You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tai."


Har ta juya za ta bar ofishin ta jiyo muryarsa ya ce,


"Ba ki ji ba."


Ta juyo da kallonta gare shi, tana jiran abin da zai faÉ—a.


"To idan kin tahi kin bar shi shi É—ai, halan wa zai hwaÉ—i min idan ya tashi?"


Shiru ta É—an yi jim! Kafin ta ce,


"Ba daɗewa zan yi ba likita. Na jima ban tai gida ba. Ina da buƙatar in koma su gan ni in gan su. Minti arba'in ya ishe ni."


Kai kawai ya jinjina ba tare da ya ce komai ba, ta kama hanya ta bar É—akin.


Kai tsaye gida ta nufa, ko kuɗin abun hawa babu a tare da ita, ta hau ne dai kawai komai ta fanjama, fanjam! Idan kuma zai haƙura ta shiga gida ta ɗauko masa to.


A ƙofar gida mai mashin ɗin ya dakata. Bayan ta sauka ta ce da shi ya mata haƙuri ta shiga gida ta fito, za ta sallame shi. Babu ko musu ta tafi ta bar shi, bayan ya faka mashin ɗinsa.


Sumi sumi ta shiga gidan, hankalinta a tashe, dan ba ta san kalar masifar da za ta tarar ba. Sallama ta yi ƙasa ƙasa, tana bin mutanen da suke cikin gidan da kallo.


Babu wacce ta amsa sai mutum É—aya, wadda har da fara'a a fuskarta ta iso ta rungumi Fiddou. Ita ma Fiddou rungumar tata ta yi, tana faÉ—in,


"Hadiza halan yaushe kika zo?"


Kafin Hadizar ta yi magana ta jiyo muryar matar yayanta ta ce,


"Tun sanda kika tahi wurin yawon iskancinki. Ke Fiddou bari ki ji in hwaÉ—i miki, na gaji da wanga iskanci naki, wanda kullum babu sauyi sai ma ci gaba da yake. Dan dai kin ga Yayanki ba shi nan ne hwa. Waton idan ya zo ya ce na bar ki kina hita yawon karuwanci ko? To walle ba ki isa ba!"


Wata budurwa da ke gefenta ta ce,


"Salon jan sharri ne kawai. Waton idan ya tashi ya ce ke kina harkar bikin gidanku, kin bar ta ita kuma tana biÉ—iÉ—inta. Makira ana magana tana bin mutane da idanuwa kamar warinta."


Wata mata ta buÉ—e baki ita ma za ta tofa na ta albarkacin bakin kenan Hadiza ta ce,


"Wai me ke damunku ne dan Allah? Wannan wane irin hali ne? Daga dawowarta babu ko maganar arziƙi kawai sai mugayen kalamai? Ku za ku so a muku haka ne? Ni fa ba na son haka gaskiya."


"Inye! Lallai ma Hadiza. Ni hwa ba na son wanga hali kuma ke sani. Ke a dole wayayya wadda ta je Katsina. To walle ba za mu ƙyale giɗe ba. Dole ne mu hwaɗi ta yi iskanci."


Kuka sosai Fiddou ta fasa. Tana matuƙar jin haushin kalmar da matar yayanta ke yawan jifanta da ita. Wai ita ce ƴar iska. Ga ƙanwarta nan Hadiza, wadda tsabar yawon bariki ya sa ma ta bar garinsu, ta koma Katsina da zama. Amma ba su ga nata ba, sai ita da ke ƙoƙarta kare mutuncin kanta a ko da yaushe.


A cikin kukan ne ta tuna da mai mashin da ba ta sallama ba. Da sauri ta bar wurinsu, ta nufi É—akinta.


A cikin lakarta ta fiddo Æ´an kuÉ—aÉ—en da take ajiya, ta zari daidai wanda za ta sallami mai mashin É—in, sannan ta fito domin ta kai masa.


Fizgo ta ta yi matar yayanta, ta matse mata kafaɗa da ƙarfi, tana binta da wani wawan kallo.


"Dan Allah dai Aunty Sahiya ki rabu da ni. Ki ƙyale ni."


"Na ƙi in ƙyale ki Fiddou. Waton in sake ki ki koma wurin iskancin na ki ko?"


