You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ji ta yi ya ɗora fuskarsa bisa kafaɗarta, ya tsura mata idanuwa ta cikin mudubi. Kallon sa ta yi ita ma ta cikin mudubin haɗe da ɓata fuska cike da shagwaɓa. Ya janye fuskar tasa.


"Daure min fuska ma za ki yi ko?"


"Ehh mana."


Ta saki kakkausan murmushi.


Bai sake faɗin komai ba ya ji wayarsa na ƙara. Ya koma ya ɗauko ta daga bakin gado sannan ya yi recieving.


"I'll be on my way now, Dady. Na tsaya karyawa ne."


Ya juyo ya kalli Maryama.


"Dady ne. Wai in hanzarta. Ashe ma a jirgi za mu tafi, kuma ƙarfe goma jirgin zai tashi. Ki ga ikon Allah, jiya-jiyan nan ashe Uncle Marwan ya je ya binciko kuma aka yi sa'a akwai jirgin da zai tashi zuwa Maiduguri ɗin yau."


Maryama ta miƙe tsaye.


"To kuma ko karyawa fa ba ka yi ba a hakan za ka tafi?"


"To ya zan yi Baby? Pass 9 fa. Ni kaÉ—ai ake jira har Uncle Marwan ma ya kai Yamairah, dayake tare za mu tafi da ita."


"Ina zuwa to."


Ta nufi É—akinta.


Cakes irin na leda ɗin nan ta ɗebo masa guda huɗu. Sai ta ɗauki lemo ta saka a ledar ta miƙa masa.


"Ban yarda ka zauna da yunwa ba. Ga shi ka samu ka ci please. Sai yaushe za ku dawo?"


Ya ce,


"Ina tsammanin in dai mun samu yadda muke so to gobe ma mu juyo. Sai idan abun ya yi tsayi ne sai jibi, wanda ma ba mu fatar hakan."


"To yanzu Yaya ya za a yi? Mugunta ma ba ta bari ka faÉ—a min yadda zan yi ba?"


Ya mata hararar wasa.


"Ashe ma dai mugunta."


"Ehh mana."


Ya taɓe baki.


"Yadda zan yi da ke a me wai?"


"Ka san fa ba zan iya kwana a gidan nan ni kaÉ—ai ba. Ko in tafi gidanmu kawai?"


Cikin shagwaɓa ta yi maganar.


Ya jawo ta ya haÉ—a fuskokinsu wuri guda, har hancinansu na gogar na juna.


"A hakan ne za ki tafi gida? Ji fa ko tsayuwar kirki ta gagare ki yi. Idan na je yanzu zan turo miki Hanan da Janan, tunda har da Momy za a tafi, dama bai kamata a bar su gidan su kaÉ—ai ba. Kawai sai a rufe."


Ta jinjina kanta.


"Allah ya kawo su lafiya to."


Turaren oud ta fesa masa sannan ta taka masa har parking space. Da kanta ta buÉ—e masa motar ya shiga sannan ta rufe. Har ya fice tana É—aga masa hannu sannan ta juya zuwa cikin gidan.


Zama ta yi bisa 3 seater ta runtse idanuwanta. Wani irin farin-ciki take ji yana sauka a duniyarta. Ashe haka aure yake da daɗi? Sai yanzu ta gasgata. Musamman ma dai mutum ya auri wanda yake so yake son sa. Sai ka ji tamkar babu yakai a duk duniyar ma. Ta sakar ma kanta murmushi bayan ta buɗe idanuwanta. Abubuwan da suka wanzu tsakaninta da Annur a daren jiya ne suka hau dawo mata a ka. Kunyar kanta ta ji, ta saka tafukan hannayenta ta kare fuskar, sannan ta miƙe domin gyaran gidan.


Yana isa ya samu duk sun hallara shi kaÉ—ai ake jira. Sai suka masa uzuri saboda sun san ango ne. Yadda ake bin sa da kallo bayan ya gaishe su kuma duk sai ya ji kunya.


Sans ya dafa masa kafaÉ—a.


"Ango ka sha ƙamshi."


