You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ma a ce ki yi ba za ki yi ba."


Dariya suka É—auka duka Æ´an matan, suna kallonta.


"Da gaske fa. Ku dai ku jira in fito ku sha labari."


Ta koma Kitchen. Plates ta É—auko sannan ta dawo, biye da ita Æ´ar yarinyar da ke mata aiki ce ta kwaso lemuka a babban tray.


Bayan ta zauna ta ce musu,


"Ku zuba abinci ku ci kafin ya dawo É—aukarku. Na tabbata kuna jin yunwa, musamman ma ke amarya, na san amare abinci ba damun su ya yi ba."


Da murmushi Maryama ta ce,


"Za mu ci Aunty Ruky. Amma ki ba mu labarin da kika ce za ki ba mu."


"To in faɗa muku lokacin aure na, ina ji ina gani kunya ta hana ni yin rawa. Kun san dai irin abun, mace ta auri wanda ba sa'anta ba, akwai jin nauyi sosai. Wallahi sai bayan biki na rinƙa da na sani. Har gobe ban daina ba. Har ji nake ina ma dai a dawo da bikin baya, ai da na yi rawa wadda wata ƴila har sai jikina ya ƙille, ke wata ƙila ma har sai Alhajin da kansa ya janye ni."


Dariya suka sake ɗauka su duka. Dama haka take matar, akwai ta da wasa da dariya, ba dai a zauna da ita a yi ɓacin rai ba. Abincin suka ci kaɗan, sannan wayar Jiddah ta yi ƙara. Tana dubawa ta ga Deedah ne ke kiranta, ta ɗauka. Ce mata ya yi su fito ga shi nan ya zo, tana tsinke wayar ta faɗa musu. Aunty Ruky ta ce,


"To kuma ko lemun ba ku sha ba. Aikam tafiya za ku yi da shi idan kun je gida ku sha."


Suna faɗin ta bar shi ta bar shi amma ta ƙi, ta ce da mai aikinta ta kawo mata leda mai girma, ta juye musu duka lemukan, sannan ta sa ta kai musu har mota.


Godiya suka mata sannan suka fita, sai famar dariya suke mata. Maryama na faÉ—in,


"Ai ku ne baƙin Aunty Ruky. Haka take da ban-dariyar tsiya."


Skwatin suka yi a motar ba ta amshe su ba, saboda yawan su, duk wanda za su kwana ne suke tare. Mutum biyu ma suka zauna a gaba; Jiddah da wata ƙawarsu Afrah.


Bayan ya sauke su suka firfito, ya ce da Jiddah don Allah ta tsaya yana so su yi wata magana.


Kallon Maryama da saudat da ke ɓoye dariyarsu ta yi, sannan ta musu gatsine da baki ta dawo ta tsaya kusa da murfin motar, shi kuma ya fito, ya zagayo inda take.


Haka kawai kuma sai ya samu kanshi da rashin samun abun faÉ—i. ÆŠan dafe kanshi ya yi, kafin ya ce,


"Ba ku da buƙatar komai dai ko?"


Da murmushi a fuskarta ta ce,


"Babu komai Yah Deedah."


"To shi kenan. Idan dai akwai abin da kuke so ko ma mene ne kina da numberna, kar ki samu damuwa kawai ki kira ni ko kuma ki min text."


"To insha Allahu. Mun gode ƙwarai Allah saka da alkhairi."


"Ameen ya Rabbi. Gobe dai na tabbata Dady da kanshi zai kai amarya gidanta. Motocin É—aukar amarya za su zo, na yi magana da friends É—ina kamar yadda suka yi yau. Please kar ki hau motar kowa, saboda ina so mu yi magana ne bayan an kai amaryar. Ai babu takura ko?"


"Ehh."


Ta faɗa ƙasa-ƙasa cikin jin nauyinsa.


"To ni bara na wuce Jiddah. Idan na koma gida insha Aahu I'll give you a call. Ki tabbatar kin saka ma cikinki wani abu."


Kai kawai ta É—aga mishi, sannan suka yi sallama ta shige ciki. Bai tayar da motarsa ba har sai da ya tabbatar ta shiga gidan.


