You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nayi da ™arfin tsiya wanda hakan yasa nayi suman dole.

Su Adama kuma suka fasa ihun Malama Babba ta kasheni.

Da ™yar na yarda na farfaWo harma ana shirin kaini asibiti kafin na yarda na farfaWo.

Baba malam ya dinga faWa a tsakar gidannan tare da gindaya sharruWa masu zafi. Ranar gaskiya an

fusata Baba malam sosai.

Gaga_gaga al'amura sukaci gaba da tafiya ranaku suna shuWewa. Abubbuwa marasa daWi sun faffaru ciki

harda yin™urin zubarmun da ciki da Malama Babba tayi har sau biyu bata samu nasara ba

Na biyun saida nayi sati biyu a asibiti kafin aka sallamoni.

Malam yayi faWan yayi rikici sosai sai da akaita zuwa bashi ha™uri daga dangin Malama Babba kana ya

hakura. Babangida kuma bai ganni ba balle yayi nashi yin™urin. Su Maigogul kuwa an Wauke ™afa gudun

kada a fasa aurena. Sai dai su kirani a waya mu gaisa kawai.

Da lokacin daya kamata na soma zuwa awo yayi Baba malam ya haWani da malama ™arama ta rakani

muka je. Duk wata hidima Baba malam ke yi mun. Duk abinda nake so zanje in sameshi a makaranta in faWa mishi in sha Allahu kuwa zaisa a aiko mun dashi.

Babangida dai ya samu da ™yar an ro™i malam ya yarda zai dinga shigowa gaishe da mahaifiyarshi

amman shi baya bu™atar gaisuwarshi.

˜iyayya babu irin wanda ba'a nuna mun a gidansu Babangida ba.

Ni kuma zaman gidan ya dameni nayi yin™urin guduwa har sau biyu Baba malam yana hanawa. Kuma

koma dai yayane ina ganin girmanshi kwarjini gareshi bana wasa ba.

Ranar da cikina ya cika wata tara cib na haifi diyata mace a asibiti

Nasha ba™ar wahala dan anyi tunanin ma na mutu

Baba malam duk ya shiga damuwa ainun

MRS BUKHARI

"[8/14, 7:22 AM] +234 802 205 9556:"

https://chat.whatsapp.com/IUKFTeul76p2VaAvQ5nk0U?mode=ac_t

IDAN KAYA YA GAJI...

GAMMO MA YA GAJI

BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ˜AMSHI

LITTAFI NA UKU

SHAFI NA SHIDA 6

"Na sha wuya sosai, abun har ya gagara ansa hannu za'ai mun aiki sai kuma na sauka da kaina."

Ana haihuwar kuma duk wahalar sai ta wuce. Sai washegari na samu kaina

Duk da yarinyata ΄ar gaba da fatiha ce sai naji duk duniya babu abinda nake so sama da wannan yarinyar.

Gashi babu ta inda ta baro Babangida Kunji wata ™udurar Allah.

Yarinyata tana gadon jarirai a kwance Malama Babba data iso yanzu da malama karama da muka tawo

tare duk sun ™i su Wauketa har sai da Baba malam ya ™arasone yasa hannu ya Wauketa. Ya daWe sosai yana kallon yarinyar. Nasan dai bazai wuce tsantsar kamanninta dashi yake mamaki ba.

"""Allah mai yin yadda yaso, yarinya ta raba duk wata kaddama. Sabuwa sannu ko. Akwai abinda kike"

"bu™atane?"""

"A_a so nake dai ΄an gidanmu su san halin da nake ciki"""

Kai ya gyaWa.

"""Nasa a sanar musu zasu zo nan asibiti su sameki. Mahaifiyarki zata zauna ta kwana dake anan zuwa"

"gobe a sallamemu sai mu koma gida"""

Malama Babba tace.

"""Nayi tunanin ai a gidansu zata yi wanka. Kasan haihuwar fari tana bu™atar kulawa daga ita har jaririyar."

"Sannan duk wannan kamannin ai yana da kyau a sake tabbatarwa ko? """

Kallo mai Wauke da tuhuma yayi musu du su biyun.

