You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi mata amman ban tuno ba."

"Mustapha wallahi saina koya ma Sabuwa hankali. Sai taji a cikin ranta ta tsaneni ta kuma tsani bariki. Cikin da take takama dashi saina zubar dashi dan ubanta ko zan mutu ba zata haihu ba."""

Haka dai sukaita tattaunawa tare da jinjina girman matsalar da Sabuwa ta saka abokinsu a ciki.

Babangida ya buWe fitar dare da neman mata a cikin kwana biyunnan sosai. A tunaninshi hakanne kaWai

zai wanke mishi damuwar da yake ciki. Dan ba ™aramin matsala yake ciki ba.

Baba malam:.

Dama jira yake yi a sallamo Malama Babba daga asibiti ya tara zama yayi musu aman abubbuwan da

suke cin ranshi da irin binciken da ya saka akayi mishi akan Babangida da ita kanta malama Babban lokaci kawai yake jira yasa a zauna yayi musu amai.

Bincikenne bai kammala damuwa kuwa sai cin ranshi take yi a kwana bakwai da zuwan Sabuwa Dattijon

saida yayi rama. Kallo Waya zaka mishi ka gane baya cikin nutsuwarshi

Sabuwa

A kwana bakwai da nayi a gidan anyi rikice_rikice masu yawa.

Dan duk waWanda suka zo ganina ba'a barinsu ma su shigo tun daga waje ake taresu a hanasu. Daga

haka sai rikici ya tashi.

"Nima nayi yin™urin fita kusan sau uku abun yaci tura, a yin™uri na huWunne na samu nasarar ficewa da"

misalin ™arfe Wayan dare motar su Yar Shuwa na bayan layin suna jirana.

A guje na ja motar muka wuce fuu sai Club.

Ina bayan mota sai sigari nake sha ina jina fayau dani tsabar jin daWi

Kwanana bakwai cib babu sigari babu yawo ™afafuna sun gaji har ™ai™ayi suke yi mun.

Ai kuwa muna shiga club na faWa filin rawa na shiga ti™ar rawa ina aikin shan sigari.

Ban jima da shiga Club Win ba Babangida ya shigo carab idanuna suka sar™e a cikin nashi duk da wuta mai

kalar dake kunnuwa ta Wauke kanta bamu kasa gane juna ba.

Kamar mahaukacin zaki haka yayo kaina a lokacin wani namiji na shafa jikina.

Fisgata yayi zuwa waje ina turjewa yana jana cike da mugunta.

Bayan motarsu ya buWe ya jefa ni ya rufe.

Ina hangoshi ta taga dafe da kanshi yayi shiru

Nasan Babangida mutum ne mai mugun kishi akan abinda yake so

Nayi mamaki daya nuna kishinshi a kaina a tunanina ai ya tsananeni shi da na farkema laya..

³ar Shuwa da saurayinta ne suka ™araso wajen motar.

"""Lafiya zaka jawo yarinya ka turata a mota. Tare nake dasu fa"""

Cewar saurayin ³ar Shuwa.

"""Dan abu ta kazanka zaka san tare kake dasu. Ba ni kake cema tare kake dasu ba?"

Ina zuwa.

Nan Babangida ya soma nannaWe hannun rigarshi

Ai kuwa ya Wane wuyan saurayin ³ar Shuwa faWa harda fasa kwalba da yankan juna.

Ni dai ina mota inata aikin bubbuga murfin motar ga zafi kamar zai kasheni.

Da ™yar abokan Babangida suka jayeshi suka turashi a mota. Mai motar ne ya cilla mishi keyn mota a

cinyarshi.

"""Kuje ka mayar da'ita gida ka dawo ka same mu."""

MRS BUKHARI

Sai mun haWi ranar litinin in sha Allah

"[8/14, 7:22 AM] +234 802 205 9556:"

https://chat.whatsapp.com/JmCasXpUuuT0J6dfLTWFNk?mode=ac_t

.

18066696785.