Tana shiga kuwa suka hau yi mata tsiya. Ba ta ce musu komai ba sai guntun tsakin da ta saki, sannan ta zauna bakin gado, tana jiran Afrah ta fito ta yi alwalla.


Maryama kuwa suna shigowa ta ce musu za ta je É—akin Abba, ba kuma can É—in ta je ba, É—akin Annur ta nufa cike da É—okin ganinsa.


Kwance ta same shi ya kalli can jikin bango, a tunaninta ma barci yake, saboda yadda ta ga ya takure wuri É—aya.


GyaÉ—a kanta ta yi cike da tausayi, ta jawo blanket ta rufa masa, ta juya da nufin tafiya ta ji muryarsa ya ce,


"Ni na yi fushi."


Sassanyan murmushi mai haÉ—e da ajiyar zuciya ta saki, sannan ta juyo tana kallonshi.


"Na'am me ka ce?"


Ta faÉ—a a hankali.


"Ba ke ce kika ƙi dawowa ba."


"A yi min afwa. Kalla ka ga na kama kunnena, alamun na tuba kenan. Ba zan sake ba insha Allah."


Tashi ya yi zaune yana kallonta, ya É—an lumshe idanuwan kafin ya buÉ—e, ya ce,


"Ai wannan mutumin ya zo nan, shi ya min wanka ma ya saka min wannan kayan masu kyau."


Ya hau gwada mata light brown yadin jikinsa, wanda ya ji aikin hannu kalar coffee brown. ÆŠaya daga cikin kayan da Kawu Imrana ya É—inka masa ne. Kuma É—azu da safe Uncle Marwan ya aiko masa da wasu kala biyu, cewa ya saka, duk da dai ba wurin É—aurin auren zai halarta ba.


"Inye angon nawan ba. Ka ga yadda ka yi kyau sosai kuwa? Tamkar na sace ka na gudu haka na ji."


Harararta ya yi, ya ɓata fuska, ya ce,


"Ai dai ba za ki iya sace ni ba. Yauwa, na tuno wani abu."


Ya ɗora hannunshi a goshi alamar tunani. Ba ta ce masa komai ba, kamar yadda ta karanta, cewa ba a ma mutum gajen haƙuri a irin wannan lamurran, musamman ma masu matsalar ƙwaƙwalwa, ko kuma wanda ake tunanin sun samu lost of memory. Barin sa ake don kanshi ya faɗa.


Ya yi kamar seconds arba'in a haka, kafin ya ce,


"Wasu mutane ne suka kai ni gidansu, har suka cire min kayan jikina."


Cike da mamaki ido a buɗe take kallon sa, ba kuma ta nemi jin ƙarin bayani daga gare shi ba, har sai da don kansa ya ce,


"Kuma sai suka saka min wasu a jikina. Ni dai kawai na ce musu Amrah Nake So!"


Ya saki dariya, yana mai bin ta da kallo. Ita ɗin ma dariyar ta ƙirƙiro, duk da cewa zancen nashi ya matuƙar ɗaure mata kai. Sosai take daɗa gode ma Allah. Domin kuwa ba laifi sauƙi na zuwa, addu'arta tana amsuwa. Kuma sannan tana saka shi shi ma yana ma kanshi, tana faɗi yana faɗi. Ga Muhammad ma ƙaramin yaro, duk sadda zai yi sallah to sai ya saka Annur a addu'arsa.


"Ka ci abinci dai ko?"


"Hammad É—an yaron nan ya kawo min, kuma ya zauna har sai da na gama ci na sha magani, sannan ya tafi."


Ya kama lila kanshi, yana dariya.


"To masha Allah! Haka nake son ji dama. Bari in je in samu ko wanka in yi, ga sallah ban yi ba. Gidan akwai mutane sosai, baƙi wanda suka zo biki. Ba za ka gan ni ba sai gobe. Goben ma ba sosai za ka samu gani na ba. Ai za ka yi haƙuri ko?"


"Ehh mana. Ba kin ce aure za a É—aura mana ba?"


Mamaki take sosai, ashe dai bai manta ba. Ta ce,


"Haka ne kuwa Yah Noor É—ina. Bari in tafi to. Sai da safe."


