You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

É—in su yi magana."


Salati Maryama ta saki.


"To garin ya wannan al'amari ya kasance?"


"Allah masani Maryam. Sai dai ya dawo É—in mu ji komai. Su Yamairah da Momy akwai inda za su kwana. Wai gidan su wata Ummi."


"Allah sarki! To Allah ya jishe mu alkhairi. Ka gaishe min da su duka. Kuma don Allah ka ce da Yaya Salman wai ya biya ni lada, saboda na kusa tsamo shi daga sahun tuzurai."


Ya ja murmushi.


"Bakya gajiya da sokana. Mata kika samar masa?"


"Ehh mana Yah Noor. Kuma ni da kai ma za mu je mu nema masa auren. Har na kira a waya na faÉ—a mata, ta kuma amince."


"Hmm! To shi kenan. Ki gaishe da su Hanan."


"Za su ji ƙwarai. Ba mu tare ni ina ɗakinka. Su kuma suna ɗakina."


Ya saki murmushi.


"Wato dai kin musu wayo kika tafi waya da mijinki."


"To ai hakan shi ne daidai. Na tabbata kai É—in ma ka baro wurin da su Yah Salman suke don ka yi waya da matarka."


"Ba ki ji wallahi."


Ya saki dariya.


"Na san hanyar da zan bi in rama wannan tsokanar taki. Wannan bakin maganar shi zan magance."


"Na ji dai."


"To ya yi. Ki huta lafiya. Wata ƙila ma gobe za mu juyo."


"Allah ya yarje mana. Sai anjima."


Suka tsinke wayoyin.


Sai bayan la'asar liƙis sannan Dady ya dawo, daf da magrib. Kallo guda za a masa a tabbatar da ba ya cikin nutsuwarsa.


Bayan ya zauna ne ya musu bayanin duk abin da ya faru kamar yadda Rita ta sanar da su.


"Na san halin da kuke ciki a yanzu dole za ku damu. Amma kalmar nan dai guda ba zan daina maimaita muku ita ba. Ku yi haƙuri ku kuma ƙara yin haƙuri ku ɗauki ƙaddara. Wannan al'amari dama can Allah ya tsara haka zai kasance. To sai mu taru mu rungumi ƙaddara. Mu kuma ɗauka cewa Annur da Salman Allah ya sauya mana da su ne a madadin..."


Bai ƙarisa ba Dady ya ce,


"Ai dama ba ta ce mana fa bai raye ba. Lambar mutumin dai tunda muka rabu da ita nake ta nema a kashe. Abin da ya ƙarisa kashe min jiki kenan. Gaskiya in har ban gano wannan mutumin ba, to lallai sai na shigar da Rita ƙara. Don ba zan lamunci wannan muguntar ba. An raba mu da gudan jininmu da gangan."


Uncle Marwan ya gyaÉ—a masa kai.


"Me ya sa za ka yi ƙarar ta? Kai da kanka kake faɗa mana irin kukan da take yi na nadama. Idan kuwa har ka yi ƙararta ai ba ka kyauta ba. Shi ya sa na ce maka ka ɗauki ƙaddara. Dama haka Allah ya tsara mana. Kuma..."


Ya kwashi duk yadda suka yi É—azu ya sanar da Dady. Cike da mamaki yake kallon Sans.


"Me ya sa ka faÉ—i haka Salman?"


Cikin girmamawa Sans ya ce,


"Sunan ya zo iri ɗaya ne Dady. Baya ga haka kuma, tabbacin da na samu daga bakin Dadyn Farouk cewa ba ɗansa ba ne, sannan a ƙarshe ma ya ambaci ba ɗan yayan nashi ba ne, wai ɗan riƙonsa ne."


Dady ya yi shiru zuciyarsa na duka da sauri da sauri.


"Dama kai muke jira ka zo sai ka karɓi lambar Alhaji Usman ɗin ka kira sa da kanka ku yi magana. Ka ga ta nan za a samu tabbacin al'amarin."


Dady ya jinjina kai sannan y karɓi wayar Sans ya rubuta lambar Dady ɗin ya latsa kiransa.


