You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

soma yi mishi magiyar yai

mata rai.

"""Dan Allah kada kasa aimun dariya. Wallahi kasan ina sonka wanne irin saki ana zaune ™alau kuma?"

acin raine da sharrin shaiWan. Wallahi zafin kwanana daga Wauka ka kaima matarka ne yasa nima na

"Sata maka ranka, amman na tuba ka maidani Wakina dan ALLAH."""

Mi™ewa yayi yana jin kanshi na sara mishi ya ™ule Wakin Hamida harda saka sakata.

"Ba yau bane ranar farko daya taSa sakin mace ba, kuma bawai Hamida na daga cikin matan da yake jin"

sonta bane. Asalima Farida daya saka tafi ko wacce macce soyuwa a ranshi daga cikin matan daya saka hakan bai hana ya saketa ba data kama.

Amman abun mamaki a karon farko sai yaji sakin yayi mishi wani bawai. Yana kuma tunanin halin da

iyayenshi zasu sake shiga matsawar suka ji labarin sakin da yayi musamman Baba Malam.

Takadda ya yaga ya rubuta sakin a matsayin shaida kana ya ciro wayarshi ya Wauki hoton sakin ya turama

Sumy ta manhajar WhatsApp.

"""Gashi na saki wacce tsautsayin sakin ya faWo a kanta. Gobe sai ki tattara ki kama hanya kamar yadda"

"muka yi dake"""

Mayar da wayar yayi gaban ajjihun rigarshi ya buWe ™ofar ya fito. Hamida na zaune zaman durshan a

™odar Wakin tana sharce hawaye taji fitowarshi babu shiri ta mi™e tare da fuskantarshi tana jaddada bashi ha™uri.

"""Ga takaddarki kiyi ha™uri aikin gama ya gama"""

Hannunta na rawa tasa hannu ta karSa ta zauna daSas a saman kujera tayi ™uri har ya fice ya barta a

Wakin kukanma ™afewa yayi tas.

"Da sallama ya shiga Wakin ³ar Shuwa duk da baiji an amsa mishi sallamar ba, sai yayi tunanin ko tana can"

ciki ne.

Falon babu kowa ga tv a kunne fanka ma a kunne sunata aiki. Kai kawai ya gyaWa ya kutsa kai cikin

uwarWakin. Turus ya tsaya ganin mata riWa riWa har su uku a kan gadonshi suna cin abinci duk sun yi watsi da Wankwalayensu.

"Da sauri ya koma, su kansu duk sai suka rikice da ganinshi tunda ³ar Shuwa ta tabbatar musu ba"

kwananta bane ranar.

"Cike da mamaki yayi komawarshi falo ya zauna a kujera ya Waga kanshi sama tare da rufe idanunshi, shi"

kaWai yasan abinda yake ji a zuchiyarshi.

Sum_sum_sum matannan suka fito suka wuce shi. Uwar gayyar ce ta zauna a kusa dashi cikin muryar

rashin gaskiya tace.

"""Sannu da shigowa ashe zaka shigo?"""

Ta faWa a Warare. Mugun kallo ya watso mata yana daga shingiWe a kujera.

"""WaWannan marasa albarkar su kuma daga ina da har kike ganin matsayinsu ya kai ba falo ba har"

"uwarWakina, akan gadona ake cin abinci. Sannan a ina kika samo su nasan dai ba ™awayenku bane tunda daga cikin ™awayenku ke da Sabuwa babu wacce ban sani ba?"""

"""Matan ma™otane suka shigo, to lokacin da suka shigo ina ciki ne ina gyara kaya a wadrop shine nace su"

"shiga"""

Zama yayi ya fuskanceta da kyau kana yace.

"""Har kinyi sabo da ma™ota irin haka? Ko da yake na fahimci matan layinnan kamar basu da kamun kai ba"

"kuma su san darajar aure ba. Ki kawo mun abinci in akwai"""

Ya ™arashe maganar cike da bambami. Ita dai bata ce uffan ba ta fita ta kawo mishi abincin kamar yadda

ya umarta.

Bai ci yafi loma biyar ba ya sha ruwa ya mi™e ya shige ciki har uzuwa lokacin mita yake yi kamar tsohon

kuturu.

