You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa™awa.

Su Sa'a dukka sai da suka shigo sukai musu sallama kana suka wuce jiki a sanyaye.

Abinci dai gashinan harma yayi yawa a asibitin.

Baba Malam:.

Yana gaban motar Wawo su Malama Babba suna baya. Sa'a da su Alawiyya sun tafi a motar mijin Sa'a da

ta tawo da'ita.

"Motar kowa yayi shiru sai tafiya akeyi, Baba Malam yana ta ambaton Allah a zuchiyarshi karfin hali yake"

yi a duk abinda akaga yana yi.

""" Baba Malam akwai abinda ya faru Wazu ina wajen aiki wani Alhaji Abubakar Baban Bola yazo ya same ni"

"akan Babangida. To maganar da yazo mun da'ita gaskiya da girma."""

"""To ai sai ka bari muje gida tukunna ko, nan ba wajen tattauna magana muhimmiya bane"""

Cewar Malama Babba wacce fuskarta duk hawaye. Sarai Baba Malam yasan abinda take nufi a wannan

karon ya shirya maganin kuwa.

"Da isarsu gida matan suka shige gida, su kuma su Wawo suka tsaya a waje."

Sai da akayi isha Malam ya shiga gida kasancewar juma'a babu karatu.

Wawo Malam yace ya kirawo Malama Babba da Malama ™arama su same shi a turakarshi.

"Malama ™arama itace ta soma shiga da sallama, Wawo ya amsa mata yana gefen kafar Malam yana"

mishi tausa.

Zamanta ke da wuya Malama Babba ta shigo idanunta duk sun kumbura halamun taci kuka ta ™oshi.

Ganin Malama ™arama ba ™aramin tayar mata da hankali yayi ba. Bata kaunar ayi maganar Babangida a

"gabanta, gashi bata san ma ko menene ba."

"""To kai Wawo muna saurarenka bismillah """

"""To shi Alhaji Abubakar Baban Bolan abinda yake cewa shine yana bin Babangida kuWaWe jimillar kuWi"

kusan miliyan Saba'in. Sabida ni yadda yai mun bayanin komai hatta injinan da Babangida ya shigo dasu daga China da kuWin shi Alhaji Abubakar Baban Bolan aka siya. Sannan akwai kuWin manyan motoci na kamfani wanda da kuWin shi aka siya. Kuma ya ari ruwan kuWaWe a hannunshi dai masu kauri.

Yadda sukai tsari da Babangida shine zai dinga cire mishi kaso huWu bisa Wari na duk abinda kamfani ya

samu.

"To an soma Allaha_Allaha sai abubbuwa suka rikirkice, sakamakon shi Alhaji Abubakar Baban Bola baya"

"™asar kusan shekaru biyar. Ya Waura wakilai da zasu dinga karSan wannan kaso amman Babangida ko sau Waya bai basu ba. Shine shi daya dawo ™asar ya nemi yazo mu gana domin hakkinshi, kuma maganar ma ya shigar da'ita kotu. Wannan shine abinda ya faru"""

Salati kawai kake ji na fitowa daga bakunan su Malama Babba. Kuka ta rushe dashi tana salati.

Baba Malam yace

"""Kuma a rubuce su kai komai ko da baki suka yi abinsu?"""

"""Yazo mun da takaddu duk ga saka hannun Babangida, kuma yana da kwafi na takaddun yarjejeniyar"

"shima"""

"""Waye yayi mishi garanto shi Babangidan?"""

Wawo yayi jim kafin yace.

"""Gaskiya ba dai muyi maganar garanto ba."""

Baba Malam ya dubi Malama dake dafe da ™irjinta yace.

"""To ke kinsan wani abu game da wannan lamarinne tunda duk abinda yake shukawa yana faWa miki. Ko"

"kai Wawo ka san da zaman maganar nan?"""

"""Wallahi Allah Malam bani da masaniya akan komai. Nima yadda ka jita yanzu, nima yanzun na jita"""

Cewar Malama Babba kenan.

Wawo yace.

