You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganin mahaukaci a duƙe yana rizgar kuka ya razana su sosai. Suka ringa bin Modu da Fiddou da kallon mamaki.


"Modu da Allah dai ka hwaÉ—i min abin da akka damunka. Halan wani abu ke maka ciwo?"


"Ba ke ce kike min ƙarya ba? Kullum kina cewa zaki kai ni wurin masoyiyata Amrah amma kina ƙin kai ni. Ni idan baki kai ni ba zan guduwata ne daga asibitin nan, kuma ba zaki sake ganina ba."


Cikin tashin hankali Fiddou ta ce,


"Na shiga ukuna ni Fiddousi! Modu ina zaka tai ka barni? Ko son kake yi in shiga tashin hankali?"


Banza ya mata yana mai ci gaba da kukansa, sai dai yanzu ya rage sautin kukan nasa.


Ɗaya daga cikin mutanen da suka zagaye su ne wani ya tako har inda suke, da alama yana jinyar wani ne a wani ɗakin na daban. A hankali ya dire ƙafarsa a gaban su Modu, ya sunkuya a saitin fuskarsa, da murmushi ya ce,


"Haba abokina! Ya zaka ringa abu kaman ba jarumin maza ba?"


Ɗago kansa Modu ya yi, ya daƙune fuska yana kallon mutumen, a hankali da wata murya kamar mai hankali ya ce,


"Ni ba jarumi ba ne."


Dariya suka É—auka su duka É—akin, har Fiddou sai da maganar tasa ta so ta saka ta dariya, sai dai ta danne, sanin cewa Modu baya son dariya ko kaÉ—an.


Wani kukan ya sake fasawa, kamar ma ya fi wancan na farkon ƙara.


"Ni kuke wa kuka? Ki faÉ—a masu fa bana so ana min kuka, yanzu zan daki yara, to ni dai na faÉ—a maku."


Yana faɗin haka kuma ya miƙe tsaye yana murmushi, kamar ba shi ne ya gama hayagaga a ɗakin ba.


"Wai dan ƙarya suka ce Amrah ta mutu. Ni na san Amrah ba zata taɓa mutuwa ta barni ba. Rayuwarta don ni aka yi ta, ni kaɗai. Ban san inda take ba da na gano ta. Na san ita ɗin ma tana can tana jira na, in je mu yi aureee." Ya ƙarisa maganar da janta yana murmusawa sosai.


Yana gama faɗin haka ya fara dafe kansa, jiri na ɗibarsa, ya faɗi ƙasa luuu haɗe da sakin kan nasa.


Ba Fiddou kawai ba, har sauran mutanen wurin sai da hankalinsu ya tashi. Da sauri suka yo kansa, wasu na bubbuga shi a hankali ko zai tashi.


A rikice Fiddou ta nufi nurses station ta kira nurse ɗin da ta karɓi evening, a hanyar dawowarta ne ta haɗu da Mahmouda da wasu ƴan mata guda biyu zasu je ɗakin Modu, sai kuma wannan ɗan sandan guda ɗaya biye da su.




Cikin sakin fuska Mahmouda ya ce,


"Fiddou a gaishe ki."


"Iyi giɗe. Shine kat tahi ka ƙyale mu ko? Tun jiya nit ta tunanin dawowarka amma na ji ku shiru."


"Giɗe ke san na hwaɗa miki Mammata ta rasu, jana'izarta ce ma nittai. Dan shi ne ban samu na dawo jiyan ba. Bawan Allah'nga ma shaidana ne. Na so dawowa to kuma sai mutane sunkai ta zuwa wurin gaisuwa. Ga ƙannena nan guda biyu ma nit taho da su."


Da murmushi ta kalli daka dakan ƙannen nasa, wanda duk girman jikinta sun ce mata kau ban wuri.


"GiÉ—e mun same ku lahiya? Ya me jiki?"


ÆŠaya daga cikin Æ´an matan ta faÉ—a da fara'arta.


"Ina hwa lahiya ga giɗe can ya hwaɗi ƙasa, dan shi ne ma nik kirayi giɗen ceniya da ta shiga ɗaki yanzu."


Da damuwa Mahmouda ya ƙara takunsa har ya isa cikin ɗakin, fuskarsa na nuna zallar tashin hankalin da yake ciki.


