You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

k'il dai mai kama irin ta shi ce kika gani."


Mik'o min wayar ta yi, ta ce,


"Umma sake duba shi dai sosai. Na yi mamaki ki ce wai baki ta'ba ganinsa ba.


Wallahi Umma duk ganin da nake masa a tare da ke ne.


Har ma fa akwai ranar da ya gaishe ki, kin dai manta ne kawai."


Kallon mamaki kawai muke binta da shi, saboda yanda muke jin zancen nata kamar a wasa, ga ta ita kuma da gaske take, har tana dagewa rantsuwa.


"Umma ashe dama shi ne Ya Noor d'in. To ni dai gaskiya na yi fushi da shi.


Ashe yana ganina kuma baya min magana ko? Bayan kuma ya san ina cike da kewarsa, ina son ganinshi sosai." Ta b'ata fuskarta cike da damuwa.


Kamo ta na yi na zaunar a kusa da ni,


"Amrah! Ki cire tunanin Annur ne kike gani a asibiti.


Na fad'a miki cewa ba shi ba ne, Annur baya k'asar nan fa.


Kin san ana kamanni a duniya, ta yiu ke kamarsu ce kika gani, bare kuma wannan a hoto ne.


Dan haka ki daina wannan tunanin, ta ya Annur da yake mararin ganinki, kuma zai ganki ya share ki?


Wannan ba abu ne mai yiuwa ba."


Haka na ci gaba da k'ok'arin ganar da ita gaskiya, amma fa sam ta k'ek'ashe ta k'i yarda da maganata. A k'arshe dai ta nunar min da ta yarda, wanda a zahirin gaskiya ba yarda d'in ta yi ba kuma.


Haka dare ya yi na ringa juya maganganun Amrah, ban san dalili ba, haka kawai na saka ma kalaman nata alamar tambaya, ta yanda kallo d'aya ta ce ta san shi, kuma har take rantsuwa cewa wai ya tab'a gaishe ni.


Washe gari da safe ta yi shirin makaranta. Wata makaranta ce a can k'asan layinmu ta gwamnati take, yanzu haka tana primary 6 ke nan.


"Abba baka kira min Yaa Noor d'in ba fa, kuma kai ka ce yau da safe zaka kra min shi kafin na tafi makaranta."


Da murmushi Mallam ya ce,


"Ai kin ga yanzu fa makaranta zaki je Amra, insha Allahu na miki al-k'awari idan kin dawo zan kira miki shi, tun da akwai kati da kuma lambar wayarsa a nan ciki."


"Oya ki yi ki kammala shan kununki ko? K'osan ya ishe ki?" Na tambaye ta.


"Ehh, ya ishe ni Umma. Na gode."


Bayan ta gama ta zo na saka mata al-barka kamar ko yaushe, na ce,


"A yi karatu da kyau 'yata. Ina miki fatan alkhairi. Allah Ya miki al-barka."


"Amin Ummana. Bara in tafi."


Ta sab'i jakar makarantarta.


Bayan ta kusa isa zaure, ta juyo ta d'ago min hannu tana murmushi, wanda wannan d'ago hannun da ta yi, kawai sai na samu kaina da samun rashin kwanciyar hankali.


Take gabana ya hau dukan uku-uku. Na d'aga nawa hannun ni ma ina d'aga mata har ta fice.


Kallon Mallam da ke shan koko na yi, cikin wata murya mai nunar da fargaba ko kuma shakku, na ce,


"Mallam, kawai sai na samu kaina da rashin kwanciyar hankali a kan tafiyar yarinyar nan. Hankalina ya tashi ban san dalili ba."


Murmushi ya yi, ya ce,


"Murja ke nan. Ban san sai yaushe zaki cire ma ranki irin wannan tunane tunanen marassa ma'ana ba.


Ko kin manta addu'ar iyaye ce a kan Amrah?


Fita goma zata yi daga gidan nan sai kin saka mata al-barka, sannan kuma ki mata fatan al-khairi.


Kin ga kuwa, ai bai kamata ma ki saka wani tunani a ranki ba.


Kin san shi shaid'an ta ko wace hanya yana bi dan ganin ya dagula wa mutum lissafi.


