You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kafin ya isarma da Mustapha sa™on Babangida.

"Mustapha yace dama suna hanya shi da matanshi gashi nan ™arasowa """

"Likita na tsaye a kanshi yana aunashi, ga nurse a tsaye da kwando Wauke da takaddu da magungunan"

"marasa lafiya"""

"""Malam Babangida ka daure ka rage ma kanka damuwa sabida jininka ya samu ya sakko. Kaga jinin bai"

sauka yadda ya kamata ba. Tunda dai kai musulmine dole ka yarda da kaddara me kyau ko akasin hakan.

"Ka duba iyalinka da iyayenka karka kashe kanka a banza yaranka suna bu™atarka a raye"""

"Dr ya dinga mishi nasiha tare da bashi musalai masu yawa, har da jawo mishi hadisai da ayoyin Qur'ani"

mai girma.

"""Nagode sosai Dr. Komai zai daidaita in sha Allah."""

Idanunshi ya runtse zuchiyarshi ke tuka mishi.

Har aka gama wanke mishi ciwon aka sake yima wajen dressing Babangida idanunshi arufe sai ajjiyar

zuchiya yake saukewa.

Bawai baya jin zafin ciwon bane har cikin ranshi yake jin motsin zafin. Amman zafin da zuchiyarshi take

Wauke dashi ya doke zafin ciwon zafi.

"""Yanzu ka samu kaci abinci kasha magangunanka, sai ka daure kayi wanka. Amman sai dai a goge maka"

jiki da tawul kada a kwara maka ruwa a jikinka.

"Magungunan ya mika ma Ramadan, yayi musu sallama ya fita."

"""Ramadan taimaka mun in soma watsa ruwan tukunna, ji nake kamar na shekara babu wanka."

"Ramadan ya taimaka mishi suka shiga bayan gida, shi ya goge mishi jiki da tawul, ya buWe mishi sabon"

brush yayi. Alwala ya Wauro mishi ta hanyar shasshafa mishi ruwa ya kuma taimaka mishi suka fito.

"Saida yaci abinci, yasha tea, ya haWiyi magungunanshi kafin daga gadon ya soma rama sallolin da ake"

binshi.

Duk wannan bidirin bakin ³ar Shuwa bai rabu dayi mishi sannu ba. Daidai da sannunta sau Waya bai amsa

"ba, inda take ma bai kalla ba."

Mustapha da iyalanshi ne suka turo ™ofar suka shigo suma ni™i_ni™i da kayan abinci a basket.

"Daga me ciki, sai me goyo, sai me jego a matan Mustapha."

Gaggaisawa akayi kafin Mustapha yace

"Dukkanku ku bamu waje zamu tattauna in mun kammala kwa dawo"""

"Matan Mustapha da Ramadan suka fice, ³ar Shuwa kuma ta gyara zama ita a tunaninta ai duk abinda"

za'a tauna yana da ala™a dasu.

"""Ke me kike nufi da ba zaki fice ki bama mutane waje ba?"""

Babangida ya faWa da Waga murya yana zare idanu tamkar zai cinyeta.

"""Kayi ha™uri jannaty da bata maka rai da nayi natuba."

"Amman kaga yanzu haka daga gida aka turo mun hoton Sabuwa ita da wani a zaune"""

A razane ya kalleta yana son ya furta kalma harshenshi ya gaza haWa kalmomin da za'a fahimta.

"""Ya haka baiwar Allah, ya ina ganinki da hankalinki zaki faWa ma mara lafiya irin wannan maganar"

"kuma?"""

Cewar Mustapha kenan.

"""Ka kyaleta wallahi so take zuchiyata ta buga in mutu a raba musu gadon dukiyata ki fice a Wakinnan"""

Cikin fushi tayi ficewarta asibitin ma ta bari baki Waya dan ji take da badan Babangida jinya yake yi ba bai

isa ya daka mata tsawa bata mayar mishi ba.

"""Mustapha yaya kuka ™are dasu Sumy ne da Ramatu, wayata na hannunka ko?"""

"""Tana wajena dukkansu so suke dole sai sun zo asibitinnan sun duba ka. Kasan Allah da ace dukkansu"

sunsan a wanne asibitin kake kwance da tuni sun Saro maka aiki.

