You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shafi, ni kuwa"

"tuni na daWe da biya wannan shafin wani sabo Sagir ya buWe mun. Ina zuwa bari kiga"""

Jakarta ta buWe ta ciro wata leda Wauke da wani abu curi biyu. Yagar ledar tayi ta sanya mun curi Waya a

ledar ta mi™o mun.

"""Kinga wannan ki tabbatar kuna shiga ki saci jiki ki cusa Hmm wallahi sai kin kusan haukata Khalid dan na"

"fahimci son da yake miki yana da ™arfi."""

˜arSewa nayi maza na cusa a tawa jakar.

"Shikenan sai munyi waya. Yau dai muma zamu kwana da ac."" Tafawa muka yi, da wannan mukai sallama"

"kowa ya kama gabanshi."""

"Muna tafe a mota hannunshi daya akan sitiyari Wayan hannun yana sar™e da nawa hannun, muna"

hirarmu har muka gida gidansu

Ashe a cikin gidan iyayenshi suke Wakinshi dai ta wajen gidan yake tsakar gida kenan. Ta ™ofar baya ya ja

hannuna muka shiga.

"Kada in jaku da tsayi saida na kwana biyu cir a cikin gidansu Khalid, dan ko washegari da muka je"

"birthday muka dawo gidansu yasa aka zarto damu, ya duramun kayan maye sosai dani dashi duk a buge muka kwana."

Khalid shi ya koyar dani shan kayan maye.

Washegarin ranar birthday Win ma sai wajajen azahar na watstsake sabida a lokacin sigari kaWai nake sha

"itama Akara ke bani in Wan ja in yazo ban taSa shan guda ba, sai dai ya kunna mu dinga sha tare."

"A gaggauce nayi wanka hankalina ya koma gida kuma, a wannan kwana biyun da nayi babu wanda da"

wasa ya kirani yaji ko lafiya. Sai Halima data kira tana mun masifa akan takalminta zata fira tanaso tasa ance mata na saka.

"Saida Khalid ya kuma yi mun shopping mai yawan gaske har kayan abinci nasa ya sai mana, ya siya mun"

"waya Soni ta wannan zamanin, ya bani dubu ashirin kash a hannuna."

"""Baby gobe zamu yi tafiya da Abbanmu zan rakashi umara. Me kike son zan sai miki?"""

Kafin in bashi amsa naga su Adama sun fito daga makotanmu ita da Labbai da tukunya ΄ar babba a

hannunsu saida suka shiga hankalina ya dawo gareshi nan na narke mishi akan nifa bazan yarda ba.

"Saida yaita lallabani kana na amince mukai sallama, da kanshi ya fito ya sauke mun kayayyakina yaja"

motarshi ya tafi.

Ina waigen yaron da zan gani ya shigarmun da kayan. Sai na jiyo ihu da faWan Maigogul da Rakiya ya fito

ta biyoshi har zaure tana yaSa mishi magana.

"""Sai kuma kiyi amman kinsan Allah Rahama nanda wata uku bata gidannan dole ta auri yaronnan bazan"

yi rantsuwa a banza ba. Yanzu da wancan Alhajinne yayi mata cikin da gasken da sai mu shiga mu fita ai

ya aureta ko dan dole. Amman tunda kunnena yaji cewar wannan mitsiyacin yaron da yake jele a ™ofar

"gidannan shi yayi mata aure dole. Ku Waura abinci anjima masu kawo kaya akace zasu kawo"""

"""Ai kuwa baka isa ba a wannan karon. Kana ganin rayuwar wahalan da Layuza take ciki, ita kanta Adama"

"jibi duk yadda ta lalace haka zakai ma yaran naka?"""

Kuguna duka biyun suna ri™e bakina a taSe nake kallonsu. Maigogul ne ya hangoni da kayan alatun dake

gabana. Da mugun sauri ya baro Rakiya.

"""Lolo wannan kayan abincin da ledojin kuma fa? Badai Akara bane yayi miki wannan hidimar ba."

