You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ku duka, babu wanda ya fi ƙarfin faɗawa a irin halin da Sans ya faɗa, domin kuwa babu wanda ya fi ƙarfin ƙaddara. Addua dai ce takobinmu, ita za mu riƙa, muna fatar Allah ya tsarkake mana zukatanmu, mu kasance masu kyautata rayuwarmu, har sadda mutuwarmu za ta zo ta ɗauke mu.*


*Daga nan kuma sai ku taya ni wangale baki, na jeren da za a je gidan Marnoor. Abun fa da gaske ne, biki sai daɗa kusantowa yake. Abun ya zo, inji mai tsoron wanka.😁🤣*


*Me za ku ce game da wannan surutu da Hammad ya yi? Shin ya kyauta ko kuma bai kyauta ba? Akwai fa ƴan bayan Hammad, masu yin ƙani da shi, wanda na san kai tsaye za su ce ai Hammad ya musu daidai😀. Yaro mai surutu fa haka yake. Akwai sadda yake yin mai maana, kamar sadda ya kira kawu Imrana. Akwai kuma sadda yake yin mara maana, wanda shi ne ma ya fi rinjaya. Ga shi dai Hammad ya kwafsa, ya kwaɗawa Dr. Islam kira ya sanar mata auren Maryama. Ko ya abun zai kaya? Za ta zo ko ba za ta zo ba? Akwai fa cakwakiya.😊😅*


*Nagode ƙwarai masu bibiyar wannan labarin. Har ma wasu lokutan nakan rasa abun faɗe, tsabar faranta min rai da masoyana suke yi. Wasu groups ɗin da bana ciki ma, ina jin labarin yadda suke ƙaunar ANS. Akwai lokutan da ake min Copy and paste na yadda ake hirar ANS. Ban san da bakin da zan gode muku ba. Sai dai addua da fatar alkhairi. Allahu ya bar zumunci, ya saka muku da dukkanin alkhairanSa. I love y'all, fisabilillah.*


Pinky durling💞
RAZ 2
[9/14, 5:33 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_




Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*




6⃣3⃣


Wattpad: PrincessAmrah


***


Washe gari tun da safe misalin ƙarfe tara na safe ƴan jere suka tafi domin aiwatar da aikinsu. Maryama kuma dama mukullin ɗaya motarsu a hannunta yake. Tare da Hammad suka tafi, bayan ta shiga sun gaisa da Annur, ta ba shi duk abin da ya dace na kalacinsa.


Kai tsaye gidan su Jiddah suka dosa. Daga nan suka wuce wurin Salon. Ba su wani tarar da layi ba. Mutum baiyu ne a gabansu. Hakan ya sa misalin biyu na rana an gama musu duka.


Daga nan suka wuce gidan su Saudat. Sun samu ta shirya su kawai take jira, da yake sai da Jiddah ta kira ta ce ta zama cikin shiri, sun kusa zuwa su É—auke ta. Sai da suka yi sallah, har abinci Saudat ta zubo musu sannan suka bar gidan, suka nufi kakkai ma wanda ba su kai ma kati ba. Har kusan biyar na yamma sannan suka gama. Bayan sun kai Saudat gida sannaam suka wuce kasuwa domin yin siyayyar da ba su kammala yi ba, ta Get Together.


*


Tun sadda Kawu Imrana ya kira shi cewa ƴan jeren sun isa gidan, yake tunanin yadda zai yi da su ta ɓangaren abinci. Ga shi kuma ba ya son iyalinshi su san da zancen auren ko kaɗan, kamar yadda ya yi ma kawu Imrana alƙawari. Hakan ya sa kawai ya yanke hukuncin zuwa Restaurant ya musu odar abincin komai yawan shi.


Falon nata ya shigo bai same ta ba, hakan ya sa ya gyaÉ—a kanshi haÉ—e da hayewa sama. Ya rasa ko wace irin mace ce ita É—in. Sam ba ta son mutane. Ko a falonta ba ta cika zama ba bare cikin masu aiki. A ranshi yake cewa dama haka Shuwa suke, ko kuwa dai ita É—in ce haka?