Sai da yayi ma jaririyar adda'a kana ya dubeni yace.

"""Akwai wani suna da kike so a saka mata ne. Ko Babanta ya riga da ya zaSa mata sunane?"""

Dukkansu su ukun ni suke kallo. Ni kuma sai numfashi nake saukewa.

"Babu sunan da muka zaSa mata"""

Kai ya gyaWa yayi. Mata huWuba da suna Mardiyya kana ya mi™o mun yarinyar na rungume abata ina jin

motsin sonta a zuchiyata.

"""Yarinya nayi mata huWuba da sunan kakarta mahaifiyar Babba wato mardiyya. """

Daga malama Babba har malama ˜arama sun kaWu sai dai babu halin tankawa.

"Ramadanne ya shigo da abinci. Malama ˜arama ta zuba mun, farfesun kayan ciki ne sai kunun gyaWa."

Nasa hannu na amsa dan dama ba ™aramin yinwa nake ji ba. Ga jikina babu ™arfi kwata_kwata har rawa

yake yi nasha wahala fa sosai.

Fita Malam Baba yayi. Ni kuma jinjirata na jikina na cinye wannan farfesun tas na kora da kunun.

Take bacci ya yanko mun.

Na daWe sosai ina baccin wahala ina farkawa naga Rahama da Labbai Sai naji wani sanyi a raina da naga

΄an uwana.

"""Sannu Lolo kin tashi? Ai kinsha baccin gajiya haihuwa ai ba wasa ba. Allah dai ya raba lafiya saura"

haramar yin aure kuma. Boyeki ya ™are ai.

Cewar Rahama dake shan tea Labbai kuma na ri™e da Mardiyya.

"""Kinga Lolo yarinya kyakkyawa sak ubanta babu inda ta baro shi."

"Sai dai mun zo muka tarar babu kowa a wajenki ga jaririya a kwance kunata she™ar bacci."""

Hmm ai basa zauna ba. Gara da Allah ya kawo ku dan ni kam daga nan sai gidanmu. Na gaji da wannan

"kullen da suke yi mun."""

"""A_a kada ma ki soma Lolo. Gara ki koma can Win dai kinga kar maganar Auren naku ya rushe kuma. Za"

dai ayi magana zan zauna dake acan Win sabida a kula dake yadda ya kamata. Ki Wan haWa da shan magungunan mata dana gyaran jiki tunda yanzu batun aurenku ne abu na gaba.

"Adama ce taso tazo ta zauna dake to bata jin daWine a kwance take babu yadda take, ga babu kuWin"

"zuwa asibiti. Lusarin mijin nasu kuma baya ma garin yabi babbar mota wai zuwa Inugu. Shi Babangidan yazo yaga yarinyar?"""

"Bai zo ba. Kuma nasan bazai zo ba. Ai hatta kayan jaririya, da duk wani kayan haihuwa Baba Malam ne"

"yayi. Babangidan da har yanzu ba'a amsa gaisuwarshi"""

³ar Shuwa ce ta katse mana hirarmu.

Ina ganinta nayi murmushin farin ciki nayi kewarta sosai duk da dai a rana ma mukan yi waya takai sau

uku inma ta kama har fi.

"Haka muka kwana mu uku ma a asibitin daga mu sai mu, an dai kawo mana abincin dare lafiyayyen"

tuwon shinkafa da miyar shuwaka har da man shanu.

Washegari sassafe su Rakiya da su Maigogul da ΄an Wakinmu dukka suka zo ganin yarinya.

Anan Baba Malam ya tarar dasu aka dai gaisa babu yabo babu fallasa

A hakan Maigogul ya nemi Rahama zata zauna dani ta kula dani acan.

Allah cikin ikonshi sai tace .

"""Dama ko baku bu™aci hakan ba ni zan bu™ata. Sabida Sabuwa na yin arba'in a ranar za'a Waura aurenta a"

"ranar kuma zata tare a gidanta in sha ALLAH"""

Murmushi Maigogul yayi yace.