"Dan ko jiya yazo nemanki gida"""

Ina dariya nace.

"Wane Akara Hmm Maigogul sabon saurayi nayi Wan masu kuWi kuma da Aure yake sona"""

Da dariya ya tuntsure dashi shi da Rakiya har suna haWa baki da fadin.

"""Alhamdulillah """

Tare da Maigogul muka dauki kayan muka soma shigarwa.

"""Gaza ga cicciSeSen buhun shinkafa fita ka shigo dashi"""

Cewar Maigogul daya saki katon din taliya a ™ofar Rakiya.

"""Kai Sabuwa farawa da iyawa, a lafiya dai kanwata ta kaina sai dake wallahi"""

Ya irin hade hannayensa irinna ™auraye yace.

"""Cau_cau Lolo """

"Dariya kawai nayi na shige Waki inda anan na tarar da Rahama zaune tanata kuka, Adama da Labbai sun"

"rufu a kanta"""

"Rahama meke faruwa naji ana cewa zaki Auri iliya. Shi Alhajin ™aryatawa yayi yace ba cikin nashi bane?"""

"""Ke dai Lolo bari kinsan Maigogul dai in yaso kafiya. Munje ges house wajen Alhaji kamar yadda yace"

"mana. Allah kaWai yasan irin kudin da aka ba Maigogul dan ko Rakiya dubu Wari ya bata, ni kuma ya bani dubu hamsin. Daga ges house muka wuce aka bani maganin zubar da ciki a wajen Abacha."

Ina kwance cikina na murWawa Iliya yake faWamun yana ™ofar gida na faWa mishi cikin nashine sabida

dama nashi ne.

Muna tsaye muna mayar da zance Ashe Maigogul yana jinmu shine yace nan da sati Waya ya turo kayan

Aure da akwati da sadaki nan da kwana goma a Waura mana aure. Shine ya ro™i a barshi wata uku. Shine

"tun shekaranjiya Rakiya dashi suke rigima, Hauwa na kuma zugashi"""

Rahama ta karashe tana jan tsaki. Adama tace.

"""Ni da wannan yawon gara ki auri iliyan ai kin huta. Jibi fa Lolo da kamar ba zata yi yawo ba. Amman"

"kunce kwananta uku ko biyu ne bata gida."""

Labbai tace.

"""Adama kenan. In bata fita ba so kike ta zauna ba™in cikinsu Rakiya ya kasheta, sannan sutura, abinci,"

"magani in baka da lafiya, audigar yin jinin al'ada, sabulu turare, kayan kwalliya a matsayinta na mace"

"waye zaiyi mata. Ni burgeni tayi fa. Ke meye baki shuka ba, ke da kika kwashe kayanki kika koma shagon saurayi."

"Ina Aliya take bata gida sai jifa jifa take zuwa. Waccan ΄ar iskar ta Wakin Hauwa itama zuwanma ta dena"""

Su Gaza ne suka shisshigo da kayayyakin dana shigo dashi.

"Kayan daWin aka rarraba kowa ya Wauki kasonshi, kayan abinci Rakiya ta adanasu a gefe Maigogul sai"

"koWani yake ta faman yi, daga ranar Maigogul ya soma ji dani dan na fita zakka cikin ΄an uwana."

Ni sabida ma kaina da nauyi baccina nayi na barsu suna girkin masu kawo akwati ance yau zasu kawo.

"Sai bayan magriba suka iso Hmm kayansu a jakar buhu ta bacco atampa kala biyu lesiri kala Waya, shadda"

"Waya, sai takalmi da jaka, da turare shikenan suka bayar da ha™uri haka dole aka karSa. Hauwa kuwa saita samu abun faWe taita yamaWiWi da wannan kaya a ma™ota."

"Rahama dai duk da Sari tayi hakan baisa ta zauna ba, kullum bata gida"

Kwana uku da yin wannan ranar asabar da rana Rakiya ta haifo Wiyarta itama fara sol da'ita. Abun tausayi

yarinyar wallahi. Ashe ma ba mai tsayin rayuwa bace.