A kan Sofa ya same ta riƙe da wayarta, ta miyar da dukkanin hankalinta ga wayar. Har ya ƙariso ya zauna a gabanta ba ta san ya iso ba, sai da ya yi gyaran murya sannan.


Da murmushi take kallonshi, bayan ta saka wayar a duhu.


Murmushin ya sakar mata shi ma, ya ce,


"Wane irin littafi kuma ake karantawa yau?"


Cike da soyayya take kallonshi, ta ce,


"Har ma ka san littafi nake karantawa kenan."


Hannunta ya kama ya riƙe, ya ce,


"Dole in sani ai, saboda aikinki ne. Ya sunanshi, faɗa min? Wata ƙila idan sunanshi ya min ma kin ga kawai sai ki karanta min."


Sai da ta É—an yi far da ido kafin ta ce,


"Sunanshi WANDA YA DAKA RAWAR WANI...Labari ne a kan wata yarinya Farha, wacce ta shiga gararin rayuwa, ta dalilin ƙawa da kuma namiji. A ƙarshe ta faɗa harkar karuwanci, inda tun a duniya ta girbi abin da ta shuka. Marubuciya Maimuna Bashir Miemie Queen ce ta rubuta shi."


GyaÉ—a kansa ya yi, ya ce,


"Allah sarki! Har na ji ta ba ni tausayi. Yo wannan rayuwar ta yanzu ka ɗauke ta da sauƙi ma ya ka ƙare bare kuma ka zafafa ta? Allah dai ya shige mana gaba, ya yi mana jagoranci a dukkanin lamurranmu."


"Ameen."


Ta faÉ—a tana kallonshi.


Yarinyar da ke kwance bisa gado tana barci ya kalla, ya bi a hankali ya cire mata takalmin ƙafarta, ya ce,


"Wani abu sai Shereefa. Wato in dai ba barci ta yi ba ba a taɓa raba ta da takalma."


"Kai ma dai ka faÉ—a. Ai ni kam ban san kalar Yesmeen ba. Sosai ta gado Yaya Salman. Aunty ta sha ba mu labarin yadda ya yi yana yaro. Ko kaÉ—an ba ya yarda a raba shi da takalma. To ga mai gadon shi nan ya samu ai."


Miƙewa ya yi tsaye, ya ce,


"Ni zan fita, wata ƙila daga Office akwai inda zan wuce. Ban ma dai yi niyyar zuwa Office ɗin ba gaskiya, saboda na tashi jikin ba daɗi. Wani dalili ne mai girma zai fidda ni."


Miƙewa ta yi ita ɗin ma, suka ci gaba da taku tare, har suka sauko daga bisa bene. A falo ta mishi sallama da fatar alkhairi, sannan ya fita, ita kuma ta nufi ɗakinta.


*


Wuraren ƙarfe shida na yamma ƴan jere suka koma. Fuskokinsu a sake, dangin Mama ne da kuma na Abba, da yake kansu a haɗe yake, akwai kyakkyawar alaƙa a tsakaninsu.


Da faraa Mama ta tarbe su, ta ce,


"Sannunku da dawowa. Har an gama kenan. Sannu, sannunku da aiki."


Amsa mata suka yi, wata babbar mace daga cikinsu, wacce ta kasance Yaya ce ga Mama, ta ce,


"Gaskiya ba laifi Maryama ta yi sa'ar dangin miji. Domin kuwa wani mutumi yadda ya rinƙa hidima da mu abun sai godiya. Akwai kirki sosai wallahi. Gaskiya ki ce da Alhaji Balarabe ya jaddada mana godiya a gare su, domin kuwa ba kowa ba ne zai iya yin wannan hidimar."


Mama baki a sake ta ce,


"Aikam zan faÉ—a masa insha Allahu."


Daga nan suka fara haramar tafiya. Da zummar wasu idan suka zo gobe sun zo kenan har sai bayan biki.


A gajiye Maryama ta dawo gida ita da Hammad. Sai da ta fara zuwa inda Annur ta É—an jima kafin ta dawo É—akinta, ta watsa ruwa sannan ta saka kayan barci, a daidai sadda ake kiran sallar magrib. Zumbuleliyar hijabinta ta zumbula, sannan ta kabbara sallah.


