You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka ci gaba da hirarsu.

Sai wajajen biyar ruwannan ya tsagaita Samira taja motarta suka wuce. Har ™ofar gida ta sauke Mama ta

wuce da ³ar Shuwa gidan Alawaiyya. A ™ofar gidan suka tsaya har zuwa wannan lokacin ruwan ana

"yayyafi"""

"""To inaga abinda za'ayi saka number ki anan. Na zama direbanki in kun gama ki kirani a waya zan zi in"

Waukeki in kaiki har gidanki. Ni dama zaki bani wajen kwana ai sai in kwana a wajenki gobe in kama hanyata ban fuye son zaman hotel ba sabida mijina babban mutum ne kuma yana siyasa kinsan hakan ka

"iya haifar mishi da yarfe irin nasu ΄an siyasa."""

"""Ai babu damuwa duk da nice da miji akanki zan iya sadaukar da kwanan nawa ga abokan zaman nawa"

"ma."" Baki ta taSe tace."

"""Amman har sai kin sadaukar da kwananki shin baki da Wakinki daban kike nufi tare kuke kwana a Waki"

"Waya wai?"""

Murmushi ΄ar Shuwa tayi tace.

"""A da dai yana da turakarshi Wakunanmu kuma a yalwace suke suma. Amman tunda karayar arziki ta"

"sameshi shikenan muka daqo gidan haya da zama haka dai aketa ha™uri"""

Da haka dai ganin su Sa'a dasu Sumy sun fito suna dariya yasa ³ar Shuwa tayi sallama da sameerah ta

fito daga motar. Kallonta Sa'a tayi da mamaki tace.

"""Wai sai yanzu kika iso ke da akace tun safe kinma riga kowa fitowa shine saida taron sunan ya ™are tas"

zaki zo? Kin ganmu fa ko wacce guduwa zata yi ruwane ya™i ya tsagaita.

"Da bama zaki zo ki tadda mu ba"""

MRS BUKHARI

"[8/26, 8:42 AM] BADA'AT IBRAHIM: Follow this link to join my WhatsApp group:"

https://chat.whatsapp.com/GV5vhgDl7ul6aRQ08xqvVy?mode=ems_share_t

"Barka da zuwa wannan group me albarka,kina business amma kullin kina yawan ayimiki ,logo, sticker da"

sauransu

Kiyi joining wannan linki din insha Allah zan koya miki yanda zaki yi da wayan hanninki batare da ko sisin

kiba

Ina nufin !

Yes !

Harma kidinga yima wasu kina samun kudin ki

Daga gida

Kawai waya kike nema da datan ki

Kawai kishiga group din for more update

Thank you

IDAN KAYA YA GAJI...

GAMMO MA YA GAJI

LITTAFI NA UKU

SHAFI NA GOMA SHA TARA.

Tsallakawa tayi inda suke. Sumy ta kawar da kanta gefe. Ita kuma ΄ar Shuwa tayi mata dariyar muguntar

da yake Wauke da fassarar zaki shigo hannune yarinya.

"""Wallahi tun safe na fito sabida ayi aikin komai dani. To kana naka Allah na nashi ina hanyar zuwa sai ga"

kira daga gida Mamanmu babu lafiya. Duk wuninnan a asibiti muka yi shi amman da sau™i na mayar

"da'ita gida ma. Ga kuma yanayi na ruwa"""

Murmushi Sa'a tayi ta saki fuskarta tace.

"""Allah sarki to Allah ya bata lafiya. Ramatu ma bata daWe da tafiya ba Anty Sumayya ma tafiya zata yi"

"nima gida zanyi ki shiga gidan dai babu kowa gaskiya duk kowa ya tafi sunan baiyi armashi ba sabida ruwa"""

Sallama tayi ma Sa'a ta shige a tunaninta ruwa ai ta sha.