Bayan ya É—auka da sallama suka gaisa. Dady ya masa bayanin kansa sannan cikin faran-faran Dadyn Boby ya sake gaishe da Dady.


"Wato Alhaji Usman wata Æ´ar matsala ce ta sa na kira ka..."


Ya faÉ—a masa komai da ya faru.


Kuka ya ji ya fasa bayyananne. Hakan ya sa Dady ya saka wayar a handsfree ta yadda duk za su jijji maganar. Ya ce,


"Subhanallahi! Alhaji Usman lafiya?"


"Dole na yi kuka Alhaji IA. Ashe da gaske zan ga iyayen Farouk na gaskiya?"


Mamaki ya kama su su duka.


"Na gaskiya? Kenan da gaske É—an namu ne?"


"Babu ko tantama Marigayi Farouk ɗanku ne. Domin kuwa ba Yaya Abubakar ne ya haife shi ba. Labarin yana da tsawo, sai dai zan taƙaita maka shi."


Komawa baya


Cikin wata irin murya mai nuna zallar tashin hankali yake magana.


"Usman ciwon nan nawa da alamu ba na tashi ba ne. Wani irin abu nake ji da tunda nake a rayuwata ban taɓa jin irinsa ba. Don Allah ga amanar Farouk nan, ka kula da shi, tamkar yadda za ka kula da naka da za ka haifa da cikinka."


"Ka daina faÉ—ar haka Yaya Abubakar. Insha Allahu za ka tashi ka ci gaba da rayuwarka. Shi ciwo ai ba mutuwa ba ne."


"Ko kaɗan ba na jin haka a jikina Usman. Ga amanar Farouk nan ɗan shekara uku. Don Allah ka kula da shi, ka ga yadda muka rabu da matata Safina, rabuwa mara daɗi, ashe ita kanta waccan yarinyar da ta haifa ba ƴata ba ce, wai maza take bi a waje. Sai da ciwon nan ya kama ni asirinta ya bayyana. Babu nadama ko kaɗan a tattare da ita kuma ta nemi saki na sake ta. Ba ta nemi tafiya da Farouk ba, don ta san komai game da shi, ita ta ƙara ba ni ƙwarin guiwa ma a lokacin. Ashe kawai don ta cutar da ni ne, ita ma waccan ƴar ba jinina ba ce. Ga kuma karayar arziƙi da ta same ni, na rasa komai nawa sai kai da kuma ƙanwarmu Sailubah. Rashin jin daɗin rayuwa ta sa na baro Maiduguri na dawo nan garin Kano wurinka, don na san kai kaɗai ne mutumin da ba zai taɓa gudu na ba. Akwai wani sirri da nake ɓoyo, wanda babu wanda ya san shi sai ni, Safeena da kuma mutum uku da suka taimaka min (Asabe, Rita da kuma ƙanwar Rita). Farouk da kake gani ba shi ne asalin ɗana ba, na same shi ne daga hannun wasu malaman asibiti ta dalilin rasa ƴata da na yi. Riƙonsa kawai nake yi, amma ban haɗa komai da shi ba. Na sani, cewa ban aikata abun kirki ba da na yaudari iyayensa a matsayin ya mutu, wato na ƙuntata musu ni kuma na faranta wa kaina, bayan kuma su za su fi ni jin zafi ma. Tabbas abin da na aikata ne yake bibiyata, ya sa rayuwa ta juye min har izuwa wannan lokacin. Usman ka riƙe shi da amana, don Allah kar ka cutar da Farouk."


Kwana biyu da faruwar haka Allah ya karɓi rayuwar Abubakar. Sosai Usman ya yi kuka, ya ƙudiri aniyar riƙon Farouk tamkar ɗan da ya haifa da cikinsa.


Ya haÉ—iye kukansa. Ya ce,


"Mu ƴan asalin Kano ne, surutu ya rinƙa dawo min cewa ina riƙon ɗan yaya Abubakar. Gudun kar yaron ya tashi da tunanin ba ni ne mahaifinsa ba, ya sa na nemi transfer daga wurin aiki muka dawo nan garin da zama. Amma duk da hakan labari sai da zo masa har ya gano ba mu ne iyayensa ba. Sai dai bai taɓa tsammanin ba jinina ba ne, a zatonsa ɗan Yaya Abubakar ɗin ne shi kamar yadda na faɗa masa."