Ya faɗa ƙasa-ƙasa, yana sakin murmushi. A take kuma sai ya tuno da alƙawarin da Farouk Sardauna ya nemi ya cika masa, na cewa ya auri Maryama. Ga shi bai samu damar cika alƙawarin ba, amma ɗan uwansa ya cika masa. Ya kuma sakin murmushi da ya tuno wasu abubuwan da suka faru a tsakaninsa da Maryama. Ƙaunar da ya yi mata daga kallo ɗaya , yadda ya gagara fitar da ita daga zuciyarsa har sai da boka ya masa aiki a kanta. Sai kuma ya tuno ranar da ya je har ƙofar gidansu ɗin nan.


"Yaya ina kwana?"


Yamairah ta gaishe da Annur cikin ladabi. Dama tun isowarta suka gaisa da Sans cike da ƙaunar juna, tana jin yadda ƙaunarsa ta shiga zuciyarta a lokaci guda, duk sai ta ji kewar iyayenta ta ragu daga cikin zuciyarta.


"Lafiya lau ƙanwata. Kin tashi lafiya?"


"Alhamdulillah."


"To madalla. Ina su Hanan ne?"


Momy da ke daidai fitowa ta ce,


"Suna É—aki Annur. Ka iso kenan."


Ya sosa ƙeyarsa.


"Na samu isowa Momy. Dama cewa na yi ko za a tura su Hanan ne wurin Maryama? Na ga su É—in ma bai kamata su zauna su kaÉ—ai ba. Ga ta ita ma can ita kaÉ—ai."


"Ehh gaskiya bai kamata ba. Amma kana ga kamar babu takura a tura wa Maryama su?"


Ya É—aga mata kai.


"To ai shi kenan. Kawai sai ka shiga ka sanar da su su shirya É—in."


Ƙarfe goma saura kwata suka rankaya zuwa Airport. Goma da minti biyar jirginsu ya tashi. Mintuna arba'in suka saukar da su a babban Airport ɗin garin Maiduguri.


Taxi biyu suka tsayar drop. Dady ya ce da su FMC yake so a kai su. Kai tsaye aka nufi can É—in da su. Bayan sun sauka suka sallame su, sannan suka rankaya zuwa cikin asibitin.


Maternity suka nufa, a baki-baki su Dady suka zazzauna bisa benci. Sai Momy da Yamaira suka ƙarisa cikin labour room ɗin, ta baro Yesmeen wurin Babanta. Daga farko ba a bar su shiga ba, saboda labour room ba wurin shige-da-fice ba ne. Sai suka musu bayanin abin da yake tafe da su sannan suka shiga ciki.


Inda ke da tarin takardu aka nufa da su. Momy ta faÉ—i exact date É—in haihuwar su Annur, sannan aka hau bincikar takardun. Ba a wani sha wahala ba aka gano, tunda komai jere yake an saka tambarin shekarar a jiki. Files guda goma sha É—aya ne ta É—auko, alamun a ranar yara sha-É—aya aka haifa kenan.


A hankali aka ringa dudduba kowanne. Sai a na uku da buɗewa ta ga sunan shereefah a jiki. Dukkaninsu sai da gabansu ya faɗi a daidai lokacin. Aka duba sunan wacce ta karɓi haihiwar, sunanta Sister Feenah, amma an rubuta cewa har da taimakon Dr. Rita, kasantuwar ba nace guda ke karbar haihuwar ba. Kuma twince ne ta haifa amma a lokacin na farkon ya rasu. Aka ajje file ɗin daga gefe sannan aka ci gaba da neman na Momy. A na biyun ƙarshe aka ga nata sunan a jiki. Ita kuma Sister Rita ce ta karɓi haihuwarta da taimakon Sister Feenah. Matar da ke duba musu ta ce,


"Sister Rita Stephen ce ta karɓi haihuwar. Sai dai kuma ta ɗan jima da yin retire gaskiya."


Gaban momy ya faÉ—i. Ta ce,


"Please ba ki san a inda za mu same ta ba?"


Ta É—an yi shiru jim! Kafin ta ce,


"Ehh to, da dai na san tana da wata babbar chemist a kusa da asibitin da mijinta ya buÉ—e, dayake ko sadda asibitin nan take a Bama to ita gaskiya nan garin take aure, weekend ne dai take zuwa wurin mijinta, a yadda na ji labari. Amma yanzu ba zan ba ku tabbaci ba gaskiya, don na jima rabon da in ji wani labari a kanta ko kuma in gitta ta asibitin. Sai dai ko na rubuta muku address na asibitin, sai ku je ko za ku dace."


