You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

samun sauƙi ba sai idan yana barci?"


Shiru ya yi Mahmouda. Ko kaɗan ba ya son ya ƙara tasar mata da hankali ne. Amma fa ko shi ba ya ba Modu tashi. Babbar matsalar da abin ya shafi zuciya; yana da wuya wanda zuciyarsa ta samu matsala ya tashi, sai dai idan dama ba daga zuciyar ba ne, saboda wasu matsalan ƙirji ne kawai suke fama da shi sai su ce zuciyarsu na ciwo, alhali in zuciya ce ma ba za su faɗa ba, sai dai a gane.


A tsayen da suke suka fara ganin Modu na motsawa, yana ƙoƙarin buɗe idanuwansa da suka gama kumbura tsabar kuka.


Da hanzarinta ta isa gare shi tana ambaton sunanshi,


"Modu..."


Ta zauna a bakin gadon haÉ—e da taimaka masa wurin tashi.


"Sannu Modu. Yanzu kam nan É—in ka ya bar ciwo ko?"


Ta gwada masa saitin da tata zuciyar take.


Baki kawai ya washe mata yana bin ta da kallo. Murmushi ta sakar masa sannan ta miƙe tsaye.


"Nurse ta ce idan kat tashi in hwaÉ—i mata. Za a yi maka gwajin zuciya. (Electrocardiogram (ECG) )"


Barin É—akin kawai ta yi, ta nufi nurses station.




Bayan ta sanar da nurse É—in ne ita kuma ta samu likita ta faÉ—a masa. Izini ya bayar cewa ta je da wasu daga cikin nurses maza, a je da Modu electrocardiograph room (É—akin da injin É—in yin ECG yake) don yi masa aikin yanzu.


Hakan ce kuwa ta kasance. Sai da suka haɗa da dabara kafin Modu ya yarda ya ɓaɓɓako daga bisa gadon, jin sun ambaci sunan Amrah; da duk iya taurin kansa in dai aka ambaci wannan suna, to fa tabbas zai aikata duk abin da aka umurce sa.


A bisa ƙafafuwansa yake taku, akasin tunaninsu kenan. Su a tsammaninsu ma ba zai iya yin tafiyar da kanshi ba, dalilin ma da ya sa likitan ya haɗa da maza kenan. Amma da mamakinsu, ambatan sunan wata mace ya saka shi dauriya haɗe da yin tafiya da kansa.


ECG room É—in suka nufa kai tsaye, a buÉ—e suka tarar da shi, Technician É—in da zai masa gwajin suka samu har ya shiga ciki, su kawai yake jira.


A bisa gado suka kwantar da shi, nan take ya fara ƙoƙarin yi masa gwajin, da na'urar yin aikin. Bai fi minti biyar zuwa goma ba ya kammala, saboda dama ba wani ɗaukar lokaci ake wurin yi ba.


Bayan an gama ya je ya ma likitan magana cewa ya kammala, sai ga shi kuwa har room ɗin ya zo ya zauna a bisa kujera, Technician ɗin kuma ya fita ya bar shi da result ɗin a hannu. Shi kanshi ya yi mamakin result ɗin na Modu; yanda ya tsammani ciwon kwata-kwata ba haka yake ba. Ashe ma bai wani ta'azzara sosai ba. Abin da ya sa Modu ɗin yake yawan jin ciwon, saboda abin ya shafi zuciya ne, ita zuciya kau ko kaɗan ba ta son baƙon abu, duk yanda wani abu ya nemi kawo mata tangarɗa, fat ɗaya za ta iya aika mutum lahira.


Hamdala ya yi bayan ya zauna. Kwance yake Modu idanuwansa a rufe, Dr. Huzaif na bin sa da kallo.


Riyawa yake a ransa akwai magunguna manya guda biyu, wanda ya tabbata ko su kaɗai sun isa su kawo waraka ga zuciyar Modu. Bayan haka kuma, zai ƙoƙarta kyautatawa haɗe da faranta masa, zai barsa da zama a asibitin na wani lokaci ba tare da ya ba shi sallama ba, dan ya samu kula mai kyau. Dan da ganinshi an san ba wani galihu ne da shi ba, ita kanta Fiddou ɗin ba lokacin kula da kanta sosai gare ta ba, to bare kuma Modu mai larurin da dole sai an yi taka-tsan-tsan.


