You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɓaɓɓalla ki? In banda hauka da shashanci, daga haɗuwa da mahaukaci bisa godabe sai taimako? Ke ko san mutanen yanzun ga yanda suke abin tsoro? Haka ɗai muna zaman zamanmu ki jawo mana bala'i inda muke, sam! Ban lamunci wanga hauka ba. Kuma ki tahi daga wurin ga tun ban saɓa miki ba."


Sosai jikinta ya tsananta kyarma. Tana tsananin tsoronsa, amma duk da hakan bata jin zata iya tafiya ta bar shi a wurin ba tare da ta san inda zai nufa ba.


Suna cikin haka wayar yayan nata ta hau ƙara. Ɗauka ya yi suka gaisa da mai kiran nasa, sannan ya shaida masa cewa ya gaggauta dawowa kasuwa, an samu mai siyan dozen biyu na takalma.


Da murnarsa ya tsinke wayar. Yana jin daÉ—in cikin da zai yi a lokaci guda.


"GiÉ—e ki hankali. Zan tahi yanzu, amma walle ki tabbatar ke shiga gida, tahi ma tun yanzu ina kallonki."


Ta É—an samu sassauci a zuciyarta. Daurewa ta yi ta shiga gidan, ya tabbatar ta shiga sannan ya karya kwana, yana mai son dakatawa ya kori mahaukacin daga wurin, amma kuma yana ji kamar idan ya tsaya zai iya rasa cikin da tun É—azu yake so ya yi, amma kuma babu kasuwa.


A zaure ta tsaya tana leƙensa har sai da ta tabbatar ya ɓule, sannan ta fito tana masa murmushi.


This page is in your honour, Asea Bashir Aliyu (Asisi). Ina yinki irin sosai da sosai ɗin nan. Ina ƙaunarki fi sabilillah. Kin sani kuwa?




Ko ta wace hanya su Annur suke ga kaman zasu shagaltar da rayuwar Maryama? Shin zasu yi nasara kuwa? Miye dalilin da ya sa asirin ya gagara tasiri gare ta? Me kuka hasko a cikin wannan labarin da Fiddou ke ba ma likita?


Na gode ƙwarai masoyana. Ina son ku all fi sabilillah.


Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:48 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)


Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


3⃣3⃣


Bakin wani tsohon gini ta nufa da shi, ginin da alama babu mutane a cikinsa.


Da murmushi a fuskarta ta ce,


"Bara na kawo maka tabarma, ina zuwa."


Bai ce da ita komai ba, a tsaye yake yana binta da kallo, har sanda ta je gidansu ta dawo.


Wata tsohuwar tabarma ce duk ta gama yaƙunewa ta shimfiɗa masa. Bayan ta daidaita ta ta ce,


"Taho zauna ka huta giɗe. Dan da ganinka ka gaji ko tantama babu. Ka ga hwa yanda ƙahwarka ta tsatssage."


Bai musa mata ba ya zauna a bisa tabarma, ya dunƙule baki ɗaya jikinsa, sai faman kyarma yake.


Ganin kyarmar da yake ta tsananta ya sa hankalinta tashi, ta ce,


"GiÉ—e mi ya hwaru kuma?"


Bata tsaya jin komai daga gare shi ba ta kara hannunta a wuyansa. Zafi ta ji rau kamar garwashi. Ta kuma dafe masa kai, nan ma zafi ta ji sosai da sosai.


"GiÉ—e baka da lahiya walle. Yanzu ya zan yi da kai?"


Hawaye ne ta ji suna zarya a kumatunta. Shi kanshi mahaukacin ruwan hawaye ne ke kwarara a kumatunsa, wanda na azabar zazzaɓi ne kawai.


"Bari in ga ko ina samo ma magani."


Ta tashi da hanzari ta nufi gida.


A ɗakinta ta ci burki, ta hau bincikar lakokin madubinta a haukace, tamkar ciwon a jikinta yake. Da ƙyar ta samu ta gano katin paracetamol, wanda guda biyu tal ya rage a jiki. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta miƙe, ta fito daga ɗakin nata, ta nufi kitchen. Kofin roba ta ɗauko ta nufi randar ɗibar ruwa, ta ɗiba zata bar wurin ke nan ta ji muryar matar yayanta cikin masifa ta ce,


"Ke Fiddou halan ina zaki tai min da kohi?"