A lokacin ina da kuWi kace_kace dan ko tafiyar Khalid ya aiko Abokinshi Sagir ya kawo mun kuWi. Ga waya

"munayi akai akai, dubu ashirin na ™irga ranar suna na dan™ama Maigogul ya sawo rago aka yanka ga kayan abinci dama muna dashi. Ni ranar a gadon Mamansu ³ar Shuwa muka wuni munata hirarmu ta"

΄an mata muna dariya. Bayan suna Allah yayi ma yarinyar rasuwa. Mu dai mun taya ta murna.

Gaza ya saka tijara akan su Rakiya suyi ha™uri da haihuwa haka. Maigogul yaita kutuntuma mishi

ashariya shi kuma yanata karta wu™a a ™asa.

Sagir wajen taran dare yazo ya fita da ³ar shuwa kafin na nufi gida.

"""Ke Sabuwa"""

Cewar Akara da yazo ™ofar gidanmu harda yaranshi biyu sun wani tattare hanya dole naja na tsaya tare

da harWe hannayena a ™irjina.

"Lafiya kake mun kiran karnuka Akara?"""

Hannu yasa a baki. Ya lailayo wani ashar ya Wuma.

"Kar ka sake irin wannan zagin a ™ofar gidannan"""

Daga faWan haka ya ™araso gabana kamar zai dageni.

"""Dan uwarki in aka kuma me zaki yi?"""

Kafin ya rufe baki nasa hannu na hankadeshi yaje cikin yaranshi sai su suka rikeshi.

Wu™a na zara a ™ugunshi na saka mishi a wuya. Take yaranshi suka zazzaro wu™a. Da hannu yayi musu

"nuni da su mayar, ni kuma ya dubeni yayi dariya."

"""Dama ance mun akwai wani Wan balaja'u da yake sunturi a ™ofar gidannan a mota. An tseguntamun"

wajenki yake zuwa. Kina so ki jama Wan mutane wahala ko?

"Kar kiga ina sonki kiga kamar bazan iya hukuntaki ba"""

Hannuna ya dam™e ya murWe hannuna zuwa bayana ya zare wu™ar.

"""Kuntun uba me nake gani a ™ofar gidannan Akara?"""

Muka jiyo muryar Gaza da fitowarshi kenan.

"Babu shiri suka shiga taitayinsu. Cukumeshi Gaza yayi ya makureshi a bango. Bawai ™arfi Gaza ya fishi ba,"

"a lokacin baifi Gaza iya iskanci ba. Amman kunsan irin Wannan mutanen suna girmama na gaba dasu, a harkar dabanci Gaza na gaba dashi."

"""Sai mai gida tuba muke yi adaiyi ha™uri. Sabon Wan balaja'u ta samu shine wai yarinyarnan harni take"

"zaranma wu™a ta dauramun a wuya"""

Tsaki nayi na dubeshi nace.

"Daga yau sai yau kada ka sake zuwa inda nake soyayya ce na dena bana sonka"""

Ya suka ™are sai Allah ni dai nayi shigewata ciki

"Gaga gaga lokaci yaita tafiya har KHALID suka dawo umara ya kawo mun tulin tsaraba, kuma a ko da"

"yaushe muna yawan haWuwa dan sai in kwana uku hudu tare dashi ko a gidansu ko a Hotel club kuwa kullum sai munjeshi Khalid dai ya bude mun idanu ya koya mun shaye_,shaye gashi da shegen san sigari"

duk ya Waurani akan layi.

Da bikin Rahama Khalid ya bani kuWaWen anko da duk wani gyaran jiki. Akai biki lami lafiya aka kai

Amarya Wakinta.

Bayan wata uku da bikin Rahama Adama ta haifo Wanta namiji na biyu kenan kunsan ai ta farkon macece.

"Gaga_gaga abubbuwa sukaita faruwa daga Sangaren gidanmu. Wannan tayi ciki a zubar, wannan tayo"

nata a haka har Labbai tayi aurenta ita dai babu laifi a lokacin mijinta yana da Wan na rufin asirinshi.