"""Nima gaskiya bansan komai ba. Amman biri dai yayi kama da mutum irin yadda lokaci guda Babangida"

"ya samu manyan kuWi yanata damawa. Amman dake sana'ar Baban Bola sirrine a cikinta ni shi yasa ban zargi komai ba."""

Baba Malam dai sai gyaWa kai yake yi gami da murmushin da shi kaWai ya barma kanshi sanin dalilin

yinshi.

Malama Babba kuwa bata aikin komai sai kuka. Ta rasa dama me zata ji abubuwa goma da ashirin sun

"dameta. Ga Babangida babu lafiya, ga wannan tonon sililin daya kuma samun Babangida, ga SABUWA ta"

"shigar da ™ara, kotu biyu a lokaci guda."

Malama ™arama kuma Allah kawai take ambato.

Baba Malam yayi gyaran murya yace.

"""Inaga kai Wawo ka garzaya ka sanarma shi Baban nashi Manga domin yasan halin da ake ciki. Banyi"

tunanin yasan Šan nashi ma babu lafiya ba. Kuma shi yaji zai iya Waukar Babangida a matsayin Wa.

Wannan takaddar ta kotu itama ka tafi mishi da'ita.

"Ko da yake zan ajjiyeta a wajena."""

Wawo jiki a sanyaye yace.

"""Amman Malam """

"""A_a wallahi Wawo kar ka soma. Dan nasan inda kake nufin isa, ka adana kalamanka."

"Kuma na kirakune domin kuji halin da Wanku yake ciki, da rayuwar da ™addara ta sake zana mishi. Tashin"

hankalin Babangida ba yau bane farau ba yau bane ™arau ba. Ni wallahi ko ma a jikina.

"Kuna iya tafiya kowa ya kwanta"""

Dole suka mi™e suka fice ko wacce ta nufi Sarayinta. Wawo ya wuce wajen kawunsu ya shaida mishi duk

"halin da ake ciki. Yayi mishi al™awarin gobe sassafe zai garzaya asibitin, kuma yana son ya gana da Alhaji"

Abubakar Baban Bola.

A cikin wannan daren

"Cikin Malama Babba, Malam Baba, Wawo, Malama ™arama babu wanda ya runtsa, ko da yake ba a"

wannan karon ne kaWai Babangida ya hana idanun iyayenshi bacci ba.

"Baba Malam kwana yayi akan sallaya, yana sallah yana istigifari domin istigifari tana warware matsaloli"

masu yawan gaske. A kunnuwanshi akai kiran sallar assalatu.

SABUWA:.

Muna shiga ciki Maigogul da Rakiya suka dira a kaina da zagi da cin mutunci iri daban daban. Fatansu da

burinsu shine duk wuya in zauna a gidan Babangida. Ni kuma a wannan gaSar na gwammaci in koma

gidan masu zaman kansu da dai in koma gidan Babangida. Kuma nayi al™awarin ko sama da ™asa zata

haWe bazan yadda muci gaba da aure ba.

"""Šauki mayafinki ki wuce mu mayar dake Wakin ki marar Wa'a kawai. Labbai Malam Habu zai barki ki je"

"yau ku kwana da Lolo gobe ki dawo?"""

Maigogul ne yake tambayarta.

"""Zai yarda dake ba nike da girki ba sai nanda kwana shida ma girkina zai zagayo, har kwana biyu ko uku"

"ma ai sai inyi"""

Ta ™arashe maganar tana fara'a.

"""Rakiya fito muje in dena ganin fuskar ΄ar abu ta kazan ubannan a gabana"""

"Ni dai na zari mayafina wayata akai mata neman duniyarnan ba'a sameta ba, sai lokacin na tuno sanda"

wayar ta faWi sanda nake ™o™arin ceton raina a hannun Babangida.

"A motar da Maigogul ya aro ya kaimu, sai murza sitiyaei yake yi tamkar motarshi."

Basu yi shiru ba har muka kawo gida maigogul ya matsa hon maigadi ya buWe muka shiga.

"Su Mardiyya na gani a zaune a bakin part Wina Mardiyya na tsakiyarsu Malama na cinyarta, AWWa'u da"

Aminu ko wannensu na gefenta hannunsu dafe da cinyarta.