Amman ni ba wannan ba batun Alhaji Abubakar Baban Bola shi yafi Waga mun hankalina in fa bawan

Allahnnan kudinshi za'a biya shi Babangida wallahi dukiyar daka tara kab sai ta ™are kuma bata kai ka

biya shi kuWinshi ba. Nace kenan asirin rufin bakin da akayi mishi tsawon shekaru shine ya karye?

Cewa nayi ko zan kuma komawa Inugun ne in samu malamin a sake rufe bakin shi Alhaji Abubakar Baban

"Bolan?"""

"Kai Babangida ya shiga girgizawa tunda Mustapha ya soma magana, saida ya jefo mishi tambayar ™arshe"

ya samu zarafin cewa.

"""Kaiya Mustapha bakin alkalami ya bushe. Ai tunda Alhaji Abubakar Baban Bola ya samu baki ya fallasa"

wannan maganar taje har kunnen Kawu Manga da Wawo kaima kasan tabbas Baba Malam yasan da

maganar. To shi in an rufe bakinshi su iyayena da ΄an uwana yaya zanyi dasu? Asirina ya riga daya

"fallasu"""

Mustapha ya busar da iska daga bakinshi yace.

"""A_a Babangida kacigari karka sare. Har su Baba Malam Win ba sai a sa a rufe musu bakinsu ba? Talauci"

"da tsiyane fa suke shirin tukaroka. Ka bari a sake sabgarnan kaci gaba da dama dukiya"""

Hannu ya Waga mishi hakan ya tilastama Mustapha yin shiru.

"""Mustapha ba zaka gane bane. Mu ajjiye wannan maganar a gefe ta riga tazo ™arshe mu dawo maganar"

"Sabuwa zuchiyata jinta nake tamkar zata tarwatse Mustapha. Kai a tunaninka wanne matakin ya cancanta in Wauka wanne hukunci zata karSa ita Lolon?"""

"""Hmm ni a nawa muguntar duk runtsi kada ka saketa tunda abinda take so kenan. Kaga duk bala'i dole ta"

ha™ura da wannan Wan iskan. Ai tunda takai ™ara kotu kada ka sake ka saketa. Sannan in ka saketa

"Malama fa sakinta Baba Malam zaiyi"""

Dafe kai Babangida yayi yana kallon Mustapha.

"""Kotu ta kaini akan me wai?"""

Nan Mustapha ya bashi labari. Dariyar da tafi kuka zafi da ™una yayi.

"""Zata ga sharri. Lolo zata gane kuranta sai tayi nadamar shigar da wannan ™ara, kazalika sai tayi nadamar"

"tunzurani da tayi. Zata ga makircin lauyoyi kuwa shi kuma farkanta zai sha mamaki wallahi"""

Sun daWe sunata tattaunawa da Mustapha kan yadda zasu Sullo ma lamarin.

"""Kaga fa wayarta na hannuna amman babu ma chaji farkan nata yaita kiranta tare da tura mata kalmomi"

"daWaWa akan ta kwantar da hankalinta. Tana fitowa daga gidanka zasu yi aure. Duk iyakar runtsi kada ka sake a rabu da'ita wallahi"""

Tari Babangida ya soma babu shiri Mustapha yayi shiru da bakinshi. Babangida yayi juyin duniya

Mustapha ya bashi wayar Lolo amman ya™i fur ya kaWa ya raya fur Mustapha ya hana wayarnan.

Mikewa yayi yai mishi sallama ya fita akan da yamma inya taso aiki zai zo.

Yana fita Hamida ta shigo ta nemi waje ta zauna a farar kujerar dake gefen gadon.

Babangida kuma yana jingine shiru yanata lissafin halin da zai shiga in Alhaji Abubakar Baban Bola ya

"™wace dukiyarshi, ga shariar sabuwa dole tana bu™atar makiran lauyoyi masu yima mutum sharrin da sai ya tsani shari'a. To su kuma ba ™aramin kuWi suke bu™ata ba."

Wani Sangare na zuchiyarshi yanata jaddada mishi ya saki Sabuwa kawai ya huta tunda ba sonta dama

yake yi ba.