Kansa ya É—aga mata, sannan ya koma ya kwanta. Sai da ta kashe masa wutar É—akin sannan ta fice zuwa nata É—akin.


*


Washe gari Jumu'a, tun da sassafe Maryama ta yi wanka, ta shirya cikin atamfarta Julios Holland wadda ta ji É—inkin riga da zani half gown. ÆŠaurin É—ankwalin Zahra Buhari da ake yayi ta cancaÉ—a, ta feshe jikinta da turaren Cinema, sannan ta yafa gyale madaidaici. Kyau iya kyau ta yi shi, duk da cewa ba wani make up ta yi sosai ba. Sai da ta gama duka sannan ta ce da su Jiddah tana zuwa. Ko ba ta faÉ—a ma Jiddah ba ta san inda za ta je. Hakan ya sa kawai ta sakar mata tattausan murmushi, sannan ta fice daga É—akin.


A hanyarta ta yi kiciɓus da Umman Amrah. Aikuwa cikin fara'a sosai ta rungume ta, tana faɗin,


"Umma baccin Æ´a ba ta isa ta yi fushi da Ummanta ba, nikam dai da na yi da ke."


Ta ɗan ɓata fuskarta alamun shagwaɓa.


Umma ta ce,


"Yi haƙuri ƴata. Wallahi abubuwa da yawa ne suka hana ni sake dawowa. Na farko dai kin ga Mallam ya sha ciwo kwanakin nan, wanda ko kaɗan kin ga bai kamata na fita ba. Na biyu kuma sai na yi baƙuwa, ƙanwata ta zo daga Kano musamman gidana ta sauka. Kin ga ai bai kamata na fita na bar ta ba."


Murmushi Maryama ta saki, ta ce,


"Allah sarki! To ya jikin Mallam É—in yanzu?"


"Jiki da sauƙi sosai Maryama. Ya warware ma har ya koma wurin aikinsa. Sai jiya ai na ga saƙonki na waya. Cewa yau Jumua za a ɗaura miki aure da Annur. Da yake wayar na jefar kin san halina, ban kuma waiwayarta ba sai jiya, ina buɗewa na ci karo da saƙon. Wallahi inda na sani da da ni za a yi komai. Rashin sani ne."


"Babu komai ai Umma. Mu je na raka ki wurin Mama."


"Ai har na zauna a falo kuma dai na ga babu wanda na sani. Na kusa minti talatin fa a zaune."


"Eyyah! Ai ban sani ba wallahi. Kin san gidan taro ya gaji haka. Kuma ban ma san cewa Mamar ba ta fito ba. Mu je ko?"


Suka nufi É—akin Mama.


Tun daga bakin ƙofa mutane ke ta famar tsokanar Maryama suna faɗin ga amarya ga amarya, wasu sai waƙar tsokana suke mata. Murmushi kawai take sakar musu har suka ƙarisa gaban Mama.


Da faraa Mama ta yi ma Umma marhabun da zuwa. Sannan ta gyara mata wurin zama ta zauna. Sai da Maryama ta tabbatar da Umma ta samu wurin zama sannan ta bar É—akin, ta nufi É—akin Annur.


Wata irin dakakkiyar farar shadda ce a jikinsa, wacce ta ji surfani kalar light blue. Fuskar nan tasa ta yi sayau, saboda sabon askin da mai gadi ya masa, har da gyaran fuska. A gefensa ta zauna, tana ƙare mishi kallo, shi ɗin ma yana bin ta da kallo. Kafin ta ce mishi komai ta ji ya ce,


"Kin yi kyau."


Ya langaɓe kanshi yana murmushi.


"Kai ma haka."


Ta faÉ—a tana mai juya zoben hannunta. Sai da ta É—an sassauta muryarta sannan ta ce,


"Jiya kana ta juya zoben nan sannan ka dawo da shi ka saka min. Akwai damuwa ne?"


Shiru ya yi jim! Kafin ya ce,


"A ina kika same shi?""


Ta ji ya faÉ—a, yana miyar da dukkanin hankalinsa gare ta.


Ɗan jujjuya zoben ta yi sannan ta zaro shi daga yatsar tata. Ta miƙa masa ya karɓa ya riƙe shi.


