You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsaf gwanin ban shaawa. Ta fito kuma ta nufi kitchen. Haka ta zagaye gidan tsaf tana duba tsaruwarsa, kafin ta koma É—akin Annur. Har a lokacin bai tashi ba, a bayyane ta furta,


"Sai sharar barcinsa yake yana morewa. Kai ma kenan da babu gajiyar biki a tattare da kai."


Ta cire hijabinta sannan ta shiga wanka. Bayan ta fito daga wankan ta wuce ɗakinta. Mai ta shafa sannan ta yi light make_up. Ta feshe jikinta da body spray lungu da saƙo, har a bayan kunnenta. Bayan ta gama ta ɗauki cotton bud ta goge bayan kunnen nata da shi. Bakin wardrobe ɗinta ta isa, ta fiddo wata atamfa kalar light blue, da aka ƙawata da manyan flowers kalar pink. Ɗinkin riga da skirt ne da suka bi jikinta, suka bayyana shape ɗinta sosai. Bayan ta saka ta ƙarisa gaban madubi, ta kalli kanta sosai sannan ta ɗaura ɗankwali. Turarukan oud kala kala ta feshe jikinta da su, ta saka takalma high heels ta bar ɗakin.


Isar ta É—akinsa ta same shi ya tashi, sai famar dube-dube yake, da alamu ita yake nema. Yana ganinta ya saki tattausan murmushi, yana motsa bakinsa.


"Mi Amor ka tashi?"


Bai san me take nufi da kalmar da ya ji ta kira san da shi ba, sai dai kai kawai da ya ɗaga mata, fuskarsa har yanzu ƙunshe da faraa.


"Then, mu shiga toilet ka yi alwalla ko?"


"Ban iya ba."


Ya faÉ—a yana gyargyaÉ—i da kansa.


"Mu je zan yi maka ne. Daga yanzu kullum zan rinƙa koya maka sallah. Insha Allahu sannu a hankali za ka iya. Mu je."


Miƙewar kuwa ya yi, ya bi bayanta suka isa ban-ɗakin. Sai da ta matsa masa toothpaste a brush ta goge masa lungu da saƙo na bakinsa, sannan ta wanke mishi tas, ta masa alwallar. Tare suka fito, ta ce ya hau bisa kafet ɗin, duk abin da ya ga ta yi shi ma ya yi, ta saka hijabi.


Raka'a biyu kuwa suka yi, sai famar waige-waige yake yi, sai ya saki murmushi, sai kuma ya ɗaure fuska, har suka ƙarisa sallar. Addua ta saka shi ya ma kanshi sosai, sannan ta ce,


"Yanzu sai wanka ya rage ko?"


Ya É—aga mata kai.


"To ina zuwa. Ban kunna heater É—in ba ma."


Ta shiga toilet É—in.


Knocking ta ji ana yi daga bakin ƙofa, ta gaggauta fitowa daga toilet ɗin ta isa ƙofar falo. Tana buɗewa ta ga Hammad ne da wata cousin ɗinta Aysha, hannuwansu riƙe da basket mai girma, sun kamo su biyun. Murmushi ta sakar musu, ta ce,


"Sannun ku da zuwa ƙannena. Ku shigo."


Ta yo gaba suka biyo bayanta. Zama suka yi bayan Aysha da Hammad sun azzo basket É—in a bisa dinning table.


"Ina kwana Yaya?"


Suka faÉ—a a tare.


"Lafiya ƙalau. Ya gida ya su Mama?"


"Sun ce ma a gaishe ku."


"Aikuwa muna amsawa."


Ta isa gaban electronics, dama jiya su Jiddah sun haÉ—a mata komai, kunna musu kallo ta yi, African Magic Hausa ta kai musu, ana yin film É—in Maula.


"Ku yi kallo Sholie. Zan je in dawo. Idan ba ku karya ba ku É—iba ku karya."


Hammad ne ya ce,


"Mun karya Yaya. Naku ne ku kaÉ—ai ke da Yaya Noor."


Dafa kansa ta yi sannan ta ce,


"To shi kenan. Ku yi kallo kafin in dawo."


Ta nufi É—akin Annur É—in. A yadda ta bar shi haka ta same shi, ya yi zaune a takure bakin gado, yana jiran ta.