Wani shashe na zuchiyarshi kuma sai yaji yayi nauyi. Sosai da sosai

MRS BUKHARI

Ina manyan mata masu capacityn suke? ku fito lambarku ce ta fito.

³ar uwa turaren wuta kike nema nau'ika daban_daban masu musulmin ™amshi da kama muhallu? Ba

itacen banza masu sanya gida ™auri da hayaki kamar an kunna taohuwar bespa ba.

Matso gasu MRS BUKHARI B4B GIDAN ˜AMSHI nazo miki da duk abinda kike bu™ata na ™amshi. Kama

daga turarukan wuta irin na gidan alfarma. Zuwa humrori iri daban daban masu musulmin ™amshi da ri™e jiki.

"Bugu da ™ari muna da turarukan kaya, na fesawa dana turara kaya."

"Muna da kulaccam nau'i daban daban masu gyara jiki da lausasa fata mata, ga kuma ™amshi mai inganci."

Muna da turarukan tsugunno na musamman masu sirri Hajiyata

Muna da room freshener iri_iri

Muna da mopping mix masu kama waje.

Akwai turarukan kafet dana kujeru.

Sannan akwai box _ box setika na Hajiyoyi masu ™yallin goshi.

Muna da Amarya package.

Muna da uwargida package

Muna da maijego package

"Muna bayar da sari ko a ™asar waje kike, muna tura kaya"

Saudiyya

Nijar

Ghana

Camaron

A duk ™asar da kike kayanmu zai iso miki cikin aminci da yardar Allah.

Hajiya akwai Humrar matan aure wannan ta musamman ce.

Duk wani abu da kika sani na ™amshi babu irin wanda bamu dashi a kamfaninmu.

Muna da turaruka designer na maza da mata wanda kamfaninmu ke bugawa Hajiya babu inda zaki je ki

ci karo da mai irin ™amshinki.

MRS BUKHARI B4B GIDAN ˜AMSHI TAZO MUKU DA DUK ABINDA KUKE SO NA ˜AMSHI HAJIYA.

KUNSAN KANURI MUNE ˜AMSHI DAMU AKE KOYI

SIYAN NAGARI MAIDA KUDI

MUNA MARABA DA MASU SIYAN ŠAYA KO SARI.

LAMBAR DA ZA'A SAMENI KAI TSAYE ITACE.

Wa.me/2348179523215

SAI NA JIKU

IDAN KAYA YA GAJI...

GAMMO MA YA GAJI

LITTAFI NA BIYU

SHAFI NA BIYAR

BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ˜AMSHI

INA MI˜A SA˜ON GODIYA GA ŠAUKACIN MASOYANA NA FAŠIN DUNIYA.

MRS BUKHARI TAKU CE.

Sabuwa:.

Bani na farka ba sai ukun rana.

Da hanzari na mi™e amman jiri sai ya mayar dani na koma kan kujera.

Kasancewar yau alhamis yaran suna gida babu islamiyya.

"""Sannu ummi kin tashi. Ya jikin?"""

Mardiyya ta faWa da salon tausayawa. Su Adama ina jiyosu a kitchen kamar ba basu biyu bane.

"Jiki da sau™i Mardiyya ina AWWa'u naga kowa shi banda shi?"""

Sadiya ta fito daga kitchen tace.

"""Gaskiya Lolo yaranki na da shegen yawo. Yau mune har kogi ammman babu shi babu dalilinshi. Muka"

"dinga zagaye gidajen abokanshi wallahi suma abokan basa nan"""

Take na sake shiga sabuwar damuwa dan na lura AWWa'u yana da rashin ji sosai kuma yaron bashi da

tsoro sam.

Ni dai ko da nayi wanka nayi Sallah Allah na ro™a akan Allah ya shirya mun AWWa'u ina ro™on Allah kada

"AWWa'u ya Webo halina ko halin mahaifinshi na sa iyaye a cikin magana """

Kafinma in fito Labbai ta biyo ni da jallof Win taliyar Hausa taji attaruhu da albasa ga kifi an warwatsa.