Hussaina Bello

HAJIYA KAYAN KITCHEN KIKE SO MASU SAU˜I DA KYAU. KO KUMA SARIN KAYAN KITCHEN KIKE SO KI

SOMA KIN RASA INA ZAKI SAMU AKAN FARASHIN DA KEMA ZAKI SAMU ALKHAIRI?

H@H AVAILABLE WHOLESALE AND RETAIL DUNIYA NE

MAZA TUNTUE HUSSSAINA BELLO KAI TSAYE A LAMBAR WAYARTA.

KO KUMA SHIGA CIKIN ZAURENTA DOMIN KASHE ˜WAR˜WATAR IDANU

IDAN KAYA YA GAJI...

GAMMO MA YA GAJI

BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ˜AMSHI

LITTAFI NA UKU

SHAFI NA BIYAR 5

*SON SO MASOYAN AL˜ALAMINA*

*WANNAN SHAFIN DOMIN SOYAYYARKU NE MASOYAN ASALI INA JIN DAŠIN YADDA KUKE NUNA

˜AUNA GA AL˜ALAMINA. YA ZAME MUN DOLE IN FARANTA MUKU KAMAR YADDA KUKE FARANTA

NAWA RAN SON SO *

Ai kuwa da mugun gudu ya figi motar saida kaina ya gwaru.

Haka yaita watangaririya da rayuwarmu a titi.

Yana yi yana kutuntumo manya zaguna yana Wumamun.

Nima bakina kunsan bazai taSa yin shiru ba yana zagina ina ramawa.

Wallahi sai kawai ya faka a gefen wata unguwa ya fito ya dawo gidan bayaa ya kama wuyana ya sha™eni

sosai.

Taimakona Waya akwai wu™a a jikina jin ina kiciniyar zareta a gidanta yasa ya saki wuyana.

Na shiga sauke numfashi. Gashi ya haye kaina yayi kane_ kane.

A cikin motar ya tumurmusheni tas har saida ya samu biyan bu™atarshi.

Yana haki yace.

"""Wallahi saina sa da kanki kinyi nadamar zuwanki gidanmu"

Kin ga wannan tsinannen cikin da bama nawa bane kika li™a mun?

In sha ALLAH shine ajalinki tare zaku mutu dake da tsinannen Wan dake ciki saina zubar da cikinnan

wallahi.

Sabida ke tacacciyar ³ar balaja'u ce shine har zaki fito kuzo Club wani Wan iska na shafa ki. Kuma kike

"tunanin ni Babangida zan yarda cikin jikinki wai nawa ne?"""

Sauka yayi a kaina ya dawo gidan gaba yana gyara zaman wandonshi.

Duk da jikina yayi laushi marata har wani zargewa take yi sabida ba ™aramar mugunta Babangida yayi

mun ba. Amman

baisa na ragama Babangida ba.

Ai kuwa sai di mu mutu mu uku dani da cikin da kai ribar ™afa ™ila harda mahaifinka

Wallahi na tsanake bana ™aunar in buWe idanu in ganka a duniya .

Sabida kana ganin kai Wan iska ne. Ni zakaima ciki kayi tunanin kaci biredi ka yaga leda kuma Maigogul ya

barka?

Kayi kuskure ™aramin Wan iskan dake Soye shi Wan iskane a gidansu.

Ciki saina haifeshi kuma a cikin gidan da aka haifi ubanshi. Shima shegen sai ya taka doron ™asa yayi

adawa da ubanshi.

"Wallahi in bakai wasa ba wannan shegen sai ta zama ajalinka"""

Haka yaja motar har muka iso bayan layinsu muna farfaWama juna maganganu.

Inya faWi goma zan faWi ashirin dan bana tsoronshi sam.

"""Fitarmun daga mota ³ar balaja'u kawai"

"ke da Club har abada duk inda kika je zan kamaki dan dole zan ganki."""

Baba Malam:.

Yana zaune akan sallayarshi yayi raka'a biyu a sallar data zame mishi jiki.

Ya jiyo sallamar Malama ™arama a hankali tare da Wan doka ™ofar shima a hankali.

Mi™ewa Baba malam yayi tare da sake duba agogo.