Momy suka miƙe jiki a saɓule. Godiya suka ma matar bayan ta rubuta musu address ɗin a paper suka tafi.


Suna fita duk su Dady suka mimmiƙe. Tambayarsu suke yi yadda ake ciki amma Momy ta ce musu babu nasara. An dai basu address na matar da ta karɓi haihuwar tasu, wata ƙila su dace.


Dady ya ce,


"Tunda dai mace ce. Dole ku za ku jagoranci komai. Kai Alhaji Marwana ku je ku sama mana Hotel, alah-bishi mu sai mu je neman nata da Suhailah da kuma Yamairah. Idan mun gama sai mu yi waya da ku mu same ku."


Yamaira ta ce,


"Dady mu banda mu ni da Momy. Na kira Ummi na faÉ—a mata ni zan sauka a gidanta, Momy kuma sai a turo driver daga gidan su Ummi É—in a kai ta can ta kwana."


"Babu damuwa dai ko?"


Dady ya faÉ—a yana kallon Yamaira.


"Babu damuwa insha Allahu."


"To shi kenan ai. Annur ku tafi. Duk yadda ake ciki zan rinƙa kiranku a waya."


Daga nan suka tsayar da abun hawa. Su Annur suka ce a kai su hotel mai kyau, Momy kuma ta faÉ—a wa dreban address na waccan asibitin sannan suka tafi.


A gaban asibitin ya dire su. Daga gefensa suka hangi RS Pharmaceutical, hakan ya ba su tabbacin chemist ɗin ne na Rita. Suka sallami mai mota sannan suka taka zuwa cikin chemist ɗin. Babbar chemist ce, hakan ya sa take da maaikata a cikinta wanda aƙalla za su kai mutum huɗu. Sallama Dady ya yi sannan ya ba wani hannu suka gaisa kasantuwar ya ga alamun musulunci a tattare da shi, tafkeken tabon sallah da ke goshinsa, da kuma counter da ke maƙale a ƴar yatsarsa yana tasbihi.


Amsa sallamar ya yi, Dady ya ce da shi suna tambaya ne.


"Don Allah nan ne chemist É—in Sister Rita Stephen, wata tsohuwar maaikaciyar FMC?"


Matashin ya ce ehh nan ne, suna da buƙatar wani abu ne?


Nannauyar ajiyar zuciya suka sauke su duka ukun. Momy ta yi saurin faÉ—in,


"Don Allah a ina za mu same ta?"


"Tana gidanta. Amma takan zo nan chemist É—in a irin ranar yau. Bari na kira muku ita."


"Godiya muke."


Dady ya faÉ—a cikin murmushi.


Bayan ya kira ta ta ɗauka. Yake tambayarta za ta samu zuwa yau kuwa? Ta ce da shi wani abun ne? Ya ba ta amsa da baƙi ne suka zo neman ta. Wayar ta ce ya ba baƙin ta ji ko su waye. Momy ta karɓa suka gaisa cikin sakin fuska. Ta mata bayani cewa ta taɓa karɓar haihuwarta ne, to wata magana take so su yi da ita. Cewa ta yi su jira ta a nan ga ta nan zuwa yanzu.


Matashin mai suna Ibrahim ya basu wurin zama, sannan ya bayar aka siyo musu ruwan roba. Godiya sosai suka yi masa.


An ɗauki kusan tsawon awa ɗaya sai ga Rita ta iso. Kallon ta Momy ta yi sosai. Tabbas ita ce. Kamanninta ba su sauya ba, sai dai dattijanta kawai da ta yi. Tana ganin Momy ta ƙwalalo ido tana mata kallon sani. Da hannu ta rinƙa gwada ta tana son ta tuno sunanta. Momy ta tare ta da faɗin,


"Mrs. Suhaila IA..."


"Ezactly"


Rita ta faÉ—a haÉ—e da rungume Momy. Sai kuma kuka daga nan. Momy ta raba jikinsu tana tambayarta me take wa kuka?


"Its a long story Suhaila. I did the wrong things to you. I dont thing you can forgive me."