Cikin kuka Dady ya ce,


"Babu shakka Farouk É—ana ne! Ashe É—ana ne Farouk..."


Ya saki kuka haÉ—e da tsinke wayar.


Sai yanzu yake tunowa da ranar da Farouk zai rasu. Irin riƙon da suka wa junansu, nutsuwar da suka rinƙa samu. Ashe da rabon zai riƙe ɗan da ya haifa da hannunsa. Da rabon zai ji irin gumin da yara ke ji idan sun riƙe hannun iyayensu. Shi ya sa ya ƙi sakinsa ashe.


Da dare Dady ya kira Momy, cikin kuka yake sanar mata yadda abubuwan suka faru. Hankalinta ya tashi sadda ta ji wai ɗanta ne Farouk da ya rasu. Sai ta kuma sakin kuka. Sai da mahaifiyar Ummi ta rinƙa rarrashinta tana ba ta baki.


Washe gari


Tun da safe suka fara haramar tafiya. Sai dai kuma jirgin sai huɗu na yamma zai tashi. Alhaji Marwan ya kawo shawarar su daure su ƙarisa garin Bama, saboda su Annur su nemi danginsu wanda suke a raye su yi zumunci. A tasha ne aka ba su shawara cewa kar su shiga garin na Bama, har yanzu akwai sauran tashin hankali, kawai dai abun ya yi sauƙi ne.


Haƙurar kuwa suka yi. Ƙarfe uku da rabi suka isa Airport, Momy da Yamaira ma drivern gidan su Ummi ya kawo su, bayan an haɗa musu sha-tara ta arziƙi.


***


*Na warware muku komai yanzu kam, da alama. Na tabbata cewa akwai wanda ba su taɓa tsammanin cewa Farouk Sardauna ne asalin ɗan su Momy ba. Sai dai na ba ku alama. Ku duba shafi na 53 da kuma na 54, za ku ga alamomin da na bayyana muku, wanda ya kamata a ce tun nan jikinku ya ba ku wani abu. Sai dai ba zan manta ba, Basman Mai sanyinta ta yi wannan hasashen, har ta yi comment a kai. To Habibty Basmah, yau dai kam kin tabbatar da wannan hasashen naki, don haka na ba ki kyautar shafin ma baki ɗaya.*


*Gaisuwa zuwa ga Lolita. Na gaishe ki lodi lodi.*


*Me ya rage?*


*Shafin ƙarshe ko? Za ku ji shi insha Allahu. Na gode ƙwarai da jimirin bibiya ta.*


Thanks all.


Pinky durling💞
RAZ 2
[9/29, 5:13 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taɓa zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_


Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


7⃣5⃣


END


Wattpad: PrincessAmrah


***


Sadda suka dira cikin gida a lokacin har magrib ta kusa. Maryama da su Hanan dama sun zo sun gyaggyara gidan sannan suka musu girki. Islam ma ta zo sun yi tare da ita.


A falo suka zazzauna duka ana miyar da magana. Maryama kuma suna serving É—insu abinci. Bayan sun gama jido kayan duka suka zauna. Ta É—an saci kallon Annur ta ga ita yake kallo, sai ta sakar masa murmushi haÉ—e da É—auke kanta. Muryar Sans ta ji ya ce mata,


"Maryama sai kika ji wani al'alamarin ubangiji ko. Ashe Farouk Sardauna jinin su Momy ne. ÆŠansu ne na cikinsu."


Annur ya ce,


"Ta san shi ne?"


"Sosan sosai ma kuwa. Mallam ai da shi za ta aura sai Allah bai nufa ba. Da yanzu shi ne ba kai ba."


Ya ƙarisa maganar cikin zolaya. Bugu Annur ya kai masa. Uncle Marwan ya ce,


"Salman ka cika tsokanar faÉ—a na kula."


Duka aka yi dariya har da Dady da Momy. Sai dai su kam ta ciki na ciki, suna jimamin rashin gudan jininsu.


