You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da wayarta a jikin chaji ta miƙe, ta nufi ban-ɗaki domin gabatar da alwalla, ta yi ƙiyamul-laili, ta sanar wa Allah damuwarta, da neman agaji a wurinSa.




*


Washe gari da sassafe Maryama ta tashi. Sosai take jin dukkanin nutsuwarta da ta rasa tana dawo mata. Sassauci take ji sosai a cikin zuciyarta.


Sauka ta yi daga bisa gadonta. Ta cire hijabin da ke jikinta, sannan ta nufi hanyar barin É—akin, ta doshi kitchen.


Dankalin turawa ta hau ferewa. Bayan ta gama ta kama aikin suyarshi, ta jajjaga tarugu da albasa da maggi, sannan ta fasa ƙwai ta ma Abbanta sauce ɗin ƙwai.


Sai da ta gama duka sannan Mama ta shigo Kitchen É—in. A tsammanin Maryama Mama ba za ta kula ta ba. Sai dai kuma ta ga akasin hakan. Da murmushi Mama ta ce da ita,


"Sannu da ƙoƙari. Yau barci ya so ya ƙwace min wallahi. Allah dai ya sa kin tashi Hammad daga barci."


Dafe kanta ta yi Maryama.


"Shaf na manta Mama. Bara na hanzarta to. Har bakwai ta wuce."


Da saurinta ta nufi É—akin Mama, inda Muhammad ke kwana shi kaÉ—ai.


A zaune ta same shi. Ya ɗora tafin hannunsa na dama a bisa haɓarshi, ya yi zurfi a tunani.





Tsaye ta yi tana ƙare masa kallo. Ta rasa abin da yake tunani. Ba ta farga ba ta ga ya kuma juyawa, ya koma ya yi kwanciyar rigingine a bisa gadon ya ƙura ma wuri ɗaya kallo, hannayensa ya tallabe ƙeyarshi da su.





Take Maryama ta ji hankalinta ya tashi. Jiki saɓule ta iso gare shi. Ta saka hannunta na dama tana bubbuga shi.


"Tunanin me kake haka Hammad?"


Ta nemi wuri ta zauna.


Sai a sannan ya ji ƙwalla ya zubo masa. Cikin muryar kuka ya ce,


"Yaya Maryama ina tunanin rabuwa da ke ne. Wai yanzu shi kenan aure za ki yi ki bar ni? Tafiya za ki yi ki bar ni Yaya? Zan yi kewar ki sosai."


Hawaye ya gama wanke mishi fuska.


Hannunshi na dama ta kama ta riƙe. Cikin kwantar masa da hankali ta ce,


"Ba na son ganin hawayenka ƙanina. Ka share su please. Don an ce za a min aure ai hakan ba wai yana nufin na bar ka ba kenan. Sannan kuma yanzu ko an yi auren ma ai a nan gidan za mu ci gaba da zama, har sai sadda Annur ya samu lafiya. So, ka kwantar da hankalinka. Okay?"


Kai ya É—aga mata kawai, ba tare da ya furta komai ba.


"Then, stand up and act like a man, not a boy. Its already time for school. Hurry up and get ready for going to school."


Cike da jarumta ya miƙe, ya nufi ban-ɗaki domin shirin makaranta.


Gyaɗa kanta ta yi Maryama, tana jin tausayi haɗe da soyayyar ƙaninta na daɗa shiga duk wata kusurwa da take cikin zuciyarta.


Bayan fitar ta ta samu babu kowa a falon, ta leƙa kitchen babu Mama, hakan ya sa ta nufar ɗakin Abba, tana jin zuciyarta na bugawa sosai, tunanin abin da za ta tarar daga wurin Abbanta. Zai kula ta ko ba zai kula ta ba?.


"Mama na duba ban gan ki ba."


Ta faɗa bayan ta duƙa har ƙasa, ta ce,


"Barka da tashi Abba."


"Yauwa."


Ya faɗa ƙasa-ƙasa.


"Ina kwana?"


"Lafiya."


Duk da yanayin yadda ya amsa mata gaisuwar, hakan bai hana ta samun sassauci a zuciyarta ba. Sosai ta ji daɗi, ta kuma tabbatar cewa ya rage jin haushinta, da alama Kawu Imrana ya roƙa mata gafara a wurin shi.


