You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amman ai"

kema tarbiyya Maigogul ne tunda a cikin gidan kikai rayuwarki.

Ashe ke butulu ce Yar Shuwa har haka. Waime Sabuwa ta tsare miki ne haka? Wallahi Sabuwa ko yanzu

"tayi miki fintinkau, ta tafi data tashi tafiya saita warce zuchiyata tayi tafiyarta dashi. Aisha babu komai a"

"™irjina Sabuwa ta tafi da komai, kuma bazan iya karSowa ba. """

Yana isada maganarshi ya ajjiye kuWin cefane akan kujera.

"""Sakwara da miyar kifi za'aci yau a gidan."

Sannan kada ki cika ma doyar ruwa sakwara in ba Sabuwa ce tayi ba bana gane kanta duk saita sake. Ko

"ita zaki kira a waya ta taimaka ta faWa miki yadda take yi ne?"""

Ya ™arashe zancan yana dariya ya barta a wajen zuchiyarta kamar zata toye dan ™una.

Su Mardiyya kuma Babansu na fitowa suma suka fito ko wanne cikinsu zuchiyarshi cike da murna.

Mota suka shiga Babangida ya ja motarshi fu.

Wayarshi ce tayi ruri Sumy ke kiranshi amman bai Waga ba dan tun da dai ta fahimci Babangida ta ™are

"mishi bashi da komai saita buWe faifayin rashin mutuncinta gashi tazo a lokacin da rashin Sabuwa ya ladabtar dashi da kuma al™awarin daya Waukarma kanshi in ba dai da wani ya kama matarshi ba, ko kuma tayi yin™urin kasheshi ba. To babu batun saki haka su ukunnan zasu ci gaba da zama har mai"

rabawa ta raba su.

Suna isowa bakin layin ya hango motar Khalid a ™ofar gidan. Tabbas ya shaida motar sarai. A madadin ya

tsaya saiya kunna kan motarshi zuwa cikin layin. Kafin ya ™araso ya hango Sabuwa ta shige motar Khalid.

Wani yawu mai Waci ya haWiye take jijiyoyin kanshi sukai raWa_raWa. A bayan motar yayi parking. Yana ta

ambaton Allah dan har wani duhu_ duhu idanunshi suke yi.

"""Mardiyya ku shiga gidan ku gaisa da kowa ku fito mu wuce"""

Yadda yayi maganar kaWai yasa kowa ya shiga taitayinshi kawai.

"""To Baba"""

KaWai

Mardiyya ta iya cewa ta tusa ™annenta a gaba.

Yana yin™urin fitowane ya hango mahaifiyar ³ar Shuwa ta le™o tana waige_waige ga waya a manne a

kunnenta.

Jikinshi ne ya bashi ³ar Shuwa ce duk yadda akayi tasa a le™oshi a gani..zuchiyarshi na tafasa Allah _Allah

yake yi ya fito yaje ya samu Khalid ya fesar musu da maganganun da suka daWe a zuchiyarshi.

Bai jira komawar Maman ³ar Shuwa ba ya fito ya tunkari motar tasu.

SABUWA:.

˜ur mukaima juna ni da Khalid.

Wallahi har ga Allah har kuma a cikin raina inason Khalid. Sai dai matsala guda biyu.

Na farko rayuwar da muka gudanar a baya.

Na biyu rayuwar da muke gudanarwa a yanzu tun da aurena a kaina.

Inna Auri Khalid banyi ma kaina adalci ba. Kuma duk bala'in sona da yake yi bazai hanashi zargina ba.

Kuma zai iya fin Babangida rashin ganin darajata da kimata.

Zan iya komawa gidan da yafi na jiya. Ai ina ganin zai fi mun sau™i in Auri mutumin da wani abun bai taSa

shiga tsakaninmu ba. Duk da wannan shine abu mai wuya duk wani Wan mutunci bazai zo neman aurenmu yazo Waya biyu ΄an unguwarnan su barshi yazo na uku ba.

Ina tunanin irin su Khalid sune daidai da irin rayuwarmu.

