You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ruwan hawaye ba.


Napep d'in na shiga, bakina bai daina addu'a ba, tunani da k'wak'walwata basu daina tababa a kan abin da na gani ba.


A cikin napep d'in ne abokan suke fira, duk da halin da nake ciki, duk da rabin hankalina baya tattare da ni, hakan bai hana ni mayar da hankalina gare su ba.


"Baabaa amma fa na yi mamakin Oga. Gashi dai abin da ya fi so, amma bai yi tsiyar ba."


Dariya wancan di'n ya k'yalk'yale da ita,


"Ina ganin dai ciwon k'afar nasa ne ya motsa. Baka ji har da magani ya ce mu siyo masa ba? Da alama shi ya sa ya sallame ta."


D'ayan ya ce,


"Zan iya yarda da hakan kam. Duk soyayyarsa da son falle sababbi dal a leda, amma ya bar garab'asa. Gaskiya Oga Sans akwai damuwa a tattare da shi."


Baki na bud'e ina mamakin sunan da suka k'ira sa da shi, ina mai jinjina sunan 'Sans' a bakina.


To waye shi? Wannan wane mutumi ne wanda kamanninsa iri d'aya da Yaa Noor d'ina? Duk ta k'are shi ne wanda na yawaita gani a asibiti. Shi ne wannan gurgun da nake gani a keken guragu tsawon shekaru da dama da suka gabata.


Amma kuma ta ya zan gasgata cewa ba Yaa Noor d,ina ba ne bayan kamar tasu babu banbanci?


'Ta d'abiu da sa'banin halaye.' Wani sashe na zuciyata ya bani wannan amsar.


"Ke mun zo Gidan dawa. Ta ina zamu bi?"


Muryar gardawan ta dawo da ni daga duniyar da bani na kai kaina ba, duniyar da tunane-tunane ce kawai ta jefa ni.


"Kwanar gaban shagon can zaku shiga."


Na fad'a da disasshiyar murya, wacce kuka ya gama dishasarwa.


Har gaban gida suka kawo ni, suka kuma k'ara bige min warning a kan kar maganar ta fita, kar na bari hukuma ta shiga, saboda komai zai iya faruwa da ni."


Amrah na kai wa wannan gab'ar ta dakata, tana shesshe'kar kuka sosai, jikinta sai faman rawa yake.


Cike da tashin hankali na jawo ta a jikina, ni d'in ma kukan nake sosai.


"Ya isa haka to. Ai gashi babu abin da ya same ki ko? K'arfin addu'a ke nan."


Ni d'in ma ban daina kuka ba.


"Gaskiya ba za a bar maganar nan ba. Ya zama dole hukuma ta shiga wannan maganar, ko dan gaba."


Mallam ya furta yana mai jinjina lamarin.


"Dan Allah Abba kar a shigar, wallahi ina tsoro."


Ta fa'da cike da muryar kuka.


"To ke ya kike ganin gaskiyar lamarin? Ni dai na tabbata ba Annur ba ne, na san Annur yaro ne mai hankali, yaro ne mai sanin ya kamata, wanda na yi imani da Allah ba zai kasance mai irin wancan halin ba.


Ga kuma babbar hujja, wancan d'in ma da kike fad'i gurgu ne, kuma ga wannan ma maganar ta kusa zuwa d'aya. Da alama dai kama ce mai tsanani suka yi. Kin san ana samun irin haka."


Cike da gamsuwa Amrah ta jinjina kanta,


"Na yarda da wannan bayanin Umma. Tabbas na san ba Ya Noor d'ina ba ne. Kuma dan ya nunar da alamun mamaki a lolacin da ya gan ni bai zama hujja a ce shi ba ne, tun da shi d'in ma na san shi a asibiti, shi ma ya san ni, mun sha had'uwa da shi, har gaishe ki ma yana yi. Da alama dalilin da ya sa ya sallame ni ba tare da ya min komai ba ke nan. Wallahi na yarda ba Hammana ba ne, wancan mutumin banzan dai ne. Fasi'ki, mazinaci, azzalumi!" Ta k'arisa da share hawayenta.