"""Dubi can Lolo. Tun ba'a kwana Waya ba rayuwar yaranki ta soma wula™anta ji besu a yashe. In baki yi"

wasa ba sai sun dawo yaran tsakar gida ki dai kiyaye wallahi. Kin sakko mun shiga ne koko Yaya ³ar abu

"ta kazan uba?"""""

Ya karashe maganar da tsawa.

"Da sauri na fito ina kwalla, ta ganin yarana a zaune illahin jikinsu da ruhinsu cike da kewata, a guje"

Malama tazo ta rungumeni. Su Mardiyya kuma suka nufi wajen Maigogul.

Sai da muka zauna a falo Mardiyya tace.

"""Ummi har bakin titi muka je muka tsaya ko zamu ga dawowarki. Anty Amarya tazo har Wakinnan tace"

"wai har abada ba zaki sake dawowa ba, kuma wai kinyi abin kunya"""

AWWa'u yayi carab yace.

"""Da naje masallaci ma tureni abokina yayi wai an kamaki da wani a mota"""

Wani abune naji ya tokaremun zuchiyata da ruhina yana barazanar tarwatsa nutsuwata da lissafina.

"Nayi nadama nadama ta har abada, ni Sabuwa na jawoma yarana abun kunya kan abin kunya dam abun"

kunya mufa a cikinshi muke dumu dumu gaba da baya ma.

Maigogul ne ya hau yara da faWa yana faWa musu sharri akaimun.

"""Rabu dasu sharrine yaushe lolo zata yi haka. ˜aninane ya kawota a mota to shi Babanku bai sanshi ba"

"shine su ka Wanyi rikici fa """

Ku tashi ku tafi kuje ku kwanta.

"Mardiyya in kin dafa abinci ki kawo ma su Rakiya."""

Bajewa Maigogul yayi tare da cewa.

"""Amman a hakan kike son ki dawo gabana ga ™annenku in banda yawon tambaWa basu saka komai a"

"gabansu ba, kema so kike ki koma ruwa kiyi fatali da damarki."

"Ke da Adama kun ™i nutsuwa son maza ya shiga jikinku ainun"""

Dawowar Mardiyya da abinci ni™i_ni™i ta zuzzuba a plate ta jerosu a ™aton tire shi ya katse mishi zancan.

Da kanshi ya amshe tiran.

"""In akwai moltina Wakko mun Mardiyya mai sanyi"""

Ya karashe yana dariya. Itama dariyar tayi tace.

"""Bari dai a kawo muku koka kola moltina jiya ta ™are."""

"""³ar baWo to kawo mana hahahaha """

"Zaman cin abinci su Labbai suka zauna yi, anayi ana ™ara jaddadamum in gode Allah abinci da nama"

zu™u_zu™u ga koka kola ga A c ko ina tas.

"""Wallahi da nice ke ko kullum sai Babangida ya lakaWamun duka saina zauna dashi har ™arshen rayuwata."

"Ke nifa ko sakina yayi ban saku ba"""

Carab Maigogul daya cika nama a bakinshi yace.

"""Allah yayi miki albarka Adama haka akeso."

"To a aure irinna zamaninnan a banza talaka ma zai jibgeki ya haWaki da tuwo miyar kuka lami, kuma kiga"

"mace tayi zamanta. Balle ki dubi irin gida da cimar da Lolo take ci. Dake tasa muguwar nufa™a a zuchiyarta ko ™iba da irin murjewarnan irinna matan masu dashi ta kasa yi"""

Rakiya tace.

"""Yo ba ga Labbai ba. Jiya fa Malam Habu ya haWasu du matan nashi yaita labtarsu har ™ofar gida."

Ina Waya daga cikin ΄an kallo. Ina kallon mitsiyaciyar yadda take shafa kuncinta daya fasa mata. Zuwam

"Gaza ne fa ya lafar da rikicin."""

"Haka dai sukaita nacin zance, ni dai har saida suka tafi na sauke ajjiyar zuchiya."

"A daren ko baccin kirki wallahi banyi ba, in sa™a wannan in kwance wancan haka na dinga yi."

