You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaki ji ba. Dan kina aminiyatane

yake Waga miki ™afa fa. Ya zaki dinga aibatamun masoyina dan wula™anci ina fa sonshi

Amarya tace.

"""Uhm kan ku ake ji. Ni in kuna da sigari bani in zu™a ko zan samu sukuni yaushe da rabon a hadu"""

Sigari na ciro dukkanmu muka kunna ko wacce tana zu™a cikin ™warewa muna hirarmu.

Yanzu ke mijinki yana tunanin wata ta kirki ya auro haka ma surukanki basu san kurace da fatar akuya

"ba"""

"Ina gama maganar na zuba ™wayoyi a bakina na bisu da lemo"""

"""Uhm haka fa kafin ya tafi muka je gaishe da uwarshi. Harda ni™ab na saka yanata masha Allah. Ni kuma"

"na sane sabida tsaro wallahi. Amman fa auren ya isheni gashi ba wani jarumi bane, babu armashi abun sam. Yadda samarin waje suke suna da bambanci da mazajen aure fa. Shi wannan baifa iya wata soyayya ba ko sumba kala Waya rak ya iya. Baya Sata lokaci wajen yimun wasa burinshi biyan bu™atarshi gasu da"

"san kai in tasu bu™atar ta biya ke ko oho in faWa miki."""

A nan gidan muka wuni muna hirarmu da shaye_shayenmu sai bayan la'asar mukai mata sallama. Ni

bamma koma gida ba wajen madubala na wuce ita kuma ³ar Shuwa gari ta shiga abunta.

Ina dira cikin tabkeken kangon yaranshi dake murza tabar wiwi na siyarwa suka hau jinjina mun cikin

"girmamawa a matsayina na yarinyar ogansu. Kunji nace na dura ko? Kangon bashi da ™ofa, an fitar da ™ofar amman sai aka shafeta kuma. Wannan kangon a hannun wani bawan Allah wani mai kuWi ya siya, bai siya domin ya gina ba, ya siyane domin su madubala su zauna a ciki suna sana'arsu ana biyanshi kamisho. Da yawa yawan kangwayen da suka kasance matattarar ΄an shaye shaye in kun lura ba'a fiye ginewa ba, zaku iya sanin kangon da yafi shekara goma a matsayin kanko ko? Yawancinsu a kangon akeson a barsu. Shi yasa wannan aikin masu unguwannine daya kamata su dena barin kangwaye cikin unguwanninsu suna daWewa. Da zaran sunga kango ya daWe kamata yayi a tuntuSi mamallakin kangon domin aji daga gareshi. wallahi babu irin baWalar da ba'ayi babu irin Sarnar da ba'ayi, idan nace komai"

ina nufin komai. Kafin a lalata na waje ΄an cikin layi suke soma lalacewa.

"""Matar OGA ki shiga yana ciki sai dai suna ganawa ne da ba™i"""

Cewar Laka wanda ya kasance na amanar madubala.

"To Laka bari in shiga ba wani abu godiya nake yi """

Inayi ina cicciza tare da gyara zaman wu™ar dake ™uguna ina tafe irin ta ΄an daba mata.

Babban falon dake cikin kangon a ciki madubala yake duk wani ganawa da ba™inshi. Manyan mutane

"masu faWe aji, da wanda baki bazai ma iya faWinsu ba sabida mu™amin su. Ina zaman zamana ni Badiat"

azo a tattareni babu ruwana ehe

Babu sallama babu komai na shiga ina haWe hanya a mugun cake nake sosai.

Kujerar da Madubala yake kai na faWa idanuna a rufe nayi_nayi in buWesu na kasa maganganunsu daga

saman kaina nake jinsu.

"""Wai yane Alhaji ya da mugun kallone haka. Kayanane wannan ka kuma zuba mata na jiyamu eh"""

Figo yayi maganar yana Waga murya tare da daka tsawa.

"""Ayi mun afuwa ai bansan Madam dinka bace na zaci irin ΄an balaja'un da suke zuwa siyan kayan ™ari"

"ne."""