"""Lolo yaya ™arfin jikin naki? Ki samu ki daure kici abinci zuwa yamma mu le™a ³an asibiti. Naga waccan"

"ba™ar kadarar ta dawo daga asibitin mun haWu da'ita a tsakar gida kinga kallon banzan da take yi mun kuwa? Taci sa'a yau aka sakeni jikina da sanyi da sai naci abu ta kazan ubanta"""

"Adama ce muka jiyo tana rangaWa mana kira da ji ba lafiya ba, babu shiri na tsallake abincin na fito da"

sauri.

Na'ila na gani sha™e da wuyan AWWa'u ga bakinshi na fitar da jini.

"Lafiya meya faru Na'ila. Kai kuma meya same ka sarkin yawo?"""

Tana jijjiga tace.

"""Ai dole kice haka kin koya ma yaro sata. Kamar wannan yaron ace har ya iya shigowa Wakin mutane"

"saWab saWab ya yi sata?"""

Da mamaki na kalleta na dawo da kallona gun AWWa'u. Tabbas ya sata ga rashin gaskiya Saro_ Saro

tattare dashi na gani. Dama bai dena satar ba kenan?

"""Baiwar Allah ai nutsuwa zaki yi ki mana bayani a tsanake ba kizo kina jijjiga ba. In hau kike ji dashi"

"iyayenki ne a gabanki. Ki sake yaron mutane ko?"""

Adama tana ™arashe maganarta ta fincike AWWa'u a hannunta. Ni dai numfashi kawai nake ja da fesarwa.

Kudina gasu ya shiga ya satan mun daga shiga banWaki. Allah yasa yana ™o™arin guduwa ni kuma na shigo.

Narantse da Allah in ya kuma shiga yayi mun sata na lahira sai ya fishi jin daWi.

Ko da yake tarbiyyar da aka koya mishi kenan.

"Uwarshi ma da ranar Allah aka kamata a mota"""

Tana faWin haka naji wani abu ya tsirgamun

Ga yara duk suna wajen sunyi cirko _ cirko.

"""Ke dakata ™aramar ΄ar balaja'u mai tafe da wando. Ya zaki shigo har Wakin mata kina faWa mata magana."

Sata dai ai ba a kanshi aka soma ba. Kuma da kike cewa an kamata a mota ke a kamaki mana. Ya yi satan

"kuma ya saci banza"""

Ai Labbai bata rufe baki ba Na'ila ta shiga Waga murya tana kwaroroto dan mutane suji dama nasan da

"biyu, amman Wan kuka shi ke jama uwarshi jifa. Na'ila kowa yasanta ba ™atamar munafuka bace ita da ™awarta Hamida."

A guje ³ar Shuwa ta le™o tana tambayar meke faruwa ai kuwa Na'ila ta faWa mata.

"A lokacin har Maman Safara,u ta shigo."

"""Uhm Allah ya kyauta. Sata yaro kamar wannan?"

Ashe duk ΄an canjinan da muke ajjiyewa mu rasa shine yake sacewa.

"""Ya sata dan uwarki kiyi abinda zaki yi in baki bar wajennan ba zaki sha mamaki"""

Inji Adama.

"""Hehehe me zanyi kuwa. Kuji da sakin duk da akai muku itama Lolo tana hanya dan baku isa kun tare"

"mana a gida ba"""

"Nayi mamakin yadda akayi ³ar Shuwa tasan auren Adama ya mutu, gara ma na Labbai tunda anyi rikici"

harda motar ΄an sanda.

"""Ayi ha™uri Labbai dan Allah kada ku sake cewa uffan."

Ke kuma maman Fatima ki koma Sarayinki.

"Na'ila tunda dai kinga kuWinki sai kiyi ha™uri duk a taru ayi ha™uri """

Tsaki yar shuwa tayi ta wuce fuu. Adama ta tasanma zagi

Na'ila kuwa saida ta dinga zage_zage tukunna.

Ni tana zage_zagenma na zame na shiga ciki na dira a wuyan AWWa'u kamar Allah ne ya aikoni har gwara

kanshi a bango nake yi.

A tunanina ya dena sata tunda muka baro tsohon gidanmu. Sata babu irin wacce AWWa'u bayayi har

atampa ya sata ya siyar ya kashe kuWin. Nasan jarabawace tunda guda nawa yaron ma yake.