Cikin jarumta ta fizge jikinta, a hanzarce ta fita daga gidan, ta bar su sake da baki.


Bayan ta sallame shi ta dawo. Tana jin yanda tsoron Aunty ke fice mata daga zuciya. Ita fa in dai kan Modu ne, to za ta iya jure komai, wulaƙanci da kyara, matuƙar dai ba zai cutu ba.


Tana shiga Aunty ta jawo hannunta da masifa. Ba ta ankara ba Hadiza ta janye Fiddou da fushi sosai, ta ce,


"Wallahi ba ki isa ba! Wai me ya sa ba ku da imani ne? Yarinya marainiya amma babu imani sai a ringa cutar da ita? Wuce mu tafi Fiddausi."


ÆŠakin Fiddou É—in suka nufa, Fiddou sai kuka take, Hadiza na rarrasarta.


"Fiddou in dai ba za ki fitar da tsoronsu ba wallahi a haka za ki ci gaba da rayuwa. Yo wannan rayuwar ko naka na jikinka wa ya ce miki ana gwada tsoronsa a fili? Ai sai ya raina ki. To bare kuma matar yaya. Me ake ci da matar yaya ko ta ƙwarai ce bare kuma muguwa kamar Aunty Safiya?"


"Ban san yanda zan yi ba Hadiza. Ina cikin matsala. Aunty Sahiya ta kasa ganewa. Ta ƙi ta bar ni da damuwad da ac cikin zuciyata. Ga Modu can kwance ba lahiya. Ni ban ma san inda zan dosa ba. Rana zahi inuwa ƙuna!"


Kuka sosai take a wannan gaɓar. Tana ƙara tuna halin da ta baro Modu a ciki.


"Yi haƙuri ya isa haka to. Yanzu ki samu ki yi wanka mu je na siya miki abinci, dan nan gidan dai babu komai, idan ma akwai na tabbata masifaffun can ba za su bar ki ki ci ba."


Nufar yin wankan kuwa ta yi Fiddou. Kafin ta fito har kaya Hadiza ta fiddo ta ajiye mata. Tana jiran fitowarta.


Bayan ta shirya suka kama hanyar fita. Ko kallon inda su Aunty suke ba su yi ba. Saboda Hadiza na ƙoƙarin fitar da shakku da fargabar Aunty Sahiya da Fiddou ke yi.


Kai tsaye wurin sayar da abinci suka nufa. Siya suka yi suka ci, sannan Hadiza ta sa a ma Modu take away su tafin masa da shi.


Bayan Hadiza ta biya kuÉ—in suka fito. Mashin suka tara ko wace ta hau É—aya, kai tsaye suka nufi asibitin da Modu yake.


Fiddou ce a gaba sai Hadiza bayanta, har suka shiga cikin É—akin Modu.


Modu suka samu a zaune, hannunsa ɗaya dafe da ƙirjinsa, ɗayan kuma a cikin bakinsa, yana tsotsar duka yatsun hannun.


Dariya ya saki da ƙarfi a lokacin da ya haɗa ido da Fiddou. Ya yi yunƙurin miƙewa amma kansa ya sara masa, dolensa ya runtse ido, ya dafe kan nasa.


Ledar hannunta ta saki Hadiza a lokacin da ta haÉ—a ido da Modu. Ta zaro duka idanuwan nata. Hannunta bisa kai tana bin sa da kallo.


Kallon mamaki Fiddou ta bi ta da shi. Saboda yanayin kallon da Hadiza ke bin Modu da shi, da alama ta san shi ne.


"Hadiza, halan lahiya?"


Kai Hadiza ta gyaɗa har yanzu ba ta ɗauke idanuwanta daga gare shi ba. Hannunta na dama ta miƙe daidai saitinshi. Ta ringa gwada shi da yatsarta manuniya, bakinta na ƙoƙarin furta magana amma ya kasa.


Da ƙyar ta iya ɗaga laɓɓanta ta yi magana, wanda idan ba ka kalli bakin nata ba ba za ka taɓa cewa ta yi magana ba.


"Annur!"


Ta faÉ—i a daidai isowarta gaban Modu.