"Am sorry na bar ka Mi Amor. Su Hammad ne suka zo. Mu shiga ko?"


Ta jawo light blue towel ɗinsa jikin ƙofa, ta riƙe a hannunta.


Bayan sun shiga toilet ɗin ta rufe ƙofar, nan fa ake yin ta. Samun kanta ta yi da jin kunyar ganin tsiraicinsa, sosai ba kadan ba. Shi kam ko a jikinsa, ya hunce sannan ya tsuguna. Idonta ta rinƙa rurrufewa, sai idan za ta shafa sabulu take buɗe su, da haka dai aka yi wannan wanka, da ƙyar da jiɓin goshi. Idon a rufe ta ɗaura masa towel ɗin sannan suka fito. Ɗan ƙaramin towel ta ba shi cewa ya tsane ruwan jikinsa da shi, sannan ta ƙarisa gaban wardrobe ɗinsa ta fito masa da wani baƙin yadi mai matuƙar kyau. Feshe kayan da turare ta yi, har da boxer ɗinsa. Ta shafa masa mai, da mayukan turare a jikinsa, ta fara ƙoƙarin saka masa kayan. A nan ma an sha wata dagar, da ƙyar dai ta samu ta gama shirya shi, sai famar dariyar yaƙe yake yi, yana kallon kayan jikin nashi, yana tattaɓa su yana motsi da kai.


"Kayanka ko? Suna da kyau sosai Mi Amor. Sun kuma karɓi jikinka. Amma ka san me? Ka fi kayan kyau. Sirrin kyawun kayan ma daga kai ne. Inda a ce wani namijin daban ne ya saka su to ba za su yi kyawun haka ba."


Ta kama hannunsa suka ƙarisa falon, cike da ƙaunarsa, tana jin duniyarta na mata matuƙar daɗi.


***


*My pipu ku yi maneji da wannan. Na san ya yi kaÉ—an, amma dai ku min uzuri. Kuma sai da na yi 1k words duka suka goge sai da na sako sabo.*


*Ya kuka ji wannan shafin? Kun ga soyayyar Marnoor ta fara ƙarfafa sosai ko? Irin hakan shi ya fi komai daɗi.😍😘*


*A wani ɓangaren kuma, mun ga yadda Sans ya luma ma cikinsa wuƙa, da nufin kashe kansa.* *Wanann wace irin damuwa ce mutum ke gare shi da har zai gwammaci ya rasa rayuwarsa? Duk wanda ya kashe kansa fa ya mutu kafiri, wutar Jahannama ita ce makomarsa.*
*Ko Sans ɗin ya mutu? Alƙalamin Amrah kawai zai warware mana.😥😪*


*My Sister na gode ƙwarai da haɗaɗɗiyar video da kika haɗa ma wannan littafin. Video fa ta yi kyau masha Allah! Kowa ya yaba. Allah ya saka miki da alkhairi ya bar zumunci.❤💃*


*Kar a manta a rinƙa yi ana tunowa da danna ƴar tauraruwar nan mai kyau da daɗin taɓawa.😀*


Thanks all.


Pinky durling💞
RAZ 2
[9/21, 12:06 AM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taɓa zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_


Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


6⃣7⃣


Wattpad: PrincessAmrah


***


Emergency aka karɓi Sans, aka shiga ciki da shi domin tabbatuwar yana raye ko ba ya raye? Idan yana raye to sai a ba shi taimakon gaggawa.


Tun sadda aka shiga da shi hankalin su Dady bai kwanta ba. Momy sai zirga-zirga take, ba ta nan ba ta can, tana ta aikin zubar da ƙwalla. Sosai suke son sanin halin da Sans yake ciki. Hakan ya sa Dady ya kasa daurewa, bai jira an ba shi izini ba kawai ya afka cikin ɗakin.


Ganin ya yi malaman asitin sun yi cincirindo a bakin wani gado, duk da bai ga wanda suka zagaye É—in ba, amma ya tabbatar da cewa Annur É—insu ne. Hakan ya sa ya gaggauta isa inda suke, hankalinsa a tashe. Kallo É—aya za ka ma Dady ka tabbatar cewa ba ya cikin nutsuwarsa. Saboda yadda duk ya bi ya koma tamkar zararre, rigar jikinsa ma a birkice ya saka ta, saboda har ma ya shiga mota daga shi sai singlet da gudu Janan ta koma ta É—auko masa rigar ya saka.