Wajajen sha biyun dare motar ³ar Shuwa ta shigo gidan ita da Hamida ina tsaye a window ina kallonsu.

Suma mamaki suke yi ganin Sarayina da gaske har'a Wakin baccina.

arayina naga sun nufo nayi murmushi na koma kan gado.

Ina jiyo sunata dukan ™ofa har Mardiyya ta taso zata bude ™ofar na le™o nace.

Maza je kiyi baccinki basai kin bude ba.

Dama idanunta a rufe yake dan bacci. Sun daWe sosai suna buga kofar da suka ga dai babu sarki sai Allah

sai suka ja jikinsu ko wacce ta tafi ta kwanta.

Da sassafe kuma na tashi da kaye_kayen tattare suturuna tare da fitar da kayan wanki.

Ga babu waya a hannuna inaso in ro™i Khalid alfarman ya Waukar mun lauyan da zai tsaya mun a kotu.

Babangida dai nasan yana da lauyanshi na kamfani dake kular mishi da dukiyarshi.

"Labbai naje na samu a kitchen tana bare dafaffen ™wai, Mardiyya kuma na zuba indomi a plate."

"""Lolo kinata aiki jiki ba lafiya ba maimakon tunda kin sha tea kin hadiyi magungunanki ki kwanta ki huta"

"ma ranki, amman sai haWa kaya kike yi"""

Baki na taSe kawai na dubi Mardiyya dana fahimci kamar taso ta gane wasu abubbuwan.

"Mardiyya kuyi sauri ku tafi makarantar islamiyya kada ku makara takwas fa saura kuna gida"""

"""To ummi yanzu da munci zamu tafi. Amman ummi gidannan zaki bari kiketa haWa kaya?"""

Kallonta nayi tsab na jima bance komai ba rungumar da malama taima kafafunane yasa na lumshe

idanuna.

Kuje ku dawo Mardiyya zan yi miki bayani in sha Allah.

Sannan ku taya Babanku adda'a baida lafiya an kwantar dashi a asibiti. Mardiyya ki kula da ™annenki ke

"kanki inaso ki kula da kanki sosai"""

Malama tace dani.

"""Ummi zaki bani cake naje dashi makaranta?"""

"Dariya dukkanmu muka yi, kuruciya dadi gareshi."

"Zan baki uwar masu gida. Amman kuWi zan ba Mardiyya ta sai muku."""

A gurguje suka gama karyawa na sallamesu.

Ina shirin karSan aron wayar Labbai sai kira ya shigo wayar tata.

Šagawa tayi ta kara a kunnenta. Baba Malam ne yake nema na ashe. Mi™o mun tayi.

"""Surikinki ne Sabuwa"""

Da sauri na karSa kana na kara a kunnena gami da sallama.

Cikin ruwan sanyi Baba Malam ya amsa mun. Na gaisheshi ya amsa mun da fara'a.

"""Sabuwa inaso Labbai ta rakaki kije ki wuni da Babangida a asibiti. Ki girka abinci ki kai mishi."

"Sannan ni zan taimaka miki har sai kin rabu da Babangida."""

Naso nayi gaddama dan nasan zuwana bazai haifar da Wa mai ido ba. Amman dattijon tausayinshi nake ji

kuma nasan yayi mun ™o™ari ni dai bai taSa hantarata ba.

"To Shikenan zamu je"""

"""Ki daure har a sallamoshi ki dinga zuwa Win. Har gobe mijinki ne tunda bai sake ki ba."

"Kin Wauki lauya ne?"""

A kunyace cikin ruWewa nace.

"A_a"""

Murmusawa yayi yace.

"""To in kin amince zan Waukar miki lauya a matsayin gudunmawata ta son rabaki da Babangida kamar"

"yadda kike so. In kuma zaki Wauka da kanki Shikenan. Sannan kada ki tanka abokan zamanki, ko su Sa'a in suka kawo miki fitina."""

"Nagode Baba Malam. Kuma na amince ka Waukar mun lauyan nasan ba zaka cutar dani ba"""

"Albarka ya saka mini tare da yi mun sallama."""

Wayar na zare a kunnena kawai.