Kab cikin gidanmu kowa sha'awata yake yi yadda nake dama kuWi. Sai dai ko da yaushe ni da Khalid a

"cikin faWa muke, yadda samari suke kulani in mun fita. Da mun koma Hotel zai lulluSeni da faWa yai ta"

"tayi, inna bashi ha™uri ya™i hakura sai in watsar dashi dan kanshi yake ha™ura yazo har gida ya sameni."

Muna dai tare anata murzawa har Khalid ya gama jami'arshi. A lokacin ne ya tunkaro iyayenshi da batun

aurena mahaifinshi yayi fur yace shi atafau ba lokacin Khalid zaiyi aure ba. Kuma sun riga da sun zaSa

mishi diyar ™anwar mahaifiyarshi Zaliha.

Ranar da Khalid yazo yake faWa mun wannan maganar naci kuka tun yana iya rarrashina har ya kasa sai

³ar Shuwa ya kira tazo ta fito dani daga motarshi. Gashi a daren da yazo mun da wannan Maganar

washegari zai bar ™asar zuwa yin digirinshi na biyu ya kasa faWa mun.

Yana jan motarshi jini ya ballemun babu shiri na dur™ushe a ™asa.

"³ar Shuwa zan mutu ki kaini cikin gida """

"Na faWa da muryar kuka, sabida tsabar ruWewar da tayi a wajen ta barni taje ta kirawo Hauwa a guje suka"

"dawo. Rakiya bata gidan, ΄an matan gidan babu kowa."

Da dai ina kwance a tsakar Wakin Hauwa da jinin ya™i ya tsayane dole Hauwa ta Waukeni zuwa Wan

™aramin asibitin kuWi dake kusa damu. Sannan ta kira wayar Rakiya ta sanar mata bata jima ba sai gata.

"""ari tayi cikine a jikinta da bai wuce wata biyu ba. zamu bata gado sakamakon ta jima tana zubar da jini."

"Sannan akwai wani tashin hankali da taji wanda shine yayi mata silar zubewan cikin dake jikinta."""

Kamar a mafarki naji Dr ta yima su Maigogul bayani. Babu shiri na buWe idanuna na kalli Maigogul shima

ni Win yake kallo.

Idanuna na lumshe wasu hawaye suka gangaromun.

Nasan da Khalid yananan yaji labarin halin da nake ciki da yanxu yananan cikin matsananciyar damuwa.

"Yanzu wai da gaske Khalid ya rabu dani kenan?"""

"""Ai baki yi kuka ba tukunna. Dan nayi ba™in ciki da cikinnan ya zube ba tare da nasan ubanshi ba. To"

"kukan na uban me kike yi haka nace?"""

Na tsinkayo muryar Rakiya a kaina.

Maigogul ne ya hanata magana.

A gurguje

"nayi jinya kusan na sati guda, sabida rashin gata ban warke ba aka sallameni. Ina kwance babu lafiya, ga"

"damuwar rashin Khalid, ga takaicin ni nake saima kaina komai na ci ko sha hatta kuWin asibiti ni na biya da kuWina, face Wan abinda ba za'a rasaba da Rakiya ta biya. Amman Maigogul ko ficika."

Wannan shine rabuwata da Khalid zance a ta™aice.

Amman mun buga soyayya sosai da sosai

Mahaifanshi sun gama bincike a kan gidanmu ne suka ci karo da mummunan labari a kanmu.

Banga laifinsu ba gaskiya.

MRS Buhari

https://chat.whatsapp.com/JmCasXpUuuT0J6dfLTWFNk?mode=ac_t

.

18066696785.

Hussaina Bello

HAJIYA KAYAN KITCHEN KIKE SO MASU SAU˜I DA KYAU. KO KUMA SARIN KAYAN KITCHEN KIKE SO KI

SOMA KIN RASA INA ZAKI SAMU AKAN FARASHIN DA KEMA ZAKI SAMU ALKHAIRI?