Taje taba maijego abinda zata bata tayi mata irin bayanin da tayi ma su Sa'a. Mintinta arba'in ta kira

Samirah akan tazo su tafi. Bata haura minti goma ba sai gata ta iso ™ofar gidan. Sallama tayi da Alawiyya ta fice Samirah taja motarta suka nufi gidan ³ar Shuwa zuchiyarta cike da tunanin yadda zata yi da B house. Ga yara ta barsu a gidan Mama dan ta kasa tsayawa a fito dasu ta tawo dasu sabida sauri ta dai

ce ma Mama gobe a kawo su.

Šakinta a gurguje ta buWe hannunsu ni™i_ ni™i da ledoji da fantimoti mai taya suka shiga Samirah ta

zauna a kujera tana ™arema Wakin kallo.

"""To bari in yi sallah in zo in Waura abinci ko azahar banyi ba gashi har magriba ake kira"""

"""Nima banyi ba bari inyi nima"""

³ar Shuwa ce ta soma shiga banWaki ta Wauro alwala a gurguje so take kafin Babangida ya shigo ya

zamana ruwan tuwonta na wuta tunda dai tana da miyar kuSewa Wanya

Ai kuwa ina suna kan Sallah Babangida ya le™a uwar Wakin da sallama ganin mata biyu ne yasa ya dawo

falo ya zauna ranshi ya Saci sosai. Ya rasa sai yaushe zaiyi magana Waya a kan abu ne a dena.

Idanunshi ya lumshe tunanin chus na ragargazar ruhinshi dama gangar jikinshi.

Wayarshi ya zaro ya shiga cikin ma'adanar hotunan dake cikin wayar folda ta musamman sha™e da

hotunan Sabuwa ya shiga yayi ma hotonta ™ur shi kaWai yana murmushi yana kallon bakinta. Fitowar Yar Shuwa ne yasa ya kashe hasken wayar ya zuba mata idanu.

"""Sannu da dawowa ka ganni sai yanzu ko? Kasan yanayin ruwa yanzu ma zan Waura girki amman kafin"

"isha ma na Kammala in sha ALLAH"" tana faWin haka ta fice ta je ta kunna risho ta Waura ruwan tuwo kafin ta dawo taja ta zauna tana son sanar dashi batun yaje Wakin Ramatu ya kwana."

"""Amm dama ba™uwa nayi ³ar uwarmu ce daga Maiduguri tazo shine nace ko zaka je Wakin Ramatu ka"

"kwana ne tunda ni ina da ba™uwa gobe zata tafi ma"""

Kallonta yayi kawai yayi murmushin da shi kaWai yasan fassararshi.

Tashi kawai yayi ya fice zuwa can Wakin su Mardiyya. Yayi zamanshi cikin yaran yaje ya samesu suna cin

shinkafa da miya harda latas. Hannu ya saka shima ya shiga ci yana tambayarsu yaya sunan ya kasance da suka je

Malama baki abun magana itace ta shiga bashi labari. A haka har suka gama ci ya ja hannun su AWWa'u

zuwa Masallaci.

A masallacin bayan sun idar da sallah na™ocinsu ya tareshi yake sanar dashi AWWa'u ya tare yarinyarshi a

hanya an aiketa ya ™wace kuWin dake hannunta. Bayan haka kuma yaran anguwa suna kiranshi da

Sarawo dan har kaji yake sacewa. Hankalin Babangida ba Wan ™aramin tashi yayi ba take ya shiga ba wannan bawan ha™uri da godiyar dole kan faWa mishi halin da Wanshi yake ciki..

Hmm ranar a Wakinsu Mardiyya ya kwana a falo a tsakiyar su AWWa'u.

³ar Shuwa ta kawo mishi abinci yace baya ci. Tayi juyin duniya akan sai ya bar dakin ya koma Wakin

Ramatu sabida tafi kishin yaran Sabuwa fiye da yadda take jin kishin Ramatu da Sumy.

"""Kije bana son damuwa dan ALLAH. Gobe da safe in ba™uwar taki ta tafi kya bani labarin abinda ya kai ki"

"Ringim ko?"""

