You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

komai ba.

"""Sabuwa nayi miki al™awarin zan baki farin ciki a aurenmu irin farin cikin da tuni kika yanke ™auna da"

"samun shi. KHALID ne kaWai yasan mutuncinki."""

Šagowa nayi na dubeshi ha™i™a ga dai soyayya ™arara nakan iya karantata daga ™wayar idanun Khalid a

zahirin gaskiya zuchiyata ko kusa ta™i gasgata Khalid da maganganunshi. Taya zai ga darajata bayan ni dashi muke ™etare katangar Babangida. In mu kai Aure bazai taSa samun nutsuwa da yarda dani ba wannan kam ya shuWe har gaba da abada in dai a wajen Khalid ne. Jibi irin zargi da ukubar da nake sha da Babangida yanzu haka akan zargi. Ina kuma ga na auri Khalid kai ina da sakel. Ajjiyar zuchiya na sauke

tare da cewa.

Allah yasa mu dace kai dai ka taya ni da adda'a bari dai auren nawa ya ™are tukunna. Amman inaso mu

"nesanta da juna sosai ni nayi maka al™awarin da zaran aurena ya mutu Khalid zan nemoka da kaina"""

Na faWa tare da sauke kaina ™asa.

Acan ™asan zuchiyata ina son Khalid so mai tsanani fa ina dannewane domin aure da kuma darajar

³a΄ana.

"""Kina nufin ba zaki sanar dani inda kike ba, kuma ba zaki bani number wayarki ba ko me kike nufi."

"Sabuwa anya ba yaudarata kike son yi ba kuwa?"""

"Babu yaudara kasanni farin sani Khalid ni kaifi Waya ce. Da kaina zan nemo ka, ina son samun nutsuwar"

"da zata bani damar mallakar kaina domin in samu ™arfin kashe wutar dake gabanane, mutuwar auren"

"yafi komai wuya ka fahimceni dan ALLAH """

Hannuna ya saka tare da jingina bayanshi a kujerar da yake zaune ya lumshe idanunshi.

"Gilashin motar na sauke na yar da sigarin dake hannuna na rufe gilashin, kafin na ba Khalid dukkan"

nutsuwata

Ha™uri na share fin minti biyar ina bashi kafin ya buWe idanunshi da sukai ja ya zuba mun su.

"""Naji kuma na amince, ki ri™e amanar zuchiyar da ta daWe da yin sabo da ri™onki. Ki bani account number"

"ki lokaci zuwa lokaci zan dinga tura miki kuWin da zaki dinga bu™atunki."""

"Dole na bashi account number na sannan ya harba motar zuwa titi, katafaren shagon siyayya ya shiga"

"dani ya sai mun kayan ma™ulashe kafin ya sauke ni a bakin layinnu tare da sake jaddadamun girman al™awarin dana Waukarma kaina, da wannan mukai sallama da Khalid. Kai tsaye gidan da su Adama suka kama na nufa, Labbai na hango a bakin ™ofar Wakin nasu da ™aramin risho tana shirin kunnawa, ganina"

yasa ta washe bakinta.

"""Ah Lolo kece da safe haka? Yanzu kuwa Maigogul ya fita daga gidannan baku haWu ba?"""

Ina dariyar ya™e wanda yafi kuka ciwo nace.

"Bamu haWu ba kuwa"""

"Shigewa ciki mu ka yi, Adama na kwance a tabarma sai shantaka bacci take yi."

Hiye ba shakka su Adama an samu waje bacci ma take yi har yanzu bata samu damar tashi ba. Da ace a

"gidanta ne ai da yanzu tana bakin murhu"""

Dariya muka saka ni da Labbai. Dariyar ce tasa Adama ta buWe idanunta. Yamutse fuska tayi ta mi™e tana

"tsaki, cikin muryar bacci tace."

"""Lolo yaushe kika zo?"""

Kallon fuskarta nayi dama dama da kwalliya nace.

"Naga fuskarki duk kwalliya ta dame"""

Dariya tayi tace.

"""Bari in wanko baki inzo ki sha labari ni dai nayi kamu ALLAH."""