Bayan an kira magrib duk suka mimmiƙe. Uncle Marwan ya ce da Yamaira ta tashi su tafi. Maryama ta cicciɓar mata Yesmeen da ke barci. Ta ce,


"Ummina da alama ta ji daÉ—in barcin nan. Tunda kuka shigo take abu É—aya."


Yamaira ta ce,


"Ai haka take da barci Yesmeen. Ba ta ko gajiya. School dai za a saka ta idan an koma hutu duk kowa ma ya huta."


Bankwana ta ma Momy. Momy ta mata nasiha kan ta ƙara riƙe zumunci, yanzu ba kamar da ba ne. Idan da kawai a matsayin matar alhaji Marwan take to yanzu ba haka ba ne, ta shigo sahun ƴaƴan gidan. Ta ma Momy godiya sosai sannan suka tafi.


Bayan Maryama ta dawo har za ta zarce ɗakin su Hanan sai Momy ta kira ta ta dawo. A ƙasa ta zauna kanta sunkuye tana wasa da yatsun hannunta.


"Maryama..."


Ta ji Momy ta kira sunanta. Da jin haka sai ta tabbatar da cewa magana ce za su yi mai muhimmanci. Ta miƙa dukkanin hankalinta ga Momy.


"Maryama a haƙiƙa bani da kalmar da zan yi amfani da ita wurin jinjina miki. Jiya lokacin da Alhaji Marwan yake ba mu labarin gwagwarmayar da kika sha na yi matuƙar mamaki. Ban taɓa tsammanin kyawawan halayen naki har sun kai haka ba. Ashe ƙaramar yarinya kamar ki za ta iya siyar da farin-cikin ta domin nema wa wani bawan Allah lafiya? Na yi mamaki sosai.


Yanzu dai nasiha zan daÉ—a yi miki a matsayina na uwa..."


Sallamar Annur da Sans ta ji hakan ya sa ta dakata tana kallon su. Sans ya ce,


"Bro fira ake fa tsakanin Æ´a da uwa."


Annur ya ce,


"Ah to ai sai mu zauna a yi da mu."


Murmushi Momy ta yi haÉ—e da ci gaba.


"Halin nan naki da na san ki da shi nake son ki ƙara wani a kai. Ki zama mace mai haƙuri, mace mai kamun kai, sannan kuma mace mai adanar sirrin mijinta. Kin ga ciki da kike gani, ba wai don cin abinci kawai aka yi shi ba, har da don ajiyar sirri. Ki guji duk wata ƙawar banza da za ta nemi gusar da farin-cikin mijinki. Ki masa ladabi daidai gwargwadon ikonki. Ki riƙi haƙuri, domin kuwa shi ne baki ɗaya a zaman aure."


Ta juya ga Annur.


"Kai ma na dawo gare ka. Gwara da Allah ya sa ka shigo ma. Don Allah Annur kar ka zalunci Maryam. Na san ka san yadda ta sha wahala da kai a lokacin da ba ka da wani gata sai Allah. Ta ƙaunace ka da zuciya ɗaya a irin lokutan da ba lallai ba ne ba ka samu masoyi. Ta bijirewa zaɓin iyayenta duk don ta faranta maka. Ina son ka ƙoƙarta saka mata da kyautatawa, kamar yadda Allah maɗaukakin sarki ya ce sakamakon kyautatawa yana ga kyautatawa. Ka fitar da haƙƙin iyalinka. Ka guji duk wata zugar abokan banza, babban burinsu shi ne su ga sun raba kanku. Ina so ka zama ita ta zama kai. Ko mu nan ba na fatar ranar da za ka kawo min ƙarar Maryama cewa ta yi maka wani abu. Idan ma ta maka ɗin, to don Allah ku daure ku sasanta kanku a tsakaninku. Ka yi haƙuri da ita, duk wuya duk runtsi kar ka butulce mata."


Kanshi a ƙasa yana jin daɗin nasihar ta Momy ya ce,


"To insha Allahu Momy. Mun gode ƙwarai."


"Saura kuma nan da shekara ɗaya mu ji ka ce za ka ƙara aure, don ba za mu lamunci wannan ba."


Dungurar masa kai Momy ta yi tana murmushi.


"Allah kuwa Salman sai na ci maka. Kuma ko ka fitar da mata kai ma ko in je cikin matan nan masu kawo tallar fura a wancan sabon ginin da ake yi na nema maka auren É—aya."