"Ya Allah ka kawo mun Wauki amman dai irin rayuwar da nayi a baya har abada bazan koma ba, ya Allah"

kayi ri™o da hannayena.

Hannuna da Khalid ya ri™e gam ne yasa na buWe idanuna muka ™urama juna idanu.

"""Sabuwa naga kinyi ™iba kin sake yin haske. Da ganin yanayinki kamar kin samu ΄ar nutsuwa."

Na buWe baki zan yi magana tare da yin™urin fisge hannuna kenan saina ga Babangida ya zuro kanshi

cikin motar ta Sangaren da Khalid yake.

Da sauri Khalid ya waiga jin hucin mutum a gefenshi.

Idanu suka haWa da Babangida idanunshi sunyi jawur jijiyoyi duk sun tattaso a fuskarshi.

Da sauri Khalid ya saki hannuna ya haWe ranshi shima.

"""Kai a tunaninka kaci nasara ka rabani da Sabuwa ko? Hmmm ka sani duk wanda yayi guga da nufin zai"

Webi duniya ko ya jawo bazai ga komai ba. Ka neme ta da aurena a kanta ma balle yanzu da saura kwana uku ta gama idda. Ke kuma kin kyauta dama halinki ne.

Abu Waya nake son sanar muku wallahi _wallahi wannan mitsiyacin bai isa ya aureki ba. Yadda na rasa

"shima sai dai ya rasa. Sannan in dai irin hannun wannan ™azamin kike son komawa ai kinyi gwari kuma kinci baya. Mutumin daya nemeki yake kwanciya dake, ya kai ki hotel_hotel shine harda yo miki tsarabar rigar mama da Wan kamfai, da sigari da aure a kanki shine kike tunanin gidanshi zaki koma kuma ki samu"

"nutsuwa, shi kike tunanin ki aura Sabuwa?"""

Murmushi yayi mun idanunshi tamkar zasu zubo da ruwan hawayen da suka taru yace.

"""Kinyi gwari Cus kinyi gwari Cus. Ajjiyeki zaiyi a gida yaita zarginki, kuma ba zaki taSa burgeshiba neman"

matanshi zaici gaba dayi ya lalata miki rayuwarki a banza daga ™arshe hawan jinin dana Waura miki ya kasheki a banza.

"Dake ke jahila ce ai lissafinki bazai kawo mik..."""

Ya isheka nace Babangida ka sani kai ba ubana bane. Kuma na yarda na gamsu zam auri Khalid ko dan in

™unsa maka ba™in cikin da zai yi ajalinka ko yayo maka sanadin kamuwa da cuta marar warkewa kamar

dai yadda ka haddasa mun hawan jini.

"Yaya kuke so in saka kainane"""

"""Rufa mun baki ko in bubbuge bakin naki wallahi """

Ya Waga hannu Khalid ya cabke.

"""Sanda take gidanka ma..."""

Fisge hannunshi Babangida yayi ya sha™e wuyan Khalid da mugun ™arfin da Khalid ya kasa ™watar kanshi.

Fitowar yaran da Maigogul ne yasa ya sake wuyan Khalid.

Da sauri na fito a motar yaran suka nufo ni.

Maigogul kuma ya nufo wajen Khalid har jikinshi na rawa.

Sororo Babangida yayi yana kallon yadda Maigogul yake Sare_Saren son karasawa wajen Khalid har

yatsu Maigogul ya take mishi.

"""Ummi ashe kina waje. Ina wuni?"""

Cewar Mardiyya da take kallona cike da fara'a.

"Ina nan ai banga shigowarku bane shi yasa. To ya karatun? Aminu, Yaya AWWa'u yaya rashin ji? Malama"

"yaya rashin son magani."""

Babangida yace.

"""Ku dallah ku tawo muje ni na gaji"""

Jin yadda yayi maganar da zafine yasa yaran sukai saurin juyawa.

Da harara ya bini kawai ya tusasu a gaba suka wuce.

Maigogul yana wajen Khalid yana zubar da mutunci.