"Mallam tun da dai abun haka ne, kuma shi d'in bai mata komai ba, kawai mu hak'ura, mu barsu, akwai ranar da zasu ha'du da dai-dai ya su."


"Haka ne. Allah Ya tsayar nan to. Allah kuma Ya k'ara karewa."


"Ameen ya Rabb. Kuma sai fa da ta nunar da bata son tafiyar, kamar ta san abin da zai faru. Ni na tilasta mata tafiyar, ashe abin da zai faru ke nan."


Wani kukan ya sake kufce min.


"Ya kamata ku yi shiru haka nan. Babu abin da addu'a ta bari. Kuma na yarda cewa addu'ar da ta yi ne ya sa abin ya tsaya nan, har zuciyarsa ta sanyaya, ya iya tuna ma ya ta'ba ganinta.


Kin san mafi yawancin mutanen banza irin wa'innan, sun fi d'aukar mummunan hukunci a kanka ma sanda ka nunar da ka sansu. Amma hikima irin ta Allah, da taimakonSa sai suka sallame ta.


Lallai babu k'arfi babu dabara face a wurin Allah ma'daukakin sarki! Shi ya halicce mu, shi muke bautamawa, kuma shi ne maji k'anmu. Shi ne mai taimakonmu a duk lokacin da Ya ga dama. Shi ke kare mu a duk sanda muka nemi kariyarSa.


Babu babban butulci sama da neman taimako ko kuma agaji ga wanin Allah. Sau da dama wasu sukan butulce, su nema taimako ga d'agutu, wanda shi d'in kanshi sai Allah ya bashi iko.


Me zai hana duk sanda muka samu kanmu a cikin tashin hankali, mu ambaci "INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!"? Ita ce kalma mafi girma, wacce ya kamata mu ambata a duk sanda wani tashin hankali ya riske mu.


Kin kyauta sosai y'ata, kin buk'aci taimako ga Allah kuma Ya taimake ki. Ina alfahari da ke, ina alfahari da baki d'aya halayenki, ina alfahari da iyalina."


Ya 'karashe maganar da murmushi shimfi'de a saman fuskarsa.


Take muka manta da duk wani tashin hankali, muka ci gaba da rayuwarmu kamar kullum, tana min labarin yanda wa'azin auren ya kasance.


Tun daga wannan tashin hankalin da muka shiga, bamu sake samun kanmu da shiga wata damuwa ko matsala ba, Annur kuma dama na fad'a ma Amrah ko da wasa kar ta masa tad'in. Tun da dai mun tabbatar cewa ba shi ba ne, kawai dai mai kama da shi ne. Na tabbatar idan muka fa'da masa ba zai ji dad'i ba, kuma zai yi bincike sosai har a gano mutanen, bayan kuma mun saki maganar, gwara dai mu barsu da duniya, saboda ta fi bagaruwa iya jima.


Haka kwanaki suka ci gama da gudanya, har su Amrah suka fara zana jarabawar WAEC.


Ranar da suka fara ne ta dawo cikin yanayin zazzab'i, irin mai zafin jikin nan sosai, wanda ko rintse idonta cikin wani hali take yinsa.


Mallam Mu'ammar ne da kanshi ma ya dawo da ita bisa mashin d'insa, bayan sun fito daga exams.


A yanayin da na ganta, sai da hankalina ya tash, gabana ya ringa fad'uwa.


"Me ya faru da ke?"


Na gaggauta tambayarta.


Tab'a fatar jikinta da na yi ne ya bani amsar tambayar da na mata, tun kafin ita d'in ta amsa min.


"Subhanallahi! Lafiya lau fa kika fita Amrah. Ko kin shiga ruwan saman nan da aka yi ne"


A daburce na sako zancen, ina mai sake tab'a jikinta.


"Umma an caccanza mana hall ne har sau uku, daga farko aka kai mu Class, sai aka sake canza wani, a 'karshe kuma aka kai mu exam hall. Kuma duk a cikin ruwa muka yi yawon. Tun daga sannan ne na ji jikina ya mutu, zazzab'i mai zafi yana sauko min, da k'yar ma na rubuta jarabawar."