H@H AVAILABLE WHOLESALE AND RETAIL DUNIYA NE

MAZA TUNTUE HUSSSAINA BELLO KAI TSAYE A LAMBAR WAYARTA.

KO KUMA SHIGA CIKIN ZAURENTA DOMIN KASHE ˜WAR˜WATAR IDANU

IDAN KAYA YA GAJI..

GAMMO MA YA GAJI

BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ˜AMSHI

LITTAFI NA BIYU

SHAFI NA SHA TAKWAS

Gaga_gaga_gaga_gaga

Haka abubbuwa sukaita faruwa sannu a hankali rayuwar take ta murWawa. Yau ace Gaza yayi sara an

"kama shi, gobe ace sun yi faWan daba tsakanin ΄an wannan unguwa da ΄an wannan unguwa. Haka Sama shima shine wannan sitetion gobe shine ya saci akuya gata rago zai sato. Ga ΄an matan gidanmu yau ciki, gobe zubarwa ko wanne cikinmu da irin jawo maganarshi. Ni kuwa tun bayan dana warke daga ciwon rashin Khalid na sake zamewa bo™ararriya, samari masu kuWi na yisu basu da iyaka, kuma dukkansu babu laifi suna kulawa dani a lokacin da muke tare, Allah ya saka mun wani irin farin jinin da duk inda muka shiga sai an tayani wannan dalilin yasa na zama ta gaban goshin Maigogul yana matu™ar ji dani sosai ."

"Duk wannan farin jinin Sai dai su babu al™awarin aure a tsakaninmu kamar yadda mukayi da Khalid, a lokacin ni kaina babu wani aure a gabana ina ganin yanda su Aliya, su Rahama, da Layuza sukai aure aka sakosu duk suna gida a matsayin zaurawa a wannan ™adamin. Kana ina ganin masu auren gidan namu irin ™orafe_™orafen da suke kawowa da irin yadda suke yau yaji gobe kome dai, jibi anyi doki in doka ko da miji ko da ™anin miji. Wannan rashin mutuncin ba ya Aliya da Labiba a kaf gidanmu. Su baku ji labarinsu ba, da sauran ragowar ΄an uwan namu ko? Uhm kunsan ba komai bane zai zanu a rubutashi"

ba shi yasa. Haka nake yin samarin a rabu wasu da dalili wasu babu wani dalilin kirki.

Maigogul kuma tukuru ya dawo harkar tsubbu a lokacin anyi wani irin rikicine na kawalai kunsan suma

"harda asirce_asirce suke jifan junansu. Maigogul da wata azal ta kamashi saida yayi wata shida a gidan yari abar kaza cikin gashinta. To da fitowarshi sai ya tsiri harkar kuma abun mamaki yana samun kudi sosai, sai ya jefi tsuntsu biyu da dutse Waya ga bokanci, ga kawalci yana tallatama matan aure da zawarawa ha dama ΄an matan. Ni Maigogul ya ja a jiki nake ™ulla mishi magunguna sabida a cikin ΄an gidanmu na fisu sau™in kai. Kuma a lokacin ina tare da Tijjani yana mun Sarna da ™udi, hannuna a sake yake ko nawa Maigogul ya tambaya in ina dashi ina bashi haka ma Rakiya, kuma ko fita nayi ina siyo kayan abinci in ajjiye musu sai suji dana cefane. Wannan dalilin yasa Maigogul ya jani a jika sosai, da"

"sannu har nasan yadda ake dukan ™asa, a duba taurari, da ma karanta bayanin ™asa. Abinda ya shigemun"

duhu ina tambayarshi yana faWa mun. Yace mun gada yayi a wajen mahaifinshi shi kuma ni ya zaSa da ya

gadarma.