Ki yi ta'awizi ki kore shaid'an, a duk lokacin da tunani irin wannan ya fad'o miki."


Kalaman Mallam suka sa na ji wani sanyi a zuciyata, na kuma samu kwanciyar hankali d'ari bisa d'ari.


"Maganarka gaskiya Mallam. Duk wanda al-barkar iyaye ke biye da shi, to tabbas baya tab'ewa.


Ko da a ce wani abu zai same shi, matuk'ar ya rik'e adhkar d'insa, sannan iyayensa na saka masa al-barka, ko ma me zai same shi, zai zo masa da sauk'i.


To bare kuma Amrah, yarinya 'yar shekara goma, wadda a kullum burinta shi ne ta ga ta faranta mana rai.


Ba wai dan Amrah tana tawa ba, amma wallahi zan iya cewa tun da nake a rayuwata, ban tab'a ganin k'aramar yarinya mai kyawawan halaye da d'abi'un kirki kamar ta ba.


Dama dukkan hani ga Allah baiwa ne, na gasgata wannan zancen.


Gata dai yarinya mara wadatacciyar lafiya, Allah Ya rage ta ta fannin lafiya, amma kuma sai ya wadatar da ita da halaye na gari.


Ina mata fatan d'orewa da wannan halaye nata, wanda nake fatan ko bayan babu ita a doron k'asa, zata zama abar koyi da kuma al-fahari ga al-ummah."


Daga nan wani irin kuka ya kufce min, wanda na rasa gane ko na me nene.


Ajiyar zuciya Mallam ya sauke,


"Haka ne Murja. Amrah kam sai dai mu dad'a godiya ga mahalicci.


Ga ta da k'walwa, tun daga b'angaren Islama har b'angaren boko d'in.


Ta zama yarinyar da duk wani abun da za a yi da ya danganci masu k'ok'ari, to ita ce farkon da za a saka a lissafi.


Idan wata gasa ce za a yi da ita a ciki,


Musab'aka har ta k'ananan hukumomi ta je, ta wakilci Katsina Local Government, sahun 'yan izib goma.


Duka wannan halaye nata sun ginu ne ta dalilinki Murja. Ke ce kika d'ora ta a bisa wannan tafarkin na kirki.


Tabbas! Samun uwa ta gari kamar ki sai an tona, ke jajirtacciyar mace ce, abar al-fahari kuma abar kwatance."


Du'kar da kaina na yi ina wasa da warwaron hannuna, ina k'ara jin tausayin Amrah a cikin zuciyata.


Ba dan komai ba sai dan kasa gafartawa kaina da na yi, saboda na san tabbas mu ne sila, ciwon Amrah tamkar mu ne silarsa.


Tun da inda a ce tashin farko mun yi abin da ya dace kafin aure, da duk hakan bata faru ba.


Sai dai kuma k'addara ta rigayi fata, kamar yanda Dr. Xarah ta fad'a mana.


Da wanann tunanin na mik'e, na tattaro kayana da na Amrah masu datti, zan wanke su.


Mallam ya ce,


"Na ji fa ta rok'e ki al-farmar kar ki yi wankin nan har sai ta dawo ku yi tare, shi ne kuma kika fiddo zaki yi?"


Ajje kayan na yi a k'asa sannan na ce,


"Wahalar da yarinyar nan ke yi ce nake ga kaman zata yi yawa Mallam.


Ka ga fa Dr. Xarah ta hane mu a kan saka ta aiki da yawa, musamman ma wanda k'asusuwanta zasu yawaita motsawa.


Shi ya sa ba zan sake barinta ta yi wanki ba. Girki da shara dai da ba wani wahala ne da su ba, sai in ringa taimaka mata wurin yinsu."


"Ehh to, haka ne kuma.


Ni bara in tashi in nufi wurin k'wadago. A yi min addu'a."


Kallonsa na yi da murmushi na ce,


"Allah Ya kare ka da kariyarSa mafificiya.


Allah Ya baka ikon ciyar da mu da halal.


Fatan al-khairi."


"Ameen." Ya fad'a had'e da tafiya.