"""Ke Lolo tawo mana me kike yi a tsaye da yara ki barsu su tafiyarsu"""

Yana juyowa yaga ni kaWaice a tsaye.

"""Au ashe sunma tafi ai dai yafi."

Kinyi ba™o maimakon kiyi ciki dashi a_a sale_salin ΄an unguwa su ganku aje a tareshi ai mishi munafurci.

"Ki kaishi can gidanku """

Wani ™ududun ba™in cikine yasa nace.

"Ai mun gama Maigogul."""

Ina faWin haka nayi shigewata ciki na barshi da Khalid Win.

Ya suka ™are oho ya dai shigo ya nemi gefen gado ya zauna yana dandalan yawu yana ™irga kuWi.

Rakiya sai harara take zabga mishi.

"""Wai Sabuwa shi wannan Win da dai batun aure yazi dai ko? Naga akwai gari a hannunshi ni dai na shaida"

"mishi nanda kwana huWu ma ya turo magabatanshi"""

A_a Maigogul wallahi ni ba aurenshi zanyi ba. Gaskiya karma ka karbi kuWinsu Rakiya ki saka baki fa a

wannan karon ba yadda zanyi ba wallahi. Yaushe ma na gama warkewa akan ciwon ba™in cikin

"Babangida """

Takalmi ya jefo mun nayi maza na rufe fuskata.

"""Mara kunyar kawai ni zaki ma ba™in ciki dan abu ta kazan """

Mi™ewa nayi da sauri zan gudu yako yi nasara ya tare ™ofa.

"""Yau ga tsiya da wasali ™asa. Wai meye haka ne Maigogul karyata zaka yi ne ko me?"""

Yana huci ga takalmi a hannunshi yace.

"""Kinga wata shirgegiyar mota ce fa tazo wajenta Rakiya baki ga wanda yake cikin motar ba yaro matashi"

mai tsabta. Ga kuWi yanzu wannan kuWin da kika ga ina kirgawa duk shi ya dun™ulo ya bani har jikinshi fa

yana rawa.

Dama meye dalilin da yasa muka nace ta zauna a gidan wancan fitsararren tambaWaWWen yaron ba

sabida arzikin da take ciki bane? To kuma yanzu Allah ya aiko mata da wani shine zata ce bataso. Ga

yayyenta da ™annenta babu ma mai shinshinarsu in banda Adama da gobe za'a Waura aurenta.

Tana gani nine kwana a buzu ina buga ™asa hakan baiyi ba har saida muka bi ΄an tsubbu kafin auren ya

kusan tabbata zamu ce.

Shine wannan yarinyar zata mun haka?

"Rakiya ™yaleni da'ita nace"""

Tare suka haWu sukaita zagina Rakiya ta rufeni da duka Hauwa ce tazo ta fincikeni.

"""Ke Hauwa babu ruwanki ki bari Rakiya ta ladabtar mana da'ita kaga ΄ar ba™in ciki""?"

Ficewa nayi a gidan ina haki na koma can gidanmu. Ina shiga Khalid ya kira wayata a zaure na tsaya na

amsa wayarshi.

"""Sabuwa ashe aurenki ya mutu shine kika kasa sanar dani, ko dai kina sha'awar komawa gidan mijinki ne"

"ni ina can ina haukana a kanki?"""

Ajjiyar zuchiya na sauke. Na samu damar saisaita kaina dan na fahimci in banyi ma Khalid dabara ba

wallahi sai dai inji labarin an Waura mana aure.

Harga Allah bana fatan sake faWawa matsala. Maganganun Babangida sun sake farkar dani ainun.

"Ba haka bane. Dama ni niyyata shine inna kammala iddata sai in neme ka."""

Murmushi yayi mun yace.

"""Burinmu ashe ya kusan ciki Sabuwa. arayinki yananan a rufe madam Wina ma tuni na faWa mata aure"

"zanyi in saka matar a wannan wajen""."

Murmushi nima nayi mishi tare da cewa.

