You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Shuwa ta rakouu barayina ko zama sun kasa yi.

"""Ku haWa kayayyakinku waje guda zaku tashi a gidan. Za'ayi ma gidan gyara sosai ne"""

Bata bari na amsa ba suka fice.

"Amman jikina yana bani matsala ba tun yau ba, dan na fahimci su Kawu Manga sai kai kawo suke yi"

hatta motar ³ar shuwa babu. A zuwa na duba Baba malam na ukunne ma na tarar an sallamo Malama

Babba sai na shiga na dubata da jiki.

Ta rame ta komaWe sosai.

"""Sa'a ku bamu waje inaso zanyi magana da Sabuwa"""

Bani kaWai ba harsu Kudidi suma sun yi mamaki. Ni ko kaina cike da tambayar da babu wanda zai iya

amsa mun.

Nan duk suka zame suka fita. Cikin gadara Malama Babba tace.

"""So nake ki janye wannan shar'ar da kika shigar da ™ara kotu. Na yi miki al™awarin ko nawa kike bu™ata"

"zan baki"""

Da mamaki na kalleta sai kawai nayi murmushi nace.

"Bazan iya janye wannan ™aran ba, ko da duniya da abinda ke cikinta zaki bani. Takaddar sakina yafi mun"

"komai"""

A_a dai kije kiyi tunani nan da kwana biyu kinga lokacin shiga kotu ya kusa. In kika janye zan baki kuWi

"masu kauri """

Daga sama muka jiyo muryar Baba Malam

"""Babu mahalukin daya isa yasa ta janye. Da kike maganar kuWi kuma a ina kika samesu ni bani da"

masaniya a kansu? Ai dani kika bama kya samu lada.

"Ke Sabuwa taso ki kama hanya ki tafi gidanki"""

Sum_sum na ficewata ya suka ™are sai Allah.

Ina isa gida a ™ofar gidanmu naga wata ™atuwar mota tana ta loda kayayyakin Waki harda gadona na

hango a cikin motar.

Ban gama mamaki ba Labbai ta fito da ™atuwar randa ta cike da kwanuka da su cokula.

Ga Hamida itama a gefe tanata zuba kayayyaki a buhu. Gidan duk ya hautsine

"Hannuna Labbai taja muka shiga cikin gidan"""

"""Kinga muna zaune Wawo ya le™o yace mu fito da kayanmu. Lallai Sabuwa zaku sha gyara. Amman naga"

"gidannan babu abinda ya sameshi sai samannan da ake tadawa"""

Jikina a sanyaye nace.

"Sunce gyara za'ayi sosai a gabanki fa Sa'a ta faWa mana. Ina Adama fa?"""

"""Tana ciki tana fito da kaya muje daga ciki"""

Ciki muka shiga muka ci gaba da harhaWe kaya.

Motar ma ta cika har sun tafi kai kayan.

"Ni ko har mun gama fitar da kab kayanmu waje, har Adama ta share Wakunan, ni da Labbai mun goge"

komai da komai.

"Har wajajen bayan la'asar yara suka shigo suka samemu muna jira, Adama dai tabi motar kaya da suka"

dawo.

Ma™ota duk an shisshigo dan jin ba'asi.

Da an faWa musu gyara za'ayi mana sai su shiga taya mu murna.

"Maman Safara,u ta daWe sosai tare damu taso binmu ma taga waje amman ganin har an kira magriba"

ba'a zo ba yasa tace.

"""Maman Mardiyya ni kam zan tafi gida yau nice da oga, gashi dare yayi inaga sai zuwa gobe zan kiraki a"

"wayar Labbai sai in zo in sha Allah. Allah ya sanya alkhairi ya ™ara arziki"""

"To Ameen Maman Safara,u nagode sosai Allah ya bar zumunci. Sai zuwa goben."

Ta fita bata jima ba Wawo ya shigo yai kiranmu duk aka duramu a siyana muka Wau hanya.

Motar tayi tsit kowacce da abinda take sa™awa.