"Bari kuji wani sirri. Harkar bokanci duk fa yaudarace, mafi yawanci ™aryane da hasashe wallahi, sai wasu"

"΄an siddabaru da basu da wahala da ake yi( Mata muji tsoron Allah bokaye su dena yaudararmu suna rabamu da Ubangijin mu. Duk abun bugace kawai ga tarin zunubi da mutum ya Waukarma kanshi, uwa uba ga rashin biyan bu™ata. In Allah yaso ya kamaka kuma sai kije wajen bikan ™arya ya daka kuka ya baki, kisha kuma ki samu biyan bu™ata. Amman fa ku sani Ubangijin da yayi bokan, ya yiki yana madakata yana jiranku acan zaki yi mishi bayani a inda ba'a ™arya) Wani sa'in in naga mata sun dawo suna ma Maigogul godiya harda tukuici sai inta mamaki, domin nasan bayan tukunya da ruwan tawada nake ji™a mishi a bokitin fenti in ban fita ba in tayashi da daddare mu Waura a matsayin rubutu. Mafi yawan magungunan da yake basu na sha ararraSine, na haya™in kuma itacen dorot ne yake bulbula turaren binta Sudan a ciki. A hakan har sai da takai ta kawo sai Maigogul ya faWi mata nawa zai iya gani sabida layin da ake yi mishi. Kaji kuwa lokacin su Rakiya a gaskiya sun goge wuyansu dan har wani ™iba sukayi sunci uban talauci Rakiya ta sake haske, Maigogul ya sake wani irin kyau. A harkar bokanci aka biya ma maigogul kujerar makka na biyu, na farkon muna yara yaje wannan a harkar kawalcinshine ya samo. Gidanmu ya sake yin ™aurin suna, da an tashi faWa sai kaji ana kiranmu yaran ™ananan mutane"

"gidan mutanen banza, marasa tarbiyyar islama."

"Gaga_gaga dai nayi saurayi ri™a™™en Wan daba, ko da yaushe ina cikinsu duk wani lungu da sa™o tare"

"muke shiga kullum cikin shigar maza nake, wu™a kuwa a lokacin har dauri nake sha maganin wu™a. Tare da Madubala ake farararmu mu gudu, ni dai sau biyu kwalawa na kamasu tare dani sai daga baya Rakiya, ko Maigogul su zo suyi belina, a haka ina Wan fita club ko zuwa Hotel haka a Soye ba tare da sanin Madubala ba, sabida son kuWi da kuma sabo da yawon kawai, ko kuma a buWe kada in rufeku ince muku sabida sabon da nayi da maza namiji Waya harga Allah bai isata gundurata ma yake yi. Yana daga cikin illa mafi girma ga mace da tasan maza da yawa. Wallahi Allah ko ta tuba mijin aurenta sai dai kawai ta zauna dashi domin Allah, amman ba wai dan shi kaWai zai iya gamsar da'itaba. Wasu bisa wannan dalilin suke komawa ruwa ko da auren nasu sai su kasa katange kansu ga mazajen waje, wata kuma da hannu take ™ara biya ma kanta bu™ata, ko kuga sun Sige da yin maWigo. Iyaye muji tsoron Allah, ³a΄a muji tsoron Allah domin wani sa'in daga yaranne ba daga iyayen ba, wani sa'in daga iyayenne. Kamar"

gidanmu daga iyayenmu ne. Kunji wata sabuwar ™addara mai rikitarwa?

"Dani Sabuwa ake fita faWan daba ina gaba_gaba in sari namiji, namiji ya sareni na mayar da kaina"

"samodara ( samodara itace macce mai shigar kayan maza) kullum ina soke da wu™a a ™uguna, a rigar Mamana kuma ina sa™e da askata."

Ina zaune na gasa tagumi a tsakar gida da rana fetal gidan babu kowa sai ni ni kaWai. Maigogul yau

"harkar kawalci ya tafi, ina zaune mata sunfi goma da suka shigo nemanshi ina cewa dasu bayanan. Nima"

³ar Shuwa nake jira tace zamu je gidan wata ™awaemu da tayi aure tun Wazu nake jiranta.

Da tunani da kaWaici yayi mun yawa sai nake tunanin bari inje in sameta a gidansu ma wuce daga can.

"Madubala ne ya kira wayata wai yana kofar gidanmu."""

"Ina zuwa"""

Na faWa a cige irinna asalin ΄an dabannan.