Amman ai ina bu™atar lokaci. Maigogul ya shigo yake sanar mana cewar ya faWa maka nan da kwana

"huWu ka turo. To a zahirin gaskiya ina bu™atar kamar wata biyu masu kyau ko babu komai ai ya kamata in gyara jikina. Kuma yanzu haka gobe za'ayi bikin Yayata, ni kuma goben ma tafiya zamu yi da Uzairu Zuchiyata."""

"""Uzairu zuchiyarki fa kika ce?"""

Dariya nayi nace.

Au kishi ya motsa kenan? Yayanane uwa Waya uba Waya. Kano zamu je gobe dashi akwai abinda zamu yi

"ne"""

Bamu gama wayar ba saida na tabbatar Khalid ya janye da batun turo magabatanshi nan da kwana huWu

an Wage sai zuwa wata biyu masu zuwa.

Har a cikin raina bana jin zan iya aurenshi ko da maza sun ™are. Amman ina tsoron yin saki na dafe. Naso

batun bikin Adama ayi komai dani ko cikin abokan ango zamu dace duk da ko wacce cikinmu ro™onta shine ta dace wani abokin ango ya ™illota yace yana so.

Da tunanuka ratata na wuni. Dik da dai muna ta hira ana yima Adama tsiya sunje sun siyo kayayyakin

bacci harda wanduna shine su Aisha da yaranta da suka zo zamu kwana tare suke ta mata dariya.

Sai naji ina kewar nawa yaran da yanzu suna gefena.

Amman inna tuno Babangida ya tafi da tulin buhunhunan Sacin rai da kishi sai inji wani sanyi a zuchiyata.

"Tabb yau babu zaman lafiya duk wacce take da girki yau zata gane kurenta in tayi wani wargi."""

Washegari sassafe dan masifa muka wuce tasha ni da Uzairu Zuchiyata yaci uban gaye ya ™wama gogul

yayi kyau sai kamanninshi ya sake fitowa sak da Maigogul.

Maigogul har tasha ya raka mu bai baro tashar ba ™arewarta har saida motarmu ta tashi.

˜arfe taran safiya a Kano tayi mana.

Uzairu zuchiyata ya kira wani abokinshi ko ina suka san juna oho sai gashi anzo har tasha an Waukemu a

"™atuwar mota, ni dai ina bayan mota nayi zuru."""

Mrs BUKHARI ce taku

Babangida :.

"[8/24, 10:16 AM] BADA'AT IBRAHIM:"

https://chat.whatsapp.com/IUKFTeul76p2VaAvQ5nk0U?mode=ems_copy_c

IDAN KAYA YA GAJI...

GAMMO MA YA GAJI

LITTAFI NA UKU

SHAFI NA GOMA SHA BAKWAI

BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ˜AMSHI

BABANGIDA:.

Tu™in cikin rashin nutsuwa yake yi. Babu nutsuwa tattare dashi ™wa™walwarshi sai hasko mishi fuskar

Sabuwa da Khalid take yi.

"""Yanzu kana ji kana gani zai rabaka da matarka ya kuma aureta kai kana kallo?"""

Zuchiyarshi ce ta shiga tunzurashi.

Tsaki ya saki kawai ya girgiza kai.

"""Ina wallahi bazan taSa bari haka ta faru ba. Sai dai ni dashi mu rungumi juna mu mutu amman ba dai ya"

"auri Sabuwa ba."""

Wawan burki yaja a daidai bakin layinsu.

"""Ku sauka kuje akwai inda zanje"""

Yayi musu maganar a kausashe. Babu shiri suka sakko yaja motarshi fuu sai majalisa dama acan suka yi

da Mustapha zasu haWu ya karSi motarshi mashin Winshi ma yana majalisar.

Ko daya ajjiye motar bai zauna ba cewa yayi dasu yana zuwa. Kai tsaye ya nufi gida Baba Malam yana

zaune a kujera cikin almajirai yana karSan karatu Babangida ya shiga da sallama.

Ita data zame mishi wajibi ita ya amsa amman dur™uso da gaisubar Babangida basa gaban Baba Malam.

"""Baba Malam dan Allah kaimun aikin gafara kaimun izini in dawo da Sabuwa Wakina tunda har yanzu"

iddarta bata cika ba.