Bamu tabbatar da akwai matsala ba sai da muka ga motarmu tasha kwanar wata unguwar da kaWan tafi

unguwar da muka taso na da kyau.

Ga hanyar shiga unguwar bata da kyau ga ba wuta sai faWawa ramuka muke yi.

"A bakin get Win wani gida motar ta tsaya, get Win irin get Winnanne da baikai har ™asa ba, kai me wucewa"

kana iya hango har guiwar na tsaye gashi duk tsatsa.

"""To masha Allah ga gidan da zaku zauna nan. Muje in nuna muku Wakunanku dan ba jere suke ba."""

Wawo yayi gaba muka bishi a baya da yaranmu.

"Gidan shiru babu hayaniya, babu ko macce Waya a tsakar gidan."

"Gidane dogo ga Wa™una a jere suna kallon juna. Hagu Wakuna huWu dama ma haka, daga bakin get akwai"

wani lungu dana hango Wakuna kamar huWu suma a jere . Wannan lungun shima lungu yake kallo da

Wakuna huWu a jere suma kunji wata ™udurar Allah.

"""Ga Wakinki Maman Fatima can na ™arshen hagun dama."

"Maman usama ga naki Wakin na farkon hanun hagu, Amarya naki shine na tsakiyancan na hannun dama."

Maman Mardiyya naki na baya ta can kwanar muje in nuna miki sauri nake yi muna da meeting a gida.

Gashi muna sa ran gobe za'a sallamo Babangida daga asibiti ma.

Muna biye dashi har zuwa lungun Wakina shine na ™arshe a lungun. Harma na hango Adama tana ta

"faman moping Win wata ΄ar baranda dake ™ofar Wakin, ko wanne Waki naga da baranda, kuma kamar babu kitchen a ciki dan naga duk a barandar naga iyakar Wakunan dana hanga kitchen Winsu yake."

Saida na shiga barandar naga harda kwanon wanke_wanke na turawa. Adama sun jera mun durowowin

kitchen Wina a wajen sun ciccikasu da kwanuka da tukwane da dai tsarkacen kayan kitchen namu na mata.

"""Sai yanzu kuka shigo irin wannan jimawa me ya tsayar daku haka?"""

Labbai ce taba Adama amsa.

Su Sadiya suna ciki sunata shewa.

"""Wallahi Wawo ne baizo da wuri ya Webo mu ba. Yinwa kamar zata kashe ni."""

"""Yinwa? Hmm muma ita muke ji. Baku haWu dasu Gaza ba?"""

Sun zo ne?

"Gaskiya bamu haWu ba dake muna cikin mota"""

Ciki muka shige yara dama tuni sun shige sai AWWa'u da Malama sai murnar sabon gida suke yi.

"Falon ™aramine sosai gashi kujeruna suna da girma gabaki Waya sai suka takure falon, banga 1 sitter ba"

ma.

"˜ofar da nake tunanin uwar Wakine na shiga sai naga dogon falo ( Coridor) ne ga ™ofofi guda biyu a jere,"

amman suna da taraza ™ofofin.

Šaya ashe banWakine Wayan Wakin kuma Wakin baccine.

Sai a falo kuma akwai wani ™aramin Waki sosai yafi kama da store.

"""Kinga wajen Lolo amman babu Wakin yara. Ma™ociyarki tace duk wannan Wakin suke mayarwa na"

yaransu. Amman asalinshi kitchen ne. Sai mai gidan ya dawo da Kitchen ΄ar barandar waje. Wasu ma da

kansu suka yi aiki.

"To kinga gadone kaWai ya shiga, dorowarsu ta™i shiga, amman ta shiga Wakinki."

Sai kayayyakin Babangida na turakarshi duk su Wawo basu sauke ba dashi suka juya ™ila sabida babu

"wuri ne. Amman dai tulin kayanshi mun jera a durowarki, Wankunnayen su Mardiyya da naki duka kuma"

"suna ™aramar jakarki."""

Ajjiyar zuchiya na sauke tare da neman waje na zauna ina sake ™arema falon kallo.