"""To hakan yayi kyan al™awari cikawa. Sai dai wani hanzari ba gudu ba. Ni ina zanga kuWin kayan gado nan"

da kwana arba'in? Ka gansu nan dukkansu lokacin aurensu su suke yima kansu kayan Waki. ˜arya da ciwo

"bani da kuWin da zanma Lolo komai. Sai dai a Wan ™ara mana lokaci"""

Rakiya tace.

"""Gaskiya kam muna bu™atar ™arin lokaci. Dan inta wannan za'a daka ma auren bazai yiwu ba in dai da"

"kudinshi za'ayi bikin."""

Ai da faWin haka Maigogul ya hau nuna ma Rakiya hannu tana faWa yana faWa har sai da ma'aikatan jinya

suka zo suka musu magana akan su fita.

Baba Malam yana tsaye motsin kirki ya kasa yi sai zuwa can yace

"""Ya yara ba zasu lalace ba ace yarinya ita zata ma kanta kayan Waki ita ba aiki ba ba sana'a ba. Shin"

"waWannan waWanne irin mutanene Babangida ya kwaso mana wai? Hmm babu damuwa. Sabuwa ku shirya ga mota a waje an riga an baku sallama"""

Yana gama fadin haka ya fice.

Su Labbai ne suka haWa mana kayayyakinmu. Suka kawo mu har bakin mota.

"""To Rahama duk yadda ake ciki mayi magana ko ta wayane"""

"""To Rakiya. Amman fa ni ina ganin babu bukatar a Waga aurennan. Bari dai in muka isa can Win zamu yi"

"waya"""

Da wannan muka rabu.

Muna shiga gidansu Babangida Malama Babba dake tsaye a tsakar gida rike da bokiti ganinmu yasa ta

sau bikitin.

"""Ohh ni Saratu yanzu Malam ashe da gaske yake yi wannan yarinyar a nan Win zata yi jego? Babu komai"

"ai zata gama jegonne"""

Rahama tace.

"""To da a ina kike son tayi? Akayi renon cikin da haihuwarshi ma sai wankan jegone ba za'ayi ba."

"Ke Lolo inane Wakin da zamu zaunan yake?"""

Nuna mata nayi da hannu muka wuce muka bar Malama Babba na sababi a tsakar gida.

Ina kwance Rahama tace.

"""Kinga Lolo tashi ki ba yarinyarnan mama tasha sai mutsu mutsu take yi. Ko ruwan nonon bai zo ba ki"

"bata in tana Wan zu™a zai zo da kanshi."""

"Mi™ewa nayi nasa hannu zan karSeta Malama ™arama tayi sallama ta shigo da gaushi ta dire ta fita, bata"

daWe ba sai gata da ruwan wankan jinjira a sabon bawon na cikin seti da Baba malam ya bayar aka siyo.

"""Gama bata Maman sai ki mi™ota ayi wanka. Rahama ko? Sai kuje kiyi mata wankan yamma. Ni na dunga"

"mata na safe"""

Baki Rahama ta taSe tare da mi™ewa.

"""Lolo kafin ta gama sha bari in wanke kayan jinin da muka dawo dashi. Baiwar Allah sabulu da omo fa"""

Malama ™arama tace

"""Zan je in tambayo Malam duk yadda akayi ya manta ne bai siyo a siyayyar haihuwar ba. Bari a gama ma"

"Mardiyya wanka tukunna"""

Tayi maganar babu annuri kamar a yadda Rahaman tayi mata kenan.

Mi™a mata jinjirar nayi na fita Rahama ta bi bayana zuwa banWakin tayi mun wankan tawul ta gargasa

"mun jikina, in tasa tawul dinnan a ™asan marata ta danna sai jini yaita zuba."

Naji daWin jikina sosai ana kiran sallar muka fito daga wankan.

Mun shiga mun samu Malama ™arama harta gama yima Mardiyya wanka tayi mata gashin cibi tana

wanke kayan da aka cirema yarinyar ne a cikin ruwan wankan. Muna shigowa ta suri bawon ta fice tana faWin.