Bin bayansa suka yi su duka, har ɗayan ɗan sandan da yake biye da su ƙiƙam, kamar suna masa jagoranci.


Ko da ya je har an cicciɓi Modu an dirar bisa gadonshi, Sister kuma ta koma ta kira likita ta dawo, dan a yanda mutanen wurin suka faɗa mata matsalarsa kamar abun ya fi ƙarfinta.


Dafa kan Modu ya yi Mahmouda, cikin tausayi ya ce,


"Yi haƙuri Modu, ni ne sila, ni ne najja maka wagga wahala da kake cikinta. Damuwar da nake cikinta tassa na kasa controlling temper ɗina, har sai da nik kaɗe ka ban sani ba. Do Allah de ka yahe man."


Ko motsi Modu bai yi ba bare Mahmouda ya sa ran zai farka, ko kuma yana jinsa. Suna cikin haka ne likita ya iso da nurse biye da shi. Hakan ya sa sauran nutanen da ke ciki duk suka watse, har su Fiddou ma a bakin ƙofa suka dakata.


Dudduba shi likita ya yi sosai kafin ya ce,


"Ina ga kamar akwai wata asalin damuwa ne a cikin zuciya tai. Ba wai bankar da mota tai yi mai ce kawai matsala tai ba. Kuma matsalad da ac cikin zuciyatai bata rasa nasaba da taɓin ƙwalwar da garai. Dole sai na ji daga bakin wani nashi ko ina sanin abin da ka hwaruwa da shi."


Cikin gamsuwa da girmamawa nurse É—in ta ce,


"Bari in kira wacceni da suke tare."


Ta kama hanyar ƙofa, ta ci burki a inda su Fiddou suke, ta sanar mata cewa likita na son ganinta. Tare suka tafi wurin likitan, ita da nurse.


"GiÉ—e halan ya kuke da Modu?"


Muryar likitan ta daki kunnuwanta tun bata ƙarisa isa kusa da gadon ba.


Shiru ta É—an yi na wani lokaci tana nazarin abin da zata faÉ—i. Jin babu amsa ya sa likitan ci gaba da maganarsa,


"Ke ga ga abun gwajin zuciya nan, da shi na auna nagga yanda zuciyatai bata tahiya daidai yanda aka son ta yi. Kuma wannan matsala ko kaɗan bata da alaƙa da wanga kaɗe shi da giɗe ya yi da mota. Sai na tabbatar da komai kafin in san matakin da zan ɗaukar mai, idan ma likitan zuciya ya kamata in haɗa ku da shi sai in hwaɗi mai."


A yanzun ma shiru ta yi dan bata san ta inda zata fara ba. Tsayuwar ta yi yawa ya sa likitan cewa,


"Giɗe biyo ni Office mu yi magana. Ba maganar a tsaya a yi nan ce ba. Ina son taimakon giɗe, wata ƙila idan na san komai har likitan ƙwalwa sai a haɗa ku. Amma hwa yanzu dole a tari matsalar zuciyag ga tun abu bai yi nisa ba."


Yana direwa ya fara takawa zuwa hanyar fita. Ita ma Fiddou binsa baya ta yi.


Har ya yi nisa kuma ya juyo ga nurse ya ce,


"A kuka da shi sosai hwa. Kar ki bar wuringa dan kar ya hwarka babu kowa a tattare da shi. Tun da na hidda kowa daga É—akin, na kuma hana su shigowa. Matsalar da ta shafi zuciya hwa dole sai ana taka-tsantsan."


Fita suka yi tare da Fiddou suka nufi Office ɗinsa. A zuciyarta tunanin yanda zata yi da likitan kawai take. Bata san ta yanda zata fara faɗa masa a haka ta ganshi har suka shaƙu ba.


***


Da gudunshi ya shigo yana faÉ—in,


"Yaya Maryama! Yaya Maryama!!"


ÆŠago kanta ta yi daga latsar wayar da take da sauri tana binsa da kallon tuhuma, tuhumar dalilin shigowarsa É—akin babu ko sallama kuma sai ihu yake mata.


Raina kansa ya yi ganin kallon da take binsa da shi.


"Uhmm...dama, dama Maman Abdul ce ta zo. Tana falo Mama ta ce na kira ki."