Bakina a sake har Adama ta fita. Labbai kuwa tana kwance a kasa tana dariyar mugunta dama halinta ne

duk yadda akayi ba kamun arziki Adama tayi ba.

Sai da Labbai ta gama dariyarta harda birgima kana tace.

"""Kafin tazo baki labarin bari in dafo mana taliyar yara, kinga muna ci muna hirar abun zaifi daWi."""

"Wata ™atuwar leda naga labbai ta buWe ta ciro indomi manya uku, da ™wai uku. Ni dai mamaki ne ya"

gama isata nama rasa tacewa.

Wayar Adama ce ta shiga ruri tana gefe na Wakko wayar nayi na duba naga an rubuta Alhaji Bilya. Kai na

"gyaWa kawai na ajjiye mata wayarta na ciro ice cream a ledar siyayyana dana Wakko babban roba dama dan mu sha dasu Labbai ne, Rakiya ma na dakko mata ™aramar roba da meat pie babba nasan tana son meat pie aikinta kenan ba da sallahun a tawo mata dashi. Adama ce ta shigo da sallama tana ganin"

kayan daWi ta shiga washe bakinta. 5 alive ta Wauka ta Salle ta sha_ta sha kafin ta sauke.

"""Baki ji sanyin shi ba har maWigata wallahi kai Lolo Allah yasa a wannan karon mu shiga gidan da zamu"

"huta."""

Kafin in bata amsa Labbai ta shigo da faranti sha™e da indomi da daddaffen ™wai. Wayar Adama ce ta

"shiga ruri da sauri ta Wakko, da taga sunan sai naga ta washe bakinta. Labbai kuma nan ta shiga dariyar"

"iskanci. Nima dai a wannan karon dariyar nake yi duk da bansan meke faruwa ba, amman kamar bazawari Adama tayi."

Tsahare ce ta shigo da sallamarta.

Ganin kayan ciye_ciye yasa ta hau washe baki.

"""Na dawo a daidai ashe a daidai. Lolo ashe kinzo?"""

"Kaga manya manyan zawarawa ban jima da zuwa ba. Fita kika yi ne?"""

"""Wallahi a gidan ™awata na kwana ta haihu mijinta baya nan shine ma ya nemi alfarman inje in zauna"

"da'ita. Yanzun ma kaya nazo zan Wiba zuwa bayan suna zan dawo"""

Adama fa tana gefe tana waya wallahi sabida ™asa da tayi da muryarta mu kammu bama iya jin abinda

take cewa. Tana gama wayar muka saki shewa tamkar bamu da wata matsala a rayuwa. Alhalin ko wacce cikinmu da damuwa ™unshe a ranta. Amman da zaran an haWu an zauna saimu wanke ma kanmu da kanmu ba™in ciki.

Muna cin abinci Adama tace.

"""Lolo sabon bazawari nayi mai malum malum shine Labbai ta saka shi a gaba shegiya da dariya tun jiya"

"da dadare. Ma'u ce tazo gari ta Waukeni muka je bikin ma'aikatan kamfaninsu. To acan muka haWu dashi. Ba™auye ne amman wallahi akwai kuWi, kuma kamar lusari ne kashe ma mace kuWi bai fiye damunshi ba."""

Labbai tana gama haWiye ™wan data saka a baki tace.

"""Wai ke kinga malum_malum Winshi zata yi yadi goma, gashi ™ato sosai gashi da tsayi. Lolo ™afarshi duk"

"faso, amman ke da ganin motarshi wallahi kuWin akwaisu, amman a fatarshi babu wani halamun hutu"""

Dariya mu ka yi dukkanmi.

"Ahh Adama kice koma ta kama babban kifi? Amman ai baki gama idda ba yana da kyau ki sanar mishi"""

Saida Adama ta tsotse romon hannunta kana tace.

"""Na sanar dashi tun jiya. Ya kuma ce zai jirani in gama iddata sai yazo mu sasanta kanmu."""

Yauwa hakan yafi. Amman gaskiya ki aureshi da zaran dai kin gama idda kar mahassada su shiga su fita.

