You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi take away mu tafi da shi, idan mun ji yunwa sai mu ci."


GyaÉ—a kai ya yi Abba. Da murmushi a fuskarsa ya ce,


"Ke dai zakwaÉ—i ne kawai. Sai a yi a tafi ai. Mallam Ya'u tun É—azu ya iso, yana zaman jiranki."


Muhammad ne ya fito daga ɗakinsa sanye da pyjamas light brown. Yana miƙa da muryar barci ya ce,


"Yaya Maryama ina za ki je?"


"Zan yi tafiya ne Hammad. Include me in your prayers, please!"


Matsowa ya yi daf da ita ya ce,


"Ina za ki je haka Yaya Maryama? Ba fa ki sanar min ba."


Harararsa ta yi cikin wasa, ta kama hannuwansa duka biyu, ta ce,


"Naughty you. Kawai dan zan yi tafiya dole sai na sanar da kai? Yaron nan fa ka raina ni ma."


"A'a fa Maryama. My boy is not a naughty boy, he's a good boy, right?"


Ya kalli Muhammad yana masa murmushi.


Kai ya É—aga ma Abban nasa, ya ce,


"To Abba ka ce mata ta tafi da ni."


"Abba ka gani ba? Da gaske yaron nan ya raina ni fa. In banda rigima ko wanka bai yi ba sai ya ce wai a ce na tafi da shi?"


Mama ta murmusa ta ce,


"Rabu da ita yarona. Super market za mu je anjima idan ta tafi. Just let her go, wayo za mu mata."


"To Yaya Maryama a tafi. Daike iyayena suna so naaa!"


Ya ƙarisa maganar da jan ƙarshen, yana mata gwaliyo haɗe da rugawa ya ɓoye bayan Abba.


"Uhm...kanka dai ake ji yaro. Abba barin fita."


A tare Mama da Abba suka ce,


"To Allah Ya tsare hanya."


Mama ta taso ta matso inda take.


"Allah yana tare da ke, Maryam. Insha Allahu zai kare mana ku, za kuma ku yi nasara a kan wannan nannauyan aiki da kuka fara. Ki tafi cikin aminci, adduata tana tare da ke, everywhere you go. Please contact me or your father when you need any help, okay?"


Kai ta É—aga Maryama, da murmushi a fuskarta ta ce,


"Insha Allahu. Thank you very much Mama."


Ta fita daga É—akin.


Sai da suka fara biyawa suka É—auki Jiddah sannan ta kira Hadiza cewa sun taho ta fito bakin titi. Ko da suka isa kuwa ta fito É—in, su kawai take jira suka tafi.


***


Tun bayan shigarsu asibitin take rarraba idanuwa, zuciyarta ƙagare take da ganin mara lafiyan, idanuwanta na burin yin tozali da shi.


Hadiza ce gaba sai Jiddah da Maryama biye da ita a baya. Babu mai furta komai a cikinsu.


Suna isa bakin ƙofar ɗakin Modu suka ringa jiyo maganganun Fiddou da Dr. Huzaif. Masifa yake mata da iya muryarsa. Iya ɓacin rai yau ya shige shi. Dr huzaif bai kasance ɗaya daga cikin mutane masu saurin ɓacin rai ko kuma ɗaukar zafi ba, sai dai kuma yau a yanayin yanda yake faɗan ya isa ya tabbatarwa kowa cewa ransa ya hasala.


"Ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba na hwaɗi miki a gaggauta siyan maganin nan. A ƙarshe har tambayarki nai yi akwai kuɗin siyan maganin? Baƙar magana kika yi min. Kuma sai yanzu in zo ki kama ce min wai ba a samu kuɗi ba? Halan ban hwaɗi miki zuciya tai tana iya kai matakin da ba za mu so ba? Siyan magungunan nan ne kaɗai zai kawo ma giɗe sassauci, to kuma ke banda rashin kunya babu abin da kika ƙware da shi. To ni kam iyakar abin da zan iya yi kenan, magani kuma idan kin ga dama kar a siya, I did my best, and leave you the rest."


Ya kamo hanyar barin ɗakin. Kiciɓis ya yi da su Hadiza, hakan ya sa shi ɗan kauce musu, yana neman barin ɗakin.