Da uwar harara ta bishi harda gajeren tsakinta marar sauti.

"""Mutum sai shegen faWin rai da mitar tsiya. Nifa wallahi bazai yiwu ba ehe"""

"Ta mi™e tare sa tattare kayan da yaci abinci ta fita dashi, tana shiga cikin coridor ta ji halamun wanka"

yake yi. Cike da mamaki ta shige ciki a gurguje ta gyara inda duk aka Sata.

"""To wannan ciwonne yasa ya mance ba kwanana bane, ko ko tsabar jarfar da Sabuwa ta Webo mishi ne"

"ya rikirkitashi? Ni dai nasan Hamida ke da kwana, tun yamma taci kwalliya take ta falli a tsakar gida, sai miji kuma ace Wakina zai shigo yaci abinci harda wanka? Tabb gobe akwai rikici kenan"""

"Dariyar mugunta ta saki, a haka Babangida ya shigo ya taddata, bai ko kalleta ba daga shi sai gajeren"

wando yayi kwanciyarshi.

"Amman me? Shine har biyun dare idanunshi a soye, idanu ya ™urama ³ar Shuwa wacce take ta sharar"

"bacci abubuwa da yawa yake tunanowa a kanshi game da farkon soyayyarshi da'ita da irin yadda yake jin in ba samunta yayi ba zaima iya mutuwa."""

"""Aisha! Aisha"""

"Babangida ya shiga kiranta a hankali"""

Cikin bacci ta buWe idanunta ta kalleshi.

"""Jannaty bakai bacci ba na ganka a zaune Aisha ka dawo kirana kuma hmm?"""

Idanunshi ya lumshe yana jin motsin san kasancewa da mace a jikinshi. Dan in Sacin rai ya shiga

kasancewa da mace ke saukar mishi da fishin nashi.

Kallon da yayi mata tuni ta bugo jirginshi take ta ba da kai bori ya hau. Cikin dabara komai ya gudana duk

da a hakanma saida ya Wan fama ciwonshi. Bayan komai ya lafa ne bacci ya sureshi. Yayinda ita kuma ³ar Shuwa ta zauna zaman dirshan zuchiyarta cike tab da tunanin yadda zata kawo ™arshen sabon asirin jawo hankalin da Sabuwa taima Babangida da har ya iya zuwa Wakinta yayi kwana biyu. Kuma Sabuwa ta ji mata ciwo Babangida ya kasa Waukar matakin komai akai. Gashi yau da Aisha gatsau ya kirata kafasiti

nata zubewa.

"""To ko dai yana son matarshi ne daman? Duk da dai yace sabida bakin da Baba Malam yayi mishine ne"

yasa yake zaune da'ita. To amman a wannan karon me yasa har Malama Babba bata son a saki Sabuwa?

Ya zame mun dole gobe in ziyarci gidan Yaya Sa'a a canne zan iya dukan cikinta in ji komai tunda ita na

fahimci lusara ce.

Washegari da safe

SABUWA:.

"Bayan mun kammala karyawa yara sun yi wanka kowa yasa kayan makaranta, saina Wauki jakata da"

mayafina nima na fito. A lokacin harsu Mardiyya sun fice.

Ina kulle ™ofa Malama tace.

"""Ummi gidan Baba Maigogul zaki je? Nima zan biki ummi dan ALLAH"""

Murmushi nayi nace.

"To yanzu kuje makaranta nima makarantar taku zanje, in kuka taso kuma kinga kuna da islamiyya. Ranar"

"juma'a nayi muku al™awari zamu je mu kwana ma a gida asabar ma dawo"""

Nan suka shiga murna abunka da yaro

Maman Sa'idu dake haWa kayan karyawa tayi dariya itama. Gaisawa muka yi a gurguje nayi mata sallama

muka fita.

Kafin in fice a gidan na hango fitowar Babangida daga Šakin ³ar Shuwa tana biye dashi da halama

unguwa suma zasu je.

Da sauri Babangida ya sha gabanmu.

Yaran suka gaisheshi ya amsa yana fara'a harda Wauko Wari biyar yana ba Mardiyya.