"Kalli da kyau Yah Noor. What can you remember about it?"


Shiru ya mata, bai daina jujjuya zoben ba, bai kuma miyar mata da shi ba. Sai da ta gaji da shirun don kanta, sannan ta ce,


"Uncle Marwan É—in nan da na faÉ—a maka, shi ya haÉ—o min da shi a cikin lefena."


Zumbur Annur ya miƙe tsaye. Idanuwansa suka gama firfitowa, ya ce,


"Ba naki ba ne! Wallahi ba naki ba ne ba, na Amrah ne!"


Miƙewar ita ma ta yi, idanuwanta suka cicciko, ta ma rasa abin da za ta faɗa. Ba ta san me ya sa ba, a yanzu ta fara jin kishin Amrah. Ita kanta tana mamaki, ta yadda lokaci guda ta fara kishi da matatta wacce ba ta raye. Amma kuma me zai sa ya dame ta da xzncen Amrah, bayan kuma ita zai aura? Kenan ma zoben yana da wani asali, da ba ta gama sani ba?


Fizge zoben ta yi daga hannunshi, ya bi ta da kallon mamaki. Cikin drowar da magungunansa suke ta jawo ta ciri wata takarda daga jikin jotter. Ta nannaɗe zoben a ciki sannan ta jefa dunƙulen takardar cikin drowar, ta rufe. Dawowa ta yi a gabanshi, ta rusuna har ƙasa, tana hawaye ta ce,


"Da alama dai zoben nan asalinsa ba nawa ba ne ba, duk da dai ban gama gasgatawa ba. Amma dai ga shi nan, na miyar maka a inda karikitanka suke. Duk ranar da ka dawo cikin hankalinka, ka ba ni kyautarsa da hannunka, to zan karɓa. Amma for now, bai zama haƙƙina ba."


Ta miƙe haɗe da ficewa daga ɗakin. Sai da ta ja ƙofar ta rufe, sannan ta ƙarisa isa part ɗin Abbansu.


Ta samu daidai Abban nata zai fito shi da Kawu Imrana. Har ƙasa ta duƙa ta gaishe su, kawu Imrana ya ce,


"Amarya kin sha ƙamshi. Sai wani haske kike ba ki gan ki ba."


Murmushi ta saki kanta a sunkuye tana jin kunya sosai. Kawu ya ce,


"Akwai abin da kike buƙata ne?"


Ba ta É—ago kanta ba ta ce,


"Dama muna son key ɗin ɗakin Abba ne, ɗakina ba zai ɗauki ƙawayena duka ba."


Cire mukullan ɗakin nashi ya yi daga jikin na motarshi, sannan ya miƙa mata, yana faɗin,


"A kula sosai don Allah. Ko ki rufe min bedroom, tunda dai falon da girma."


"To Abba insha Allah."


Ta faɗa bayan ta miƙe tsaye, ta basu hanya suka wuce ita kuma ta koma ɗakinta domin tahowa da ƙawayen nata.


*


Ƙarfe uku daidai na rana al'umma da yawa suka shaida ɗaurin auren Annur da Maryama, wanda Uncle Marwan ya zama wakilin ango, kawu Imrana kuma waliyyin amarya.


*


Dafe zuciyarsa ya yi sanadiyyar sauya salon bugawa da ya ji ta yi. Cikin ƙanƙanin lokaci ya rinƙa jin wani irin sanyi na ratsa duk wata tsoka da ke cikin zuciyarsa. Samun kansa ya yi da murmusawa, yana jin yadda ƙamshin turaren da ke jikinsa ke rikeɗewa izuwa ƙamshin turaren Maryama da ta bar ɗakin tun kusan awanni biyar da suka shuɗe.


*


Guɗar da suka jiyo ana rangaɗawa ne ya basu tabbacin an ɗaura. Nan fa ƙawaye suka fara faɗin,


"Amarsu ta ango! An daura..."


Ba ta san sadda ta fashe da kuka ba. Ta duƙar da kanta bisa cinyarta, tana zubda ruwan hawaye. Jin abun take tamkar a mafarki, wai yau ita ce ta zama matar Annur, matarsa ta sunnah. A wani ɓangaren kuwa tausayin kanta take; ta auri mutumin da bai kasance mai hankali ba. Wanda ta tabbatar da duk sadda ya dawo cikin hankalinsa ba lallai ba ne ya iya ci gaba da rayuwa da ita. Me ya sa zuciyarta za ta mata haka?