Cikin azama Hadiza ta ce,


"Dr. Dan Allah ka yi haƙuri. In dai kuɗin magani ne ga su a siyo a ba shi. Ka ma Fiddou uzuri, wallahi ta kanta take ita ma."


"Biyo ni na rubuta miki, a gaggauta siyo masa su yanzu."


Ba ta ko bi ta kan su Maryama ba, ta bi bayan likitan kawai suka fice daga É—akin, hankalinta a tashe.


Tun bayan shigowarsu hankalinsu yake gare shi. Zaune yake ya naɗe ƙafafuwansa kamar mai zaman tahiya. Ya fuskanci daidai ƙofa sai faman yaƙe yake. Cikin dariya ya ce,


"Na faÉ—a miki ki ringa ramawa. Haka kawai sai yaita miki masifa?"


Sai kuma ya yi shiru, take hawaye ya fara kwaranya daga idanuwansa.


"Halan missa kake kuka Modu? In dai dan ka ga ina yi ne to ni ma na daina, ka gani ba? Na share hawayen."


Ta ƙoƙarta yin murmushi.


Mamaki bai gushe daga fuskokin ƴan matan biyu ba. Da gaske babu bambanci tsakanin Annur da Modu. Sai dai kuma kallo ɗaya duk wani mai ƙwalwar kirki zai ma Modu ya tabbatar da cewa ya jima a cikin halin taɓin hankali. Saboda har idanuwansa sun juye, irin na mahaukata sosai. Komai nasa abun ƙyama ne; kayan jikinsa, fuskarsa, gashin kansa da komai ma.


"Ka tsaya da kukan nan ge, walle na yi shiru hwa."


Murmushi ya yi kuma, cikin wata murya kamar mai hankali ya ce,


"Amrah ta taɓa faɗa min a duk halin da na tsinci kaina na zama mai haƙuri. Ko tana raye ko ba ta raye, in rinƙa tunowa da wannan maganar, ta ce wai hakan zai sa na samu riba mai girma a rayuwa."


Sai kuma ya ci gaba da yaƙe haƙoransa.


Mutuwar tsaye kawai su Maryama suka yi.


'Amrah!?'


Su duka biyun suka jinjina a ƙasan ruhinsu.


19th Aughust 1987
BAMA, BORNO STATE.


A yi haƙuri na ji na shiru kwana biyu, abubuwa da dama suka sha kaina, kuma dai har yanzu ban gama samun ƙarfin jikina ba. Dan Allah ina barar addua'arku, Allah Ya biya mana buƙatummu na alkhairi baki ɗaya.


Yanzu za ku fara jin salon labarin yana sauyawa; za mu koma yinsa kwan-gaba kwan-baya, sai kun ajje hankalinku sosai sannan za ku fahimce shi. Fahihtarsa na ɗaya daga cikin warwaruwar labarin. Don haka ɗaure ɗamararku, the game has just started.😀


ummiieeterh jinjina da fatan alkhairi. Ƙaunarki nake fisabilillah!


Ba sai na faÉ—a muku me ya dace ku yi ba a yayin da kuka karanta ko wanne peji. Na san kun sani.


Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:53 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_


Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


4⃣4⃣


Follow me on wattpad:
PrincessAmrah


***


Kallonta yake cike da so da ƙauna, idanuwansa ƙyam a bisa fuskarta, yana jin yadda soyayyarta ke azalzalar zuciyarsa. Sosai yake tausayinta, rayuwarta, da komai nata abun tausayi ne.


"Dadyn Nadrah wannan irin kallo haka, ai sai ka sa mutum ya ƙware."


Hannunsa ya sa ya shafo fuskarta, da yatsunsa ya taɓa hancinta da murmushi shimfiɗe a bisa fuskarsa.


"Ba zan taɓa gajiyawa da daina kallon matata Suhaila ba, komanta burge ni yake; murmushinta, kallonta da komai ma. Kin ga kenan za ki shekara kina ƙwarewa in dai don ina kallonki ne."


Ya ƙarisa maganar tasa da faɗaɗa murmushin nasa.


"Yauwa, ni kam Dady akwai maganar da nake so mu yi; batun yaran nan ne, ya kamata a ce sun shiga makaranta haka nan, musamman ma Nadrah da ta fara girma, ya ci a ce ta jima da shiga makaranta."