"Sannunku Adama, Sadiya sannunku fa. Ashe har kun garzayo."

"Kinga Wakinnan sai dai su Aminu su dinga kwana a ciki, ni da matan sai mu kwana a Wakina"""

Carab Aisha dake waya tace.

"""Babansu in a Wakinki yake kuma fa?"""

Adama tace.

"""Ato kema kya tambayeta."""

Dana waiga naga yaran basa wajan sai nace.

Ai kunsan rabuwa zamu yi tunda saura kwana uku ma zaman kotu. Kuma ai dama baya raba mana

"kwana da matanshi balle kuma yanzu kuma duk kun sani. Yanzu dai su Aisha su siyo mana ko da biredi ne sai mu sha tea tunda akwai wuta. Labbai muje ciki muyi Sallah """

Ciki muka shiga bayan na sallami su Aisha da kuWin biredi kayan tea ina dashi dama.

Ina rama sallolina maimakon in huta saina shiga tattare kab suturun Babangida da Adama suka jera mun.

"Ko da suka shigo suka samu inata tarkace komatsenshi babu wacce ta tanka mun, kuma nasan dan sunga na mugun haWe rainane."

"Akwati uku na cika, banda manyan jakunkuna huWu dana ciki, ga takalma cikin ™aramin buhu."

"Labbai taya ni muje mu kaima matan Babangida wannan kayan nashi, ni bana son Magana. Ke Mardiyya"

"Aisha ku taso"""

Haka muka kinkimi kaya na ™wan™wasa ™ofar Hamida duk muka jibge mata kayan a ™ofa.

Da waya a kunnenta ta fito. Ganin kaya yasa tace.

"""Zan kiraka Baban Usama ina zuwa'"""

Ta sauke wayar tana kallon kayan.

"""Wannan kayan daga ina kuma?"""

"Kayan mijinku ne, ku ke da hakkin adana mishi"""

Da harara da taSe baki tace.

"""Ni ina naga wajen da zan ajjiye wannan tulin kayan. Šakuna tsukuku kamar kabari. Sannan ai bani kaWai"

"bace matarshi ba. Ga Ramatu me yasa ba'a raba an kai mata ba tunda Maman Fatima tana asibiti?"""

Kallonta kawai nayi nace da su Labbai su tawo mu tafi dan bani da lokacinta

"""Maman Mardiyya kizo ki debe mun wannan kayan daga nan duk bala'in da kike nema na dashi kin tara"

"kin samu."""

Babu wanda ya juyo balle ya tanka mata.

"Tea da biredi harda tsire su Sadiya suka siyo mana. Muka ci muka baje, su Aminu suka tafi Wakinsu,"

Mardiyya da Malama suka sauke katifarsu sukai kwanciyarsu.

A wannan daren nayi bacci sosai da sosai.

"Washegari sassafe muka tashi da aiki, yara suka ci gaba da kacaniyar shirin makaranta. Na Wakko kuWin"

mota da abun break na basu jarabawa ma suke yi Mardiyya za'a shiga ss 3 karatu ya zo ™arshe za'ace.

Aminu na jss 3 Adda'u za'a shiga jss 1 Malama kuma aji huWu zata shiga.

Har titi na rakasu saida suka shiga abun hawa sannan na dawo bayan na jaddadama Mardiyya kada fa ta

mance sunan layin.

Dariya tayi tace.

"""Ai Ummi akwai ΄an makarantarmu da yawa a layinnan. Mum ma taSa zuwa gaisuwar rasuwar yarinyar"

"ajinmu a layin dake bayan namu"""

Sannan hankalina ya kwanta

A hanyar komawata gida kuwa naita cin karo da ΄an makarantar tasu.

Ina shiga gidan na tarar matan gidan ko wacce tana bakin ™ofarta tana haWa abun kari.

Sai ™amshin toye_toye ke tashi abunma kamar gasa a yadda na fahimta. Matan dake cikin lungummu na

"tsaya duk aka gaggaisa da fara,a na gabatar musu da kaina."