"Amarya na kukan murna. Mun san komai yarinya, gwara ma kawai ki yi shiru ki daina yin shi."


Ba ta ko kula su ba ta ci gaba da kukanta. Ganin haka ya sa kuma suka hau rarrashinta. Jiddah ta dafa bayanta sai famar ba ta haƙuri take, har suka samu ta yi shiru.


Miƙewa ta yi a bisa ƙafafunta, cikin rashin kuzari ta fara takawa, duk irin taron mutanen da ke wurin a haka ta rinƙa kukkutsawa har ta isa ɗakin Annur.


Tana zuwa ta gan shi zaune, ba ta san sadda ta rungume shi ba. Tsam-tsam ta masa tamkar wani zai ƙwace mata shi. A tare bugun zuciyarsu ya rinƙa tafiya, suna jin yadda ni'ima ke sauka a cikin duniyarsu. Cikin muryar kuka Maryama ta ce,


"An ɗaura Yah Noor! Shi kenan na zama mallakinka, ka zama nawa. Rayuwarmu ta dawo a ƙarƙashin inuwa guda. Ina ƙaunarka Yah Noor, da dukkanin zuciyata. Daga farko na ɗauka ko tausayinka kawai nake, a zato na taimakon ka ne nake da muradin yi. Sai a yanzu nake daɗa tabbatar da ƙaunarka nake, ƙauna mai tsananin gaske. Don Allah ka min alƙawari, cewa ba za ka taɓa rabuwa da ni ba, duk wuya duk rintsi. Don Allah ka ba ni fili a cikin zuciyarka, ni ma in gwada kwance tawa hajar a cikinta. Na ɗauki alwashin zame maka Amrarka, na maka alƙawarin ba ka duk wani gata wanda ya kamata mace ta bai wa mijinta. Zan kasance mai alfahari da kai, duk tsanani duk jin daɗi."


Ta janye jikinta daga nashi, tana faÉ—in,


"Say something please. Ni ma ka ce da ni kana so na. Na zama halaliyarka Yah Noor."


Murmushi kawai yake sakar mata, ya gagara furta komai.


"Tunda ba za ka faɗi komai ba ni zan tafi. Ina da baƙi sosai. Amma please idan na ce wani abu kai ma ka maimaita. Ka ji?"


ÆŠaga mata kai ya yi, yana kallonta.


"Allah ya ba ni lafiya"


Ya maimaita shi ma a hankali.


"Ya warware min dukkanin damuwata."


Bayan ya faɗa har sau uku sannan ta tafi, ta jawo masa ƙofar ɗakin, tana yi tana waige.


Sai zolayarta ake har ta samu ta isa É—akin Abba. Dr. Islam ta samu zaune kan stool, tana latsa wayarta.


Isa ta yi inda take, ta rungume ta da murna, tana faÉ—in


"Aunty Islam ashe kin zo."


"Na zo Maryam. Kin je ina ne?"


"Na zagaya baya ne. Kun zo lafiya? Ina Abdul É—ina da kuma Momyna?"


"Abdul na can sun haɗe da Hammad tun muna shigowa, daidai su kuma sun dawo daga wurin ɗaurin aure. Momy kuma tare muka shiga ɗakin Mama, ta ga Mahaifiyar wata yarinya da ta rasu ne, Amrah. To suna abun arziƙi ta zauna inda take suna fira."


Dariyar yaƙe ta yi Maryama. Tana gudun kar Umman Amrah ta kwafsa, kodayake dai ta san komai, ta san cewa basa son dangin Annur ɗin su sani yanzu.


Ƙarfe biyar na yamma motocin ɗaukar amarya suka hallara a ƙofar gidan su Maryama. Nan fa mutane suka isa gaban motocin, aka hau shiga.