A hankali ya iso bakin ™ofar

"""˜arama lafiya a cikin darennan zaki tawo?"""

Kafin ta bashi amsa Malama Babba ta ™araso wajen.

"""Me zan gani ni da kwanana Karama na son ™wace mun miji?"""

"Ta faWa ba'a faWa ba, ba da wasa ba amman. Dan tasan halin mijinsu sarai. Kuma tasan a cikin halin da"

Babangida ya saka gidan.

Kallonta kawai yayi ba tare da yace mata uffan ba.

"""Ina jinki ™arama menene?"""

"""Uhm dama Alawiyya ce tace mun wannan yarinyar da take zaman Babangida bata nan ta gudu."

"Na dudduba cikin gidannan kab har banWaki amman malam bata nan"""

Kai Baba malam ya shiga jijjigawa yatsanshi Waya saye akan leSenshi ya Wan ciza.

Malama Babba babu shiri tayi ™asa da kanta tana jinjina girman munafurcin ˜arama. Da kuma kalar

rashin tarbiyyar Sabuwa.

"""Ya zame mun dole in san menene mafita. Duk da Yaya Hanne tace in bar komai har zuwa gobe ta iso"""

Malama Babba a zuchiyarta take maganar.

Wucewar Baba malam ne ya dawo da'ita hayyacinta. Taji dai sun yi magana amman Allah cikin ikonshi

bata ji me yace ba.

A tsaye a wajen ya barsu. Yana ™ulewa Malama Babba ta sha gaban ˜arama dake ™o™arin barin wajen.

"""Wato sabida dama kina hassada da irin son da Malam yake yima Babangida shine kika tawo sanar dashi"

"halin da ake ciki sabida ya sake tunzura ki kara mishi wutar tsanar Babangida ko?"""

Murmushi Malama ™arama tayi tace.

"""Wallahi ko Waya a tunanina dukka kuna nan tare tunda nasan kece da miji. Kuma a gabana kika zo kika"

wuce zuwa turaka.

"Babba babu dalilin da zaisa in yi hassada da soyayyar da Malam yake ma Babangida. Babangida Wanane,"

kuma son da Malam yake yi mishi ai baya nufin su ragowar yaran baya sonsu. Sannan hatta ni dake ko wacce tana da Wa mafi soyuwa a gareta wanda tafi ™auna.

Babu kyau dai nuna fifikone domin ina tunanin yana daga cikin kuskuren da aka aikata har aka samu

"wannan matsalar ma data afku"""

Tana kaiwa iyakar nan tayi tafiyarta.

Malama Babba dake jan numfashi da ™yar sabida ciwo da kuma nauyin kalaman da ˜arama ta faWa mata

yasa ta kasa ma magana.

Wannan itace rana ta farko a cikin tarihi da ˜arama ta mayar ma da Babba martani a iyakar tsawon

rayuwar da suka yi tare.

Da ™yar ta daddage ta shiga Wakin Baba malam ta kwanta a kan doguwar kujera tare da shiga dogon

tunani da fargaban abinda zai biyo baya. Ta wani Sangaren na zuchiyarta tana ro™on Allah yasa kada

Sabuwa ta sake tako gidannan.

Baba malam kuwa yana fita ya le™a Wakin samarin yaranshi su shida da sukai ragowa.

"Auwalu, Ramadan da Magajin malam ya taso suka soma zagayen neman Sabuwa cikin tsakiyar dare"

unguwar babu motsin kowa da komai.

Suna shan kwanar layin dake bayan layinsu daidai lokacin Babangida ya faka motarshi kenan.

Kashe fitilun motar da yayi yasa bai hasko su Baba Malam ba.

Sabuwa ce ta fito tana kun™unni Babangida ya biyota tare da matseta a jikin motar.

"""Babu shakka Babangida"""

"Cewar Malam daya iso inda suke"""

SABUWA:.

Da mugun sauri Babangida ya sake ni jikinshi har rawa yake yi. Baba malam kuwa sabida tsabar tashin

hankali da ruWu kusan faWuwa yayi daga tsaye. Da sauri magajin malam da Ramadan suka tareshi.

