You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su a baya. Dr. Huzaif kuma ya koma Office É—insa.


A reception suka ga Mallam Ya'u zaune yana jiransu. Yana ganin su ya miƙe yana musu sannu. Shi ya karɓi Modu ya saƙalo hannuwansa a ƙarƙashin hannun Modu na dama, ya dafo hannun Modu ɗin ya dafa a kafaɗarsa, suka ci gaba da tafiya a hankali har suka isa bakin mota.


Bayan sun isa ya miƙawa Maryama makullin motar, ita ta buɗe sannan ta buɗewa Modu gidan gaba, Mallam Ya'u ya zaunar da shi, yana yi yana masa sannu.


Shisshiga suka yi cikin motar, Fiddou na tsaye tana ta faman kuka, Mallam Ya'u ya tayar da mota suka bar wurin. Har suka ɓacewa ganin Fiddou ba ta daina ɗaga musu hannu ba. Wani irin ƙunci take ji a tattare da ita, wanda ita kanta ba za ta iya misalta shi ba.


A nan inda take tsaye ba ta san sadda Mahmouda ya tsaya a gabanta ba. Duk ta yi nisa a duniyar tunani har ya shigo da motarsa ya faka, ya fito daga motar ya tsaya a gabanta.


"Fiddou lahiya dai ko?"


Ya ambata cikin wata irin murya, mai nuna zallar tashin hankali, saboda shi a tunaninshi ma ko Modu ne ya mutu, ko kuma ciwon nasa ne ya tsananta.


"Sun tahi da shi, Æ´an uwa nai sun zo sun tahin min da Modu."


Ta duƙe a wurin tana kuka sosai, wanda duk wani mai zuciyar imani ya ji shi sai ya tausayawa mata.


"To ai ba kuka za ki yi ba Fiddou. Abu ne wanda yak kamata ki ɗaga hannunki ki godewa Allah, da ya kawo miki dangin Modu, har suka tahi da shi inda suke. A gani na ai hakan zai hiyewa Modu sauƙi, zai samu kula sosai daga wurin dangi nai, wata ƙila ma ya haɗu da wannan Amrah da yake yawan hwaɗin sunanta."


Kanta ta gyaÉ—a masa Fiddou, cikin sanyin murya ta faÉ—a masa cewa Amrar ma ba ta raye. Kawai dai sun yi soyayya ne sosai, wadda ita ce ma silar haukacewarsa.


Ajiyar zuciya ya sauke Mahmouda, ya ce,


"Ki daure to ki tashi da Allah de. Kukan naki ai babu abin da zai anhwana miki baya ga ya sakar miki wata cuta, wacce za ki rasa maganinta."


Cikin sanyin jiki ta miƙe a bisa ƙafafuwanta. Sosai take jin jiri na ɗibarta, tana neman zubewa ƙasa ba tare da ta shirya ba.


Komawa ta yi ta zauna a ƙasa, dafe da kanta da ke barazanar fashewa.


"Daure dai ki miƙe in kai ki gida Fiddou. Dole ki ƙoƙarta rangwantawa kanki damuwar nan, Modu dai ya tahi, duk wata damuwa taki ba za ta taɓa dawo da shi ba."


Ya sunkuya ƙasa ya taimaka mata, hannunta na dama ya riƙe ya miƙar da ita tsaye, bai sake ta ba har sai da suka isa gaban motarsa.


Ƙoƙari yake ya buɗe mata ƙofar ta shiga, amma ina, tuni ta sulale ƙasa, ta baje wurin a sume, idanuwanta rufe.


***


Satin da Annur ya cika kwana goma da haihuwa ne transfer É—in mahaifinsa ta tabbata, inda aka miyar da shi cikin Katsina, Federal Medical Center É—insu. Sosai suka yi farin ciki, ko ba komai gida suka koma. Dama rabonsu da gida kusan shekara É—aya kenan, ko zumunci ba su je ba, saboda rashin wadataccen lokaci. Yanzu kam godiya ya ma Allah, ya kuma yi fatan Allah sa can É—in ya fi zama alkhairi a kan cikin garin Bama, saboda a wancan lokacin a Bama FMC É—insu take, can ne gari mafi girma, mai kwanciyar hankali a duk Borno State.


