You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baƙinta ba ne, ta san hanyar sarrafa shi sosai. Hatta makarantarta ta sahale da zuwa, babban burinta kawai ta shawo kan matsalar Modu, saboda ta fuskanci yana buƙatar wadataccen lokaci, yana buƙatar mai tausar zuciyarsa, haka kuma yana da buƙatuwar mutum mai muhimmanci a tattare da shi. Wannan dalilin ne ya sa ta sadaukar da lokacinta gare shi, take son zama mai muhimmanci a rayuwarsa, ta yadda burinta zai yi saurin cika.


A islamiyya ma da yake sun gama rehearzal, yanzu jiran ranar yi kawai ake, nan da kwanaki huÉ—u za a yi ta.


Babban burin Maryama shi ne ta kammala da abin da ke gabanta; wannan walimar saukar, sannan ta hau bincikar inda za ta samu babban likitan ƙwaƙwalwa, wanda zai duba Modu, ya kuma sama masa lafiya da ƙarfin mulkin Allah.


Zaune take da waya a hannunta, browsing take, sosai take bincikar matsalar Modu. Tun daga farkon damuwarsa, har izuwa haukansa, da kuma ciwon zuciyar da ya samu ta rubuta, tana mai neman shawara, tana son sanin haƙiƙanin abin da ya kamata ta fara bi, wurin tabbatar da lafiyarsa.


Shawarwari ta samu kala daban daban, wanda duk wadda ta ɗauka, sosai za ta iya zame mata mafita. Sai dai kuma inda matsalar take, ita ɗin ba ta kasance wacce ya san ta tun asalinsa kafin ya haukace ba. A mafi rinjayen shawarwarin kuma, sun ginu ne a kan ta nemi wanda ya sani kafin haukansa, wata ƙila zai iya tuna wani abu, har memory ɗinsa ya dawo daidai.


Mafi ƙaranci daga cikin shawarwarin, sun nunar mata da cewa wai ba hauka ba ne Modu yake, kawai dai ya yi losing memory ɗinsa ne. Don haka kawai ta ci gaba da zama a haka, ta yi haƙuri, a kowanne lokacin memory ɗinsa zai iya dawowa daidai, zai iya tuna komai da ya faru a baya.


"How could this happen? Ban gasgata wannan ba. Idan har losing memory ɗinsa ya yi, ai ba zai riƙe suna guda a rayuwarsa ba. Ba zai riƙe sunan Amrah, wacce ta kasance mai muhimmanci a gare shi ba. Da sai ya manta har ita ɗin, babu wanda zai zauna a ƙwalwarsa."


Ta faɗa a bayyane, tana mai rubuta comment a ƙasan wannan maganar, cike da al'ajabi.


Bayan ta rubuta wata mace mai suna Sandra ta sake rubuto mata; hakan ba abun mamaki ba ne. Ai don an ce mutum ya yi losing memory nashi, ba lallai komai ne zai fice masa a ka ba. Akwai abubuwan da ka iya zaunawa zaman daram a kwanyarsa, musamman ma Amrah da ta faɗi kalar darajarta a gare shi. Sosai tashin hankali kan kawo matsalar losing memory; ta yiu wata mummunar kalma ce mutum ya ji, wani tashin hankali ne ya gani, duk sukan iya ruɗa mutum, ya fita hayyacinsa, har ya manta komai na shi, sai dai kuma za ta iya yiuwa ya riƙe wancan abun wanda ya ji, ko kuma ya gani, har ya yi silar mantau ɗin. Shawarar da take ba ta, ta ci gaba da kula da shi, ta ci gaba da kyautata masa, tana bin duk wata maganarsa. A duk sadda zai furta Amrah yake so, ta ringa ƙarfafa masa guiwa, ta tabbatar ba ya yawaita shiga ƙunci. Kukan nan da yake, ta san duk yadda za ta yi wurin faranta masa, har ya mance da ɓacin ran da yake ciki. Ta kasance mai yi masa labaran soyayya, tunda dai ta silar soyayya ya shiga ƙuncin, da har ya miyar da shi haka. Ta nuna mishi ƙauna sosai, ta ba shi kulawa, har lokacin da za ta zama mai muhimmanci a gare shi, tamkar Amrar da ta yi silar komai na shi.