Cike da mamaki suke kallon ta. Ta ce da su su bi bayanta zuwa ƙuryar chemist ɗin, inda tarkacen kwalaye ne kawai a ciki. Cikin kuka ta ce,


"I've been waiting for this day, ranar da Allah zai haɗa ni da ke, na faɗa miki wani ɓoyayyen al'amari da babu wanda ya san shi, daga ni, sai Sister Asabe sai kuma Alhaji Abubakar Abu Sardauna."


Komawa baya.


Bayan Suhaila ta haihu, yaron da ta haifa pre-tamp ne bai isa haihuwa ba. Sai ya zamanto ba shi da lafiyar kirki, har numfashinsa ma ba ya fita da kyau, da alama ma yana da pneumonia. Ita kuma Shereefa ta haifi yaro guda, kamar dai yadda labarin ya zo a baya. To bayan Nurse ɗin da ta karɓi duty daga hannun Rita ta tabbatar wa Suhaila cewa ga yaronta nan, ta ma yi mamakin yadda numfashin nasa ya koma daidai, kamar ma bai taba yin ciwon ba. Suhailah ta koma resting room, shi kuma ainahin yaron da ta haifa ɗin aka saka shi a kwali a tunanin Rita ya mutu. Ganin halin da Shereefa ke ciki na naƙuda, kawai sai Sister Asabe ta yi tunanin ta miƙa gawar yaron ga mahaifinsa, tunda yana waje zaune. Dubawar da za ta sake yi, sai ta ga yaro na fitar da numfashi sama-sama, alamar da bai mutu ba. A tsorace ta sake duba shi, nan ta sake tabbatar da cewa fa yaron yana da rai. Ba ta yarda ta faɗa wa kowa ba, tunda babu wanda ya gane cewa yaron da ran shi. Sai ta latsa kiran Alhaji Abubakar Abu Sardauna, bayan ta lelleƙa ta ga babu mai kallon ta. Yana ɗauka cikin murya ƙasa-ƙasa ta ce,


"Alhaji where are you now?"


Cikin muryar damuwa ya ce,


"Sister ba mu da wani zaɓin da ya wuce mu tafi da gawar ƴarmu. Ga mu nan a gida yanzu haka ma mun iso, zan tattara mutane a yi shirin yi wa ƴarmu wanka a kai ta ƙabarinta."


Ta sake lelleƙawa ta ga babu mai kallon ta. Ta ce,


"In da hali ka dawo yanzu da gawar. Na samar maka yaro."


Ya ƙwalalo ido cikin mamaki, kafin ya faɗi komai cikin hanzari ta zayyane masa yadda abin ya faru, cewa iyayensa sun yi zaton ya rasu. Kamar ba zai yi ba dai ya ce,


"Sister bakya tunanin faruwar wani abu a gaba?"


Ta ce,


"Idan har ka ga wani abu ya faru to tabbas ba ka ba ni wadatattun kuɗi ba ne. Amma matuƙar ka bani, to tabbas maganar za ta kasance a lulluɓe. Tsakanina da Sister Rita da kai ne kawai, ita ma ɗin don ya zama dole sai ta ji, tunda dai ta san cewa ƴar da ka haifa mace ce, tunda kafin ta tafi ne kuka bar nan, sannan kuma ta san fuskar wannan jinjirin."


Alhajin ya jinjina lamarin, sannan ya ce ga shi nan zuwa yanzu, amma ta yaya zai shigo da gawar yaron?


Ta ce,


"Abu ne mai sauƙi wannan, zan kira Rita yanzu. Idan ka iso dai just call me."


Ya tsinke wayar. A ranta tana nazarin dukiyar da za ta samu ta wannan hanyar. Ta san tsawon lokacin da Alhajin ya É—auka yana son haihuwa saboda unguwarsu guda. Sai ga shi Allah ya ba shi ita, kuma lokaci guda Æ´ar ta rasu. Ta yi murmushi sannan ta kira Rita a waya.


Bayan Rita ta É—auka ne ta mata bayanin abin da ke faruwa. Rita ta yi dariya, ta ce,


"Sister Asabe kin fi ni son kuÉ—i fa."


"Sister Rita to wa ya ƙi kuɗi? Yanzu dai ina so ki faɗa min yadda za a yi a shigo da gawar yarinyar, da kuma yadda za a fita da wannan jinjirin mai rai."