A falo suke zaune, Suhaila na shayar da Annur suka ji wayar Dady ta yi ƙara. Gaggauta ɗaukar kiran ya yi, hannunsa saƙale da na Momy, wanda ta tallabo Annur ɗin da shi.


Bayan sun gaisa da mai kiran nasa ya ce,


"Zan shigo asibitin ai gobe kafin mu wuce, ban ma karɓarwa Annur takardar haihuwarsa ba. Ga kuma bankwana da ba mu yi ba da sauran al'umma."


Ya É—auki kusan mintuna bitu yana wayar kafin ya tsinke, ya miyar da wayar ya ajje, sannan ya dubi Suhaila cike da soyayya ya ce,


"Dr. Hamdana ne, young Dr. ɗin nan da nake faɗa miki, wanda bai wuce sa'an ƙanina na uku ba."


Bayan ta daidaita kwanciyar Annur da ya yi barci ta ce,


"Ai yanzu kam ya wuce ƙarami, tunda ya taka matsayin da manyansa ma ba su taka ba."


Tana murmushi cike da tsokana.


Hannunsa ya sa ya kamo haɓarta, ya mata hararar wasa ya ce,


"Babu komai dai, na ji. Ai ni É—in ma zan zama babban Pharmacist."


"Insha Allahu kuwa. Ina ma mijina fatan hakan, ya zama abun alfahari ga kowa, ga iyalinsa da dukkanin al'umma ma."


Cikin tattausan lafazi ya É—ora idamuwansa bisa kyakkyawar fuskarta, ya ce,


"Ina son kalar addu'ar nan taki a kodayaushe. Sosai take ƙarfafa min guiwa, nake ƙara jin ƙaunar matata na daɗa hauhawa a cikin zuciyata."


Miƙewa ta yi ta ƙarisa bisa ƴar katifar Annur mai haɗe da gidan sauro, ta shimfiɗar da shi ciki sannan ta dawo ga mijinta, ta zauna ƙugu da ƙugu da shi.


"Ba zan taɓa gajiyawa da yi maka addu'a ba mijina. Shin menene amfanin matar da za ta gaza buɗar bakinta ta ma maigidanta addu'a? Bata da amfani a ganina. Ta zama sokuwa, wawuya, kuma ƙatotuwar mai sakaci."


A wannan karon kam sumbatar hannunta ya yi cike da bege, ya ce,


"Ina alfahari da ke, zan kuma ci gaba da yin alfahari da ke har ƙarshen rayuwata, insha Allahu."


Ya É—aga kanshi ya dubi Nadrah da Saddiqa da ke tsaitsaye suna kallonsu, ba ma su san sun shigo falon ba.


Da hanzari Suhaila ta gaggauta matsawa daga jikin Dady da take, saboda nauyin yaransu da ya É—arsu a cikin zuciyarta. Ta ce,


"Nadrah me ya sa bakwa sallama ne? In ce ko na sha gargaÉ—inku a kan ku daina shigowa wuri ba tare da kun yi sallama ba?"


"Momy mun yi sallama fa, har sau biyu ba ku ji ba."


Nadrah ta faÉ—a tana É—an ja da baya, saboda ta san halin Momynsu, ba ta da wasa in dai wurin tarbiyya ne.


Rasa abun faÉ—e ta yi Suhaila, hakan ya sa ta ce,


"Ai da sai ku dakata daga bakin ƙofa har sai kun ji an amsa sannan ku shigo. Ina aiken da na muku?"


Da tsoro ta ce,


"Momy mun faÉ—a mata, ta ce wai to, goben kafin mu tafi za ta shigo ta kawo miki."


"Good."


Suhaila ta furta bayan ta murmusa kaÉ—an.


Washe gari da sassafe suka gama shiri, motar da za ta kwasar musu kaya ma har ta tafi, da yake tun da asubah aka fara lodi.


A ƙofar gida maƙofta ne da dama suka zo yi musu bankwana, har da masu kuka a cikinsu, saboda zaman arziƙi da aka yi.


FMC suka fara biyawa, Pharmacy suka tasanma, Pharm IA ya yi bankwana da mutanensa, cike da jin zai yi kewarsu sosai, suka tasanma Amenity, inda za su karɓarma Annur takardar haihuwarsa.