Babangida kuwa kanshi ya sauke ™asa jikinshi na wani irin kakkarwa.

"Ni kuwa sai tsilli_tsilli nake yi da idanuna"""

Baba Malam ya kafe mu da idanunshi kallon ™yama da tsana yake watso mana.

"""Daga ina kuke Sabuwa?"""

Ya tambayeni murya a kausashe.

"Daga gidan rawar dare muke"""

"""Shi ya nemi kuje kenan. Dake ke shashashace wacce bata da hankali baki san inda yake miki ciwo ba"

"shine kika bishi? Mutumin da yayi miki ciki ya kafa tarihi mai muni a rayuwarki ya nemi ya tsere miki shine har kika kuma bashi yadda. Kuma a gidana za'ayi wannan iskancin ni Baba Malam?"""

Ni dai ban tanka ba.

"""Yayi kyau ki wuce mu tafi. Daga yau in kika kuma fita wallahi zan yi mummunan saSa miki zaki yi"

"mamakina sawa zanyi a ban™areki"""

Iyakar abinda ya faWa kenan ya juya magajin malam da Ramadan na ri™e dashi

Bayansu na bi muka bar Babangida a tsaye a wajen.

A tsakar gida kuma Alawiyya da Malama ™arama muka tadda

"""An ganota kenan Malam?"""

Kai kawai yake girgizawa ba tare daya iya furta wata kalma ba.

Malama Babba tana kwance taji shigowar Baba malam ya tsaya a kanta yana kallonta.

"""Kin cutar dani sosai Saratu. Amman ki sani abinda kika aikata sai yafi damunki fiye da ni."

"Za kuma kiga matakin da zan Wauka wanda daga ke har Baban naki bazai muku daWi ba."""

Zama yayi yana huci kawai. Ji yake yi tamkar ya cire zuchiyarshi ko ya huta da irin zugin da take yi mishi.

Vidiyon Babangida da Sabuwa sai sake haska kansu da kansu suke yi a ™wa™walwar Baba malam. Tunda

yake bai taSa ganin mace dana miji a rungume da juna a cikin gida ma ba a waje ba. Amman sai gashi yau yaga Babangida ido da ido rungume da mace a tsakiyar layi. Idanunshi kawai ya lumshe.

Tsugunnawa tayi a gabanshi tana hawaye. Tayi magana ta kasa sabida ba tasan me zata ce ta kare kanta

"ba. Tasan bata isa ta iya fahimtar da Malam har ya sake yadda dasu ba, shi sau Waya tak yake yadda da mutum."

"""Ai dole Saratu ki kasa furta kalmar da zaki kare kanki da Šanki."

Ki fitarmun a Waki bana ko ™aunar in buWe idanuna nayi tozali dake. Babangida kuma har abada ya fita a

raina kenan. Kinsan Allah ba shi kaWai ba hatta da zuriyar da Babangida zai tara bazan taSa jin na

™aunacesu ba abadan.

"Tashi ki fita, ki fita nace ko in bar muku gidan baki Waya"""

Ya ™arashe maganar cikin Waga murya.

Cikin Sacin zuchiya ta saka kai ta fice tana rausa kuka tamkar yarinya ™arama.

A wannan dare haka wannan iyaye suka sake kwana idanunsu biyu ras.

Asubar fari Baba malam ya sanar da ya dawo da zaman da za'ayi yau. A kira yaran duk a sanar musu

"takwas na safe za'ayi zaman."""

Babangida:.

Su Baba Malam na juyawa ya runtse idandunanshi gabaki Waya babu laka a tattare dashi. Bawai tsoron

"dan an gansu tare yake yi ba, tsoronshi a yadda aka gansun, dakuma irin tashin hankali da zai ™ara saka"

Malama Babba a ciki su suka fi komai Waga hankalinshi.

Da ™yar yayi da gaske ya shiga motar ya ja zuwa Club Win. Da ba dan mai motar na can yana jiranshi ba

bazai koma ba.

Amman ko da yaje bai wuce uku da rabi na dare ba suka saukeshi a bayan layi ya shige gidan Kawu

Manga ta hanyar haure katanga.