Jikinta na rawa ta rasa me zata faɗa, tana gudun tonuwar asirinta. Saboda sam matar yayan nata bata da kirki, abu kaɗan zata mata ta kai ta ƙara a wurin yayanta, shi kuma babu bincike kawai ya hau hukunta ta.


"Fiddou halan kin zama kurma ne?"


Ta sake jiyo muryar matar cikin ƙaraji.


"GiÉ—e ajje min kohi, dan na ga alamun baki da gaskiya ne."


Bata da wani zaɓin da ya wuce ta juye ruwan, sannan ta koma kitchen ta ajje ranta a ɓace. Tana ƙara tuna cikin halin da ta baro mahaukacin.


A saɓule ta fice daga gidan, tana jiyo muryar matar yayan tana ƙwala mata kira amma ta mata banza, dan bata jin zata iya ƙyale mahaukacin a cikin yanayin da ta baro shi.


Wani shago ne kusa da su ta nufa. A can ta roƙi mai shagon shi ya bata ruwan leda guda ɗaya, idan ta koma gida zata kawo masa. Bai ko musa mata ba ya ce ta buɗe fridge ɗin ta ɗauka. Ɗaukar kuwa ta yi, sannan ta kama hanyar kangon da ta kwantar da shi.


Karkarwar da ta samu yana yi ta fi waccen ta farkon, abun nashi ya ta'azzara sosai. Hankalinta ya matuƙar tashi, gabanta ya tsananta duka, tana masa magana amma tamkar ma ba da shi take ba.


"Giɗe yi haƙuri do Allah de, ka daure ka tashi ga magani nan na samo ma. Insha Allahu da ka sha kana samun sassauci."


Buɗe idonsa ya yi ya sauke a kanta. Yana son ya tashi amma ya kasa,nauyi yake jin jikinsa na masa ƙwarai da ainun.


Cikin tausayi ta kama shi ta tasar zaune, ta jinginar jikin bangon wurin, tana son ganin ya buɗe idonsa dangar-gar a fuskarta amma ya kasa, duk yanda ya buɗe su dole sai ya rufe, saboda zafin zazzaɓi.


Ɓallo masa maganin ta yi sannan ta miƙa masa, bai jira wata wata ba ya jefa bakinsa. Tana ƙoƙarin fasa ruwan ta bashi amma har ya taune maganin, shi ko ma ɗaci bai ji ba.


Sai da ya taune tas sannan ta ce masa,


"Inhi ga ruwa giÉ—e. Sha ko maganin na saurin yi maka aiki."


Karɓa ya yi ya kai bakinsa. A raunane take binsa da kallo. Tana tausayinsa sosai, tana mai tsananin jin shi a cikin zuciyarta.


Bayan kamar kwana uku mahaukacin ya ji sauƙi sosai daga zazzaɓin da yake. Saboda Fiddou ta kira wani malamin asibiti har cikin kangon da yake ya duba sa, ya tabbatar cewa wahala ce kawai, saboda yanayin nasa, da kuma yanda ƙafafuwansa suka koma, da alama ya yi tafiyar ƙasa mai matuƙar yawa, wadda ita ce ta galabaitar da shi, har ya tsinci kansa a wannan yanayin.


Tun bayan da ya ji sauƙi ta saka masa suna Modu, saboda sunan mahaifinta da ya rasu Muhammadou, tana matuƙar son mahaifin nata, shi ya sa ta masa takwara da mutumin da ta kamu da tsantsar ƙaunarsa cikin lokaci kaɗan.


A wannan kangon da yake ne wata rana aka ce za a ci gaba da ginin, saboda masu gidan suna so su dawo. Hakan ya sa ta mayar da shi can tsallaken titi, shago ne wanda babu kowa a cikinsa, jikin gidan su wata ƙawarta suka ce mata ya zauna, har sanda zasu nemi shagon.