*


Tun da sassafe mai lalle ta iso. Ƙarfe goma na safe ne dama aka saka za a yi sa lalle. Daidai lokacin kuwa gidan ya fara ɗaukar harama. Ƴan mata duk sun zo domin gabatar da sa lalle. Wanda shi kanshi ɗin akwai wani ɗan guntun casu da za a yi bayan laasar, a lokacin an gama yi ma kowa lallensa, tunda ita amarya dama sai da dare za a mata, sadda duk aka warwatse. Jiddah da Saudat kuwa gidan suka dawo da zama daga yau, saboda za su fi jin daɗin hidimar, da kuma aiwatar da komai a kan lokaci.


Da yamma kuwa aka ƙawata gidan da simple decoration, kalar Pink and gold. Wurin ya yi kyau sosai, aka jera kujeru, da kuma gefe guda da aka ajje royal chair, wacce amarya za ta zauna a kai.


Ƴan RAZ NOVELLA da kansu suka ɗauko Ado Gwanja, wanda musamman saboda ranar yau zai zo ya nishaɗantar da su. Har Gwanja ya iso harabar wurin amarya da ƙawayenta ba su fito ba. Bai damu da hakan ba, kawai ya fara sakin kiɗa. Sautin na tashi tamkar an tsakuri ƴan Nagarta Fans Group ne. Ummu Aysher ba ta ko ƙarisa naɗin ɗankwalinta ba ta fito, gyale a hannunta tun daga bakin ƙofa take rawa, har ƙasa-ƙasa take yi. Mienerh ce a bayanta, sun haƙiƙance tsakaninsu da Allah rawa suke, har suka iso harabar da Gwanja ɗin yake. Aikam yana ganinsu ya canza salo, aka sako wakar A sha rawa rawa. Kafin ka ce kobo fili ya cike da ƴan mata, ƴan group group sai cashewa ake, har lokacin da Jiddah da Saudat suka fito da amarya. Aunty Maijiddah Musa ce biye da su a baya, sai famar sakin murmushi take, tana ɗan taka rawar dattako, irin ta manyan mutane.


Amarya ta sha gayunta, cikin dressing kalar golden.





Da haka dai Ado Gwanja ya nishaɗantar da su, ƙarfe shida da rabi na yamma aka gama. Cike da nishaɗi aka warwatse.


*


Da dare mai lalle ta hau zana ma amarya nata lallen, inda Maryama ta ce ita kam ba ta son mai yawa, ta fi son kaÉ—an irin wanda ake yayi yanzu.












Sai kusan sha É—aya na dare sanann suka sallami mai lallen ta tafi.


*


Ranar alhamis da safe aka fara shirin yin walima, inda aka gayyaci Malama Zulaihat Rano da aminiyarta Khadija S Mohd suka gabatar da waazi mai ratsa zukata. Sosai suka jawo hankalin amarya a kan ladabi da biyayya ga mijinta.


Amarya ta sha kyau sosai, inda ta sha bakin dressing abunta.




















Sosai aka ci aka sha a wurin wa'azin. Ba wai amarya kaɗai ba, har ma da sauran mutane sai da suka girgiza da yadda malaman suka rinƙa tsoratar da amarya daga zaluntar mijinta. Suke hasasho mata rahama matuƙar ta kyautata ma mijinta. Sai sha biyu na rana sannan aka gama wa'azin, saboda da yamma kuma za a yi Get Together a gidan Kawu Imrana.


Wanka ta yi ta saka wata ƴar ƙaramar riga iya guiwa. Rijif! Ta faɗa bisa gado, tana faɗin,


"Kuma wai fisabilillahi anjima wani abun za a sake yi. Ni wallahi in da za ku bi ta tawa da an fasa. Na gaji sosai."