Ko da ya shiga Wakin ya tarar da ˜asimu yana kan dadduma yana ta tilawa da halama sallah yayi ma.

HaWe girar sama data ™asa Babangida yayi dan ko da ˜asimu ya juyo da nufin tuhuma fuskar Babangida

saita tsoratashi sosai

Babu shiri ya mayar da hankalinshi kan abinda yake yi.

Babangida ya mi™e ya fita tsakar gida dan bacci ya gagareshi..

Ruwa ya diba a randa a bokiti ya shiga banWaki ya tsarkake jikinshi kana ya dawo ya ta da Sallah.

Da asubar Fari Malama Babba tayi kiranshi akan za'ayi zama yau ba gobe da Malam Baba yace ba.

Amman bata san ko za'a bu™aci yazo ayi zaman dashi ba.

A sanyaye Babangida ya sauke wayar a kunnenshi tare da sauke gwauran numfashi.

SABUWA:.

Ni kam ta Sangarena ina komawa ciki nayi baje_baje akan katifa sai bacci.

Sai daf asuba Alawiyya ta tasheni.

Da ruwan sanyi na tsarkake jikina ina idar da Sallah na yi komawata gado.

"Abuna, bani na farka ba sai wajen bakwai da minti goma, shima Win Adama ce ta kirani a waya."

"Adama da sassafe kira haka kin tashe ni a bacci"""

Sai cewa tayi.

"""Wallahi kuwa kinga dama dai yau zamu sake zuwane Maigogul ne ma yace zai kawo mu ke harda"

magazin babu wani shege ko shegiya da zasu hanamu shiga yau.

"A shirye sosai zamu tawo"""

Dariya na saka.

Kice unguwa yau zata Wauki harami ga Maigogul ga Mazagin kinga ai babu magana. Sai kun zo dan ALLAH

Adama in zaku tawo ki kawo mun littattafan hausa zan Wan kakkaranta nifa zaman ya isheni ban saba da haka ba.

Jiya ma na fita ai.

Nan na labarta mata duk yadda fitar da dawowar ya kasance.

Dariya tayi.

"""To zan yo miki rentin amman ina kawo miki zaki lale kuWaWen mutane ki basu dan mai rentin Win bata"

da mutunci ko na mis™ala zarratin dan ko daWewa littafinta yayi saita yi rashin mutunci kuma sai an ™ara

mata kuWi.

Baki na taSe ganin shigowar Alawiyya da masa da miya da kunun tsamiya.

"To shikenan sai kun karaso baro in karya sai zuwa anjima"""

Datse wayata nayi na karSi abincin dake hannun Alawiyya.

Tana bani ta fita. Ni dai ina daga Waki matan gidan masu aure duk wacce tazo sai ta Waga labule ta ganni

ta taSe bakinta.

Ko wacce da irin nata salon da take le™owa dashi. Ni dai inata harkokin gabana ko in kula dasu har dai

suka gaji suka gama.

"Gidan cike da hayaniyar muryoyin maza da mata, harma da yara ™ananu."

˜ila wani taron akeyi a gidan yau.

"Ina gama faWar haka a zuchiyata na mi™e na fito tsakar gidan na yi zamana a kan turmi ina yanke farce,"

ina kallon yadda suke ta shigewa Sarayin Baba Malam.

Murmushi nayi ni kaina nasan ba ™aramin saka Babangida da iyayenshi nayi a uku ba.

BABA MALAM:.

Manya manyan taburmaine malale a farfajiyar shayyar Baba Malam.

Yana zaune a kujera wan sita. Yaranshi maza da matan suna ta shigowa kamar dai yadda ya bu™ata. Sai

daga can kusa da ™arshe can sosai kafin Malama Babba ta tawo Yaya Hanne na biye da'ita.

"Baba malam yayi ™ur ya zuba ma Yaya Hanne idanu, ya mayar da idanunshi tsakiyar idanun Malama"

Babba.