"""A_a Baba ka barshi Ummi ta bamu kuWin mota"""

Kallon yaran yayi sai yaji kunya.

"""To ku dai ™ara kunji"""

Hannu tasa da ladabi ta amsa suka wuce.

"Babangida ya dubeni, ni ko kaina gefe yake kallo, mutuniyarku tana tsallake ta cika ta batse."

"""Ina zaki je da sassafe haka ke da bakya kaunar zaman gidanki kisan bana son fita ko?"""

"Idan kaga mace na ™aunar zaman gidanta, kaje ka bincika ha™i™a wannan gidan a ciki take samun"

"nutsuwa. Ire_irenmu kuma sai mun fito daga gidan namu muke samun nutsuwa""."

"Ina gama faWin haka nabi gefenshi zan raSa, yayi maza ya kuma shan gabana."

"""Amman kinsan mace ta fita ba tare da izinin mijinta ba mala'ikun Allah ba zasui ta tsine mata har sai"

taje ta dawo ko? Ko da yake nasan ba lallai kisan wannan ba tunda...

Sai yaja bakinshi ya rufe.

˜uri nayi ina kallonshi har yayi shiru.

Ba'a bani tarbiyyar sanin hakan ba a gidanmu. Mahaifina Kawaline ba Malami ba. Amman dai nasan zina

"masifa da bala'ice kuma mai yinta baya taSa kasancewa cikin arziki, dama lafiya, kuma bashi ce kayi da matar wani ayi da taka matar shi wannan na sansu"""

Wucewa nayi da ™arfina dan nayi niyyar da ya sha gabana to ha™i™a saina tunkuWeshi ya faWi.

"Inaji yana kiran sunana yana bina a baya, nayi fumfurunfus. Ina zuwa titi na faWa cikin Bus Win da yara"

suka tara muka wuce abinmu.

BABANGIDA:.

Shiru yayi a gaban titi zuchiyarshi na suya mishi. Tare da tunanin to ina Sabuwa zata je da safe haka?

Wata zuchiyar ta ayyana mishi.

"""Ko wajen Khalid zata ne kasan sun daWe basu haWu ba"""""

Take ya runtse idanunshi.

"""Ai sai ka tare mana abun hawa mu wuce ko tunda ita matar taka tayi tafiyarta muma ai sai mu tafi ko?"""

"Idanunshi ya buWe take taga sun sake nauni dole ta haWiye masifa da bala""in da take son sauke mishi."

Mashin ya tare ya Wane.

"""Bus dincan da tai kwana zaka bi mun."

"Ke kuma ki kama hanya ki tafi wajen yaya Sa'a ni sai na dawo"""

Fuu mai Acabanshi ya ja suka wuce.

Wasu hawayen ba™in cikine suka sulalo a kumatun ³ar Shuwa tayi kasa™e a titi tana mamaki har saida ta

dena hango Babangida kafin ta tari abun hawa ta wuce gidan Sa'a

Babangida yana biye da Bus Win su Sabuwa har sanda ta diresu a ™ofar makarantar yara.

Nannauyan ajjiyar zuchiya ya sauke tare da lumshe idanunshi yaji wani irin sanyi da baisan na menene

ba a zuchiyarshi.

Wayarshi ce take ta ruri lauyanshi ke kiranshi babu shiri ya Wauka.

"""Babangida ya kamata ace uwarhaka muna kotu tare da kai domin mu sake samun damar tattaunawa"

kafin a shiga Chamber. Sannan da fatan baka mance da takaddun lissafin kuWaWen ba ko?'

Kai Babangida ya dafe dan ya mance da takaddar.

"""Barister wallahi na mance da takaddar kaina ya Wau zafi da yawa. Amman yanzu zan juya in Wakko"

"bazan jima ba zaka ganni."""

"Kashe wayar yayi, kana yaima Šan AcaSa kwatancen inda zai kaishi zai kuma jirashi ya shiga ya Wakko"

takadda ya fito.

"Basu juma ba suka iso, Wakin Ramatu ya soma shiga tana zaune tana karyawa da doya da ™wai ya shiga a"

™agauce.