A mota ta bar su Nadrah da Dadynsu, ita kuma ta ƙarisa daga ciki, inda za a bata takardar.


Bayan ta karɓa daidai za ta fita ta ci karo da wannan matar shuwa mai suna Shereefah, tafe da wata yarinya ta goyo jinjirin, wanda da alama Nanny ɗinsa ce.


Da fara'a suka kalli juna, suka gaisa cike da aminci a fuskokinsu.


"ÆŠan yaro kana goye? Miye ne sunansa?"


Shereefah Shuwa ta faÉ—a da murmushi.


Murmushin ta sakar mata ita ma Suhailah, ta ce,


"Sunansa Annur, bari na sauko miki shi."


"Barshi ya yi barcinsa dan Allah. Suna mai dadi, Allah Ya raya Annur."


"Ameen fa. Ya sunan na wajenki?"


Karar sunan nasa take kasantuwarsa haihuwar fari, duk da kuwa ba shi É—in ne farko ba, a tunaninta wancan É—in da ya rasu ne farko, amma tunda dai babu shi, dole wannan É—in za ta yi kara, tunda shi É—in ne matsayin babba yanzu. Hakan ya sa ta kalli Nanny É—in, alamun ta ba Suhaila amsa.


"Sunansa Salman."


Yarinyar ta faÉ—a tana fara'a.


"Masha Allah! Allah Ya raya Salman. Ga shi ba su gaisa da abokinsa ba har za mu wuce."


"Za ku wuce ina? Ba dai garin za ku bari ba ko?"


Ta faÉ—a cike da zaro idanuwa tana mamaki.


Suhaila ta ce,


"Wallahi fa. Mu dama Æ´an cirani ne, aiki ya kawo mu nan, ga shi kuma ya É—auke mu, ya miyar da mu asalin garinmu."


"Allah sarki! Allah sa hakan ne mafi alkhairi a gare ku. Amma ko sunanki ban sani ba, ga shi bani da lambarki bare a cigaba da zumunci."


Introducing ɗin junansu suka yi, a ƙarshe suka yi musayar lambobin waya sannan suka rabu, ba tare da kowace ta ga yaron kowa ba.


Bayan ta samu su Dady a mota ne ya ce daga nan kuma ɓangaren psychiatric za su nufa, saboda ya ma Dr. Hamdana alƙawarin za su haɗu su yi bankwana, kafin su wuce.


Hakan ce kuwa ta kasance, ɓangaren da marassa hankali suke suka dosa, kai tsaye suka nufi Office ɗin Dr. Hamdana, wanda ke cike da kayan alatu, da na more rayuwa.


Nadrah da Saddiqa suka gaishe shi, sannan Suhaila ma ta gaishe shi da fara'a.


Dr. Hamdana mutumin kirki ne, ƙaramin yaro amma mai matuƙar girmama na gaba da shi. Shi ne the most youngest Dr. A duk asibitin, haka kuma shi ne mutum na uku da ake ji da shi a duk cikin likitocin mahaukata.


Ba su wani jima ba dady ya miƙe, yana miƙewa suhaila da yaranta ma suka miƙe, Dady na faɗin,


"Bari mu lallaɓa Dr. Ka san tafiyar ta mu ba ta kusa ba ce, dole sai an tafi da wuri. Na so ma a ce tun 7 mun bar nan, amma maƙota sukaita bamu shawara cewa kar mu yi fitar nan ta dugu dugu, ta cika hatsari da yawa. To motar kayanmu dai ta yi gaba, na ce da dreban yai haƙuri har gari ya waye ya nunar min da babu abin da zai faru da yardar Allah, ya tafi kawai."


Dr. Hamdana ya murmusa ya ce,


"Hakan ya fi ai. Allah ya kai ku lafiya ya tsare mana ku. Mr. IA please kar a yar da zumunci, a ci gaba da kula da juna, da yardar Allah ni ma ba zan taɓa mantawa da kai da ahalinka ba."


Musabaha suka yi cikin aminci, Dr. Hamdana ya buɗe wata loka ya zaro kuɗi masu yawa, ya miƙawa Saddiqa yana faɗin,


"'Yata ga wannan, a sha ruwa a hanya."