Jijiyoyin da suke aika jini zuwa zuciyar Modu ne suka É—an samu tangarÉ—a, sai kuma wadda ke kai jini har ciki kidneys É—insa. Kuma duk fargabar ko kuma damuwar wani abu ce ta haddasa hakan.


PA ɗinsa ya ƙwala ma kira ya zo, ya aike shi ya kira masa Fiddou. Babu jimawa sai ga ta ta zo, hankalinta a tashe, fargabar abin da za ta ji daga bakin likitan kawai take.


Wurin zama ta nema bayan ta yi sallama ya amsa, ta tsurawa inda Modu yake idanuwa, tana kallon yanda ko motsi ba ya yi.


"Uhm..."


Ta jiyo shi ya yi gyaran murya, alamun yana da buƙatar karkatowar hankalinta gare shi.


"Duk yanda na tsammani ciwon ba haka yake ba. Yau kam za ki ji hwarin labari daga gare ni."


Ya faÉ—a haÉ—e da kanne mata ido É—aya.


Duk da ta ji daɗi sosai a zuciyarta amma ba ta bayyana masa ya gane ba, saboda haushinsa da take ji. Nannauyar ajiyar zuciyar da ta sauke kuwa ita ta tabbatar masa da cewa ta matuƙar jin daɗin furucinsa.


"A cikin kashi ɗari na zuciyar Modu, kashi talatin da biyar za a iya cewa ya gurɓata, ma'ana shi ne yake masa ciwo. Kashi sittin da biyar na zuciyarsa lafiya lau take. Wannan kashi talatin da biyar ɗin ne yake damunsa, shi ne yag gagara daidaita tafiyar numfashinsa, da kuma bugun zuciyarsa yanda ya kamata. Magunguna ne zan rubuta mai, wanda nake da yaƙini da amincewar Allah in dai ya yi anhwani da su tabbas zai samu waraka, zuciya tai za ta koma aiki yanda aka son ta yi."


Ya dakata daga nan, ya É—an juyar da kallonshi zuwa ga Modu, sannan ya sake kallonta ya ce,


"Matsala guda É—ai ce..."


"Da ma na sani walle. Dole dai sai ka tayar min da hankali. Wai dan Allah kai wane irin likita kake?"


Murmushi ya yi wanda har sai da fararen haƙoransa suka bayyana. Ya ɗan tauni leɓonsa na ƙasa, ya lumshe idanuwansa duka biyun, sannan ya buɗe su a fuskar Fiddou.


Duƙar da kanta ta yi ƙasa, tana mai jin takaicin ha ido da shi, saboda muguwar tsanar da ta masa.


"...matsalar ita ce, magungunan suna da tsada sosai, dole sai an fitar da maƙudan kuɗi wurin siyansu."


Dafe gabanta ta yi da jin kalamansa. Lallai kuwa matsala mai girma. Ita yanzu ya za ta yi ta samu kuÉ—in siyan wannan magungunan? Ta kanta take.


"Duk kati guda yana kai sefa dubu ɗaya da ɗari biyar, kuma sai ya sha a ƙalla kati huɗu. Gudan shi ne ad da sauƙin kuɗi; yana kai saifa ɗari takwas, kuma shi kati guda ne zai sha. Insha Allahu matuƙar ya sha wannan magungunan a kan tsari, giɗe zai samu lahiya, matsalar zuciya kuwa sai dai wata ta taso, ba dai wadda yake kan yi yanzu ba."


Sosai da ji daɗin maganarsa ta ƙarshe. Har da murmushin farin ciki ta saki. Sai dai kuma ba a nan gizo yake saƙa ba, a ina za ta samu wannan maƙudan kuɗin wanda za ta siya ma Modu magani? Ta dafe kanta, zuciyarta na jefa ta wata duniyar ta daban, ba tare da ta san ta isa ba.


"Jinkirin siyansu kuwa, tabbas zai iya dagula komai, ciwon na shi ya kai inda ba za a ji daÉ—i ba. A yanzu haka bugun zuciyar Modu a hankali a hankali yake tafiya, saboda wanann jijiyoyin da ba su aika jini yanda ya kamata (blood vessels).


