You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce da Maryama ta amince amma dai ya kamata su yi maganar face-to-face. Tana cikin shiri Jiddah ta kira ta cewa ga ta nan ta zo tana knocking a buɗe mata. Da farin-ciki Maryama ta je ta buɗe mata ƙofar.


Zama suka yi fara'a ƙunshe a fuskokinsu suka gaisa. Ledar hannunta ta miƙa wa Maryama cewa kayan saka ranar su ne ita da Deedah. Tun shekaranjiya Abba da Kawu Imrana suka kai kayan. Maryama ta kumburo fuska.


"Yanzu don Allah sai a kai kayan saka rana amma a rasa wanda zai faɗa min? Ko da safen nan fa sai da na yi waya da Abba da Mama. Dama na ji Hammad na neman faɗa min wani abu kuɗin wayar tawa suka ƙare kuma bai kira ba. Ashe ƙawata amarcewa za a yi. Yaushe ne auren?"


Jiddah ta ce,


"Wata ƙila zance ne bai kawo ba. Yanzu dai ai ga shi nan kin ji daga gare ni."


"Na ji kam. Yaushe za a yi ba ki faÉ—a min ba."


"Wata biyu ne aka saka."


"To Allah ya nuna mana."


"Amin ya Allah. Ina Yah Noor da jiki?"


Maryama ta yi murmushi.


"Yah Noor kam alhmdulillah. Bari in kawo miki shi ku gaisa."


Ta tafi É—akinsa. Labari ta ba shi sannan ta kamo hannunshi suka dawo falon.


Tana ganin shi sai ta ga duk ya mata ƙwarjini, saboda duk wannan yaƙen da yake yi a baya babu shi yanzu. Ga kyau da ya yi sosai kamar ba shi ba. Ta gaishe shi. A maimakon ya sakar mata dariya kamar yadda ya saba yi idan an gaishe shi sai ta ga akasin haka.


"Lafiya lau Jiddah. An zo lafiya ya su Mama?"


Cikin mamaki ta ba shi amsa da lafiya lau. Maryama kanta ta san cewa Jiddah mamaki ne ya cika ta. Annur ya kalle ta da murmushi.


"Baby your friend is suprised. Zan shiga É—aki, explain everything to her."


Ya ba ta peck a hannu, sannan ya nufi É—akinsa. Jiddah ta bi shi da kallo har ya shige É—aki.


Maryama ta dawo kan kujerar da Jiddah take, ta zauna bisa hannun kujera. Nan ta labarta wa Jiddah duk yadda abubuwan suka faru. Sai ta riƙe baki cike da mamaki.


"Maryam kina nufin duk zaman nan wai Yah Noor ya warke kallon mu yake kyar?"


Kai Maryama ta É—aga mata.


"Ba ma wannan ne abun mamakin ba. Wai Farouk Sardauna dai da na sani shi ne ainahin É—an su Momy? Dama dai gaskiya akwai alamar tambaya. A ce tsakanin Sans da Annur babu wani bambanci kamar su É—aya. Ba zai yiu a ce coincident kawai ba ne. Dole sai identical twince ne za su yi irin wannan kamar."


"Haka ne kam. Kin dai ji yadda Allah ke tsara al'amarinSa."


Miƙewa Jiddah ta yi.


"Ni zan tafi Maryam, akwai wuraren da zan je idan na koma gida."


"Ke don Allah Jiddah tun yanzu?"


Jiddah ta ce,


"Zan dawo ai kar ki damu. Amma fa ina son jin kyakkyawan labari in the next two weeks."


Harararta Maryama ta yi, ta raka ta har bakin ƙofa, ta shaida mata cewa Maraɗi ma za su tafi yanzu.


"Aikuwa kun kyauta sosai wallahi. Please ki gaishe min da Fiddou, ki ce ina mata fatar alkhairi. Hadiza kuma idan komai ya tabbata insha Allahu da mu za a yi biki."