To masu karatu. An zo wurin ko? Na san haka wasu za su faɗi,😁 indeed, an zo wurin.


Tighten your belts readers, sannu a hankali mun fara isowa wurin, wurin da nake yawaita faɗa maku za a zo. Akwai gwagwarmaya, akwai kuma sarƙaƙiya.


Thanks all.
Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:50 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)


Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


3⃣7⃣


follow me on wattpad @PrincessAmrah


***


"Annur!?"


Fiddou ta maimaita a bayyane, tana sake bin Hadiza da kallon tuhuma.






"Kin san shi ne halan?"


Ta jefo wa Hadiza tambaya, bayan ita ɗin ma ta ƙarisa a gabansu.


"Annur me ya kawo ka nan? In ce ko jiyan nan muka rabu da kai lafiyarka lau? Na shiga uku! Hadiza ba dai shi ne mahaukacin da kika ba ni labarinshi ba ko? Wallahi wannan Annur ne."


Duka a jere ta sako wannan maganganun, zuciyarta na ƙara tabbatar mata da cewa lallai wannan Annur ne ta gani, Annur ne zaune a gabanta.


"Wace irin magana kike yi halan giɗe? Wane irin ko jiya ke ganai bayan kuma Modu gashi ya ɗauki kwanaki a asibiti? Shekararsa kusan uku a Maraɗi hwa. Kallarsa da kyau dai Hadiza. Ƙila dai ya yi miki kama da wanda kika magana ne."


Hannunta ta sa ta fiddo yatsun Modu da suke cikin bakinsa. Ta É—ora su a bisa tafin hannunta. Idonta cikin nashi ta ce,


"Annur ka fito fili ka faɗa mata gaskiya. Da alama dai wani mugun abun ka ƙulla shi ne ka yo nan a shekaran jiya rabuwata da kai kawai. Ka faɗa mata gaskiya na ce Annur!"


Kallonta kawai yake yana yaƙe baki. Shi kanshi bai san dalilin shigarsa nishaɗin ba, kawai daga jin ta ambata masa sunan da ba nashi ba.


"Ka daina wannan dariyar yaƙen Annur. Wallahi kai ne, na tabbata. Wace irin rayuwa ce ka jefa kanka a cikin kwanaki biyu kacal?"


Har a lokacin Fiddou ba ta daina kallonta ba. Ba kuma ta sake furta mata komai ba.


Sallamar Dr. Huzaif suka ji, sai nurse biye da shi ta riƙo file ɗinshi.


Amsa sallamar ta yi Fiddou, har a lokacin ba ta daina mamakin kalaman da suke fitowa daga bakin Hadiza ba.


Bayan Dr. Huzaif ya ƙariso inda suke ya ce,


"Fiddou ba haka muka yi da ke ba. Kin san dalilin da yas sa na ce kar a kai Modu male ward, dan dai kar a damai da hayaniya. Sannan ko da za ki tahi gida sai da nis so in hana miki tahiya, saboda idan Modu ya tashi ki hwaÉ—i min. Amma abun mamaki sai ga shi har ya tashi ba ki taho kin hwaÉ—i min ba, sai nurse ce ta zo gittawa taj ji abin da ke hwaruwa. Sannan kuma ga hayaniya kuna yi, bayan matsalar zuciyar da giÉ—e ag garai."


Sosai Hadiza ke binsa da kallo.


'Matsalar zuciya?'


Ta tambayi kanta, bayan ta sake mayar da dubanta ga Modu.


Ita ba ma ciwon zuciyar ne ya fi ɗaure mata kai ba. Yanayin nasa ne babban abun dubawa. Kayan jikinsa da sumar kanshi, haƙoransa da tun ɗazu yake yaƙewa duka abun mamaki ne.


Ba ta gama mamaki ba ta jiyo muryar Dr. Huzaif ya ci gaba da magana.


"Bari in sake hwaɗi miki maganar ɗazun nan wadda ba ta yi miki daɗi ba. Wallahi giɗe da kike gani ga shi ya kusa mutuwa. Zuciya tai tana daf da tsayawa, ta daina aiki baki ɗaya. Matuƙar ba ki kiyaye sharuɗɗa ba, to ki tabbata ya mutu kawai."