"Su Maman Safara,u ne suka kwaceshi a hannuna duk goshinshi ya fashe, ni kuma sai haki nake yi"

"Maman Safara,u da Labbai ne suka garzaya dashi kemis ni ko dana shiga Waki sai kuka, na daWe ina rera"

"baitukan kuka kafin nayi shiru. Adama na zaune tana cewa in gode Allah a hakanma,"

"Su Mardiyya kuwa kowa ya shiga taitayinshi, ban fiye dukansu ba amman inna tashi dukan yaro ni saina"

fitar mai da jini hankalina yake kwanciya.

Da sallama Labbai ta shigo.

"""Lolo ki daure kici abincin ki tuttura nasa Mardiyya ta kawo miki tea wancan yayi sanyi. Kinga biyar har"

"tayi mu samu muje asibitinnan ko?"""

"Ko magana na kasa yi, ina gani sukai wanka duk suka saka suturuna. Da ™yar nayi ma abincin loma uku"

tean ne ma na rufe ido na shanye na tashi.

"Sallah nayi na sake kayana muka nufi asibiti harda yaran duka, AWWa'u naso barinshi a gida amman da nai"

wani tunanin dole na ja hannunshi muka tafi asibitin.

Hamida na ciki tana ba Babangida tea muka shigo.

HaWa idanu muka yi dashi na wani haWe girar sama data ™asa na nemi waje na zauna.

Su Adama ma da suke yi mishi ya jiki babu na wacce ya amsa.

Yara dai sun yi mishi ya jiki ya amsa musu ciki _ ciki.

"Hamida bata kula kowa ba, babu wanda yabi takanta in banda yara da suka gaisheta."

Jigum_jigum muka zauna na kusan minti talatin.

"To Labbai ku taso muje ko magriba har tayi"""

Mun tashi kenan muka ga an turo ™ofar an shigo

Mustapha ne ya soma shigowa abokanshi suka mara mishi baya.

Suna ™arasa shigowa nayi ficewata su Adama ne suka tsaya aka gaisa kafin suka fito suka same ni muka

wuce gida.

"Sai bayan isha muka shiga gidan. A tsakar gidan muka tarar da Kawu Manga da Wawo, da ³ar Shuwa a"

tsaye tana mi™a ma Wawo key kamar dai na mota ne.

˜arasawa mukayi aka gaisa. Kawu Manga yake tambayar meya samu AWWa'u. Kafin in yi Magana

mandiya tace.

"""Sata ya shiga yayi a ma™ota shine matar tai mishi irin wannan dukan."""

Jim yayi muma duk mu kai shiru kamar ruwa ya cinyemu.

"""Allah shi kyauta. Ai sai a ci gaba da bashi rubutu yana sha ko Allah zaisa ya dena"""

Wawo kuwa girgiza kai kawai yake yi.

A sanyaye mukai musu sallama muka shige Sarayina.

"Duk bamu zauna ba Alwala kowa ya shiga yi, saida akayi Sallah suka soma kiciniyar cin abinci kuma."

"Ana gamawa yara suka tafi Wakinsu, muma muka kwanta"

Ni dai juyi kawai na dingayi har iya awannin da ban isa sani ba.

Washegari:.

Bayan hantsi muka shirya ni da Labbai Adama yaranta sunzo wajenta dama tace ita ba zata je wani

asibiti ba.

"A can muka tarar da ΄ar Shuwa da Hamida, Kawu Manga da Wawo ma suna Wakin muka shigo."

"Ba'a ko gaisa ba wasu mata su su biyu suka shigo da ganin kamanninsu uwa da ³a ne, ga yarinya da bata"

"wuce ³ar wata takwas ba a ri™e a kafaWar wannan dattijuwar, wata kyakkyawar matashiya na biye da'ita"

"""Ohh Babangida ashe haka jiki ya tsananta ji hannunka yadda ya aune"""

Inji wannan dattijuwar.

Ni yaron dake ri™e da hannunta ma nake kallo yaro mai kama da Babangida tamkar an tsaga kara.

To su kuma suwaye waWannan na faWa a raina

Bani kaWai ba harsu Hamida wannan Wan yaro suke kallo.

A murya kawai na fahimci Babangida bashi da gaskiya yadda duk ya daburce yana zare idanu.

"""Bayin Allah ina wuninku, yaya kuma me jikin?"""