"""Allah ya sauwa™e wallahi ko a cikin labaran hikayoyi ban taSa jin labarin da yayi kama da wannan ba."

"Wannan abun kunyar da yawa yake"""

Tsaki muka ja ni da Rahama. Ni dai tsabar daWin wanka har wani bacci_ bacci nake ji.

Ina gyangyaWi Rahama na gyaran Wakin Alawiyya ta shigo da ™aton filas na ruwan zafi sabo fil. Bayan ta

"ajjiye ta kuma shigowa da ™atuwar leda sha™e da kayan tea komai na gongoni sai sikari ne kaWai na kwali mai zaki ce, wasu na kiranta mai iyali."

Data sake shigowa sai ta dure ™atuwar kular abinci da wata babbar farar leda.

"""Ga sabulun da omo Baba malam yace a kawo muku. Allah ya raya Mardiyya """

"""Ameen in da gaske kike yi. Shi zakaran da Allah yaso sai yayi cara ko ana shawo ana muzuru sai yayi"

"caranshi."""

Rahama na gama faWin haka ta buWe ledar ta suri ™aton omo ta fice zuwa tsakar gidan.

"Ni kuma tea kakkauta na haWa cikin ™aton kofi, na saka lokaci a cikin kular da aka sha™o mun da"

lafiyayyar jallof mai nama da kifi.

Sosai na zage ina cin abincin.

Na jiyo Rahama tana ta dura ashariya a tsakar gida.

Ban dai ji muryar kowa ba halamu ya nuna wani abun ta gani shi yasa.

"Muryar Baba malam naji yana gargaWinta akan ba'a mishi hayaniya bare ashariya a gida, ta kiyaye in ba"

haka ba zata koma inda ta fito.

Daga nan na jiyo takun tafiyarshi zuwa Wakin da nake. A bakin ™ofa ya tsaya.

"""Sabuwa an kawo miki kayan shayi da sabulai?"""

"E an kawo gasu nan"""

"""Akwai wani abu ne da ake bu™ata wanda ban siyo ba?"""

Shiru nayi ina nazari gaskiya yayi ™o™ari ya sai komai da komai ko Wan halak albarka.

"A_a babu a yanzu dai"""

"""To shikenan gobe za'a soma miki naman gashi. Ki zauna da shirinki kina yin arba'in zaki tare a gidanki."

"Allah zai rufa asiri ko babu yawa ni zanyi miki kayan Wakin sai ki sanar ma iyayenki"""

Nan ya tafi ya barni da mamaki baki a hangame jin wai zai mun kayan Waki.

"A idanunshi kaWai inna kallla ina hango ™iyayyar da yake yi mun, amman duk da haka yana ™o™arin lallai"

sai Babangida ya aureni.

Murmushi kawai nayi naci gaba da kora tea.

Malam Baba:.

Daga wajen Sabuwa kai tsaye Wakin Malama Babba ya wuce.

Suna zaune ita da Yaya Hanne suna tattaunawa dangane da batun haihuwar Sabuwa suka jiyo muryarshi

da ma abinda suke sa™awa mummuna.

"Basarwa yayi tamkar bai ji ba dan ko a fuska bai nuna ba, Malama Babba kuma sai tasha jinin jikinta."

Ganin babu damuwa a fuskar Malam yasa ta fito da fara'arta shi kuma ya riga da yaji komai murmushi kawai yayi.

"""Yauwa Babba batun auren Babangida da Sabuwa ne. Ki faWa ma Wanki ina neman dubu Wari biyu a"

hannunshi kafinnan kafin sati uku.

Kafinnan kuma ya kawo kuWin ragon da za'aima ³arshi hakika nera dubu talatin cib.

"Ku kuma mata ta Sangarenku sai ku soma shirye_shiryen biki"""

Mamaki yasa Malama Babba ta kasa rufe bakinta data hangameshi hangangan.

Har Malam ya kusan barin Sarayin sai taga ya juyo.

"""Af Babba na mance. Zai soma iya fara neman gidan haya tun yanzu kinsan gidajen haya tsada suke yi"""

Dole ta haWiye malolon daya tokare ma™oshinta murya a dashe tace.