"Kinsan da yazo Waya biyu layinnan ba lallai yazo na uku ba magulmatan layinnan zasu korar miki shi"""

"""Ke dai bari Lolo. Duk da naji yana cewa ba'a cikin garin dutse iyalanshi suke ba, bazan ™i aurenshi ba"

tunda yana da kuWi. Dama na rantse na maya da in kuma auren wahala gara in zauna inta zawarci. Ke

"tunda wannan babban kifi yazo hannu Lolo ai babu sanya. Zan Wanje ma wajen wani malami ya Wan rubuta mun fahami, ko ke zaki rubuta mun ne Lolo?"""

Dariya kawai nayi dan nasan tsokanata take yi sarai. Rakiya ce ta buWe labulen Wakin.

"""Babu shakka Lolo ashe da gaske ke Win Uzairu Zuchiyata ya gani Win. Wato yanzu sai dai ki wuce gida"

"kizo nan ki baje duk abinda kika kawo kuci anan ko? Yayi kyau"""

Shigowa tayi ta nemi waje ta zauna.

Ba haka bane Rakiya yanzu zuwana ban jima ba. Kuma kema ga naki tsaraban da ban na ware miki.

"Indomi kuma nasu Labbai ne suka dafa mana"""

Mi™a mata ΄ar ledar ice cream da meat pie Winta nayi ta karSe tana washe bakinta.

"""Allah yayi albarka. Jibi ™o™arin duk da Babangida yake yi a kanki amman a haka kike son. Tozarta kanki."

"Yanzu jibi Adama goWai goWai da'ita tsofai_tsofai tana zawarci, banda sauran ™annenki. Abidan Hauwa ma mijin ya sakota yanzunnan da Wanyen goyo yanzu isowarta tun jiya suke cin tafiya a mota. Wannan bai isheki ba a_a sai kin kaso aurenki kema kinzo kin jeru dasu kuci gaba da Wakko mana maganar da"

kuka saba.

"Ni dai bance komai ba, gabaki Waya farin cikin ma da nake ciki sai naji ya gushe mun. Babu shiri na mi™e"

nayi musu sallama.

"""Kifi ruwa gudu dan ubanki. Yara babu da wacce ka isa, babu dama ai muku magana sai ku hau dokin"

"zuchiya. In kinso kada ki sake zuwa har mahadi ya bayyana ja'irar kawai."""

Harna fita Rakiya ina jiyo muryarta tana zagina.

Kai tsaye na hau abun hawa ya mayar dani gida.

"Ina shiga uwarWakina naga kaya a zuzzube halamun an yi mun bincike, ga takaddu baja_baja a gadone, a"

™asane.

"Cikin takaici da tunanin to waye ya buWe mun Waki na shiga gyara kayana ina tsaki, duk da zuchiyata na"

"zargin Babangida ne. Na fi awa biyu ina gyara wardrobe dan kusan dukka kayana gogaggu ninkakku an zubo mun dasu, haka na gyara komai na mayar da komai muhallinshi, kana na fito kitchen dan in gyara kwanuka."

"Yauwa Maman Sa'idu dan ALLAH waye kika ga ya buWe mun ™ofa?"""

Na tambayi Maman Sa'idu dake shanyar kayan yara.

"""Babansu Mardiyya ne ya shiga. In banda abinki waye zai shigar miki. Ko da yake abu da me kishiyoyi"""

"Murmushi kawai nayi mata, dan a zahiri da wasa tayi maganar, amman ni nasan har cikin ranta tayi"

maganar.

"""Ab maman Mardiyya ashe kuma Babansu Mardiyya ya saki Maman Usama? Kaik abu baiyi daWi ba"

"Wazunnan ta fita daga gidannan da kaya ni™i_ni™i ita da wata ™awarta"""

"Wani irin mamakine ya kamani, bawai na sakin ba tunda ba abu bane sabo a wajen wanda yayi sakin ba."

