You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yaya ba ka tunanin wani abu zai iya hwaruwa idan aka mata dole? Yanzu hwa lokaci ne da aka daina yayin auren dole, gwamma dai a bar ta ta zaɓa da kanta, gudun samun matsala."


"Kar ka damu kanka Mahmouda. Fiddou ba ita tai yi kanta ba, muna da magabata, wanda dole ne ta ji maganarsu. Don haka ka ƙyale duk wannan tunanin, tana da sauƙin kai sosai, kawai dai damuwa ce da tai yi mata yawa. Kawai dai ka ci gaba da lallaɓarta, namiji kake, ka san hanyoyi da yawa da za ka iya shawo kan mace."


"Haka ne Yaya. Allah ya taimaka mana."


"Ameen ameen Mahmouda. Ka tafi kawai, bayan sati guda É—in sai ka dawo."


Miƙewa ya yi Mahmouda. Fuskarsa a sake ya ma Yaya da Aunty Sahiya bankwana, ya kama hanyar fita.


*


Miƙewa ta yi a bisa ƙafafuwanta, fuskarta ɗauke da murmushi, ta kalli Modu da faɗin,


"Zan je in dawo Ya Noor. Ka min addua."


Murmushi kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba, ya bi ta da kallo har ta fice daga É—akin.


A falo ta tarar da Mama tana kallo. Ta ce,


"Mama shiryawa zan yi yanzu, gidan su Amrah da na faÉ—a miki zan je nake son zuwa."


Mama ta ce,


"To madalla. Kar ki manta fa, ki sanar mata duk halin da ake ciki, wata ƙila akwai wata gudummuwa da za ta iya bayarwa wurin samun warakar Annur."


"Insha Allahu zan faÉ—a mata Mama."


Ta tashi ta shige É—akinta.


Green ɗin atamfa ce ta saka mai zanen ganye pink. Ɗinkin riga da skirt ne da ya karɓi jikinta. Ɗaura ɗankwalinta ta yi sannan ta zira pink hijab iya guiwarta, ta shafa turaren humra, ta fito daga ɗakin hannunta riƙe da wayarta.


ÆŠari biyar Mama ta bata, sannan ta mata fatar alkhairi ta fita.


A bakin ƙofa ta ci karo da Mahaifinta da kuma Yayansa, suna ƙoƙarin shigowa. Da faraa a fuskarta ta duƙa har ƙasa ta gaishe su.


"Kawu Imrana an dawo lafiya?"


Ta furta kanta sunkuye ƙasa.


"Lafiya ƙalau Maryama. Sannu kin ji. Ina ta ganin saƙunanki ta inbox duk Friday na happy Friday ai. Allah ya miki albarka."


"Ameen Kawu."


"Sai ina?"


Abba ya tambaye ta.


"Zan je gidan su Amrah ne Abba. Jiya da muka haÉ—u wurin sauka duk sai na ji kunya. Ban koma ba fa tun ranar farko."


Abba ya ce,


"Lallai fa ya kamata ki je kam. Ba jimawa zan yi a gidan ba Office zan koma ai da kin tafi da motar, Mallam Ya'u kuma a can Office na baro shi."


"Babu komai ai Abba. Zan hau napep."


"To Allah ya tsare. Ki gaishe su."


Miƙewa ta yi tsaye haɗe da ambatar to, sannan ta tafi.


Isar ta gidan su Amrah ta samu Umma zaune da baƙuwa a tsakar gida. Jin sallamar Maryama ya sa Umma sakin murmushi haɗe da amsa sallamar, tana mata sannu da zuwa.


"Iso daga ciki Æ´ata. Ga tabarma ki zauna."


Da faraa Maryama ta zauna bisa tabarmar, sannan ta gaishe su.


Amsawa suka yi su duka biyun, baƙuwar ta miƙe tsaye, tana furta za ta wuce.


"Ina zuwa Maryama. Bara na mata rakiya."


BaÆ´uwar ta murmusa ta ce,


"Babu komai wallahi Yaya Murja. Ki sha zamanki."


"A'a Zaliha. Mu je ko bakin ƙofa ne."


Ba ta jima ba ta dawo, tana ba Maryama haƙuri.


"Babu komai ai Umma."


Bayan ta zauna ta ce,


"Ya kika baro su Mama?"


"Lafiya ƙalau Umma. Sun ce ma a gaishe ki."