Gabanta ya tattake ya faWi babu guiwa a jikinta da ™yar ™afafuwanta suka iya janta zuwa ciki.

Murmushin takaici da ba™in ciki kawai yayi. Ya dubi AWWa'u wanda yake bacci kamar shi sak da Yan

"gidansu Sabuwa gashi har dabi'unsu ya Wakko dan dai shi tunda yake bai taSa sata ba."""

Yar Shuwa babu guiwa ta shiga Wakinta ta tadda Samira tsirara haihuwar uwarta da ubanta da sunan

tana shafa mai.

Zama tayi a kan gadon ba tare data ce uffan ba.

Matsowa Samira tayi ta rungumeta ta baya ta shiga mata raWa a kunnenta.

"""Tun sanda na haWa idanuna dake naji a raina kin kwanta kinyi lub. Shuwa ina son zan baki duniya ki juya"

"duniya da mutanen cikin duniya yadda ranki yake so. Ki mallaki gidaje, motoci, duk shekara kije umara dan aikin Hajj akwai wahala sau Waya ma ya isheki. Amman in kin bani haWin kan abinda nake da bu™ata a wajenki. Sai dai ina da tarin tulin sharuWWan da nake gindayama duk macen da zanyi mu'amala da'ita."

"Wannan kuma in kin shirya zaki sameni ne a Bamaina."""

Iska ta hura mata a kunnenta mai sanyi. Tuni ta lumshe idanunta. Abunda yafi komai bata mamaki shine

yadda taji ta kwaWaitu da Samira.

Sakkowa tayi daga gadon ta zura rigar baccinta kana ta jawo musu leda mai cike da kaza da gurasa.

"""Baby sakko muci kinji duk da dai na ganki a damuwa wani abunne?"""

Ajjiyar zuchiya ΄ar Shuwa ta sauke ta sakko suna cin kazar tana faWa mata halin da take ciki a gidan

tsakaninta da kishiyoyinta musamman ma Sabuwa da yaranta. Duk da a tunaninta ta gama da yaran Sabuwa.

"""Hmm ki dena damun kanki da Ša namiji kina tare dani. Duk taurin kanshi nan gaba kaWan da kanshi zai"

dinga ro™onki yana so kuyi mu'amalar aure kina ™i. Daga lokacin babu wata kishiya da zata sha gabanki.

Su kam ki dena ma ta tasu baga magani kin karSo ba? Ai maganin bokannan yankan wu™a ne

Mijinki kuma ai ya baki wata damane da zaki yi nazarin abinda zaki ce mishi ya kaiki Ringim. Ga dabara

"kice magani kuka je karSowa da Mama na rashin lafiyarta. Ba lallai bane ya tsananta bincikenshi ba. Ke kofa ya tsananta an gano inda kuka je wajen boka ne. Tuburewa zaki yi akan cewar ku baku sani ba kwatance akayi muku zuwanku na farko kenan"""

Ajjiyar zuchiya ³ar Shuwa ta sauke haka ta kwana cike da tunane _tunanen tayin Samira. Ta riga ta

jarabtu da soyayyar Babangida tsoronta Allah tsoronta kada ya kamata da wani abun da za'ace har aure ya ™are a tsakaninsu ji take yi zata iya mutuwa. Gashi tana son kuWi tana da burin ganinta a cikin sahun manyan matan da akeji dasu.

Washegari asussubar fari ³ar Shuwa duk taje ta zuzzuba magungunan da boka ya bata a ™ofofin Wakunan

waWanda akeso su taka. Har a ™ofar Wakinsu mardiyya saida ta barbaWa

Sumy tana kitchen Winta zata dafa ruwan zafi taga sanda ³ar Shuwa take mata barbaWe a kofar Waki. Sai

da ta shige Wakinta tayi dariya kawai. tana shiga ciki tayi fitsari a kofi ta fito ta watsa a ™ofar Wakinta ta cillar da kofin cikin kwandon shara. Su mardiyya kuwa data basu abinci basu ci ba Mardiyya haka siddan

taji jikinta bai bata ba ta ko juye abincin a ba™ar leda suka zubar.