Murmushi Maryama ta yi a daidai wannan lokacin. Ta jinjina kanta alamun gamsuwa, ta É—an lumshe idanuwanta sosai tana jinjina lamarin. Sosai ta yarda da hakan. Sai dai fa mafi rinjaye na zuciyarta, ya fi yarda ne da cewa lallai hauka ne yake yi, tana da wata tambayar.


A ƙasan comment ɗin Sandra ta sake rubuta; na gamsu sosai da bayananki, amma kuma idan har losing memory ne ya yi, ai kamar ba zai ci gaba da yin abubuwa irin na taɓaɓɓi ba. Da hankalinsa, kawai dai ya manta komai na shi ne, sai Amrah kawai.


Alamun murmushi Sandra ta turo mata, ta ce babu abin da losing memory ba ya haifarwa. Zai iya zautar da mutum ma, koda ba mahaukacin ba ne, a ga ya zam tamkar mahaukacin. Kar ta taɓa tunanin hauka ke damunshi, domin yana da wuya irin haka ya haukatar da mutum, sai idan wani mummunan hatsari ya samu kansa ya bugu har ya taɓo sashen ƙwalwarsa, wanda zai gaggauta harbar wani sashe na daga cikinta da zai tsayar da duk wata hanyar da za ta yi ordering mutum abu. Kenan komai mutum zai yi zai koma disorderly. Abu na biyu kuma idan ya kasance kafin mutuwar Amrah, shi ɗin drug abuser ne, a hankali kwanyarsa ta fara taɓuwa, sai kuma aka yi katari da case na mutuwar ya iso, a take komai zai iya jagulewa, ya haukace kenan.


Mafi zargi dai losing memory É—insa ne kawai ya yi, amma mai tsananin gaske, mai haÉ—e da juyewar hankali kaÉ—an.


Ɗan taunar leɓonta ta yi Maryama. Sosai take mamakin kalaman Sandra. To amma, alzheimer's disease (Ciwon mantau) ta kama shi kenan?


Sake rubuta ma Sandra ta yi; tun daga mutuwar Amrah kenan alzheimer's disease ta kama shi?


Sandra ta ce ko kaɗan ba zai yiu a ce alzhermer's disease ba ce ta kama shi. Saboda ita alzhermers fa komai mutum mantawa yake, including his language. Ya koma tamkar ɗan koyo, komai sai an koya masa. Kuma abun haushi da zarar an koya masa zai manta. Akwai wanda na shi ke iya ɗaukar tsawon awoyi kafin ya manta ɗin, akwai kuma wanda a take za a koya masa, kuma a take zai manta. Shi kuma wannan har sunan Amrah yake faɗi, ya iya yarensa sosai. Ba za a taɓa alaƙanta shi da mai alzheimer's disease ba.


Godiya sosai Maryama ta ma Sandra, sannan a ƙarshe ta tambaye ta ko ta san wani likita wanda yake da wannan ilimin sosai ta haɗa ta da shi? Sandra ta ce ita kanta ɓangarenta kenan, sai dai kuma ba a Nigeria take ba yanzu, UK take. Idan har za su iya kawo shi nan ɗin, babu damuwa, she can help them.


Maryama ta ce ko a cikin abokan aikinta ba ta san wani da ke Nigeria ba? Ta ce mutum biyu ta sani sosai da wannan ilimin; Dr. Aqaaq Saifullah, sai kuma Dr. Hamdan M Ramat, wanda ya kasance mentor É—inta. Za ta nemi amincewarsu idan sun yi waya, ko me kenan, tai dropping digits É—inta, she will contact her.


***


Tun daga sadda rayuwar su Suhaila ta dawo Katsina Pharm IA ya koma karatunsa, a Sudan. Da haka rayuwarsa yaran nasa ta fara ginuwa a bisa turbar kirki, Nadrah da Saddiqa sun shiga wata makaranta mai kyau, domin samun ingantaccen ilimi kamar yadda mahaifinsu yake so.