"Ni daga haka ban sake jin muryoyinsu ba, na dai ji sanda Madubala ya gyara mun kwanciyata, ya Wakko"

jaket dinshi ya lulluSemun ™afata dashi.

"Bani na samu kaina ba sai bayan isha na farka babu kowa a kangon, ga dai fitilar aci balbal nan a ajjiye a"

™asa.

Mi™ewa nayi na shige inda suka mayar banWaki fitsari nayi na zari ruwan leda ina yin alwala na jiyo

motsin durowar su Madubala cikin kangon.

Magariba da isha duka na haWa ina sallamewa muka haWa idanu da Madubala yayi shiru yanata kallona

amman sai naga jikinshi duk a mace a karon farko da naga karaya cikin idanunshi kenan.

Matsowa nayi kusa dashi ina shirin zama saiya Waurani a cinyarshi. ( kui ha™uri dan Allah yanayin

labarinne yazo da hakan)

"""Damuwata guda Waya kar muje zubar da cikinnan a samu matsalar da zata iya cutar mun da lafiyarki."

"Kinji sharaWin da Dr Hashim ya bayar. Šazu bayan mun rabu can asibitin naje na sameshi nayi mishi dukkan bayani.yaita wani mun faWa uwa ya samu Wanshi saida na taka mishi birki. Sabuwa anya ba zaki bar cikinnan ba? Ni dai ina sonki yaro kuma ina da tabbacin nawa ne, inma ba nawa bane dani a cikin"

"ubanshi. Muyi aurenmu kawai"""""

Lamo nayi a ™aton ™irjinshi inajin gabana na dokawa.

A_a a gaskiya bazan haihu a gaban iyayena ba. Sannan inma ina son in haihu Maigogul bazai yarda ba. Ko

"ka mance yadda kuka kwashe watannin baya ne? Yanzunma dafa ya sani da wani zancan akeyi. Kaini kawai a zubar in huta"""

Rungumeni yayi tsam a faffaWan ™irjinshi harda wani bubbuga mun bayana.

"Banci abinci ba madubala ina jin yinwa"""

Šago fuskata yayi muka kurama juna idanu ba™in bakinshi ya zura a nawa. (Afwan dan Allah)

Mun jima a wani yanayi shigowar Laka ne ya katse ma madubala hanzarin shi.

""", Kai Laka zo kaje ka karbo ma Sabuwa abinci maza. Sabuwa to me zaki ci?"""

Saida na jujjuya idanuna na sake rikirkita madubala kafin nace.

"Soyayyar taliya mai hanta, sai dafaffen ™wai da Fanta ŠaWWara"""

"""Kaza fa bakya so?"""

Uhm bana so waWanda ka kawo mun ma suna gida bansan ko Rakiya ta dafesu ba. Amman nasan tana

"gani tasan aikinka ne"""

"Nan da nan Laka ya siyo mun abinci, fargabar abinda kaje kazo sai muntsinar raina yake yi bai bani"

damar dai cin abincin yadda ya kamata ba. Madubala ya kama hannuna muka nufi katanga.

A wuyanshi ya saSani na Wale katangar na zauna. Ina kallo yayi tsalle ya kama bulo ya hauro ya same ni.

Saida yayi dube dube na marasa gaskiya kafin ya dira ni kuma ya taimaka mun na kuma hawa wuyanshi.

Tara a asibiti tayi mana a gaban Dr.

"""To tunda ka biya sai ta biyoni mu je ciki ko""?"

Madubala yayi mishi wani irin kallo.

"""Ahhh ban gane ta bika ku shiga ba. Ban gane ba anyi yamma da kare?"""

Dr cikin Laluma yake magana tare da cewa.

"""Dr Tabawa tana cikin Wakin ita zata yi mata kamar dai wancan. Abinda yasa nace da'ita tazo muje akwai"

"matane a ciki guda biyu suma cikin ake cire musu Waya matar aurece kaga bazai yiwu ka shiga ba"""

"""Sabida me shine kai zaka shiga? Kaga bari in faWa maka gaskiya sai dai mu shiga tare ko kuma mu jira a"

"gama musu su matan cikin"""

Yana ciccijewa ni dai nayi zugum.