Su Babangida asubar fari suka fito zuwa Masallaci bayan dashi da yaran duk saida suka yi adda'ar fitowa

daga Waki kafin suka taka maganin suka yi wucewarsu cikin kariyar Ubangiji. Kafin su fita daga gidanma saida suka yi adda'ar fita daga gida suka nufi masallaci.

Ramatu kuwa tana fitowa ta taka wannan maganin taji wani zumm zumm a ™afafunta yana haurawa a

hankali har izuwa kanta. Ta Wan jima a tsaye saida taji kamar ta dawo daidai saita wuce Wakin aminiyarta da asussuban dan gulma na cinta na kwanan Babangida a Wakin su Mardiyya

Sai da safen Babangida ya zaunar da AWWa'u ya dinga mishi nasiha yana karanto mishi illar sata da

matsayin Sarawo a musulunci. Daga ™arshe ya ™arashe nasihar a kansu baki Waya kana ya fita zuwa Wakin ³ar Shuwa yana tafe yana ambaton Allah ya tattake asirin baiji ko gezau ba.

A falo ya samu ³ar Shuwa da Samira suna cin ragowar Wunamen kazar jiya. Samira da shirinta tsab

harma ta fito da akwatinta falo.

Zama yayi a kujera suka gaisa da Samira yake tambayarta yaya Maiduguri.

"""Maiduguri alhamdulillah yanzu ma nake shirin inna karya in kama hanya garinmu da nisa."

"""Allah sarki hakane kam. To Allah ya tsare a gaida mutanen gidan"""

Mi™ewa yayi ya shiga ciki. Samira tace.

"""Bishi kiyi mishi bayani Baby. Ki tafi mishi da kaza in zaici."""

Mi™ewa tayi ta haWa mishi kayan kari ta shiga. Ta wuce shi yana wanka bata daWe da zama ba ya fito da

jallabiya a jikinshi zama yayi a gadon yana goge ruwan jikinshi.

"""Ina kwana?"""

˜ur ya ™ura mata idanunshi yayi murmushi tare da cewa.

"""Me kika je yi a Ringim a iyakar sanina baku da ΄an uwa a ko'ina sai a Maiduguri. Sannan meye ya hanaki"

"zuwa sunan Alawiyya da wuri har saida taro ya watse alhalin da safe kika fita da zummar tafiya gidan sunan?"""

"""Mamace babu lafiya harma asibity na kaita to shine wata ™awarta ta mana tayin mai maganin gargajiya."

Kaji abinda ya kaimu Ringim kuma ko kafin mu isa nayi kiran wayarka bata shiga har a Ringim Win na

"kiraka wayar ta™i tafiya. Ga ruwa ya taremu a hanya kaji dalilin daWewar da dalilin zuwa Ringim """

˜ur yayi mata yana mata kallon tuhuma sai yaji bai gamsu sosai ba da abinda tace.

"""Zargina kake yi da wani abun?"""

Ajjiyar zuchiya ya sauke illar bariki kenan kab matan zarginsu yake yi da zaran sun tambayi zuwa anguwa

baya taSa samun nutsuwa har sai yaga sun dawo. Wannan matsalar ma yanata kaita gaban Allah akan ya nutsar da zuchiyarshi waje guda

"""Tuwon da kika yi jiya shi zaki kawo mun Wumamen inci maza in fita kada inyi latti."

Da sauri ta fita kafin ta dawo ya gama shiryawa tsab. Yana cin tuwonne ta soko mishi zancan dawowar

su Mardiyya wajenta.

Ai sai ya ajjiye cokali ya kurSi ruwan shayi ya mi™e yana gyara zaman hularshi.

"""Wannan maganar nace dake a barta kada a sake yinta ma. Ai su Mardiyya basu da inda zai ishesu anan"

"a ina kikeso su zauna sabida Allah in ba dai kin shirya son takurama yaran bane amman yaushe uhm dan ALLAH ya ma za'ayi haka?"""