A tsawon wannan lokacin sosai Annur ya fara yin wayo, dariya yake sosai duk da cewa watansa biyar kenan da ƴan kwanaki duniya. Kyakkyawan yaro ne jajur da shi. Idanuwansa farare ne sol, masu matsakaicin girma. Jikinsa ɓul-ɓul irin wanda kowa ke da muradin ɗaukar irinsu. Sumar kansa kwance take luf-luf, wacce idan yau aka aske ta, gobe za a fara ganin alamun tsirowarta. Bakinsa ɗan ƙarami ne, da siririn hanci, wanda kumatu ya cinye fiye da rabinsa. Komai na yaron abun birgewa ne. Ga uwa uba kuma fara'ar da gare sa, wadda kan jawo hankalin mutane a kodayaushe.


Kwanaki na tafiya, awanni na tserayya, mintuttuka na gudanya, sakan na kwararar gudu, har Pharm IA ya cika shekara huɗu a Sudan, inda ya kammalo karatunsa, ya zama babban pharmacist, wanda irinsu ke wuyar samu a ƙasarmu ta Najeriya.


Bayan ya dawo ƙasarsa ne kuma aka saka Annur makaranta ta boko da ta islamiyya. Watansa huɗu da dawowa kuma Suhaila ta samu wani cikin, wanda ta haifi kyakkyawar yarinyarta, sai dai ita ɗin baƙa ce, kamar sauran danginta mata. Jameela sunanta; sunan kakarta aka saka mata, mahaifiyarta ta mata laƙabi da Islam, saboda tsananin son sunan da take.


A cikin lokutan da Annur ya fara mallakar hankalin kansa ne Allah ya jeho Amrah a rayuwarsa, sanadiyyar wani dalili da ya sa mahaifiyarta ta zo ƙofar gidan su Annur ɗin, har ya ga Amrah, a lokaci ɗaya ya kamu da begenta, duk da kasantuwarsa ƙaramin yaro. Ya ɗauke ta ya ajje a cikin zuciyarsa. Ya sadaukar da komai nasa saboda Amrah. Duk inda zai je sai ya biya ta gidan su Amrah ya ganta sannan yake samun kwnaciyar hankali. Haka ita ma Amrah, tun tana ƴar ƙaramarta ta shaƙu da shi, ta saka shi a cikin zuciyarta, izuwa lokacin da aka raba su, aka miyar da shi Cyprus wurin yayarsa Nadrah.


A ɓangaren Salman ma dai haka ya ringa yin wayo, kyakkyawa da shi wanda ko kaɗan ba shi da bambanci ko kaɗan da Annur, kamarsu ɗaya, komai nasu ɗaya. Sai dai matsalar babu wanda ya sani, babu kuma wanda zai iya fayyace musu gaskiya sai Dr. Rita, saboda ita kaɗai ta san kamannin Annur, ta kuma san cewa shi ne a hannun Suhaila. Matuƙar za ta ga hoton Salman na jarintaka, to tabbas za ta tabbatar da cewa kamanninsu iri ɗaya ne da Annur.


***


Tunda suka zauna a gaban teburin likitan gabansu ke tsananta faÉ—uwa, barinma Farouk Sardauna da hankalinshi ya gama tashi, jikinshi ya gama ba shi cewa lokacin mutuwarsa ya kusa.


Suna cikin haka sai ga likita ya shigo sanye da lab court, idonsa sanye da medical glasses yana faÉ—in,


"Afwan na barku da jira. Abokin nawa sai da na kai shi har gaban mota ne."


"Babu komai."


Annur ya furta haɗe da ƙirƙiro murnushi yana bin Dr. ɗin da kallo.


Bayan ya zauna a mazauninsa ya zare glasses É—insa, ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, sannan ya hau duba results É—in Bobby.


Sosai Bobby ke jin raɗaɗi a zuciyarsa, yake jin duniyarsa na sauya masa, tashin hankali wanda tunda yake a rayuwarsa bai taɓa yin irinsa ba yake ji. Firgigit ya zabura haɗe da dawowa hayyacinsa, a lokacin da ya ji tattausan kalaman likitan, ya ƙura masa idanuwa,


"Ya kake da wannan bawan Allah'n? Ina nufin can I say anything infront of him?"


