bin komai a hankali ne kinata ihu so kike matan gidannan su gane irin zaman

"da muke yi ne?"""

Murmusawa tayi ta Waura ™afarta Waya a kan kujerar da yake zaune Wayar ™afar tana ™asa ta matso da

"fuskarta ta yadda suke jin Wumin numfashin juna"""

"""Wallahi baka isa kaimun wayo ba. Naji zanje gida in yi istibiraWi, sai dai ka sani a matar auren da mijinta"

ya saketa zanje. Iyayena bazan taSa bari su san Amiru shege bane. Ina gama wata ukuna sai kazo a Waura mana aure. Amman wallahi a ranar da zan soma ™irgen istibiraWi a ranar Waya daga cikin matanka zata soma ™irgen idda. In kuwa baka yadda ba in tona asirinka in saki videos Winka da su suka cika wayata in

"sakarma duniya a dauwama ana tsine maka"""

Mi™ewa yayi ya Waga mata hannu.

"""Ya'isheki Sumayya nace miki naji zan aureki. A cikin matana kafin wayewar gari zan sallami Waya. Gobe"

"ki shirya ki tafi garinku, ki bani adireshinki"""

Dariya Sumy ta saka. Kafin ma tayi magana wayar Babangida ta soma ruri Kawu Manga ke kiranshi

"anacan an taru za'ayi meeting uban gayyar baya nan."""

"""Assalamu alaikum Kawu ina hanya in sha Allah bada jimawa ba zanzo""."

Amsa sallamar tashi yayi tare da cewa.

"""To Babangida ka same ni a gidana acan zamu gudanar da meeting Win Malam fur ya™i mu shiga gidanshi."

"Kai atakaice dai ya aikata abinda baima kowa daWi ba. Kaga su Wawo suna ciki sai koke_koke suke yi"""

Rararasas gaban Babangida ya tattake yayi mummunar faWuwa. Yana son tambayar abinda ya faru yana

tsoron bugun zuchiya.

"""Shikenan gani nan zuwa"""

Da mugun sanyi yayi maganar tare da sauke wayar.

"""Ni zan tafi gobe ki tattara ki koma garin iyayenki. Duk halin da ake ciki zamu yi waya."""

Har yasa kai zai fita tace.

"""Babangida!"""

Cak ya tsaya ba tare daya ™ara ko ta™i Waya ba.

"""'wallahi Allah bazan yaudaru ba. Kafin in tafi goben sai ka kirani ka tabbatar mun da sakin Waya daga"

"cikin matanka, sannan ka turo mini da copy na sakin ta wayata. In kayi haka ni kuma sai in tafi"""

Baice mata komai ba ya fita. Da sauri ya faWa mota ba tare daya ce uffan ba. Idanunshi ya rufe kai da

zuchiyarshi suna harbawa da ™arfi.

Basu daWe ba suka iso ™ofar gidan Kawu Manga kamar yadda yace nan zasu kawo shi.

"""Shikenan ni anan zan wuni da yamma zan le™o majalisa"""

"Mustapha yace"""

"""Amman yaya kuka yi da Sumy Babangida. Karfa ta tona maka asirinka?"""

"""Mustapha in nazo majalisa da yamma zaku ji yadda akayi"""

Shiga cikin gidan Kawu Manga yayi da sallama. Babu kowa a tsakar gidan duk suna ciki kenan. Ga

takalma birjik a ™ofar falon Kawu Manga harda tashin muryoyin ΄an uwa.

Da sallama Ya shiga tare da neman waje ya zauna kusa da Wawo. Jikin kowa a mugun mace. Kawu

Manga yace.

"""To kai Wawo buWe mana taron namu da adda'a"""

Da adda'a ya buWe taron kafin Kawu Manga ya soma magana.

"""Abun dai babu daWi Malam ya yanke hukunci yayi tsauri gaskiya. Yanzu idan Sabuwa tayi nasara a"

"wannan shari'ar shikenan Malam ya rabu da Babba kenan? In kuwa da gaske yake yi ha™i™a bai yima Babba halacci ba, Malam bai kuma duba shekaru da ³a΄a ba. Ya kori Babangida daga gidanshi a baya, tsakanin Babangida da gidan mahaifinshi sai dai ya shiga ya gaishe da iyayenshi mata. To yanzu yayi mai Wungurungum yace ko mutuwa yayi

Please Login or Register in order to submit comment