"Ina amsawa."


Daga nan shiru ya biyo baya. Miƙewa ta yi Umma, ta ce,


"Akwai kwaÉ—on zogale na nan kuwa da na ma Mallam ya yi saura. Bari na kawo miki."


Murmushi kawai ta yi Maryama, ta bi Umma da ido har ta ƙarisa cikin kitchen. Sosai take yabawa da kirkin matar. Tana da karamci sosai ba kaɗan ba.


Roba ce ta taho riƙe da ita a hannunta, ta rufe da wani ƙaramin plate.


A gaban Maryama ta ajjiye, da faraa ta ce,


"Ci ki ƙoshi. Idan borkonon bai miki ba sai in kawo miki ki ƙara."


BuÉ—ewa ta yi Maryama ta fara ci, sosai kuwa ya mata daÉ—i, saboda dama ita É—in maabociyar cin zogale ce.


Sai da ta ci kamar rabinsa, sannan ta yi hamdala ga Allah, ta miƙe haɗe da nufar randar gidan, ta wanke hannunta sannan ta sha ruwan ta dawo.


A rayuwar Umma, tana son ganin mutum well social, wanda ba ya da jiji da kai ko kuma ƙyamar talaka. Ko ba a faɗa mata ba ta san cewa Maryama suna da rufin asiri a gidansu, amma kuma ga shi babu ƙyama babu komai ta ci abincinsu, ta sha ruwan randarsu. Wasu halayen na Maryama sukan tuno mata da Amrarta, sosai ba kaɗan ba. Girmama na gaba da yawaita fara'a, duka haka Amrah take.


Bayan ta zauna Maryama, ta sake yi wa Umma godiya, sanan ta É—ora da faÉ—in,


"Umma dama akwai wata magana da nake son sanar da ke."


Gyara zamanta ta yi Umma, ta ce,


"Allah ya sa lafiya."


Murmushi ta yi Maryama, ta ce,


"Lafiya ƙalau Umma. Dama kan maganar Annur ne."


"To ina saurarenki."


Umma ta faÉ—a.


Bayan ta sauke ajiyar zuciya Maryama, ta ce,


"Umma abubuwa da dama sun faru bayan bari na gidan nan. Na shiga cikin rayuwar Annur sosai, na gano munana halayensa da kika faɗa min, har ma sun zarce yadda kike tunani ɗin. Sannan kuma wani katari da aka yi, ƙanwar nan tashi Dr. Islam da kike faɗa min ƴar wulakanci, yaronta Abdul tare suke da ƙanina Muhammad a makaranta, har ta silarsa ma mun ƴulla zumunci da ita. A taƙaice dai, na shiga rayuwarsa Annur tsamo tsamo, na nemi ceto shi daga halin da yake ciki, sai kuma wata matsala ta kunno kai."


Shiru ta yi daga nan, tana nazarin ta inda za ta fara sanar da Umma cewa ba shi ne real Annur ba, shi ɗin na ƙarya ne.


"Uhm, ina saurarenki Maryama."


Maryama ta ci gaba da,


"Ta hanyar wata kilakin Annur, na gano cewa ba ainahin Annur ba ne a gidansu."


Ido Umma ta ƙwalalo tana kallon Maryama. Ta ma rasa gane inda maganar tata ta dosa.


"Mun gano inda Annur É—in Amrah yake. Cikin halin hauka muka same sa, wadda aka tabbatar mana cewa ya É—auki kusan tsawon shekaru uku a wannan halin, a garin MaraÉ—i. Yanzu haka maganar da nake miki Umma, Annur na gidanmu ajje, ana ba shi kulawa."


Ta kasa gasgata maganganun Maryama, sai dai kuma tana hango tsantsar gaskiya a cikin ƙwayar idonta. Cikin muryar mamaki ta furta,


"Ta ya hakan za ta faru? Me ya sa kuma kamanninsu É—aya babu bambanci? Kenan su É—in Æ´an biyu ne?"


"Abin da har yanzu nake tambayar kaina kenan, na kuma gaza samo amsa. Kawai dai abin da na sani É—aya ne, shi ne basu da bambanci ko kaÉ—an. Bambancin kawai shi wannan cikin halin hauka yake. Kuma kullum cikin ambatar sunan Amrah yake, yana furta Amrah yake so. Amrah zai aura. A kai shi inda Amrah."