"""Ramatu kayayyakina suna Wakinnanne dan ALLAH?"""

"""A_a kamar suna Wakin Maman Usama ko Wakin Maman Fati ban dai sani ba ka tambaye su"""

"Bai bata amsa ba ya fice zuwa Wakin ³ar Shuwa neman duniya baiga takaddun ba, akwai kayayyakinshi a"

Wakin takaddunne babu.

Dakin Hamida ya shiga ya sameta a ciki tana kan haWa kayanta ya shiga birkita kayayyakinshi na Wakin

nanma babu waWannan takaddun sam.

Yana shirin fita ne Hamida tace.

"""Ni inna gama zan wuce garinmu. Zan tafi da diyata, Usama kuma a wajen wa zan barshi?"""

Tsaiwa yayi ya dubeta ita da yarinyar dake bacci a bayanta kana yace.

"""Ki ba Ramatu shi kice in jini. Zan tura miki kuWin mota Allah ya tsare"""

Yana gama faWan haka ya fice zuwa lungunsu Sabuwa estira key Win kwaWon Wakin ya saka ya buWe Wakin

"ya shiga zuwa uwarWakinta ya hau dube_duben takaddu, ya birkita kaya sosai kafin ya gansu a killace a cikin wani fail fari mai Wauke da sunanshi. Ajjiyar zuchiya ya sauke kana ya mi™e tsaye yana ™o™arin mayar da kayan Sabuwa daya wargaza mata. Ananne wata ™atuwar leda fara mai Wauke da hatimin"

shagon siyayya ya faWo.

Haka kurum yaji ya kasance cikin son ganin menene wannan abun dake cikin ledar.

Hannunshi na rawa ya zazzage ledar kayan dake ciki suka zubo. Idanunshi suka sauka akan kwalin sigari

Wan ™asar waje.

Wani yawu ya haWiye mu™ut a hankali ya tsugunna ya Wauki kwalin sigarin yana kallo

Ko daya buWa saura guda huWu kacal a ciki duk sauran an shanye.

Yarwa yayi ya kuma Waga wani net sai yaga rigar bacci mai raga_raga da wandonta ™arami shima mai

"raga, harda rigar Mama masu tsadar gaske dan Designer ne take jijiyoyin kanshi suka shiga shocking"

suna kumbura suna sakewa da kansu. Yana ri™e da Wan kamfai numfashinshi na yin sama_sama.

"Wannan tsarabace khalid yayo ma sabuwa shiru kawai yayi baisan a wanne yanayi shi kanshi yake ciki ba, baya iya fahimtar komai face raWaWin da zuchiyarshi take yi mishi, da irin luguden da zuchiyar tashi take"

dokawa.

Sake lumshe idanun nashi yayi tare da tariyo adadin matan da yayi tarayyar banza dasu. Sai dai kash

sabida tsabar yawansu tuni wasu ya mance ma dasu. Wani irin wutar kishine take ci a zuchiyar Babangida wanda hakan ya haifar mishi da jikewa sharkab da ruwan gumi.

"Har sau biyu lauyanshi na kiranshi amman baima sani ba, sai a kira na uku ne Allah ya bashi ikon ji."

Nannauyan ajjiyar zuchiya ya sauke kana ya Wauki wayar sai dai harshanshi sai yaji sun sar™e ya kasa

magana.

"Zare wayar yayi a kunnenshi kawai ya tattare wannan kayan ya mayar ledarsu, ya haWa d takaddunshi"

jikinshi a mugun mace ya fita

Mrs Bukhari

Sai mun tara gobe

IDAN KAYA YA GAJI...

GAMMO MA YA GAJI

LITTAFI NA BIYU

SHAFI NA SHA ŠAYA

BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ˜AMSHI

(BANA JIN DAŠIN YADDA MUTANE DA YAWA SUKE MUN DM SUNA TAMBAYATA SHIN DA GASKE NAKE

YI LABARIN SABUWA YA FARU A GASKE. ALAL HAKI˜A DUK SANDA NACI KARO DA WANNAN TAMBAYAR INA MATU˜AR JIN BABU DAŠI DOMIN HAKAN YANA NUFIN MAI TAMBAYAR YANA TANTAMAR ˜ARYACE

KAWAI NAKE YI. KO KUMA INA CEWA LABARIN GASKIYA NE DA WATA MANUFA.