"A ajjihu ya saka hannu ya ciro dubu uku ( bafa ta yanzu bace dubu ukun, ta da ce)"

"""Ga kuWin cefane nan kiyi shinkafa da miya da latas"""

Ya fito yayi ma Samira sallama ya fita daidai yaran sun fito zasu tafi makaranta Mardiyya kuma zata tafi

koyarwa. Hijabinta har ™asa kamarshi sak da yarinyar kamar an tsagakara.

Samira ma bata daWe ba ta tafi dubu arba'in ta ™irga taba Yar Shuwa data rakata mota tana zaune ac na

dukanta ta dam™a mata kuWin.

"""Baby sai yaushe zan jira zuwan naki?"""

"""To zanyi ™o™arin sanin yadda zan ninkeshi baibai. Shi mutumne mai zargi da kulle wallahi gashi baya"

"barin ayi tafiya amman zan san yadda duk zanyi zan zo"""

Shafa ™irjinta tayi murya ™asa ™asa tace.

"""Kiyi ™o™ari kisan duk ™aryar da zaki yi mishi ya barki ki tawo sabida mu samu mu tattauna kuma in"

"gabatar dake ga manyan mata a matsayin sabuwar Baby na."""

Da wannan suka rabu ³ar Shuwa ta dawo Cikin gida. Suna haWa idanu da Ramatu sai taga tayi saurin

sauke kanta ™asa.

Murmushi tayi a ranta ta ayyana magani ya cisu kenan. Anjima in tayi abincin rana zata ma Sumy gargaWi

akan kada ta sake yin girkinta daban duk ranar girkin ita ΄ar Shuwan kamar yadda aka saba.

Hakan kuwa akayi bayan ³ar Shuwa ta kammala girkinta na rana ta kira Ramatu ta kawo kularta ta zuba

mata sai muzurai take yi mata.

Tsulum ta mi™e ta nufi Wakin Sumy ta sameta a zaune tana shan ™anzon masara na kwali da madara

(cornflakes)

"""Yayi kyau wato ke an Waure miki ™un™uru ko duk ran girkina sai ki nemi abun ci sabida baki da mutunci"

ko?'

Da ™arfi take maganar wai ita ga shugaba. Ai kuwa ranar an kwashi ΄an kallo dan Sumy data mi™e saita

watsa mata ™anzon masarannan a fuskarta ta jawota suka soma dambacewa.

Ko da Babangida yazo lefin ³ar Shuwa ya gani cikin ™osawa ya raba girki baki Waya sabida ya gaji. Kuma

kuWinshi na wajen Alhaji Abubakar Baban bola ya fito miliyan goma sai kawai ya raba girkin abun dai

baima ³ar shuwa daWi ba sam ga kuWi da aka narka a wajen boka amman ace Ramatu ce kaWai ta mallaka. Ai dama Sumy ta mallaka da abun yafi mata sanyi.

Haka abubbuwa suka jagwalgwale ma ΄ar Shuwa. Gashi duk dabararta Babangida ya™i barinta tayi tafiya

"bare ta je ta samu Samira a Bamaina. Suna dai waya, kalaman soyayyar da Samira take yi mata ko namiji albarka Saida biki ya taso a Maiduguri sai tayi amfani da wannan damar. Mama da kanta tazo ta ro™i Babangida akan zasu je biki da Yar Shuwa Maiduguri ba jimawa zasu yi ba kwana biyar kawai zasu yi."

"Shine Babangida ya amiince ba dan ranshi ya so ba, ba kuma dan ya yadda dasu ba gabaki Wayansu ba."