Dariya suka saka su duka. Dady da ke daidai shigowa É—akin ya ce,


"Ai dai ya ga ga É—an uwansa nan ya zama magidanci. Shi kuwa ya yita zama a haka."


Maryama cikin zolaya ta ce,


"Dady ai ya tsayar da mata fa. Ni kaÉ—ai ya faÉ—a wa ita."


"Ah to faÉ—a min sarakuwar in ji ta mana Æ´ata Maryama."


"Dady kar ka damu. Ai tsakaninmu ne, kar kuma ya ce ba zai sake faÉ—a min sirrinsa ba."


Momy ta taɓe baki haɗe da yin murmushi.


"In ta yi tsami ma ji ai."


Hararar Maryama ya yi Sans.


"Ni da yaushe na yi da ke wai na tsayar da mata?"


Ta É—ora hannunta a ka kamar da gaske. Ta ce,


"Ji min mutum zai nuna bai san an yi ba. Kai dai kawai ka yi ladabi ko kuma na fallasa sirrin."


Islam ta fito hannunta riƙe da na Abdul da ke neman faɗuwa saboda barcin da ya yi. Da sauri Maryama ta je ta riƙo shi.


"Haba mana Aunty Islam. Ji fa yadda kike jan shi kamar ba mutum ba."


"Yo Maryama idan ba jan nasa ba ya zan yi da shi. Wannan gardin dai ai ba iya É—aukarsa zan yi ba."


"Ni zan iya."


Maryama ta faÉ—a. Ta kuwa É—auke shin sannan Islam ta ma su Momy bankwana. Momy ta ce,


"Mun yi waya da Saddiqa ai. Ita ke faÉ—a min wai kun yi waya kin ba ta labarin komai. Ta dame ni da kuka nikam na kashe wayar. Za ta zo jibi ma wai."


Islam ta ce,


"Ehh haka ta faɗa min. Ta damu ne sosai ni ma kukan take ta yi min, har na ji dama ban faɗa mata ba tun farko. Wai za ta zo har gidan su Amrah mu je mu ba ma Ummanta haƙuri abubuwan da suka faru a baya."


Sai Annur ya ji faɗuwar gaba. A duk sadda zai ji an ambaci sunan nan to sai gabanshi ya faɗi. Hakan bai rasa nasaba da zaman dirshan ɗin da ta yi a cikin zuciyarsa, wanda fitarsa ba abu ne mai sauƙi ba.


Maryama na dawowa daga rakiya Momy ta ce ta tashi su tafi dare na yi. Dady ya ce da Annur next week zai koma aiki a matsayinsa na architecture na companynsu. Shi kuma Sans ya ci gaba da zama a matsayin CEO baki É—aya.


A cikin mota Annur ya kamo hannun Maryama. Ya kalle ta sannan ya miyar da kallon sa ga tuƙi.


"Na yi kewarki sosai."


Ta harare shi.


"Ban taɓa gani ba sai yau."


"Me?"


Ta faÉ—a cikin mamaki.


"Yo da Hausawa ke cewa wai aikin banza harara cikin duhu. Ban gasgata ana yin ta ba sai yanzu a wurin matata."


Ta taɓe baki.


"Ashe dai ba a duhun ba ne tunda dai har ka san na harare ka É—in."


"To na ji. Yanzu dai faÉ—a min wace mata ce kika ce kin wa Salman? Don kar sai mun je gida ki ce ki faÉ—a min, bayan kuma kin san ba lokacin irin wannan hirar ba ne."


"Mutumin nan kai ko."


"Ni me? Gaskiyata fa na faÉ—a malama."


"To na ji. Hadizar nan ka tuna ta?"


"Wace ma?"


Ya tambaye ta.


"Wacce na faɗa maka ita ta yi silar da har muka san cewa kana Maraɗi. Budurwar Yah Salman ɗin ce dama. To ita na zaɓa masa a matsayin mata. Na tabbata ba za ta ƙi shi ba, kamar yadda shi ma ɗin ba zai ƙi ta ba. Na yi waya da ita ma ta ce ta amince. Ina so ne mu ƙulla zumunci da ita har ƙarshen rayuwarmu. Saboda gudummuwa da ta bayar na samuwar ka."