"""To Malam zan faWa mishi sa™onka."""

Šaki ta shiga ta zauna daSas a kusa da Yaya Hanne. Sai salati kawai suke yi a cikin wannan yanayin

Babangida ya shigo da sallama ya samesu.

Yasan baya raba Wayan biyu shi yasa ma bai tambayesu meke faruwa ba.

"""Babangida kaga dai abinda ka jawo mana yanzu muna ji muna gani zaka auri wannan yarinyar maras"

tarbiyya ta zamema uwar ΄a΄anka. Wannan wanne tarihi Malam yake son kafa mana mai zafi haka. Yaya

Hanne duk wani shirinmu ya rushe ki duba sunan uwarmu ya saka ma yarinyarnan sabida ya nuna ma

"˜arama iyakata"""

Babangida ya razana sosai da wannan labari daya riskeshi. Har ™asan zuchiyarshi baya jin ko Wigon son

"Sabuwa face zallar sha,awarta. Manufarshi shine cin moriryar ganga kawai kamar yadda akema duk wata karuwa."

Sai gashi yaci biredi yana tunanin ya yaga leda ashe ledar bata yagu ba.

Yafi kowa sanin rashin tarbiyyar gidansu Sabuwa shi a iyakar saninshi ma bai taSa ganin gida maras

"tarbiyya da kowa Wan iskan kanshi bane kamar gidansu Sabuwa ba, wai ashe Malam Baba zai yarda a"

"auro Sabuwa a matsayin surukar gidan malamai gaba da baya? Tunaninsu duk barazanace duk da sun san malam kaifi Wayane amman duba da tarbiyyar gidansu Sabuwa yasa suke tunanin ba za'ayi auren ba"""

Iska ya busar yana jin wani zazzaSi_zazzaSi na buso mishi.

"""Saratu ku kwantar da hankalinku. Gobe ki tambayi Malam zuwa ™auyensu in ya barki zamu je a motata."

Inma hagu ta™i yi zamu koma dama. Kinsan Allah Babangida bazai Auri wannan yarinyar ba. Kuma dena

"damun kanku"""

"""To Yaya Hanne ai bazai taSa barina zuwa ™auyansu ba sabida yasan abinda zai kaini. Kuma kinsan"

"kafiyar Malam kuwa? Balle wannan abun yadda ya Waukeshi da zafi. Kuma duk ya fimu tsanar Sabuwa da danginta ma."""

Yaya Hanne ta dafa Malama Babba tace

".""zanzo gobe zaki ji zuwa da dawowan Saratu. Kai kuma saika kiyaye gaba kana ganin halin da kasa"

"mahaifiyarka a ciki. Gata da kishiya sun samu abun goranta mana marar goguwa."""

"Shi dai Babangida yama kasa cewa komai, zuchiyarshi sai tu™a mishi take yi. Duk duniya babu wanda"

"yake so sama da sabuwar budurwarshi wadda a lokacin ita ce a gaba. Duk da baya jin aurenta, amman"

tana da dukkan abinda yake bu™ata a jikin mace.

"""Ka fasa bankinka ka ciro dubu talatin zan kaima Malam kuWin sayen rago kamar yadda ya bu™ata"""

Cewar Malama Babba.

Haka dole Babangida yayi abinda Malam yace musu. Malama Babba taje ta sameshi ta bashi kuWin.

Ta Sangaren Babangida yamma nayi ya isa majalisarsu nan akaita kacancana zancan masu zugashi ya

aureta ya koya mata darasi sunfi masu cewa kada ya aureta yawa.

Ya gamsu da ya aureta yai mata wula™anci na fitar hayyaci yai mata sakin wula™anci.

Murmushi mugunta yayi da ya hango irin rashin mutuncin da zaiyi mata.

Sai yaji hankalinshi ya kwanta a sauwa™e zai koyar da'ita darasin rayuwa.

"Washegari."""

Malama Babba tai ta jiran Yaya Hanne ba ita tazo ba sai wajajen sha biyun rana.

Abunda tazo mata dashhi yafi ™arfin tunaninta bata taSa zatin haka ba.