KU SANI BABU RIBAR DA ZANCI DAN NAYI MUKU ˜ARYA.

SHIN BAKU TAA JIN UBANDA YAYI ŠIYARSHI CIKI TA HAIHU BANE? AI LABARIN YAFI NA SU SABUWA

MUNI TUNDA MAIGOGUL BAI TAA JIN SHA'AWAR YARANSHI BA.

WALLAHI BILLAHI NASAN GIDAJE DA YAWA DA SUKA FI GIDANSU SABUWA KAZANTA.

SANNAN KU SANI DUK LITTATTAFAINA LABARAINE DA SUKA FARU A ZAHIRI KI AMINCE KO KADA KI

AMINCE WANNAN YA DANGANTA DA YANAYIN YADDA KIKE ŠAUKAN ABU.

AMMAN TABBAS LABARIN SABUWA LABARINE NA GASKE. NAGODE SOSAI DA SOYAYYA ALLAH YA BAR

˜AUNA)

SABUWA TACE IN MI˜A MATA SA˜ONTA GA DUK ŠAUKACIN MASOYANTA.

IYABO MA TACE TANA BIBIYAR WANNAN LABARIN KUMA TANA TAUSAYIN SABUWA SOSAI.

"( IYABO MAI RAYA SUNNAH A GARKEN SHANU TSUNTSUN SOYAYYA BA. TA HAMMA BADA KANKI A SARE,"

"AMINIYA A WAJEN UWANI TA BALBALIN, CINYAR SA MAGANIN MAI HAŠAMA BA )"

Yana fitowa Šan AcaSa ya soma bambamin faWa akan sai an ™ara mishi kuWi shi wallahi shi tallahi bazai

yarda ba.

"""Zan ™ara maka ko nawa kake so muje ka kaini kotun cikin gari"""

Ya faWa cikin wata nutsuwar da shi kanshi baisan yana da'ita ba.

Yana zaune a AcaSa amman tunaninshi yana wajen Sabuwa da kayan dake ledar hannunshi.

"""Khalid Allah dai ya tsine maka albarka. Dake kai tantirin Wan iskane hankalinka kwance kake mu'amala"

"da matar wani, harda kawo mata tsarabar kayan karuwai. To mijinta ka siyo ma ta saka mishi, ko ko A_a ka siyo ne dan a saka maka ka kalla kaji daWi?"""

Duk wannan maganganun a cikin zuchiyarshi yake yinshi. Kanshi ne ya sara mishi take wani jiri da zazzaSi

ya sakko mishi. Babu shiri ya soma ambaton Allah

"Amman zuchiyarshi sam ta™i nutsuwa, in bansa tunzurashi da zuchiyarshi take yi bata komai. Har hango"

sabuwa yake yi a Wakin hotel a gaban Khalid da wannan rigar baccin a jikinta.

"""Malam anya kuwa kana da hankali ka duba nafi minti uku ina cewa mun iso amman babu um babu"

"um_um."""

"Sai lokacin Babangida ya fahimci dashi fa ake Magana, Wago kan da yayi yaga lauyanshi da Kawu Manga a"

gaban AcaSar.

"""Ashsha Babangida jikin naka ne ya kuma tashi ne, da ganin yanayinka kana cikin matsanancin ciwo."""

"""Kawu mai girma ma kuwa. Ku taya ni da adda'a kawai ita nafi bu™ata ba lallai bane in warke daga cutar"

"da zuchiyata da tunanina suka kamu dashi ba"""

"""KuWina dubu biyu waye wai zai bani ne?"""

Cewar Šan AcaSa da aka ™ureshi har zuwa bango.

Dubu biyu Kawu Manga ya ciro aka sallami mai acaSa ya wuce su kuma suka rankaya izuwa Chamba.

"A ciki ya tadda Alhaji Abubakar Baban bola tare da lauyanshi da Wanshi, sai al™ali dake kujerarshi a zaune."

Bayan sun samu waje sun zauna al™ali yace.