"Ya za ku bar ni a cikin duhu ku kasa fa min haƙiƙanin abin da yake damun yarona?"


Ya faɗa a fusace, yana kallon yadda suke aiki bakin ƙoƙarinsu domin taro numfashinsa, kafin a fara yi masa ɗinki a cikin nasa.


Babban likitan da ke wurin cikin tattausan lafazi ya dafa kafaÉ—ar Dady, ya ce,


"Ka kwantar da hankalinka Alhaji. Insha Allahu yaronka zai ci gaba da rayuwa kamar kowa, zai tashi da kafaɗunsa. Akwai bayanin da ya kamata na maka, amma ka yi haƙuri ka fita har mu shawo kan babban lamarin, sannan zan buƙaci ganawa da kai. Kar ka ji komai fa, da yardar Allah komai zai daidaita."


Sai a sannan Dady ya É—an samu nutsuwa. Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, ba tare da ya furta komai ba ya nufi barin É—akin.


Da sauri su Momy suka ƙarisa gabanshi, suna tambayarsa halin da Sans ɗin yake ciki.


"Da ransa bai mutu ba. Suna can suna aiki a kansa sosai. Mu taru mu saka Annur ɗinmu a addua, ita ya fi buƙata daga gare mu a daidai wannan lokacin ba wai kuka ba."


Yana gama faÉ—in haka ya koma bisa teburin da aka jera a reception É—in ya zauna haÉ—e da rafka uban tagumi, yana ta famar ambaton sunan Allah daga bakinsa.


Jin hakan ya sa su É—in ma suka É—an samu kwanciyar hankali. Amma duk da haka ba su daina yin kukan ba.


Hanan da Janan suka zauna kusa da Dady, momy kam zaman ya gagare ta, zirga-zirga kawai take hannunta tallabe da bayanta tana hawaye tana addu'a a bakinta.


*


Kanta ta ɗora a saman cinyarsa. Fuskarta ƙunshe da fara'a, ta jawo hannunsa saitin kanta tana faɗin,


"Mi Amor kai fa nake jira don Allah. Ka ringa bubbuÉ—a tsakiyar gashin kana duba inda ke da dandruff sai ka kankare min."


Saurarenta kawai yake, amma fa ba ya fahimtar komai, sai murmushin da yake saki shi ma ɗin. Ta san da hakan sarai, ta san cewa ba ya gane abin da take nufi, amma da gan-gan take komai, tana son ƙara kusancin zukatansu ne.


Tashi ta yi zaune haɗe da girgiza kanta, gashinta da ya barbazu bisa fuskarta ya koma ya kwanta har bisa gadon bayanta. Ribbon ɗinta ta sa ta ƙulle gashin, sannan ta shafa mai a gaba-gaban ya ƙara kwanciya, kwantaccen gashin goshinta ya kwanta luf.


"Yah Noor ka san me?"


Ya girgiza mata kai.


"Ina ƙaunarka sosai."


Ta saki sassanyan murmushi.


"Kai ma ba za ka ce kana ƙaunata ba?"


Ta ɗan turo baki alamun shagwaɓa. Kallon ta kawai yake tana daɗa birge shi. Sai dai kuma bakinsa ba zai taɓa iya furta yana son kowa ba face Amrah. Duk yadda ya buɗe baki da nufin faɗa wa Maryama cewa yana son ta, sai bakin ya gagara faɗi, ya ambaci sunanta da Amrah.


"Kana jin kunya ta ne? Well. Zo ga kunnena ka raÉ—a min a ciki. Don Allah for once dai ka furta min cewa kana so na. Zan ji daÉ—i sosai Mi amor"


Ta kanga masa kunnen nata, tana sauraren abin da zai faÉ—a mata. Ji ta yi ya yi murmushi a kunnen nata, ya ce,


"Amrah nake so!"


Janye kunnenta ta yi a fusace, ranta in ya yi dubu ya ɓaci. Ta fara jin haushi sosai, da kuma kishi da ke nuƙurƙusar zuciyarta. Ita kanta ba ta san yadda akai ta kamu da kishin matacciyar da ba ta duniyar ba ma.