Ya jinjina kansa haɗe da riƙo hannunta.


"Kina da brain sosai Baby. Tabbas tunanin nan naki ya yi sosai."


"Dama ina so mu je MaraÉ—in, an ce Fiddou ta yi aure. Ina so mu je mata kana cikin hankalinka, ka mata godiya na É—awainiya da kai da ta yi, da kuma soyayya da ta gwada maka a lokacin da ka yi rashin gata."


Yana murzar hannunta ya ce,


"Ni ma kaina na yi tunanin hakan. Amma me ya kamata mu kai mata?"


"Ina da manyan frames a ƙarƙashin gadona, dayake nawan sun so su yi yawa, Mama ta siya kuma sai ga gifts da akaita samu na frames ɗin. Sai a ɗauki ko guda uku a tafin mata da su."


Annur ya ce,


"To masha Allahu. Hakan za a yi. Ɗazu a mota bayan an ɗauko mu daga Airport Uncle Marwan ke ce min wai dole sai na miki lefe. Saboda ba wani abun kirki ne a cikin wanda ya yi ɗin ba. To Momy dai ta ce in bari ba sai na yi ba, za su yi komai a kawo miki. Ni dai na ga cancantar na yi miki ɗin, zan kuma yi insha Allahu sai ki haɗa duka. Dady kuma ya ce zai yi ƙoƙari a ci gaba da wannan ginin na jikin namu, part biyu ne a cikinsa, amma da ƴar tazara a tsakaninsu, sai mu zauna ni da Salman idan ya yi aure."


Cikin jin daÉ—i ta ce,


"Allah ya tabbatar mana da alkhairi Yaya. Allah kuma ya bar mu tare har ƙarshen rayuurarmu. Allah ya kawo ranar da zan haifa mana little Amrah."


"Amin."


Ya faÉ—a a daidai isowarsu bakin gate. Horn ya yi mai gadi ya buÉ—e musu gate É—in suka shige.


Dama sun yi sallolinsu. Kai tsaye bedroom kawai suka wuce saƙale da juna.


"Yaya ka samu ka watsa ruwa. Ni ma zan je É—akina na watsa ko zan ji daÉ—i a jikin."


"Ki je ina?"


Ya ƙwalalo ido yana kallon ta.


"Dakina mana."


Ta ba shi amsa haÉ—e da tunzuro baki.


"Ai malama ki ɗauka cewa wanan ɗakin naki ya zama ɗakin baƙi. Kayanki ma duk kwaso su za ki yi ki dawo da su nan. Shara kawai za ta rinƙa kai ki can. Bari ma ki ga."


Ya kama hannunta suka nufi toilet É—in. Sai ta tuno ranar farko da ta fara yi masa wanka. Ta runtse idonta tana sakin murmushi.


Bayan sun gama suka fito a cikin towel ɗaya. Mai suka shafa sannan suka miƙe a tare ta fitar masa da rigar barci. Sai da ta saka sannan ta ce da shi za ta je ɗakinta ta ɗauko kayan barcin ita ma. Doguwar riga ce ta sako wacce iyakacinta bisa guiwa. Yadinta santsi gare shi irin mai kwnaciya a jikin nan. Ga wata irin humra da ta shafa wacce Islam ta kai mata yau. Sai duk ko'ina ya game da ƙamshin humrar.


Ta same shi ya zauna bisa stool ya dumtse hannunsa na dama. Murmushi ta saki bayan ta iso gare shi. Ya kama hannunta na hagu. Yatsar kusa da ƴar ƙarama ya kama, ya buɗe hannun nasa ashe zoben nan ne a ciki. Ta bi shi da ido har ya zura mata zoben.


"Haƙƙin Amrah ne, amma mahaifiyarta ta ba ni kyautarsa. To ni ma na ba ki kyautarshi da zuciya ɗaya. Ina so ki ɗauka cewa ke kaɗai ce a zuciyata idan har aka cire Amrah da ta daɗe a ciki tun ina yaro. To ki saka a ranki ƙaunar da nake yi ma Amrah ba komai ba ce a yanzu, tunda dai ta tafi babu ita. Ke ɗin dai ce, zan kuma ci gaba da ƙaunar ki har ƙarshen rayuwata."