Misalin k'arfe sha biyu na gama komai, har gyare-gyaren gida duka na yi.


Muroyoyin yara na ji ana hayaniya sosai, kuma abun na k'ara kusantowa a cikin gidanmu.


Saurin mik'ewa na yi jin sun shigo daga zauren gidan, wasu ma har sun iso daga ciki.


Ko da suka k'ariso na tambaye su, lafiya?


Wata yarinya 'yar za'kal d'insu ce ta yi caraf ta ce,


"Amrah Abdallah ce..." muryarta ta sark'e tsabar sauri da take ta fad'a min.


Cikin tashin hankali na ce,


"Fad'a min me ya faru da Amrata? Me ya samu yarinyata?"


"Wani malaminmu ne ya dake ta sume, har yanzu bata farfad'o...."


"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Na furta ban ko jira ta gama maganar ba.


_Duk wasu masu cutar sickler, tun daga manya har izuwa k'ananan yara, ina masu fatan samun sauk'i. Allah Ya sauk'ak'a masu, Ya kawo rahamarSa a gare su._


*Ku yi comment da AMEEN, Please👏🏻😢.*


Pinky durling💗
*RAZ 2👌🏻*
[8/30, 3:32 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)


Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


1⃣2⃣


Tafiya nake gudu-gudu, sauri-sauri. Baki d'aya hankalina a tashe yake, ban ma san inda nake dosa ba, sai dai kawai na san biye nake da yaran da suka zo fad'in sak'on.


A haka muka isa makarantar, kai tsaye muka nufi ofishin head master tare da yaran.


Amrata na gani kwance tamkar bata numfashi, malamai kusan guda biyar zagaye da ita, wani na tofa mata addu'o'i wasu kuma tagumi suka yi cike da tausayinta.


"Amrah!" Na fad'a a firgice.


"Ku fad'a min dan Allah me ya faru da 'Yata? Me aka mata?"


Na jawo ta na rungume tsam a jikina.


"Wallahi idan har yarinyata ta mutu ba zan tab'a yafe wa hukumar makarantar nan ba.


Tun lokacin da za a saka ta sai da muka zo nan tare da mahaifinta, ya maku bayanin lalurinta, gashi a k'arshe kun kasa kare min yarinya.


Wallahi matuk'ar ta mutu sai na yi shari'a da hukumar makarantar, in ya so sai ku fitar da ko ma wane malami ne ya mata wannan dukan."


Kuka sosai nake, ina sake dubar jikinta da aka farfasa da bulala, har a lokacin jini bai daina kwarara ba.


Wannan yarinyar 'yar zak'al ce ta ce,


"Kuma wallahi Mama ba fa ita ce ta yi laifin ba. Amrah babu ruwanta da kowa, bata fitina, ko fad'a ta ga ana yi a cikin ajinmu ma fita take.


Sai da ta rantse ma Mallam Mu'ammar cewa ba ita ce ya aika ba, amma ya ce wai ita ya aika ta d'auko masa red pen d'insa a staff room, gashi kuma bai ga sabon littafinsa ba, wai ita ce ta sace.


Duka 'yan ajin sai da muka bata shaida, amma bai yarda ba, sai da ya mata wannan wawan dukan."


Kai kawai na gya'da, hankalina a tashe na sab'e ta had'e da mik'ewa.


Ban san ma ya zan yi ba, kasantuwar ban fito da ko sisi ba tsabar tashin hankali.


Wani Malami wanda na tarar yana mata addu'a ne ya ce,


"Mu je na kai ku asibiti a mashin."


Ban musa masa ba, dan bani da wani zab'i da ya wuce na bi sa d'in.


Head master'n ne ya zaro dubu d'aya daga aljihunsa,


"Mallam Hafeez ga wannan, ko da za a buk'aci kud'i."


Ya juyo gare ni,


"Dan Allah Hajiya a yi hak'uri, an yi kuskure wanda k'addara ce kuma ta rigayi fata.


Insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba. Fatanmu dai yanzu ta farfad'o, sannan duk maganar da za a yi a yi."


Ko kallonsa ban yi ba kawai na fice, da sauri malamin da aka kira da Mallam Hafeez ya biyo bayana.