"Yah Noor ba zan ƙara cewa ina son ka ba tunda har yau na gagara ka ambata kana so na. Haba don Allah! Kullum dai Amrah! Amrah! Amrah!? Ya kamata by now a ce ta fita daga ranka. Matar da ba ta duniyar baki ɗaya, amma ta gagara fita daga bakinka. Haba mana ka samu ka fitar da ita daga ranka ko za ka samu dawowa a cikin hankalinka..."


Ta kwantar da muryarta a daidai sadda hawaye ke fita daga idanuwanta, ta ce,


"Don girman Allah Yah Noor ka so ni koda rabi-rabin ƙaunar da nake maka ne. Ya kamata a ce ka farga, ka fitar da Amrah daga zuciyarka. No more Amrah in your life yah Noor. No more Amrah in this world. Amrah ta tafi inda ba a dawowa. Ta tafi inda mu ɗin ma za mu je mu same ta, amma ba dai ita ta dawo ta same mu ba. Na sani, cewa Amrah masoyiyarka ce ta gaske. Ka ƙaunace ta, kamar yadda ita ma ɗin ta ƙaunace ka. Kun yi soyayya ta tsakani da Allah, mai cike da tsafta da yarda da juna. Amrah was your first love, amma kar ka ɗauka cewa ita ce last love ɗinka. Saboda har yanzu kana da masu yi maka irin ƙaunar da Amrah ke maka."


Ta dakata daga nan, tana kuka sosai mai cike da tashin hankali, duniyarta na mata juyin waina, kamar yadda zuciyarta ke juyewa daga farin-ciki zuwa baƙin-ciki.


Kanta a duƙe yake ƙasa, tana sakin kuka mai cike da tashin hankali, kamar wasa ta ringa jiyo shessheƙar kukansa, ta gaggauta ɗago da kanta, ta ɗora idanuwanta a bisa kyakkyawar fuskarsa da ruwan hawaye ya gama wankewa.


Kallon sa take cike da mamaki. Me ya sa shi kuka? Ta tambayi kanta. Ganin yadda bil-haƙƙi yake kuka ne ya daɗa tayar mata da hankali. Kuka yake mai cike da tashin hankali, jikinsa na karkarwa, idanuwansa sun kaɗa sun yi jajur a cikin ɗan taƙi kaɗan. Ƙasa ya ƙura ma ido yana kallon wuri guda, hannunsa ɗaya dafe da kansa, ɗayan kuma ya ɗora a bisa cinyarsa, ya dunƙule shi.


Gyaɗa kanta ta hau yi, tare da ƙarfafa kukanta, tana faɗin,


"Ni ce? Don Allah ka yi haƙuri ka yafe min. Ban san cewa abun zai maka zafi har haka ba. Ba zan so Allah ya rubuta min zunubi ta dalilin saɓa maka ba. Wajibi ne a gare ni na faranta maka, na ba ka duk wani farin-ciki kamar yadda na yi alƙawari."


Ta dakata daga nan, ta ci gaba da binsa da kallo. Ji ta yi cikin sanyin murya ya fara magana,


"Amrah nake so! Amrah ce kaɗai a cikin zuciyata. Amrah me ya sa za ki min haka? Me ya sa za ki tafi ki bar ni? Ina ƙaunarki Amrah. Ke ce rayuwata. A kullum da ƙaunarki nake kwana nake tashi. Soyayyarki ke ɗawainiya da duk wata gaɓa da ke cikin gangar jikina. Ki dawo gare ni Amrah. Ki zo ki tallafi rayuwata Amrah. Ki zo ki bayyanawa duniya cewa ke kaɗai nake so, kamar yadda ke ma ni kaɗai kike so..."


Kuka sosai yake yi, a hankali yana tuno wasu abubuwan, wanda dama yakan tuno su, sai dai wasu lokutan da zarar ya tuno su, sai kanshi ya hau sarawa, tare da manta komai da ya fara tunowar.