Hannunsa na dama ya ɗora a bisa haɓar Suhaila, cikin shauƙin so ya furta,


"Na jima ina wannan tunanin, sai dai kuma abin da nake ji taɓarɓarewar karatunsu, kin ga yanzu haka maganar transfer ake mana, shi ya sa ba na son aikin federal wallahi, babu wuya sai a lalata karatun yaro, saboda yawace-yawace."


"Huh!"


Ta sauke ajiyar zuciya, ta ce,


"Duk da haka dai ai ba za mu tsaya jiran inda za a mayar da kai ba, waye ya san sadda za su É—auke ku É—in?"


"Gaskiya ne. Bari insha Allahu ranar Monday zan binciki makaranta mai kyau sosai, ina son gina ilimin yara sosai, babban burina shi ne yarana su ginu bisa turbar karatu, both na boko da na islama É—in."


"Haka ne Dady. Allah Ya kai mu to."


Ta yi shiru daga nan, ta dafe ƙasan mararta da take ji yana mata ciwo sosai ba kaɗan ba.


"Suhaila ya dai?"


Ya tambaye ta bayan ya dafe mata marar tata, yana kallon cikin idonta don jin amsar da za ta ba shi.


"Babu komai Dady, kawai dai marata ce nake ji tana É—an katsa min, amma ba sosai ba."


Ta ƙoƙarta ƙirƙiro murmushi.


"A'a Suhaila, ki faÉ—a min gaskiya fa, ko haihuwar ce?"


Hararar wasa ta masa, da murmushi ta ce,


"Dady akwai sauran lokaci fa, edd É—ina fa sai nan da sati biyu zai cika."


"Hmm! Suhaila kenan. Don an ce expected day of delivery ai bai zama dole a ce sai a ranar za ki haihu ba. Su ma kansu hasashe ne, ba wai sun tabbatar ba ne. Kuma za a iya haihuwa mako biyu kafin edd É—in, ko kuma mako biyu bayan edd É—in, babu yanda ba ta kasancewa. Don haka..."


Salatin da ya ji Suhaila na yi ne ya sa ya kasa ƙarisa zancensa, cije laɓɓanta ta yi tana jin yanda ciwon ke ƙara nuƙurƙusarta, kodai haihuwar ce da gaske?


"Suhaila na faÉ—a miki haihuwa ce wannan, ki tashi kawai mu tafi asibiti. Nadrah! Saddiqa!"


Ya ƙwala musu kira. Nadrah ce ta yo gaba sai Saddiqa biye da ita a baya.


"Nadrah kawo hijabin Momy, asibiti za mu tafi, ba ta jin daÉ—i ne."


Da saurinta Nadrah ta nufi uwar É—akar Suhaila domin ta É—auko mata hijabin, Saddiqa kuwa tambayoyi kawai take jerowa Dadynta, cewa baby boy za a siyo musu? Baby girl? Dady a tafi da ni...


Ko saurarenta bai yi ba Dady, ya gaggauta karɓar hijabin da Nadrah ke miƙo masa, cikin kaɗuwa yake zira mata hijabin, har yana mayar da ƙasa sama, sai da Nadrah ta taimaka masa.


"Nadrah yi sauri ki É—auko ma Saddiqa mayafi ke ma ki É—auko na ki."


Cikin kaÉ—uwa ya yi wannan maganar, yana É—aukar mukullin motarsa daga bisa tv stand, wanda yake haÉ—e da na gidan baki É—aya.


Fita ya fara yi ya buɗe motar, ya wangale gate ɗin gidan sannan ya dawo ciki da sauri, ya taimaka ma Suhaila ta miƙe tsaye, hannunta dafe da mararta har yanzu ba ta saki ba. Ganin kamar dai tafiyar tata ba za ta mata daɗi ba, ya sa ya cicciɓe ta da iya ƙarfinsa, ya kai ta bayan motar ya kwantar, lokaci zuwa lokaci yana yi mata sannu.


Komawa ya yi ciki ya É—auko kayan jarirai adadin wanda suka fara tarawa, kamar sun san cewa haihuwar za ta zo yanzu, sun siya komai, sai dai haÉ—a su ne wuri guda kawai Suhaila ba ta yi ba. Kwaso su ya yi da yawa ya jera a cikin riyo, ya fito daga É—akin. Yaran ya umurta cewa su isa bakin motar, shi zai rufe gidan sannan ya fito.