Wannan matsalar da kike ga kamar ƴar kaɗan, tsaf za ta iya dagula komai. Kin ga a yanzu haka yana fama da matsalan ciwon ƙirji, wanda duk waccan matsalar ce sila. Sannan kuma numfashinsa ba ya tafiya yanda ya kamata. Irin wannan matsalar takan haddasa yawan ƙunci, da mutum ya ringa tunanin ya kusa mutuwa, dan ma dai shi ɗin ba hankalinsa ɗaya ba. Tana saka yawan gajiya; ki ji ko ba abun gajiya kika yi kina yawaita gajiya, komin ƙanƙantar abu. Za ta iya saka wa ki ringa jin nauyi sosai a ƙirjinki, kamar an ɗaura miki wani nannauyan abu, wanda ba za ki iya sauke shi ba."


Ya É—an dakata daga nan, sannan ya ci gaba,


"Dole zai daina cin duk wani abu wanda ya shafi cholesterol (masƙi) na tsawon wani lokaci, har mu ga yanda Allah zai yi da shi. Akwai wani mai na nan na musamman non cholesterol ne, ko abinci zai ci da shi ya kamata a yi amfani wurin girkawa. Kar ya sha madara, gyaɗa, mangyaɗa, manja, nono da sauransu, duka dai zan rubuta miki a takarda idan na koma Office. Magungunan da za a nema shi DIXOGIN yana taimakawa ne wurin aika jini, ya isa cikin gaggawa, kamar yanda ya kamata ya tafi, zai improving blood circulation. Shi kuma DIURETICS yana taimaka ma magudanyar zuciya zuwa ƙoda ne, ya taimaki ƙoda wurin tace gishiri da kuma suga wanda ba a buƙata, it makes it easier for your heart to pump. These medicines are very important."


Ya yi shiru daga nan, yana karantar yanayinta mai cike da tsantsar tashin hankali mara misaltuwa.


Kallonsa kawai take, ba ta san sanda hawaye suka fara wanke mata kumatu ba. Bayanan nasa ma jinsu kawai take, ba wai komai ne take fahimta ba, musamman ma da yake faɗo mata kalmomin da tunda take a rayuwarta ba ta taɓa jin su ba. Ita daga Hausarsu sai French wanda ba za a rasa ba kawai take ji. Shi kuwa dama a US ya yi karatunshi, ba zai taɓa iya magana ba dole sai ya sirka turancin, saboda ba komai ne zai ce ya sani da French ko kuma Hausa ba.


***


Ku ma page ɗin nan kyakkyawar fahimta, wata ƙila zai ma da dama daga cikin masu karatu amfani nan gaba.


Na gode, na gode, na gode ƙwarai masoyana. Har ma ban san da bakin da zan gode muku ba. Ina yin ku, ina son ku, ina ƙaunar ku fi sabilillah.


To Gosties👿 kun san kanku, ehen...kuna discouraging ɗina. Shin aikin wahala ne dan ka danna wannan ƴar tauraruwar kawai don ka faranta min rai? Ina tsananin jin daɗin in ga an yi voting, sai in ji ƙarfin guiwar yin typing kodayaushe😁


Duk wacce ke son na yi posting gobe ta ɗaga hannunta. Idan na ga yawanku zan maku, idan kuma na ga babu votes, alamun dai ba kwa son post gobe ne.😎


Me kuke hasashe? Shin yaya Fiddou za ta yi da wannan bawan Allah, wanda yake da buƙatar taimako a halin yanzu? A ina za ta samu kuɗin siya masa wannan magungunan? Ɓangaren su Maryama kuwa, ko kuna hangen nasara a tattare da lamarinsu? Idan sun yi wancan plan ɗin ya ɓaci, shin kuna tsammanin za su dace a wannan? Drop your comments, and then forward it to family and friends🙌


PINKY DURLING
RAZ 2
[8/30, 3:52 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)


Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


4⃣0⃣


Follow me on wattpad: PrincessAmrah


***


Tashi ta yi jiki babu ƙwari, hawaye bai daina kwaranya daga idanuwanta ba, tunani fal a cikin zuciyarta. A hankali take taku har ta isa ɗakin Annur, wanda ta baro Mahmouda a cikinsa.