Mamakin da nake yi wani auren Babangida zai sake jajiSowa a hakan a gidan haya ga kudin da yake

"ta™ama dashi babu? Wato maza masu auri saki tamkar masu aljanu suke, da zaran aljanin saki ya hau"

kansu to fa sai sunyi suke jin daWi. Haka da zaran aljanin ™arin aure ya hau kansu to sai sun ™aro.

"Hmm Allah sarki, Allah yasa hakan ya zame mata alkhairi. In kuma da sauran shan ruwan auren nasu"

"Allah ya daidaita tsakaninsu"""

Ina gama faWin haka na koma ciki nayi kwanciyata a gado ™wa™walwata ta shiga tariyomun haWuwata ta

farko da Babangida haWuwar da har gaban abada bazan dena dana saninta ba. Ranar data zame mun ranar tarihin da bazai taSa ciruwa a cikin tarihin rayuwata ba. Ajjiyar zuchiya na sauke tareda share hawayen da suka gangaro daga guraben idanuna.

Mrs Bukhari

Sai mun tara gobe

IDAN KAYA YA GAJI...

GAMMO MA YA GAJI

LITTAFI NA BIYU

SHAFI NA GOMA SHA BIYU

BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ˜AMSHI

GIDAN SA'A:.

Da sallama ³ar Shuwa ta shiga gidan Sa'a ta taddata a bakin pampo kan kujerar tsugunno ga wanki a

gabanta cikin ba™in bawo. Amman a lokacin data shiga waya take yi sai salati take rabkawa.

Jarka ³ar Shuwa ta ja kiyy ta samu waje ta zauna kusa da Sa'a.

"""Kai amman Babangida kwai Wan banza. Yanzu dan ALLAH in Baba Malam yaji wannan maganar me"

zamu ce mishi. Ace Babangida tunda dai ya soma girma yake jaye_jayen magana?

"Allah ya kyauta gobe dai zan shigo yau da wanki na tashi mun tara kayan wanki da yawa"""

Kashe wayar tayi tana tsaki.

"""Lafiya Yaya Sa'a ake aibata mana miji me kuma yayi?"""

Baki ta taSe tare da cewa.

"""Hmm ke dai ki bari kawai Abokiyar zamanki Hamida Babangida fa ya saka wai jiya da daddare. Yanzu ya"

"dace kenan abinda yayi fisabilillahi yana ganin anata tunanin yaya za'ayi da batun kotu da Sabuwa ta dokashi, ga batun karayar arzikinshi hakan duk bai isheshi ba. Yanzu nan da wasu watannin in dai Babangida ne sai dai kuji ana shigo da kayan Amarya, koma yayi a Soye kamar yadda ya auro waccan"

"marar kunyar Amaryar taku."""

Shiru ³ar Shuwa tayi tana tunanin dalilin da yasa Babangida ya kwana a Wakinta jiya kenan alhalin ba

kwananta bane. Wani farin ciki taji a zuchiyarta marar misaltuwa a zahiri kuma sai ta nuna ma Yaya Sa'a abun ya taSa ta sosai.

Amman ita bama Hamida bace a gabanta ba dan ta riga da tasan tafi karfinta.

"""Hmm ni dama Sabuwa ya saka daya fi ai. Kinsan Yaya Sa'a kamar Sabuwa ta asirce Abban Fatima kuwa?"

"To kinga yama dawo yana mana rabon kwana da'ita matar da take bin maza kalan yaje ya kwaso cuta ya saka mana. Yanzu ma haka tare fa muka fito dashi muka sameta a hanya zata tafi yawon barbaWanta data saba, shine ya tareta ta faWa mai inda zata je ta™i fur a titi ta tafi ta barmu shine ya tari AcaSa ya bita shi, ni kuma nayo nan. ˜addarace dai tasa kuka haWa iri da su Sabuwa. Mahaifinta fa kullum zaki ganshi da mata, har cikin gidansu yake kawo ajjiyar karuwai duk wani iskancin duniya ya ™are a gidansu"

"Sabuwa, ai gara ya saketa ya huta da wannan tozarcin"""

Wawuyar ajjiyar zuchiya Sa'a ta sauke a duniya babu wacce ta tsana sama da Sabuwa. Kuma tana mai

ba™in cikin tseratar mata da aurenta da Baba Malam yake son yayi. Da ba dan ya riga ya haWe igiyar auren Sabuwa data Malama Babba ba ai da tuni wani zancan akeyi ba wannan ba.