Ficewa nayi daga gidan ina fito Madubala yana zaune a dakali hannunshi da leda bibbiyu ya ™urama

™ofar gidanmu idanu. Yana ganin fitowata yayi murmushi. In muna tare a keSe ba tare da yaranshi bane kaWai yake iyayimun murmushi. Amman in muna kangon da anan suke rayuwarsu cikin ™azanta da

guje_guje rayuwa mara ΄anci rayuwar wahala baya mun dariya sam.

Zama nayi ina kare mishi kallo. ˜atone sosai a ™irji dan ba ™aramin cin ™arfe yake yi ba. Madubala

hatsabibine kuma yana da haWari sosai. Duk iskancin Gaza a ™asan ™afar Madubala yake dan a dabanci

siniyanshi ne sarki Gaza ke kiranshi fadarshi cike take da matasa ire_irenmu da suka rasa kafaWar da zasu jingina.

"""Yaya akayi Sabuwa? Naga kinyi wani kwalliya kamar fita kike son yi. Nifa kwana biyu bana gane miki kin"

"Wauke ™afarki a wajena ni sai dai inzo inda kike?"""

Yana magana yana wani ciccijewa. Kallonshi nayi da kyau na daWe sosai ina kallonshi amman bance mishi

komai ba. Sai can nace.

"Madubala gajiya nayi a gidanka kullum kwalawa basu da aiki sai kawo sumame, yau a kamamu gobe mu"

"gudu"""

Dariya yayi kawai ya daki dakalin da muke zaune yace.

"""Wallahi ba sabida haka bane ke da nasan jarumace, kina da jarumin maza kamar madubala har kina"

"shayi? Sabuwa in kullum mutum sukum da guda zaki kashe wallahi ko an Waureki zansa a sakoki, mu da"

"muke da manya a hannunmu, yarinyar Goga da kika burma ma wu™a a ciki kinji labarinma ya tashi eh in"

"ba yanzu ba. Ke dai faWamun meye matsalar?"""

Ajjiyar zuchiya kawai na sauke.

"Madubala cikine dani ni kuma tsoron zubarwa nake yi"""

˜ur ya zuba mun idanu.

"""To Sabuwa ba sai abar cikin ki haife ba tunda kina tsoron cirewa? Ni wallahi bani da wata matsala da"

"kika ganni. Bayan kin haihu sai muyi aurenmu, ki ba masu ganin yaudarata kike kunya eh wallahi madubala zai zama Abba"""

Harararshi nayi.

"Wanne irin in bar ciki kuma? Kawai dai tsoron nake ji, naji ka bani to kuWi in zubar dashi, da kuWaWen da"

zanyi jinyar kaina. Kana ganin irin wahalar dai da nasha a baya da ka kaini aka burge mun cikina kana jin sharaWi da gargaWin da Drn ya bayar akan yawan shan magungunan zubar da ciki.

Girgiza kai yayi.

"""A_a Sabuwa ™afata ™afarki ina da likitan da zai zubar miki da cikin. In kin shirya muje in kaiki kawai"

"faka_faka yanzu zai zube tu™eshi za'ayi."""

Idanuna na lumshe nace.

"Fita zamu yi da ³ar Shuwa ka ganta ma sai yanzu taga damar fitowa ita nake ta jira"""

Na nuna mishi ³ar Shuwa da take zuwa.

Ko kusa madubala baya son ³ar Shuwa bai taSa faWan alkhairi a kanta ba. Yace akwai wani ba™in cikin da

take Soyewa a zuchiyarta game dani.

"Ranar daya faWa mun hakan saida tayi kwana bakwai bai ganni ba, ana takwas ne muna tsakar gida muna"

jimamiin mutuwar auren Labbai sai ga Madubala ya shigo jaye da ™aton karenshi.

Haka yaita bani ha™uri da ™yar su Rakiya suka saka baki na yafe mishi.

"Tun daga ranar bai sake maganar banza akan ³ar Shuwa ba, amman baya mata fara'a itama ba ™aunarshi"

take yi ba ko kaWan.