Bakin mashin d'insa ya isa, ya fiddo sannan na hau ina rungume da Amrah.


Tambayata ya yi asibitin da muke kaita na fad"a masa, hakan ya sa kai tsaye muka doshi can d'in.


Muna isa risafshan da sauri na k'arisa inda medical recoarder yake, tsabar yawan zuwa asibiti har ma na hardace lambar katinta, babu b'ata lokaci ya fiddo fayil d'inta.


Ganin tana unconcious ya sa ko tsayawa bin layi bamu yi ba, kai tsaye aka shigar da fayil d'in nata muka shiga wurin likita.


Dr. Rabi'atu ce yau muka tarar, ganinmu ya sa ta zare glasses d'inta cike da tausayi ta ce,


"Amrah jikin dai?"


Ta karb'e ta daga hannuna.


"Ehh..." kawai na fad'a ina son ci gaba da magana amma tashin hankali bai bar ni ba, sai faman kuka nake tamkar yau ne ta fara yin ciwon.


Da k'yar na iya jawo magana daga k'asan mak'oshina, na ce,


"Dr. Tun da yarinyar nan take ciwo bata tab'a irin wannan ba. Duk irin sumar da zata yi bata wuce minti biyar ko goma ta farfad'o.


Amma ki ga wannan, tun d'azu take a haka, ga jikinta ya yi zafi rau kamar garwashi."


Kuka ya sake cin k'arfina.


Ajiyar zuciya Dr. Rabiatu ta sauke,


"To yi hak'uri Maman Amrah, daina kukan mana. Insha Allahu zata samu sau'ki.


Amma me aka mata ne har haka?"


"K'awayenta ne suka zo har gida suka shaida min, wai wani malami ne ya dake ta." Na bata amsa ina mai k'ok'arin had'iyar sabon hawayen da ya fito min.


"Subhanallahi! Dama kuwa akwai irin wannan malaman, wanda basu da tausayi ko kad'an.


Banda abinshi, ina abun duka ga wannan 'yar halittar?


Idan ma dukan ne, ai sai ya san kalar wanda zai mata.


Amma ki ga fa, har yanzu jini bai tsaya ba."


Ta hau dudduba ta.


"Ina ga kaman dole sai ku kwanta fa, ko da kwana d'aya ne ta yi sannan. Tana da bu'katar kula sosai a nan kafin ku koma gida."


Mik'o min ita ta yi, sannan ta rubuta wata allura ta bani,


"Ki karb'o wannan allurar yanzu a famasi, sai na mata ita kafin komai."


Mik'ewa na yi a hanzarce, na nufi d'akin magani da takardar.


Su kansu sun san ni, sun san cewa a kyauta muke karb'ar duk wani maganinta ko kuma allura.


Bani allurar suka yi da sauri na koma wurinta.


Bayan ta karb'a, ta had'a ta sannan ta sa na kwantar da Amrah a bisa gadon da take duba marasa lafiya.


Allurar ta mata, wanda sai a lokacin na d'an samu kwanciyar hankali, ganin yanda ta d'an zabura a lokacin da allurar ta shiga cikin fatarta.


Bayan ta gama ta jefa allurar a cikin dustbin, sannan ta dawo mazauninta.


"Ki je nurses station ki kira min duk Sister d'in da kika had'u da ita." Ta ce da ni. "Daga nan ki kira min patient na gaba."


Fitar kuwa na yi, bayan na turo mata nurse ne ta umurce ta da a kaimu d'akin irin na mutum d'aya d'in nan (amenity) sannan ta dawo ta kar'bi sauran magungunan da ta rubuta ta karb'o a pharmacy, idan ta farfad'o sai a bata su.


Ina fita na ci karo da Mallam Hafeez, ya tambaye ni halin da ake ciki na shaida masa, sannan na bi bayan nurse d'in.


Bai tsaya ba shi ma d"in binmu ya yi a baya, kwantar da ita ta yi sannan ta tafi ta bar mu a wurin ni da Mallam Hafeez.


"Alfarma guda tal nake nema a wurinka Mallam Hafeez." Na furta ina mai dubansa.