"""Hmm ke dai ki bari. Ai kinsan Baba malam yace in ya saketa to tsinuwace zata bishi kinji dalilin da yasa"

Sabuwa ta samu waje ta mi™e take tatala rashin mutuncinta. Kuma ai kema kinsan in mijinku ya saketa a bakacin auren Malama babba ne kinsan komai ai. Babangida kuwa da kike ganin yana lallaSata so yake ta janye ™arar data shigar gudan kada tayi nasara tsinuwar Baba Malam ta bishi. Kinsan akan wannan

maganar Malam Baba ya hana ma Babangida shiga cikin gida kwata_kwata?

Ai Sabuwa sai dai muce Allah ya tsine mata albarka. In sha ALLAH sai ta wula™anya a gidan Babangida

"muguwa azzaluma"""

Ajjiyar zuchiya ³ar Shuwa ta sauke a ranta take furta.

"""Kenan babu ta yadda Babangida zai saki Sabuwa kenan, tare zasu ™are rayuwarsu?"

Ina wallahi ko tsirara zanyi yawo sai na karaWe bokayen Dutse da kewayenta na farra™a Babangida da

"Sabuwa, so nake yai mata korar kare. Dan nasan babu wanda zai aureta muddin ta bar gidan Babangida."

"Ga ™annenta da yayunta nanma duk an sakosu suna gaban iyayensu"""

"""Gaskiya in yana neman albarka bazai iya sakinta ba. To amman Yaya Sa'a in al™ali yasa dole ya saketa"

"fa?"" ³ar Shuwa ta kafe ta da idanu."

"""Hakanma in sha ALLAH bazai faru ba. Kinsan Allah ai in tasan wata bata san wata ba. Wannan shari'ar"

"data jajiSo da bakinta zata janye in sha ALLAH. Bata isa taci nasara ba, ba wai dan muna sonta ba"""

"Haka sukaita tattaunawa ³ar Shuwa na taya Sa'a wanki har suka gama, suka kuma runtuma zuwa kitchen"

itace da girki.

"""Ni Banga Anty Nasiba ba yau tunda nazo. Nasan kuma ba mai zaman Waki bace"""

Baki Sa'a ta taSe.

"""Tana asibiti mahaifinta ne babu lafiya shine take jinyarshi"""

³ar Shuwa tace.

"""Ah kice ke kaWaice da gida kiyi yadda kike so. Kishiya ko masifa"""

Sa'a an sosa mata inda yake mata ™ai™ayi tace.

"""Ai kuwa ji nayi kamar kada ta dawo gidan. Ai da ™yar fa ta yarda ta tafi jinyar. Kinsanta da maganar son"

turaka. Saida yatta tazo gidannan tayi mata tatas shine ta haWa kayanta ta tafi. Kuma fa mai gidan kullum sai ya je asibitin ya kai musu garar arziki. Ai kishiya komai zaman lafiyan da kuke yi to ta ciki kawai na ciki. Kinga matarnan ba ™aunata take yi ba. Kishi dai_kishi dai da taga sutura a jikina ko jikin yara ta soma zafin zuchiya kenan tai ta tuhumarshi shi kuma yana mata rantse_rantse namiji_namiji sai dai a barsu da

"halinsu kawai."""

Haka har suka gama girkinnan bakinsu bai huta ba sai aibata abokan zamansu gami da yi musu ™age suke

yi.

Babangida:.

Ranshi a mufun haWe ya shiga ya gurfana a ™asa a gaban Malama Babba.

Kawu Manga ya nemi waje a saman kujera .

"""Yaya kuma akayi Malama irin wannan kiran gaggawa ya sake yo wata tsiyar ko?"""

"""Ina kwana Kawu?"""

Cewar Hamida wacce da ganinta taci kuka ta ™oshi.