"Kin tashi Hammad É—in dai ko?"


"Ehh Mama. Na tashe shi. Ya shiga wanka ma na baro É—akin"


Ta ƙarisa da fita ta bar ɗakin.


Kai tsaye daga nan ɗakin Annur ta nufa. Fuskarta cike da fara'a. Zuciyarta na tsananta ƙaunarshi. Duk wata gaɓa ta jikinta tana jin yadda jijiyoyi da jininsu ke yawo da soyayyar Annur.


***


*How y'all? I hope you're all fine. Ban ma san me zan faɗa ba. Bakina ya gagara furta komai. Zuciyata na cike da ƙaunarku. Hannuwana na cike da son rubuta sunan nan. RAZ NOVELLA 1. Ina yin ku, ina ƙaunarku, ina muku soyayya ta fisabilillah. Haƙiƙa na matuƙar jin daɗin comments ɗinku na jiya. Na yi farin ciki fiye da tunaninku. Ina fatar ɗorewar hakan, ba wai a kaina kaɗai ba, ga kowa ma.*


*Masu mutunci ba sai na ce komai ba. Kun san me ya dace, I know.*


Team Marnoor
Team ANS
Team Princess Amrah
Team NWA


Thanks all.


Pinky durling💞
RAZ 2
[9/10, 7:30 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taɓa zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_




Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*




6⃣0⃣


Wattpad: PrincessAmrah


***


Runtse idanuwansa ya yi boka Gagarabadau. A hankali ya buÉ—e su, ya sauke a saman kurciyar. Take nashi idanuwan ma suka rikiÉ—e, sukai jajur, tamkar jan gaushi.


Kallonshi take yi sosai kurciyar, a hankali idanuwanta na komawa normal, kamar na kowacce irin kurciya.





Haɗe dukkanin tafukan hannayenshi ya yi, ya kanga su a saman fuskarshi, ya rinƙa ambaton wasu irin kalamai, wanda shi kaɗai ya bar ma kanshi saninsu. Sai dai kawai yana ambatar Salman Sans, a cikin yaren nashi, sannan kuma sunan Annur ya biyo baya.


A hankali kurciyar ta rinƙa tasowa sama, har ta iso a daidai saitin fuskar bokan, sannan ta dakata a saman iska.


Ciro hannuwan nashi daga jikin fuskarsa ya yi. Sai ga wata irin ƙatuwar laya ta fito, ya saƙalo zarenta a jikin wuyan kurciyar, sanann ya sake yi mata wani tsafi. Jinin da ke cikin ƙwaryarsa ya ringa ɗiba yana watsa mata, a hankali ta rinƙa yin sama, har ta ɓula rufin ɗakin ta fice, sanann ya daina watsa mata ruwan.


Murmushi ya saki mai ƙarfin gaske. Ya ce,


"Ta tafi kenan, har abada. Ka ga yadda ta tashi sama, haka za ta ci gaba da tafiya, ba za ta tsaya ba har sai ta fice daga ƙasar nan, koma dai ina ne. To a duk inda ta dakata, a nan wanann mahaukacin zai dakata shi ma. Kamar yadda za ta ci gaba da rayuwa a wurin, shi ma a haka zai ci gaba da rayuwa a wurin. Duk ranar da ta tafi, shi ɗin ma zai tafi. Abu guda ɗaya ne tal zai iya dawo da shi garin nan. Shi ne a samu wani wanda zai cire layar nan daga wuyan waccan kurciyar, to lallai daga sannan zai iya dawowa garin nan, koma ta wacce hanya ce."


Ajiyar zuciya ya sauke Bobby. Yana mai fahimtar dukkanin bayanan bokan.


Akwai dokoki sosai na wannan aikin. Sai dai kuma ba wasu masu tsauri ba ne. Doka ta farko, babu soyayyar gaskiya (True love). Daga sadda ya aikata haka, lallai za a iya samun matsala da wannan aikin, komai zai iya lalacewa. Abu na biyu, zai samu karuwa, ina nufin mace mai zaman kanta, wacce zai rinƙa aikata zina da ita, na tsawon lokuta. Ina mai tabbatar maka da cewa, matuƙar ya tsaida dokokin nan, ya aikata komai yadda ya kamata, to zai dauwama a gidan. Rayuwarsa da komai za su koma ƙarƙashin mutanen, ba tare da kowa ya fahimta ba. Fatar kana fahimta."