"""Kinga wannan maganin ? Kina zuba ma Malam a abincinshi wallahi zancan wani aure ya ™are. A ta™aice"

"duk taurin kanshi sai yadda kika yi dashi Allah"""

Jikinta da hannunta har rawa suke yi ta amshi maganin. A ranta ta gamsu kota wanne irin haline da dai a

auro Sabuwa gara ta kauce hanya.

"""Amman Yaya Hanne babu abinda zai sameshi ko?"""

"""Babu abinda zai sameshi. Ke dai ki saka mishi maganarnan a kasheta kowa ya huta"""

"Haka ta amsa akan nan da kwana biyu in girkinta ta zago zata zuba mishi."""

SABUWA:.

"Sassafe Malama ™arama tamun wankan jego, tayi ma jinjira wanka, Rahama kuma ta wanke kayan da"

muka cire har da nata.

Ina daga gado ina cin tuwo Rahama kuma tana waya dasu Rakiya tana sanar dasu halin da ake ciki biki

saura kwana talatin da bakwai kenan.

"""Rakiya inaso kije ki samu Zahira ta gidansu Malam Bala ta haWo mana magunguna zamu biyata daga"

"baya sabida a tari abun da wuri kunga bamu da lokaci"""

"""To ba zuwan bane matsalar ba. Kuma nasan Zahira zata baku bashi. Waye zai kawo muku gida babu"

"kowa sai Uzairu zuchiyata kuma kun dai san halin wannan kafaffen tsohon."""

Rahama tace.

"""Aba Uzairu zuchiyata ya kawo in yazo ™ofar gidan ya ba almajiran gidan zasu kawo nana."""

"""Rakiya tace."

"""To shikenan zanje yanzu, dan dama gyalena na hannuna inaso zanje dubo Adama ne jikin dai ya™i ance"

"kishiyoyinta sun rarrafa sun kaita ™aramin asibiti kuma ga ba kuWi. Da ™yar na haWa dubu biyu su Sadiya suka harhaWa mun shine zanje. Zan soma zuwa wajen Zahiran tukunna"""

Da haka sukai sallama.

"""Lolo kinji jikin Adama yayi tsanani kishiyoyinta nema suka kaita asibiti."

Ni dama gida Rakiya ta dawo da'ita duk da gidanma babu daWi. Inma ta dakkota abinda zata ci shine aiki.

Amman wallahi da kashe auren akayi da sai yafi.

Kwananta nawa dama a gida tayo yaji da kanta yinwar gidan da rigimar gidan yasa ta kwashi jiki Aisha ta

"rakata ta koma Wakinta."""

Ai da tana jin magana da tuni ta kashe wannan ™addararren auren. Allah dai ya bata lafiya. Amman

"Rahama ni da an bar wani maganin matan. Ni ba auren soyayya ba ba komai ba ina ni ina wani shan magunguna azo a barni da biyan bashi."""

Rahama tace.

"""Ai ko ba aure zaki yi ba yadda kika haihunnan yana da kyau kiyi gyara sosai. Ki bar ganin irin auren da"

"zaku yi kenan. Sanda zai lallaSo ya biyo dare mu muna ina? Su Labbai su Adama da Layuza duk ba irin auren da suka yi ba kenan?"""

Haka dai mukaita hirarmu muna daga Waki.

Da yamma sai ga kunun kanwa da naman gashi sha™e da kwano naci naci har saida na ture.

"Ina samun kulawa a gaskiya fiye da tunani. Kullum sai naci naman gashi, ga magunguna Rahama sai"

durkamun take yi harda nasu tsugunno a gaushi duk inayi.

Ranar suna aka yanka mun katuwar tinkiyata a soye marau aka kawo mun halamu sun nuna ko tsoka

Waya basu Wauka ba. Ni dai nasa Rahama ta raba nama gida biyu aka kira Uzairu zuchiyata yazo ™ofar

"gida Rahama ta bashi ya kaima Rakiya harda dubu biyar na bashi dan Adama tana gida auren nata ya mutu ga jinya har yanzu bata warke ba."""