A daburce yake aikata komai, dakiya kawai ya yi da bai rafka kuka ba. Dama haka yake yi a duk haihuwar da Suhaila za ta yi, sosai take shan wahala kafin ta haihu, kuma kusan a tare suke jinyar, dan ba ya zuwa ko ina har sai ta haihu.


Cikin motar ya dawo ya tada, sannu yake ta maimaita mata, sanda zai yi reverse ma sai da ya ƙura mata ido yana ƙara jin tausayin mata a zuciyarsa, lallai mata abun a tausaya musu ne, abun a ma uwa mace biyayya, shi ya sa manzon Allah SAW ya ambaci kyautatawa uwa mace har sau uku sannan ya ambaci uba namiji. Gyaɗa kansa ya yi cikin ƙarfin hali ya ƙirkiro murmushi, ganin yanda yaran ke kuka riris, mamansu da ba ta da lafiya.


"Ya isa haka Nadrah, ke fa babba ce bai kamata kina kuka ba. Ke da ya kamata ki rarrashi ƙanwarki Saddiqa amma ke ce ma za ki zama Oganniya?"


Shessheƙar kukan suke har a lokacin, sosai suke tausayawa mahaifiyarsu.


Bayan ya fitar da motar waje ya dawo ya rufe gate É—in, a gaggauce ya koma cikin motar ya tayar suka lula sai FMC da yake aiki.


Da suka isa ba wani ɓata lokaci sosai aka yi ba, kasantuwar a can take awo, kuma shi ɗin staff ne a asibitin, yana ɗaya daga cikin manya manya a Pharmacy.


Ɗakin haihuwar aka nufa da ita, wata nurse kuma ta karɓa riyo ɗin da ke hannunsa, shi kuma ya zauna daga can nesa, kasantuwar ba a barin maza matsowa kusa da labour room ɗin.


Tagumi ya rafka da duka hannuwansa, Nadrah na daga gefensa na dama, sai Saddiqa a gefensa na hagu, ta kasa daina kukan, duk da yarintarta.


A can labour room kuwa wahala sosai Suhaila take sha, banda salati babu abin da take yi. Ta sani, ta san cewa tana shan wahala sosai a wurin haihuwa, amma fa tunda take ba ta taɓa shan wahala irin wannan ba. Sabbatu take tana furta a kira mata Dady ta roƙi gafararsa, ta san cewa tata ta zo ƙarshe, mutuwa za ta yi.


Sosai mid-wives É—in ke bata baki, arniyar ciki na furta "push." Musulmar kuma na faÉ—in "yi ta addua, haihuwar na kusa."


Haka dai sukaita fama har suka É—auki kusan awa biyu da rabi babu haihuwa.


A daidai wannan lokacin ne kuma aka kawo wata shuwa da ciki ƙerere, da ƙyar take tafiya, naƙuda ta ci ƙarfinta ita ma.


Nan da nan masu karɓar haihuwar suka raba kawunansu, wasu na wurin Suhaila da suka fara tunanin ko ba za ta iya haihuwa da kanta ba sai an yanka ta, wasu kuma na kan wannan shuwar kyakkyawa, wadda a shekaru ba za ta wuce sa'ar Suhailar ba.


A daidai lokacin da arniyar nurse É—in ke furta,


"Lemmi go and call the doctor, it seems like there's a problem..."


Kukan jaririn da ta jiyo ne ya dakatar da ita daga maganar da take yi, ta É—aga kanta ta hango ashe wannan shuwa É—in ce ta haihu, hakan ya sa ta sake juyowa ga Suhaila, a daidai sadda kan jinjirin ya gama fitowa.


Da taimakon abokiyar aikinta suka ƙarisa fiddo jinjirin, ɗan ƙarami da shi, kamar wani pre-tamp (Yaron da bai isa haihuwa ba, amma kuma ya wuce bakwaini. Ɗan kimanin watanni takwas kenan). Juya kanta ta yi ta sake ganin waccan shuwa ɗin tana sake yin wata naƙudar, alamun da sauran wani yaron a cikin cikinta kenan.