Idanunshi ya lumshe yana jin zafin rashin Sabuwa a rayuwarshi. Komai nashi ya sukurkuce sabida

"Sabuwa har koyarwar ma baya wani maida hankalinshi. Gashi yanzu ya kama waje yana siyan kayan baban bola in ya tara sai masu kamfani su zo su siye a kwashe a mota. KuWaWen shiga sai suka Wan ™aru mishi,iyali kuma ya ™ara musu kuWin cefane kuma kullum ko wacce ita da yaranta da shayi da ™oyi da"

mummu™i suke karyawa kunsan dama ta Sangaren ciyarwa babu wasa mutumin naku

Amman kullum zuchiyarshi babu daWi hoton Sabuwa da tunaninta shine abincin cin shi da shanshi. Wani

jirin jarabar sonta da kishinta yake ji.

Matanshi kab sun san halin da yake ciki cikinsu babu wacce bata ™orafin rashin samun lokacinshi da suke

yi musamman ma ³ar Shuwa data damu kanta ta hana kanta sukuni sai bokaye mayaudara ke cin

kuWinta a ™o™arinta na ganin ta mantar da Babangida Sabuwa abun ya ci tura.

Ita kuma ta lashi takobin ko tsirara zata yi yawo saita cire Sabuwa a zuchiyar Babangida hatta su

Mardiyya sai ya koresu a gidan.

Ta saka su a gaba da zagi da hantara yarannan. Kullum a cikin azabtar dasu take amman a bayan idanun

Babangida. Sai dai labarin na dawowa kunnenshi ta bakin Sumy. Suna Wauki babu daWi da yar Shuwa sosai kullum suna cikin faWa kuma yana faWa mata ta cuceshi data shigo rayuwarshi dan shigowarta ne ya

tunzura Sabuwa har ta dage saida suka rabu. Ya mai nadamar saninta a rayuwa baki Waya.

MRS BUKHARI.

"[8/26, 8:43 AM] BADA'AT IBRAHIM: https://chat.whatsapp.com/EEK9H2V5iSOFXz0Xud5Eox?mode=ac_t"

"Yar uwa ta, kin dade kina neman in da zaki samu nighties da lounge wears masu musulmin kyau, saukin"

"farashi da kuma kyan gani? To ki daina nema! A thrift bae closet, mun bude exclusive group inda za"

"a dinga kawo thrift nighties, lounge wears da sauran su masu kyau, kamar Sabbi kuma farashinsu abin"

"mamaki ne, very affordable ."

A nan ne za ki kasance cikin na farko da za su ga sababbin kaya kafin su kare. Idan kina son kada ki rasa

"mafi kyawun kaya kafin a sayar da su gaba Waya, to shiga cikin group Win yanzu kafin ya cika "

https://chat.whatsapp.com/EEK9H2V5iSOFXz0Xud5Eox?mode=ac_t

IDAN KAYA YA GAJI...

GAMMO MA YA GAJI

LITTAFI NA UKU

SHAFI NA ASHIRIN CIB

SABUWA:.

Yau dai sassafe muka fito da akwatunanmu zamu wuce garin kano. Dani sa Uzairu zuchiyata da Maigogul

daya tubure shi sai yayi mana Rakiya har izuwa Lagos kafin ya dawo. An yi juyin duniya ya™i yarda haka Uzairu zuchiyata ya ha™ura.

"""To Rakiya Hauwa mufa arziki ya kiramu dama dai ance kashine to ni dai na tako nawa. Kuma ko babu"

"komai ta sanadiyyata Sabuwa zata keta hazo."""

Baki Hauwa ta taSe ba tare da tace uffan ba.

Maigogul bai ce uffan ba sai gyara zaman hularshi yake yi ya caSa adon burgewa.

Gaza da madamcy suka fito muka yi sallama muka kama hanyar zuwa kano bayan mun yi sallama da ΄an

"uwa, dan Adama ma a gida ta kwana sun samu saSani da mijinta. Layuza ma dai auren ya ™are dama igiya Waya ce jol take yawo a kanta to ya tsinke igiyar da yaga ya soma samun faraga. Gata da goyo amman a hakan ya korota Maigogul dai yace yana dawowa daga Lagos zai tusa Layuza a gaba a mayar da"

goyon Wan nata.