Runtse idanuwanta ta yi Umma. A hankali ta buÉ—e su, cikin mamaki ta ce,


"Na tabbata ba za ki min ƙarya ba Maryama. Na yarda da ke, na kuma yarda cewa wanda kika tsinto ɗin shi ne ainahin Annur, saboda ko bayan haukacewarsa kafin a ce mana ya warke, subbatunsa kullum a kan Amrah ne, yana faɗin ita yake so. Amma da mamaki. Ta ya aka yi hakan ta kasance?"


*


Ruwa da lemo Mama ta kawo ma Kawu Imrana da kuma Abba. Bayan sun gaisa ne take ce masa,


"DaÉ—a Alhaji tunda ka tafi sai muka ji ka shiru, kamar ma ka manta da kana da dangi a Katsina."


Murmushi ya yi bayan ya sauke glass cup daga bakinsa. Ya ce,


"Ta ya zan iya mantawa da ku? Kuna raina a kodayaushe. Aiki ne kawai ya sha gabana. Amma yanzu komai ya daidaita, na gama, na kuma dawo gida cikin iyali da dangi."


Abba ya murmusa, ya ce,


"Hakan ya fi ai. Muna ta fama da kewarka."


Sosai suke wasa da dariya da junansu, tamkar Kawu Imrana ba shi ba ne babba. A ƙarshe ya yi gyaran muryarsa, ya ce,


"Wata shawara ce na yanke da ni da zuciyata. Cewa zan haÉ—a yaran nan aure. Ina nufin Ahmad Deedah da kuma Æ´ata Maryama."


Idanuwansu buÉ—e cike da farin ciki suke dubar Kawu Imrana. Tun Abba bai ce komai ba Mama ta yi saurin faÉ—in,


"Lallai gaskiyar Hausawa ne da suka ce, abin da babba ya hango yaro ko ya hau turmi ba zai taɓa hango shi ba. Da gaske na ji daɗin wannan al'amarin sosai, na kuma tabbata akwai kyakkyawar alaƙa a tsakanin yaran, za su daidaita kansu."


Tana kaiwa nan Abba ya ce,


"Sau ɗaya wannan batun ya taɓa faɗo min a rai, sai dai kuma na bar wa cikina, sanin halin yaran yanzu, kar su watsa mana ƙasa a ido."


Kawu Imrana ya ce,


"Kafin na tinkare ku da zancen sai da na yi maganar da Deedah, cikin hikima na nemin jin tsakaninsa da Maryama. Yake faɗa min yadda suke, akwai zumunci sosai a tsakaninsu. Saboda haka ba na ji ko kaɗan za su baɗa mana ƙasa a idanuwa. Addua kawai za mu musu, Allah ya sa wannan haɗin ya zama alkhairi a tsakaninmu baki ɗaya."


"Ameen ameen Yaya. Gaskiya ka yi tunani mai kyau. Tunda dai dama yana aikinsa, ai sai maganar aure kawai. Ita É—in kuma za ta iya ci gaba da karatunta ko a gidansa."


Da haka suka miƙe, Abba ya ce zai miyar da shi gida, shi kuma daga nan zai koma Office.


Bankwana Mama ta musu, sanann ta dawo ta zauna. Tana jin farin ciki sosai lulluɓe da zuciyarta.


***


*To fa! To fa masu karatu! You see ba. Kun ga abin da yake shirin faruwa ko?😱 wai Deedah za a haɗa aure da Maryama, wacce ke da burin zame ma Annur Amrarsa da ya rasa. To ya wannan abu zai kaya? Ko Maryama za ta amince da wannan zaɓin na iyayenta? Idan ta amince ya makomar rayuwar Annur? Tirƙashi! Akwai aiki mai girma.*


*Shin akwai wani taimako da Maman Amrah za ta iya yi ma Maryama ta hanyar warwaruwar wannan ƙullin?*


*Mun dai ga halin da Sans ya shiga, a wasu shekaru da suka gabata. Shin komawar da zai yi Bama ko zai zame masa alkhairi? Iyayensa sun mutu kuwa? Wane dalili ne ya saka shi dawowa Katsina bayan kuma shi É—in É—an Maiduguri ne? Me ya sa halayensa baki É—aya suka munana, har ya koma halin da yake kai a yanzu?*


*Ku ci gaba da bibiyata, sannu a hankali duk za a samu wannan amsoshin. I love y'll Fisabilillah. Kun sani ai.😀*