"""Gaskiya Lolo ni ina baki shawara ko dan Baba Malam da ³a΄anki ki zauna a Wakinki dattijonnan yana"

"sonki"""

In zauna sabida su in kashe kaina ko Labbai?

"To ku dena Sata bakinku kinsan Allah da girma yake ko Babangida bai sake ni ba, to na gama zaman"

gidanshi abadan. Kuma ni dashi daga nan har kotun ™oli. Ke dai gama karyawa ki samu abu me sau™i mu

"dafa mu tafi asibiti"""

Kafin tace wani abu kawai muka ga ³ar Shuwa a kanmu a tsaye ri™e da ™ugunta.

"""Au ke dake marar zuchiyace an kasa zama a gidan me dattin hula shine ashe dawowa kikayi. Kuma har"

"kin samu damar cin abinci Jannaty yana kwance a asibiti silarki har yanzu bai farfaWo ba? Babu shakka uhm lallai"""

Sama da ™asa Allah baisa dukkanmu mun kulata ba.

Sai ji mu kai ta kuma cewa.

"""Ai dai ™aryarki ta ™are Sabuwa, kuma wallahi saina fasa ™wan da kika daWe kina tsoron warinshi. Kuma"

"dole ki bar mun Babangida """

Mi™ewa tsaye nayi ina murmushi nace.

"Babangida na bar miki shi ke da matarshi Hamida, da sauran waWanda zasu biyo baya, harma da tulin"

karuwanshi na waje.

Batun fashewar ™wai kuma da kike magana akai ya daWe bai fashe ba dan uban ™wan. Kuma ki sani

"wallahi duk yadda kike jin kina son Babangida, kuma shima yana sonki, fashewar ™wannan zaki yi"

mamakin yadda zai raba aurenki da Babangida babu zato babu tsammani.

Ni kuwa kinga a daidai wannan lokacin ma nafi son ™wan ya fashe ™ila ba saimun shiga kotu ba salin alin

zai bani takaddata in wuce gidanmu.

Ke kuwa nayi imani kinfi son zama dashi fiye da komawa gidan ubanki. Kina nan a gidannan babu rabuwa

a tsakaninku.

"Gaki ga Babangida wallahi kinji na rantse babu kaffara akwai wata rana da zata zo, wacce ko sunan"

Babangida baza ki so jin an ambata ba.

"Ke a tunaninki wai butulci kikai mun, ko kuma kin haWe kai da Babangida domin ku sake cusgunamun,"

alhakin baki san kanki kika kashe ba.

Kinga takani da cin kashin da Babangida yayi mun sai yayi miki wanda yafi nawa munanan ranar zata zo.

"Labbai gareki ki fitarmun da wannan shegiyar a Wakina. Ko kuma wallahi in farke mata ciki"""

Na dubi Labbai tare da sake faWaWa murmushina.

Ai kuwa dama me neman ayi ce dama Labbai tana mikewa ta daki ™irjin ³ar Shuwa.

"""Ke ™aramar karuwa ™aramar ΄ar balaja'u zaki fita ko saina rungumeki mun kashe juna."""

"""Bazan fita ba ni da gidan mijina. Wannan part Win nawa ne da zaran Sabuwa ta bar gidannan"""

"Dariya nayi na nufi kitchen Wina na zaro wu™a mai kamar adda wacce ake sara kaza ko jan nama, ina huci"

na fito ina ciccije bakina dan tsohon tsumina na daba ne ya tashi.

"Ina fitowa da dai ³ar Shuwa taga wu™a kuma sarai tafi kowa sanin wacece Sabuwa, tasan maza da mata"

nawa na sassara a gabanta.

"Babu shiri ta fita a guje nima na take mata tana gudun ceton ranta, ina gudun cin mata."

˜asa na sara inda ta Wauke ™afarta take wajen yayi wani irin tartsatsin wuta.

Da mahaukacin gudu ta faWa part dinta.

˜aramar ΄ar balaja'u kawai kika ce bakya ji. Ni daku da duk wanda zai kawo mun iskanci mu zuba na

"dawo asalin Sabuwa ta wacce ake tsoron nuna ma yatsa"""

Labbai ta jijjiga kafaWata tace.