Da misalin ™arfe sha Wayan rana muka shiga Kano. Kai tsaye daga tasha muka yi shatar tasi ta kaimu har

Airport na kano dan jirginmu na zuwa Lagos ™arfe biyu cib zai tashi.

A Airport muka yi sallah muka ci abinci.

Maigogul sai waye_waye yake yi da jama'arshi ta Lagos dan baya rasa mutane a ko wanne jaha yanda

"kuka san wani mai babban mu™ami a hannu."""

"""To Shikenan mun samu an kama mana babban Hotel a Lagos Win Waki biyu Lolo naki Waya, sai ni da"

"Uzairu Zuchiyata mu ri™e Waya. Amman lolo akwai wani Alhaji da matarshi ta mutu yana ta son ya sake aure shine nake son in tambayeki in Khalid bai shirya ba me zai hana in haWaki dashi?"""

Wani irin kallo nayi ma Maigogul wanda shi kanshi saida ya dibibice mamakine ™arara a fuskata da

abinda naji yace.

"""To Shikenan na fahimci bakya so. Amman ni sonki da arziki nake yi babban hamsha™ine Lolo shi kanshi"

"ma ba lallai fa ya amince da tayin nawa ba dan babbane a mu™ami abokin hulWata ne"""

Idanuna na lumshe kaina ya wani sara mun.

Uzairu zuchiyata ne yace.

"""Maigogul ai daka bar Lolo ta nutsu ta fitar da wanda ya dace ya kuma yi daidai da rayuwarta. Sannan shi"

"mutumin da kake so ka hadasu ya yanayin ™arfin kuWinshi yake?"""

Dariyar da Maigogul da Uzairu Zuchiyata suka saka abun mamaki sai kawai naga sun tafa.

Nan Maigogul ya dinga Sarin zance yana ba Uzairu zuchiyata shi kuma tuni yai na'am da wannan mutumi

har hotonshi ya nuna ma Uzairu zuchiyata a waya.

"""Wallahi ke Lolo da sa'arki ma dai aka haifoki wallahi irin wannan mai arziki haka a rayuwarnan wa yake"

"son wahala? Jibi Adama fa yadda a lokaci ™an™ani tabi duk ta lalace har ta yo yaji. Ni dama Maigogul ne ya dage saita auri Wan ™auyannan amman wallahi ni nasan dama ba za'ayi abun arziki ba. Shifa Wan ™auye baifa san cima mai daWi ba fa kuWinshi ba bana ci bane na cizo ne"""

"""Ai in faWa maka wallahi a lokacin da aka haifi Sabuwa mun samu alkhairai da yawa fa. Ai a lokacin ne"

"Alhaji tsalha ya biya mun kujerar umara fa naje, shi yasai ragon sunanta. Wani maigidana Marigayi Alhaji"

mutta™a shima ya sai rago ti™e™e ya bani. Ya Wakko dubu ashirin ta zamanin baya ya bani. Uzairu

"zuchiyata a sunan Lolo shinkafa da miya aka ci saida kowa yaci ya ™oshi shi yasa take da sa'a"""

Uzairu zuchiyata yace.

"""Amman ni lokacin da aka haifeni fa? Gara inji insan wacce iriyace sa'ata ya ™arfin taurarina suke na"

"zahiri?"""

Harara na zabgama Uzairu zuchiyata na ba™in ciki da takaicinsu su duka biyun.

"A jirgi ya ™arashe mishi labarin yadda sunanshi ya gudana, ya dinga soki buritsun zance Uzairu zuchiyata"

yana ™ara turashi dama shi haka halinshi yake.

Karfe uku cib muka sauka a Airport dake garin Lagos. Ni dai dana shiga jirgi na sake gane Allah da girma

yake. Ashe jirgi haka yake da girma amman a sama a hangoshi ™arami?