"""Lafiya lau ya kwanan yaran, da abokan zaman naki?"""

"""Duk muna lafiya"""

"""To madallah"""

Babangida ne ya gaishe da Malama Babba tace.

"""Ni ban kiraka dan ka gaisheni ba. Ai burinka bai wuce hawan jini ya kasheni ka huta ba. Yanzu ana cikin"

"damuwowi kala_kala me yarinyarnan tayi maka daka saketa?"""

Kawu Manga ya shiga salati harda cire hularshi.

"""Saki kuma? Yaro sai kace mai aljanu. Shin Babangida lafiyarka ™alau kuwa nace kana da hankali da zaka"

"saki yarinyar mutane a irin wannan lokacin duk mutunci da karamcin iyayenta. Tukunna ma mai tayi maka da har ka saketa?"""

Shiru babu amsa ya™i magana fur. Kawu Manga yace.

"""Ke hamida faWa mana abinda ya jawo sakin. Sannan saki nawa yayi miki?"""

Nan ta labarta musu iyakar abinda tasan ya haWasu. Kawu Manga yace.

"""Babangida ka mayar da'ita Wakinta yanzu kaji na faWa maka. Mu birne maganarnan tun kafin ta tsallake"

"gidannan."""

Malama Babba tace.

"""Zancan banza zancan wofi kenan ma. Ai ya zame mishi dole ya maidata Wakinta. Sabida kai saki baya"

"baka wahala akan shinkafa saika saki mace"""

Dundu ta sakar mishi a gadon bayanshi na ba™in ciki.

"""Ashsha abi komai a hankali Malama duka da Waga murya ba naki bane. Ke ba ishasshiyar lafiya ba. Zai"

mayar da'ita ma kiyi ha™uri.

"Kai Babangida"""

"Ya ambaci sunanshi, sai lokacin ya Wago kanshi ya dubi kawu Manga."

Kafin Kawu Manga yace wani abu wayarshi ta shiga ruri Mustapha ke kiranshi.

"""Zaka iya Waga wayar taka in tana da mahimmanci"""

"""A_a Kawu Manga babu damuwa Mustapha ne, inna fita zan kirashi"""

"""To to ai shikenan. Yarinyarnan kayi ha™uri ka dawo da'ita Wakinta. Ka kuma ba mahaifiyarka ha™uri."""

"Shiru ya kuma yi, ga Mustapha ya dameshi da kira sai saka wayar a silet yayi. Can dai yace."

"""Kuyi ha™uri bazan iya ci gaba da zaman aure da'ita bane, sabida wani dalilin da fasuwarshi dani daku"

"bazai mana dadi ba. Malama Babba kiyi ha™uri ba ™in bin umarninki nayi ba. Dole ce tasa nayi sakin akan dalili mai ™arfi. Kuyi ha™uri bakin al™alami ya riga da ya bushe"""

"Ya ja baki yayi shiru. Malama Babba ma ta rasa abinda zata ce, domin bata taSa tunanin zata bashi"

umarni ya ™etare ba. Tasan yana bakin ™okarinshi wajen bin umarninta. Abinka da Ša da uwa kuma Wan dama yafi soyuwa a zuchiya fiye da sauran. A take Malama Babba taima Wanta uzuri da wannan kalmar

ta malam bahaushe da yake cewa mai Waki shi yasan inda yake yi mishi yoyyo.

"""To shikenan Babangida dani da gyatunarka ba zamu matsa maka ba akan dole sai ka dawo sa matarka"

"ba. Domin babu dole a cikin aure. Ke hamida sai ki daure ki koma Wakinki ki yi idda in iddarki ta cika Allah bashi saiki tafi in rakaki har garinku"""

Hamida da jin haka ta mi™e rai a Sace diyar ta mi™ar tsaye ta Waura akan cinyar Malama Babba ta suri

akwatinta.