Ta k'arisa maganar tana mai yin hamma, irin mai nuna yanayin zazzab'in nan.


"Aikam tashi zaki mu tafi asibiti, tun da wuri ma.." ban rufe baki ba muka ji sallamar Annur.


Sanye yake da suites ba'ka'ke, sai light blue riga mai dogon hannu daga k'asa, neck tie di'nsa bak'i mai di'go di'gon light blue d'in.


Amsa sallamar tasa na yi, ina mai k'oka'rin k'irk'iro masa murmushi.


Bayan mun gaisa da shi, Amrah ma ta gaishe shi ne yake tambayar lafiya? Dan ya kula da yanayin namu.


"Ehh to, ta dawo exam ne ka ga ko uniform ma bata cire ba. To kuma zazza'bi take sosai, ga hawaye nan sai fita suke da kansu. Yanzu haka shawarar kai ta asibiti ma nake."


Kallonshi ya miyar ga Amrah, cike da soyayya, kallo mai nuna zallar tausayi, k'auna da kuma irin kewarta da ya yi.


Kalar idanuwan nasa ne suka sauya, daga farare tas da suke, zuwa jajaye. Haka yake, a duk sanda zai tarar Amrah bata da lafiya, kuka ne kawai baya fasawa.


Cikin wata irin murya ya ce,


"Ta shirya zan kai ta Umma."


Maganar da ya yi ce ta sa na tuno zancen da nake so mu yi da shi, wanda na jima ina yi masa amma ya yi kunnen uwar shegu da ni.


"Yauwa, Annur ba dai zan gaji da rok'onka ba, dan Allah..."


Saurin dakatar da ni ya yi,


"Wallahi Umma bana jin zan iya yin awon genotype. Ina ji a jikina ni ba AS ba ne, AA ne da ni. Ban san ya zan yi ba idan na yi wannan awon aka ce ina da AS, ban san wane hali zan shiga ba. Bana jin kasantuwar Amrah SS zai sa na hak'ura da aurenta."


Gya'da kai na yi ina kallonshi. Cikin k'wayar idonshi na kalla, na karanci yanda soyayya ta makantar da shi, ta sa baya ganin komai sai Amrah. Soyayya ta kurumtar da shi, ta sa baya jin maganar da nake masa a kan wannan awon. Sosai na fahimci yanda soyayya ta jirkitar da tunaninsa, ta sa ya kasa gane muhimmancin wannan awon.


"Amma Annur, baka tunanin halin da yaranku zasu shiga nan gaba? Me kake tunani idan yaran da kuka haifa suka shiga cikin hali irin na Amrah, ko kuma ma wanda ya fi nata?"


"Wannan ba abun damuwa ba ne Umma. Zamu iya tsaida haihuwar ma baki d'ayanta. *AMRAH NAKE SO* ba wai abin da zata haifa min ba.


Wallahi ko AS nake da shi ba zan iya hak'ura da ita ba. Bana jin zan yi rayuwa mai kyau ba tare da Amrah ba. Bana jin zan ta'ba yin aure matu'kar ba Amrah na aura ba. Saboda haka, Umma, awon genotype bashi da wani tasiri a gare ni. Dan Allah yau dai a tsayar da maganar nan. Tun kafin a saka ranar aure muke yinta, Umma ta gagara k'arewa, har gashi yanzu bai fi mana watanni uku a d'aura aure ba."


Jin ya dakata daga nan, ya sa na dafe kaina, baki da'ya jikina ya yi sanyi.


"Ai shi ke nan. Amrah tashi mu tafi. Bara na d'auko makullin gidan a d'aki. Amma ki fara kiran Abbanki ki sanar masa."




_Addu'a na sauk'ak'a masifu da bala'iku sosai. A duk halin da zamu tsinci kanmu, na ciwo ne ko kuma wata damuwa, kar mu manta da INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!_




Pinky durling💗
*RAZ 2*
[8/30, 3:36 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)


Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


1⃣9⃣


Bayan mun isa asibitin ne muka buk'aci a had'a mu da Dr. Xarah ko kuma Dr. Rabiatu, amma aka shaida mana Rabiatu bata nan, dole sai dai Dr. Xarah.