*Kar ku manta, sai kuna yi kuna kankaro mutunci. Yanzu kam abun ba dama, ghosts sun yi yawa. Sannunku kun ji? Babu kunya a karanta a ƙetare kyakkyawar tauraruwar nan mai daɗin dangwalawa.😁*


Thanks all


Pinky durling💞
RAZ 2
[9/1, 1:39 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_




Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*




5⃣2⃣


Wattpad: PrincessAmrah


***






Tsaye ta miƙe bisa ƙafafuwanta. Fuskarta ba yabo ba fallasa ta fuskanci Umma da faɗin,


"Umma zan tafi. Amma don Allah ina buƙatar taimako daga gare ki."


Da fara'a Umma ta ce,


"Allah sa bai fi ƙarfina ba."


Maryama ta furzar da zazzafan iska daga bakinta, a lokaci guda kuma ta sauke ajiyar zuciya, ta ce,


"So nake ki ringa zuwa gidanmu akai-akai wurin Annur. Ina tunanin ganinki da zai ringa yi ƙila ya ringa tunowa da wasu abubuwa na Amrah, ta sanadiyyar haka har ƙwalwarsa ta dawo daidai. Da na yi tunanin na ringa kawo shi nan da kaina, sai kuma nake gudun faruwar wani abu; kar wancan Annur ɗin na ƙarya ya aikata wani mummunan abu, duk da yake dai har yanzu ba mu san taƙamai-mai yadda abun nan ya kasance ba."


Dafa kafaÉ—ar Maryama ta yi Umma. Ta ce,


"Insha Allahu zan ringa zuwa kamar yadda kike da buƙata. Amma a ganina, me zai hana ku miyar da shi gidansu, tare da bayyana duk yadda abin ya kasance? Kamar hakan zai fi wannan ɓoye-ɓoyen ai."


Maryama ta ce,


"Zan yi hakan Umma. Sai dai lokaci bai yi ba har yanzu. Ko kaɗan ba na so Yaa Noor ya koma gidansu da hauka, saboda ba mu san ƙudirin wancan na ƙaryar ba. Amma kin ga idan ya ji sauƙi, zai iya nemawa kansa kariya, zai kuma iya tabbatarwa iyayensa cewa shi ne ainahin Annur."


"Tabbas kuwa kin yi gaskiya Maryama. Allah Ya ba shi lafiya. Ki min kwatance gidanku insha Allahu zan zo gobe."


Kwatancen kuwa ta yi ma Umma, sannan ta kama hanyar barin gidan.


Da faraa ta shiga gidansu bayan ta yi sallama. A falo ta samu Mama zaune da hijabi a jikinta, da alama sallar azahar ta gama, saboda lokacin har sha biyu ta wuce.


"Sannu Maryama. Har an dawo?"


"Na dawo Mama."


Ta faÉ—a cikin muryar gajiya haÉ—e da cire hijabinta.


"Umman Amrah ta ce na gaishe ki Mama. Gobe ma za ta zo ta duba Yaa Noor."


Mama ta ce,


"To Allah Ya kai mu. Ina amsawa. Sai ki nufi sallah ko. Idan kin fito ki kai ma Annur É—in abincinsa, ki ba shi magani. Ki zo ki ci naki ke ma."


"To Mama."


Ta furta bayan ta miƙe. Ta nufi ɗakinta.


Sai da ta ɗan watsa ruwa sannan ta saka ƙananan kaya ta fito. Abincin na Modu ta zuba masa a plate, sannan ta nufin ɗakin nasa, fuskarta ƙunshe da murmushi.


Yana ganinta ya miƙe tsaye, da alamun dama ita yake tsumaye.


"Ya Noor sannu da hutawa."


Ta faÉ—a cikin sassanyar muryarta, bayan ta zauna a bakin gado.


Bai ce da ita komai ba, kamar yadda dama ba ta yi tsammanin jin wani furuci daga gare shi ba.


"To ga abincinka nan. Ka ci sai ka sha magani. Ina zuwa bari in dawo."


Ta bar ɗakin, babu jimawa sai ga ta ta dawo hannunta riƙe da wayarta.


Samunsa ta yi bai ci komai ba. Hakan ya sa ta ɓata fuskarta, ta saita idanuwanta a cikin nasa.