"To Maman Amrah." Ya fad'a had'e da matsowa bakin gadon.


"Dan Allah wurin k'wadagon mahaifinta zan kwatanta maka, ka taimaka ka shaida masa halin da muke ciki."


Na kwatanta masa inda Mallam yake gyaran babur a k'ark"ashin wani bayerabe.


Dubu d'ayar da Head mastet ya bashi ce ya zaro ya bani, sanann ya tafi.


Bayan tafiyar Mallam Hafeez ba da jimawa sosai ba Amrah ta tashi, hawaye duk ya bushe a kumatunta.


Da hanzari na isa gare ta, bin ta nake da kallo har sanda na k'arisa dai-dai gadon da take kwance.


Ganina da ta yi cikin yanayin damuwa da kuma tausayinta ya sa ta sakar min murmushi,


"Ummah..." ta k'o'karta fad'i annuri bai kau daga fuskarta ba.


Duk da na san cewa 'karfin hali ne irin na Amrah, a rayuwarta ko kad'an bata so ta ganmu cikin damuwa, ba wai mu iyayenta kad'ai ba, kowa ma.


A haka ni ma na sakar mata murmushin wanda iyakarsa bisa fuskaka kawai ina kallonta.


"Sannu Amrah." Na fad'a cike da tausayi.


"Yauwa...Ummah, k'ashin bayana ciwo kamar zai tsage." Ta fad'a tana k'ok'arin kai d'ayan hannun da ba a lik'a mata drip ba a bayan.


"Dama dole zai miki ciwo ai. Ki kwantar da hankalinki, zan kira Nurse yanzu zata baki kulawa sosai. Insha Allahu yanzu zai daina yi miki ciwon."


Na kama hanyar nurses station.


"Sister ta farka...ina nufin Amrah Abdallah, mai sickle cell."


Da hanzari ta tashi tsaye, wani kwando ne wanda already ta had'a medications d'in Amrah baki d"aya. Na yi gaba ta biyo ni a baya.


"Ki samo mata ruwa tukuna, wanda zata sha maganin da shi."


"To Sister." Na fad'a ha'de da nufar wajen asibitin.


Da kud'in da Mallam Hafeez ya bani na siyo mata ruwa da lemo, sai kuma biskit.


Bayan na iso, zaune na same ta, Sister kuma tana b'ab'ballo mata magnungunanta, tana d'orawa a wata container wacce suke saka magungunansu a ciki.


"Umma yanzu ya bar wurin nan..." ta fad'a cike da mamaki tana nuna k'ofa.


"Umma baki had'u da shi ba?"


Bayan na k'ariso ciki na tambaye ta,


"Wa ke nan?"


Had'e da d'ora robar ruwan sona a bisa teburin ajiye-ajiye.


"Umma, Ya Noor mana." Ta furta cike da yak'ini.


Gyad'a kai kawai na yi, dan a tunanina ko zafin ciwo ne kawai ya sa ta fad'in hakan.


"Umma wallahi da gaske nake. Sister dan Allah ba yanzu wani gurgu ya bar nan ba?"


Kai sister'n ta gyad'a alamar ehh.


"Na san ke ma kun had'u a dai-dai shigowarki sai dai ko baki ga fuskarsa ba ne.


Amma wallahi Umma shi ne nake gani. Na fad'a maku ke da Abba kun k'i yarda.


In dai wannan wanda kuka nuna min a hoto shi ne Annur, to tabbas shi ne yake kai da kawowa a cikin asibitin nan."


Kai na dafe cike da mamaki, tabbas na ha'du da wani a cikin keken guragu, sai dai kuma ban tsaya na kalli fuskarsa ba bare na tabbatar da gaske ne ko akasin haka.


Zama na yi ba tare da na sake furta komai ba, sai binta da kallo kawai da nake tana dafe da bayanta, amma hakan bai hana ta k'ok'arin tabbatar min da gaskiyarta ba.


"Maman Amrah, sai a kula sosai da magungunan nan. Sannan kuma a kula kar ta yawaita motsawa har sai sanda allurar nan ta sake ta sosai.