Sai da suka nemi waje aka zazzauna kana Baba malam yayi gyaran murya ya soma da sallama. Duk suka

haWa bakunansu wajen amsa sallamar tashi.

"""Kafin in soma magana a kan abinda ya tara mu anan. Hanne inaso ki yi ha™uri ki jira Babba a Wakinta."

"Wannan taron na cikin gidane"""

Yaya Hanne ta dubi Baba malam ta dubi Kawu manga kafin tace.

"""Zamu tafi ni da Manga ™aninka kenan?"

"Dan in ni bare ce a cikin wannan maganar to Manga ma ai bare ne ko?"""

Baba malam bai yi mamakin abinda Hanne tayi mishi ba. Dan a baya ma babu irin zigin da bataima

"Malama Babba ba akan dole saita Sokare mishi. Har anyi lokacin da ya dakatar da ita Malama Babba zuwa duba Hannen sai dai ita tazo ta dubata. Gadararta shine mijinta hamsha™in mai kudine kuma su ΄an boko ne sosai. Kuma tana matu™ar son Malama Babba tana taimaka mata. Duk wani kwancen kayanta masu tsada tsada Malama Babba take bama ita ta soma bata kwancen gwal, ita kuma ta soma"

bata kwancen atampa supa da aura.

"""Babba kisa Yarki ta tafi ta jiraki a can falonki"""

Bata da yadda zata yi tasan halin mijinta ba daWi gareshi ba yana da bauWaWWen hali.

Da ™yar ta jaye Yaya Hanne ta fita zuwa falonta.

"""Ke Saratu haka mijinku yake tsinkaki a gaban kishiya?"""

Ta faWa tare da ™an™ance idanunta irin na masifarnan.

"""O_o _o_o Wanki ne ya jawo mun. Kinsan tunda ya aikata wannan abun wallahi in faWa miki Malam bai"

"sake sakin fuskarshi dani ba."""

"""To meye naki ke a ciki halin Wan yau? To ni dai ki cire tsoro ki sanar mishi ciki bana Babangida bane"

fa™at. Kuma kiyi ™o™arinki cikin ya zube ki tabbatar yarinyarnan taci maganin dana kawo miki.

"Ji yarinya a tsakar gida tanaima mutane kallon WaWWaya almura idanta kamar soyayyar gyaWa"""

Malama Babba da sauri ta fita ta koma wajen taron.

"""Wawo a buWe taro da adda'a"""

Wawo yana daga zaune ya buWe taron da adda'a kafin Baba malam yace.

"""Dangane da batun wancan shashashan Wan iskan yaronne Babangida. Shine dalilin taruwarmu anan"

sabida tunda abun ya faru inata aikin nazari da binciken duk daya dace.

Kuma naga saka hannun mahaifiyarshi ta Sangarori manya wanda hakan ba ™aramin mamaki ya sanya ni

a ciki ba.

"To abu na farko dai shine. Kamar yadda nace Babangida ya bar gidana, to ina nufin ko bayn raina ban"

yadda yaronnan ya dawo cikin gidannan ba zaici gaba da zama tare da Manga.

"Kai Manga"""

Baba malam ya dubeshi.

Cike da tsantsar ladabi ya amsa.

"""Na'am Yaya"""

"""Sai kasa idanu sosai akan su ˜asimu dan gudun kada ya lalata maka tarbiyyarsu ya rusa maka ginin daka"

daWe kana ginawa. Ni da a so nane ma yabar gidan naka ya shiga uwa duniya.

Amman dana je Ringim nake labartama Kawu da Goggo Amfana halin da ake ciki. Suma sai suka ce lallai

Babangida ya zauna a wajen naka tunda dai kai kaji zaka iya.

Wannan itace maganata ta farko.

Maganata ta biyu kuma itace.

Sabuwa zata ci gaba da zama a gidannan har saita haihu zata bar gidannan.

Sannan na saka doka duk wanda a cikinku ku mata matannan kuka sake takalar yarinyarnan tazo tana

mana rashin mutunci a gida zan saSa muku.