"""Babangida inaso inji daga bakinka shin da gaske kamfanin da kake ri™e dashi babu ko sisin kwabonka a"

"ciki, naka juya kuWinne da yarjejeniyar raba riba?"""

"""Hakane mai shari'a babu jayayya ga duk abinda Alhaji Abubakar Baban bola ya faWa. Nayi mishi laifi ina"

"neman afuwa a sassauta mun"""

Anan dai aka ™ar™are magana da kissafe_lissafe a ta™aice da nera million goma kacal Babangida ya tsira

shima a hakan ba ™aramin adalci akayi mishi ba. Shari'ar dake a chamba ce kuma akwai sanayya sannan

"Babu jayayya ko musu a take aka gama komai Babangida ya sanya hannu shi da lauyanshi, haka ma Alhaji Abubakar Baban bola ya sanya hannunshi shi da Wanshi da lauyanshi. Batun bama Babangida"

million goma kuma yace a i mishi alfarma zuwa wani lokacin zai bayar da haka aka rufe case Win

kwata_kwata.

Suna fitowa sai ga kiran malama Babba ya shigo wayar Kawu Manga. Šagawarshi ke da wuya Malama

Babba tace in suna tare da Babangida su tawo su sameta a gidan Wawo yanzunnan.

"""To shikenan gamu nan. Amman lafiya naji muryarki haka a firgice?"""

Malama Babba tace.

"""Babangida hankalinshi bazai taSa kwanciya ba har sai yaga ba™in cikinshi yayi ajalina tukunna. Wallahi"

"da zan iya ha™ura dashi kamar yadda Malam yayi dana huta"""

Kawu Manga ya girgiza kai. Babangida Kuma ya sauke kanshi ™asa dan shi baisan kuma me ya kuma

aikatawa ba.

"""To ko Sumy ta kai Amir gidane danta fallasa asirina? A_a ai duk sharaWin data bani ban tsallake ko Waya"

"ba bafa ita bace"""

"""Babangida muje gyatumarka na son ganinka yanzu. Barrister mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi """

Hannu Babangida yaba Barrister sukai musabaha kafin yabi Kawu Manga da wani irin sanyin jiki.

Yana bayan bespa Kawu Manga na tukasu tunaninshi kacokan yana wajen Sabuwa da tsarabar da take

hannunshi har suka iso ™ofar gidan Wawo bai daina tunani ba.

"""Sai ka shige mu je ai ko, sai wani sanyin jiki kake yi kamar gaske a haka kamar ba kaiba in ka kuntuka"

"wata tsiyar sai mutum ga ri™e bakinshi mutumin banza."""

Har suka shiga Kawu Manga faWa yake yi.

Matan Wawo suna tsakar gida suna aikace_aikacen mata na yau da kullum su Kawu Manga suka shigo.

"Nan suka shiga rige_rigen gaishe da Kawu, yara da basa makaranta suka iso wajen Babansu a guje suka"

rirri™e mishi kafa

"Murmushi Babangida ya dinga yi musu yana shafa musu kansu. Da ™yar iyayensu suka rabasu dashi,"

"saida ya bada Wari biyu kuWin biskit, ya gaishe da matan yayan nashi kana ya shiga."

Da idanu yu suka bishi suna mamakin irin halayenshi a ido gashi dai mutum har mutum mai zubin

"kamala, hankali da tunani."

"Da sallama suka shiga part Win da Malama Babba take ciki, ga wata yarinya tana shanya a igiyar dake Wan"

tsakar gidan da halama mai aiki ce Wawo ya Wakko.

"Suna saka kai Babangida yayi tozali da Hamida da ³a΄anta suna zaune dirshan a gaban Malama Babba """

SABUWA:.

"Bus Winmu ta sauke mu a daidai bakin makarantar, haka nabi ayarin dalibai muka shiga cikin makarantar."

"Mardiyya kaini ofishin shugaban makaranta"""

Mardiyya ta shige gaba ina biye da'ita har ofishin.

Na shiga na tarar da wata uwa itama ta kawo ™orafi akan Walibai sun saka yaronta gaba da duka da

tsangwama suna neman su burkita mishi tunaninshi.