Tsabar jin daɗi ba ta san sadda ta rungomo shi ba tsam-tsam a jikinta. Numfashi take saki, tana jin yadda ƙaunarsa ke ƙara shiga cikin zuciyarta. A nashi ɓangaren ma haka ne. Daga nan sai suka faɗa duniyar soyayya.


A gida kuwa tun bayan tahowar su Annur Momy ta shige É—aki tana kuka sosai. Tana jin yadda soyayyar É—anta da ya rasu ke daÉ—a wanzuwa a cikin zuciyarta. Dady ke ta rarrasarta yana ba ta baki har ya samu ta yi shiru.


Washe gari


Misalin sha É—aya na safe Maryama na kitchen ita da Annur suka ji knocking.


"Mallam ka ƙyale ni in dubo mai knocking please, ka wani ƙanƙame ni duk ka hana ni saƙat wallahi."


Annur ya ce,


"Su ma dai baƙin, su rasa lokacin zuwa sai irin wannan da nake jin daɗin kasancewa manne da ke?"


Ta gyaÉ—a kanta.


"Please mana yah Noor. Babu fa daÉ—i mutum yaita tsayuwa ba a buÉ—e masa ba."


"Aunty masifa na ji to. Je ki, amma ki yafa mayafi."


Ba ta ko tsaya saurarar sa ba ta doshi falo. Sai da ta fara saka hijabinta sannan ta isa ta tambaya waye. Muryar mace ta ji ta ce,


"Maƙoftanku ne da suka dawo shekaranjiya."


Da sauri Maryama ta buɗe ƙofar. Kyakkyawar mace ta gani tsaye da mijinta, sai kuma wasu yara guda biyu babba da ƙarama.


Murmushi ta sakar musu haÉ—e da ba su izinin shigowa har da mijin.


"Sannunku da zuwa. Last week fa na ji ana ta kawo kaya, ashe ku ne kuka dawo gidan."


Matar cikin sakin fuska ta ce,


"Wallahi kuwa mu ne. Yau kwananmu biyu da dawowa ai."


"Ah to masha Allah. Ƴan yara sannunku."


Ta kama hannun babbar.


"Good morning Mama."


Yarinyar ta faÉ—a cikin ladabi har da rusunawa.


"Morning my dear. Ina zuwa."


Ta miƙe. Kitchen ta nufa ta same shi. Ta ɗika masa duka.


"Mallam ai sai ka fito mun yi baƙi. Sabbin maƙwaftanmu ne har da mijin duk na ce su shigo."


"Ok to bari in je."


Ya fita. Ita kuwa lemuka ta jera a tray ta fita da su.


Hannu ya ba namijin suka gaisa. Sannan matar da yaran duk suka gaishe shi.


"Ga lemu nan ku sha."


Maryama ta faÉ—a tana murmushi.


Matar ta ce,


"Wallahi mun gode. Ai dayake safiya ce, karyawarmu kenan."


Mijin ne ya yi magana cikin sakin fuska.


"Ni sunana Khalid, matata kuma Ikram (Wanda ya karanta littafin SHI NE SILAH zai san su) waƴannan kuma yaranmu ne, Feenah da Ummu Ruman. Ina so mu ƙulla zumunci, tare da riƙe amanar juna."


Annur ya murmusa.


"Insha Allahu kuwa. Daga yanzu ka zama abokina Khalid. Ikram ma kuma ta zama ƙawar Maryama. Zumunci ya ƙullu kenan har abada."


"To masha Allahu."


Khalid É—in ya faÉ—a.


Sun ɗan jima suna taɓa fira kafin Khalid ya ce su tashi su tafi rana ta yi. Sosai Maryama da Annur suka nuna jin daɗinsu, sannan suka yi musu alƙawarin za su shigo su ma da izinin Allah.


Washe gari


Bayan sun gama karyawa Annur ya ce da Maryama ta shirya yau su tafi MaraÉ—i. Saboda ya fi son a yi komai kan lokaci, duk da dai cewa Hadizar ta

Please Login or Register in order to submit comment