"""Baki taSa burgeni irinna yau ba Sabuwa, naso ki sari ™ugun matsiyaciya gaba bata iya haihuwa da kanta"

"ba."""

"Ciki muka koma labbai ta shiga aikin girki, ni kuma ina kwance ina numfasawa sama_sama har ta gama"

mukai wanka kana muka kama hanyar asibiti.

Dama da shirina tsab na tafi duk wacce ta nuna mun yatsa saina Sallashi abinda ya tafasa ya daWe bai

™one ba. Wu™a na soke a ™uguna duk shegiyar data nuna mun yatsa saina sareshi.

Da tambaya aka nuna mana ward Win maza muka shiga.

"Anan muka ga gungun abokan Babangida sun zo dubiya, sai Ramadan dake jinyarshi."

Dukkansu babu wanda baiyi mamakin ganina a asibitin ba. Kunu nasha nayi kamar bansan Allah yayi

"ruwan tsaron kowa a wajen ba. Sai mamaki suke yi, da girgiza kai gayyar marasa kamun kai kawai."

Ramadan ne ya mi™o mun kujera na karSa na zauna ina ciccije bakina

MRS BUKHARI

Sai Allah ya kaimu gobe kuma.

#Team Uzairu zuchiyata

#Team Maigogul

#Team Gaza

#Team Sabuwa

#Team Babangida kacigari

https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA

Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??

Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??

Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??

Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.

Muna da kaya available masu kyau da rahusa

Ko kimin mgn ta

08093932955

IDAN KAYA YA GAJI...

GAMMO MA YA GAJI

LITTAFI NA BIYU

SHAFI NA UKU

BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ˜AMSHI

https://chat.whatsapp.com/E3bH5OKBh9jH2aYygj0ArA

Kina bukatar kaya masu kyau da inganci??

Kina bukatar kayan kitchen wnd suke available ba order ba??

Kina bukatar adashin gata wnd zaki dauki kaya kamar kyauta??

Kiyi joining wnn group din namu insha Allah xakiji dadin kasancewa a ciki.

Muna da kaya available masu kyau da rahusa

Ko kimin mgn ta

08093932955

"""Sabuwa ya me jikin?"""

"Jiki ai ku zan tambaya tunda dai zuwana kenan a gabanku ai kuna gani"""

Da gatsali nayi ma Mustapha maganar. Tsohon munafuki. Babu shiri suka dawo cikin nutsuwarsu.

Bashiru ne yace.

"""Allah dai ya kyauta ya kiyaye gaba. Mujenku zuwa yamma in mun taso wajen aiki mazo"""

Fita suka yi Ramadan ya take musu.

Mtwss ΄an iska gaiyan marasa mutunci. Kinga WaWannan shaiWanun abokan nashi su suke sake ingiza

"me kantu ruwa. Matayensu wahala kab suke sha, gasu da shegen son mata. Dubi yadda Mudassir ya"

"™ura miki idanu kamar tsowon maye"""

Baki Labbai ta sake.

"""Tabbb lallai da ganin idandunansu ΄an duniya ne."

"Ai bazan mance lokacin bikinki ba irin akuyancin da suka goga mana ba."""

Shigowar Ramadan yasa mukai shiru.

Babangida nake ™arema kallo a kwance samSal hannunshi a mugun kumbure ga bandeji naWe da

"kafaWarshi, bakinshi ya bushe leSennan ba™i™™irin sigari ta gama cinyeshi."

Isowar Malama Babba da su Kudidi da Naja'atune ya dawo dani daga duniyar tunanin da nake ciki.

Malama Babba ta wani kalleni ta girgiza kanta bata ce mun komai ba. Sai Kudidi ita uwar fitsara sai cewa

tayi.

"""Sabuwa bakya ganin Malama Babba ne da ba zaki gaisheta ba. Sannan mema ya kawoki asibitinnan"

"babu kunya babu tsoron Allah? Alhalin kece silar kwanciyarshi a asibiti. Sannan maganar kotu dan baki san menene shari'a ba shi yasa. Mu kanmu kotu zamu maka Gaza wallahi sai mun yi shari'a daku."""