Yayanta kuma ya gaji ya ƙyale ta, ganin bashi da yanda zai yi da ita, ta riga da ta sa ma ranta ƙaunar Modu.


Abinci ma ya amince mata tana kai ma Modu, sai dai matarsa ce marar kirkin, ba dai da izininta a kai abincin ba, sai idan Yayanta yana nan. Idan baya nan kuwa dole sai dai ita Fiddou É—in ta É—auki nata ta kai wa Modu.


***


"A ranar da wannan haɗarin ya hwaru, na jima ban kai masa abinci ba ne, hakan ya sa ya nemi ƙetare godabe da kai nai, zai tai inda nike. Kaji abin da ya hwaru likita. Ni kaina ban san Modu ba, ban san asali nai ba. Da hauka nai na ganshi. Sai dai abin da na sani game da shi kawai, yana yawaita kiran sunan wata, yana yawan yin kuka a lokuta da dama idan ya tuna ta."


Tana kai wa nan ta kalle shi, tana kallon yanda yanayin likitan ya sauya, kamar ba shi ba.


"Halan mina ne sunan wadda yake kira É—in ma? Sister ta hwaÉ—i min kuma na manta sunan."


"Sunanta Amrah. Ina jin a jikina wata ƙila mata tai ce. Dan in ba mata tai ta ba, ban ga dalilin da zai na hwaɗin sunanta ko yaushe ba."


Rubuta sunan ya yi a takarda, kafin ya ce,


"Yanzu dai tun da ya ji sauƙin wanga haɗari da ya hwaru, ina ganin kawai zan yi maku reffer daga wannan asibiti zuwa asibitin gwamnati. A can ne ad da ma'aikata ƙwarai da kuma kayan aiki masu tsada. Akwai abokina likitan zuciya, zan haɗa ku da shi, na san zai kula da giɗe ƙwarai, kamar yanda zan kula da shi."


Godiya ta masa sosai kafin ta miƙe a kan ƙafafuwanta, ta share guntuwar ƙwallarta, ta ce,


"Bari in tai likita, ina jiranka cikin É—aki nai."


Kai kawai ya É—aga mata, kafin ya ci gaba da rubutunsa, ita kuma ta kama hanyar fita.


***


A hanzarce ta lalubo wayarta da ke ruri a cikin jaka, tana gudun kar ta tsinke, saboda jimawar da ta yi tana ringing É—in, sannan kuma wannan shi ne kira na huÉ—u da aka mata, tana cikin napep bata É—aga ba.


A hankali ta murmusa ganin sunan wanda ya kira ta É—in, ta kara a kunnenta da faÉ—in,


"Wa ke magana?"


Cikin mamaki ya zaro ido kamar tana gabansa ne. Ya ce,


"Jiddah, ba dai baki da lambata ba."


"Mallam ka kira kana wani faÉ—in ba dai bani da lambarka ba, kai É—in waye da za a ce dole sai na yi lambarka a cikin wayata?"


Cikin sanyin murya Annur ya ce,


"Calm down, Annur ne."


Tana jin yanayin da ya yi maganar ta tabbatar akwai damuwa, akwai abin da yake so ne kamar yanda take buri.


"Ehen, go on."


Ta faÉ—a cikin muryar faÉ—a.


"Please Jiddah...please ki taimaka min. Dan Allah lambar ƙawarkin nan Maryama nake so ki turo min."


Janye wayar ta yi daga kunnenta tana bayyanannen murmushi, a ranta tana faÉ—in 'Tarkona ya kama kurciya.'


Samu ta yi ta mayar da wayar a kunnenta, ta ce,


"A kan me zan baka lambar Maryama? Me zaka mata?"


Cike da damuwa ya ce,


"Ina ƙaunarta ne, kamar yanda na faɗa miki a baya. Wallahi bana nufinta da komai face da alkhairi. Ba zan taɓa cutar da ita ba."


Ajiyar zuciya ta sauke ta ce,


"Zan turo maka lambar Maryama, amma fa sharaÉ—i guda, duk abin da ya faru da ita kai ne. Ka amince?"


Da sauri ya ce,


"Ehh, ehh wallahi na amince, na amince Jiddah."