Ƙin karɓa ta yi har sai da ya kalli Suhaila cewa ko ita ce ta hana Saddiqa karɓar kyautar da ya mata? Da fara'a ta ce da Saddiqa ta karɓa, sannan ta karɓa ɗin da godiya a bisa laɓɓanta.


Har bakin mota ya raka su Dr. Hamdana, sannan ya ga sun tashi ya koma Ofishinsa.


***


sai bayan magrib sannan su Maryama suka isa Katsina. Sai da suka fara biyawa suka sauke Hadiza sannan suka wuce gidan su Jiddah, ita É—in ma aka sauke ta. A lokacin Modu ya jima da yin barcinsa, bai ma san me ke faruwa ba.


Horn É—in da Mallam Ya'u ya yi ne ya sa mai gadinsu ya gaggauta buÉ—e musu gate, suka shigo da motar a cikin gida.


Ƙarar motar ya sa Muhammad fitowa da gusunsa, fuskarsa ƙunshe da fara'a ya tarbe su.


Bayan Maryama ta fito daga motar ne ta amsa sannu da zuwan da Muhammad ke mata, ta ce,


"Ka je ka ce da su Mama mun iso, kuma har da mara lafiyan, wai ina za mu kai shi?"


"To."


Ya faÉ—a haÉ—e da barin wurin da gudunsa, ya isa cikin falon yana faÉ—in,


"Mama dama na faɗa miki su ne ba Abba ba. Haka Yaya Maryama ta ce wai sun zo tare da baƙo, ina za a nufa da shi?"


Miƙewa ta yi Mama, ta fara ajje takunta har ta isa harabar gidan, ta inda ake faka motoci biyu da suke da su.


"Barkanku da dawowa. sannu ya hanya?"


Ta faÉ—a tana kallon Mallam Ya'u da murmushi, sannan ta ce da Maryama,


"Ashe tare É—in kuka zo."


"Ehh mama, mun tabbatar É—in shi ne fa, bari mu shiga ciki zan miki bayanin komai insha Allah."


"To madalla."


Ta furta bayan ta zagaya ta inda Modu yake, tana kallonsa da gyaɗa kai, tausayinsa take sosai, yanayinsa da komai nashi abun tausayi ne. Kayan jikinsa babu kyawun gani, ga wani irin zaurin fitsari da yake yi, wanda sai mutum ya kai zuciyarsa nesa zai iya haɗiyar yawu. Sosai ta yaba da ƙoƙarin su Maryama, na yadda suka taho a haka tun daga Maraɗi har Katsina. Tamkar ta zubda masa ƙwalla haka ta ji. Lallai mai rai ba wata tsiya ba ce. Duk a yadda Allah ya yi ka kawai ka gode masa, haƙiƙa ka fi wani. Duk yadda kake ganin kai mai larurin ciwo ne, ɗaga hannu ka godewa Allah, saboda akwai wanda sun fi ka larurin, wasu ga cutar ga kuma talauci da ya musu katutu, wanda ko kuɗin da za su nemawa kansu magani ba su da.


Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke Mama, fuskarta ƙunshe da tausayin Modu, ta ce,


"Dole inda mutane suke za a ajje shi, gudun kar ya buƙaci wani abu ba a sani ba. In baccin haka ai da sai a kai shi part ɗin can na baya, idan an gyara. Ya yanayin nasa yake? Ina nufin yana duka ko kuma attempting guduwa?"


Sassauta muryarta ta yi Maryama, ta ce,


"Ba ya ko ɗaya gaskiya, haukan nasa fa ba wani mai ƙamari can can ba ne, surkulle ne a kan Amrah, yai ta subbatu cewa wurinta zai je, sai idan bai samu wata maganar kirki ba ne har ya yi ƙoƙarin guduwa, cewa shi zai je da kansa ya nemo ta."


Mama ta ce,


"Ah to in haka ne, bida irinsu ai ba abu ne mai wahala sosai ba. Kenan dai shi É—in ne Annur da kuke zato?"


Ta ƙarisa maganar da firfito da idanuwanta, cike da mamaki.