"""Jiki da sau™i gashi nan"""

Hamida ta ba dattijuwar amsa a yatsine.

"""Baby yaya ™arfin jikin naka kaga yadda ka rame kuwa? Na kira Mustapha sai yi mun hanya hanya yake yi."

"Ni kuma ina ganin lokaci yayi da zan bayyana kaina ga iyalinka sabida tsoron halin mutuwa ko dan sabida wannan yaron"""

Inji wannan matashiya.

Mu dai duk munyi tsit muna sauraren ikon Allah

Dattijuwa tace.

"""Gaskiya ne kam. Ni kaina sai bayan kwanciyarka a asibiti nayi nadamar biye muku da nayi a matsayina"

"na uwa. Yarinyarnan tun sanda labarin rashin lafiyarka ya sameta take cikin damuwa sabida abokanka kab sun kasa faWa mata a wanne asibitin kake."""

Babangida ya kalli su Kawu Manga da sukai tsuru_tsuru ya dawo da idanunshi kanmu kafin ya runtse

"idanunshi tare da dafe kanshi da hannunshi mai lafiyar"""

"""Hajiya mu bamu gane ba fa. Ku Win su waye ne daga ina?"""

Cewar Wawo da kanshi yafi na Kawu Manga daurewa. Ni kam tuni na gane matarshi ce tabbas ko kaffara

babu.

"""Bawan Allah ka tambayeshi wa™a a bakin me ita yafi daWi ai. Ke Ramatu jeki ki zauna acan baki fiye"

"juran tsaiwa ba."""

Kusa dani da ³ar shuwa tazo ta zauna tace.

"""Sannunku"""

Tana mana kallon banza.

"Yauwa sannu"""

Na amsa mata.

"""Kai Babangida su waye waWannan matan, menene ala™arka da me kiranka Baby?"""

Ya daWe sosai yana tauna maganar kafin a sanyaye yace.

"""Matatace Kawu kayi ha™uri """

Salati su Hamida suka shiga yi tare da tafa hannaye.

Ni kuwa sai murmusawa nake yi.

Ba ™aramin tashin hankali da damuwa ³ar Shuwa ta shiga ba.

"""Matarka, yaronma da cikin duk naka ne kenan naga kamar ciki ne da'ita ai?"""

Kai kawai ya Waga ma Kawu Manga.

Shiru yayi yana nazari kafin yace.

"""To ai Shikenan babu damuwa tunda dai aure kuka yi."

"Waye maWaurin auren to?"""

"""Baba na shago ne"""

Kawu Manga yayi shiru ya kasa cewa komai Wawo kuwa inya kalli Babangida sai ya kalli Kawu Manga.

"""Hajiya gara da Allah yasa ku kai tunanin zuwa tun wuri ba har saida lokaci ya ™ure muku ba."""

Wannan dattijuwar tace.

"""Hala mahaifinshi ne kai ko?"""

"""E uba nake a wajenshi"""

Sai tace.

"""Alhamdulillah ga Ramatu itama a bata Waki a gidan mijinsu ta zauna a haWu ayi jinyar Babangida tare"

da'ita. Gidan da suke ciki ma Wanta ya karSe har ya siyar sakamakon wani iftila'in daya afka mishi.

Ni kuma bazai yiwu taci gaba da zama a gidana ba tunda dai mijinta yana da gida. Dama kuma ba da son

"ran dangin mahaifinta aka yi auren ba. Ganinta a gida da akeyi sai aka soma tsogumin ko aurenne ya mutu"""

Kawu Manga yace.

"""To yayi. Ke Sabuwa in zaki tafi ki tafi da wannan baiwar Allahn ta zauna a turakar Babangida tunda a"

"halin yanzu babu inda zata zauna zuwa a sallamoshi"""

"To Kawu in sha Allah"""

Na faWa da ™arfin guiwata.

"""Keyn turakar a hannun wacce matar taka yake?"""

"Babangida tsabar kunya ne, ko meye yama kasa Wagowa ya kalli kowa yace."

"""A hannun Maman Fatima na barshi"""

Kawu ya dubi ³ar shuwa yace.

"""Kin yana tare dake ne, ko yana gida?"""

A kumbure tace.