Bayan mun shiga Ofishin nata, kallo d'aya ta ma Amrah ta tabbatar da bata jin dad'i.


"Sannu Amrah." Ta furta cike da tausayi.


"Jikin dai kuma" ta jinjina kanta.


"Wallahi kuwa Dr. Daga makaranta ta dawo min haka. Wai ruwa aka saka suka shiga wurin canjin hall, har ruwa ya mata duka."


"Subhanallahi! To Allah Ya kyauta gaba."


Ta zaro lokar dake gaban teburinta.


"Ungo thermometer, ki saka a armpit d'inki."


Karb'a ta yi kuwa ta saka, ta d'an jima kafin ta nemi ta fiddo ta.


"Subhanallahi! Temperature d'inta har ya haura ma 47. Lallai zazza'bi ya shige ta sosai. Bara na rubuta mata magani. Ku tsaya ku karb'a sannan a mata awon jini, idan ya sauka dole a tarbi abun, a mata k'arin jini."


Ta hau rubutu.


Bayan ta gama ne ta mik'o min takardar, tare da yi mana fatan alkhairi.


Har zan fita ta dakatar da ni,


"Maman Amrah wai yaushe ne ma aurenta?"


Murmushi na yi na ce


"Wata biyu ne da 'yan makwanni suka rage. Insha Allahu idan ya matso zan zo na sanar miki."


"To Allah Ya kaimu. Ina fatan dai an san genotype d'in angon nata." Ta furta a hankali.


Kallona na mayar ga Annur, ina k'ok'arin magana ne ya yi caraf ya ce


"Ehh, an yi Dr. AA ne da shi"


"To masha Allahu. Haka ake so ai." Ta fad'a.


Bankwana muka mata sannan muka fita.


D'akin magani muka fara zuwa aka bata, sannan muka nufi laboratory domin awon jini.


Bayan an gama auna mata mun fito, Annur ya ce,


"Umma bari dai na je a min wannan awon, ba dan komai ba sai dan na tabbatar, idan AS gare ni tun wuri sai na san hanyar bi domin tsayar da haihuwa, duk da dai jikina baya bani hakan."


Ajiyar zuciya na sauke,


"Haka Nake so Annur. Bari mu jiraka a can har ka dawo."


Ya tafi, mu kuma muka zauna jiransa.


Kusan awa d'aya ya da'uka sannan ya dawo, fuskarsa k'unshe da murmushi, farin ciki ya gagare b'oye kansa. Hannunshi d'aya rik'e da takarda, d'ayar kuma a cikin kansa yana wasa da sumar kansa.


Tun daga nesa yake furta,


"Umma kin gani ba, dama na fad'a miki."


Bayan mun mik'e taye na ce,


"AA gare ka ke nan?" Ni d'in kaina ina murmushi.


"AA gare ni Umma, kar'bi takardar ki gani."


Bayan na duba ne na tabbatar da maganarsa. Da gaske abin da ya fad'a. Wani irin dad'i na ji ya kewaye ilahirin zuciyata, na kalli Amrah da ita kanta da'din ne ya mamaye ta.


Da farin ciki muka isa gida, wanda sai da muka biya ta Crispy ya mana take away na abinci da lemo kafin muka isa.


***
Rayuwa ta ci gaba da tafiya, kwanaki na gudanya, muna 'kara kusanta ga Allah, har Amrah suka gama jarabawarsu duka, WAEC DA NECO d'in. Wata da'ya kacal ya rage aurenta.


A iya wannan lokacin har lefenta an kawo, akwati saiti biyu, da kaya na ji da fad'a, zan iya cewa tun da nake a rayuwata, ban ta'ba ganin kayan lefe kamar na Amrah ba.


Sadakinta naira dubu d'ari aka kawo, komai dai sai hamdala. Fatana a ko da yaushe, shi ne Allah Ya kawo farin ciki a rayuwar auren Amrah. Yanda Hajiya Suhaila ke nuna mata gata da soyayya, ina fatan d'orewar hakan har gaban abada.