Yana kaiwa nan ya ƙariso gaban Modu, yana kallonsa da murmushi sosai, haka shi ma Modu ɗin murmushi yake ma Dr. Huzaif.


Mamaki fal a fuskar Hadiza. Wai da gaske Annur ya haukace? Kuma yana da ciwon zuciya, har ma za ta iya zama ajalinsa?


Hawaye ta ji suna zarya bisa kumatunta. Tausayinsa take. Duk da ta san cewa rayuwar bariki ce suke yi da Annur, amma fa tana ƙaunarsa. Tana masa soyayyar da tun da take a rayuwarta ba ta taɓa yi wa wani ɗa namiji irinta ba. Sai dai kuma ta san a banza, tun da shi ba irin son da yake mata ba kenan. Jikinta kawai yake so, kawai ya biya ta kuɗi bayan ya samu biyan buƙatar kansa.


Wayarta ta zaro daga cikin jakarta. Gabanta na tsananta duka ta nemi lambar Annur ta kira sa. Abun da ya daɗa tayar mata da hankali shi ne ƙin ɗaukar wayar da ya yi. Har kusan sau biyar tana maimaita kiransa amma ba aauka ba. Hakan ya tabbatar mata da tunaninta. Lallai wannan Annur ne, Annur da ta rabu da shi kwanaki biyu da suka gabata. Shi ɗin dai ne a gabanta yanzu, a matsayin mahaukaci kuma mai lalurin ciwon zuciya.


Ba ta ko sake kallon inda Fiddou take ba a guje ta bar ɗakin, tana jin zuciyarta kamar za ta fashe. Hankalinta ya matuƙar tashi. Lallai dole ne a gare ta ta koma Katsina yau, kuma yanzu ma, domin ta sanar da iyayensa halin da ake ciki. Dole ta sanar masu, saboda su ƙoƙarta sama masa lafiya. Ta tabbatar har ƙasar waje ma za su iya fitar da shi, saboda mahaifinsa mai dukiya ne, dukiyar da za ta iya siyan duk wani abun siya, ciki kuwa har da fita wata ƙasa domin nemawa tilon ɗansa lafiya.


Takowa ta yi Fiddou jiki sanyaye za ta bi bayanta, tana son sanin abubuwan da suke fitowa daga bakin Hadiza. Tana son tabbatar da gaskiyar lamarin. Wata ƙila ko ƙarshen wahalar Modu ce ta yi. Ƙila ko tana da masaniya da asalinsa ne. Sai dai kuma abin da ya ɗaure mata kai, jin ta ambaci shekaranjiya ma wai ta ganshi, alamun dai rashin ingancin zancen kenan. Kafin ta isa ƙofa ta jiyo muryar Dr. Huzaif ya ce,


"GiÉ—e a samo ma abokina abinci ya ci."


Sai a lokacin ma ta tuna da ledar abincin Modu da Hadiza ta saki tsabar mamaki. Fasa fitar ta yi ta dawo. Ledar ta ɗauko daga ƙasa, har miyar shinkafar ta ɗan fara zuba cikin ledar, mai duk ya gama tsiyayewa.


Bayan ta buɗe ta motsa masa, tana ƙoƙarin zama a bakin gado ta bashi amma likita ya karɓa, ya ce shi zai ba shi da kansa.


"Abokina Modu. Kai É—an gata kake hwa. Ka ga abinci ma da kaina zan ba ka."


Bai furta komai ba sai wannan yaƙe da ya zame masa abun yi ya yi. Sai lokaci zuwa lokaci yake ɗan dafe ƙirjinsa, ta gefen da zuciyarsa take.


"Uhmm...abokina, ba ka bani labari ba."


Shiru ya yi daga nan yana kallon yanda Modu ke ciccije bakinsa, hannunsa dafe da zuciyarsa, hawaye na ƙoƙarin fitowa daga idanuwansa.


"Sannu ka ji Modu. Jarumi ba ya kuka saboda wani ciwo. Kar ka ba ni kunya do Allah de."


Ya ƙirƙiro murmushi duk da tausayin Modu da ke cikin zuciyarsa.


Murmushin ya yi shi ma Modu, hawaye kuma ba su daina fita daga idanuwansa ba.