"To, zan turo maka yanzu idan mun gama waya. Amma kar ka kira ta sai dare, saboda yanzu ban riga da na faÉ—a mata ba."


"Ok, thanks."


Ya furta cike da farin ciki.


Tana kashe wayar ta kashe recording É—in da ta yi, ta yi savinginsa a kan wayarta sannan ta lalubo lambar wayar Maryama ta kira ta.


"Hello Jiddah."


Maryama ta faÉ—a cikin sassanyar muryarta.


"Maryama hau watsapp yanzu zan turo miki wani audio."


"Ok."


Kawai ta faÉ—a haÉ—e da tsinke wayar ta buÉ—e datarta.


Tana saurare tana murmusawa. Sosai hakan ya mata daɗi, dan su a tunaninsu ko haƙarsu ce zata cimma ruwa. Basu san cewa wani mummunan ƙudiri ne a zuciyar Annur ba. Duk da yana son Maryama, yana ƙaunarta har cikin zuciyarsa, baya jin ko kaɗan zai juri fallasar asirinsa. Zai haƙura da ita, ko da hakan yana nufin ƙarshen numfashinsa, matuƙar dai asirinsa bai tonu ba.


Voice note ta ma Jidda cewa lallai sun yi sa'a sosai, su da suka ji shiru sun ma zata ko komai nasu ya lalace.


A ƙarshe dai haka Maryama ta ƙarisa yinin ranar zuciyarta fal da farin ciki, tana jiran dare ya yi ko zai kira ta, ta ji yanda zasu kaya.


Ana yin magrib sai ga Bobby ya kira ta. Haushinsa ta ji dan ta yi tsammanin Annur ne. Bata tsayar da adhkar É—in da take ba kawai ta latse silence, tana mai ci gaba da addu'o'inta.


Jin Bobby ya sake kira ya sa kawai ta mayar da wayar silent baki É—aya, sannan ta ci gaba da addu'arta.


Bayan sallar isha'i ta miƙe, ninke hijabin ta yi ta ɗora bisa kafet, sannan ta nufi falo inda iyayenta suke. Sam! Ta manta da bata cire wayar daga silent ba.


Annur kuwa kiran Bobby ya yi a waya cewa ya gama tsara komai, da yamma ya koma wurin boka ya sanar da shi duk ma yanda zai yi ya ƙoƙarta fara aikin a cikin daren nan, saboda zai san duk yanda zai yi ya shagaltar da ita, ya yaudare ta, har ta rasa yin ibadar da ta saba yi a cikin dare.


Sosai Bobby ya ji daÉ—in hakan, yana son farin cikin abokinsa, yana son ya ga sun yi nasara a wannan aikin.


Bayan ta je falo ta tarar Mama zaune, sai Abbanta da Muhammad da dawowarsu ke nan daga masallaci sun yi zaune a ƙasa, suna zaman jiranta.


Cikin ladabi ta gaishe da Abbanta. Da fara'a tana mai gasgata masa irin kewarsa da ta yi, saboda cikin kwanakin nan bai cika samun zama gida ba sosai.


"Kin yi zaune Maryama. Ki kawo mana abinci, na san wannan kasan bacci yake ji, dan gashi nan ya fara hamma."


Miƙewa ta yi tana miƙa, ta ce,


"Ai Mama ba wai Muhammad kaɗai ba, ni kaina yau baccin nan nake ji. Ina son na kwanta da wuri, saboda zan tashi ƙarfe sha biyu, karatu nake son yi sosai, gobe zazzafan rehearzal ne."


"To fa! Maryam ashe abun ya matso dai. Yaushe ne zaku yi wai?"


Da fara'a ta ce,


"Ashirin da biyar ga wannan watan ne Abba. Yau saura kwana goma sha huÉ—u ke nan, tun da yau sha É—aya ga wata."


"To masha Allahu! Allah Ya nuna mana Maryama. Ina alfahari da ke."


Murmusawa ta yi haÉ—e da barin falon, ta nufi kitchen domin kawo masu abinci.