"Me kake nufi na ga ko taɓa abincin ba ka yi ba. Ko wani abu ya faru ne? Akwai abin da kake so Yaa Noor?"


Duk ta marairaice fuska, cike da damuwa.


GyaÉ—a mata kansa ya yi, take ta fara ganin ruwan hawaye a idanuwansa. Nan take jikinta ya É—auki rawa. Ba ta san me ke damun Modu ba. Yau ga shi yana kuka, wanda tunda ta É—auko shi yau ce rana ta farko da ya yi kuka.


"Yaa Noor na maka laifi ne? Bayan na tafi Mamana ta maka wani abu ne? Ko Abba ne? Please tell me."


Runtse idanuwansa ya yi tare da matso wasu ruwan hawayen. Ya sunkuyar da kansa ƙasa.


"My God!"


Ta dafe kanta, tana jin wani yanayi mai wuyar fassarawa. Ba ta san me yake damunsa ba.


"Amrah ta ƙi dawowa gare ni, bayan kuma ta san ba zan iya rayuwa ba tare da ita ba. Me ya sa za ta min haka? Me ya sa za ta min nisa ta ƙi waiwaya ta?"


Cike da tausayi ta sauke ajiyar zuciya, cikin kwantar da hankali ta fara masa magana,


"Ka daina kukan to ya isa haka. Mun yi waya da Umman Amrah, ta ce min gobe za ta zo..."


Bai ko bari ta rufe bakinta ba ya yi caraf ya ce,


"Tare da Amrah za su zo? Yeee! Na ji daÉ—i zan ga Amrata."


Ɗan taunar leɓonta ta yi Maryama. Ta ce,


"Ai in dai har ba ka daina kukan nan ba to zan hana ta zuwa."


Hannuwansa duka biyun ya sa ya ringa shafar hawayensa, yana faÉ—in,


"Na daina. Allah ba zan kuma yin kukan ba."


"Yauwa Yayana. To ka ci abincinka. Ko ni kake so na ba ka a baki?"


Bai ce mata komai ba ya fara zira abincin a bakinsa, hannu baka hannu ƙwarya.


Sai da ta tabbatar ta ba shi magani sannan ta masa sallama ta fita, saboda jin Mama ta ƙwala mata kira, kuma ma akwai abin da take son yi a waya, kukan da ya yi ne ya dakatar da ita.


Kusa da Mama ta zauna bayan ta É—ora wayarta a bisa cinya. Ta ce,


"Mama ga ni."


Tun kafin Mamar tata ta ce komai suka ji sallama. Wata ƙawar Mama ce ta yi sallamar, fuskarta ƙunshe da faraa.


Amsa sallamar suka yi a tare, Maryama ta gaishe ta, sannan ta ba su wuri.


A bisa gadonta take kwance. Ta kunna datarta, sannan ta shiga website É—in da suka fara magana da Sandra.


Tana shiga ta inbox ɗinta ta ci karo da lambar Dr. Hamdan M. Ramat, sai kuma ta Dr. Aqaaq Saifullahi daga ƙasa. Ta ba ta haƙuri cewa ta ji ta shiru ba ta neme ta ba, ayyuka ne suka sha kanta. Ganin kamar ba ta kusa Dr. Sandra ɗin, ya sa Maryama ta sauka, bayan ta ɗauki lambobin.


Ta Aqaaq Saifullahi ta fara nema Call forwaded, hakan ya sa ta latsa ta Dr. Hamdan É—in.


Bugu uku ya ɗauka da sallama ƙunshe a bakinsa, ita ɗin ma haka. Hakan ya sa suka amsa sallamar a tare, Maryama ta gaishe shi cikin girmamawa. Cikin seconds kaɗan ta gano cewa Dr. Hamdan mutumin kirki ne, babu girman kai ko kaɗan a tattare da shi, a yanayin da ya amsa gaisuwarta kawai.


"How may I help you?"


Ta jiyo muryarsa ya ambata, cikin sassanyar muryarsa mai cike da dattako.


"Ahmm...I'm Maryam by name, calling You from Katsina."


"Go on..."


Ta ji ya ambata, da alama yana wani aiki ne, kasantuwar likitoci dama lokutan kansu ƙalilan ne.


"I heard alot about you, from Dr. Sandra. So, I just decided to contact you, am sure you'll help me out of my problems."


"Uhm."


Ya faÉ—a yana saurarenta.