"""Ayya sannu da dawowa Maman Mardiyya. Aini da naga an tashi su Maman ummi nayi mamaki, sai daga"

"baya ne muka ji labarin wai matan ™anin abokin me gidanne zasu dawo su huWu"""

Murmushi kawai nayi mata na wuce ciki.

"Labbai na tsaye tana toya ™wai, Adama na haWa tea a ™aramar robar fenti. Sai kwatsam muka jiyo muryar"

Maigogul yana gaisawa da matan lungun.

"""Sannunku fa. Nine mahaifin Sabuwa uwargidan Babangida wanda suka dawo jiya. Ga mahaifiyarta nan,"

"wannan kuma yarta ce"""

"Nan suka shiga rige_rigen gaishesu, sai washe bakinsu suke yi."

"""Masha Allah Allah ya baku zaman lafiya. Megidan nasu yana kwance a asibiti ne, amman yauma za'a"

"sallamoshi daga asibitin muke anata ™o™arin biyan kuWaWen jinya ma, dake ya jima a asibitin. Ai faWane..."""

"""Maigogul dan Allah ku shigo daga ciki, Rakiya ku karaso"""

Cewar Adama data katse hanzarin Maigogul danta fahimci so yake daga zuwa ya watsarmun da

mutuncina a idanun matan gidan ga gida gidan yawa.

˜arasowa suka yi.

"""Ahh Adama anata haWa haWin murtuk an baro gidan miji an rabu da dumamen tuwo. In sha Allah"

"aurenku sai masu arziki a wannan karon. Sai ku ™ara sanwa dan ko ruwa bamu kurSa ba."" Maigogul yana"

"gama magana ya tsallake ya shigewarshi ciki. Babu mamaki matan lungunmu sunji sak abinda maigogul yace, tunda ko wacce tana bakin aikinta."

Tattare kayan karyawan muka yi zuwa cikin falon. Adama ta zuzzuba ma kowa muka zauna zaman

karyawa tare da tattaunawa.

Maganar dai Waya tak.

Ni dai in yi ha™uri in zauna a Wakina in janye ™ara akwai al™awari mai tsoka da Malama Babba tayi musu

muddin na jaye wannan ™arar.

Wasu zafafan hawayen ba™in cikine ya zubo mun.

Shikenan mu iyayenmu a kullum sunfi fifita abin duniya sama da farin cikinmu. Wato Malama Babba ta

hanyar su Maigogul ta bullo? Wallahi koma menene ™udurinta sai dai ta mutu wallahi sai Babangida ya sake ni ko sama da ™asa zata haWe. Nasan sabida kada aurenta ya mutu ne take son lallai saina janye ™arar dana shigar. In zauna suci gaba da tsangwamamun.

A fili nace da Rakiya da Maigogul.

"Ni wallahi bazan taSa iya janyewa ba. Maigogul nifa sai Babangida ya sakeni, wallahi na fishi taurin kai a"

"wannan karon ni ku ™yaleni kawai ni kaWai nasan halin da nake ciki"""

Duka Rakiya ta kawo mun. Maigogul kuma ya sauke murya.

"""A_a Lolo cewa fa tayi zata iya bamu gida. Kar muyi haka dake, ina laifin me sonka da Wanshi. Shifa"

"Malam da kike ji da gani ingiza mai kantu ruwa yake yi miki. Babu ™auna a tsakaninku, in kin mance bada™alar data faru a baya da irin matsananciyar ™iyayyar da yake yi miki a baya sai mu tuna miki dan ubanki."

Harni zaki ma ba™in ciki tun tasowarku a Waki Waya kuke rayuwa ku da uwarku ya yau ance za'a bani gida

Lolo kina son kawo mana cikas. So kike in bi malamai a kanki a juya miki kai. Ko ko a_a so kike in kwaso

tsofaffin kayan tsubbuna in soma turo miki aljanu ba™a™ene su birkita miki lissafinki bafa tsoronki muke

ji ba.