Rita ta ce,


"Bari in zo kawai. Zan zo da sisterna, na san me za a yi after that."


Babu jimawa Rita ta iso ita da ƙanwarta da ta umurta ta ɗauko showel na goyo. Isar ta ta yi daidai da isar alhaji Abubakar. Sister Asabe ta haɗa su ta waya. Bayan Rita ta karbi gawar yarinyar, sai ta ba ƙanwar tata ita ta goya kamar mai rai, sannan ta laɓe daga nesa, ta ce da ita ta nufi labour room kai tsaye ta ce wurin Sister Asabe ta zo.


Abin da ya faru ɗin kuwa kenan. Tana zuwa aka kai ta inda Asabe, ta ma wacce ke zaune wurin wayo ta tashi, sannan ta lelleƙa ta ga babu mai kallon ta. Ta fiddo yaron daga cikin kwali, wanda har yanzu bai daina fitar da numfashi sama-sama ba. Ta gaggauta saka gawar yarinyar a cikin kwalin, ta mata kwanciyar ruf da ciki wai don kar a gane cewa mace ce. Cikin rawar jiki yarinyar ta tafi, kallo guda za a mata a tabbatar cewa ba ta da gaskiya.


Tun daga nesa Rita ta iso ga ƙanwar tata tana mata murmushi. Kai yarinyar ta ɗaga mata alamun sun yi nasara. A tare suka isa wurin Alhaji Abubakar.


"Alhaji ga yaro. Amma sai ka hanzarta ka kai shi asibiti, saboda ba shi da wadatacciyar lafiya."


Ya ce,


"Zan kai shi private hospital a ba shi first aid, in ya so ya ji sauƙi sai na fidda shi waje."


Ya buɗe dash board na motarsa. Kuɗi ne bandir na ƴan dubu dubu har guda uku. Ya miƙa wa Rita, ya ce nasu ne su kaɗai, zai sallami Asabe daga baya, tunda dai dama can ya san ta, sun taɓa zama a unguwa ɗaya. Suka masa godiya sannan ya tafi. Matarsa da ta karɓi yaron sai kallon sa take yi.


Gawar wancan yaron kuma saboda tashin hankalin da mijinta Shereefar ya shiga, bai tsaya duba gawar ba kawai ya damƙa ta ga wani ɗan uwansa da ya zo, ya ce a sallaci yaron tunda an jima da haihuwarsa, shi zai tsaya nan har Shereefar ta ƙarisa haihuwa.


Yadda abun ya kasance kenan, wato dai su kansu su shereefar ba ainahin É—an Suhailah ba ne aka ba su. Mace ce ma É—iyar wani mutumin na daban.


Washe gari bayan Rita ta dawo aiki, take dudduba record na yaran da aka ɗora a gadon auna lafiya jiya. A nan ta ga sakamako, cewa yaron nan mai pneumonia shi ne asalin yaron Suhailah, saboda ta san cewa yaron Suhailar ne ta haifa pre-tamp, wanda har numfashinsa ba ya fita daidai, to kuma sakamakonsa shi ne ya yi daidai da wanda ke hannun Alhaji Abubakar sardauna. Shi kuma wanda aka rubuta sunan mahaifiyarsa Suhailar a ƙasa, lafiyayye ne, ga kuma hotonsa a jiki, shi ne asalin ɗan da Shereefa ta haifa.


Ta dafe kanta tana tunanin mafita. Ita kanta ta san akwai kuskure cikin lamarin. Ta tabbatar cewa ainahin yaron da Shereefah ta haifa ne zai ci gaba da rayuwa a gidan Suhaila. Shi kuma na Suhailah da ta haifa, shi ne a hannun Alhaji Abubakar, sai aka ba Shereefa gawar Æ´arsa a matsayin shi ne É—anta da ya rasu.


"Wannan shi ne ainahin abin da ya faru Mrs. Suhaila. Na jima ina neman inda zan haɗu da ke na roƙi gafararki. Su ma su Shereefa na neme su ban samu ba. Sannan kuma na tona asiri, kasantuwar nadanar da na yi, na tabbatar cewa ba mu aikata daidai ba. Son kuɗi da neman duniya ne kawai ya ja mana aikata wannan babban kuskure, sai ga shi kuɗin ko daɗewa ba su yi ba, banza da wofi suka ƙare."