"""Yana gida"""

Bai damu da kumburinta ba yace.

"""In kin koma sai ki ba Sabuwa keyn. Wawo da Ramadan ku taso muje. Matanshi zasui jinyarshi su dinga"

"yin kama_kama"""

"Ai kuwa suka haWu su uku suka fice, da gani a ™ule Wawo yake ainun dama gashi da faWa."

"""To Ramatu da Alkhairi in kin isa gidanki mayi waya ki mana kwatance ko. Babangida Allah ya ™ara sau™i"""

"""Ameen nagode Mama"""

Wannan dattijuwa ta fita Amarya ta bita a baya.

Yaro kuma yana wajen Babangida a yanata mishi kwarance

"""Hmmmm. Hmmmmm. Hmmmm"""

Shine abinda ³ar Shuwa take ta nanatawa idanunta sunyi jawur dasu. Wallahi ni kuwa raina fes tamkar

audiga.

"Labbai muje masallaci muyi Sallah sai mu Wau haramar gida ko?"""

"Na faWa tare da mi™ewa. Kafin mu fita Amarya ta dawo, mu kuma muka fice."

"""Lolo haka mijinku yake kamar bunsuru wajen son mace?"""

Haba Labbai ai sai dai ki kirashi Ayu baban bunsurun kenan. Ni wallahi abun yayi mun daWi. ³ar Shuwa ai

"gani take ta mallake Babangida sai yadda tayi dashi. Bata san ya fita cin kai ba, a tafin hannunshi take."

"Ya kika ga Amarya kyakkyawa da'ita gashi a doke ba dokuwa zata yi ba ba"""

Dariya muka saka.

Har muka isa masallaci bamu dena dariyar ba. Ko da muka idar da Sallah a hanyarmu ta komawa cikin

asibiti zancan dai muke yi.

"Muna tura ™ofa muka tarar ana gurmi, wai damme Amarya da zuwanta zata shiga tattaSa Babangida a"

gaban matan gaban goshi. Ita kuma Amarya tace ai mijinta ne itama.

"""Ya isheku haka ko, kasheni kuke so kuyi ne kome. Ke Maman Fati me yasa bakya son a zauna lafiya ne?"""

³ar dariya ce ta subuce mun da naji yau babu Habibaty sai Maman Fati

"""Maman Fati ka kirani yau gatsau Jannaty sabida wannan abun?"""

"""Wacece Abu? Ai wallahi nafi ™arfin abu ke da gani kinsan ni dake babu haWi"""

Da ™yar dai sukai shiru sai da ya daka musu tsawa sannan suka nutsu.

"Amarya mu zamu tafi, kin shirya tafiya ne yanzu?"""

A wula™ance tace.

"""Ni anan zan kwana kije kawai"""

Tana faWin haka ni da Labbai muka juya muka fice abinmu.

Ya suka ™are ohon musu dai.

Baba Malam:

"Yana zaune a zaure gashi ga Malama Babba da Malama ™arama da Wawo, da Kawu Manga."

Kawu Manga ya kwashe komai ya faWa musu ya Waura da cewa.

"""Kai tsaye wajen shi Baba na shago muka je. Ya tabbatar mana shekara Waya da kusan rabi kenan da"

Waura auren

Wannan shine abinda yake faruwa a gaskiya na kusan cire hannuna akan Babangida koma ince na cire

"hannun nawa. Shi wanne irin yarone?"""

Malama Babba dake ta faman salati sai ta sau kuka.

"""Yanzu ashe a duniya akwai abinda Babangida zaiyi ba tare da ya shawarceni ni mahaifiyarshi ba?"

"Wannan yaro ina zansa ba™in cikinshi?"""

"""Ai tukunna ma Babba. Ba dai kina bayan rashin gaskiya ba, in dai kuka ne ai bakiyi ba."

A baya irin kunyar da Babangida ya saka mu ta wasa ce.

Bari in faWa miki ki kuma sani batun Sabuwa data maka ku a kotu. Kisa a ranki muddin al™ali ya saki

Sabuwa tamkar ke ya saka in baki sani ba ki sani igiyar auren Sabuwa a ™ulle suke tare suke tafiya da

igiyar taki auren. Ai sanan kinsan da zaman wannan sharaWin

Kuma daga yau ban amince Babangida ya sake tako ™afarshi ya shigarmun gidana ba.