Sosai take mamakin Annur. Sau da dama yakan yi abubuwa irin na masu hankali. Yakan yi kalamai masu sanyaya zukatan ma'abota soyayya. Duk yadda yake gwada yana son ta, lokaci kaɗan zai birkice mata, tamkar ma bai taɓa ganin ta ba. Abun nan yana ci mata tuwo a akushi. Tana shiga tsantsar damuwa a duk sadda irin hakan ta faru. Sai dai kuma tun da ta san shi, daga lokacin da ta ɗauko shi daga Maraɗi ta dawo da shi gidansu, ba ta taɓa ganin shi ya yi irin wannan kukan ba. Tabbas kalaman ba baƙi ba ne a gare ta, to sai dai abin da ya tayar mata da hankali yadda yake kuka riris, jikinsa na ta famar karkarwa.


Hannunsa ta kama duka biyun, ta damƙe su a cikin nata. Sosai take jin nutsuwa na saukar mata. A duk sadda za ta taɓa shi, sai ta samun sauyin yanayi irin haka. Sai ta ji yadda ƙaunarsa ke ɗaukar ta tana kai ta can wata duniyar ta daban, duniyar da masoya ne zallah a cikin ta.


Ji ta yi hannunsa zafi rau, saɓanin yadda ta taɓa su ɗazu sadda tana kwance a cinyarsa. Cikin damuwa ta ce,


"Ka gani ko? Ga shi nan wannan kukan da kake ya sakar maka zazzaɓi. Ka ji yadda jikinka ya yi zafi sosai Yah Noor. Don Allah ka daina kukan nan. Wallahi ba zan sake tayar maka da irin wannan maganar ba. Na maka alƙawari."


Bai daina kukan ba, sai dai ya rage ƴarfinsa. A hankali ta isar da gangar jikinta gare shi, ta haɗa jikinsu, tana jin yadda bugun zuciyarsa ke tafiya. Hannuwanta ta zira ta rungumi bayanshi, ta ɗora fuskarta a bisa kafaɗarsa. Ji ta yi nutsuwa na saukar mata, kamar yadda shi ɗin ma a nashi ɓangaren hakan ne. Shiru ya yi da kukan da yake yi, bugun zuciyarsa na daidaita, yayin da yake jin duniyarsa ta damuwa na rikiɗewa izuwa ta farin-ciki.


Jin ya dakata da kukan ya sa cikin saukar da murya ta ce,


"Ka san yadda zuciyata take ƙuntata a duk lokacin da zan ga ɗigar hawayenka ɗaya a bisa kumatunka? Ka san irin halin da nake shiga a duk sadda kake cikin halin ƙunci? Sosai nake shiga tararrabi a duk sadda zan gan ka takure alamun rashin walwala. Ka taimaka ka daina, matuƙar ba so kake a zo a kwashi gawata daga gidan nan ba."


Saukar ajiyar zuciyarsa kawai take ji. Tana jin yadda ya langaɓar da kansa a tata kafaɗar, ya sadaukar da kaf gangar jikinsa gare ta. Sun jima a haka, har sai da dukkaninsu suka samu wadatacciyar nutsuwa, kafin ta raba jikinsu da juna, ta ɗora idanuwanta a kan rinannun nashi idanuwan, tana bin sa da kallo.


Murmushi ta ƙirƙiro kafin a hankali ta ce,


"Ya isa to ai, komai ya wuce. Bari in tashi in kawo maka abinci."


Kanshi ya É—aga mata.


"To ai ban ga ka yi murnushi ba."


Muenushin ya saki wanda har sai da hakoransa suka bayyana. Sosai ta ji dadi, wani sanyi ta ji ya dira a cikin zuciyarta. Kai tsaye ta nufin kitchen domin ta kawo masa abincin.


Vegetable noodle ce ta dafa, kasantuwar ta dawo exam ne a ƙurarren lokaci, saboda yau suka fara kuma da guda biyu suka fara. A plate ɗaya ta zubo musu, ta duba pepper soup ɗin da ta ɗora a wuta saura ƙiris ruwan ciki ya ƙare. Da sauri ta gaggauta kashe gas ɗin, sannan ta zuba ruwa madaidaici ta motsa, ta kuma kunna gas ɗin amma ta rage ƙarfin wutar.


Fork guda É—aya ta saka a plate É—in, sai kuma ta É—ora spoon É—aya, ta nufi fitowa. A gabanshi ta ajje, sannan ta ce,


"Bari in kawo mana drink."