Ta ƙarisa maganar tana kuka sosai, kukan nadama.


Ita kanta Momyn kukan take yi. Tana jinjina mummunan hali irin na Rita da Asabe. A kan dubu É—ari uku da wani abu ne suka yi wannan aika-aikar.


Cikin kuka ta ce,


"Ba ku kyauta ba Rita, ba ku mana adalci ba. Babu babban mugu kamar shi Alhaji Abubakar ɗin da ya karɓar mana yaro, bayan ga gidajen marayu can idan ya so zai iya zuwa ya karɓo yaro duk irin wanda yake so."


Dady ya dafe kansa cikin jinjina lamarin. Ya ce,


"Yanzu dai kenan yaronmu yana wurin Alhaji Abubakar Abu Sardauna."


Rita ta É—aga kanta tana kuka.


"Please forgive me Alhaji. Na san ban kyauta ba, and I've regret it. Ku yafe min, don Allah ba don ni ba."


Dady ya gyaÉ—a kansa.


"Shi kenan ai, ya wuce sai mu tari gaba."


"Na gode Sir. Bari na ba ku contact na Alhaji Abubakar. Zan fara kiransa na masa bayani, ku ma sai ku kira shi. Idan ya musa har kotu zan iya zuwa na fallasa shi, in ya so ni ma a kama ni, saboda na san ban aikata abun kirki ba, daga ni É—in har Asabe."


Ta zaro wayarta daga hand bag ta hau neman lambar tasa.


"Har bayan wannan case ɗin mun yi waya da shi, saboda ya ji daɗin abin da muka masa ya karɓi lambata daga wurin Asabe. Sai dai bayan an yi kamar shekara biyu da faruwar abun, bai sake nema na ba, kamar yadda ni ma ɗin ban neme shi ba."


Ta latsa kiran nasa. A kashe ta ji, hakan ya sa ta sake kira, nan É—in ma dai ba ta samu ba.


Dady ya ce,


"Ba ni lambar tasa kawai, in ya so ko daga baya ne idan ya buÉ—e wayar sai ki sake kiransa. Ni ma zan yita gwadawa har a dace."


Bayan ta ba shi lambar ne suka miƙe za su tafi. Sosai Momy ke jin haushin ta. Sai dai yadda ta ga babbar mace kamar ta ta dage rusar kuka tana musu magiya, har ƙasa ta duƙa tana roƙonsu su yafe mata. Hakan ya sa ta ce sun yafe mata ɗin.


Da haka suka rabu, Yamairah dai ba uhm ba uhm uhm. Mamakin al'amarin kawai take yi. Shiru ya ratsa tsakaninsu har suka tsayar da taxi. Yamaira ta kwatanta masa gidan Ummi sannan suka tafi.


Wayar Dady ce ta yi ƙara. Ko da ya duba sai ya ga Sans ne ke kiransa, kasantuwar Annur babu waya a hannunsa. Ya ɗauka cikin sassanyar murya. Sans ya tambaye shi yadda ake ciki, ce masa kawai ya yi


"Ainahin É—an namu wai yawa wurin wani mutumi Alhaji Abubakar Abu Sardauna."


Cike da mamaki Sans ya miƙe tsaye, idanuwansa a buɗe. Ganin haka ya sa Uncle Marwan da Annur ma suka miƙe suna tambayarsa lafiya. Jin shiru ya sa Sans ya ce,


"Ga ni nan zuwa dai zan muku bayanin komai. Ya sunan Hotel É—in da kuka sauka É—in?"


Da ƙyar ya iya tattaro maganar ya faɗa wa Dady sunan Hotel ɗin, sannan ya kashe waya.


Uncle Marwan ya ce,


"Ba ka mana bayanin komai ba Salman."


Sannan ya koma ya zauna. Ya ce,


"Wai yaron yana wurin Alhaji Abubakar Abu Sardauna."


"Subhanallahi! To garin yaya haka?"


Annur ya ce,


"Abun tambayar kenan Uncle."


Sans ya ce,


"Ba wannan nake wa mamaki ba."


Duk suka tsura masa idanuwa.


"Ina jin sunan nan a bakin Farouk Sardauna kafin ya rasu, wai Yayan babansa ne haka."