Harararta Jiddah da Saudat suka yi, Jiddah ta É—ika mata dukan wasa, ta ce,


"Lallai ma yarinyar nan kin raina mutane. Ai in Allah ya yarda Party an yi shi an gama. Gwara ma ki saka a ranki cewa babu fashi, da izinin Allah. Bari ma ki ga in kira matar nan mai make up, kar ta ɓata mana lokaci, shi ya sa na so kar ta tafi ɗazu amma ta nace wai da wuri za ta dawo."


Ta latsa kiran mai kwalliyar. Bugu biyu kuwa ta É—auka, Jiddah ta ce,


"Dama ce miki zan yi don Allah ki taimaka mana ki zo da wuri. Wallahi ba ma so a yi dare ne. Get together ne fa har da iyaye duk za su je. So muke amarya ta shirya da wuri, in ya so duk wacce ba ta shirya ba sai a yi babu ita."


Mai make up É—in ta ce,


"To insha Allahu da an yi sallar azahar zan zo. Kar ki ji komai."


"To shi kenan, sai kin zo."


Ta tsinke wayar tana faÉ—in


"Oya tashi ki yi alwallah, yadda idan lokacin sallah ya yi yi kawai za ki yi. Ni fa kin san ni da uzurta mutum, don ba na son ɓata lokaci a komai nawa."


Tashi ta yi Maryama, ta ce,


"To Aunty Masifa."


Ta nufi ban-É—aki.


"Na dai ji koma me za ki ce da ni ki ce. Ni ma wankan zan yi yanzu. Bara na je na fara faɗa ma dattawan can, su taimaka su shirya da wuri su ma. Don na yi waya da Yaya Deedah, ya ce ƙarfe biyar daidai za su zo da motocin kwasar mutane."


Saudat da ta miƙe kan gado ta ce,


"Ai kin san su manyan mutane ba su cika ɓata lokaci da yawa ba. Matsalar dai dama daga ƙawaye ne. Amma da yake mun jaddada musu cewa da wuri ne na san insha Allahu za su je da wuri ɗin."


"To Allah ya sa."


Sannan ta nufi fita zuwa É—akin Mama.


Maryama na fitowa wayarta na fara ruri. Koda ta duba ta ga sunan Dr. Islam ne. Da hanzari ta goge jiƙar da ke a hannunta sannan ta ɗaga kiran da sallama a bakinta.


"Habawa Maryana. Ai wallahi kin ba ni mamaki."


Furucin da ta ji Dr. Islam ta yi kenan, ba tare da ko saallamar ta amsa ba.


"A yi haƙuri Aunty Islam, duk da dai ban san me na yi ba amma dai na ɗauki laifina."


"Hmm! Na ji to. Ya shirye-shirye?"


Cikin faɗuwar gaba Maryama ta dafe ƙirjinta, da rawar murya ta ce,


"Na me fa?"


GyaÉ—a kanta ta yi Dr. Islam tamkar tana a gaban Maryama É—in ne. Ta ce,


"Aure za ki yi Maryam amma ko ki sanar mana? Maryam amana ba ta ce haka ba. Tamkar ƙanwata ta jini haka na ɗauke ki. Amma da alama ke sam ba ki ɗauken tamkar yayarki ba."


Sosai bakin Maryama ya ɗinke. Ƙoƙarin tattaro magana take amma ta kasa. Sai famar muzurai take kamar wacce ta yi ƙarya aka turke ta.


"Dole za ki yi shiru ai. To duk da dai ba a gayyace mu ba muna nan zuwa anjima ni da Momy da yaronki. Za mu zo matsayin gayyar nagayyaro."


"Uhm...Aunty Islam kina ji na? Wallahi ba haka ba ne. Komai da komai a cikin ƙurewar lokaci ya kasance. To ni kuma ba na so na tayar muku da zaune tsaye. Wannan dalilin ne ya sa ban sanar muku ba. Don Allah a gafarce ni, insha Allahu ba zan kuma ba."


Dr. Islam ta ce,


"Uhmmm! Kamar da gaske, sai wani marairaicewa take. To na ji. Sai ki turo min address na inda za a yi. Kuma ki ce da angon ya tanadi kalaman da zai kare ki a wurina idan na zo. Ina jiran text na address É—in yanzu."