Wallahi tunda muka rabu ban sake samun kwanciyar hankali bane. Kuma a yanzu wallahi na tuba na

dena duk abinda nake yi. Nayi maka al™awarin bazan sake sakin ko wacce mace ba ba kuma zan sake

"jajiSo Aure ba"""

˜ur Baba Malam yayi yana kallonshi yama rasa me zaice dashi. Domin dashi da shi ai sun san saki ne da

babu kome a tsakaninsu. Ha™i™a yaga Wimuwa da gushewar tunani tattare da Babangidan.

Yau ga ranar da yake yawan tunatar da Sabuwa zuwanta tazo. Murmushi yayi yace.

"""Bakin al™alami ya riga daya bushe. Hala baka san ™arfi da zafin shari'a bane ko?"

To ka sani in ma sabida uwarka kake yi Babba ta bar gidana kenan har abada.

Kasan har saida na rabu da'ita na samu nutsuwa kuwa? Kai yaro tashi ka kama gabanka kada ka sake

zuwanmun da irin waWannan yashasshun zantukan. Inma turoka akayi ga amsa ka samar in kayi wasa ΄ar

"gaisuwar taka da nake amsawa sai in dena nan ba wajen wasa ko wajen gwaji bane"""

Da sauri Babangida ya mi™e har yana tuntuSe ya fice a makarantar ya nufi gidan Malama Babba. Acan ya

tadda Kawu Manga a tsakar gida sunata tattaunawa duk akanshi ne.

Waje ya samu kusa da Kawu Manga ya zauna jiki a mace ya gaishesu dukkansu kana ya Wauki tagumi.

"""Toh kin dai ji abunda ake ciki. Nayi nayi ya amince yaronnan yaci gaba da koyarwa a makarantar Wallahi"

"ya™i fur. Dana matsa ma sai ya dena magana. Nifa Babba bana ganin lefin Yaya sabida a tsari na tafiyar rayuwar Yaya shi yadda da amincewa Waya ne tak. Daga ranar daka ci amanarshi ko ka aikata abinda zatonshi bai zata ba shikenan kai dashi yadda har abada"""

Malama Babba tace.

"""Toh shikenan babu komai tunda haka Malam ya zaSa ai. Babangida nayi nayi dashi ya Webi kadarorina"

"yayi amfani dasu tunda yana da ido a harkar baban bola amman ya™i. Filina sukutum na mallaka mishi ya samu ya gina ya zuba matanshi a ciki ya™i amsa, nice zanyi mishi ginin yaronnan wallahi ya™i. Ni ba daWin wannan faWi tashin da yake yi nake ji ba. Nace to ya sai da filin ya samu mota ya Wan dinga hawa yana"

"sana'a da'ita duk dai abinda aka kawo Babana ya™i yadda."""

Babangida yace..

"""Ba™in amsa nayi ba. Ke Malama ce kina da saninki kada sona ya rufe miki idanunki. Ba daidai bane ki"

Wauki wani shashe na dukiyarki ki bani ni ni kaWai ba tare da kinba sauran yaran naki ba.

Inma lallai akwai bu™atar hakan dole saida amincewarsu Wari bisa Wari da saka hannu kan takaddar

"yarjejeniyar cewar an bani abu kaza da amincewarsu bakuma ya cikin gado, ko hakan akayi an tauyesu."

Malama in kowa ya yarda Kudidi da Sa'a ba zasu taSa yadda ba. Ayi ha™uri kawai ina kan nema da izinin

Allah komai zai wuce.

"Ni da magana nazo Kawu inason in mayar da Sabuwa Wakinta gaskiya """

Idanu Malama Babba ta zare kawai sai ta saki kuka kawai. Kan Babangida ya sake cajuwa shi kaWai yasan

irin azabtuwar da zuchiyarshi take yi. Ga wani irin masifaffen kishin Sabuwa da yake ta danne mishi numfashinshi.