"Banda abun ka Salman, ka sani ko sunan ne ya zo É—aya?"


Bobby ya ce,


"Kuma Uncle sai duka sunayen a jere ya zamto guda? Baban Farouk É—in ma kansa sunansa Alhaji Usman Abu Sardauna, amma Alhaji Usman Sardauna kawai ake ce masa."


Ya kuma zaro idanuwa.


"I can remember something. Cikin ciwon Farouk ya tsananta, na rinƙa jin wasu kalamai na fitowa daga bakin Dadynsa. Haka kuma bayan ya rasu ma, na ji shi yana cewa wai ya kasa cika alƙawarin da ya ɗaukar wa yayansa na riƙon Farouk yadda ya kamata, bai ba shi kyakkyawar tarbiyya ba."


Duk suka bi shi da kallo.


"Kuma na ji shi yana cewa wai Farouk ya bi mariƙinsa na ainahi inda ya tafi (lahira). Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Kar dai a ce Farouk ne ainahin ɗan da su Momy suka haifa."


Annur ya ce,


"Wanene Farouk Sardauna?"


Sans ya ce,


"Wani abokina ne da ya rasu. Wanda ya fara taimakona bayan na shigo garin Katsina."


Uncle Marwan ya ce,


"Yadda za a yi, idan kana da lambar wayar Alhaji Usman É—in, sai Dadynku ya kira sa idan ya dawo. Saboda zai fi kamata a ce daga bakinsa maganar ta fito."


Sans ya ce,


"Ina da lambarsa Uncle. Lallai al'amarin Allah ba ya taɓa ƙarewa. Farouk Sardauna ɗan su Momy ne?"


Alhaji Marwan ya ce,


"Tukuna dai, ai ba mu gama tabbatarwa ba. Dalilin da ya sa na ce ka kira shi ɗin kenan. Idan muka ji daga bakinsa same da wannan, to sai mu tabbatar da komai, ka ga gobe sai mu juya zuwa Katsina. Idan kuma ba shi ɗin ba ne, dole mu bincika mu gano ainahin wanda ya karɓe shi ɗin, sannan ko muna tunanin tafiya."


Annur ya riƙe haɓarsa, ya jinjina girman lamarin Ubangijinsa.


Wayar Sans ce ta yi ƙara, sai ya yi zaton ko Dady ne, yana dubawa ya ga lamba ce da bai san ta ba. Da sallama ya ɗauka haɗe da karawa a kunnensa, muryar Maryama ya ji ta yi sallama, yana ji ya gane muryar tata. Tun ranar da ya baro gidansu ɗin nan dama ya goge lambarta daga cikin wayar tashi.


"Mai miji, na dai san shi kika kira nema. Ga shi to."


"Yaya Salman..."


Ta faÉ—a cikin kunya. Shi ma Annur É—in da kunyar Uncle Marwan ya gaggauta fita. Yana faÉ—in,


"Ta kasa haƙura dole sai ta ji muryar mijinta."


"Ah to ya son ranka. Dole na kira na ji lafiyar mai gidana. Na kuma ji da Æ´an mata nawa ya yi magana yau?"


Ya É—ora hannunsa a goshi alamar tunani.


"Ina ji duka ba za su wuce goma sha biyar ba. Ai ban yi da yawa ba ko?"


Ta harare shi tamkar yana kusa da ita ne.


"Ai da sai in biyo ka da yammacin nan, in ji dalilinsu na kallar min miji har suka yi magana da shi."


"Lallai ma yarinyar nan. Ba wannan ba. Ya lafiyar iyalina?"


"Suna lafiya ƙalau. Ya gajiyar tafiya? Fatar dai an dace."


Annur ya É—an yi jim kaÉ—an, kafin ya ce,


"Dady dai bai dawo ba tukuna, dayake mu muna hotel ne. Amma na ji shi yana waya da Salman, wai wani Farouk Sardauna shi ne asalin É—an nasu..."


Tun bai rufe baki ba Maryama ta jeho masa tambaya.


"Wane Farouk Sardauna? Bobby dai da ya rasu wanda na sani?"


"Ehh, shi fa. Don na ji Salman ya ce wai ya rasu. Amma dai ba mu gama tabbatarwa ba tukuna. Sai Dady ya dawo zai kira Baban Farouk

Please Login or Register in order to submit comment