Da kai Bobby ya ba likita amsa, cewa ya faɗa ɗin kawai. A wannan lokacin kam ya gama sadaƙewa, ya kuma tabbatar da cewa ba ƙaramin ciwo ba ne a tattare da shi, tunda har likitan ba ya son faɗi a gaban Annur.


"A bisa hotuna da aka maka ga su, sun bada tabbacin cewa hunhunka ne ke da matsala. Shi ne ya yi damaged, gurɓatarsa har ta fi lafiyarsa yawa. Ko ka san abin da ya jawo haka kuwa?"


Ya sake gyara zamansa, har yanzu bai É—auke idonsa daga fuskar Bobby ba.


Bai jira amsar da Bobby É—in zai ba shi ba, ya É—ora da faÉ—in,


"Smoking ne, shi ne sila Farouk!"


Ido buÉ—e Bobby ke sake dubar Dr. Ba tare da ya furta komai ba yake zubar da ruwan hawaye, yana É—an gyaÉ—a kansa.


Annur É—in ma bai iya faÉ—ar komai ba, sai dai fa cike yake da tausayin amininsa, sosai yake jinshi har cikin zuciyarsa. Me ya sa ciwo zai musu haka?


"A duk sadda mutum yake shaƙar hayaƙi, ko kun san cewa wannan da kuke tutiyar ai kuna fiddo shi ta baki da hanci, ba dukansa yake fitowa ba? Sannan kuma dole sai ya isa cikin hunhunku, sannan ma duk abin da zai yi ya yi? Wannan smoking ɗin da kuke ji da gani, ba shi da wani amfani a gare ku face matsala, wadda za ta iya kai mutum ƙabari. Yanzu dai ga shi, baki ɗaya hunhunka ya yi damaged, sauran amfaninsa kaɗan ne, matuƙar ba a tashi maka tsaye ba, akwai babbar damuwa.


Abun haushi, har da wata sabuwar sigari aka kawo yanzu, wai ita shisa. Kun san cewa duk illar da sigari za ta yi ita ɗin ma za ta yi shi? Yes! Za ta yi shi. Saboda hayaƙi ce ita ma, an shaƙe ta ne kuma aka isar da ita cikin ciki, kuma kai tsaye hunhu za ta kai mawa.


Shi hunhu wani irin abu ne, wanda babu wuya yake shafewa. Yanzu ku ɗauki misali, a nemi hunhun rago a yanka shi manya manya, sai a tsoma shi cikin ruwan mai, wuta ta bige shi. Ya zai yi? Zai koma ya laƙume, tamkar ba manyan yanka aka yanka shi ba. To haka ko na mutum ma yake yi, da zarar ana kai masa hayaƙi, wannan laƙumewar haka zai yi ta, a hankali har ya kai minzalin da zai gama lalacewa.


Ko mata masu amfani da icce wurin girki, ana yawaita faɗakarwa a kan hakan, cewa su daina zama a bakin wutar sosai, matuƙar suka haɗu da icce mai hayaƙi. Saboda wannan hayaƙin zai iya yi musu illa, sosai zai harbi hunhunsu. Su ɗin ma da ya zamewa dole kenan.


Amma ku sai ga shi kuna kai kanku halaka da kanku. Kuna yin abin da ba zai amfane ku da komai ba. Ba za ku ƙaru da komai ba face ciwo mai girma. Why? Me ya sa kuke haka?"


Ya dakata daga nan, yana mai tsananin jin takaicin Farouk Sardauna. A wani ɓangaren na zuciyarsa kuwa, tausayinsa yake, ta yadda yake yaro matashi, amma wannan cutar ta kama shi, wacce ba lallai ma ya ci gaba da rayuwa ba.


Dafe kansa ya yi Dr. Da ƙyar ya iya ci gaba da faɗin,


"Akwai drugs da zan rubuta maka, a dage amfani da su, bayan sati biyu sai ka sake dawowa."


Godiya Annur ya masa, zuciyarsa cike da rauni. Tausayin abokinsa ya gama mamaye duk wata gaɓa ta cikin zuciyarsa. Ƙwaƙwalwarsa yake ji tana juya masa, tana neman dagula duk wani lissafi nashi.