Ko fitsari zata yi gwara ki fita waje ki siyo mata fo, dan yawaita motsawar kanshi zai iya lalata mata treatment.


Sannan kuma sai kin yawaita tab'a jikinta, idan kika ji zazza'bin yana yawiata sauko mata sai ki kirani,


Ina jin dole za a mata awon jini dan tabbatar da ya k'one ko bai k'one ba?


Sannan a san madosa."


"To insha Allahu zan kula Sister. Na gode Allah Ya saka da alkhairi."


"Ameen maman Amrah. Allah Ya bata lafiya."


Daga nan ta fita ta bar mu.


Tana fita sai ga Mallam Hafeez a gaba, sai Mallam biye da shi, hankalinshi a tashe.


"Amrah 'yata me ya same ki?" Ya furta cike da damuwa, yana k'ok'arin isowa bakin gadon da take kwance.


"Sannu kin ji? Ashe ciwo ya tashi, Allah Ya kyauta ya tsare gaba."


"Ameen Ya Allahu." Mallam Hafeez ya furta.


Sai a lokacin ma na tuna da ba a mata treatment na raunin da aka mata wurin bulala ba.


Da hanzari na ce,


"Mallam ina zuwa." Na nufi wurin Sister.


Bayan na fad'a mata dalilin zuwana ta ce,


"Ehh ina sane da shi ai, small injury ne ba abun a damu sosai ba.


Gwara a bar mata shi a bud'e ya sha iska,


Dan kar a je a tab'a k'ila k'ashin wurin bashi da wani k'wari sosai. Wurin gyaran gira a rasa ido."


Na gamsu da maganarta sosai, hakan ya sa kawai na mata godiya had'e da tafiya.




_Yawan zazzab'i mai zafi wanda baya sauka, yana d'aya daga cikin alamomin sickler. Lura da kyau, mu zama masu kula da ciwukan da yaranmu ke yi, kar mu zama masu sake, har ciwo ya fara yi masu yawa. Allah Ya bada lafiya._


Pinky durling💗
*RAZ 2👌🏻*
[8/30, 3:33 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)


Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


1⃣3⃣


Washe gari da sassafe sai ga Malaman makarantarsu sun zo, su kusan ashirin ko ma fin haka. Har d'akin ma bai iya d'auke yawansu ba.


A lokacin da suka zo Mallam baya nan, ya zo ya kawo mana abinci, ya wuce wurin aikinsa.


Har k'asa na du'ka muka gaisa, sannan na d'an bubbuga Amrah ta tashi.


Head master'nsu ne ya 'kariso dai-dai inda take,


"Sannu Amratu. Ya k'arfin jikin naki?"


Da fara'a k'unshe a fuskarta ta ce,


"Jiki da sau'ki sosai Mallam. Na gode."


Da haka malaman sukaita mata ya jiki, a k'arshe Mallam Mu'ammar cike da kunya ya dafe k'eyarsa, ya ce,


"Insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba. A yi hak'uri." Ya juyo gare ni, "Ban tsammanin abun zai kai har haka ba, da tun farko ban dake ta ba.


Insha Allahu ba zan kuma maimaitawa ba. Zan zama mutum mai tausayi, ba wai gare ta kawai ba, ga baki d'aya d'alibaina."


Ya juya ga sauran Malaman ya ce,


"Dan Allah ina mai neman afuwarku, daga yanzu duk wani d'alibi wanda za a kawo mai sickler, mu ringa kula da shi, mu san ta hanyar da zamu masa hukunci.


Sai mun kula sosai, mun basu kulawa tamkar 'ya'yanmu ko kuma k'annenmu na jini.


Ita rayuwar nan baka san wanda zai maka rana ba, sanann kuma kana naka Allah Na naSa."


Head master ya yi gyaran murya ya ce,


"Haka ne Mallam Mu'ammar. Na ji da'di k'warai da ka gane hakan, har kake bada taka shawarar.


Allah Ya tsayar nan, ita kuma Allah Ya bata lafiya."


"Ameen." Duka Malaman suka fad'a a tare.


Ku'di Head master ya zaro daga aljihunsa ya d'ora bisa gadon Amrah,


"Ga wannan a sai miki lemo. Allah Ya sauwak'a ko?"