"Uhm...shi ne fa Mama. Abin da na ce zan faɗa miki kenan ai idan mun shiga ciki. Ta subbatunsa kaɗai muka tabbatar da cewa shi ne real Annur, wancan ɗin na ƙarya ne."


"Subhanallahi! Lallai akwai damuwa, there's something behind, Allah kaÉ—ai ya bar wa kanSa sani. Yanzu dai a tafi da shi É—akin Muhammad, shi Muhammad É—in sai ya kwana É—akina. Kamar hakan zai yi ai."


"Tunanin da na yi ni É—in ma kenan Mama. Allah Ya taimaka, Ya ba mu ladar taimakon baki É—aya."


"Ameen Maryama. Mallam Ya'u ko za a kamo sa a shigar cikin gida?"


"To ranki ya daÉ—e."


Suka fara ƙoƙarin kama Modu, shi da Mai gadi.


Cikin gidan suka shiga su Maryama, cikin yanayin gajiya ta ce,


"Barin tafi sallah, ban yi ko magrib ba, ga isha na gabatowa."


"To ya yi, bara na kai masa abinci, in saka Mai gadi ya taimaka ya masa wanka, zan nemo masa kaya daga cikin na Abbanku."


"To Mama. Da kau ya ji daɗin jikin nasa, don da gani ya jima bai yi wanka ba. Kodayake Fiddou ta ce wai ta taɓa biyan wasu yara suka masa wanka sau ɗaya, wai yaran sukai ta masa dariya tun daga nan ba ta sake sakawa a masa wankan ba. Na tabbata zai ji sassauci a jikinsa yau. Gobe kuma sai mu saka a masa aski, gashin nan na fuskarsa duka a aske shi."


Tana gama faÉ—in haka ta doshi É—akinta, domin sauke farali.


A lokacin da suka kai Modu É—aki ya farka daga barcin, bin É—akin yake da kallo sosai, yana tunanin a inda yake, saboda shi ya ma manta da inda za su je, ya manta cewa wai wurin Amrarsa za a kai shi.


Ganin irin kallon da yake bin É—akin da shi ya sa Mallam Ya'u murmusawa ya ce,


"Kwantar da hankalinka, garin su Amrah ne nan, za ka ganta amma sai ka nutsu, ka yi duk abin da aka ce da kai ka yi."


Bai ce komai ba sai murmushi da ya saki, miyau ya fito masa dalala, duk bisa haɓarsa.


Murmushi ya yi Mallam Ya'u sannan ya fice daga É—akin, shi kanshi yana mai tsananin jin tausayin Modu.


Yana fita sai ga mai gadi ya shigo da plate ɗin abinci da cokali a ciki, ya ƙarisa gaban Modu da murmushi, yana faɗin


"Na Amrah bada kanka a sare, ka je gida ka ce ya faÉ—i. In ba Amrah ba sai rijiya, ita kaÉ—ai ce taka, haka kuma kai kaÉ—ai ne nata..."


Kanshi ya ringa jinjinawa Modu, alamun yana jin daÉ—in kirarin da mutumin ke masa. Murmushin nan bai kau daga fuskarsa ba, sai lila kansa yake, yatsunshi biyu a cikin baki, É—aya hannunsa kuma a bisa kansa.


"Abinci ne na kawo maka, idan ka ci sai na maka wanka, ka saka sababbin kaya na tarar Amrah sarauniyar mataye."


Bai musa ba ko kaɗan, haka ya ringa cin abincin nan kamar wanda ya tashi daga ciwon yunwa, rabi na shiga bakinsa, rabi na sauka a ƙasa, har abincin ya ƙare.


Mama da kanta ta shigo ta kawo masa kayan Abbah, masu matuƙar kyau, kuma sababbi ne sau biyu ya taɓa saka su.


Bayan ta miƙa su ga Maigadi ta fita, da kanshi ya cire masa kaya, ya ɗaura masa towel ɗin da Mama ta haɗo da shi a cikin kaya, ya ɗaura masa, sannan suka nufi banɗaki.


Sosai mutumin ya dirje shi, saɓi uku ya masa amma duk da haka ruwan kumfan jajur yake, tsabar datti da ya yi. A ƙarshe ya wanke masa kansa sannan ya ɗauraye shi suka fito.