"Malama Babba har mun faWa mata kin janye ma kin gama shine kike wannan maganar"""

Mi™ewa nayi na shige uwar Waki a guje na faWa gaWo dan ba™in ciki da takaicin dake shirin ™arashe

rayuwata.

Su Adama ne sukai mun tsaye a kaina sai faWa suke yi mun akan in daure ko ba dan komai ba in zauna a

Wakina dan yarana.

Ni dai nasan a musulunci babu wani zaman yara da hausawanmu suke yi. Kaga mace ma an saketa

kamar tsohuwar maiya tace ba zata tafi ba zatai zaman ΄a΄anta.

Maigogul har uwarWakin ya shigo yace.

"""Ku barni da'ita dan ubanta nace. Zata gane kurenta inna dinga yi mata ture ba zata ji da daWi ba. Wai ya"

"zaka haifi yaro ya zama baya jin maganarka Rakiya tawo muje. Kuma duk ku bar mata gidanta taci kanta"""

Ai kuwa ilai suka tarkace komatsensu suka tafi sai ni kaWai. Na jima ina kukan ba™in ciki can baccin

wahala da gajiya ya debeni bani na farka ba sai azahar shima jiyo kiran Sallah nayi rangaWaWau a kunnena kamar a cikin gidan da muke.

"Babu shiri na duro, shi ciwon hawan jini muddin kana cikin ™unci, musamman haWi da ciwon damuwa"

baka taSa rabo dashi.

A zaune nayi Sallah na Waga hannu na dinga ro™on Allah akan ya bani sa'a da nasara akan shari'ar da

"zamu zauna gobe. Ya kuma kareni daga sharrin lafuzzan Maigogul dan wabillahillazi la'ilaha, illahuwa akan gidannan da Malama tace zata bashi, zai iya mun shige shigen malamai dan a rikirkitamun ™wa™walwata, hmm ku dai a gaba akwai labarai da dama da muka tsallakesu dole zamu Wakkosu daga"

tushe.

"Kuma komawa gado nayi na du™un™una, zuchiyata ta shiga aikin tunanin son gano meye manufar"

Malama Babba akan wannan shari'ar da take so in janye tunda ai dama tasan igiyoyin aurenmu a sar™e

suke

Nasan koma menene zata yi ne dan kawai tafi son a kullum taga ina kuka Babangida yana jana a ™asa.

Ni kuma na lashi takobin ja ya ™are a tsakanina da kowa. Dole a sake mu ni in bar gidan mijina in kama

haya. Ita kuma ta koma ™auye ko hannun ΄a΄a.

Sallama naji anata dokawa a falo dole haka na fito kaina na sarawa.

"Ma™otane suka shigo ganin waje, tare da matan gidan."

"Wasu ma a tsaye suka tsaya suna yaba kyan wajen, sune harda le™a uwar Waki. Wata zabiya ce tace."

"""Waje yayi kyau komai nason gyara ji waje yadda ya sha fenti da tsadaddun kaya kamar ba Wakin maman"

"ummi mai kitso ba."""

Sai suka saka dariya. Wata ΄ar ™awutar mata da zata yi Amina madaki a ™iba da duhun fata mai she™i

tace.

"""Ashe an sallamo mijin naku, ai Wazu ΄an uwanshi suka wuce dashi Wakin Waya daga cikin abokan zamsn"

"naki. Ni da nama Wauka a Wakinki zai zauna yayi jinyar har sai ya warke. Maman Bello naga sanda Baban Bello mota ta bijeshi a Wakinta ya zauna yayi jinya"""

"To ni bamma san sun dawo ba, ina ruwana da dawowarshi mutumin da in ina ™aunar mutuwata to ina"

™aunarshi.

"Šan murmushi kawai nayi musu, sukaita hira a tsakaninsu daga ™arshe suka fice."

"Ajjiyar zuchiya na sauke, na shiga kaye_kaye nice harda shara. Kitchen na fito dan in Wan samu ruwan"

"zafi in kurSa. Sai ko ga Sa,a a ™ofar Wakina."