"""Madubala"""

"³ar Shuwa ta ambaci sunanshi bayan ta iso"""

"""Shuwa yane?"" """

"""Lafiya lau. ˜awata muje ko? Ina jiranki a titi"""

Ta faWa tana wani keSe bakinta tare da gangarawa.

"""Kinsan Allah in yarinyarnan bata bini a hankali ba saina sa an mata abinda abadan ba zata mance dani"

ba? Sabuwa yarinyarnan ba™in ciki take dake ko ki yarda koma kada ki yarda watarana saita saki kuka eh

wallahi munafukace.

"Ga wannan kajine yara suka fita farauta suka samo, eh ki mana dabgensu sauran su Rakiya sa ci."""

Yana ajjiyewa ya haura da gudu.

"Madubala"""

"Na mi™e tsaye tare da ambaton sunanshi, da gudu ya dawo gabana yana murmushi."

"""Wallahi ina sonki da yawa ΄ar farata yaya akayi yau kinyi laushi duk maganar cikinne?"""

Hannu yasa ya shafo cikina ta cikin riga.

"Yaushe zamu je a zubar da cikin to?"""

"""Duk lokacin da kika dawo kinsan inda zaki sameni ai sai mu tafi aje a cire. Ki kwantar da hankalinki kece"

"kin™i yadda muyi aure sai jana kike yi"""

"Ya jima yana rarrashina, ni kuma duk fargaba ta rufeni."

Gida na shiga na juye kajinnan a tukunya na rufe sauran kayan alatun shopping Win kuma na buWe bokitin

fenti na zura ledojin a ciki na fito.

Sai a gidan ˜awarmu ne Yar Shuwa ta samu zarafin tsigaleni akan na barta ita atsaye sabida wani

Madubala

Dariya nayi.

"Oh ³ar Shuwa ke da Madubala dai kamar mage da bera bakwa jituwa"""

Hararata tayi tace.

"""Ai har adda,a nake yi Allah ya kawo wanda zai ture gwammatin Madubala a zuchiyarki wallahi"""

Dukan kafafarta nayi nace.

Ke hattara ³ar Shuwa na faffardeki ΄ar abu ta kazan... Inason abuna fa kada kiga madubala a haka

"wallahi yasan abinda yake yi mutumne shi mai son ibada asalima a sanadiyyarshi sallata ta gyaru, duk irin har™allar da ake ™ullawa da lokacin Sallah yayi yake dakatar da komai har sai yayi Sallah. Bugu da ™ari Madubala mutumne mai kirki yanayi ne fa kawai yasa ya zama haka kamar yadda muma yanayi da"

"™addara ta maishemu haka"""

Amarya ce ta iso inda muke da ture sha™e da kayan ciye_ciye na amare da abubuwan sha.

"""To ³an mata asha lemu kafin abincin ya sauka."

Saida na cika bakina da dambun nama kana nace.

"Me kika Waura mana Amarya?"""

Zama ta gyata tace.

"""Nasan kina mugun son jallof din manja mai bushasshen kifi to ita na Waura mana ina fatan wuni zaku yi"

"dai ko? Oga bayanan yayi tafiya, koma ince ya koma bakin aikinshi saini kaWai kaWaici kamar ya halakani kai zaman takura babu daWi, ku kam kunji daWinku ina mugun kewar club sosai"""

³ar Shuwa tace.

"""Mu da muke fatan mu shige daga ciki ya kike sage mana guiwa kuma"""

Ki shige daga ciki dai. Wa yadda nake zamaninnan bafa zan zauna a ™ar™ashin mutum Waya ba wallahi. Ya

"gama sukurkutani ya sakoni, ko kuma ya sake auro wata"""

Hararata ³ar Shuwa tayi tace.

"""Sai a ™ar™ashin madubala ri™a™™en Wan iskan da bai isa yayi yawo a fili ba?"""

Yafa isheki haka wallahi ³ar Shuwa. In fa nabar madubala dake ba daWi

Please Login or Register in order to submit comment