"Labarin Anrah nika son ka ba ni. Halan...?"


Bai ƙarisa maganarsa ba Annur ya sake dafe ƙirjinsa, hawaye na tsananta fito masa. Da ƙyar ya iya ɗaga laɓɓansa, cike da ƙarfin hali ya ce,


"Amrah!"


Haɗe da fasa kuka da ƙarfi, ya buɗe duka muryarsa.


Cike da tausayi Dr. Huzaif ya ajje robar abincin a gefensa. Ya yunƙura tashi ya hau bisa gadon. Kama Modu ya yi ya kwantar a hankali, yana tunanin ta inda zai ɓullowa lamarin. Lallai wannan Amrar ba ta rasa nasaba da matsalar zuciyar Modu, har ma da taɓin ƙwalwarsa.


Ya ma rasa yanda zai yi da Modu a daidai wannan lokacin. Ba ya son ya masa allurar barcin nan, dan ya kula jininsa bai da ƙarfi sosai, tana jimawa ba ta sake shi ba. A daidai wannan lokacin kuma ba barcin Modu aka fi buƙata ba. Dole sai yana farke ko zai samu sauƙin hanyar kawo waraka ga Modu.


Dafe kansa ya yi bayan ya koma ya zauna. Yana kallon yanda Modu ke riƙe da ƙirjinsa da duka hannuwan nasa biyu. Ya ciccije laɓɓansa sai faman gyaɗa kanshi yake.


"Dr. Do Allah de ka ƙyale shi da maganar wagga Amrah. Da alama ba ya son maganarta ne."


Fiddou ta jefo masa wannan maganar tana mai cike da jin haushinsa. Saboda ita fa babu abin da zai yi ya burge ta. Tun da ta kula da imaninsa ragagge ne, ga uwa uba rashin iya magana.


Banza ya mata bai kula ta ba, sai murmushi da ya ƙirƙiro ya ce,


"Amrah na nan tana jiranka Modu. Babban burinta shi ne ka koma gare ta, ku ci gaba da rayuwarku tare, ta ƙaunace ka, kai ma ka ƙaunace ta."


ÆŠago kanshi ya yi da murmushi ya kalli likitan, hawayenshi na shiga har cikin bakinsa ya ce,


"Da gaske...Amrah...Amrah nake so!"


"Na sani ai Modu."


Dr. Huzaif ya faɗa da murmushi. Yana mai jin yaƙini a ranshi, lallai da alama za su yi nasara.


"Amrah nake so! An ce wai ta tafi ta bar ni. Na san kuma ba za ta tafi ba, saboda komai na mu tare yake tafiya."


Ido buɗe likitan ke kallon Modu. Mamaki ƙarara a fuskarsa. Bai taɓa tsammanin jin wannan kalamin daga bakinsa ba. Kamar dai mai hankali? A yanayinsa da komai da ya yi maganar, babu wanda zai ce marar hankali ne. Sai dai kuma bayan ya gama maganar, ya tabbatar masu da cewa lallai mahaukacin ne kuwa.


"A tona rami zurun zurun a binne ni. Sai a ɗauko ta a saka a ciki. A rufe mu da ƙasa mu yita soyayyarmu a ciki ko?"


Ga tausayi, ga kuma dariya. Har ga Allah Ya bashi dariya sosai wannan maganar da ya yi.


Murmushi ya yi haÉ—e da faÉ—in,


"hakan za a yi kuwa Modu. Ai ni ka ganni nan? Farin cikinka nake so. Dan haka dole zan kai ka inda take, musamman ma idan ka natsu, ka kuma zama abokina."


"Da gaske kake? Na yarda. Mu ƙulla ma daga yanzu. Mun zama abokai."


Ya yaƙe haƙora bayan ya miƙowa Dr. Huzaif hannunsa.


Shi ma nashi hannun ya bashi suka dunƙule alamun yarjejeniya. Suna sakarwa junansu murmushi.


Fiddou da ke tsaye dai hankalinta a rabe yake. Ga tunanin Modu da tausayin halin da yake ciki, ga kuma tunanin maganganun da Hadiza ta yi. A ƙarshe kuma ta tafi da gudu.