Maryama kuwa ta canza kaya, ta saka wani jan material da aka ma É—inkin doguwar riga, ta saka alkyabba kalar golden. Yayar Mama mai suna Goggo Rabi da Umman Amrah ne suka taho da Maryama, bayan ta samu nasihu sosai daga mahaifiyarta da kuma danginta. Kuka sosai take yi, har suka iso gaban motar kawu Imrana, saboda dama ita kawai yake jira tun É—azu.


Ƙawarta Saudat ce ta zauna a gaban motar Kawu Imrana ɗin, sai amarya da iyaye a baya, tana tsakiyarsu. Jan motar ya yi kawu, a hankali sautin kukan Maryama ke fita, wanda tun ɗazu take yin sa.


***


*To mutanena. An ɗaura fa. Are you happy? Na san kun ji daɗi, confirm. To sai a ba ni ladar aikina🤒.*


*Maryama dai ta auri mahaukaci Annur. Ko ya zaman nasu zai kasance? Wannan zoben na zinare da suka yi maganarsa, me yake ƙunshe da shi? Amsoshin suna gaba, insha Allah.*


*Don Allah ku taimaka min gobe kar wacce ta nemi ANS, ni ma in huta haka nan.*


Thanks all.


Pinky durling💞
RAZ 2
[9/17, 1:27 AM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taɓa zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_


Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


6⃣5⃣


Wattpad: PrincessAmrah


***


Hangame gate ɗin gidan aka yi, Kawu Imrana ya shiga har cikin gidan da motarshi. Bayan ya gyara parking ne iyayen suka fito da Maryama da har yanzu ke ta famar cizgar kuka. Sadda suka isa bakin ƙofar shiga part ɗin nasu, sai da ta karanta addu'o'i sosai kafin ta ɗora ƙafarta a bisa ƙofar ta shige ciki.


Sauran ƴan ɗaukar amarya kuwa sai da aka sha zagaye da su sosai, kusan duk girman Katsina sai da suka zagaye shi. Ring roads ɗin nan kaf sun ga bayansa, kafin suka ƙarisa isowa gidan amaryar. A lokacin har magrib ta bada baya, gari ya fara yin duhu.


Daga can nesa kaɗan da gidan Deedah ya faka motarshi, rage ƙarfin AC ɗin ya yi, yayin da ya juyo ya fuskanci Jiddah da dukkanin hankali da nutsuwarsa. Kanta ta sunkuyar ƙasa, tana bin zanen lallen hannunta na hagu da yatsunta na hannun dama, tana sauraren abin da zai fito daga bakinsa.


Ajiyar zuciya ya sauke, yana bin ta da kallo, kafin ya saita kansa, ya ce,


"Jiddah..."


Ya dakata daga nan, jin yadda sunan nata ke neman yi masa nauyi a bakinsa.


"Na'am."


Ta faɗa haɗe da ɗan ɗago kanta ta kalle shi, sai kuma ta samu kanta da ƙoƙarin rasa nutsuwarta, haɗa idanuwan da suka yi a lokaci guda.


"Jiddah ina neman wata alfarma daga gare ki."


"Am all ears Yah Deedah."


"Jiddah please, will you marry me?"


Duk da cewa ta karanci yadda soyayyarta ke É—awainiya da shi duk a cikin kwanakin nan. A É—an haÉ—a idanuwan da ta yi da shi cikin seconds kaÉ—an, ta ga zallar soyayyarta a cikin idanuwansa. Amma bai hana ta mamakin jin kalaman nasa ba. Sai ta rasa abin da za ta faÉ—a, kawai ta masa shiru.


"Don't say no Jiddah. Wallahi I love you with all my heart. Don Allah kar ki watsa min ƙasa a ido. Kin ga Maryam ta ƙi ni, kar ki min irin nata. Please."


Baki ɗaya ya gama marairaice fuska tamkar ba shi ba. Ita kanta mamakin yadda ta ji yana ƙanƙan da murya take.


"Yah Deedah..."


Ya gaggauta kasa kunnuwansa domin jin kalaman da za su fito daga bakinta.


"Akwai wanda nake tare da shi, tun kusan shekara biyu muke tare. To matsalar da aka samu, tun tsawon watanni biyar zuwa shida da suka shuɗe, Abbana ke bin kansa da ya turo, amma ya ƙi turowa. Ni kaina na kasa fahimtar inda ya dosa. Sannan kuma kullum idan muka yi waya da shi sai famar cika ni yake da daɗin baki. Ina ƙaunarsa duk da hakan Yah Deedah."