Bayan Dr. Ya rubuta musu maganin ne suka miƙe, jiki ba ƙwari suka bar Office ɗin na shi.


***


My pipu how are y'all? I hope na same ku lapia😍 its been a while ba mu hadu ba ko? Tun kafin sallah. Hidimomi ne suka sha gabana, kun san sallah akwai dadi, zumunci ake sadawa sosai😀 yanzun ma fa kar ku zata an gama. Masoya ANS ne kawai suka taso Amrah a gaba,🤒 don dole na na kokarta taipa muku wannan, ba wani mai yawa sosai ba🤦


To ya kuke gani fans? Waye ne Dr. Hamdan M. Ramat din nan, wanda Dr. Sandra ta ce mento dinta ne? Kamar dai farkon haukar Annur ai Dr. Aqaaq Saifullah ya duba shi ba a dace ba.🤔 Bayanan da Dr. Sandra ta ma Maryama hakan zai iya kasancewa ko ba zai iya ba?


Ina za mu iya gano Sister Rita bare ta warware mana wannan kullalliyar, mai wiyar kwancewa?


Me kuka hasaso ne a wannan ciwon da Farouk Sardauna (Bobby) yake yi? Kar fa ya mutu, ina kaunar Bobby nawa🤧😱


A tabbatar an dropping comments, kafin zuwan next chapter.


Vote, comment and share with your family and friends.


Thanks all


Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:56 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_


Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


4⃣8⃣


Wattpad me: PrincessAmrah


***


Tun bayan shigarsu mota Bobby ke kuka sosai tamkar ƙaramin yaron da ba ya jin rarrashi. Yana yin kukan yana wani irin tari, wanda da zarar ya tara hannunsa ya fiddo kaki sai ya ga gullamar jini ce. Hakan ba ƙaramin ƙara tayar da hankalin Annur ya yi ba. Ya ma kasa rarrasarshi, shi kanshi ji yake ina ma dai ruwan hawayen ya zo, da bai ga abin da zai hana shi barinsa wanzuwa a saman fuskarsa ba.


Da ƙyar ya iya rintse idanuwansa Annur, ya buɗe su da wani guntun ƙwalla, mai matuƙar zafi a gare shi. Cikin nutsuwa da kwantar da kai ya fara ajje kalamansa, zuciyarsa na ƙuna sosai.


"Ka yi haƙuri Guy, ka kai zuciyarka nesa. Kar ka zata wai don kana cuta hakan na nufin ka kusa mutuwa ne, ko kaɗan ba haka ba ne. Cuta ba mutuwa ba ce..."


Yana neman ci gaba da magana Farouk ya dakatar da shi, cikin sassarfar murya, bakinsa na rawa sosai ya ce,


"Kar ka damu guy. Ka kwantar da hankalinka, na ga ka tasarshi sosai kawai don ba ni da lafiya. Idan ma mutuwar ce ina da maganinta ne?"


Ya saki guntun murmushi, wanda za a iya kiransa da na yaƙe, ya ci gaba,


"Abokina hunhuna fa ne ya lalace, kana sa ran zan ci gaba da rayuwa ne? Na cire rai da rayuwa guy. Ka kai ni gida please!"


Babu musu Annur ya ja motar tashi, suka bar harabar asibitin. Ko a mota babu mai cewa kowa uffan, sai saukar ajiyar zuciya kawai da ke fita. Abun mamaki, su ɗin da suka kasance masu ƙure sautin mota, sai ga shi yau babu. Su ɗin da suka kasance ba a raba su da kayan maye a cikin mota, yau babu. Su ɗin da suka kasance masu raha da shewa a cikin mota, yau babu ko ɗaya. Lallai wannan rayuwar abun tsoro ce. Kana taka Allah na naSa. Kana nan sake da baki kana bankaura, ba ka san ya rayuwarka za ta kasance ba. A duk inda rayuwar ɗan maye take, ba ta taɓa tasiri a ƙarshe, ba zai taɓa aikata abun kirki ba a ƙarshe, matuƙar bai shiryu ba.