Fasa yi masa faÉ—an da ta yi niyyar yi ta yi, gyaÉ—a kanta kawai ta yi ta ajje wayar bisa gado, sannan ta zira hijabinta iya guiwa, ta nufi hanyar falon.


Ko da ta isa ta samu Mama suna fira da Maman Abdul, firar abun da ya faru É—azu, na rashin zuwa É—auko sa.


Da fara'a Maryama ta zauna, gaishe da Maman Abdul ta yi sannan ta miƙe ta nufi kitchen. Fruits ta yayyanka cikin lokaci ƙanƙani ta haɗa ftuit salad ta fasa ƙanƙara ta ɗora a kai. A bowl ta juye ta haɗa da cokali sannan ta koma falon ta ajje a gaban Maman Abdul da faɗin,


"ÆŠazun nan kuwa Muhammad ke ce min wai ya ji ku shiru har yanzu, gashi kuma babu lambarki bare na kira ko kun fasa zuwa ne."


Cokali guda ta kai bakinta sannan ta ajje ƙasa, ta dubi Muhammad da fara'a ta ce,


"Abdul ne zai ƙyale ni bamu zo ba? Ai yanda ya saka ka a ranshi abun ba a magana. Kullum damun Abbansa yake da maganarka. Abban nasa ma ya tilasta lallai kar mu wuce yau bamu zo gidanku ba."


Mama ta ce,


"Yara kuwa sun haÉ—a zumunci."


Ta faÉ—aÉ—a murmushinta.


Sun jima suna hira har magrib ta kusa. Muhammad da Abdul kuma suna harabar gida suna buga ƙwallo. Miƙewa ta yi ta ce,


"Bari dai mu kama hanyar gida Mama. Maryam mu yi musayar number mana."


Miƙewa ta yi ita ma Maryama ta ce,


"Aikam mu ma insha Allahu muna nan zuwa gobe ko jibi. Zamu zo mu ga gidan su Abdul daga nan sai zumunci."


"Da kuwa na ji daɗi ƙwarai."


Suka yi musayar lambobin wayar sannan Maryama ta taka mata har tsakar gida. Ta ce,


"Maman abdul baki faÉ—a mana sunanki ba."


"Dr. Islam sunana."


Daga nan suka isa tsakar gidan.


"To malami sai a zo mu tafi ko?"


"Oh Mami! Muna kan yin ball ne zaki ce mu tafi?"


Ya faɗa cikin shagwaɓa da yarinta. Duka a shekaru ba zai wuce shekara uku ba, ba ma lallai idan zai yi ukun ba. Amma sai wayo da son mutane yaron.


"Abdul-Ahad dare ya yi fa. Ko gobe zaku haÉ—u a School, ko ka manta? Kuma sun ce zasu zo mana yawo mu ma."


Murmushi ya saki haÉ—e da faÉ—in,


"Yauwa Mami. Na ji daÉ—i da zasu zo gidanmu."


Ya bi bayanta yana dariya.


Har mota suka raka su sannan suka dawo gida. Fuskokinsu É—auke da dariya.


***


Tsaki ya yi a bayyane haÉ—e da É—aukar wayarsa da ke ringing, ya kara a kunnensa da faÉ—in,


"Hello guy."


"Abokina ya dai?"


Bobby ya faÉ—a da fara'a.


"Ba lafiya fa guy. Akwai damuwa sosai. Ina tunanin ɓalli na neman kwancewa fa. Tun ɗazu nake kiranka baka ɗauka ba."


Dafe kansa ya yi Bobby, ya tausasa muryarsa ya ce,


"Tell me something, what is going on? (Ka faÉ—a min wani abu, me yake faruwa ne?"


"Guy kiran da Dady yake min sanda nake gidanku ɗin nan, ashe laifin da na yi a company aka faɗa masa. Guy baka ga faɗan da ya min ba, ban taɓa tsammani ba. Kuma abun haushi hasarar da ta fi wannan ma na jawo amma bai min faɗa ba sai wannan. Kamar dai sai mun koma wurin boka, dan da alama maganarsa ke neman tabbata. Gwara tun wuri ai wa tufƙar hanci."


Bobby ya ce,


"Lallai kuwa. Daddyn ne ya maka faÉ—a? Akwai damuwa tabbas. Dole zamu koma masa. Gashi kuma yanzu dare ya yi. Sai dai gobe da sassafe na zo na É—auke ka sai mu tafi."