"""Baka fahimta ba"""

Mi™ewa madubala yayi ya zaro wu™a daga ™ugunshi ganin wu™arnan Dr yayi saurin mi™ewa yace.

"""Muje ayi mata mu sallameki"""

˜wafa madubala yayi yace.

"""Da dai yafi. Sabuwa wuce muje"""

Haka madubala yasa Drn nan a gaba muka wuce Wakin wankin ciki inda a ciki likitocin da basa tsoron

Allah suke zubarma da ire irenmu ciki da matan auren da bansan dalilinsu na zubar da cikin sunna ba.

Dokace a ko wanne asibiti ba'a cire ciki sai da babban dalili wanda za'a iya rasa rai.

Amman a ko wanne asibiti kuma duk tsaronshi akwai ire_iren Dr da Dr Tabawa marasa tsoron Allah

masu cin amanar aikinsu

Haka na kwanta ina dam™e da hannun Madubala har aka gama duk abinda za'ayi.

Jinine ya soma Wibata nadai ji Madubala na ambaton sunana da ihu daga haka ban sake sanin a ina nake

"ba dama ga Allura anyi mini."""

MRS Buhari

Tsokana anan shine

Wannan littafin wallahi babban darasine a garemu

³ar uwa ki nutsu da yawa ki dinga bin komai daki daki zaki fi fahimta sabida kiyi al™alancin gaskiya da

gaskiya.

A iya wannan page Win akwai darrusa da yawa.

Wanne darasi kika ™aru dashi a cikin wannan page Win dan Allah?

FaWi ra'ayinki a Wakin sharhi. ³an uwa ku fito mu tattauna

Ni ina da abun faWa da yawa amman na zaSi magana akan yawan ibadar Madubala da duk iskancinshi

Sabuwa tace shi ya sata take sallah akan lokacinta.

IDAN KAYA YA GAJI...

GAMMO MA YA GAJI

LITTAFI NA BIYU

SHAFI NA GOMA SHA TARA

BADIAT IBRAHIM MRS BUHARI B4B GIDAN ˜AMSHI

https://chat.whatsapp.com/JmCasXpUuuT0J6dfLTWFNk?mode=ac_t

.

18066696785.

Hussaina Bello

HAJIYA KAYAN KITCHEN KIKE SO MASU SAU˜I DA KYAU. KO KUMA SARIN KAYAN KITCHEN KIKE SO KI

SOMA KIN RASA INA ZAKI SAMU AKAN FARASHIN DA KEMA ZAKI SAMU ALKHAIRI?

H@H AVAILABLE WHOLESALE AND RETAIL DUNIYA NE

MAZA TUNTUE HUSSSAINA BELLO KAI TSAYE A LAMBAR WAYARTA.

KO KUMA SHIGA CIKIN ZAURENTA DOMIN KASHE ˜WAR˜WATAR IDANU

Farkawa nayi naga ledar ™arin jini a hannuna Waure. Madubala na zaune a farar kujera fuskarshi saye da

takunkumin hanci (facemask) da suwaita mai hula ya sauke hularnan ko ™wayar idanun nashi ba'a gani.

Šakin nabi da ido ga marasa lafiya ratata a cikin Wakin.

"Madubala"""

A mugun razane ya Wago muka haWa idanu hawaye na bin gefen idanuna.

"""Sabuwa kar ki kuma kiran sunana nemana akeyi ruwa a jallo sabida ke nake garinnan su Laka duk"

"yarana suna Lagos. Nima ke nake jira Sabuwa ki farka inga yanayin jikinki bazan iya tafiya in barki ba, tare zan tafi dake"""

Fuskata ya shafa ya zame hular tashi baya kaWan ta yadda zan iya ganin idanshi.

"Me ka aikata kuma kisa?"""

Duk cikin raWa muke wannan Maganar.

Kai ya girgiza yace.