Wani irin sakayau yake ji a jikinsa Modu, shi kanshi yanayin da yake cikinsa ba kaɗan ɗin daɗi yake ji ba. Banda murmushi babu abin da yake saki, haƙoransa sun ɗan yi haske, saboda dirzar da suka sha.


Mai ya shafa masa ko'ina na jikinsa, sannan ya feshe shi da body spray na explore, har kayansa sai da ya fesa ma turare, kafin ya saka masa su a jikinsa.


Take asalin sifarsa ta fito, ya koma real Annur Iqra Al-hussei; mutum mai matuƙar kyau na fuska da na sifa, mutum mai tsantsar ƙwarjini, wanda ba kowa ke iya haɗa fuska da shi ba, tsabar ƙwarjininsa. Mutumin da murmushinsa ke haskaka kyawun fuskarsa, murmushinsa ke daɗa ƙayatar da fuskarsa.


Shi kanshi mai gadi mamakinsa yake. Kyakkyawa da shi, ashe dai yanayi ne kawai ya miyar da shi a halin da yake ciki. Alwashi ya É—auka a ranshi cewa shi da kanshi zai ci gaba da kula da Modu, zai bashi kulawa É—ari bisa É—ari har ranar da zai bar gidan, ko kuma ya samu lafiya.


"To ka ga yanzu sai ka kwanta ka yi barcinka ka huta, a cikin barcin za ka ga Amrarka ta iso gare ka, ta tabbatar maka da cewa tana cikin aminci, kai kawai take jira."


Bai ko jira ya gama jin maganar ba ya haye bisa gadon É—akin, ya runtse idanuwansa yana son barci ya É—auke sa.


Murmushi kawai mai gadi ya yi, ya kashe masa wutar ɗakin sannan ya jawo ƙofar, yana mai matuƙar jin tausayin Modu, tunda Mama ta masa bayani kafin ya shigo yi masa wanka.


Tun bayan ta yi sallah ta yi wanka ta fito falon, ta tarar Mama ta zubo mata abinci, ta haÉ—a mata komai tana jiran ta je ta ci.


Zama ta yi a ƙasa ta jawo abincin kusa da ita, ta jiyo muryar Muhamnad na faɗin,


"Yaya Maryama ya bani taisayi sosai. Ina jinsa yana faÉ—in Amrah, hala dai wacece Amrah?"


Murmushi ta yi Maryama, ta ce,


"Masoyiyarsa ce."


Kawai ta yi shiru haÉ—e da fara kai lomar abinci a bakinta.


Sai da ta yi nisa ma ta tuno da wani abu, ta ce,


"Mama na tuna, Annur fa an hana ba shi duk wani abinci mai cholesterol a cikinsa."


Da fara'a Mama ta ce,


"Na sani, duk wani mai larurin zuciya akan hana ba shi choleterol, shi ya sa na yi wannan tunanin, na tura aka siyo min non cholestetol oil, da shi na yi girkin."


Ajiyar zuciya ta sauke Maryama ta ce,


"Yauwa. Sai kuma abu É—aya, bai sha maganinsa na dare ba."


"Subhanallahi! Kuma da ƙyar idan ba ya kwanta ba. Tashi mu je mu ga, Allah sai bai yi barci ba."


Tashin kuwa suka yi a tare har da Hammad, suka isa É—akin da ke É—an nesa da na Abbah.


Kunna wutar ɗakin suka yi, yanayinsa kawai ya saka su murmusawa su duka ukun. Kwance yake idonsa a rufe, sai ƙyaƙƙyaftu yake, wanda kallo ɗaya za ka masa ka tabbatar cewa ba barci yake ba.


Cikin murya mu ƙunshe dariya ta ce,


"Angon Amrah tashi ka sha maganinka, sannan ko koma barcin."


Firgigit ya buɗe idonsa, yana sakin murmushin yaƙe ya miƙe zaune.


Deep freezer ta buɗe ta ɗauko ruwan Sona guda ɗaya, sannan ta buɗe, ta ɓallo masa magungunansa da ke can bisa side drawer ta ba shi.


Sai da suka tabbatar ya sha sannan suka bar É—akin, bayan sun kashe masa wuta.