Malama Babba:.

Ta Sangaren Malama Babba tayi iyakar yinta Malam yaci wannan maganin a ranar da yaci sai batai mishi

maganar ba sai washegari ta tareshi da maganar suna kwance.

"""Malam yanzu wai da gaske kake yi yaronnan Babangida shi zai auri wannan yarinyar ΄ar marasa"

tarbiyya? Ka duba watan yarinyarnan ta shiga na gomaa kenan a gabanmu mahaifinta kawaline kuma maras mutunci yanzu duk girma da darajar wannan gidan namu mai daraja da surukan da yaranmu suka

"auro daga gidan malumta a rasa wacce za'a gaiyato cikin haular sai Sabuwa?"""

Tsam yayi yana kallonta. Tunda ta iya tunkararshi da wannan maganar tabbas yasan akwai abinda take

sa™awa abinda yaji suna faWa ta aikata kenan. Sai yayi ™o™arin gwadata ta hanyar cewa.

"""To yaya za'ayi Wanki ne ai ya jajiSo mana ita. Sai nake ganin kamar dashi da ita ™waryar sama ke dukan"

"ta ™asa. Ko wacce ™warya da abokin burminta, in banda abinki mugu ai shi yasan makwancin mugu, ba'a"

"abota sai hali yazo Waya"""

Yayi shiru tare da kafeta da idanu yana karantarta

"""Malam bambamcinsu a fili yake. Kai mai mutuncine, malami mai koyar da al'umma. Ka duba"

makarantarka Walibai nawa garemu muna ba mutane karatu harda tarbiiya. Nima Malama ce da

taimakonka na zama hakan. ˜arama ΄ar gidan malamai ce. Kaf surukanka daga gidan malumta suka fito.

"Taya zamu haWa iri da Sabuwa"""

Dariya yayo sosai wanda ya daWe bai yi irinta ba.

A baWini kuma zuchiyarshi ji yake tamkar zata faWo dan raWaWi. Yafi kowa ™in Sabuwa yafi kowa ™unsan

"ba™in ciki da takaici in yaganta, ko yaji muryarta da duk danginta da abinda ma ya shafeta baki Waya. Shi ta Sangarenshi zai aurama Babangida Sabuwa ne sabida ita yarinyar da aka haifa, an riga da an haWu ko ba'a soba. Dalili na biyu zai aura mishi itane a matsayin horarwa dan yayi imanin Babangida zaifi son ya auro ΄ar mutunci, ΄ar manyan mutane, ™ila ma ΄ar malamai kamar yadda sauran ΄an uwanshi suka yi hakan. Na uku, zaiyi hakanne a matsayin hannunka mai sanda ga sauran yaran gidan. Duk da baya fatan a sake samun Babangida kashi na biyu, amman kashi na farkon ma ai baisan za'a samu ba. Hausawa suka"

ce gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah.

Dalilinshi na huWu shine ita kanta Sabuwan ai mata adalci a taimaki rayuwarta a tsamota daga cikin

duhun da take. ˜ila ta sanadinta ΄an uwanta su shiryu. Domin har ga Allah duk yadda yake ™in Sabuwa yafi ™in Babangida fiye da'ita. Ita gaskiya gaskiya ce baya bayan kowa sai bayan adalci. WaWannan sune

manyan dalilinshi.

"""Yanzu dai mu kwanta da safe ma ™arashe maganar na gaji, gashi ina da raWin suna da asuba"""

Yana faWin haka ya juya mata baya.

Zuchiyarta fes ta kwana amman da asuba kafin ta bar turaka Malam ya kankare mata hadda ta hanyar

wasu kalmomi marasa yawa sai firgitarwa da sare guiwa.

"""Babba ki sake sanar da Babangida batun kuWaWennan lokaci nata gabatowa, sannan ya tabbatar a"

"satinnan ya nemi inda zai zauna sabida ayi fenti da komai. Za'aje ayi mata jere ranar talata mai zuwa rana ita yau kenan."""

Yana gama faWin haka ya nufi hanyar waje saida ya fita ya girgiza kai yace.