Kanshi ya É—aga da sauri Bobby, ya ce,


"Na fahimci komai Boka Gagarabadau."


"Da kyau. Sai ka ɗauki ƙwaryar nan ka sha jini a madadin abokin naka. Ka ajje abin da za ka aje."


Bayan ya ɗauki ƙwaryar ya kwankwaɗi jini, ya zaro kuɗi daga aljihunshi, ya ajje a gaban bokan. Sai da ya masa kirari sosai, sannan ya tashi ya tafi.


Annur da ke zaune ya takure jikinshi, ya ɗora tafukan hannayenshi a bisa fuskar, yana sanye da wata baƙar T-shirt wadda Sans ya umurci Yax ya saka mishi.





Ji ya yi kamar wani abu ya daki zuciyarsa da ƙarfi. Bai san sadda ya miƙe tsaye ba. Ya fara waige-waigen gaba da bayanshi. Bai ga kowa ba, hakan ya sa ya gaggauta barin ɗakin da sauri, ya isa falo.


Yax da Esien a zaune suna fira, suna ganinshi suka mimmiƙe da mamaki, Yax na faɗin,


"Me ka fito yi?"


Bai ko damu da su ba bare su sa ran zai amsa musu tambayarsu. Da iya ƙarfinsa ya bangaje Esien da ya matso daf da shi. Ya gaggauta isa bakin ƙofar, ya buɗe ta.


Haka ya rinƙa tafiya da sauri da sauri, babu waiwaye haka kuma bai damu da kallon gabanshi ba, har ya fita titi. Tafiya ya yi sosai, sai dai idan ya gaji ya nemi wuri ya zauna ya huta, har duhu ya fara yi. A lokacin ya isa wani ƙauye ne, a bakin wata bishiya ya zauna hutun, bai ankara ba barci ya ɗauke shi. Shi ne bai farka ba sai da safe, kamar wanda ake tsikara ya miƙe, bai damu da yaran da suka zuba mishi ido suna kallo ba, ya ci gaba da zura sauri, har ya fice daga ƙauyen.


Da haka da haka har Annur ya isa MaraÉ—i, inda ya É—auki kusan kwanaki huÉ—u yana tafiya a hanya, kafin ya isa MaraÉ—in. Saboda dama daga Katsina zuwa MaraÉ—i ba wata tafiya mai tsayi ba ce. Sadda ya isa boarder, Æ´an sandansu na can sun so su dakatar da shi, amma wani daga cikinsu ya ce su bar shi, tunda dai ba shi da hankali.


Wannan dalilin ne ya sa rayuwar Annur ta koma MaraÉ—i. A ranar da ya isa ya haÉ—u da Fiddou, wacce ta taimake shi, ta ba shi dukkanin gata, tamkar dama can ta san shi.


*


Tun bayan da boka ya gama aiki, iyayen Annur suka samu kansu da samun nutsuwa sosai, dangane da Sans. Ko kaɗan babu wanda ya taɓa tunanin cewa ba Annur ɗinsu ba ne, duk kuwa da cewa ba duka abu ba ne za a ce iri ɗaya da Annur ɗin, dole za a samu bambanci komai ƙanƙantarsa. Sai dai kuma asiri ne ya ci su, ya ci dukkanin wani makusancinsu. Abokanan Annur baki ɗaya wanda suka zo yi mishi jaje, Sans ya wulaƙanta su, ya ci mutuncinsu, sannan kuma ya musu korar kare.


Muguwar rayuwarshi ta shaye-shaye da bin mata ta ta'azzara. Baki ɗaya zuciyarsa ta gama ƙeƙashewa, ta bushe, babu tsoron Allah ko kaɗan a cikinta.


A lokacin ne kuma Bobby ya gabatar da Annur a gidansu, cewa ga babban abokinshi, sun haÉ—u ne ta dalilin wani biki da suka yi. A take iyayenshi suka aminta da Sans, saboda asali sun san Pharm. IA. Sun san cewa mutumin kirki ne. Haka kuma yaransa na da tarbiyya sosai.