A haka suka isa gidan su Farouk ɗin, bayan ya kashe motar ya zagayo ya taimaka masa ya fito, tafiyar kanta a wahalace yake yin ta, saboda cin ƙarfinsa da tarin ya yi. Kuma idan ana kuka dama tari ya fi ta'azzara.


Har ɗakinsa ya kai shi sannan ya kunna masa AC, saboda zufar da yake yi. A zuciyarsa Annur yake tunanin yadda rayuwa ta juyewa abokinsa a tashi guda. Dafe kansa kawai ya yi, yana ƙoƙarin shanye kukan da ke niyyar kufce masa.


***


Cike yake da mutane gidan na su, sai shige da fice ake, ana ta shirye shiryen tafiya wurin walima. Tun bayan da ta yi wanka sam hankalinta ba ya jikinta, yana ga Modu da take tunanin za ta fita ta bar shi yau. Ga shi kuma idan ta tafi wurin walimar, ba da an gama za ta dawo gida ba. Sai sun yi tasu ta musamman a tsakanin Æ´an ajinsu.


Tagumi ta rafka, ta rasa uwar ubanta. Ji take kamar ta É—aura hannu a ka ta yi kuka, sai dai babu dama. A wani sashe na zuciyarta kuwa ji take ina ma a ce an É—aga wannan walimar, har zuwa wani lokaci, duk kuwa da zakwaÉ—in zuwanta da ta ringa yi a baya.


Sallamar Muhammad ce ta dawo da ita daga duniyar da ta lula ta tunani. Saurin amsa sallamar ta yi haɗe da ci gaba da shafa powder, tana ƙoƙarin miyar da komai ba komai ba.


"Yaya Maryama, Mama ta ce wai ba ki gama shiryawa ba? Wai kar a makara. Kuma kar ki manta da maganin Yaya."


"Na kusa kammalawa Hammad. Ka ce ina zuwa. Na ba shi maganin tun kafin na yi wanka."


Ficewa ya yi a guje tare da sanarwa Mama saƙon Maryama.


Jiki babu ƙwari ta gama kimtsawa. Hijabinta ta zira har ƙasa sannan ta fito, mutane ta gani dangin Mama da na Abba, zazzaune da yawa, wai a haka ma wasu sun yi gaba tare da Abbah, wasu kuma Mallam Ya'u ya tafi da su, sai ya dawo ya ɗauki Maryama sannan a kwashe sauran mutanen.


Har ƙasa ta duƙa ta gaggaishe su, sannan ta nufi ɗakin Hammad inda Modu yake, ta same shi zaune ya yi tagumi, ruwan hawaye na kwaranya a bisa fuskarsa. Yana ganinta ya yi gaggawar janye hannuwansa daga tagumin da ya yi, saboda ta ce da shi matuƙar bai daina yin tagumi da kuka ba, ba za ta taɓa kai shi inda Amrah ba. Wannan dalilin ne ya sa duk sadda za ta shigo zai kwantar da hankalinsa, ta ci gaba da saka shi cikin farin ciki da walwala.


"Ba ka daina ba ko?"


Ta faɗa tana harararsa, bayan ta ƙarisa shigowa cikin ɗakin.


Kansa ya ringa gyaɗa mata, yana ƙoƙarin yin dariyar yaƙe, wanda a kodayaushe ya yi shi, sai zuciyar Maryama ta sake karaya, saboda ji take ina ma dai ya dauwama a haka cikin walwala, ina ma a ce hankalinsa ya dawo gangar jikinsa.


"Yauwa É—an albarka. Yau ba za mu samu damar yin wannan darasin ba. Amma dai ina fatar ka haddace wancan É—in da muka yi."


Kansa ya gyaÉ—a har yanzu bai daina mata murmushi ba.


"To É—an tuna min ma, a ina muka tsaya?"


Ta karkaÉ—e kunnenta haÉ—e da nuna masa shi da hannunta.


Toshe bakinsa ya yi sannan ya fara magana ƙasa-ƙasa, wacce duk kusancinka da shi ba za ka taɓa gane me ya faɗa ba.


"Ya Noor ba na jin ka fa."


Ta faÉ—a da wata murya, tana kallon cikin idanuwansa.