"""Wai ke Sabuwa me kike ji dashi, da me kike ta™ama da har zamu fi awa biyu da shigowa gidannan an"

"dawo da Babangida amman ba zaki zo ki duba jikinshi ki gaishe mu ba?""."

"Wu™ar dake hannuna da na Wauka zan yanka albasa na kalla, take bakina naga ya soma cijewa da kanshi"

tsumin dabancina nason ya tashi.

Abinda kike ji shi nake ji Sa'a. In ke kina jin mara ji ce ki shigo daga ciki in ban faffarWeki ba kice ba

"Sabuwa bace"""

"Zaburowa nayi ina shirin buWe ™ofar. Wallahi saita danna a guje ta bar lungun, a yadda taji ina magana"

"ma kaWai ya isa yasa ta tsorata, kuma a baya tasan waye Sabuwa."

"Ba kince bakya ji ba, dana koya miki ji, inda aka fito da Wan uwan naki ke ki maye gurbinshi."""

Dariya na saka dana tuno yadda ta saka gudu Sakatar_Sakatar ga sifukun zama kamar na masoyiya

"maidoki sai sama da ™asa suke yi. ˜wai na soya na dafa indommie guda Waya, na haWa tea nayi komawata ciki."

"Inaci kamar magani nake ci haka nake ji, bana jin daWin komai"

"Haka naita turawa har yamma lis yara suka dawo makaranta, sai dai daf magriba suka dawo sakamakon"

nisa da muka ™ara yi.

Dole na kira Malam a waya nake sanar mishi sai yace daga makarantar zai sa a dinga haWosu da yaran

Wawo ana wucewa dasu can gidan in yaso in aka tashi makarantar islamiyya Ramadan ya kawo su gida.

"""Amman Sabuwa kin shiga kin duba Babangida da jikin kuwa naji labarin an sallamoshi ko?"""

Kai na girgiza kamar yana gabana kafin nace.

"E an sallamoshi, amman banje ba"""

"""Assha Sabuwa a dinga daurewa yaci albarkacin haihuwa. Ki taimaka mishi yaranshi suga darajarshi. Ki"

kama hannunsu kuje zuwa bayan isha ku duba shi ™ila ma akwai ™arin bayanin da zai zaunar daku yayi

"muku"""

A sanyaye nace.

"To in sha Allah zamu je nagode"""

"""To mu kwana lafiya sai Allah ya kaimu jibin in mun haWu a kotu"""

Ajjiye wayar nayi naci gaba da tu™a tuwona.

"Mardiyya ku samu kuje kuyi wanka ayi Sallah sai azo aci tuwo ko?"""

Malama nan tahau bori ita ba zata ci tuwo ba abinci take son taci.

Ma™ociyarmu tana ji maman Sa'idu tayi dariya tace.

"""Zo ki karSi abinci to. Yarinya fa da gaskiyarta Maman Mardiyya wanne tuwone za'a tareta dashi."""

"Dariya kawai nayi, banso ba amman bana so tayi tunanin wani abun. Taci kwalliya ta gani a faWe, matan"

"gidan gaskiya ΄an gayune sosai, dukkansu kayan kantine a jikinsu, daga masu riga da wando sai masu"

"dogayen riguna, ga abinci na alfarma ko wacce tana yi."

"Kwano ta ciko ma malama da lafiyayyar shinkafa da miya, ga ™atuwar kaza a saman abincin, ga ko slow"

harda WaWWaran zoSo da samosa guda Waya. Da kanta ta ™araso ta mi™o mata lokacin ina juya miyar

zogalena da taji gandar naman kan saniya da dama yake tafashe a firiza tuntuni.

"Ah angode sosai. Wannan ai yayi mata ma yawa."""

Dariya tayi tana ta sake le™a mun miya tana.

"""Ahh babu komai wallahi saci da yayyenta"""

Ana kiran sallar magriba ina gama kwashe tuwona na saka a filas na tuwo da miya Mardiyya ta

shigarmun dashi ciki.

"Saida mukai sallah mu matan kafin muka zauna, mazan masallaci suka tafi, saida na haWa Adda'u da"

Allah akan ya rufamun asiri da an idar ya biyo Aminu su dawo.