"To zan jira ka guy. Dan Allah kar ka bari na yita jiranka. Ka san a matse nake, kar a samu matsala mai girma."


"Babu wannan a tsakaninmu, ka sani. Kawai ka jira ni da sassafe. Kar kuma ka sha komai, kar bacci ya É—auke ka. Sai ka yi shigar zuwa wurin aiki, daga can kawai ka wuce aiki."


Daga haka suka yi sallama zukatansu a raunane.


Ummu Ayeesher where are you? Ban manta da ke ba. Gaisuwar taki ta musamman ce. Ina yinki irin sosai da sosai din nan.


Duk members na NAGARTA WRITERS FANS na gaishe ku. Ina yinku irin totally din nan. Fatan kun san da hakan.


Alhamdulillah! Jiki kam ya yi sauki sosai. Na gode kwarai da adduoinku. Allahu ya bar zumunci da zaman tare.


What do you expect here? Shin wacece Dr. Islam din nan Maman Abdul? Menene dalilin kulla wannan alakar da marubuciyar ta yi?


Modu mai matsalar zuciya, yaya abun zai kaya? Me Fiddou zata fada wa likita bayan kuma ita kanta bata san asalinsa ba?


A dai juri zuwa rafi, wata rana tulu zai fashe.


Marubuciyar zata yi amfani da alkalaminta wurin fayyace mana komai, kawai mu ci gaba da bibiyar labarin. Zamu yi mamakin komai a karshe.


Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:47 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)


Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


32


Tun da sassafe ya hau shiri. Manyan kaya ya saka, farar shadda mai matuƙar kyau, an mata surfani da kalar baƙi. Hakan ya sa ya saka baƙar hula, baƙar agogo da kuma baƙin takalmi. Kallo ɗaya ka ma Annur zaka ji ya shiga ranka, kamar ba shi ne wannan mugun mashayin ba.


Turaren cinema ya shafa a jikinsa sannan ya fesa explore.


Lakar madobinsa ya jawo ya fiddo kuÉ—i ya saka a aljihunsa, sannan ya kama hanyar fitowa daga É—akin nasa.


Sai da ya fara biyawa part É—in su Momy. Ya same ta a falo tana zirga zirgar haÉ—a kalaci ita da mai aikinta.


Har ƙasa ya duƙa ya gaishe ta. Akwai fa ladabi ko ba komai. Ko da yake, dama an ce wai masu irin mugayen halayen nan sun fi kowa ladabi da girmama na gaba da su. Ladabin kunama ke nan.


"Ya da fitowa haka tun da wuri?"


Ta faÉ—a bayan ta iso daidai inda yake zaune.


"Yau da wuri nake son zuwa aikin ne Momy. Akwai ayyuka da dama da nake son na warware su."


Ajiyar zuciya ta sauke tana binsa da kallo. Kallon yanayin nasa na yau. Babban mutum mai ƙwarjini a fuska, sai dai kuma babu halaye na gari. Ya yi rashin halayen kirki tun shekaru uku da suka gabata. Ko ma fin hakan.


"Annur dan Allah ka kula. Ka ga ka ɓata wa mahaifinka rai ba kaɗan ba. A kiyaye gaba, bana fatan hakan ta sake faruwa nan gaba. Ka ji?"


Miƙewa ya yi ya zauna bisa kujera, yana sosa ƙeyarsa ya ce,


"Insha Allahu Momy na miki alƙawari hakan ba zata sake faruwa ba."


"Ina fatan hakan, Annur. Allah Ya maka albarka ya ƙara shirya ka, ko ka samu ka ajje hankalinka wuri ɗaya ka tsayar da matar aure."


Bai furta komai ba wayarsa ta ɗauki ƙara. Dubawar da ya yi ya ga Bobby ne ke kiransa ya sa shi saurin miƙewa a kan kafafuwansa. Ya ce,


"Momy har an fara kirana. Usman ne secretary na san jirana yake. Zan tafi, sai na dawo."


"Au! Kalacin ma ba zaka tsaya a kammala ba?"


Taku ya yi haÉ—e da furta,


"Ina sauri ne Momy. Ina son gyara kuskuren da na tafka a baya. In gyara tsakanina da Dady."