Zama ta yi a ƙasa dirshan, hawaye na fita daga idanuwanta. Wannan wace irin jarrabta ce take cikinta? Tana fatan Allah Ya ba ta ikon cinye wannan jarabawa. Allah kuma Ya kawo ranar da Modu zai warke tas, ta miƙa shi ga danginsa. Tsayawa ta yi da zancen zucin a daidai wannan lokacin, haushin kanta kuma take ji. Ta miƙa shi ga danginsa ita kuma fa? Shin za ta iya ci gaba da rayuwa ba tare da Modu a kusa da ita ba? Za ta iya auren wani namiji baya ga Modu? Gyaɗa kanta ta yi kuma, tana jin wasu sabbin hawayen suna zarya a kumatunta. To idan ya warke kuma ya nunar da bai santa ba fa? Tabbas duk wata shaƙuwa da suka yi a yanzu ta banza ce, tunda ba a cikin hankalinsa yake ba. A haka ma da bashi da hankalin kodayaushe cikin ambatar Amrah yake, ina ga ya warke? Ta tabbatar aikin banza take. Dakon son banza take yi, tunda bai ma san tana yi ba.


***


Tun bayan da suka dawo daga wurin boka bai nufi zuwa wurin aikinsa ba, sai gidan su Farouk Sardauna da suka wuce, domin sharholiyarsu, na nasara da suka samu.


Zaune suke bayan sun yi mankas, suna ta zuƙar shisha, hankalinsu a kwance.


Bayan gama shan shishar kuma sai barci ya ɗauke su su duka biyun, ba su farka ba sai kusan ƙarfe uku na rana, shi ma sai da mai aiki ta shigo ta kawo wa Bobby abinci ta masu knocking.


Abincin ya karɓa Bobby, sannan ya rufe ƙofar ya fara ƙoƙarin tashin Annur daga barci.


Bayan ya tashi ne wayarsa ta hau ruri. "Babe" ya gani a bayyane, hakan ya sa shi sakin tsaki, haÉ—e da mayar da wayar a silent.


"Abokina tashi ga abinci an kawo. Na san shishar nan ta gama zazzage maka ciki, dama kuma ko abincin kirki ba ka samu ka ci da safe ba, ban ma ce ka ci komai ba."


GyaÉ—a kai ya yi Annur. Ya ce,


"Wallahi kuwa guy. Ina wannan zullumin ta ya zan iya sakawa cikina wani abu?"


Suka kece da dariya su duka biyun.


Yana kallo har sau biyar Hadiza na kiransa amma ya ƙi ɗauka. Bobby ya ce,


"Wai abokina ba babe ba ce ke kiranka?"


Yatsine fuska ya yi Annur, ya ce,


"Ita ce fa. Ban san kuma me take so da ni ba. Shekaranjiya ta sa na tura mata kuÉ—i wai za ta je biki MaraÉ—i. Ga shi kuma yanzu tana sake kirana, kuma ma da lambarta ta Nijar, alamun dai ba ta dawo ba kenan. Na tabbatar wasu kuÉ—in za ta nema, ni kuma na gama da ita. Kai wallahi ka san, wannan É—in ma ba a banza ba. Na faÉ—a mata sai na fanshe abuna."


Suka sake saka dariya su dukansu a daidai nan.


***


"Ya kamata dai mu fara haramar tafiya gida haka nan. Ai mun sha yini."


Maryama ta saki murmushi bayan ta yi wannan maganar.


"Ke É—in wa ku tafi tun yanzu? Ko fa la'asar ba a yi ba. Yinin da za ku mana kenan?"


Dr. Islam ta jefo mata wannan tambayar.


"Aunty Islam ai na ga ya kamata mu tafi haka nan."


"To ba yanzu ba. Sai magrib ko kuna barin nan. Ki ma kira dreban naku ki sanar masa, ku da barin nan sai dare, zan mayar da ku da kaina."


Murmushi kawai ta saki Maryama, sannan ta cigaba da latsar wayarta.