Isarmu titi ke da wuya muka tare abun hawa zuwa hotel Win da aka turama Maigogul adireshin a waya

da lambar Waki kamar haka uku sifili da uku Waya (30 da 31) Eco Hotel Banana Island. Wannan hotel Win a tsada in akwai wanda ya fishi tsada a Lagos to tsadar da kaWanne amman abinda na sani hotel ne

wanda yawanci turawa da hamsha™an ΄an kasuwane suka fi iya kamawa sabida bala'in tsadarshi.

"""Yauwa Sabuwa ke shiga mai uku sifilin kiyi odar duk abinda kike so akwai abinci kyauta ko sau nawa"

"zaki ci. Kuci ku ™oshi banza ta faWi. Ni dana huta zan shiga garine"""

Ni dai Wakin na buWe na shiga na shiga ™arema haWuwar Wakin kallo. Zamana nayi akan gado ina ajjiyar

zuchiya. Ni bana ma jin yinwa tunda munci abinci a Airport. Mayafina na zare kawai na haye gado inaso inyi bacci.

"Sai nayi shiru kawai ina kallon yadda ac yake buso haya™in sanyi, sanyin na ratsa jikina. Fuskar Alhajin da"

Maigogul ya nuna ma Uzairu zuchiyata ce ta faWo mun na lumshe idanuna. Ina tunanin da ba dan bansan wanne iri bane shi dana amshi tayin Maigogul. Abu Wayane yake sani tunani da tsoron komawa gidan jiya.

Nasan abune mai wuya in ba mazinaci bane tunda har Maigogul ya sanshi. ˜ila mata yake kai musu tunda yace abokin cinikaiyarshi ne. To inma nace ba shi Win ba waye zai aureni wai? Bana tunanin akwai nutsattse kamammen da zai iya neman aurena in dai gaskiya zamu faWama kanmu tunda ubanmu ma kawaline. Sannan maza da yawa suna cikin harkar zinace_zinacennan in dai zai ri™eni da mutunci ba gara

in aureshi ba me ku kuke gani amma?

In kuma na tuno da kuWurar Allah sai in ji a raina nagartaccen miji kintsattse yananan zuwa lokacine bai

ba. Tunda Allah ya sani na tuba nayi nadamar gabaki Waya ma rayuwata ta baya wallahi Allah kenan.

Dan na gaji da irin rayuwar gidanmu Allah ya sani so nake in nesanta dasu sosai ko zam samu nutsuwa a

rayuwata. Kuma nafi ™aunar auren gudun sake tsundumawa rayuwar dana tsinci kaina a baya.

Lumshe idanuna nayi a hankali banfi minti goma da rufewa ba bacci ya kwasheni.

Maigogul

Suna shiga ya cire babbar rigarshi ya faWa banWaki yayo wankanshi ya fito daga shi sai wandon

shaddarshi da tawul a wuyanshi.

"""Uzairu zuchiyata kirasu a waya su kawo mun farfesu mai zafi in sha ni fita zanyi."""

Uzairu zuchiyata daya ™yafe a gado yana waya da Felisha ya gyaWa mishi kai tare da Waura yatsanshi a

saman labSanshi ma'ana yayi shiru. Shiru Maigogul yayi harda kama bakinshi. Zama yayi a kujera ya ciro manshi ya shafa ga shadda ya zarota ya kintsa tsab wanka iyakar wanka ya feshe jininshi da turaruka masu ™amshin daWi ya ™arama yatsanshi zobe guda Waya mai ba™in dutse kasancewar agogon hannunshi

cikinshi ba™ine yana son kwalliyar ta fita da kyau.

Uzairu zuchiyata saida ya sallami Felisha kana ya kira Hotel ya faWa musu sa™on Maigogul cikin minti sha

biyar suka kawo farfesun naman akuya lafiyayyen gaske suka dire mishi yana ci yace.

"""Uzairu zuchiyata ka shawo kan Lolo ta amince da batun dana kawo mata sabida naga tafi su A'isha"

"wayewa ne kuma turancinma babu laifi tana kwaciSawa shi yasa nayi mata wannan tayin fa. ˜arshe in nace su Labbai zan bashi kaga harkar ta

Please Login or Register in order to submit comment