"Na zame shi daga cikin jerin ³a΄ana ko mutuwa nayi kada yazo kan gawata."""

Salati Kawu Manga ya shiga yi ganin yadda Malama Babba take shiWewa.

"""Kawu mu kaita asibiti kada ta mutu. Malama Babba"""

Wawo ya shiga kiran sunanta.

Babu shiri suka kwasheta zuwa asibiti cikin rashin hayyaci.

Malam ya runtse idanunshi wasu hawaye masu Wumi suka zubo mishi.

"Ya lura Babangida shine zaiyi ajalinshi da ba™in cikinshi. Sai kace shi kaWai aka haifa duk yabi ya fitineshi,"

bashi da aiki sai jaye_jayen magana tun yana ™arami.

A daddafe ya rarrafa ya shige turakarshi ko gani bayayi.

Jin har an kira Sallah a masallaci Baba malam bai fito bane Idirisa ya shiga turakar ya samu Baba malam

a ™asa babu yadda yake.

Kan kace me mazan gidan suka rufu a kanshi.

Su Wawo suna asibiti aka bugo musu waya ana sanar dasu halin da Malam yake ciki.

Babu shiri Wawo ya baro asibitin ya bar Malama ™arama acan da Sa'a da bata jima da zuwa ba.

Malam dai anyi juyin duniya a kaishi asibiti ya™i fur. Dole sai likita aka kira mishi har gida yazo ya duba shi.

Jininshi ne ya hau sosai da sosai.

A wannan rana iyalan gidan Malam Baba basu runtsaba a cikin wannan dare da ya shiga tarihin daren da

Babangida ya tashi hankalin kab ahalin gidan. Gashi a wannan karonma silar Babangidan ne.

Babangida:.

Shima yana asibiti jikinshi ya tashi sakamakon fargabar abinda kaje yazo. Yasan matsawar Baba Malam

yaji abinda ya aikata tamkar sake rura wutar ™iyayyarshi yayi a zuchiyar Baba Malam. Hatta Malama

Babba da a kullum burinta ta kareshi yasan in taji wannan labarin zai ruguza mata zuchiya.

Wannan abunne duk suka taru suka haWe mishi.

Gashi da ™yar ya kori ³ar Shuwa da Hamida a asibitin suka bar Ramatu ta yi zaman jinyarshi na kwana

Waya.

"""Baby jikinne yake damunkane? Wai garinma yaya kaji irin wannan ciwon ne?"""

"""Kar ki damu. Ki daure ki kiramun likita hannuna tsami yake yi mun"""

"Mi™ewa tayi ta fita, yabi bayanta da ido kawai."

Takamaimai ya rasa tunanin me zaiyi ma zuchiyarshi a cunkushe take sosai.

Haka dai wannan daren ya kasance musu dare dubu da Waya

MRS BUKHARI

Babangida yana ruwa

IDAN KAYA YA GAJI...

GAMMO MA YA GAJI

LITTAFI NA BIYU

SHAFI NA SHIDA

BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ˜AMSHI

GA ˜ARIN SHAFI ALLAH YASA ZUKATANKU SUYI SANYI.

SABUWA:.

Haka dai lamura suka ci gaba da tafiya suna jiyawa.

Matan Babangida suka ci gaba da jinyarshi yau wannan ta kwana gobe waccan.

"Amarya dai tana turakar mijinta. Yadda na fuskanceta bata da ha™uri kamar zawayi haka take, shi yasa"

"kusan kullum ita da ³ar shuwa sai sun hau sama sun duro, gata da gadara da girman kai."

Ni dai tun daga wannan ranar kafata bata sake taka asibiti ba.

Malama Babba ma har aka sallamota banje ba.

Baba Malam kam naje har sau biyu gida na duba shi.

"Shine ma ya sanar dani a tsanake in tattare kayayyakina waje guda, in SaSSalle gado da komai nawa dai."

"Bai mun bayanin komai ba, nima ban tambaya ba na dai bi umarninshi nida su Labbai mukai ta"

kaye_kaye. Sai da su Sa'a suka zo gidanne ³ar

Please Login or Register in order to submit comment