Idanuwanta suka yi rau-rau tamkar za ta yi kuka.


"To ya isa Jiddah. Ni dama ban isa na miki dole ba. Yadda duk kike so haka za a yi."


Yana jin yadda kishi ke masa tuƙuƙi a cikin zuciyarsa. Har ji yake inda ma a ce wancan saurayin nata yana a gabansa, zai iya faffalla masa mari zafafa kala biyar. Sai dai kuma me, a kodayaushe ƙoƙari yake na ganin ya rangwanta ma kansa wannan zazzafan kishin da ke gare shi. So yake ya ga ya rangwanta wa zuciyarsa, ya rinƙa kai ta nesa a duk sadda kishinsa ya motsa.


Shiru ne ya biyo baya a motar, kafin Jiddah ta yi ƙarfin halin faɗin,


"Sai dai kuma son nashi a banza ne, tunda shi ya ƙoƙarta ƙaryata kansa na faɗar da yake yana so na. Duk wani namiji matuƙar yana son mace tsakaninsa da Allah, to daɗi zai ji idan aka ce masa ya turo iyayensa a yi maganar aure. Ba wai halin yin auren ba ne Tahir ba shi da shi, na samu raɗe-raɗi ne cewa akwai wacce ake so a aura masa a gidansu, duk da dai shi ya ƙaryata min hakan. Yah Deedah..."


Ta sassauta muryarta tana kallon shi.


"If you are ready to marry me, then I'm ready too to accept you as my fiancee."


Kansa da ke jingine da sitiyari ya É—ago da mamaki yana kallon ta. KarkaÉ—e kunnuwansa yake kamar dai ba daidai ya ji zancen ba. A tunaninsa ko don yana son ta amince É—in ne ya sa kunnuwansa suke masa wannan gizon. Ganin haka ya sa Jiddah murmusawa, ta ce,


"Na amince Yah Deedah. Na amince zan aure ka, da dukkan zuciyata."


Sassanyan murmushin da ke daɗa ƙawata fuskarsa ya saki. Bai san sadda ya furta 'Alhamdulillah!' ba. Sannan ya ce,


"Na matuƙar jin daɗin kalamanki Jiddah. And I promise to make you happy, till the end of my breath. Ina ƙaunarki Jiddah. Ina matuƙar son ki."


Tattausan murmushi ta sakar masa ita ma. Ta ce,


"I know, Yah Deedah. I can see it in your eyes."


Jinjina mata kansa ya yi, kafin ya ce,


"Na samu abin da nake so, sai ki shiga ciki ko? Duhu ya fara, ga shi ba ki koma ba. Ba na so zargi ya shigo ciki."


"Haka ne."


Ta faɗa kanta a sunkuye, sai kuma ta samu kanta da jin kunyarsa. Wayarta ce ta ɗauki ƙara, tana dubawa ta ga sunan Hadiza a bayyane. Ɗaukar kiran ta yi haɗe da karawa a kunnenta.


"Na shigo cikin GRA É—in Jiddah. Ta ina zan yo kuma?"


"Kina daidai ina yanzu?"


Jiddah ta tambaye ta. Alama Deedah ya mata kan ta dakatar da ita, sai su je su zo da ita kawai. Abin da ya faru É—in kenan. Ta ce mata tana daidai round about na GRA. A nan ta ce ta tsaya ta jira su, za su zo su É—auke ta.


A can ɗin kuwa suka same ta zaune kan wata kujerar ƙasa, irin wadda ake ajjewa kusa da manyan rounds. Tana ganinsu ta taso ta yo inda suke. Bayan motar ta buɗe ta shiga, tana faɗin,


"Sannunku."


Jiddah ta ce,


"Yauwa. Hadiza masu zuwa biki da dare."


Ta dafe kanta.


"A yi haƙuri. Kin san na koma Maraɗi ne, shi ya sa ma da kika ce za ku kawo min IV na ce muku bana nan. Na koma gida ne, a gaban iyayena.

Please Login or Register in order to submit comment