"My brother is seriouly ill, for a long time. He has a mental problem, or may be a lost of memory, I don't exactly know."


"Oh! This is serious. The most important thing is that in gan shi zahiri. Kin ce you are from Katsina right?"


"Yes Dr."


Ta faÉ—a cike da girmamawa.


"Can you come to Maiduguri?"


Ras! Ta ji gabanta ya faÉ—i. 'Maiduguri?' ta ambata a birnin zuciyarta. A yadda take jin matsaltsalun Borno ne za ta yi fatar kai kanta can? Lallai kuwa akwai damuwa.


"Are you with me?"


Ta ji ya ambata. Hakan ya sa ta gaggauta faÉ—in,


"Ye...yes Dr."


"Ok. The best solution shi ne a kawo shi É—in, saboda I can't decide anything without seeing the patient. Zan duba schedules nawa, zan ba ki appointment. Ki kira ni by 8pm today."


"Thank you very much Dr. I'll call you by Allah's will."


Ta kashe kiran. Tana jin yadda gabanta ke faɗuwa. Saboda har ga Allah ita kam tinkarar Borno a ganinta babban siyar da rai ne. Idan ma har ta amince za ta je ɗin, ta tabbata iyayenta ba za su amince mata ba. Miƙewa ta yi jiki babu ƙwari ta jona wayarta caji, sannan ta koma falo wurin Mama.


Ta samu har baƙuwar ta tafi, sai Mama kaɗai zaune tana kallon tashar Arewa 24, da suka saka film ɗin Ƴar Duniya.


Yanayinta kawai Mama ta karanta ta tabbatar akwai abin da yake damunta. Ba ta damu da sanin ko miye ba, saboda ta fahimci kamar tirsasa sanin damuwarta ne ke haddasa take shirga mata ƙarya.


"Maryama albishir kuwa nake so na miki."


Kwantar da kanta ta yi a ciyar Mama, ta zame É—ankwalinta da nufin ta mata susar kai.


"Ina jin ki Mamana. An dai je a É—auko Hammad daga School ko? Don ni kam tsoron mitarsa nake."


Murmusawa ta yi Mama, ta ce,


"Mun yi waya da Abbanku yanzun nan, ya ce ya tura Mallam Ya'u ya É—auko shi."


"Yauwa. Don ni kam tsoron Hammad nake. Rigimarsa yawa gare ta."


Murmushi kawai ta yi Mama. Ta ce,


"ÆŠazu Kawunku ya zo, kin sani ai."


"Ehh Mama."


Ta faɗa tana jawo tsoron kalabarta guda, tana gyara tufƙarta.


"Sun yanke shawarar haÉ—a ku aure, ke da yayanki Deedah..."


Zabura ta yi Maryama haɗe da miƙewa zaune, ta tsura duka idanuwanta a fuskar Mama. Cike da mamakin jin kalamanta.


"Me ya faru?"


Mama ta faÉ—a, ita ma tana kallon Æ´ar tata.


"Mama don Allah ki ce min wasa kike ba gaske ba."


"Ta ya zan miki wasa a abu mai muhimmanci kamar aure? Hukunci ne daga kawunku ya yanke shi, na kuma tabbata babu abin da zai sa a canza shi."


Cikin daƙiƙu kaɗan ruwan hawaye suka gama wanke fuskar Maryama, tamkar an ɗebi ruwa an kwara mata.


"Mama me ya sa kawu Imrana zai mana haka? Me ya sa ba zai bar kowa da ƙudirinsa ba? Na tabbata Yaya Deedah na da wacce yake so, yana da wacce yake da ƙudirin aure, kamar yadda ni ma ba ni da ƙudirin aurensa, nake masa irin soyayyar yaya da ƙanwa. Don Allah a bar ni da ƙudirina Mama, a bar ni na fidda gwanina da kaina, wallahi ba na son auren Yaya Deedah."


Ta faÉ—a a jikin Mama, tana kuka sosai tamkar wacce aka ma dukan tsiya, ta ko'ina jikinta karkarwa yake.


Me ya sa za a mata haka? Me ya sa ba za a bari ta ƙarisa kyakkyawan aikin da ta ɗauko ba? Don me ya sa ba za a bar ta ta zame ma Annur Amrarsa da ya rasa ba? Sai da suka gama shaƙuwa da Annur ne za a mata wannan zaɓin? Yaushe rabon da a yi auren haɗi? Kamar iyayen yanzu sun waye ai, sun daina yi wa yaransu auren dole, saboda sun fuskanci matsalolin da yake haifarwa.