Ganin yanayinta da ya yi kawai ya tabbatar masa cewa ba lafiya ba. Kuka take wiwi, har da shessheƙa sosai, hannuwanta duka biyu a ka.


A rikice ya miƙe tsaye, ya fara gyaɗa kansa, cike da tausayi ya ce,


"Ki bar kuka giÉ—e, Allah'n da Ya halicce shi ya hi mu so nai, idan kuma ya tahi ne, to tabbas lokaci nai ne ya yi. Ina gudun kar a yi biyu, ke ma ki kamu da wani ciwon."


Rijif! Ta faɗa ƙasa da ƙarfi ta zauna. Kanta ta haɗe da guiwowinta, tana ƙoƙarin shanye kukanta.


"Ya jiki nai? Halan dai da rai nai? An ƙare wancan awo?"


Duk a jere ya sako mata wannan tambayoyin.


Da ƙyar ta samu ta ɗago kanta, cikin sanyin murya ta ce,


"An ƙare wancan awo yana can yana barci, saboda waccan allura ta barci da aka yi mishi ba ta ƙare saki nai ba."


Da mamaki ya ce,


"Ah, to mi da kike kuka halan?"


HaÉ—iye sabon hawayenta ta yi, ta ce,


"Likita ya hwaɗi min magungunan da za a sai ma Modu, wanda siyan su ɗai ne zai sa Modu ya samu sauƙi. Suna da tsada sosai, ko ni ban san inda zan samu kuɗin siyan su ba."


GyaÉ—a kansa ya yi, da tausayi ya ce,


"Halan har nawa ne kuÉ—in?"


Bayani ta masa na kuɗin maganin, da kuma adadin wanda ake so ya shanye. Ta ƙarashe da faɗin,


"Ya ce duk da abun ba mai girma sosai ne ba, zai iya zama mai girma in dai ba a daure an sai mai maganin nan ba."


Da sabon kuka ta dire maganar, ta sake duƙar da kanta a guiwowinta.


Dafe kansa ya yi, zuciyarsa na masa raɗaɗi, tausayin Modu yake, ji yake tamkar ciwon a jikinsa yake. Ina ma dai a ce yana da kuɗin siyan maganin nan? Bai da su. Shi kan shi rufin asiri ne da shi. Lokacin da ya kaɗe Modu ma daga wurin neman aiki ya dawo, kuma bai samu ba. Tashin hankalin da yake ciki a lokacin, ba wai na lururar mahaifiyarsa ne kawai ba, har da takaicin wahalar da ya sha wurin neman aikin, kuma a ƙarshe ya ƙi samu.


Ajiyar zuciya ya sauke, cikin kwantar da hankali ya ce ma Fiddou,


"To do Allah dai ki cire damuwag ga daga cikin zuciyarki. Kar wani abu ya same ta, kin ga dai yanda ta Modu tai yi."


"Ba zan iya ba, ba zan iya ba Mahmouda! Modu na cikin haÉ—ari, haÉ—ari mai wuyar shawo kai. Ban san yanda zan yi ba, ba ni da halin taimakonsa."


"Allah zai rufa asiri, ki kai kokenki kawai wurinSa, ba Ya gyangyaɗi Allah, Yana jin ƙan bayinSa, Yana kuma karɓar adduar bayinSa a duk sanda suka kai maSa kokensu."


Shiru kawai ta yi tana kallonsa. Mamakinsa take, mamakin kalamansa take. Ta ya za ta iya kwantar da hankalinta bayan kuma ba ta da wata mafita?


***


Mai napep É—in take É—aga ma murya ta yanda zai iya jin ta sosai, saboda sautin da ya kunna a ciki.


"Mallam!"


Ta faɗa a karo na biyar, da ƙarfi fiye da yanda ta kira shi a baya.


Rage sautin ya yi sannan ya ce,


"Lafiya? Ai kaman ba a zo inda zan kai kin ba."


"Ehh ga shi tana kira na cewa mu dakata ta hange ni. Dama ita ce ba ta yi kwatancen da kyau ba."


Reverse ya yi, saboda sun wuce ta da yawa. Bayan sun kai inda take ta sauka, ta miƙa masa kuɗinsa sannan ta ta yi taku uku, wanda ya kai ta gaban Hadiza.