Idan ta haihu zata bar gidan izuwa gidan Babangida zan sa a Waura aurensu ta tare a matsayin matarshi

"suje can su reni abinda suka haifa yafi ace suna yawo gidan rawa_ gidan rawa, dan wani cikinma sai ya sake Wirka mata ba komai bane."""

Shiru yayi yana nazarin fuskar kowa.

A cikinsu babu wanda yaji daWin hukuncin daya yanke musamman mata_matan.

Malama Babba kam hawaye ma take ta sharewa.

"""Dangane da batun Sata tarbiyyar da nace Babba na da saka hannu ciki shine."

Na daWe da hana Babangida mu'amalar abota da yaronnan Mustapha Wan gidan Baba na shago. Sabida

yarone da sunanshi yayi ™auri a unguwa.

Bincike ya tabbatarmun da sahalewar Babba yaci gaba da abotarshi da yarannan ba tare da sanina ba.

Sai abu na biyu tana sane da yawon dare sarai da Babangida yake yi. Da saninta yake yin wannan yawon

daren. Sabida bata son Sacin ranshi ita a kullum ta saka Babangida farin ciki. Wanda daga tsakiya ga

abinda yaje ya jajiSo mana jibi yanzu ba hawaye take yi ba? To in dai Babangida ne kukanma banyi tunanin in an soma ba.

Sabida a cikin wannan halin da ake ciki har rashin kunyar Babangida ta kai ya kira Sabuwa su fita zuwa

gidan rawa har yana iya rungumeta a layi wa'iyazubillah

"Tarbiyya, da ilimin addinin dana Waurashi akai bai amfaneshi da komai ba kaico. Magajin malam sunji"

tsoron sanar dani fitar dare da Babangida yake yi dan gudun su jefani a mawuyacin hali. Wai ashe har

"™ananun kaya yake sakawa yaita yawonshi a gari ma. Kuma ita Babba tana sane sarai"""

"Duk waWanda suke cikin wajen taron hankalinsu ba ™aramin tashi yayi akan lamarin Babangida ba, dama"

abinda ya aikata jiyan.

Wannan wani sabon lamarine a cikin wannan zuriyar mai Wauke da Wumbun tarbiyya da ladabin yi nayi

bari na bari.

Malama Babba taji tsoro da fargaba irin wanda bata taSa ji ba a rayuwarta. Shikenan ashe ma duk

"abinda suka Tsara da Yaya Hanne babu aikin da zaiyi anan. Bata da kalmar da zata iya dawo da martabarta da kimarta a idanun Baba malam ko Qur'ani zata haWiye tana aman surori bazau kuma yadda da'ita ba. Ita yadda Waya ce a wajenshi, baya kuma bayar da wata dama ta biyu bare har aje ga ta"

"uku."""

Kai Baba malam ya girgiza yace

"""Ko akwai wanda yake jin yana da magana ko wata shawarar?"""

Babu wanda yace shine ba dan basu da abinda suke son faWe ba. Sai dan kawai gudun fishin Baba

"malam da faWin abinda ka iya tunzurashi yayi fishi da mutum"""

"""To shikenan tunda babu mai magana na sallameku dukka, banda kai Manga """

Kafin su soma yin™urin tashi suka jiyo hayaniya mai ™arfi a tsakar gidan harda ihun wani almajirin Baba

malam da halamar wata muguntar akai mishi.

Šuu suka fice matan harda Wan gudunsu dan son ganin menene ke faruwa.

Suna fitowa suka tadda ΄an uwan Sabuwa ne a tsakar gidan Almajiran Malam Baba na ™o™arin hanasu

"shiga shine har aka yanki magajin malam a hannunshi."""

SABUWA:.

Ina zaune a tsakar gida na jiyo hayaniya daga nesa tanata tahowa. Murmushi nayi dan nayi imani su

Adama ne suke shirin zuwa ganina.

Ai kuwa ban aune ba sai gasu a tsakar gidan almajirai nata faman tattaresu.

Magajin malam magazin ya ri™e yana ja ai kuwa kamar ™ibtawa da bismillah Magazin ya zaro wu™a ya

"yanki tsintsiyar hannunshi ya sake shi babu shiri, tare da yin wani ihu. Ihun da yayi sanadiyyar fitowar su"

"Sa,a Šuu."