"""arnar da akasa muka aikata tafi kisa Sabuwa. To amman yaya zamu yi da rayuwarmu kullum ana"

"farautarmu. Iyayen da sukai silar zuwanmu duniya tun muna yara suka watsar damu a titi muna gararamba babu arabi babu boko, babu tarbiyya. Kullum a cikin zaginmu da aibatamu suke."

"Nifa mahaifiyata tun ina yaro take yawan tsine mun. Kinsan wacce kalmar tafi amfani dashi a kaina?"""

Kai na girgiza mishi dan bakina ya™i ko motsawa.

"""Kullum in nayi mata ba dai_dai ba sai tace mun matsiyaci, marar albarka, Wan iska shege."

Duk waWannan kalaman ga tasirin su a tattare dani shi yasa har gobe nake Waura alhalin lalacewana a

kanta. Duk Wan da yake son yayi albarka ai zai kula da mahaifiyarshi ko? To ni har ta mutu ban kula da'ita ba tunda na bar mata gidan ban koma ba har sai lokacin da ˜anwarta ta kirani tana faWa mun jikin Mama yayi tsamari kuma sai sambatun kiran sunana take yi.

Shine naje tsakanin uwa da Wanta sai Allah take naji tausayinta muka Wauketa muka Kaita asibiti a

hannuna ta cika tana saka mun albarka tare da cewa in yafe mata tasan bakinta ke yawo a rayuwata. Sai dai kash a lokacin daya fi dacewa ta kula da rayuwata a lokacin ta barma duniya taimun tarbiyya.

Sabuwa ina tuno lokacin da mahaifina yake ri™e hannuna muje masallaci sallah. Ina tuno lokacin da yake

sani a gaba ya bani hadda. Shafi biyu nake haddacewa kullum fa.

Tun daga mutuwar Mama na sake fanWarewa na bo™are rayuwar matasa masu shaye_shaye rayuwace

"abar tausayi, rayuwar guje_guje rayuwar shan muyagun ™wayoyi, rayuwar da duk kuWinka ba zaka iya"

"morarsu yadda ya dace ba. Rayuwar da al'umma kullun cikin tsine maka suke. Yanzu jibi inda nake kwana fa"""

Idanuna na runtse ganin shigowar jami'an tsaro cikin Wakin da nake bisa jagorancin Dr.

Madubala ga yan sanda ka gudu ka gudu.

Bai juyo ba yayi tsalle ya taka cikin wata marar lafiya ya haye taga ya fice.

"""Tunda kika sa ya gudu to ke zamu kama ΄ar iska marar mutunci"""

Cewar wani Wan doka mai ™aton ciki.

Ko Wigon hawaye babu a idanuna a wannan lokaci idanuna a runtse kawai suke na jiyo muryar madubala

kamar almara yana cewa.

"""Gani ku kamani kada ku cutar da'ita bata san komai ba, ni kuke nema ha™i™a na kamu"""

Da sauri na buWe idanuna ina yin™urin tashi amman wani irin azabar daya ratsa ™asana yasa dole na

koma.

"""Sabuwa sha kuruminki madubala naki ne har gaba da abada. Zanfa dawo ke dai ki kula da kanki kema"

"kinsan zan fito. """

Ina gani aka sama madubala an™wa a hannu.

"""Sabuwa zan fito karma ki damu kan ki."

Ki ri™e mun al™awarina da na fito zamu yi aure Sabuwa. Duk wanda kika kula kin ja masa.

"Kai kuma Dr ka rubuta ka aje nine ajalinka"""

"""My friend wuce mu tafi dalla kana Sata ma mutane lokaci."""

Wani Wan sanda ya daka mashi tsawa.

"Ina gani aka fita dashi daga cikin Wakin da nake kukan da nake yi sabida ciwo ko fitowa bayayi, ni dai"

tunda wata nurse tayi mun allura ban kuma farkawa ba sai zuwa washegari na farka naga Labbai da Uzairu zuchiyata a gefen gadona suna Wan hirarsu.

"""Uzairu zuchiyata maza kira Dr Lolo ta farka"""

Da sauri Uzairu zuchiyata ya fita. Labbai kuma hankalinta ya dawo gareni.