Ta koma ta É—auko kwalbar blue cocktail guda da cups guda biyu, ta fito.


A baki ta ringa ba shi abinci a hankali yana ci. Sai ya ringa kallon ta yana murmushi, tamkar ba shi ne ya gama rusar kuka yanzu ba.


Da haka har suka ƙoshi, ta zuzzuba drink ɗin a cup, da kanshi ya kai baki ya sha nashi, sai da ya shanye duka sannan ya ajje cup ɗin. Ita ma ta sha. Kwashe kayan ta yi duka, kafin ta dawo kusa da shi, ta gyaggyara wurin ta feshe da tangerine freshner. Bayan ta gama duka ta jawo handout ɗinta da take dubawa tun sadda take kwance a cinyarsa, ta hau dudduba kaɗan-kaɗan, shi kuma ta kunna masa kallo, tashar Zee World.


***


Kakkausan murmushi ta sakar masa a lokacin da ta same shi a É—akin. Da nashi murmushin ya tarbe ta, cikin idanuwansa nata idon suke, har sadda ta iso gare shi.


"Har bakin sun tahi?"


Ya tambaye ta, bayan ya haÉ—a jikinsa da nata.


"Uhm sun tahi. Sun ce ma in gaishe ka."


Ta ƙoƙarta ɓamɓare jikinta da nashi.


"Mi halan rowa za ki yi mini?"


GyaÉ—a kanta ta yi ta murmusa.


"Lokacin sallah dai yak kusan yi."


Ɗan taɓe bakinsa ya yi, ya ce,


"Hakanan hwa. Bari in nuhi masallaci to."


Ya miƙe haɗe da ɗaukar hularsa daga bakin gado ya saka.


"A yi min addu'a."


Hannunsa na dama ta kama ta saka a cikin nashi, ta ce,


"Allah ya sa a dawo lahiya. A yi mana addua."


"Insha Allahu. Amma wace iri kika son na yi miki?"


Sai da ta É—an yi shiru alamar tunani, kafin ta ce,


"Zaman lahiya da zuri'a mai albarka."


"To na yi alƙawarin zan yi. Amma hwa ni ma ina da buƙatar wani abu."


"Mi halan?"


Ta tambaye shi cikin yatsinar fuska.


"Kawo kunnenki ki jiya."


Ta kanga masa kunnen nata. Magana ya mata ƙasa-ƙasa, wadda duk iya ƙwa-ƙwar mutum ba zai taɓa jin abin da ya faɗa mata ba. Da alama dai zance ne na ma'aurata. Murmushi kawai ta saki haɗe da gyaɗa masa kanta, ta ce,


"To na jiya. A dawo lahiya."


Ya fice daga É—akin yana dariya, haka ita É—in ma dariyar take.


Kitchen ta nufa, farar shinkafa ce take dafawa, koda ta duba har ta dahu, ruwa kaÉ—an ne kawai bai tsane ba. Ta duba miyar ita ma ta dahu. Ta sauke sannan ta kashe reshore É—in. A flask ta juye miyar sanann ta bar ta buÉ—e don ta É—an sha iska. Kafin nan har ruwan shinkafar ya tsane, ta sauke shi ma ta kashe Æ´ar bouncing burner É—in, ta kwashe shinkafar a food flask babbar ta miyar.


Kafin Mahmouda ya dawo daga masallaci Fiddou ta gama shirya komai ta kai falo bisa kafet ta ajje. Dama ta yi wankanta, kaya kawai ta sauya, daga atamfa zuwa wata doguwar rigat roba, wadda ta kame jikinta. Kanta babu ɗankwali, sai yalwataccen gashinta da ta faka ya zuba har bisa gadon bayanta. Tana fitowa ta same shi ya dawo yana jiran ta. Da sauri ta ƙarisa gabansa tana masa sannu da zuwa.


"Madem ke yi kyau sosai hwa. Irin wanann kwalliya ai sai ki saka na kasa cin abinci."


Harararsa a wasa ta yi, ta ce,


"Aikam ba zan so mijina ya zauna da yunwa ba. Saboda haka bari in hanzarta zuwa in cire kayan in sako wanda ba za su hana maka cin abinci ba."