Akai-akai ya rinƙa ziyartar likita, domin tabbatuwar lafiyar ƙafarsa, kuma ya yi nasara, ƙafar ta gyaru sosai, sai dai ƴan lokuta da ciwon yake ɗan taso mishi.


Maganar aikinsa kuwa dole ya bar shi, saboda shi kam bai iya zane ba. Ko sadda suka koma wurin boka, sai dai bokan ya ce ya haƙura da zanen kawai, ya rungumi kowanne irin matsayi aka ba shi a kamfanin. Wannan dalilin ne ya sa ya bar zane. Ya zama CEO na kamfanin ƙere-ƙeren ƙarafan Pharm IA, aka nemi wani mai zanen daban.


*


Bayan wasu lokuta.


Wasu mutane ne zaune a majalissa, sai fira suke a tsakaninsu, suna maida yadda akai.


Kamar wasa suka ga wata kurciya ta faɗo ƙasa a inda suke, da laya maƙale a wuyanta.


Wani daga cikinsu ya ce,


"Ilu ji ikon Allah. Kurciya ce ga ta nan maƙale da laya a wuyanta."


Wanda aka kira da Ilu ya ce,


"Hala ma wani ne akai ma tsahi, aka korai daga garinsu. Wayyo Allah! Ke duniya, ina za ki tahi da mu?"


Wani dattijo da ke zaune gefe ya ce,


"Aikam cire ta nikai yanzu, babu ko ɓata lokaci."


"Mallam Rabe mi ruwanka halan? Kai dai ka ƙyale ta, bari ma in tada ta ta tashi, koma ina za ta tai ta tahi."


Mallam Rabe ya ce,


"Kar ka kore ta Ilu. Cire layar nan daga wuyar kurciya ga ta, tamkar jihadi ne, mai matuƙar girma. Allah kaɗai ya san ladar da za mu samu, idan har wanda akai ma ita ya koma ga dangi nai."


Kai suka jinjina su duka, alamun sun gamsu da zancen Mallam Rabe.


Da sanɗo da dabara ya lallaɓa ya cafke kurciyar, tana ta ƙoƙarin zille mishi, amma ya riƙe ta tam! Bai sake ta ba, har sai da ya cire layar daga wuyanta. Jifa ya yi da ita, ba ta isa ƙasa ba ta tashi sama.


Kwance layar ya yi, sai ga wasu irin tsummuna a cikinta, da takardu ƙanana-ƙanana, wani irin rubutu ƙunshe a jikinsu.


Ƙwala ma wani yaro da ya zo gittawa kira ya yi. Bayan yaron ya zo ya ce,


"Shiga gidan can ka ce in ji Mallam Rabe wai a bada ashana. Ka hanzarta ka ji."


Da gudun yaron ya isa gidan, babu jimawa sai ga shi ya dawo, ya miƙa ta ga Mallam Rabe.


Ƙyasata ta ya yi a layar, take ta kama da wuta.


"Mutane babu imani. Ku kalli ku ga wannan mugunta don Allah. Yanzu ƙila wanda aka ma wannan kurciyar ya yi shekara da shekaru rabonshi da gidansu. To yau Allah ya yi, ƙarshen munahukan ya zo. Insha Allahu zai koma ga danginshi. Yau yau ɗin nan."


Da haka zaman majalisar nasu ya kasance, cike da al'ajabin wannan al'amari.


Daidai lokacin da suka cire layar kurciyar ne Maryama ta iso, suka tafi da Annur, zuwa ƙasarshi Najeriya, garinshi Katsina.


***


Zaune yake a takure, hannunsa bisa haɓa yana tunanin duniya. Sosai ya yi zurfi a tunani, har ma bai san abubuwan da suke faruwa ba.


Bubbuga shi ya ji an yi, ya zabura haɗe da shafe guntuwar ƙwallar da ta fito daga ƙwayar idonsa.


"Annur..."


Muryar Dadyn Bobby ce ta daki kunnuwanshi.


"Na'am Dady."


Ya faɗa cikin sassanyar muryarshi, wacce tun daga ranar da Farouk Sardauna ya rasu, ta koma haka. Komai nashi ya koma a nutse, tafiya ma kanta idan yana yi tamkar ƙwai ya fashe mishi a cikin cikinsa haka yake yin ta.


"So nake in tambaye ka."