"""Sannu Lolo ashe dai abubbuwan da suka faru kenan? Shine kika kasa faWama Rakiya ko ni halin da kike"

"ciki. Shi yasa kwana biyunnan nake ganinki sukuku"""

"Yinwa nake ji Labbai ku bani abinci"""

Na faWa cikin muryar ciwo.

"""To wallahi kinga ruwan zafine kaWai muka tawo dashi in akwai kuWi a jikinki bayar a sawo kayan tea sai"

"in siyo miki abinci a cikin asibitin."""

Shigowar wata Nurse da Uzairu zuchiyata yasa bance komai ba.

Tazo ta gama gwaje_gwajenta da tambayoyinta ina bata amsa a hankali.

"""Kin samu kinci abinci ne?"

"""A_a yanzu ta farka fa. Amman itama yanzunnan take batun yinwar za'a nemo mata abinci"""

"""To shikenan ta soma sa ruwan tea a cikinta tukunna. Zuwa yamma in sha ALLAH zamu sallameta ma."

"Taci abincin zan kawo magani da zata haWiya."""

"Ficewa tayi, ni kuma na dubi Uzairu zuchiyata da Labbai inason in tambayesu da gaske an kama"

madubala? Amman yinwa ta hanani magana. Da hannu na nuna ma Labbai jakata ta Wakko ta zuge ta ciro kuWin dake ciki.

"""Uzairu zuchiyata ka fita ka siyo ma Sabuwa kayan tea da abinci a waje. Muma ka siyi abincin damu."

Dubu uku ta ™irga ta bashi ya fita. Yana fita ³ar Shuwa ta ™araso ita da ummansu.

"""Labbai yaya kuma jikin na Sabuwa, naga tayi muguwar rama tayi fiyau"""

Cewar Mama kenan.

"""Wallahi kuwa Mama kin ganta. Mu bamu san bata da lafiya ba Gaza ne yazo yana faWa mana wai yaji a"

bakin wasu ΄an shaye_shaye abokan faWansu Madubala suna faWin wai a wannan asibitin aka kama

"Madubala yana jinyar budurwarshi daya kawo aka zubarma da ciki. Shine muka garzayo muka tawo ashe kuwa da gaske suke. Allah sarki Madubala ance duk ragowar yaranshi suna hannu firzin za'a kaisu"""

³ar Shuwa tace.

"""Ance sauran suna Lagos sun riga da sun gudu. Shima Madubala ya tsayane sabida Sabuwa shi yasa har"

"suka iya kamashi"""

Haka Uzairu zuchiyata ya dawo ya samesu sunata mayar da ba'asi.

"Da yamma Rakiya da Hauwa, da Maigogul suka zo suka duba ni. Da rana su Adama da ragowar ΄an"

Wakinmu suma duk sunzo dubiya harma Aisha ta kawo lemo da Ayaba.

Da yamma lis aka sallameni muka koma gida naci gaba da jinya dan da ™yar nake zama da ™yar nake

"tashi, da kudina na dinga kulawa da kaina nice shiga ruwan zafi, nice shan farfesu, har yajin daddawa nasa Rakiya tayi mun."

³ar Shuwa kuwa kusan dawowa tayi baki Wayanta gidanmu da zama sabida yadda ta damu da ciwona.

Ni a jikina a lokacin inajin tamkar rayuwata ba zata kai ba. Harna soma warkewa ciwo ya dawo sabo jini

ya sake Sallemun ranga_ranga aka sake mayar dani wani asibitin da ban ba asibitin da Madubala ya kaini

"ba, su da muka je ™in karSata suka yi."

Likitoci suka sake jaddadama su Maigogul matsawar na sake yin™urin zubar da ciki zan iya rasa rayuwata

ma baki Waya.

"""A yanzu haka mahaifata bata da wani ™wari tana dab da lalacewa. A bincikenmu da muka gudanar"

bama lallai bane Sabuwa ta sake samun ciki ba. In kuwa ta samu zai kasance tasha wuya ainun ba lallai ta iya haihuwa da kanta ba.