Ba ta jira Maryama ta sake faÉ—in komai ba ta tsinke kiran.


Da ƙyar ta haɗiyi yawu Maryama. 'To a ina suka ji?' Tambayar da ta ma kanta kenan. Hammad ya faɗo mata a rai. A zahiri ta furta,


"Tabbas idan ba wurin Hammad ba babu inda za ta ji. Amma wannan yaro ya iya tsiya. Har sai da na ce da shi ya kame bakinsa fa."


Saudat ta ce,


"Maganinki kenan ai. Nikam Hammad ya min daidai. Ban ga dalilin da zai sa ki ƙi faɗa mata ba ai, duk da ban santa ba."


Ta sake gyara kwanciyarta.


A daidai nan Jiddah ta dawo. Tun daga bakin ƙofa take faɗin,


"To wallahi manya dai sun ce daga gare su babu matsala. Tunda dai already sun yi wankansu tun na waazi É—azu. Matsalar daga gare mu take. Na ce da su insha Allahu babu damuwa. Komai a kan lokaci za a yi shi. Tunda dai har wurin can an kimtsa komai."


"Wurin wa kika ji an kimtsa komai?"


Maryama ta faɗa tana shimfiɗa dardumar sallah a ƙasa.


"Yaya Deedah ne É—azu da yake jaddada min cewa da wuri za a zo kwasar mutane ya ce an gama decoration, kuma ya yi kyau sosai."


Cikin taɓe baki Maryama ta ce,


"Ni dama da shi kika daidaita kawai."


Harararta Jiddah ta yi.


"Yar rainin hankali. Sai aka ce miki rasa masoyi na yi da za ki min Æ´an kwashe-kwashe?"


"Ba wani kwashe-kwashe ai. Tun sadda kuna waya É—azu ai na fara fahimtar wani abu. Wannan wasa da dariya haka."


Saudat ce ta jeho wannan maganar. Ta miƙe zaune.


Bayyanannen tsaki Jiddah ta yi, ta ce,


"Duk ba ni da lokacinku."


Ta shiga toilet abun ta.


*


Bayan an gama shirya Maryama, sai da ta fara shiga É—akin Annur, a lokacin duk an gama kwashe mutane, daga Jiddah sai Saudat ne kawai a gidan, sai mai gadi kawai. Har Mama ma danginta sun ce ba za a barta a gida ba. A gabanta za a yi komai.


Rusunawa ta yi ƙasa tana fuskantarshi, har ƙamshin turarenta na dakar hancinsa.


Cikin wani irin salo yake sakin tattausan murmushi, mai cike da soyayya da ƙauna. Ya haɗe tafukan hannayensa a wuri guda, yana fuskantarta ido cikin ido. Ji ta yi baki ɗaya ya gama tsuma ta da ƙaunarsa. A haka da ba yi da hankali yake mata irin wannan kallon na soyayya, to ina ga ya samu lafiya?


"Yah Noor za mu tafi, wurin event na bikinmu. Will you say something, please?"


Shiru ya mata, amma har yanzu bai daina sakin murmushi ba.


"Say something Yah Noor, please. Yau na É—aya daga cikin ranaku masu muhimmanci a rayuwarmu. Na so a ce kana a cikin hankalinka, ka halarci wannan rana. Sai dai kuma kash! Allah bai nufa ba, haka Ya tsara ma rayuwarka. Ka kwantar da hankalinka, Allah ba mantawa ya yi da kai ba, sannu a hankali za ka samu lafiya, za ka warke ka dawo da cikakken hankalinka."


Hannunta na dama da tun shigowarta yake kallonshi, ya kama ya riƙe. Daidai tafkeken zoben zinarin yatsarta ya kai hannunsa, a hankali ya zaro shi, ta ci gaba da binsa da kallo. Bayan ya fiddo, ya kawo shi kusa da idonshi yana binsa da kallo. Tamkar ya san zoben, haka ya ji. Wani irin sara ya ji kansa ya masa, a lokacin da yake kallon zoben. Kamar zai tuna wani abu game da shi, sai dai kuma ya kasa tunawa. Ɗan taunar leɓonsa na ƙasa ya yi, sannan a hankali ya miyar mata da zoben daga yatsar da ya fiddo shi, ya miyar mata, ya zauna kuwa daram.