Saitin kayan d'akinta da Mallam ya siya mata masu kyau, ba wasu na 'karya ba ne sosai, iya k'arfinsa ya yi, kuma a hakan ya samu rufin asiri. Komai ya yi kyau sosai.


A makuna hud'un da ya yi saura na auren Amrah, babu abin da bamu gama ha'dawa ba. Hatta da kayan abincin da za a ci lokacin aure mun gama had'awa. Kayan kitchen d'inta bakin gwargwado mun had'a mata. Dama 'yan uwana sun had'a min gudunmawa tun watan da ya gabata sun bani, da su na 'kara na mata siyayyar kayan kitchen d'in, kayan 'yan gayu, wanda na san mai rayuwar Abuja zata iya buk'ata. Dama kuma sun ce kayan kitchen ne kawai za a tafi Abuja da su, kayan d'akinta a nan Katsina zata barsu, gidansu wanda zasu ringa sauka idan sun zo. Abujan babu abin da basu zuba mata ba.


Da murna ta shigo cikin gida, bayan ta cire hijabinta ta zauna kusa da ni.


"Fuskarki ta bayyanar da farin cikin da kike ciki. Da alama an faranta miki rai."


Da murmushi ta ce,


Umma, sati mai zuwa zamu tafi Sudan, kin san na fad'a miki a can za a yi musabak'ar k'asa da za a yi. Umma ni na haye a duk fad'in ka'sar nan, ni da wani namiji da'ya ne kawai zamu wakilci Najeriya, shi zai zama na b'angaren maza, ni kuma a b'angaren mata. Shi d'in d'an jihar Gombe ne."


Cike da farin ciki na ce,


"Alhamdulillahi Ya Allah! Kai amma wannan labari ya min da'di sosai wallahi. Har na ma rasa me zan yi dan murna. Allah ubangiji Ya taimaka Ya bada sa'a. Allah Ya baku ikon d'auko ma K'asarmu lamba ta farko a wannan gasa.


Oh ni Murja! Wallahi jin abun nake tamkar a mafarki, wai 'yata da na haifa da cikina zata tafi wata K'asa gasar Al-Qur'ani mai girma, kuma wai 'Kasa baki d'aya zata wakilta.


Ke alheri ce Amrah! Ke abar alfahari ce, wacce ko wace uwa zata so samun irinta. Ke abar koyi ce Amrah, wacce ko wace macen kirki zata so zama irinki.


Allah Yana tare da ke Amrah, insha Allahu zai taimaka miki, zai baki nasara. Kuma na yi alk'awarin zan hana idanuwana bacci in kwana ina miki addu'ar samun nasara."


"Ameen Umma. A lokacin da zancen nan ya tabbata, har da hawayen farin ciki na yi. D'alibaina kansu sun taya ni farin ciki. Daga masu kukan murna sai masu hawayen farin ciki. Matan auren da nake koya ma har da wacce ta rungume ni, wai ina ma iyayena zasu bata kyaur Malama Amrah, wallahi da ta gwada min k'auna fiye da yaran da ta haifa da cikinta."


Ni d'in ma rungumarta na yi, idanuwana na kawo ruwa, ban sake ta ba, haka kuma a tsaye muke bamu zauna ba.


A haka mallam ya tarar da mu, tun bai nemi bayanin dalilin halin da muke ciki ba, na hau zayyane masa komai, ina yi ina hawaye mai had'e da dariya.


"Abin da ya dawo da ni gida ke nan, Murja. Ina wurin aiki na ji wani abokina yana saurarar radio, kamar an ce na d'aura kunnuwana a bisa bayanan, caraf kunnuwana suka jiye min sunan 'yata, a matsayin wacce zata wa'kilci K'asa baki d'aya, a musabak'ar da za a gudanar ta K'asa, a 'Kasar Sudan.