"Sabida haka yana da kyan gaske a kiyaye sosai in dai kuna son rayuwarta kenan."""

Dr ne ya sanar da su Maigogul wannan jawabin.

Kwanana shida cib a asibiti aka sallamoni muka dawo gida.

Duk wata hidimar kuWi ni nayi ma kaina saida duk Wan abinda na tara ya ™are a neman lafiya ta.

Maigogul yana da kuWin amman ya™i yi mun sam. Dan a lokacin ya zama shahararren boka lamba Waya.

Kullum mata sunturi suke yi a gidanmu.

Ganin irin jinya da ramar da nayi yasa ΄an unguwa suke ta raWe_raWin cutar ™anjamau na ciyo.

"Ni ba jinyar tafi damuna ba rashin Madubala yafi damuna. Nayi suntirin gidan yari yafi sau goma, daga"

baya ne aka sanar mun ba a firzin Win jigawa aka kullesu ba. Garin aka bari dasu.

"Gaga_gaga abubbuwa sukaita tafiya da daWi babu WaWi, jikina ya warware sai dai rashin ™arfin jiki wanda"

shi kuma wannan sai a hankali.

"Yau da gagarumin tashin hankali muka tashi a cikin gidan namu har guda biyu a jejjere manya, banda"

™ananu wanda dama duk wayewar gari sai mun tashi da shi.

Duk da ma dai ai mu gidanmu ba'a rabo da fitintinu iri daban _daban.

Ina zaune a tsakar Wakinmu ina cin abinci a cikin robar ci ka yar wanda ³ar Shuwa ta kawo mun. Dan a

"halin yanzu bani ko kuWin saka kati abincin da zanci in ba dai su Sadiya bane suka fita suka kawo Wan ™walam da ma™ulashe da aka raba dani ba, sai dai in jira ΄ar Shuwa ta fita in ta dawo ta tawo mun da"

"abinda zanci, ai na faWa muku ta dawo gidanmu da zama duka."

³ar Shuwa tana gaban jakar kayana tana zaSen kayan da zata saka ta fice.

Labbai tana zaune tana ninkema Rakiya kayan data kwaso a wanki. Uzairu zuchiyata kuma sai waya yake

yi yana kashe muryarshi.

Kamar daga sama muka soma jiyo hayaniya da muryoyin maza a tsakar gida.

A guje dukkansu suka fito.

Ashe wai wata matace babbar mata Maigogul yaita damfararta kuWaWe ma™udai da sunan yana mata aiki.

Tun dai yana yaudararta harta soma ganeshi. Har wankan magani yaje gidanta yayi mata. Itace ta Wakko mishi ΄an sanda aka shigo har gida za'a kamashi. Ga mijinta sanannene sosai. Shima yace sai inda

™arfinshi ya ™are akan Maigogul.

"Anguwarmu, da gidanmu suka cika da al'umma masu gulma tabbas su suka fi yawa dan kab unguwarmu"

babu wanda yake ™aunar ΄an gidanmu.

"Muna gani, muna ji aka wuce da Maigogul Uzairu zuchiyata da Hauwa ne suka bi bayansu dan ganin ina"

za'a kaishi. Rakiya jin yaje gidan matar yayi mata wankan magani ta dinga zage_zage shine dalilin rashin binsu da bata yi ba. Tace a kashe shi uban kowa ya huta.

Mama ce taita bata ha™uri har tai shiru.

"""Rakiya ki dena wannan maganganun kina ™ara ba magauta damar suyi muku dariya ne. Tunda dai"

"Maigogul ba kisan kai yayi ba ai da sau™i damfara ce kawai. Ai ni na Wauka da gaske maganin yake bayarwa"""

"""Ina fa wani magani, muma da munyi tunanin hakan ashe kinga damfarace. Duk yadda suke son yi dashi"

"sai suyi ni bazan kashe kaina ba. Na gaji da ba™in ciki na gaji wallahi."""