Har Baba Malam ya iso kanta shi da Kawu Manga Kudidi bata sani ba sai maganganu take yi. Ni kuwa

"wallahi albarkacin Baba Malam taci yau da saina nuna mata gajanci. Dan harna saka hannu a ™ugu zan zaro wu™a in tsinke mata hannu sai naga shigowarsu shi yasa na rabu da'ita"""

"""Yayi kyau fetsararriya, ke Kudidi matar wan naki kikai ma tsaye aka kike ci mata mutunci, irin tarbiyyar"

"da Mahaifiyarku ta baku kenan? To yayi kyau. Babba kin kyauta a gabanki ake irin wannan abun. Ko da yake ga Babangida ma ke kika lalatashi. Batun kai karar Gaza kar inji kar in gani"""

Ha™uri take son bashi dan jikinta har rawa yake yi. Baba Malam ya koWa mata tafi.

Malama Babba itace aka bari da runtse idanu.

"""Haba Yaya ayi ha™uri dan Allah """

"""Manga su basui ha™uri ba sai nine zanyi. Ni dasu wake da ikon zartarwa? To wallahi in na sake ganin"

™afafuwanku a asibitinnan saina sassaSa muku. Abar Babangida matanshi suyi mishi jinya. Duk kuma wanda ya kuma tayar da wata magana zai fuskanci fishina irin wanda bai taSa gani ba a rayuwarshi.

"Mata_ matan kada inji labarin wacce tazo. ˜arama kaWai na ba izinin zuwa ta duba shi ta tafi, mazan"

"kuwa ko wanne zai iya zuwa"""

Kawu Manga yace.

"""Assha Yaya in hankali ya gushe hankali ake turawa ya nemo shi. Ya kamata a tattara komai a watsar"

tamkar ba'ayi ba.

"Malama Babba dasu Kudidi yanzu dai ku zo muje in mayar daku gida."""

"Malama Babba ta mi™e tana huci ta wuce fuu zuwa waje, yaranta suka mara mata baya. Kawu Manga ma"

ya bisu.

"Ina wuni Baba Malam?"""

Na faWa a mugun sanyaye.

Cikin kamalar da ta zame mishi ado yace.

"""Sabuwa lafiya lau. Allah yayi miki albarka da kika bi umarnina. Kiyi ha™uri da abinda su Kudidi sukai miki"

"zan Wauki mataki. Shi yaro Allah ya bashi lafiya"""

Harya juya zai fita ya dawo.

"""Sabuwa babu waya a hannunki ne, na kira layinki baya shiga. Gashi lauyan dana Waukar miki yana son"

"ku gana domin ku tattauna."""

"Wayar tawa faWuwa tayi ban ganta ba"""

Jim yayi yana nazari can yace.

"""Ramadan kaje ka siyo ma Sabuwa waya da sim ka kawo mata. Ka saka mata lambata ta kirani"""

Cikin mutuntawa Ramadan yace.

"""To Baba Malam bari inje yanzu ta kula da Yayan"""

Godiya nayi ma Baba malam. Tare suka fita da Ramadan.

Bai jima ba sai gashi da waya Asha harda sabon sim na zain wanda a yanzu ya zama Airtel da can kuma

sunanshi Econet.

Shi da kanshi ya saka mun sim Win a wayar ya kunna.

"""Gashi Maman Mardiyya. Nasa miki lambar malam akwai kyautar kuWin kira nera Wari da suke bayarwa"

"zaki iya kiranshi dashi. Sannan dan Allah kiyi ha™uri da abubuwan dake faruwa"""

Amsar wayar kawai nayi.

"Babu komai Baban Amina."""

Muna cikin haka Hamida da ³ar Shuwa suka shigo.

Mu dasu babu me kula wani. Sai harare_harare nake yi.

Šigimi har mahaifin ³ar Shuwa saida yazo ya duba Babangida. ˜annenta kuwa da mamanta sun jima

sosai sune har azahar.

"A masallacin asibitin mu kai Sallah ni da Labbai. A cikin masallacin na kira Baba Malam yaga number na,"

ya sake jaddadamun lauyan zai kirani dai.

Godiya nayi mishi na kashe wayar muka koma barandar da muke zaune dukkanmu.