"""Kul ka kuma zuwa mana da wannan maganar. Ni dai ko bayan raina kada ka sake gayyato mana Sabuwa"

"cikin haularmu, sannan ai kasan aurenku ya ™are har sai in Sabuwa ta yi wani auren ta fito ko? Ya kake"

"son sake saka mahaifiyarka a cikin mawuyacin hali alhalin kasan a cikin halin jinya take."""

Mi™ewa yayi har wani jiri na dibarshi.

"""Kuyi ha™uri bazan sake wannan zancan ba in sha ALLAH wannan shine jarabawata son Sabuwa shine"

"™addarata."""

Fita yayi a gidan yana haWa hanya.

Sai da akayi magriba ya shiga majalisarsu daidai ana cin abinci. Lokali ya zara ya dinfa cunkusa abincin

bama tare da yasan me yake yi ba.

"""Maza wai lafiya ko kuwa Sumy ce ta zaburar dakai ne haka? Hmmm kasan Allah da ace nasan haka"

matan yaren ibra suke da irin wannan masifar babu abinda zaisa in taimaki yarinyarnan Allah nake faWa

"maka. Yarinya tabi duk ta fitini kowa ni kaina bata ™yale ni ba kai Adeiza masifa ce"""

"Murmushi Babangida yayi kawai tare da girgiza kanshi. Amman ya kasa cewa uffan, yayi hankali bazai"

taSa sake fitar da maganar iyalinshi ba.

Lokalin ya ajjiye ya zuba zoSo ya sha ya idasa cika cikinshi. Kafin ya mi™e.

"""Kunga bari in samu in rarrafa anayin isha ina da Walibai yau sai mun haWu gobe."""

A hanya ya tsaya ya siya kayan tea leda biyu Waya nasu Waya nasu Mardiyya.

A gurguje ya shiga gidan ya ajjiye mashin Winshi da ledojin biredin ya fice.

³ar Shuwa:.

Babangida yana fita ta Waga waya ta kira Mama a waya.

"""Mama a saka mun idanu akan Babangida ya tawo dashi da tsinannun yarannan zai kawo su wajen"

"Sabuwa. Naga kanshi yana rawa kamar so yake ya dawo da'ita ma fa. Dan cemun yayi har maganar ta faWa ma."""

Mama daga cikin wayar tace.

"""Ah haba dai wane mutum ai wallahi bai isa ya mayar da Sabuwa ba ta fita kenan."

"Yaran basa nan da kaina zan saka miki idanu akan komai."""

Da wannan sukai sallama ³ar Shuwa ta datse wayarta tayi jigum akan kujera tana ta aikin tunani.

Ai kuwa sai can Mama ta yo mata filashin da sauri ta kira. Mama ta labarta mata ai Babangida ya haura

layin harma ya kori Sabuwa gida daya taddata tana taWi.

"""Da gaske in muka yi sake kina ji kina gani Sabuwa zata dawo gidanki. Abunyi shine gobe ki ™o™arta kizo"

nan gida sai mu je wajen wani boka zai faWa mana duk abunda ake ciki. In muka ji nasan matakin da zamu Wauka akai.

"Ga Adama ma gobe za'a Waura aurenta ai na faWa miki ko?"""

Tsaki ³ar Shuwa tayi tace.

"""Shikenan goben zanyi ™o™ari inzo muje Allah yasa ya barni kinsan shi da shegen kafiya. Bari in je cefane"

"Mama sai mun yi waya"""

Wayar ta datse ta wancakalar a kan kujera. Ta jima tana aikin tubkar mugunta a zuchiyarta sai da ™yar ta

"samu ta mi™e ta sake gyara Wakinta, ta sake zanin gado ta wanke banWakinta tas. Kana ta rufe Wakinta suka tafi cefane ita da ma™ociyarta Jamila ™awarta."

Suna tafe suna tattauna matsaloli sabida itama Maman Abdul Win saura sati biyu mijinta ya ™aro aure.

Duk ta ™arar da rabin kayan Wakinta bokaye nata faman cin kuWinta suna ta mata ™aryar auren bazai yiwu ba tana zaune zaice ya fasa amman har saura sati biyu bata ji yace uffan ba. Sai shirye shiryen biki da yake ta ™arfi. Yau danginshi ma suka kawo mata akwatin dannar kirji. Daga haka tayi saranda.