Godiya na masa sannan suka fita, suka bar d'akin baki d'ayansu.


Bayan sun tafi na duba kud'in, dubu goma ne cif, hakan ba kad'an d'in dad'i ya min ba, saboda dama babu kud'in, abincin da Mallam ya siyo mana da safe ma da k'yar ya had'a ku'din ya siyo.


Kwananmu biyu aka bata sallama muka koma gida, ranar da muka koma sai ga Hajiya Suhaila ta zo, wai Annur ne ya fad'a mata Amrarsa bata jin da'di, da yake ya kira ta wayar Amrah'n Mallam ya d'auka yake shaida masa bata da lafiya, kuma baya asibiti a lokacin bare su yi waya.


Ta kawo ma Amrah sha tara ta arzik'i, a 'karshe ta mana fatan alkhairi sanann ta tafi.


Da yamma Mallam ya kira ma Amrah Annur. Sun jima suna waya, har take masa ta'din ganinsan da take yawan yi a Turai Hospital, amma ya shaida mata cewa ba shi ba ne, saboda shi tun da ya bar Nigeria bai sake dawowa ba. Wata k'ila dai mai kama da shi ne kawai take gani.


Rayuwa ta ci gaba da tafiya a haka, yau da lafiya gobe babu lafiya, a haka dai take rayuwarta cike da wahala.


Talauci kuma sosai muka rage shi, saboda babu abin da Hajiya Suhaila bata bamu, tun daga kan kayan abinci har sutura yi mana take, Amrah ma kuma ba laifi tana zuwa gidanta, abin dai sai sam barka.


A lokacin da Amrah ta yi JSS ne, take da shekara goma sha uku da watanni.


Ranar da suka gama zana jarabawarsu, Annur yake mata albishir da cewa mahaifinsa ya barshi ya dawo Nigeria ya ci gaba da aikinsa, saboda ya da'de da zama Architecture babba, wanda yake da degree mataki na uku (ph. D) duk a 'bangaren zane-zane.


Sosai Amrah ta yi murna, dan zan iya cewa ko Hajiya Suhaila da ta haife sa, bata kai Amrah jin dad'i ba.


Ranar da suka yi waya cewa zai dawo gobe, kasa bacci Amrah ta yi, sai faman juye-juye take, ta ma rasa me ya kamata ta yi saboda murna.


Washe gari da sassafe ta fito tsakar gida ta hau shara, jin motsinta ya sa na fito a hanzarce na ce,


"Ya da shara tun da duku-dukun safiya, ba zaki yi shirin makaranta ba?"


Fuska a yamutse ta ce,


"Umma yau fa ba zan je ba. Kin manta Hammana zai dawo?"


Murmushi na yi na ce,


"Ya za a yi na manta da dawowar Annur? Ai ban ga zaman me zaki yi ba idan baki je ba? Ga ki kuma ke ce shugabar aji."


"Umma ai jiya Momy ta kira ni, wai yau da safe na je can mu yi shirye shiryen tarbarsa. Shi ya sa ma na tashi da wuri dan na kammala komai cikin lokaci."


"To ai shi ke nan. Amma ba kya gudun abin da Islam zata miki? Kin san fa ita ma yau tana iya k'in zuwa aiki saboda shi."


Tab'e baki Amrah ta yi ta ce,


"Duk abin da ta min ai sai in bata ha'kuri. Cike nake da murna yau bana jin masifarta da wulak'ancinta zasu yi tasiri a gare ni, har su hana ni tarbar Ya Noor."


Ajiyar zuciya na sauke,


"To ai shi ke nan. Amma sai kin daure, kin kai zuciyarki nesa."


"Insha Allahu kuwa Ummah. Ai kin san ni da wuya mutum ya b'ata min rai. Ina binsa da yanda yake so, sai dai ma a k'arshe shi d'in zai ji kunya."


"Na tabbatar da hakan kuwa 'yata.


Allah Ya miki albarka ya sa ki d'ore da wannan kyawawan halayen naki.


Wai har yanzu ba a saka ranar walimar

Please Login or Register in order to submit comment