"Sai kawai ta rushe da kuka tayi shigewarts Waki, hakan ya tilastama ΄an tsurku suka soma watsewa suma."

Mun shiga Waki duk munyi duru_duru ba'afi awa Waya ba wani yaron ma™otanmu ya shigo da mugun

gudu yake shaida mana anyi kame a kangon Gaza an kamasu duka ana tuhumarsu da manyan laifuka

harma an harbi Gaza a ™afarshi da ™afaWarshi da yayi yin™urin gudu.

Nan tashin hankali ya dawo sabo. Mu dai ranar duk muka shiga damuwa muka cure a Waki da ΄an

Wakinmu kab Winsu.

Hauwa ma da basu daWe da dawowa ba itama tana Waki da nata tawagar.

"""Ohh ni Rakiya miji a kulle Ša a kulle. Waini yaushe zan huta ne ni Rakiya?"""

Adama ce tace.

"""Ki dena wannan kukan Rakiya bashi da wani amfani mu dai yanzu menene mafita. Wacce hanyar zamu"

"bi Maigogul ya fito, shi kuma ya shiga ya fita Gaza ya fito?"""

Labbai tace.

"""Ga Uzairu zuchiyata dashi muka je shifa Maigogul cewa yayi muyi dawowarmu gida yana da manyan"

"mutane da zasu zo su yi belinshi. Yace dai in muka ga bai dawo ba akai mishi abinci. Gaza shi kanshi jama'ar da yake ma aiki zasu je su san yadda zaiyi ya fito."""

"Haka dai akaita jimantawa. Munafukan unguwa sukaita shigowa jaje, da Rakiya ta gaji duk wanda ya"

shigo jaje da zagi take rakashi kuma dai suma gulma ce kawai ke kawosu. Har ruwa da toka take watsowa.

Gaga_gaga yamma nayi irin dab magriba Rakiya ta zuba mana abincin da aka haWa kuWi aka dafa a

Wakinmu.

"""Lolo, da Uzairu zuchiyata da Adama ku kukai mishi abincin. Amman Adama yawan yajinnan da kike yi"

"yana yawa, anan Win ba daWi ba. In aurennan bazai yiwu ba ai gara a kaso shi musan kina gida kamar dai"

"sauran ™annenki."""

Adama ta karSi kwanon abincin.

"""Uhm Rakiya ni da auren mutuwa yayi da saina zuba ruwa a ™asa ai nasha. Kina jin ba™in mugu fa cewa"

yayi bazai taSa iya sakina ba. Yanzun wai aure zaiyi mu biyu daya ajjiyemu bai iya ciyar damu ba. Yara

wallahi wani sa'in sai dai su fita su yo bara su nemo abincin da zamu ci. Kab unguwarmu bashi ake bina

"Wakin nawa ya dawo babu komai a ciki ΄an bashi duk sun sabauta ni."""

"Baki Rakiya ta taSe kawai, muka dunguma muka kaima Maigogul abinci. Da magiya da fari da idanu suka"

yadda muka ga Maigogul ma.

"""Yauwa sannunku. Kar ku damu zan fito. Sai dai Alhajin da nake tunanin shi zai taimaka mun baya ™asar."

"Sai zuwa jibi zai turo wakilinshi da lauyanshi ayi duk wacce za'ayi. Su su Rakiya shine basu biyoku ba dake ba matan rufin asiri bane?"""

Adama tace.

"""A_a Maigogul kar ka wani ga lefinsu gaskiya"""

"Da™uwa yayi mata, ni dai ina jjingine a kanta ina kallo da jinsu."

"""Ku tafi ni zankoma ciki. Gaza ma muna nan tare dashi, amman ba sell dinmu Waya ba. Sai ku faWa ma ita"

"Rakiya. In kama uban bai kawo taba kama Šan ai ya kawota ko?"""

Šan sandane ya katseshi da cewa.

"""Lokacin ka ya cika"""

A faWace Maigogul yace.

"""Da ya cika, da kar ya cika kana ji na sallamesu ai ko? Tunda na shigo gidannan na lura ka tsaneni."""