Har suka je suka yi cefanen hira Waya ce suke yi har suka shigo cikin gidan.

"Matan gidan ko wacce tana kitchen anata girki, wasu kuma sunata shirye_shiryen Waurawa."

Ramatu tana ™ofar Wakinta anata mata lalle ja.

Sumy kuma tana Waki ta ™ure wa™ar yarensu tana ta bi.

Ita bata fitowa cikin matan gidan zaman hira sam. Asalima bata kallon kowa kota fito abinda ke gabanta

take yi. Hatta su ³ar Shuwa basa gabanta asalima kallon raini da gazawa ta ko wanne Sangare take yi musu.

Jiki a mace zuchiya cunkushe da tunanuka ³ar Shuwa ta dinga aiyukanta. Ta sha wuyar dakan

sa™wararnan sosai da sosai. Saida ta gama ta aika yara suka karSo mata kular Ramatu da Sumy. Ramatu dai ta bayar da tata kular.

Amman Sumy sai cewa tayi da ΄an aiken ace ta ™oshi.

Saida Yar Shuwa ta gama komanta ta sha wankan yamma ta nufi Wakin Sumy domin da sanar mata dalilin

da yasa bata karSan abinci duk ranar girkinta. Dake yau zuchiyar tata a kusa take.

Ai kuwa tana shiga kitchen Win Sumy ta sameta a tsaye tana kaWa ™wai ga taliyar ³an yara a kula taji kifi

da kayan lambu.

"""Wajenki nazo malama"""

A rainace Sumy ta juyo tace.

"""Ay to shiga gani nan"""

Hararar juna suka yi ³ar Shuwa ta ja ™aramin tsaki ta shiga.

Tana shiga taga atampopi da shaddaji sunfi kala talatin a ™asan kafet gasu sababbi dal dal kuma bana

akwatunanta bane dan fes ta haddace kayan akwatunanta tsab. Zama tayi taci gaba da ™are ma falon

kallo komai yana zaune a muhallinshi.

Cikin yau™i irinna matan da suka jima a bariki bariki ta sansu suka santa.

"""Gani Allah ya sa lafiya. Kuma Allah yasa inji alkhairi"""

"""Kusan ba lafiyar bace ta kawo ni ba gaskiya. Na zone cikin lumana in tambayeki dalilin da yasa duk ranar"

girkina bakya cin abincina sai dai kiyi naki kici ke da agolan Wan da kika tawo mana dashi. Naga in Ramatu

"ce take girki ai kina ci. Shin abincin nawa ne babu daWi, ko kuma tsabtatace baki yadda da'ita ba da bakya cin nawa abincin yau dai inaso in sani. Dan kwanaki nayi ma Jannaty magana yace in bar zancan."""

"""Au ashe ma yace ki bar zancan shine baki ji maganarshi ba kenan?"

To ni dai bani da lokacin amsa wannan tambayoyin wanda ya zaunar dani in yana da abun faWa shi zaice.

"Kinga anata kiran sallah kinsan mu akan lokacinta muke yi. Ku dama Shuwa Sallah bata damesu ba"""

Tana faWin haka ta shige ™ofar da zata sadata da ciki ta bar ³ar Shuwa bakinta a hangame. ˜wafa tayi ta

taso ta koma Wakinta tana jiran Babangida ya dawo ayi wacce za'ayi.

Tana sallar magriba ya shigo ya ajjiye mata ledar biredin karyawa ya fice tasan kuma sai goman dare zai

shigo.

Tana zaune har ya dawo yaran duk sunyi bacci.

Waje ya samu ya zauna da sauri ta tarbeshi harda murmushin dole. Duk da kishinshi ne fal zuchiyarta

Allah ya gani tana mutuwar son Babangida gashi ta Wauki kishin Duniya ta Waura akan Babangida.

"""Wanka zaka soma yi ko abincin zan kawo maka""?"