***
A hankali cike da mamaki suke takunsu, ba su san sanda suka ƙariso gaban gadon ba su duka biyun.


Kallonsu Fiddou ke yi ita ɗin ma mamaki bai gushe daga fuskarta ba, tana son sanin su ɗin su waye, kuma me suka zo yi a ɗakin? Tunawar da ta yi cewa tare suka shigo da Hadiza ya sa ta dakatar da wannan tunanin, da alama dai ƙawayen Hadizar ne, tunda suka zo tare.


"Sannunku da zuwa."


Ta furta cikin sanyin murya, tana ƙoƙarta ƙirƙiro murmushi a fuskarta.


"Yauwa dai, sannu."


Jiddah ta faɗa, Maryama kam ko samun damar amsa gaisuwar Fiddou ba ta yi ba. Tabbas ikon Allah ba ya taɓa ƙarewa. Al'amarin Allah mai girman gaske ne. Tunda take a rayuwarta, ba ta taɓa ganin kama irin wannan ba. Da ba don ta tabbatar cewa Annur na Katsina ba, da ita kanta ta yi irin na Hadiza, ta ce lallai shi ne wannan a gabanta. Sai dai kuma ta tabbatar cewa ba shi ɗin ba ne, tsantsar kama ce kawai da suka yi.


"Modu ga baƙi nan sun zo duba ka hwa. Ka yi musu magana."


Fiddou ta furta tana kallon Modu da murmushi.


Dariyar yaƙe ya yi ya ce,


"Ai na gan su, su ne wanda za su kai ni wurin Amrah?"


Sai a sannan Maryama ta É—an murmusa, ta kalle shi da fara'a ta ce,


"Ka dai shirya ma tarar ta ko?"


Kai ya ɗaga mata da sauri, alamar ehh, yana ƙoƙarin saukowa daga bisa gadon.


"A'a Modu..."


Ta gyaÉ—a masa kai tare da ambatar sunan da ta ji Fiddou ta kira sa da shi.


"Kai zamanka, ai ba ka da lafiya, idan ka ji sauƙi ba sai mu je ba?"


Kuka ya fasa a wannan lokacin, duk wanda zai zo ya masa maganar Amrah sai dai ya masa ƙarya cewa zai kaisa wurinta amma ba a kaisa ɗin, ga Maryama ma yanzu tana neman yi masa haka.


"Ba za ki kai ni ba, haka kowa yake yi min. Amrah nake so, Amrah nake son gani, na san ita ma a duk inda take tana can tana tunanina, tana son ta ganni a kusa da ita..."


Kuka wiwi kamar ba shi ne ya gama dariya ba.


Jinjina kai ta yi Maryama, lallai hakan ya sake tabbatar mata da zarginta. Ko tantama babu wannan shi ne real Annur, wancan É—an iskan fake Annur ne, wallahi ba shi ba ne, ta faÉ—a a ranta.


Cikin dabara Jidda ta fara rarrasar Modu, tana faÉ—in,


"Wannan karon kam ba ƙarya za mu maka ba, ba za mu taɓa tafiya mu barka a nan ba, ƙafarmu ƙafarka. Amma fa sai idan ka yi shiru, ka daina kukan nan."


Shanye kukan nasa ya yi Modu, ya ɗan dafe ƙirjinsa, saitin da zuciyarsa take. Ji yake ciwo mai tsanani, a duk sanda zai tuna da wani abu da ya shafi Amrah haka zuciyarsa ke masa zafi da raɗaɗi, ya ringa jin ƙwalwarsa tana juya masa, na tsawon lokaci kafin ya dawo daidai.


Haka suka ringa rarrasar Modu, cikin hikima da dabara har suka shawo kan Modu, ya cigaba da fara'arsa kuma.


"Halan ƙawayen Hadiza kuke?"


Suka tsinkayo muryar Fiddou ta yi wannan maganar daga inda take zaune.


Jiddah za ta yi magana kenan Maryama ta yi saurin yi mata signal alamun ta yi shiru, shirun kuwa ta yi ta zurawa Maryama idanuwa tana son sanin ainahin abin da take nufi, da hana ta maganan da ta yi.


"Uhmm...mu Æ´an uwan Annur ne..."


Tun Maryama ba ta rufe baki ba Fiddou ta zaro idanuwanta cike da mamaki tana kallonta. Me suke nufi?