Da fara'a ta ce,


"Allah Ya tabbatar da hakan. Ina ji a jikina dai hakan ya zama alkhairi. Dan ga zahirin canji nan na gani a tattare da kai. Kai ɗin nan da baka tashi tafiya aiki sai ƙarfe goma, amma gashi yau ko bakwai bata cika ba zaka tafi. Na ji daɗi ƙwarai."


"Na wuce, Momy."


A ransa mummanan ƙuduri ne kawai, a daidai ƙofar ya gyaɗa kansa haɗe da sakin murmushin ƙeta, wanda ya bayyana zallar muguwar manufarsa a daidai lokacin.


Daidai zai shiga mota ya latsa kiran Bobby. Kamar yana jiransa kuwa ya É—auka yana faÉ—in,


"Am on my way."


Kawai ya latse kiran ya shiga motarsa ya kunna.


Kai tsaye gidan su Bobby ya nufa. Ya same sa a tsaye bakin gate yana jiransa. Shiga gaban motar kawai ya yi suka kama hanyar Jani sai wurin boka Gagarabadau.


Yanda suka saba yi idan sun je wurin bokan suka yi. Bayan sun sha jini boka ya shanye sauran, sannan ya fuskanci Annur da faÉ—in,


"Akwai matsala ne a aikin. An samu an fitar da ƙaunar da kake ma ɗaya daga cikinsu. Amma ɗayar na kasa ganin komai game da ita. Aikin da na yi a kanta a gabanku ya yi, amma washe gari na kasa fahimtar abin da ke faruwa. Wani irin haske ya ringa mamaye ƙwaryata a duk sanda na tura masu aljannu. Har na gaji na haƙura. Dan haka wannan aikin naka ne. Ni ba zan iya ba, kar wani abu ya faru kamar yanda ban taɓa tsammani ba. Yau ni Gagarabadau an samu abin da ya gagare ni. Ban san dalili ba. Ka ƙoƙarta fitar da ita daga zuciyarka, idan ba haka ba kuwa asiri na daf da tonuwa."


Cike da tsoro da fargaba Annur ya ce,


"Boka a dai ƙara ƙoƙartawa. Ban san ya zan yi ba idan wannan mugun ƙullin ya kwance. Ban kuma san yanda zan yi na fitar da yarinyar daga zuciyata ba. Ni kaina jinta nake a raina, duk yanda zan yi na fidda ƙaunarta na kasa. Har ƙudira na yi zan hukunta su amma na kasa. Na rasa me zan yi boka Gagarabadau!"


"Aljannu basa magana biyu. Ka tashi ka tafi ka bani wuri! Kar kuma ka sake dawo min har sai ka fidda wannan soyayyar daga ranka. Idan ka jinkirta kuma, ka shirya zama abun tausayi, dan komai sai ya lalace."


Kansa ya dafe Bobby, yana tsananin jin tausayin abokinsa. Ya rasa ta inda ma zai fara. Da ƙyar ya samu ya ce,


"Boka a dai taimaka mana. Ka san gare ka kaÉ—ai muka dogara. Kai ne kake rufa mana asiri, a yanzu ma muna neman rufin asirin nan. A duba wannan zancen boka, a bamu mafita."


Manyan zane ya ringa yi a hannunsa na hagu, cikin wata irin murya ya ce,


"Duba ku gani!"


Ya juyo masu da hannunsa da ke fitar da haske.


"Babu nasara ko kaÉ—an. Akwai abin da wannan yarinyar ta taka wanda tsafi ya gagara yi mata wani abu. Idan da hali dole sai ta shagala da aikin ta ajje sa, ko zamu samu nasara a kanta."


Shiru suka yi su duka suna tunanin mafita. Ko kaÉ—an basu da idea a kan abin da zasu yi, kawai dai basu so bokan ya gajiya da su ne.


"Zamu ƙoƙarta boka. Zamu san yanda zamu yi dan ganin yarinyar ta shagala da aikin nata. Muna godiya da ƙoƙarinka."


kuɗi Annur ya ajje masa sannan suka miƙe a ƙafafunsu. Tunani fal a zukatan ko wannensu suka bar gidan.


***


Zama ta yi a bisa kujerar da ke fuskantar tasa. Idanuwanta a raunane take kallonsa. Zuciyarta fal da tunanin abin da zata faÉ—a ma likitan.