Mu dai da wannan muka dawo gida muka zuba idanu muga yadda abun zai kasance.

Wasa gaske Maigogul har kwana na huWu bai dawo gida ba. Sau biyu rak aka kai mishi abinci. Sauran

kwana biyu duk cikinmu babu wacce ta bayar da kuWin da za'ayi girki balle a zuba mishi. Mu bai renemu

da tausayi ba balle mu ji ™anshi.

Dama munfi gane ko wacce ta zari kwano ta siyo abinda ranta yake so. Wacce bata da kuWi kuwa sai dai

"ta sha ruwa ta kwanta, ko kuma ta fita tasan yaya zata samu abinci."

"Dama da ina dashine ni dole zan siya in kai mishi, to ban fara fita ba, babu samarin ko Waya nima a jikin"

³ar Shuwa na jingina.

A kwana na huWunne Rakiya ta rarrafa da magriba taje ta ganosu shi da Gaza duka.

Itace ta dawo mana da labarin kotu za'a tura Maigogul harma an turasu jibi za'a soma zaman kotu. Su

Gaza kuma ashe har an yi zaman kotu na farko suna ma gidan yari a tsare har zuwa yadda Shari'a zata kaya.

Ranar shiga kotun su Maigogul mu dai dukka babu wacce taje sabgogi duk yayi ma kowa yawa. Ni dai

ban soma fita ba amman dai na warware sosai sai rama.

Da wanki muka tashi ni da Yar Shuwa duk kayan namu babu wanki ta gama sakesu ta jibgesu da datti.

"Ina kewar sigari sosai. Bari kiga in le™a in aiki yaro ya siyo mun na Wan zu™a ko zan ji sanyi"""

Dariya ³ar Shuwa ta saka tana Wauraya tace.

"""˜awata lallai fa kin warke ya kamata partyn jibi mu je tare tunda har kina son komawa kan sigari"""

Dariyar nima nayi mata kana nace.

Inaso nima inje partyn ai an daWe ba'a haWu ba. Talaucinnan ya gama isata na gaji. Ni sababbin kaya nake

"son in sai mana. Ke in kika samu kuWi bakya ™ara mana suturu, sai dai aci banza aci hofi. Jibi kayan namu"

"duk sun soma shan ruwa"""

Matsowa tayi tace.

"""Kin dai ha™ura da Madubala kenan tunda kinga babu sarki sai Allah? Shi dai an yanke mishi hukuncin"

"kisa"""

Dole in ha™ura tunda na ha™ura da KHALID babu Wa namijin da bazan iya ha™ura dashi ba. Akan

"Madubala ai bazan tsayar da rayuwata ba. Yanzu kina ganin da kuWaWena duk na Wauki nauyin lalurata. Abinci ba dan kina bani ba da tuni na koma ruwa da ciwon nawa"""

Muna cikin wannan hirar su Rakiya suka shigo ita da Hauwa sunata jimami.

"Rakiya meya faru wai a kotunne?"""

"Saida ta ja turmi ta zauna, tare da cire mayafinta ta yaSa a igiya kana tace."

"""Sai nan da sati biyu za'a zauna zaman ™arshe. Maigogul dai yana firzin an ajjiyeshi kafin wannan lokacin."

Lauyoyin da aka Waukar mai sun so a bada belinshi abun yaci tura.

"Ke bari kiga in shiga daga ciki in huta. Yaran duk sun fice a gidan kenan?"""

"E sun firfita"""

Na bata amsa jikina a sanyaye.

Anyi haka washegari da yamma sai ga Maigogul ya shigo cikin gida babu ko sallama. Kusan dukkanmu

muna gida a tsakar gida anata musu da ihu duk mun cika gidan.

"""Aikin kenan. Gayyar tsintsuya babu shara. Gaku dai rigis Amman yawanku bai amfaneni da komai ba. A"

rasa wacce take da saurayi mai wani babban mu™amin da zai iya tsamoni. Kuke nan kula talakawa

"kaiconku"""

"""Kaiconka dai dan wallahi

Please Login or Register in order to submit comment