"Time is going Yah Noor. Will you let me go?"


Bai san me zai faÉ—a mata ba, haka kawai ya samu kansa da É—aga mata kai, yana sakar mata tattausan murmushi, duk da cewa har yanzu bai daina jin kansa na sara masa ba.


Tashi ta yi da sauri ta tafi, tun daga nesa take faÉ—in,


"Am so sorry Babes. Kuna ta jirana ba? Ga ni na iso."


Fitowa suka yi Jiddah na riƙe da purse ɗin Maryama a hannunta. A harabar gida suka tarar da Deedah ya yi zaune a mota, yana jiransu. Sosai yake kallon Maryama, yana jin yadda wutar ƙaunarta ke daɗa kunnuwa a cikin zuciyarsa. Amma ya zai yi? Dole ya ƙoƙarta fitarwa ko ba ya so. Saboda ya sani, Maryama ba za ta taɓa zama ta shi ba.


Murmushi ya saki bayan ya fito daga motar.


"Amarya, you know what? Kin yi kyau sosai, lemmi snap you before we leave."


Ya hau É—aukarta hoto, da Iphone X É—insa. Sai da ya mata da yawa, sannan suka shisshiga motar, Jiddah na zaune a gaba sai Maryama da Saudat a baya.


Sadda suka isa gidan su Deedah, Maryama da Saudat ba su fita ba, sai da Jiddah ta je ta sanar cewa ga amarya nan ta iso. Ƙawaye wanda suka yi ashobe su fito, za a shigo da amaryar.


Sauya kiɗa aka yi, yayin da amarya ta fito daga motar, aka yi jeri kowacce ƙawa da partner ɗinta, amarya kuma na daga tsakiya, sai Hammad da Abdul-Ahad biye da ita a tsakiyar, saboda Hammad ya ce ba za a yi babu su ba.


Isowarsu harabar gidan, sautin ya ƙara tashi, yayin da mutane suka mimmiƙe tsaye, cike da farin ciki ana tattafawa.


Yadda aka tsara wurin kanshi abun kallo ne. Decoration ɗin wurin kalar yellow aka yi, an jera kujeru masu matuƙar kyau.





Har gaban kujerar amarya suka raka ta. Sai da ta zauna sannan masu hoto suka hau yi, masu video kuwa dama tun fitowarta daga mota suka fara.


Wuri ya yi wuri fa. Domin kuwa taron mutane maabota karatun Hausa Novels ne jere, wasu ma sai ka yi mamakin ta yadda aka yi suka ji. Laakari da yadda bikin ya zo, a gaggauce aka yi komai.


Hotuna ake sosai, uwar amarya ma ta taso aka musu, dangi da ƴan uwa har da ƙawaye, sai shan hotuna ake.


Da ƙyar MC ya roƙe su suka watse, sannan aka ci gaba da gudanar da partyn.


An yi nisa sosai ne MC ya ce,


"Ga Princess Amrah nan za ta fito, za ta rera mana tata waƙar da ta yi musamman saboda ango da amarya."


Nan fa aka hau tafawa. Ana jiran isowar Princess É—in.


Cikin taku mai nutsuwa ta iso, tana sanye da wata doguwar riga kalar pink, wacce ke ja har ƙasa. Ta sha ɗaurin ɗankwalinta mai matuƙar kyau, da make up na ji da gani.


Ita ce a gaba, sai ƴan RAZ NOVELLA bayanta sun jera layi. A hankali sauti ya rinƙa tashi, nan fa suka hau takawa cikin rawa mai kyau.


Waƙar ta fara rerowa, tana faɗin,


"Biki wan shagali,
Eh biki wan shagali, ake a yau gidajen girma, Maryama da Annur masoyan asali.


Farko da sunan Rabbi ubangiji maqagin halitta,
Shi ne ya bani damar da nake zubo dukkan hajata,
DaÉ—o dubun salati ga Annabin gaban duk halitta,
Da alihi sahabbansa a kullum suna yin ƙyalli.