"""To Malama kiyi ha™uri sha'anin Walibai sai adda'a. Amman zamu sake saka idanu sosai akan shi Jamilun"

"da mu'amalarshi da yara ΄an uwanshi. Uhm kije gida kawai"""

Mi™ewa tayi tare da cewa.

"""Shikenan Malam nagode ina fatan ganin sauyi mu wuni lafiya."""

Ta fita a hankali. Shugaban makaranta ya kalleni yace.

"""Hajiya barka da zuwa menene ™orafinki, koko kin kawo yaro zai shiga makaranta ne?"""

Yayi maganar da fara'a.

A_a ni mahaifiyar AWWa'u ce nazo ne naji ba'asin dukanshi da akayi irin wannan dukan sai kace ba uwa

"bace ta haifeshi ba"""

"Take ya gintse fuska, nima na Waure fuskata tamau."

"""Uhm naga halama. Uhm Hajiya an kuwa baki labarin sata yayi aka dakeshi kuwa, sannan kuna da"

masaniyar sace_sacen da wannan yaron yake yi a wannan makarantar kuwa? In ba dan darajar kakansu

"ba ai da tuni mun koreshi dan gudun kada ya Sata ma yaran mutane tarbiyyarsu ta hanyar koyar dasu sata"""

"Yawu na haWiye muryata a kausashe, a dakushe a lokaci guda."

Malam dan yayi sata sai ai mishi irin dukan da akai mishi aka farfasa mishi jiki? Shin a matsayinka na uba

kuma babban malami kai kana ganin irin wannan dukan hanyace ta horar da yaro ko hanyace ta sake

"fanWarar dashi. Ko tunaninka satarshi mu iyayenshi mu muka koyar dashi, ko kuwa mu muka Waurashi bisa gwadaben satar? Ka sani babu wata uwa da zata so Wanta ya kasance bana gari ba. A mafiya yawan"

lokuta duka ba mafita bane musamman ga yara ire_iren AWWa'u jawosu a jiki suka fi so da kuma nuna

"musu hanyar gaskiya tunda har gobe AWWa'u yaro ne ™arami kuma ina fatan Allah kar yasa ya girma da wannan halin. Kuma ku sani kuma da naku ³a΄an suke a kimtse wallahi Allah ba dabararku bace."""

Ina dasa aya na mi™e tare da zuge jakata na zaro nera dubu Waya na ajjiye akan teburinshi.

Ga kuWin da akace ya sata a mayar ma da yaron sannan a bashi ha™uri.

Kai kuma kune malamai ya dace ku taya mu tarbiyyar yarannan domin daku suka fi rayuwa a rana awa

"nawa mu iyayensu muke samu tare dasu, rabi da kwatan lokutansu naku ne. Ayi ha™uri kada a sake mishi duka irin wannan duk yadda zai lalace ha™i™a inason kayana."""

Juyawa nayi na nufi ™ofa har na kusan ficewa naji shugaban makaranta yace.

"""Hajiya!"""

"Juyiwa nayi na kalleshi. Jikinshi yayi laushi sosai, ni kuma zuchiyata tafasa kawai take yi."

"""Ha™i™a na Wauki babban darasi a maganganunki na hikima. Na yaba da salon isar da sa™onki cikin ruwan"

sanyi kika dafa ni da ruwan jikina.

In sha ALLAH daga yau babu wani malami da zai sake dukan AWWa'u kan yayi sata. Koma me ya aikata

zamu kira lambarki ko ta mahaifinshi dake jikin form mu sanar muku inma na zuwa ne sai ku zo.

"Baya ga wannan halin na AWWa'u yaron bashi da matsalar komai. Gashi da ™wa™walwa, gashi da haza™a,"

"kuma yarone mai tausayi, bugu da ™ari yana da son ΄an uwanshi. Hajiya ai mana afuwa wallahi mun"

"dakeshi ne ba dan mugunta ba, sai don gyaran tarbiyyar shi. Amman zuwanku yasa na fahimci ta inda mu kanmu muke da kuskure kuma zamu gyara"""

Idanuna na lumshe kawai na gyaWa kaina tare da cewa.