ÆŠora idanuwanshi ya yi a saitin fuskar Dadyn Bobby, tare da miyar mishi da dukkanin hankalinsa, don jin tambayar da za ta fito daga bakinsa É—in.


Sai da Dadyn Bobby ya sauke ajiyar zuciya, sannan ya ce,


"Iya abubuwan da Farouk ya mallaka nake so na sani, idan kana da masaniya a kan wasu."


Shiru ya yi Sans yana nazari, kafin daga baya ya ce,


"Ehh to, na dai san akwai keke napep guda biyu da ake mishi haya da su. Sannan kuma ya zuba hannun jarinshi a Zamani Photography. Yana da Shop amma ba ta da girma sosai, ina ji ai kun san da wannan ma."


Dadyn Bobby ya share guntuwar ƙwallar da ke ƙoƙarin fito mishi, don kar Sans ya gane. Ya ce,


"Ehh tabbas na san da wannan. So nake duk wani abu da ya mallaka a siyarshi, sadaƙattul-jariyah nake so a mishi, ladar ta ci gaba da isar mishi har a kushewarshi. Tunda dai daga ni har Mamin tashi ba mu da gadonshi."


Kuka ya kufce ma Dadyn Bobby, ba tare da ya so hakan ba.


Duk da mamakin da Sans ke yawaita yi a duk sadda zai ji Dadyn ya yi makamanciyar maganar nan, hakan bai sa shi yin tambaya ba. Kewar abokinshi kawai ta ishe shi.


"Su keke napep da wurin mai photography ɗin, duka zan bar komai a hannunka. Sai ka san yadda za a yi kuɗin su fito. Ni kuma zan je wurin mai shop ɗin, zan ƙoƙarta siyen duk abubuwan da suke cikinta. Idan an tattara kuɗin duka, za a gina masallaci koda ba mai girma sosai ba. A zuba carpets da butoci, sannan zan ƙara da kuɗina a gina rijiya. Allah ya jaddada rahama ga Umar Farouk."


Ya gaggauta miƙewa ya bar wurin, gudun kar kukan nasa ya yi ƙarfi sosai, hankalin mutanen da ke wurin ya karkata gare shi.


Shi kanshi Sans kukan yake iya ƙarfinsa. Wannan rashin shi ne na huɗu da aka masa a rayuwarsa. Abbunshi, Aunty, ƙanwarshi Yamairah, sai kuma ga babban abokinshi, mutumin da ya kyautata mishi, ya ba shi dukkanin abin da yai rashi a baya. Ya ba shi farin ciki tamkar dama can ya san shi. Shi ma ya tafi ya bar shi. Tafiya ta har abada. Kuka ya kuma fasawa, haɗe da haɗa kanshi da guiwa, yana shessheƙa. Wani bawan Allah cikin ƴan zaman gaisuwar ne ya matso inda Sans ɗin yake, ya ce,


"Yaro ina kula da kai, tun daga ranar da Farouk ya rasu kodayaushe cikin kuka da damuwa kake. Wa ya faɗa maka kukanka zai taɓa dawowa da shi duniya? Ko ka manta cewa manzon Allah SAW ma ya yi wafati? Saboda haka dole kowa ma zai tafi. Allah maɗaukakin sarki ya ce dukkan mai rai mamaci ne. Don haka shi ma Farouk ba gaggawar tafiya ya yi ba, lokacinsa ne ya yi. Ka daina wannan kukan, ka fitar da duk wata damuwa daga cikin zuciyarka. Ka saka a ranka cewa tafiyar Farouk lokacinsa ne ya yi, duk daren daɗewa kai ma za ka bi shi. Kar ka ma ja ma kanka wannan damuwar ta jaza maka wani ciwon."


Kansa ya É—aga Sans, ya shanye kukansa, yana faÉ—in,


"Na gode ƙwarai baba."


***


Zaune take a bisa sofa, tana son ta kira Jiddah sai dai kuma ba ta so ta takura mata, tunda ba haka suka yi da ita ba.


Jin ƙarar wayarta ne ya sa ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta duba mai kiran. Sunan Jiddah ta gani ɓaro-ɓaro, hakan ya sa ta jin farin ciki ya lulluɓe zuciyarta. Tana fatan jin alkhairi a tattare da Jiddah.