***


How are y'll? Fatan muna lafiya. Ya iyali ya shirye shiryen sallah? Allah sa komai lafiya.


Ya kuka ji wannan shafin? A yanzu dai na tabbata na warware nuku kawuna, dangane da Annur da kuma Sans. Na tabbata akwai da dama masu cewa kawunansu na a duhu, wai ba su gane komai a kan salon namu na yanzu, na kwan gaba kwan baya. Kafin mu fara dama na shaida muku cewa za mu canza salon labarin, mu taɓo farko sannan kuma mu taɓo ci gaba, tun daga yanzu har a gama warware mana silar zuwan real Annur Maraɗi, da kuma silar dawowar fake Annur (Sans) gidan su real Annur. Fatan za ku ci gaba da bibiyata, har izuwa wannan lokacin.


Masu faɗin wai marubuciya Amrah ba ta kyauta ba, me ya sa za ta ce Annur Iqra Al-hussein wai ba ainahin ɗan Pharm IA ba ne? Ku ajje hankulanku ku fahimci labarin nan, za ku ga kamar ya sha bamban da dama labarukan da kuke karantawa. Salo ne a cikinsa da ba koyaushe ake amfani da irinsa ba. Ku duba tun daga jigon labarin; aure da ake yi ba tare da awon genotype ba, shin ana yawaita taɓo ire iren jigon nan kuwa? Da wuya kam. Saboda haka a yi haƙiri dai, a kuma ƙara yin haƙuri, sannu a hankali duk za mu kai ga inda za ku buɗe baki, ku yi dariya sosai tsabar farin ciki.


Ina ma kaf al'umnar musulmai happy sallah in advance. Allah Ya sa mu yi sallah lafiya. Sannan ƙarin tunatarwa, a bi a hankali wurin cin nama, dan kar a ci aita zawo😂 ahto, kar ku ce Amrah ba ta faɗa muku ba. And a ajje min nawa naman, duk wacce ba ta ajje min ba za mu ɓata, kuma sai after one week zan ringa muku posting...lol😜


Sai kuma bayan sallah idan Rabbussamawati wal-ard ya nuna mana sannan za mu sake haɗuwa. Mu dage da ibada a cikin ƴan kwanakin nan da suka rage kafin arfah, Allah Ya karɓa mana ibadunmu ameen.


4k words na muku kawai don farin cikin zuwan sallah. Fatan kun yi enjoying reading na shi.


Thanks all
Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:55 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_


Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


4⃣7⃣


Taƙabbalallahu minna wa minkum. Fatan mun sallata lafiya. Allah ya maimaita mana amin. Wanda suka yi aikin Hajj Allah sa sun yi karɓaɓɓe. Wanda suka azumci ranar arfah, Allah ya karɓa, ya gafarta mana kurakuranmu ameen.


***


Haka Annur ya ci gaba da rayuwa a gidan su Maryama, ba tare da wata matsala ko kaɗan ba. Sosai suke ba shi kula, tamkar jininsu ne shi. Yadda suke tarairayarsa ko a gidansu yake iyakacin abin da za a masa kenan. Sai dai a kowace rana ƙaranci ya kira sunan Amrah sau bakwai. Amrah yake so, a kai shi wurin Amrah, ya san ita ɗin ma tana can tana jiransa. Kalaman da yake yawaita furtawa kenan, yayin da ruwan hawaye kan kwaranya daga ƙwayar idonsa zuwa bisa fuskarsa, a duk sadda zai neme ta. Maganinsa kam babu tangarɗa haka yake shansa, da zarar lokacin sha ya yi Mama za ta ce da Maryama ta je ta ba shi. Haka abincin da yake ci duk an bi ƙa'idarsa, baki ɗaya suka daina amfani da normal oil a gidan, sai dai non cholesterol, kurum don inganta lafiyar Modu.


Yanzu haka kwanakin Modu biyu kenan a gidan su Maryama, amma yadda suka shaƙu sai mutum ya ce sun shekara guda a tare ne. Sosai ta iya tafi da mahaukaci, kasantuwarta psychologist ce, psychology take karanta. Kusan duk irin wannan abubuwan ba

Please Login or Register in order to submit comment