Na kasa gasgata hakan, sai da na ji muryar Malaminsu da kanshi, yana mai nuna irin farin cikinsa. A k'arshe na ji muryar jakadan musaba'ka na jiha, yana nuna tashi murnar, da d'aya daga cikin d'aliban jiharsa ce zata wakilci 'Kasa ta b'angaren mata.


Abun nan ya min dad'i kwarai da gaske. Na sake jinjina wa kaina, ke, da kuma 'yata. Tabbas samun 'ya kamar Amrah babbar sa'ar rayuwa ce.


Amrah 'yata, ba zan ta'ba gajiyawa da shi miki albarka ba. Ba zan ta'ba daina miki fatan alkhairi ba."


A haka wannan rana ta zame mana ranar farin ciki, farin cikin da na jima ban yi irinsa ba.


Shi yasa ake so ka gode wa Allah a duk halin da kake ciki. Ka karb'i duk irin yanayin da mahaliccinka Ya yi ka. Kar ka butulce maSa saboda wata jarrabta da Ya yi maka, ko ba komai ka fi wani. Idan baka da lafiya, ka gode maSa, idan ka gode maSa, sai Ya baka ta wani fannin.


Gashi dai duk wahalar da kika sha tsawon shekaru goma sha shida da watannin da na haife ki kike fama da ciwo, ciwo kuma mai matu'kar wahala, wanda babu wuya mutum zai iya kauce ma sharia, ya ji kamar shi ne aka fi tsana duk duniya. A haka muka jure, muka dage da addu'a, muka tsayanta Allah d'aya ne. A hakan da wahalar da kike, muka tarbiyyantar da ke, muka d'ora ki a bisa tafarkin kirki.


A k'arshe mun ga ribar hakan, kin zama abar alfahari gare mu, malamanki, makarantarki, jiharki, da ma 'Kasarki baki d'aya."


Annur kanshi sanda ya ji wannan labarin ya matuk'ar jin dad'i. Shi a gidajen talabijin ma ya ga sanarwar, kuma daga 'kasa aka mak'ala sunanta.


Cikin lokaci k'ank'ane magana ta gama kewaye 'Kasa. Sunan Amrah ya shiga wurare da dama wanda bata ta'ba mafarkin zata je ba, sai ga sunanta ya je. Mutane da dama suke son ganinta, suke san sanin wai wacece wannan yarinyar mai tarin baiwa, wacce ta k'etare mutane da yawa, ta zama wa'kiliyar 'Kasarta?


Ranar da zasu tafi, har Kano muka rakasu, ita da Malaminta.


A iya inda zamu rabu, na kama hannuwanta duka biyun, na kalle ta cikin ido, na ce


"Ina miki fatan alkhairi 'yata. Ba zan tab'a daina yi miki addu'a ba. Insha Allahu nasara tana tattare da ke. Allah Ya taimaka, Ya bada sa'a. Ki kula da kanki, Amrah."


Wasu irin zafafan hawaye suka ringa kwarara daga idanuwana.


Cikin kuka take wasa da hannuwana, cikin kuka take k'irk'iro murmushi, cikin kuka take fad'in,


"Zan kula da kaina insha Allahu, Umma. Ki yafe min duk wani abu da na miki, b'oyayye da kuma bayyananne."


Zare hannu guda na yi daga cikin nata, da shi na share hawayen da ina share sa ina dambe da wani, wanda ke shirin sake fitowa.


"Baki ta'ba yi min komai ba Amrah. Banda alkhairi babu wani abu a tsakanina da ke. Idan ma akwaishi, na yafe miki."


Na sakar mata murmushi.


"Allah Ya 'kaddara saduwarmu, Umma." Ta fad'a had'e da zare hannuwanta daga nawa, ta rik'e na mahaifinta.


Tun bata furta komai ba ya ce,


"Baki ta'ba yi min komai ba 'yata. Idan ma akwai to na yafe miki. Ina mai neman gafararki, a bisa halin da muka jefa rayuwarki a ciki. Har yanzu na kasa yafe wa kaina. Har yanzu gani nake mu ne sila, mu muka jefa ki cikin wannan cutar. Ki yafe..."