"""Ga yaranku nan ni dakai har abada. Kuma ka sani zakuntata da kayi in sha ALLAH sai surukanka kaima"

"sun WanWana maka ba™in cikin da kake WanWanama naka surukan. Ke kuma kici gaba da biye mishi in sha ALLAH sai yayi ajalinki"""

A zafafe Babangida ya mi™e zaiyi kan Hamida Malama Babba da Kawu Manga suka dakatar dashi.

"""Šan kuka mai zama uwarshi jifa. Babangida kabi duniya a sannu. Kai kaji kalaman da yarinyarnan ta"

"faWa ko? Kayi ™o™ari ka gyara Wabi'unka ina ji maka tsoron ka samu yaro irinka, wallahi duniya ba zatai ma daWin zama ba.Jibi a sanadinka kasa na bawo gidam aurena na dawo hannun Šana Malam da ranshi da lafiyarshi ya koreni a gidanshi, inta kama ma rabuwa dani zaiyi kuma duk sanadin jaye_jayen maganarka. Bazan maka baki ba abun sai yayi maka yawa. Allah ya sani ina sonka Babangida shi yasa"

kake wahalar dani.

Jibi yarinya ™arama da matarka ta dire mun a cinyata. Ga Hauwa tsohuwar matarka yau Winnan ta kawo

"Wanka ta dan™ama Malam. Shi kuma malam ya kira kudidi ya bata, ga Mufida Hamida ta dure mun ga"

Usama.

Kukane yaci ™arfinta Kawu Manga yace.

"""A dai taru ayi ha™uri dai."

Yara kuma shi Usama ya tafi dashi ya ba matanshi. Ita kuma wannan zan ba mata a cikin gida suci gaba

"da ri™onta, ga Mariya na da Wiya sa'arta kinga ta samu ™awa."

"Kai Babangida kama hannun yaronnan kuje, mutumin kawai."""

Babu shiri ya fice yana sharce zufar data tsattsafo a saman goshinshi.

Sumy ta gama dashi ta dalilinta yau yana ji yana ganin Malama Babba na zubar da hawaye amman bashi

da hannun share mata. Duk da wannan kukan daWine akan fasuwar ™wan da yake son yaga ya rayu ba

"tare da fashewa ba. Abinda Babangida ya mance shine shin za'a dauwama ana Soye ma Amir asalinshi ne, ko za'a dauwama ana tafiya a mazaunin Amir agolane da Sumy ta tawo dashi gidan aurenta?"

Yana fita ya zaro wayarshi Mustapha ne dai yaketa kira. Tabbas yasan da matsala banza bata kai zomo

kasuwa wannan kira babu ™a™™autawa.

"""Mustapha wannan kira haka. Allah yasa muji alkhairi?"""

Mustapha daga wayar yace.

"""Babu wani Alkhairi kai da nake ta kiranka tun abun na faruwa. Sabuwa ce wannan matsiyacin yazo ya"

"Wauketa a bakin makarantar yara a mota. Shine naita kiranka baka Waga ba."""

Wani irin hajijiyace ta kusan buga Babangida da ™asa babu shiri ya jingina da bango numfashinshi yana

"fita da sauri_sauri. A take kamanninshi suka sauya, idanunshi da jijiyoyin kanshi duk suka fito. Runtse"

"idanunshi yayi yana sauraren zuchiyarshi. Wani irin mugun tsananin kishin Sabuwa ke dafa zuchiyarshi da gangar jikinshi harma yake iya jin zai iya kashe Khalid ya kashe Sabuwa kowa ya huta."""

"""Babangida kana jina kuwa. Inata magana naji shiru?""."

"""Ina jinka. Ya kaimun ita Hotel ko, ya danne mun ita ko Mustapha?"""

Cikin wata iriyar muryar da baisan yana da'ita ba yayi maganar. Shi kanshi Mustapha yayi mamakin jin

"muryar abokin nashi da irin furucinshi. Ya dai san baya son Sabuwa a rayuwarshi, amman yasan Babangida na da wani irin kazamin kishi."