Allah ya bamu ikon gyarawa.

Nayi maganarne haWe da sauke ajjiyar zuchiya irin na wanda ya samu sassauci a zuchiya.

Ban bi takan yaran ba na fice a makaranta. Ina tsallake ina jiran abun hawa sai naga mota ta tsaya a

gabana. Gilashin motar aka zuge Khalid ne a cikin motar yana saye da fararen suit yayi kyau sosai. ˜uri

"yayi mun da idanuwanshi, nima shi nake kallo ina jin wani abu a raina game dashi."

"""Shiga mota in kai ki duk inda zaki je Sabuwa."""

"Da ka yi tafiyarka Khalid nagode sosai."""

Murmushi yayi ya fito daga cikin motar ya iso gabana yana murmushi.

"""Ai ban isa na barki anan wajen ba. Wai kinsan irin neman dana dinga miki ban sameki ba kuwa? Wallahi"

"da kinsan irin halin dana shiga ta dalilin son sanin halin da kike ciki tun bayan rabuwarmu da kin tausaya mun. Ki daure muje in kai kii"""

"Jakata ya karSa ya buWe mun gaban mota na shiga, ya zagaya da hanzari ya shiga mazauninshi."

Idanuna a lumshe sanyin Ac na ratsani naji Khalid yace.

"""Ga sigari ki sha ki rage nauyin zuchiya da ganin yanayinki kina cikin damuwar da tafi damuwar da kike"

"cikinta a baya kafin in dawo cikin rayuwarki."""

Sigarin na karSa na soma zu™a cikin salon ™warewa shi kuma ya ja mota ya seta ta a titi.

"""Ina zaki je dama?"""

"Gidanmu zanje can zaka kaini"""

Kai ya gyaWa yayi mun murmushi tare da cewa.

Menene abinda ya faru bayan rabuwarmu a wannan lokacin? Naso inji daga gareki nabi duk wata hanya

"amman ban sameki ba, wayarki bata shiga naje har layinku aka ce mun kun tashi dole haka na ha™ura."

"Kuma inata tunanin zaki neme ni ki sanar dani azzalumin mijinki ya sake ki nanma naji shiru"""

"Idanuna na lumshe, saida na zubar da haya™in dana zu™a tas kafin na bashi labarin abinda ya faru."""

Labarin duk abinda ya faru na bashi tare da Waurawa da cewar.

Yanzu jira muke yi zaman kotu na biyu ya zagayo mu sake komawa kafinnan hannun nashi ya warke

"kamar yadda nauyan nashi ya bukata."""

Murmushi Khalid yayi tare da sakin Wan wani ihu da yasani sakin baki da mamaki ina kallonshi.

"Lafiya kake ihu?"""

"""Wannan labarin naki ai dole in yi ihu burina kice ya kusan cika na mallakarki halak malak ba tare da"

"shamakin komai ba? Lallai zan saka himma a kan ginin da nake yi da na saka wasa amman yanzu dole in saka himma dan gidana da nake ciki bazai isheku ba."""

Murmushi kawai nayi na girgiza kai tare da cije leSena kawai.

Akalar motar ya sauya zuwa wani titi daban.

"Ina kuma zamu je, nifa ban shirya aikata komai ba asalima bazan sake aikata komai ba ko dan mutuncin"

"yarana"""

Kallona yayi da kyau ya nemi gefen hanya ya tsaya.

"""Sabuwa wallahi sosai nake sonki ina mai tabbatar miki duk duniya babu Wanda zai soki rabin son da"

"Khalid yake yi miki. Kada kiyi tunanin ko ina mu'amala da matan banza har yanzu kiji tsoro ko shakkar aurena. Ko Waya a halin yanzu bana mu'amala da ko wacce mace face ke, ke kuma kinfi kowa sanin rabin"

"rayuwata ce ke, kada kiyi tunanin sabida jikinki nake sonki. Da gasken gaske sonki nake yi sosai."""

Numfasawa yayi tare da ri™o hannayena biyu yana murzawa a hankali ni dai sama da kasa Allah bai bani

ikon cewa dashi

Please Login or Register in order to submit comment