Hannu ta ba ta suka gaisa. Da fara'a Maryama ta ce,


"Ai da mun zarce kuwa."


Ita ma Hadiza ta yi murmushin, ta ce,


"Ban wani san kan area'n sosai ba, shi ya sa ma na zaɓi nan ɗin. Kuma ga shi babu hayaniya sosai, babu ƴan sa ido."


"Haka ne."


Hadiza ta faÉ—a.


"Mu je. Akwai wani babban lambu ta can baya. Sai mu biya kuÉ—in shiga mu shiga, kamar za mu fi samun natsuwa a ciki."


Bin bayanta ta yi suka nufi hanyar lambun, ba su wani yi tafiya mai nisa ba suka isa.


Maryama ta fiddo kuÉ—in za ta bayar amma Hadiza ta hana, ita da kanta ta ciro kuÉ—in ta bayar.


A bisa wasu ƙayatattun kujeru suka zauna, babu jimawa aka kawo musu lemuka aka jera a gabansu.


Ajiyar zuciya Maryama ta sauke, ta ce,


"Mun fara magana a waya."


Buɗe robar fanta ta yi Hadiza, ta ɗan kurɓi kaɗan, sannan ta rufe, ta ajje a gabanta. Fuskantar Maryama ta yi da dukkan nutsuwarta, ta saita idanuwanta a cikin nata, ta ce,


"Yanda duk na faɗa miki a waya to hakan ne. Annur ko kaɗan bai zama mutumin kirki ba, face fasiƙi! Mazinaci! Mayaudari!"


Ta yi shiru daga nan, sannan cikin rauni ta ci gaba,


"Ina ƙaunar Annur, da dukkan zuciyata. Ina burin ya kasance nawa, na har abada. A da, ban taɓa tsammanin akwai namijin da zan ma soyayyar tsakani da Allah ba. Ban taɓa tunanin zan so yin aure a wannan ɗan taƙin ba. Sai ga shi na dulmiya, ban farga ba, zuciyata ta tsunduma da ƙaunar Annur Iqra Al-hussein. Ƙaunar da nake masa ta gaskiya ce, wacce hankalina zai tugunzuma a duk sanda zan ganshi cikin wata larura, ko kuma damuwa. Wannan dalilin ne ya sa zuciyata ta ba ni tabbacin Annur ne na gani a Maraɗi. Zuciyata da ta shi kamar akwai wani connection a tsakaninsu; wanda ke ba ni tabbacin cikin halin da rayuwarsa take.


Abin da na kasa in gane shi ne, shin a cikin awanni shidda ne Annur ya tafi MaraÉ—i? Me ya kai shi? Me zai shigar da shi cikin wannan halin, ba tare da iyayensa sun sani ba?


Akwai alamar tambaya a zancen nan. Da alama dai akwai ɓoyayyen al'amari, wanda daga Annur ɗin sai mahaliccinsa kawai suka sani..."


"Sai kuma abokinsa Farouk Sardauna!"




Ta tsinkayo muryar Maryama ta faÉ—a, tana jinjina kai.


"Na tabbata Bobby bai rasa masaniya dangane da wannan al'amarin, tunda kansu a haÉ—e yake, gudansu ba ya yin abu ba tare da shawarar guda ba. Duk wani mugun halinsu tare suke aikata shi."


Ta dakata daga nan, jin wayarta na ringing. Dubawa ta yi sai ga sunan Bobby ɓaro ɓaro ya fito, hakan ya sa ta sakin murmushi, ta ce,


"Kin ga É—an halak!"


Ta amsa kiran, tana ƙoƙarin gyara muryarta daga ta murmushin da take, zuwa ta asalin Maryama ɗinta.


"Hello-salamu alaikum."


Ta furta a tsanake, da muryarta dallah-dallah.


"Maryama ya kike? I have been calling you amma bakya É—auka. Fatan dai kina lafiya. Ya gida? Ya school? Wai, ashe hutun easter ake. Ya su Mama? Ya..."


Ta gaggauta dakatar da shi, dan wannan surutun na shi ba mai tsayawa ba ne.


"Everything is okay."


Ta faÉ—a a takaice, tana kuma jiran abin da zai faÉ—a.