Ai kuwa ana idarwa sai gasu sun shigo.

Malama da AWWa'u suka ci shinkafar da Maman Sa'idu ta basu. Mu kuma na zuba mana tuwo a faranti

dukkanmu muka sa hannu muna ci.

Daurewa kawai nake ina wurga loma dan yaushe ma rabon da muci abinci a kwano Waya. Harsu Malama

bayan sun gama cin shinkafarsu saida suka saka hannu akaci tuwon tare dasu. Rabon da inci abinci mai yawan wanda naci yau tare da yarana harna mance.

"Wanka na shiga nayi a ciki na Wan shafa maina sama sama, na Wauki doguwar rigar atampa na zura na"

saka hijabina kalar atampar na tada Sallah.

Na jima a zaune a sallaya ina ro™on Allah nasara. Dan gabana sai naji yanata faWuwa.

Mardiyya ce ta shigo da sallama.

"""Ummi wai Baba yana nemanki inji Maman Usama."""

"Kallonta nayi, itama ni take kallo sai naga ta nemi waje ta zauna."

"""Ummi da gaske jibi zaku shiga kotu ke da Baba wai akan ya sakeki?"""

Idanuna na lumshe kafin nace mata.

"Tabbas hakane jibi zamu soma zaman kotun. Kuyi ha™uri kunji, ke kinfi kowa sanin halin da nake ciki a"

gidan mahaifinki. Mardiyya nasan ke da kanki ba zaki so inci gaba da zama cikin ™as™anci ba. Abinda nake

"so dake shine ki nutsu ki kama mutuncin kanki, da kin samu miji kiyi aurenki ya fiye miki"""

Saita sauke kanta naga tana Wan murmushi sabida na ambaci mijin Aure.

"""Ummi amman a wajen wa zaki tafi ki barmu, ko damu zaki tafi? Ummi da zan baki ha™uri ki ha™ura da"

"nace kiyi ha™uri dan Allah """

Sai kuma ta soma tsiyayar hawaye shiru nayi ina kallonta ina nazari. Ta daWe tana rera kuka bance mata

uffan ba. Da dai naga kukanta na neman kassara kuzarina saina jawota kusa dani.

Dena kuka uhm Mardiyya ke da zaki yi aurenki ki tafi naki gidan mijin ma uhm ai na lura kamar kin samu

"saurayin da kike so ko?"""

Kanta ta sunne sai mukai Wan dariya.

"""E Ummi akwai wani mutum da muka haWu dashi shekaran jiya, yaso karSar lambata nace mishi"

Babanmu yace har sai nayi aure zan ri™e waya.

"Yauma mun haWu dashi a hanyar makaranta"""

A_a Mardiyya me yasa baki kwatanta mishi gidanku ba sai a waje zaku dinga haWuwa? Kema kinsan duk

"randa Babanku yaji ko ya ganki zaki WanWana kuWarki. In kuka haWu ki kwatanta mishi gidanku yazo ya samu Babanku ya nemi izini. In Allah ya dedetaku shikenan kinga Wan gidan Sa'a ya huta duk da shima fitinace kawai"""

Dariya ta saka naga jin daWi sosai a tattare daita.

"To muje ku gaishe da Babanku da jiki. In mun dawo a bani labarin me sunan sirikin nawa"""

Gaba tayi tana dariya.

Ni kuma na sharce wata ™walla mai Wumi.

"Hmmm mi™ewa nayi ni da yara muka je ™ofar Wakin Hamida muka yi sallama, daga ciki ta amsa tare da"

bada izinin shigowa.

MRS BUKHARI

Ga masu son shiga group

https://chat.whatsapp.com/IUKFTeul76p2VaAvQ5nk0U?mode=r_t

IDAN KAYA YA GAJI...

GAMMO MA YA GAJI

LITTAFI NA BIYU

SHAFI NA BAKWAI

BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ˜AMSHI

INA SONKU WALLAHI MASOYANA SON SO SAI DA KU ³AN AMANANA.