Muryarsa ce ta dakatar da ita daga tunanin da take, ta dawo da hankalinta gare shi, tana sauraren abin da yake faÉ—i.


"GiÉ—e ki kwantar da hankalinki hwa. Abin da na hwaÉ—i ba lallai bane ya tabbata, hasashe ne dai kawai nai yi. Yanzu dai ki hwaÉ—i min. Halan mi as silar haukan can nashi? Ta haka kawai zan tabbatar da hasashen da nake yi a kan giÉ—e."


Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke. Cikin wata murya rinanna ta fara bashi labari.


*


Tafiya yake da ƙafafuwansa, kayan jikinsa sun yayyage, tsiraicinsa duk ya bayyana, yana kuka kamar ransa zai fita.


Gajiya ya yi sosai da tafiyar, jiri na ɗibarsa sosai, hakan ya sa ya fara dafe kansa, da ƙyar ya samu ya duƙe ƙasa, yana wani irin kuka mai tsuma zuciyar duk wanda zai ji sa.


Tun sanda yake tafiya take kula da shi, take bibiyar lamurransa, har sanda ya gaji da tafiyar ya tsaya a ƙafafuwansa. Ya kuma gaji da tsayuwar ya tsuguna a guiwowinsa.


Cike da tausayi ta ƙarisa inda yake, tana jin tsanan fargabar tinkararsa. Sai dai kuma duk da hakan, bata jin ko kaɗan zata iya tafiya ta bar shi a wannan halin ba. Ko kaɗan ba zata iya fitar da tunaninsa daga cikin zuciyarta ba.


"GiÉ—e."


Ta faÉ—a cikin sanyin murya. Zuciyarta na dukan uku-uku, ba ma ta san ta inda zata fara ba.


Ɗagowa ya yi da rinannun idanuwansa ya dube ta. Duba ta tsanaki kafin ya sake duƙar da kan nasa, yana mai ci gaba da kukansa.


Dakewa ta yi ta sake furta,


"GiÉ—e ba zan cutar da kai ba, Allah kuwa da gaske nake."


Bai ɗago kanshi ba a wannan lokacin, sai ƙara ɗaga sautin kukan nasa da ya yi.


Duƙawa ta yi a gabansa, tana jin duk wata fargaba na fita daga zuciyarta. Zallar son taimaka masa ne a cikin farar zuciyarta.


"GiÉ—e ka hwaÉ—i min do Allah de. Mi ka damunka?"


Sai sannan ya É—ago fuskarsa yana gwada mata cikinsa da hannuwansa. Alamun yunwa yake ji sosai, da alama ita ce ta galabaitar da shi.


Bata fahimci manufarsa ba, sai faÉ—in ta yi,


"Cikinka yake maka ciwo? Bara na kawo maka magani yanzu. Dan Allah kar ka tafi, ka ji?"


Kansa ya gyaÉ—a mata, yana sake nuna mata cikin nasa da duka hannuwansa a wannan karon, ruwan hawaye na sake wanke masa fuska.


"Mina ne halan giÉ—e? Ko yunwa kake ji?"


Saurin ɗaga mata kai ya yi, kukan da yake lokaci ɗaya yana sauyawa zuwa murmushi, murmushin da duk ƙazantar fuskarsa bata hana kyawunsa bayyana ba.


Murmushin ta yi ita ma, duk da tausayinsa da take ji, da damuwar da ke cikin zuciyarta.


"Zauna a nan kar ka tafi. Yanzun nan zan kawo maka abinci."


Bai ce da ita komai ba sai murmushinsa da ya faÉ—aÉ—a, ya gyara zamansa yana bin bayanta da kallo.


Ta É—an jima bata dawo ba sai gata ta taho da plate É—in abinci a hannunta an rufe, sai kuma wani yaro biye da ita, wanda zai tafi da plate É—in idan an gama.


Yana ganinta ya hau murmushi, da haƙoransa a yaƙe, yana miƙo mata hannu tun bata ƙarisa isowa inda yake ba.


Zama ta yi a kusa da shi, ta motsa shinkafa da miyar da cokali, sannan ta miƙa masa tana murmushi ta ce,


"Ka ci gashi. Ga kuma ruwa nan idan zaka sha."