Kiran Jiddah ne ya shigo mata, da hanzari ta É—auka, saboda duk yinin yau take kiran Jiddah amma ba ta É—auka ba. Har ma hankalinta ya soma tashi. Ga shi kuma tana son sanar da ita cewa ga ta a gidan su Aanur, coincidently ta zo, ashe wai yayan Dr. Islam Maman Abdul ce, kodayake dai ba ta santa da ita ba gaskiya.


"Haba ƙawata miye duniya?"


Maryama ta faÉ—a bayan ta É—aga wayar.


"Yi haƙuri ƙawata. Wallahi wayar ta shige cikin kujera tun safe nake neman inda ta shige ban sani ba. Sai fa yanzu Allah Ya sa aka gano min ita. Sorry ƙawata."


Sai kuma ta ɓata rai,


"Ai ni ma jiya da dare ina ta kiranki, missed calls É—ina nawa kika gani? Sannan kuma ba mun yi da ke Annur zai kira ki ba, amma kika yi kwanciyarki?"


Dafe kanta ta yi ta ce,


"Afwan Jiddalona. Akwai magana da dama a bakina. Amma bana gida yanzu, idan na koma zan kira ki ko zuwa dare."


Jiddah ta ce,


"Ni É—in ma haka. Sai kin kira to."


Ta tsinke wayar daga nan.


6:30pm


A jigace ta shigo gidan, hankalinta tashe, idan ka kalle ta sai ka rantse cewa mahaukaciya ce.


Mai gadi ne ya dakatar da ita, yana faÉ—in,


"Ke É—in wacece, kuma wurin wa kika zo?"


Ajiyar zuciya kawai take saukewa haÉ—e da shessheka, ta gagara furta komai tsantsar tashin hankali.


"Fice ki ba mutane wuri tunda ba za ki yi magana ba. Ana miki magana amma dan hauka sai wata shessheka kike? To tafi ki ba mu wuri ja'irar yarinya."


Sai a sannan ta iya buÉ—e bakinta ta ce


"Ba shi da lafiya, wallahi na gan shi da idanuwana."


"Ni ban san wanda kike magana ba. Ki fito fili ki faÉ—i abin da yake tafe da ke. Idan kuma Æ´ar damfara ce ke sai in sani."


"Wallahi ni ba Æ´ar damfara ba ce. Na ganshi Annur. Wallahi na ganshi a MaraÉ—i."


Abdul da Muhammad da tuni suka isa falo domin kai rahoton wannan budurwar ne suka ci burki a bakin ƙofa. Muhammad mai wayon ya ce,


"Yaya Maryama ga wata mahaukaciya can ta zo, sai faɗa mai gadi yake mata wai ta wuce ta ba mutane wuri. Ita kuma ta ƙi tafiya."


Suna gama faÉ—in haka kuma suka ruga domin ci gaba da wasansu.


"To fa! Mahaukaciya a gidan nan?"


Momy ta furta cike da mamaki.


"Gaskiya ba dai mahaukaciya ba. Amma dai Momy bara na je na gani."


Islam ta faɗa haɗe da miƙewa.


Maryama da Momy ma bin bayanta suka yi. Suna son su tabbatar da maganar Muhammad, kar a je ma shirme ne kawai irin nasu na yara.


This page is in your honour, KHADEEJAH CANDY NOVEL GROUP. Kun ce wai last page ya maku kaÉ—an, to yau ga dogo nan na yi domin farin cikinku kawai. Fatan za ku ji daÉ—insa fiye da wancan na baya.


Kamar yanda na faÉ—a cewa fa akwai cakwakiya, to fa akwai ta É—in. Ko kun hango ta kuwa? Shin Modu zai warke daga wannan babbar matsalar da take addabarsa? Asirin da aka ma Maryama zai yi tasiri kamar yanda su Annur suke muradi? Wane abu Hadiza za ta sanar ma iyayen Annur? Za su yarda da ita kuwa? Ta wace fuska Maryama za ta kalli lamarin?


Duka wannan amsoshin suna a cikin labarin AMRAH NAKE SO! Kuma sannu a hankali duk za ku samu amsoshinsu.


Fatan alkhairi ga masoyana baki ɗaya. Ku sani cewa ina ƙaunarku, ina yinku, iya wuya ana tare fi sabilillah.


Thanks all.


Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:51 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)


Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_




Please Login or Register in order to submit comment