Baza mata na shi idanuwan ya yi yana kallo, haka kawai ya samu kansa cikin bege, ya ƙara tuno wasu abubuwa game da Amrarsa. Shiru ya yi, gabansa na tsananta duka, ya kasa koda ƙyafta idonsa ne.


Ganin haka ya sa Maryama ta raina kanta. Ta rasa gano manufarsa, ta kuma samu kanta da faÉ—uwar gaba.


"Uhm...bara na tafi."


Janye hannuwansa ya yi daga bakinsa, ya ɗan langaɓe kansa, da murmushi ya ce,


"Kin ce wai soyayya da ƙauna suna da bambanci. Soyayya takan ƙare a wasu lokuta, saɓanin ƙauna da babu abin da ke kankare ta. Kuma kika ce...me ma?"


Ya É—ora hannuwansa a kumatu alamun tunani. Sannan ya murmusa ya ce,


"Wai akan yanke soyayya ta wani dalili. Ko mutum ya naƙasa, ko ya haukace, idan soyayya ce ake yi to za ta gushe. Ita kuma ƙauna duk wuya duk rintsi ana tare. Babu abin da ke lalata ta. Kuma a ƙarshe kika ce wai irinta ce nake ma Amrahhhh."


Ya ja maganar a ƙarshe, haɗe da rufe idanuwansa alamun kunya.


Tafa masa ta yi tana dariya.


"Good job Ya Noor ɗina. Lallai kana ganewa sosai, kwanyarka tana ja. Na tabbatar kam ka fahimci wannan darasin, sai kuma gobe insha Allahu za a ƙara maka wani."


Ɓata fuskarsa ya yi alamun jin haushi,


"Ni yau nake so."


Samun wuri ta yi ta zauna a kusa da shi, ta sauke ajiyar zuciya haÉ—e da faÉ—in,


"Ka cika rigima Ya Noor. Yau fita zan yi fa. Ranar farin ciki ce a gare ni, kai ma ya kamata ka zama a cikin farin ciki. Walimar saukarmu fa ake yi."


Zullo ya hau yi a saman gadon, yana jin daÉ—i sosai ya ce,


"Amrata ma an musu walimarsu ta sauka."


Dafe kanta ta yi Maryama, nan ta fara tunowa da kalaman Sandra, inda ta tabbatar mata da cewa losing memory É—insa ne ya yi Annur. Kuma dama mutum yakan tuna wasu abubuwa da suka danganci dalilinsa na yin losing memory É—in. Wanda idan har zai samu mai É—ora shi a saman hanya, sannu a hankali zai fara dawowa hayyacinsa. Zai fara tuna komai na rayuwarsa da ya manta.


"Zan tafi. Anjima Hammad zai zo ya ba ka maganin rana. Kar ka musa masa, da zarar ya ba ka ka karɓa ka sha, idan ba haka ba kuma zai faɗa min, kuma ba za mu sake yin darasi ba."


Kai kawai ya gyaÉ—a mata, da haka ta fice daga É—akin, ta samu har Mallam Ya'u ya dawo, wucewa kawai suka yi zuwa Islamiyyarsu.


*


Taro ne na ji da faɗa aka yi. Rumfuna aka kafa manya manya, ga plastic chairs nan birjik an jera. Ga ɓangaren da manyan baƙi za su zauna, da kuma na sauran al'umma. Sai daga can gefe kuma masu saukar ne sai farin ciki suke. Maryama da Jiddah jere suke da juna, komai nasu iri ɗaya ne, hatta da yadin hijabinsu babu bambanci.


Addu'ar buɗe taro aka yi, kafin nan aka kira shugaban makaranta domin yin bayanin tarbar baƙi, da kuma nuna farin cikinsa ga wannan rana. Bayan ya gama kuma ya ɗora da bada tarihin makarantar, kamar yadda kusan kowacce walimar sauka akan yi, shugaban makaranta yana bada tarihin makarantar. A sadda ya kai gaɓar aya a zancensa, ɗai-ɗaikun mutane ne ba su koka ba. Saboda da dama an san labarin Amrah, an kuma san sadda ta rasu. Sai ya zama

Please Login or Register in order to submit comment