"""A_a basu je Hotel ba. Sun shiga store yayi mata siyayya, sai a bakin titi daya parking motar sun daWe"

suna ciki bana iya ganin me suke yi. Sai ya sauketa a gida. Lokacin da nake ta kiranka sun shiga store

"siyayyane naso kazo ka same shi mu ™addamar mishi sai baka Waga wayar ba"""

Idanu Babangida ya lumshe yana ji tamkar zuchiyarshi zata jijjige ta faWo. Yayi magana ya kasa haWa

kalmar da za'a fahimta sai in'ina kawai. Wayar ya kashe kawai ya figi hannun Usama suka bar wajen. Wani irin zafi da raWadi yake ji. Allah Allah yake ya isa gida ya ajjiye Usama yabi Sabuwa har gidansu ayi

"duk wacce za'ayi in ba dukan mutuwa yayi mata ba, ™ila ajalinshi ta shirya yi da ba™in ciki."""

"Banko ™ofar gidan yayi babu kowa a tsakar gidan, yana kallon ™ofar Wakin Sabuwa ya ganta a buWe."

"""Usama jeka Wakinsu Khalifa ina zuwa yanzu kaji?"""

"""To Baba"""

"Cewar Usama. Kama hanya yayi turyan_,turyam zuwa Wakin su Khalifa har saida yaga shigarshi kana ya"

"nufi lungunsu Sabuwa."""

Sabuwa:.

Ina kwance ina karanta wasi™ar jaki na ji an banko ™ofa an shigo. Kafin in yi wani yin™uri Babangida ya

"cabke wuyana gam ya sha™eni. Idanunshi duk sun fiffito tamkar shi aka sha™e bashi ya sha™e ba, har"

wani tararren hawaye nake hangowa a guraben idanunshi.

"""Wato ke Sabuwa har yanzu baki ha™ura da wannan la'ananne. Khalid Win ba ko? Sabida kinga ina raga"

miki ne yasa kike wasu abun. ³ar iska wacce sukai gadon iskanci. Mace da aurenta harda budurwar ³a

amman tana raba jikinta ga Wan balaja'u.

"Yau kasheki zanyi in kashe shi dan ubanku nima a kasheni duk mu huta"""

Da wani irin ™arfin murya mai salon dashewa yake magana irinta basawan india sak kun tuna maganbo

na shirin Win kwaila? To sak muryar da yayi kenan. Idanuna sai fitowa suke yi dan Babangida ba imanine dashi ba sai sake makuremun wuyana yake yi.

Ni kuma sai kiciniyar ™wacewa nake yi amman ya™i sake ni. Hannu nasa na biji ™asanshi da dukkanmin

™arfina.

Ihu yayi ya sakeni tare da ri™e ™asanshi da hannunshi mai lafiya. Mi™ewa nayi na diro daga gadon da

gudu ina haki.

"Wallahi Babangida kayi kaWan ka rabani da Khalid ni dashi sai mun yi aure mun haifi yar.."""

Kafin in karashe Babangida yayi wani kukan kura ya buge bakina da iyakar ™arfinshi. Take naji bakin

kamar ba nawa ba. Rungumarshi nayi ina shirin yin faWa dashi. Ayau dai na kasa dan ran maza ya Saci fyaWani yayi a gado yana nuna ni da yatsa.

"""Sai dai a mafarki wallahi Sabuwa bazan taSa rabuwa dake ba .Kuma ko dan sabida Khalid kina cikin"

gidannan babu inda zaki je wallahi kinji na rantse. So kike ki kasheni da ba™in ciki ne Sabuwa kome kike

"so. Shin Khalid Win fina yayi iya tarairaya, ko ™arfin mazantaka zai nuna mun ki faWa mun nace"""

Ya ™arashe maganar da tsawa tare da runtse idanunshi har saida hawaye ya surnano a idanunshi guda

Waya.

"Zama yayi jikinshi a mace a bakin gadon, nima ina zaune a gadon ina maida numfashi ga jini sai zuba"

"yake yi a bakina, bakina ya aune yayi suntum."

Ya daWe yana kallon waje Waya kome yake kallo oho. Ni kuma sai lumfashi nake yi gami da haWiye kukan

dake tunkudo kanshi da kanshi

Please Login or Register in order to submit comment