Kuka take mai sauti, mai cike da tashin hankali da neman agaji. Sosai take jin wani irin raɗaɗi da zugi a zuciyarta, tsanar Ahmad Deedah na shiga ta kowanne saƙo da ke cikin zuciyarta.


***


Suna daf da shiga garin Bama suka fara ganin tashin hankalin da ke wakana a garin. Da gawarwakin sojoji suka fara cin karo, wanda ya ƙara tsoratar da su. Sojoji duk training ɗin nasu da komai amma a haka aka karkashe su, aka yasar da gawarwakinsu, wato don ma mutane su gani su ƙara tsorata.


"Shi kenan na rasu su! Na tabbata an gama da su..."


Ya fasa ƙara mai ƙarfi, yana mai fuskantar dreban da duka hankalinshi.


"Ka gani ko? Da alama sun cinye garin baki É—aya. Sun gama da kowa da ke ciki."


Dakatawa ya yi da mota dreban. Ya ma rasa yadda zai yi da Sans. Kallonsa yake cike da tausayinsa. Wannan babbar jarrabta ce, mai wuyar hayewa. Tun sadda suka kamo hanyar garin Bama Sans ke ba Dreban labarinsa, da duk abin da ya faru tun farkon kiran da Abbansa ya masa.


Kamar da wasa suka ringa jiyo ƙarar mota, da kuma hasken fitilun motocin da suke gabatowa.


Hankulansu ne suka tashi. Dukkanin nutsuwarsu ta gushe. A hankali Sans ya buɗe murfin gaban motar, ya shawarci dreban ma da ya ƙoƙarta ficewa cikin hikima, ta yadda ba za a gan shi ba, duk dayake cewa ba su san ko su waye tafe ɗin ba.


Daga bayan motar suka ɓoye, maƙalƙale da juna suke, ƙirazansu na duka, duniyarsu na juye musu.


Suna jin sadda motar farko ta wuce da ƙara tiiiii! Kamar za ta tashi sama. Ta biyun ce ta ƙoƙarta dakatawa a gefen tasu motar, tare da kashe wutarta.


Sunan Allah suke son ambata amma sun neme shi sun rasa. Tashin hankali suke ciki wanda suka gaza tuna kalmar addua ko guda.


Fincikarsa ya ji an yi Sans, cikin wannan halin ya kalli matashin da ya finciko shi ɗin. Sanye yake da dark glasses, hannunsa riƙe da bindiga ƙarama, gudan hannun kuma ya shaƙure Sans ɗin da shi, yana kallon cikin idonsa.


Kafin ka ce me, wurin ya cike da bataliyar Æ´an ta'addan, wanda mafi rinjaye na cikinsu sanye suke da kakin sojoji, da alama mutanen sojojin da suka kashe ne, suka cire kayansu suka miyar a jikinsu.


Dariya wani daga cikinsu ya fasa da ƙarfi. Ya kalli Dreba da ya gama tsurewa ganin yadda ake jijjiga Sans. Bai ankara ba ya ji sautin bindiga, an harbi gefen titi da ita. Cikin tsoro da kiɗima ya ce,


"Don Allah don Annabi ku min rai, wallahi na tuba, ku yi haƙuri don Allah, ƙaddara ce ta shigo da mu. Kar ku mana komai don Allah."


Wani ƙato baƙi-ƙirin mai jajayen idanuwa, fuskarnan tasa ɗaure tamau ya kalli dreban da faɗin,


"Ba a magana a duk inda muke. Duk wanda ya yi ta kuwa furucinsa na ƙarshe kenan a duniya. Zan maka uzuri, ka ƙara kalma guda kawai, ko kalimatushshahada ka yi, wata ƙila ka samu rabo a can."


Matasan da za su kai kimanin biyar suka tulle da dariya, banda wanda ya yi maganar.


Bakinsa rawa yake dreban, baki É—aya jijiya da jininsa yake jin suna dakatawa da aiki, sanadiyyar harsashin bindiga da ya ji a saitin zuciyarsa.


"Allah, Allah!"


Su ne kalmominsa na ƙarshe, sanann rayuwarsa ta

Please Login or Register in order to submit comment