"Shekara da shekaru kenan ana nemansa ya ɓata, ba kuma a san inda yake ba. Duk iya inda za a duba an duba amma ba a ga Annur ba. Da haka har ya ɗauki tsawon wannan lokacin da aka riga aka cire rai da ganinsa. Kwatsam! Sai ga Hadiza ta zo nan, to ita kuma ta sanshi, shi ne fa da sauri ta kai rahoto gidanmu, iyayenmu basa nan ne shi ya sa sai mu muka zo." (Dole dai sai an yo ƙaryar nan🙊)


Kuka ta fasa Fiddou da ƙarfi, wanda ita kanta ta rasa gane ko na menene. Shin na farin cikin samun dangin Modu da aka yi ne, ko kuwa na baƙin cikin lokacin rabuwarsu ya yi? Ta sani, dama akwai irin wannan ranar, wacce ita kanta tsumayenta take, cike take da ɗokin zuwanta. Amma kuma me, ba ta san ya rayuwarta za ta kasance a lokacin da Modu ya tafi ya barta ba. Ba ta san ya rayuwarta za ta kasance ba matuƙar babu Modu a cikinta. Ƙaunarsa take, ta yi nisa a begensa. Ashe haka so yake? Ta tambayi kanta. Ita da soyayya ta tashi kama ta sai ta faɗa ga mahaukaci, wanda ba ta san asalinsa ba, wanda ko kaɗan bai kasance yana ƙaunarta ba, wata yake so daban, wadda da alama sun shaƙu iya shaƙuwa. Rayuwarsa da komai sun ta'allaƙa ne ga waccan ɗin, wacce take yawaita jin yana ambatar sunanta. Wacce a kullum yake begen kasancewa a tare da ita dare da rana. Duk yanda yake aikata wani abu idan ta so ya daina sai ta ambaci wannan suna yake dainawa. Haka zalika ko wani abu take so ya yi to dole sai ta ambaci wannan sunan zai aikata shi. Ita kam soyayya ba ta mata adalci ba, ko kaɗan ba ta kyauta mata ba.


Da ƙyar ta samu dawowa cikin hayyacinta. Hawayenta ta samu da wahala ta share, sai dai kuma wasu ne ke ƙara gangarowa a bisa fuskarta. So take ta tsaida kukan, amma abu ya gagara. Shikenan yanzu za a raba ta da Modu. Ba ta san sanda ta ɗora hannuwanta duka biyun a bisa kanta ba. Kuka take sosai, tana gyaɗa kanta, tana jin yanda zuciyarta ke mata zafi, take tafarfasa ta kowanne lungu da saƙo da ke cikinta.


Kallonta suke da mamaki. Ita fa wannan baiwar Allah'r wacece ita? Me ya sa take kuka sosai haka kawai dan sun ambaci su dangin Modu ne?


Cikin ƙarfin hali Maryama ta ce,


"Baiwar Allah please ki daina kuka. Bakya so danginsa su zo ne?"


Cikin shessheƙar kuka Fiddou ta ce,


"Babban muradina shi ne in ga ƴan uwan Modu sun zo. Abin da na jima ina jira kenan. Giɗe na tabbata zan yi kewar Modu, zan jima ina tunani nai, walle ba zai taɓa hita daga raina ba. Soyayya nike mai ta tsakani da Allah, mai cike da tsantsar tausayi da jinƙai. Ban san me ya sa ba dama, tunda kuka shigo ɗakin gabana ke hwaɗuwa, na rasa dalili. Sai yanzu nag gane dalilin, ashe dai tahiya za ku yi da Moduna..."


Kuka sosai ya ci ƙarfinta. Ita kanta mamakin kanta take. Babanta da mamanta duka sun rasu, sun bar duniyar baki ɗaya. Amma tafiyar da za a yi da Modu ji take tamkar da rayuwarta za a tafi.


Tausayinta sosai suke a wannan lokaci. Lallai so cuta ce, cuta mai matuƙar girma kuwa.


"Ke ni bana sonki, Amrah nake so! Na sha faɗa mata cewa ita kaɗai zan so, ba zan taɓa son wata mace ba bayan ita. Hehe!"


Ya kama dariyarsa, yana wasa da haɓar gyalen Jiddah da ke zaune gefensa.