Šan gajeren tsaki yayi yace.

"""Wankan dai. Abincin ki saka a firji da safe zanci a ™oshe nake tam"""

"Kanta basai ya Waure ba. To ranar data fita a girki ma baici abincinta na safe ba, baici na dare ba. Gashi"

"yauma yanaso yace mata bazaici ba. Ita kanta Ramatu da take karSan abincin sau da dama tana ganinta zata kira almajirai ta basu, duk da dai tana ci ba kamar Sumy da bata ci ba."

A sanyaye taje ta haWa mishi ruwan wankan.

Yana wankan ita kuma ta saka abinci a firji ta sake WaWWakan tsumi banda wandda ta dinga Wirka da

yamma har danshi take yi dab magriba.

Kayan baccinta ta saka mai Waukar hankali kayan da in dai ta saka ranar kam ba'a cewa komai ne.

Amman yau kam ko kallo bata ishi wanda akai dominshi ba. Asalima zazzaSi taji a jiknshi kau dole ta

"Sallo fanado ta bashi ya watsa ya bi da ruwa. Haka ya kusan kwana, ko ace ya kwana akan sallaya ko da yayi sallar ya gaji a wajen yayi bacci."

Duk rashin bacci ishasshen dake idanunshi kiran sallar farko ya mi™e ya shiga banWaki ya goge bakinshi ya

Wauro walwala da zai fita ya tashi ³ar Shuwa ya fice.

Saida yabi Wakuna biyun ya tashesu. Har zai fice a Wakin Sumy yana jaye da hannun Amir tace dashi.

"""Ji mana wallahi ka takama matarka wannan yar Shuwa Win kunne na fita buWewar idanu da zallan"

"iskanci ai kai ka sani. Wallahi Allah ka ja mata kunne kada in kamata in zauneta."""

Kai ya girgiza yace.

"""Ke kenan faWa bakya ko gajiya Sumy bakya ko jin kunyata da nauyina ji yadda kike Waga mun murya a"

"gaban yaro"""

"""Wa wai namijin duniya shi zanji kunya? Ka yaudari kanka kasan babu wata kunyarka da zanji. Yadda"

"baka ragamun ba, yanzu babu ragama Win da zanyi ina dalili ma to"""

Tana faWin haka ta shigewarta ciki. Shi kuma ya ja hannun Ameer zuwa Sarayin su Mardiyya.

Su Aminu ya kira suka tafi masallaci. Basu suka shigo ba saida rana ta fito sukai nafila kana suka shigo.

Šakin su Mardiyyan ya sake komawa ya saki Ameer ya tafi wajen uwarshi.

Shayi da biredi da ™wai Mardiyya ta ajjiye ma Babansu a gabanshi.

Murmushi yayi daya tuno irin tsugunan sak da Sabuwa take yi in zata bashi abinci irinshi sak Mardiyyan

tayi.

"""Allah yayi muku albarka. Yau babu islamiyya anyi hutu ko?"""

"""E Baba amman muna so zamu je gidan Anty Alawiyya yau suna"""

Sai da ya cinye biredin bakinshi yace.

"""Af ashe yau suna kinga na mance shaf. To shikenan ai sai ku shirya kuje. Iyayen naku ma dukka zasu je."""

Malama ce tayo carab tace.

"""Baba Adda ita take koyama su AWWa'u karatu. Ko AWWa'u?"" Ta ™arashe zancan tana kallon AWWa'u."

"Mardiyya ta harareta dan bata so ta faWa mishi ba"""

"""Mardiyya da gaske ne ke kike shiga ajinsu AWWa'u. Ri™on ™warya aka baki ko ajin Baba Malam ya baki ne?"

"Kai amman nayi farin ciki gayaa"""

"""A_a ba ri™on ™warya bane yace in dinga koyarwa a islamiyya ne kafin a dawo hutu sai in shiga sahun"

"koyar da matan Aure tunda dai na kammala karatuna, kuma yace zai dinga biyana albashi duk wata. Amman Baba inason zuwa jami'ar in

Please Login or Register in order to submit comment