Bai bi ta kan karɓar ruwan ba. Cokalin ma yar da shi ya yi ya ringa cin abincin hannu baka hannu ƙwarya. Kyakkyawar loma biyar ya cinye baki ɗaya abincin, ya miƙo mata hannu ta bashi ruwa.


Tsabar sauri ya sa ya gagara fasa ledar ruwan ma, ya ringa kai shi bisa leɓonsa ya kasa buɗewa.


Karɓa ta yi ta fasa masa, sannan ta miƙa masa a daidai bakinsa. Zuƙa ɗaya ya shanye duka ruwan ledar, ya saki kyakkyawar gyatsa, alamun ya ci ya ƙoshi ke nan.


Miƙa wa yaron plate ɗin ta yi, ta ce,


"GiÉ—e tahi ka kai mata, na gode ma ka jiya."


Ya karɓa ya tafi, yana yi yana ɗan waigen mahaukacin, wanda al'aurarsa take bayyane.


Ganin irin kallon da yaron yake binsa da shi ya sa ta yi saurin cire ɗan ƙaramin mayafinta, ta lulluɓe masa jikin nasa, tana mai tsananin tausaya masa.


Rasa yanda zata yi da shi ta yi, miƙewa ta yi bisa ƙafafuwanta, tana faɗin,


"Giɗe tashi mu tai gidanmu. Ina baka ƙarin wani abinci ka ci."


"Zaki kai ni wurin Amrah?"


A ba zata ta ji maganar tasa, dan bata yi tsammanin ko magana ya iya ba. Ta dai tabbatar ba kurma ba ne, saboda yana jinta, kuma yana yin duk abin da ta ce masa ya yi.


Da murmushin yaƙe ta ce,


"Zan kai ka mana. Amrah ko?"


Dariya sosai a fuskarsa ya ce,


"Ehh, Amrah fa. Wallahi ita nake so, AMRAH NAKE SO!"


"To can zan kai ka. Mu tahi."


Ta tasa shi gaba tana binsa a baya.


Duk ta inda suka gitta binsu ake da kallo, kallon tuhumar inda ta samo wannan ƙazamin matashin, sauƙinta ma yanda ta ɗaure masa ƙugunsa da mayafinta, ya rufe tsiraicinsa da ya bayyana.


Kallon da ake mata ko kaɗan bai sa ta ji ko ɗar a jikinta ba. Sai ma ƙoƙarin jansa fira da take, amma ko kaɗan baya amsa ta. Shiru ya yi, kuma bata yi shirun ba ita.


A daidai ƙofar gidansu suka isa. Gabanta ya tsananta faɗuwa a lokacin, tana tsoron yanda zata shiga gidansu da shi, haka kuma bata jin zata iya barinsa haka ya tafi, ba tare da ta samar masa suturar kirki ya suturce jikinsa ba. Kuma ta tabbatar cewa bai ƙoshi da abincin da ya ci ba, saboda halam halam ɗin da ta ganshi yana yi.


Runtse idonta ta yi tana tunanin mafita. Tana buɗe su ta dire bisa fuskar Yayanta, yayanta da take shakku, take matuƙar jin tsoronsa.


"Yaya...uhm..."


Ta samu ta matso da ƙyar, tana jin wani sauyi a duniyarta, ƙirjinta sai tsananta duka yake.


"Foddousi mi halan? Ina kika samo giÉ—e gashi nan tsaye?"


Kyarmar laɓɓa ta fara yi. Da ƙyar ta samu tattara laɓɓanta wuri guda, ta tsaida tunaninta wuri ɗaya, hankalinta duka ya koma ga yayan nata. Ta sanshi, ta san halinshi. Ko kaɗan baya son wasa, baya son yana magana ana ƙyale shi. Hakan ya sa ta fara magana da rawar murya,


"Yaya a saman godabe na haÉ—u da shi, cikin halin tashin hankali, ga tuhwahi nai a yage, jiki nai ya bayyana, dan shi ne nat taho da shi. Ina tausai nai ne."


Wani irin wawan kallo yayan nata ya bi ta da shi. Take Fiddou ta raina kanta, jikinta ya fara rawa tana tunanin mafita.


Bata samo mafitar ba ta ji muryarshi yana faÉ—in,


"Kina ɓace min ko sai na

Please Login or Register in order to submit comment