Bai rufe bakinsa ba ta saka tafukan hannunta ta dafe masa bakin nasa,


"Bana son jin haka daga gare ka, Abbana. Komai na duniyar nan da zai samu mutum, to k'addararsa ce. Na sani, na kuma yarda cewa tawa k'addarar ke nan. Babu mai k'in d'aukar k'addara face butulu. Kar ka damu Abbana. Na yafe maka duniya da lahira. Na yafe maku kai da Ummana."


Cikin hawaye take murmushi.


Gaban Annur ta koma, wanda tun d'azu idonsa yake cikin nata.


Murmushi ya 'kirk'iro mata, ba tare da ya furta komai ba.


"Zan tafi Hammana. Ka yi min addu'ar samun nasara."


"Nasara na tare da ke insha Allahu, Amrah. Allah Ya taimaka, Ya bada sa'ar abin da aka je yi."


Lumshe idanuwanta ta yi, sannan ta sake bud'e su a kanshi.


"Kar ka manta da ni, Hammana. Duk rintsi duk wuya, kar ka manta da Amrah. Ni ma ba zan tab'a mantawa da kai ba."


Gyad'a mata kai ya yi, idanuwanshi cike da shauk'in soyayya,


"Idan har zan iya mantawa da ke, to tabbas zan iya mantawa da kaina. Ke ce rayuwata, Amrah. Ke ce duk wani tunanina. Na so a ce tare zamu yi tafiyar nan, sai dai kuma Allah bai nufa ba. Ni ma tafiya ta taso min, zuwa K'asar Malaysia, ina tunanin sai kamar ana gobe zaku fara zan dawo. Amma duk da haka, rayuwata tana tare da ke, zuciyata tana tare da taki. Motsinki da komai naki yana tare da nawa. Ina matu'kar k'aunarki."


Juyowa ta yi ta kalle mu, cikin jin kunya ta sunkuyar da kanta k'asa.


Saurin d'auke kallonmu muka yi daga gare su.


"Na gode k'warai Hammana. Na gode da sadaukar da rayuwarka da ka yi a kaina. Na gode da k'aunar da ka nuna min. Na gode da komai ma."


Ta fashe da kuka sosai.


"Ya isa haka to, please. Kin sani sarai, kin san yanda hawayenki yake da zafi a gare ni. Kin san yanda na tsani ganin zubar hawayenki. Kin san yanda rayuwata ta tsani ganin kin yi asarar hawayenki. Ki tafi, ga malaminki can yana ta jiranki."


"To Hammana. Allah Ya k'addara saduwarmu." Ta tafi.


Har ta isa iyakarmu da su bata daina waiwayenmu ba, bata daina hawaye ba.


Baki d'aya jikina ya yi sanyi, na rasa dalili. Duk da ina son tafiyar tata, na san ci gaba ne a gare mu baki d'aya, amma a hakan ji nake kamar ta fasa tafiyar, kamar ta dawo gare mu.


A haka muka kama hanyar parking lot. Muka shiga motar Annur, muka kama hanyar dawowa Katsina.


_Tabbas soyayya gaskiya ce, wacce Allah ne yake d'aura ma mutum ita, ba tare da zuciyarsa ta shawarce shi ba. Abu mafi dad'i a soyayya, shi ne ka had'u da mai sonka tsakani da Allah. Ka had'u da mai k'aunarka, wanda zai sadaukar maka da rayuwarsa. Ina rok'on Allah Ya had'a mu da masoyanmu na gaske. Allah Ya aurar da mu ga masoyanmu na gaske._


pinky durling💗
*RAZ 2*
[8/30, 3:36 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)


Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


2⃣0⃣


_Sa'kon gaisuwa ga tarin masoyan *AMRAH NAKE SO!* Kuna da yawa sosai, lissafo ku ba abu ne mai sau'ki ba. Sai dai duk inda kuke, ku sani cewa ana tare, ina yinku irin sosai d'in nan.😍_


***
Tun da muka shiga mota nake kuka, na rasa dalilin da yasa hankalina ya gaza kwanciya, damuwa da k'unci fal a cikin zuciyata.


Mallam ne yake

Please Login or Register in order to submit comment