"""Meye haka ke faruwa. Me zan gani?"""

Cewar Malama Babba wacce dama a cikin ba™in ciki take.

"""Abinda kika gani shi kika gani. Ku dai kuna da neman fitina wallahi. Babu damar azo ganin Lolo sai ku"

"hana Malam ya hana Malam ya hana. To ko makawuyane yau dai dole yayyen Lolo su ganta"""

"Maigogul ke magana cikin Waga muryarshi akan Malama Babba."""

Tare da Kawu Manga Baba Malam ya ™araso wajen.

"Zuwanshi yasa yaranshi suka soma zamewa, ko wacce na jaye Wanta."

Malama Babba tace.

"""Allah ya wadaranku ku dai baku da kunya ban taSa ganin marasa kunyar iyaye kamarku ba. Ace kana"

"uba amman kaine jagora..."" Da mugun kallo Baba malam ya kafeta ™irjinshi na sama da ™asa."

"""Hattara Dattijuwa bari kul Wallahi. Kin ganni nan na sari mutane sunfi dubu, har kisa nayi an kulleni"

"amman na fito. Wallahi ko a barmu muga Sabuwa ko in tsigema wata kunne a gidannan"""

Kafin suce wani abun Babangida da shigowarshi kenan ya ru™un™une Magazin ta baya yana ™o™arin fitar

dashi.

Ai kuwa nan kokawa mai haWari ta shiga gudana a tsakankaninsu.

Magazin ya samu Babangida ya dinga naushinshi a duk gaSoSin da yasan zai karya mishi kuzarinshi.

Baba malam yana tsaye ya hana su Wawo raba wannan faWan. Sai gwabza dambe akeyi.

Zaro wu™ar da magazin yayi ne Babangida ya danna a guje magazin yabi bayanshi.

"""Kuje Wawo ku raba faWan maza"""

Yayi maganar cikin ba da umarni.

"""Maigogul na fahimci dukkannin take takenka burinka yin fito na fito da nine. Burinka ka kunyatani a"

idanun duniyane.

"Ku matan ku shiga ku ga Sabuwa, amman duk abinda zaku ce mata sai dai kuce mata ayau."

Wallahil azeem babu wacce zata sake shigowa cikin gidannan da zummar ganin Sabuwa In kuma da'ita

zaku tafi gata nan. Kuje ku yi duk shelar da zaku yi. In aka sake kawo mata ziyara abinda kuke tunanin

"yiyuwarshi bazai yiwu ba. Ya kamata ka gane jama'a na ganin ™imata"""

Juyawa yayi zai bar wajen. Maigogul yace.

"""Ai na faWa na maya muddin muka tafi da Sabuwa to tabbas sai abinda kake son burnewa ya fito"""

"""Saime ya fito mana. Nima bari kaji duk ranar da wani ko wata daga Sangarenka ya sake zuwa da"

zummar ganin Sabuwa to tabbas Wana bazai taSa aurenta ba ka sani bana magana biyu. Ka kuma fice mun daga tsakiyar gida babba dakai a shekaru a ido gaka babu laifi sai dai kash hauka da hauragiya su

sukai maka ado

"Ke kuma ki shige Sarayinku"""

Fuu Baba malam ya fice a gidan yana faWan maganganu domin ranshi yayi matu™ar Saci ainun.

Jinshi yake yi kamar ba shi ba. Hatta gidan da mutanen gidan gani yake ba su bane.

Jin wannan furucin sai jikkunanmu dukka suka mutu. Maigogul babu shiri ya fita.

Ni kuma na ja su Adama muka shige ciki.

Yaya aka ™are da magazin da Babangida oho.

Muna daga Waki muka jiyo kukan Malama Babba sai bata ha™uri akeyi.

Fuu ta shigo cikin Wakin da nake ta rufeni da shegen duka.

Banyi niyyar ramawa ba sabida inason sake jefata cikin uku.

Šauke numfashina

Please Login or Register in order to submit comment