"Uhm...dama Maryama please ina so ki ba ni lokaci mu haɗu. Ina da buƙatar ganinki, idanuwana na matuƙar son su yi tozali da kyakkyawar fuskarki, mai cike da walwala."


'Ya Allah!'


Ta faɗa cikin zuciyarta. Surutun Farouk yawa ne da shi. Duk haƙurin mutum sai ya ƙule sa.


"Farouk na sha faɗa maka cewa iyayena ba za su taɓa bari na tsayuwa da kai ba. Na rasa me ya sa ba ka fahimta. Ba wai ba na sonka ba ne, wallahi halayenka ne ba na ƙauna. Kai ma ka san ba ka da wani abu da zai sa a ƙi ka, fa ce gurɓatattun halayenka, wanda babu na ɗauka a cikinsu."


"Da sauƙi Maryama. Tunda dai kina so na shi kenan, kin gama min komai wallahi. Na tabbata iyayenki abin da kike so shi za su so. Wallahi zan zama na kirki saboda ke..."


"Saboda ni?"


Ta tari zancen nasa.


"Kenan ba saboda Allah za ka nadama ba? Ashe dai tubar ba ta zama ta kirki ba kenan. Duk abin da aka yi saboda wanin Allah, to wannan abun ya zama riya, Farouk."


"Please ki fahimce ni, ba wai ina nufin haka ba ne."


"Ya kake nufi Farouk? Hausa fa ka yi, wacce kai tsaye za a iya fahimtarta."


"Yanzu dai ba wannan ba. Ki min alƙawari in dai na daina komai za ki aure ni."


Ya marairaice murya haÉ—e da yin wannan maganar.


"Ni kam ba wannan ba, akwai maganar da nake so mu yi da kai."


Ajiyar zuciya ya sauke haÉ—e da faÉ—in,


"Allah sa alkhairi ne."


Bayyanannen murmushi ta yi, irin mai narkar da zuciya É—in nan, wanda ke faranta ran Farouk Sardauna.


"Alkhairi ne ma."


Ta É—an dakata haÉ—e da murmusawa, sannan ta ce,


"Wai dan Allah waye Annur?"


Shiru ya É—an yi na tsawon sakan goma, kafin ya ce,


"Wani abu ne?"


Ya gaggauta tambayarta.


"No, kar ka zata wani babban abu ne. Kawai dai tambayarka na yi."


"He's my best friend. A best friend of mine."


"Good. Can you tell me little about him?"


"Yes, why not?"


"Great."


Ta faÉ—a haÉ—e da gyara zamanta, ta É—an kalli fuskar Hadiza da murmushi. Ita ma Hadiza murmushin ta sakar mata, duk da yake ba ta san inda zancen ya dosa ba.


"He's Annur, a son of Pharm Iqra Al-hussein. He's a nice person. Mutumin kirki ne mai riƙon addini..."


"Kamar kai kenan?"


Ta tari zancensa tana murmushi.


Shiru ya É—an yi kafin ya ce,


"What do you mean?"


"Just a question."


Ta ambata har yanzu ba ta daina murmushi ba.


Ko kaɗan ba ya jin zai iya kasa faɗawa Maryama tambayar da ta masa. Amma wallahi in da a ce wata ce ba ita ba, har marinta yana iya yi idan ta masa wannan tambayar banzar. Idan kuwa a waya ne to tsaf zai iya zagin iyayenta, sannan a ƙarshe ya kashe kiran.


"Lemmi tell you the fact; Annur is a nice person, as I told you. But...ehm...duk halayemmu iri É—aya ne. Amma dan Allah me ya sa kika min wannan tambayar?"


"Babu komai fa. Kawai dai ƙawata yake so ne, shi ne take faɗa min sunanka wai kai ɗin abokinsa ne. To ina jin sunan kuma na gane kai ne. Ta ce na bincika mata halayensa ne."


Ta canza akalar zancen, ba haka suka yi da Jiddah ba, kawai dai shawara ta sake ne da zuciyarta. Ba yanzu ya kamata ta bayyana ma Farouk manufar Annur É—in a kanta ba, gwara komai a bi shi a hankali, da sannu za a zo wurin.


"Ok...ok thats nice."