Tuwon alkama ne da miyar ɗanyar kuɓewa. Ci suka yi suka ƙoshi, a lokacin tara ta yi. Sun bari abincin ya bi jikinsu sannan Maryama ta tayar da Muhamnad tsaye, ta ce,


"Oh ni Hammad! Kai gaka nan kaman ba namiji ba. Wai gyangyaÉ—i yake Mama, abun dariya."


Dariya suka yi su duka É—akin, kafin Maryama ta kai Muhammad É—akinsa, ita ma ta wuce nata É—akin.


Hamdala ta yi ga Allah, ta fiddo Qur'aninta daga cikin jaka ta É—ora bisa kafet, yanda idan ta tashi da dare ba sai ta nema ba.


Hayewa ta yi bisa gado tana miƙa da hamma duka a tare, sam! Ta manta da wayar da Annur zai kira ta, gashi kuma ta saka wayar silent.


Har ta kwanta kuma ta tuna da bata yi alwalar kwanciya barci ba, hakan ya sa ta miƙe da bacci sosai a idanuwanta. Sosai shaiɗan ke riya mata yau dai ɗaya ta haƙura da alwalar nan, saboda baccin da take ji. Ƙoƙari ta yi ta kawar da shaiɗanin, ta miƙe ta yo alwalar, sannan ta kwanta. Sai da ta tofa addu'a sosai bacci ya yi awon gaba da ita, ga ƴar agogon da ke tada ta daga bacci a gefenta.


To me kuka ce masu karatu? Boka Gagarabadau zai iya aiki ga Maryama kuwa?


Ya kuke ganin larurar Modu? Ko zai haye daga wannan mummunan ciwon zuciyar da ya kama shi?


Zaku samu duka amsoshin nan daga bakin Amrah. Mu dai namu kallo ne kawai, sannan mu mata voting idan mun gama karantawa.


Masu karatu sai kun yi haƙuri yanzu kam, saboda ba kullum zaku ringa ji na ba. Na dawo gida ne, kuma dole akwai abubuwan da zasu ringa shan kaina. Sai dai zan maku alƙawarin ƙoƙartawa bakin gwargwado, har sanda zamu kai ƙarshen labarin. Sai dai fa ku sani, akwai sauran labari sosai nan gaba. Allah Ya nuna mana mun kai aya. Ameen.


Thanks all.


Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:49 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)


Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


3⃣4⃣


Wannan ne karo kusan na goma sha biyu da Annur ke kiran Maryama amma ta ƙi ɗauka. A ƙarshe ya latsa kiran Jiddah zuciyarsa raunane, yana fatan ita ɗin ta ɗauka, ko zata kira masa Maryama a kan ta daure ta ɗauki kiransa.


Ringing É—aya wayar Jiddah ta yi ta jawo ta daga jikin caji, sunan mai kiran da ta gani ne ya sa ta hanzarta É—auka da sallama a bakinta.


Bai ko amsa ba ya ce,


"Please Jiddah ko baki faɗa wa Maryama cewa zan kira ta ba? Ina ta kiranta ta ƙi ɗauka, kuma gashi dare bai wani yi ba bare a ce ko ta yi barci ne."


Cikin mamaki Jiddah ta ce,


"Na faɗa mata mana. Amma kashe zan kira ta in sanar da ita, wata ƙila bata gane lambar taka ba ne."


"Ok please ina jiranki Jiddah."


Annur ya faÉ—a haÉ—e da kashe wayar.


Yana kashewa ta latsa kiran Maryama, sai dai da mamakinta ta ƙi ɗauka. Sai da ta kira ta sau biyar amma shiru. Cikin takaici ta ce,


"Why Maryama, why? Me ya sa zaki nemi tarwatsa mana plan? This is what we've been waiting for, gashi damar ta zo kuma kina neman ɓarar mana da ita."


Tana faÉ—in haka tana sake kiranta, amma shiru bata É—auka ba.


"Oh God! Maryama kin kofsa mana da kika yi baccin nan da wuri. Allah dai Ya sa kar shirinmu ya ɓaci."