Wannan waƙar aure ce nake a yau ba ƙyashi,
Ga wanga ango da amarya suna ta yin ƙamshi,
A duk ta inda na gitta wannan bikin ina yin son shi,
Domin ko ƙaunar junansu suke ta yi tun asali.


Ga dandazon mutanen arziƙi fa duk sun zozzo,
Farko Nagarta Writers na hanga sun zo,
Sai Raz Novella a gefe murna suke har da ƙwazo,
Nagarta Writers Fans group ƙaunarsu yau sun furzo,
Ga wannan aure rawa suke ta yi ga ƙyalli.


MH fans na gaishe ku a wannan waƙar tawa,
Queen group of Novels ku marmatso ku yi rawa,
Ga Lubbatu's Crew ma na gansu suna takawa,
House of Novels ma a gefe murna suke ba misali.


Pherty Novels gaishe ku nake a yau kun ji ni,
Asisi Fans Club ma na gaida ku fa ba bimbini,
Zauren Sadeeya Novels ku Marmatso nan ga ni,
Ƙarshe na sa ƴan Meesha group novels kun hau tubali.


Wattpadians ga taku fa gaisuwar ku yo amsawa,
Dukkan mutuncin nan da kuke yi min ina jinjinawa,
Comments da votes ɗin naku ku ƙara yo ninkawa,
Masoyiyarku fa Amrah Princess ce mai ƙyalli.


Sauran groups da dukka nake kuna cikin ruhina,
Na san kuna son auren Annur da Maryama ku nuna,
Ni ma ina ƙaunarku da gaske cikin ƙalbina,
Maryam Indabawa group Chart ƙaunarku nake yi tun asali."


Tana kaiwa nan suka rinƙa rawa sosai, har ƙasa-ƙasa suke duƙewa. Amarya Maryama da ƙawayenta suka hau yin liƙi, saboda sun ji daɗin yadda Princess ta waƙe amarya da ango.


Duk da cewa Dr. Islam ta yi mamakin sunan angon da ta ji an faÉ—a, sai ba ta kawo komai a ranta ba, aka ci gaba da cashewa.


***


*Ban yi tunanin shafin zai kai har tsayin haka ba. Sai ga shi kuwa ya kai.*


*Akwai muhimmin abu da na warware a cikinsa. Wa zai canka?*


*Well...😀 kun ga mun gangara ɓangaren nishaɗi ko? Kar dai ku shagala, akwai cakwakiya da dama nan gaba. Tahm.*




Thanks all.


Pinky durling💞
RAZ 2
[9/15, 8:06 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taɓa zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_




Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*




6⃣4⃣


Wattpad: PrincessAmrah


***


Sai dare sannan aka tashi daga Partyn. Sosai duk wanda ya halarci wurin ya yi enjoying ɗinsa, barinma ƙawayen amarya da suka sha casu wanda suka jima ba su yi irinsa ba.


Daga nan kai tsaye part É—in amaryar Kawu Imrana suka nufa. Ba wata babbar mace ba ce sosai, duka babban É—anta shekararsa goma. Hakan ya sa suke shiri sosai da Maryama, ko gidan ta zo ma a É—akinta take kwana.


A falo suka zauna ita da wasu ƙawayenta da za su bi mota guda. Matar ta fito daga kitchen hannunta ɗauke da food flask ta ce,


"Sannun ku. Kun gaji ba? Ai dole ne gajiya. Wannan uwar rawa da kuka sha. Ita kanta amaryar rawar da ta yi ai na sha mamaki."


Ta ƙarisa da ajje food flask ɗin a bisa centre table.


"Aunty Ruky ni kaina ban san yadda aka yi na dage rawar nan ba. Ni da rawa ma ba ta dame ni ba."


Taɓe baki ta yi Aunty Ruky. Ta ce,


"Ke gwara da kika yi. Komai na duniyar nan fa lokaci gare shi. Idan ba ki yi ba yanzu akwai sadda da kuÉ—i

Please Login or Register in order to submit comment