Ya faÉ—a da sauri don kar ta sake yo masa wata tambayar.


"Har ɗazu ma mun tafi Maraɗi tare da su ai. Ƙawar tawa ce ta je gidan danginta a can, to sai muka tafi tare ya kai mu."


Cikin mamaki ya ce,


"Amnur É—in?"


"Ehh fa. Sai dare ma muka dawo, suka sauke ni har gida."


"Gaskiya ba dai Annur nawa ba ne. Saboda tun safe muke tare da shi, har dare sannan ya tafi gida. Da alama dai wani ne ba shi ba."


"Ina tababa fa."


"Wallahi gaskiya nake faɗa miki. Tun safe muke tare ba mu rabu ba. Babu inda ya je, wata ƙila dai mai irin sunan ne."


Gudun kar ta yi insisting ya gano ta ya sa ta ce,


"To ina ji dai kam sunan ne ya zo ɗaya. Ƙila kuma wani Farouk ɗin ne daban abokinsa ba kai ba ne."


Ƙwalwar banza irin ta ƴan shaye shaye kawai Bobby ya ce,


"I think so. Lets back to business bae. Ina muka tsaya?"


"Call me later, please. Am busy right now."


"Please ki É—auka idan na kira ki. Bana jin daÉ—in rashin É—aukar nan da kike sometimes idan na kira ki."


"Insha Allahu zan É—auka. I promised!"


Ta faÉ—a haÉ—e da gaggauta tsinke kiran, ta fuskanci Hadiza da fara'a.


"Done."


Ta furta bayan ta ajje wayar bisa cinyarta. Ta be lemon sprite, ta kurɓa a bakinta.


"Me hakan ke nufi? Ya shafi aikin da muke ne?"


Hadiza ta faÉ—a, saboda ita É—in ba wai tana gane turanci ba ne.


Bayan ta ajje lemon ta ce,


"Sosai ma kuwa. Ina hankalinki ya tafi sanda muna wayar?"


"Yana tare da ni."


Ta faɗa a taƙaice.


Cikin halin ko in kula Maryama ta ce,


"Na gano abin da nake son sani. Ya bayyana min muhimmin abin da ya kamata na sani."


Shiru ta yi Hadiza tana sauraron Maryama. Lemonta take sha a tsanake.


"Ya shaida min duk yinin jiya yana tare da AIA. Ko kaÉ—an ba su rabu ba."


"Waye AIA kuma?"


Dafe kanta ta yi Maryama. Duk iya haƙurinta na jure tambayoyi Hadiza na neman ƙular da ita. Tambaya mara ma'ana, wacce ya kamata a ce ta san amsar. Guntun tsaki ta yi a bayyane, ta ce,


"Ban san dalili ba, kamar dai ƙwalwar taki ba ta ja yanda ya kamata. Ko kaɗan ba na son hulɗa da mutum irin haka."


Kallonta Hadiza ke yi cike da jin haushinta. Kawai dan ita ɗin kanta tana son sanin haƙiƙanin abin da yake faruwa ne, amma da tuni ta gwadawa Maryama halinta na tashanci, wanda take ma duk wani wanda ya nemi ya kawo mata wargi a lamurranta.


"Ko kaÉ—an ba su rabu da Annur ba jiya. Suna a cikin garin nan. Kin ga kenan dai ba Annur ba ne kika gani a MaraÉ—i..."


Miƙewa ta yi tsaye a fusace, cike da masifa ta ce,


"Ke kar ki nemi miyar da ni shashasha mana! Ta ya da idona in ga mutum kuma ki nemi ƙaryata ni? Dan Bobby ya faɗa miki son ransa dole ne sai ya zama gaskiya? To ni dai ko ki yarda ko kar ki yarda na ga Annur a Maraɗi jiya. Ko tantama babu shi ne na gani."


Miƙewa ta yi ita ma Maryama, ta dafa kafaɗar Hadiza, da murmushi ƙunshe a fuskarta ta ce,


"Calm down Hadiza. I din't mean to hurt you. Dawo ki zauna mu ci gaba da maganarmu."


Ba dan ta so ba ta koma É—in ta zauna, tana mai tsananin jin haushin Maryama.


"Ko kaÉ—an kar ki zaci wai

Please Login or Register in order to submit comment