Babangida yana zaune a kujera mazaunin mutum uku ya mi™e kafarshi a kujerar ga filo an jingina mishi a

wajen hannun kujerar. Matanshi duk suna Wakin ko wacce tana harWe a kujera rannan nasu kicin _ kicin.

"1 sitter na samu na zauna bance da kowa komai ba, babu wanda yace dani ™ala."

"Yara suka wuce suka duba Babangida sai wani fara'a yake yi musu ta gaibu, su kuma dake ma basu"

sababa

Sam sun kasa sakewa dashi.

"Mardiyya kuje ku kwanta nima ina zuwa"""

"Tashi suka yi suka fice, na dawo da dubana wajen Babangida nace."

"Kasa anyi kirana, gani to"""

Murmusawa yayi tare da cewa.

"""Lolo kenan. Hakane nasa an kiraki domin ina da magana uku da nake son mu tattauna muhimmai, kuma"

"ya shafi iyalin gidan baki Waya"""

Murmushin na mayar mishi ina ™are mishi kallo. Wai yau ni Babangida yake ma magana da taushi? In

baka mutu ba zaka sha kallo shegiya duniya. Katseni yayi ta hanyar cewa.

"""Ga Ramatu nan matatace da Šanmu Waya, sai abinda yake cikinta. A ™a'ida ba dole bane in zan yi aure"

"saina sanar daku ba. Sabida manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ma yayi aure ba tare daya sanar ma iyalanshi ba, sabida ba laifi bane."

"Ganin damane, amman ku mata kun Wauka ma cin amanane yin hakan. Wannan laa ba huruminku bane."

"Wannan kenan, gata nan yanzu kun santa."

Ramatu a iyakar zaman satikan da kika yi damu na san kin riga kin gane lissafin abokan zamanki. Ma'ana

"wacece babba wacece mabi da'ita ko?"""

Ya kalli Ramatu.

A gatsine tace.

"""Zan dai gane in ka ganar dani. Taya ma zan gane da kaina alhalin matan naka girman kai garesu, tunda"

"nazo suke kishi dani mun kasa samun daidaito. """

"³ar Shuwa ce ta Wan ja tsaki, hakan sai ya bani murmushin da sautinshi yasa muka haWa idanu da ³ar"

Shuwa harma dan tsokana nayi na Waga mata kira.

"Ita tasan me nake nufi sarai, a cikin shika_shikan rashin arzikin Babangida bata ga komai ba."

"""To kinga wannan itace Sabuwa matata ta fari kenan uwar manyan yarana da suka fita yanzu itace mukai"

"auren lalle. Sai Hamida gata kin ganta ita ke bi mata, sai maman Fati wacce ta kasance Amarya kafin zuwanki. Da fatan kin fahimta ko?"""

"""Na fahimta."""

To sai batu na biyu shine yafi mahimmanci.

Kunga wannan gidan da muka dawo akace muku za'ayi gyara a wancan namun? To zance na gaskiya ba

"hakan bane. Anan zamu ci gaba da zama wannan rayuwar da muka yi ta a baya ta wuce sai dai mu shiga sabon nema in da rabo sai a samu arzikin da yafi na da"""

"Da mamaki duk muke kallonshi, duk da ni mamakina ™alilinne domin bai shafeni ba. Ta wani Sangaren"

naji daWin jin wannan labari gaya.

"""Ban gane me kake nufi ba Jannaty. Kana nufin karayar arziki ka samu ko kuma me kake nufi da a"

"wannan tsukukun gidan da layin zamu ci gaba da zama. Aikin ka fa, kamfaninka fa motata kuma da aka karSa?"""

Tunda kuka ji Jannaty ai kunsan wake magana.

"Duk tabi ta ruWe dake dama ba zaman auren bane ya kawota ba, gashi na santa da idon cin nera. Ai"

wallahi bata ga komai ba tukunna.

Hamida tace.

"""Baban Usama dan Allah kai mana bayani meke faruwa mu

Please Login or Register in order to submit comment