Har wayar ta tsinke ma ba ta sani ba. Farin ciki kawai take. Kafin Jiddah ta sake kiranta ita ta kira. Bugu É—aya Jiddah ta É—auka.


"Amarya kin sha ƙamshi."


Kawai ta jiyo Jiddah ta faÉ—a, tana faÉ—aÉ—a dariyarta.


"Bana son iskanci fa Jiddah. Ai ke ce amaryar."


"Malama kar ki kawo min raini. Na tabbata kina nan kina jin daÉ—in sunan da na kira ki da shi."


Maryama ta murmusa, ta ce,


"Ashe ma jin daÉ—i. Ni dai ba wannan ba. Ki faÉ—a min abin da nake son ji daga gare ki."


"Hmm! Kuma har ki wani ce bakya so don na kira ki amarya? Na tabbata kin ji daÉ—i sosai."


"Jiddah."


Maryama ta faÉ—a.


Sosai Jiddah ta gano nufin Maryama. Ba ta cika son tsawaita abu ba. Komai ta fi son jin shi direct.


"Mun yi magana da Mama. Na mata bayanin komai dallah-dallah, tun daga farko har ƙarshe. Kuma Alhamdulillah! Ta fahimci komai, ta kuma tausaya miki.


So, a yanzu dai ta ba ni lambar wani Class mate ɗinsu, wanda yake ƙanin mahaifin Annur ne. Sunanshi Uncle Marwan. Ta tabbatar min cewa yana da kirki sosai, kuma zai fahimce mu. Ta ma ce min za ta kira ta mishi bayanin za mu zo mu same shi, sannan mu ɗin ma mu sake kiranshi. Idan mun je kar mu ɓoye masa komai, tun daga farko har ƙarshe mu sanar masa, da izinin Allah zai ba mu dukkanin taimako, zai kuma goyi bayanmu ɗari bisa ɗari."


Kamar ta yi ihun murna haka ta ji Maryama.


"I don't even know what to say. Na matuƙar jin daɗin wannan zance. Yanzu ya kenan?"


"Zan kira shi yanzu, mu ji inda yake. Sai ki gaggauta shiryawa, saboda ko Office ta kama mu same shi sai mu same shi É—in. Mami ta ce min wai a State Inland Revenue yake aiki."


"To shi kenan Jiddah. Kin yi ƙoƙari sosai wallahi. Allah kaɗai ya san ladar da zai ba ki. Bari in je in sanar da Mama, sannan in hau shiri. Ina ji akwai mota ma ajje, da ita kawai zan zo."


Jiddah ta ce,


"To shi kenan. Sai kin zo É—in."


Suka katse wayoyin.


Tsalle ta buga Maryama bayan ta haye bisa gado. Ba komai ya mata daÉ—i ba illa jin da ta yi cewa mutumin kirki ne Kawu Marwan É—in, kuma lallai zai fahimce su.


Fita ta yi zuwa falo. Mama ba ta ciki, hakan ya sa ta nufi ɗakinta. A nan ta same ta tana duba wata takardar addua. Bayan ta yi sallama ta zauna a ƙasa, har sai da Mama ta gama ta ninke takardar adduar, ta miyar a cikin side drawer.


"Miss complain. Akwai magana a bakinki, na ga alama. Mene kuma?"


Bayan Maryama ta sunkuyar da kanta ƙasa. Ta ce,


"Mama yanzu muka gama waya da Jiddah. Ta ce min wai sun yi magana da Maminsu, har ma ta ba ta lambar wani kawun Annur. To dai wai za mu same shi, mu mishi bayanin komai. Yanzu."


Ajiyar zuciya ta sauke Mama. Ta ce,


"To shi kenan. Don Allah a kula sosai Maryam. Allah ya taimaka ya sa abun ya zo da sauki."


"Ameen Mama. Zan je in shirya."


Ta miƙe tsaye, ta fara taku har zuwa ɗakinta.


Cikin lokacin da bai wuce minti talatin ba ta gama shirinta tsaf. Jallabiya ce ta saka baƙa, mai adon silver. Ba wata kwalliya ta yi ba, powder kawai ta shafa da lip gloss, sannan ta ɗauki silver hand bag ɗinta, ta ɗauki wayarta ta fito. Sadda ta fito Mama na falo. Sallama ta mata, ta umurce ta da ta shiga ɗaki ta ɗauki dubu ɗaya ta ƙara mai a mota, sannan ta ɗauki mukullin mota, ta mata fatar alkhairi ta tafi.