Gyaɗa kanta ta yu Fiddou. A duk lokacin da Modu zai faɗi makamancin haka, tafarfasa zuciyarta ke yi. Tana ƙara kunna wutar tsanar Amrah, tsanar sunan Amrah, da duk wata magana da za ta fito daga bakin Modu a daidai wannan lokacin.


Sosai take jin kanta na mata ciwo, zazzaɓi ke saukowa a jikinta. Gangar jikinta na tsananta karkarwa, zuciyarta na tsananta tafasa, idanuwanta na daɗa kawo ruwa, tsayuwar da take kuwa ƙafafuwanta sun gagara ɗaukar gangar jikinta.


Duƙawa ta yi a gabansa, ta riƙe ƙafarsa ta dama, cikin muryar kuka ta ce,


"Na san ba ka so na Modu, ba ka taɓa ƙaunata ba ko kaɗan. Amma do Allah dai ina biɗar alhwarmarka, kar ka mance da ni idan ka tahi, kar ka mance da Fiddousi a rayuwarka. Ka ajje a zuciyarka cewa Fiddou mai ƙaunarka ce, mai matuƙar ƙaunar Modu duk da bai kasance mai hankali ba. Ka ajje a birnin zuciyarka cewa babu mai ƙaunarka sama da ni, babu wanda nake ƙauna sama da kai, ba kuma za a samu ba har abada!"


Ta haɗa kanta da guiwa, sosai take zubar da ƙwallanta, kamar wacce aka sanarwa mutuwar wani mai muhimmanci a rayuwarta.


Da sauri Maryama ta tallabo Fiddou, a hankali ta zauna kusa da ita, ta ɗora kanta a bisa cinyarta, tana ɗan bubbuga bayanta kaɗan kaɗan, tana ƙara jin tausayinta a cikin zuciyarta.


Muryar Modu suka jiyo ya ce,


"Ke ki daina dariya, wai don na ce bana sonki ne kike ta faman yin dariya? To ki daina, ki yi kuka, na ji ina sonki, amma na fi son Amrata"


Ya girgiÉ—a kanshi, irin dai yanda mahaukata ke yi.


Sosai Maryama ke ƙara tunawa da labarin da Maman Amrah ta bata. Irin soyayyar da suka yi, yanda suka yi yarintarsu, soyayyarsu da komai, shaƙuwarsu da matuƙar tausayin junansu. Sadaukarwar da Annur ya yi na rayuwarsa, lokacinsa, farin cikinsa da komai ma saboda Amrah. Wannan wace irin ƙauna ce? Soyayya ta tsakani da Allah kenan, wacce kuɗi ba sa gusar da ita. Soyayya da zuciya ɗaya, wacce babu kwaɗayi ko son abun dubiya a cikinta. Ga Annur dai ya jima da haukacewa, amma ya kasa mantawa da soyayyarsa da Amrah, wacce duka silar haukan nasa ma mutuwar Amrah ne.






Ita kanta Maryama hawayen take, sosai take ƙara tunowa da labarin Amrah. Tausayin Annur take, sosai tausayinsa ke shiga cikin ɓargo da jininta. Sosai yake ratsa duk wata gaɓa ta cikin jikinta. Ina ma dai tana da damar da za ta iya zame masa Amrah, da ta yi, ko dan ya dawo a cikin hankalinsa.


A cikin ranta ta ɗauki alwashi, cewa za ta yi duk yanda za ta yi don ganin Modu ya warke, ya dawo a cikin hankalinsa. Da ikon Allah zai warke, zai koma gaban iyayensa, ƙarshen wancan mugun zai zo.


How are y'all? I hope you're all fine. Sannu a hankali an fara warware ƙullallu ko in ce sarƙaƙƙun abubuwa ba? Yes! Da haka da haka za mu zo wurin. How was this chapter? Was it nice? Oh yes! Very touching😰 tausayin Modu nake. Ina matuƙar tausayawa rayuwar da soyayya ta jefa shi. Wai wasu sai su ce rashin tawakkali ne ya saka shi haukacewa? No! Ko kaɗan ba haka ba ne. Kar ku manta, soyayyar Modu (real Annur) da Amrah soyayya ce da aka gina da tubalin kirki, mai cike da tsafta. Soyayyar tsakani da Allah, wadda babu ƙarya, yaudara ko kuma ha'intar juna a cikinta. Soyayya ce

Please Login or Register in order to submit comment