Ta nufi barin jikinsa. Jawo ta ya yi da hanzari, ta faÉ—o bisa jikinsa.


"Wa ya hwaɗi miki irin haka nake nuhi? Ai wannan kaya irinsu ne nake so ki rinƙa saka min duk sadda nake gida."


"To na ji. Ga abinci nan."


Ta ƙarisa bisa kafet ɗin, shi ma ya iso kusa da ita ya zauna. Serving ɗinsu ta yi. Ciyar da junansu suka hau yi cike da soyayya da ƙaunar juna, sai da suka ji su sun yi jim sannan ta kwashe kayan haɗe da dawowa.


"To kyan alƙawari cikawa. Na yi miki addua don haka ke ma sai ki cika naki alƙawarin."


Maficin hannunta ta duke sa da shi, ta ce,


"Halan dai ba ka gajiya?"


"Har abada! In dai da ke ne."


Miƙewa suka yi suka nufi bedroom maƙale da junansu.


***


Cike da shauƙin ƙauna take waya, tana yi tana ɗan lumshe idanuwanta, tana sakin wani tausassan murmushi. Tsabar jin daɗin wayar da take ya sa ta ringa tsigar stones ɗin lace ɗinta da aka ƙawata shi da su. Ita kanta ba ta san tana yi ba, har sai daga baya ta ankare. Cikin mamaki ta ce,


"D me ka san me ka ja min kuwa?"


"A'a J me sai kin faÉ—a."


"Uhm. In faÉ—a maka kaf stones É—in da aka ma kayan jikina ado da su na bi na cire du, duk ban san na yi ba sai yanzu na ankare."


Dariya sosai ya yi mai sauti. Ya ce,


"Ah to komai ya yi daidai. Hakan ya tabbatar min da cewa kina jin daÉ—in wayar da muke yi É—in."


"Uhm, to ni dai sai ka biya ni, tunda dai kai ne silah."


Cikin shagwaɓa ta yi maganar, har can cikin kunnuwansa ya ji dirar sautin nata.


Ya É—an lumshe idanuwansa, cike da bege ya ce,


"J me kin cika rigima. Na ji to zan biya ki. Just count, in the next 2 or 3 months zan ninka miki wannan É—in ma."


Tamkar tana a gabanshi haka ta harare shi, ta ɗora hannuwanta a daidai saitin zuciyarta, ji take yadda rijiyar ƙauna ke gudanya a cikin zuciyar tata, tamkar ta sa hannu ta yakito ta, ta gan ta da ido, ta yadda za ta ƙara azama wurin ƙaunarsa.


"D me ka san me?"


"Sai kin faÉ—a dai tukuna zan sani."


"Jiya bayan ka tafi Abbana ya kira ni. A gaban Mami ya ce wai ya ji daÉ—i sosai ta yadda ya gan ka mai ladabi da girmama na gaba da kai. Ya ce wai ya tabbatar ba zai yi asarar aura maka ni ba."


"J me am so much happy. Ashe har haka nake da daraja a wurin Abbah?"


"Ehh mana. Amma don Allah D me kar ka watsan ƙasa a ido. Kamar yadda kaken nan a yanzu, ina so ka ƙara azama wurin darajta iyayena. Sosai za ka ƙara siye zuciyar Jiddah..."


Bai bari ta ƙarisa ba da murmushi ya ce,


"Na riga da na gama saye zuciyar Jiddah. Kina nufin akwai sauran wata tsoka a cikin zuciyarki wacce ƙauna ta ba ta gama mamaye ta ba?"


"Babu."


Ta faÉ—a a hankali.


"I know, Jiddah. I've trust on you. Sosai na yarda da ƙaunar da kike min. Haƙiƙa ni ɗin na zama mai sa'ar rayuwa, da ya kasance cikin kwanaki ƙalilan na gama siye zuciyar matata Jiddah. Ina fatar ɗorewar wannan soyayya tamu, har jikokinmu."


"Ni ma ina fatar hakan Yayana. Abu É—aya ne kacal ya rage mana a yanzu kam."


"Mene shi?"


Ya gaggauta tambayarta.


"Wannan zazzafin kishin naka nake so ka rage shi D me. Na sani cewa ba abu ba

Please Login or Register in order to submit comment