Ta latso kiran Annur. Yana É—auka ta ce,


"Ina ta kiranta bata É—auka ba, da alama dai ta yi bacci. Dama fa Maryama akwaita da kwanciya da wuri. To da alama dai sai dai ka kira ta wani lokacin."


Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke Annur, ba tare da ya sani ba ya ce,


"Maryama why do you want to ruin our plan? Please pick up my call..."


Bai gama maganar ba ya yi saurin dafe bakinsa, yana tunanin yanda maganar ta suɓuce masa ba tare da ya san ya yi ba.


'Me ya sa take son lalata masu plan?' Jiddah ta tambayi kanta, take gabanta ya hau dukan uku uku, kar dai a ce fa Annur sun gano su ne, wata ƙila suke neman ɗana masu wani tarkon.


"Wane plan kake magana? What do you mean?"


Ya jiyo muryar Jiddah ta tambaye sa, muryar kaÉ—ai ka ji zaka tabbatar da cikin tashin hankalin da take.


"Ahm...uhm dama...uhm, I just, I just need her by my side. I love Maryama with all my heart. I want her to be my partner, abokiyar rayuwata ta har abada."


Duk da faÉ—in hakan da ya yi bai sa gaban Jiddah ya daina faÉ—uwa ba. Ta san Annur, ta san waye shi. Ta san cewa zai iya aikata komai domin farin cikinsa, haka Bobby ma. Tana gudun su cutar da Maryama. Sai yanzu take tunani lallai sun tafka babban kuskuren fara wannan plan É—in. A ganinta shi ke nan komai ya lalace.


"Uhm, Jiddah kina ji na? Please ko lambar Maman Maryama zaki taimaka ki turo min? I mean her mother's phone number. I really want to talk to Maryama."


"Are you out of your sense? A kan mene zan baka lambar mahaifiyarta? Idan ma ka sha wata banzar ƙwayarka ne da take faɗa maka wannan banza banzar to ka gaggauta neman gishiri ka sha ko zata fice. Dan wannan gurgun tunani ne kake, wanda ba zai taɓa yiuwa ba."


Sosai muryar Annur ke rawa, ya ce,


"Please help me Jiddah! Ba zan iya bacci ba tare da na ji muryan Maryama ba. And..."


Ya dakata daga nan, yana ƙoƙain haɗiye damuwarsa, tunanin yanda suka yi da bokansa ne ya faɗo masa a rai.


*
"Kana min wasa da hankali sosai Annur. Abu ya ƙi ci ya ƙi cinyewa. Shin ya muka yi da ku ɗazu?"


Cike da rauni ya kalli bokan, yana son yin magana amma tsoron furta komai yake.


"Kamar yanda na faɗa maku ɗazu, ku tabbatar kun shagaltar da ita matuƙar kuna so aiki ya yi tasiri a kanta."


Sai a sannan ya iya ɗaga laɓɓansa, cike da rauni ya ce,


"Boka Gagarabadau, abin da nake son aikatawa ke nan. Sai dai kuma ina buƙatar taimakonka. Dole sai ka saka hannu a wannan lamarin ko zai iya kasantuwa."


"Babu wannan maganar Annur. Ka tashi ka tafi kawai, bani da abin da zan iya yi maka."


Har ya miƙe kuma ya dawo ya zauna. Ya fuskanci bokan da jajayen idanuwansa da suke neman kawo ruwa, ya ce


"Zan yi Ya bokana! Na maka alƙawarin duk yanda zan yi yau sai na yi domin gyaruwar wannan aikin. Yau nake son aikata komai, kai ma ka shirya yin aiki a kanta a cikin daren yau. Ina baka tabbacin komai zai koma daidai, zan fitar da ƙaunarta daga zuciyata, a ƙarshe a samu gyara min wancan aikin na farko."


Murmusawa baƙin tsohon ya yi sosai, har sai da haƙoransa da suke cike da baƙin gashi suka bayyana. Ya ce,


"Bana jin ka Annur. Na tabbata zaka yi. Zan kashe duk wani aiki nawa na dare, zan tare ga aikin wannan yarinyar, a cikin daren nan za a gama komai."