"Muna zuwa muka ga dangin Hamida an taso har mata biyu da wani dattijon da in ba mahaifinta bane, to"

™aninshi ne ko wanshi tabbas.

Ni dai cikin mutumtawa na gaishesu suma kuma sun amsa da daraja harma da tambayar me jiki.

"""Sabuwa ina yini ya mai jikin?"""

Hmm kunsan wake wannan maganar?

˜awata Fiddausi wacce itama tare muka taso daga baya ne suka bar layinmu suka yi gini. Har sunan

"Malama tazo mun, duk matan da Babangida ya aura a baya duk da ita akayi mun dannar ™irji. Daga baya"

ne aiki ya mayar da mijinta kaduna ya tarkatasu suka koma sai ya zamana sai dai muyi waya. To ashe

"itama tana tare da ³ar Shuwa tunda gashi tazo mata"""

"Lafiya lau Fiddausi jiki da sau™i"""

Na faWa da fara'ata ™a™as.

"""Allah ya bashi lafiya yasa kaffara ne"""

"Ameen"""

Na faWa a ta™aice.

Ramadan ne ya fito da sauri.

"""Maman Usama, da Maman Fatima Babangida ya farka yana nemanku"""

Da sauri suka mi™e suka shiga. Har suna rige_rige

Niko da idanu kawai na bisu na taSe bakina.

Babangida:.

Yana buWe idanunshi wani irin zafi da tsamin jiki sukai mishi sallama.

Idanunshi ya runtse kawai yana tuno dukan ™irjinshi da Sabuwa ta haukace tayi mishi.

Hoton fuskar Khalid kuwa abadan bazai gogu a ™wa™walwarshi ba sam.

Idanunshi ya runtse tare da furta.

"""Kin cutar dani Sabuwa kin ruguza mun zuchiyata. Ashe haka nake kishinki?"""

Furucin daya janyo hankalin Ramadan zuwa gareshi.

"""Babangida ka tashi, bari in kira likita dan tace daka farka a kirata."""

"Fita yayi yaje ya kira likita, tare ma suka tawo ta shiga dubashi gami da mai tambayoyi."

"""Yanzu abinda za'ayi shine a nema mishi tea ya soma sha ya warware hanginshi sai yaci abinci. Zai karbi"

"allurai da magunguna. Malam Babangida sannu ko, Ubangiji Allah ya ba da lafiya. Sannan a kula da yawan motsa hannun gudun kada a dawo mana da aiki baya'"

"Tana kaiwa nan ta fita akan in yaci abinci za'azo a yi mishi abinda ya dace."""

"""Ina su Malama Babba da su Kawu Manga duk basu zo bane?"""

"Babangida ya tambaya idanunshi a lumshe, hoton yadda Sabuwa ta faWa motar Khalid ya shiga tariyo"

kanshi da kanshi a ™wa™walwarshi.

"""Sun zo Baba Malam ne yace su koma gida. Kuma yace kada su sake zuwa ma."""

Bai buWe idanunshi ba. Kuma baiyi mamakin abinda Ramadan ya faWa mishi ba. Sai cewa yayi.

"""Wayata tana hannun waye, sannan ina su Hamida?"""

"""Uhm wayarka inaga tana hannun Yaya Mustapha tunda shi ya kawo ka asibity. Ko Wazu da safe"

abokanka duk muna tare anan dazu.

"Su Maman Usama suna waje harda Maman Mardiyya ma"""

Runtse idanunshi kam yayi jin an ambaci sunan Sabuwa sai yaji tamkar an watsa mishi ruwan dalma a

kwanyarshi. Cikin hucin kishi yace.

"""Ban yarda a barta ta shigo inda nake ba sam Ramadan. Ka je ka kirawo mun su Hamida su zo"""

Shine kiran da Ramadan ya fita yayi musu.

Suna shiga suka tarar da dabara Ramadan na ™o™arin zaunar da Babangida dan yace duk jikinshi tsami

yake yi mishi.

"""Maman Usama dan haWa mishi tea mai kauri"""

Cewar Ramadan dake

Please Login or Register in order to submit comment