Kai tsaye gidan su Jiddah ta nufa. Ta same ta ita ɗin ma ta shirya, kamar haɗin baki ta saka baƙar jallabiya, amma ita baƙi ne zalla har adonta.


Gaisawa ta yi da Mamin Jiddah. Bayan nan ta musu kyakkyawar addua, sannan suka tafi.


Dayake ya ce musu bai je Office ba yana gida, address ɗin shi da ya turo ma Jiddah ta text message suka bi, babu wahala sai ga su a cikin GRA, road K. House No. 16 ne gidan nashi, hakan ya sa suka dakata a nan, haɗe da yin horn. Babu ɓata lokaci mai gadi ya wage musu gate, kamar yadda kawu Marwan ɗin ya ce da Jiddah, idan sun iso kawai su zarto har cikin gidan.


Parking space suka dosa, motoci ne manya-manya a girke, wanda za su kai kimanin guda biyar, sai wani babban bike daga gefe.


Junansu suka kalla a lokacin da suka fito daga motar, ba su san inda za su dosa ba, saboda girman gidan. Jiddah ce ta koma wurin mai gadi ta tambaye shi ta inda za su bi su shiga gidan. Ya gwada musu ƙofar gaba, wadda za su fara cin karo da babban falon mai gidan. Sai kuma ya musu kwatancen ƙofar baya, ita kuma ita ce za ta sada su da ainahin inda iyalin gidan suke. Sai su zaɓi ta inda za su bi.


Maryama ce ta ce mafi a'ala dai su fara shiga inda iyalinshi, su gaisa sannan a musu iso zuwa ga kawu Marwan É—in. Abin da suka yi kenan. Sun ci karo da babban tsakar gida, inda masu aiki ne jere rinkis, kowa na aikin gabanta.


Bayan sun yi sallama Jiddah ta ce,


"Don Allah ina masu gidan?"


Wani ɗaki ɗaya daga cikin masu aikin ta gwada musu. Nan ɗin suka nufa kuwa, sai ga su a wani hamshaƙin falo, wanda ya ni'imtu sosai da kayan more rayuwa. Bene ne daga can gefenshi, da alama ta nan ake bi idan za a shiga bedroom.







Babu kowa a falon, sai suka rasa ma yadda za su yi. Tunani suke, kar ma a je mai gidan ta wulaƙanta su. Saboda wannan tarin ni'ima da take cikinta, ba kowacce mace ce za ta iya tarbar mutane yadda ya kamata ba.


Zama suka yi bisa 2 seater, suna zaman jiran tsammani.


Wata yarinya ce suka ga ta sauko daga bisa benen, ƴar kimanin shekara biyu. Sanye take da ƴar kanti pink, gashinta an gyara shi da ƙananan ribbons su ma pink.


Har rige rigen tambayarta inda mamanta take suke, up stairs kawai ta gwada musu da hannu.


"Ki kira ta kin ji. Ki ce wai baƙi ne suka zo."


"She's sleeping."


Yarinyar ta faÉ—a, cikin gwarancin rashin iya magana.


Jiddah ta taɓe baki. Haushi ma yarinyar ta ba ta. Da alama irin yaran nan ne da ake ɓatawa da kilbibi ba a musu Hausa.


"Ok. Where's your father?"


Maryama ta mata wannan tambayar.


Kwakkwaɓe baki ta yi yarinyar kamar za ta yi kuka. Ita a dole sun dame ta da tambaya. Tafiyarta ta yi zuwa sama, ba tare da ta sake ce musu komai ba.


Tsoki suka saki a tare. Jiddah ta ce,


"Maryam tashi mu nufi part É—in mai gidan, tunda dai ya san da zuwanmu."


Suka miƙe, haɗe da ficewa daga part ɗin ma baki ɗaya. Ta ƙofar gaba da mai gadin ya fara gwada musu suka nufa. Sai da suka yi knocking ya ba su izinin shiga, sannan suka cire takalmansu, suka nufi cikin falon.


Ai ƙawatuwar da ɗakin

Please Login or Register in order to submit comment