Cike da yaƙini Annur ya zaro kuɗi daga aljihunsa ya dire a gaban boka. Jinjina masa kai bokan ya yi, kuɗin suka ɓace daga gabanshi, sannan ya ma Annur umurni da ya tashi ya tafi.


*
"Na roƙe ki Jiddah, ki taimaka min. Na miki alƙawari ba zan cutar da ita ba."


Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke jiddah, tunani take shin ta bashi lambar Mama ko kuwa dai kar ta bashi? Babbar matsalar ita ce kar Mama ta gano halin da suke ciki, ta san komai zai iya faruwa, tun da ba gaskiya Maryama ta faÉ—a mata ba.


"Ka yi haƙuri Ya Noor. Na tabbata gobe idan Maryama ta ga missed calls ɗinka zata kira ka."


Kashe wayar ya yi ba tare da ya sake furta komai ba, yana jin yanda zuciyarsa ke tafarfasa, take hararo masa bokansa da yake can sake da baki zai masa aiki yau.


Latsa kiran Bobby ya yi, cikin rauni ya ce,


"Guy akwai damuwa..."


Ya kwashe komai ya sanar masa, ya ƙara da faɗin,


"What are we going to do now?"


Shi kanshi Bobby ɗin damuwa ce fal a zuciyarsa. Ya ma rasa ta inda zasu ɓullowa lamarin, ya sani, ya san sarai boka Gagarabadau baya son wasa, ko kaɗan baya so ana kawo wargi a harkarsa.


"Ka yi shiru Farouk. Please ka faÉ—a min, ya zan yi?"


"Calm down abokina. Be a man, ban sanka da rauni irin wannan ba. Yanzu abin da zai faru, kawai ka haƙura da wannan batun na yau. Gobe da sassafe sai ka zo mu tafi wurinsa, na tabbatar zai saurare mu, zai kuma yi maka uzuri."


Sai a sannan Annur ya sauke ajiyar zuciya, yana jin sassauci a cikin zuciyarsa.


"Kana ganin boka zai saurare mu gobe kuwa?"


Ya ɗaga laɓɓansa ya furta a tsanake, yana shanye damuwarsa.


"Na tabbatar ransa zai ɓaci, saboda yanda kuka yi cewa zai kashe ko wane aiki yau ya maka wannan aikin. Amma ba komai, zai saurare mu. Kawai dai ka zo da wuri mu tafi."


"To zan zo, zan zo da sassafe Farouk. Good night."


Sallama suka yi da juna sannan suka tsinke wayoyin nasu, ko wane da tunanin da yake saƙawa a zuciyarsa.


Sai ma yanzu Bobby ya tuna cewa ɗazu sun yi da Maryama zai kira ta, sam! Ya shafa'a sai yanzu. Latsa kiran Maryama ya yi amma shiru bata ɗauka ba. Ya sake kira nan ma shiru, hakan ya sa ya mata text cewa ta yi haƙuri bai samu kiranta ba, uzururruka ne suka sha kansa.


Ƙaramar ƙwalwa irin ta mashaya, sam! Ya kasa gane cewa Maryama ita ce suke neman ɗana wa tarko. Bai yi tunanin ga suna ya zo ɗaya ba, sannan kuma Annur ya shaida masa yana ta kiranta bata ɗauka ba, shi ma kuma ya kira bata ɗauka ba.


Ajiye wayar ya yi kusa da shi, yana tsananin tausayawa abokinsa. Matuƙar wannan ƙullin ya warware, shi kanshi Bobby ɗin yana cikin matsala.


Maryama kuwa ƙarfe sha biyu daidai alarm ɗinta ya buga. Tashi ta yi da miƙa ta miƙe zaune. Tana tunanin irin baccin da ta yi, kamar matatta, tun da ta kwanta bata farka ba sai yanzu.


Tsaye ta miƙe kai tsaye ta nufi inda wayarta ke jikin chaji. Da ƙyar take buɗe idanuwan nata, har ta tarar da tarin missed calls ɗin da ke jere a allon wayar.


"Ya Rabb!"


Ta faÉ—a haÉ—e da dafe kai.


"Ashe a silent na bar wayar nan,

Please Login or Register in order to submit comment