"""Mata kenan mai ilimi ma kenan ina ga jahila kuma?"""

"Haka dole ™anwar na™i Malama Babba ta saduda, ita ta sai da sar™arta ta dan™ama Malam Baba dubu"

Wari biyu daya bu™ata a wajen Babangida. Shi kuma Babangida ta barshi da neman haya.

Harma an samu ciki da falo da bayan gida da kitchen sai dai gidan gidan yawane sosai. A haka aka kama

akayi duk gyare_gyaren daya dace kamar yadda Baba malam ya bu™ata dai.

Ta nashi Sangaren kuma Malama ˜arama ya kira ya bata dubu Wari biyu da hamsin. Da wasu dubu Wari

uku daban.

"""Šari biyu da hamsin Win kayan lefe zaki haWo mun ke da Larai. Wannan Wari ukun kuma kayan gado da"

"kayan kitchen nake son a sai ma yarinyarnan kina ganin zasu isa ?"""

Sai da Malama ™arama tayi murmushi kafin tace.

"""Na lefen dai ya isa zata samu kaya da yawa. Ammman kaga na kayan Wakin a gaskiya ba zasu isaba in dai"

"kaya masu kyau za'ayi mata. Sai dai in irin kayannan na bakin kasuwa za'a sai mata"""

Kai ya girgiza yace.

"""A_a ayi mata komai mai kyau. Kamar yadda kuke ma yaranku. Yanzu to kawo Wari ukun ki gani. In yaso"

"duk abinda ake bu™ata a rubuta komai da kudinshi da jumulla. Yanzu ku gama na lefen tukunna"""

Ai kuwa haka akayi a cikin kwana biyu da Malam Baba ya basu suka haWa akwatuna guda biyu da kit

sha™e da kaya masha Allah.

Malama Babba tana zaune tana lissafin yadda ta zama bora a gidan mijinta sai ganin Larai da akwati

kici_kici tayi.

"""WaWannan akwatunan kuma daga ina Larai""?"

"""Kayan auren Babangida ne Baba malam ne ya bamu kudin muka haWa"""

Da mamaki ta kalli Larai ta dubi Wawo dake zaune yana dama ma Baba malam fura.

"""Kuma sai baki kai Wakin uwarki ba tunda itace uwar bikin ba?"""

""" Baba malam ne yace a kawo miki"""

Kafin ta kuma cewa wani abun sai ga Malama ˜arama ta shigo da sallamarta. Sai da ta nemi waje ta

zauna kafin tace.

"""Babba ga akwatin Babangida nan na haWo. Toh Malam yace da magriba Wawo da Bashiru su kaimu"

"gidansu Ita Sabuwa mu kai musu akwatin. Sai ki ma Yaya Hanne Magana. Goggo ma tana kan hanya tare zamu je akai."""

Sai da Malama Babba ta hadiye yawu mu™ut kafinnan tace.

"""Toh shikenan. Allah ya kaimu da rai da lafiya."""

"""Ameen Babba Allah ya albarkaci auren kawai zamu ce"""

Tana gama faWin haka ta fice.

Malama Babba tace.

"""Har fishin da Malam yake yi dani yayi irin wannan ™amarin?"

"Taya zan ™aunaci wannan yarinyar ai har gaba da abada"""

MRS BUKHARI

""""

"[8/14, 7:22 AM] +234 802 205 9556: IDAN KAYA YA GAJI..."

GAMMO MA YA GAJI

BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ˜AMSHI

LITTAFI NA UKU.

SHAFI NA BAKWAI 7

"""Ai muma Malam Baba ya tutsiyemu na harhaWo kan mazan gidan dubu Wari uku muka haWa mishi."

"Babangida ma saida ya bayar. Bai faWa miki bane?"""

Kai ta girgiza tace.

"""Bai sanar dani ba. Damuwar dake damunshi yaushe zai bashi damar sanar mun da wani abun. Yau"

"bamma saka shi a idanuna ba. To me Malam zaiyi da kudi?"""

"""Sai Allah bazai wuce duk

Please Login or Register in order to submit comment