"To zan faÉ—a musu insha Allahu. Ki gaishe da su Mami."


*


Misalin ƙarfe biyu da rabi suna cikin garin Maraɗi. Hadiza ta faɗa musu inda za su yi mahaɗa, suka ɗauke ta. Kai tsaye gidan Fiddou suka fara zuwa.


Bayan Annur ya faka motar a ƙofar gida Hadiza ta fita da frames da Maryama ta ce mata ta ɗauka a bayan motar. Kafin Maryama ta fita ya ce


"Ki gaishe ta. Idan kuma mijinta ya bada izini sai in shigo har ciki na musu godiyar da kaina."


Maryama ta ce masa to, sannan ta É—auki hand bag É—inta ta fice.


A falo suka same ta kwance ƙasa, Mahmouda na yi mata fifita. Sallama suka yi, ya amsa haɗe da ɗago kai ya kalle su. Bayan sun shigo ciki suka zauna, da sakin fuska ya amsa gaisuwar da ya musu, kasantuwar bai san Maryama ba, Hadiza kawai ya sani.


"Barci ma take yi ko?"


"Walle kam ba ta da lahiya ne. Daga asibiti ma muke."


Hadiza ta yi dariya ta ce,


"Hala dai ta kamu ne."


Dariyar shi ma ya yi,


"Ba ki gajiya Hadiza."


"Aikam tashin ta za ka yi. Baƙi ne ta yi tun daga Katsina. Maryama da kuma mai gidanta Annur yana waje cikin mota shi ya kawo mu."


Ba zai taɓa manta duka sunayen biyu ba. Saboda har gobe suna da daraja sosai a zuciya da kuma bakin Fiddou. Sau da dama takan ambaci sunayen a duk sadda wani abu zai faru mai kama da nasu. Sai ya saki murmushi.


"Ahh sannunku da zuwa. Halan mi da bai shigo ciki ba? Bari in tai in shigo da shi. Fiddou!"


Ya bubbuga ta ta tashi. Murtsukar idanuwa ta fara yi.


"Sahibi mi kuma?"


Murmushi ya sakar mata.


"Baƙi kika yi."


Ta tashi zaune shi kuma ya nufi waje domin kiran Annur.


Tana haɗa ido da Maryama ta ƙarisa murmurewa. Ta saki baki da ido tana kallon ta.


"Wata nake gani kamar dai Maryama."


"Ni ce fa da kaina mai ciki."


Harara Fiddou ta kai mata.


"Babu ko gaisuwa sai tsokana ko?"


Hadiza ta ce


"Babu wani tsokana sai gaskiya. Malama ki ga yadda kika koma, ko mutum bai san mai ciki ba ya gan ki sai ya gane. Mu dai Allah ya raba lafiya mu samu É—a ko Æ´a."


A daidai nan Mahmouda ya shigo riƙe da hannun Annur suna dariya.


Fiddou na haÉ—a ido da shi sai da ta yi mamaki. Ba ta bar maganar a zuciyarta ba sai da ta tambayi Maryama.


"Halan dai Modu ya warke Maryam?"


Maryama ta É—aga mata kai tana murmushi.


"Ya warke Fiddou. Hadiza ba ta faÉ—a miki aurena da shi ba?"


Ta gyaÉ—a kai.


"Ta dai hwaÉ—i min ana aurenki rana guda da nawa. Amma ba ta hwaÉ—i min Annur za ki aure ba."


Maryama ta ce,


"Aikuwa shi na aura Fiddou. Ga shi nan kuma ya warke garas kamar bai taɓa yin wani ciwo ba. Abin da ya sa muka zo dama godiya za mu sake yi miki, shi ma kuma ya miki da kansa."


Annur ya yi murmushi, ya ce,


"Haka ne. Malama Fiddou ya gida ya ƙarfin jiki? Mallam Mahmoud ya ce min daga asibiti kuke."


Cikin kunya ta ce,


"Alhamdulillahi."


"To masha Allah! Duk da dai ban san ta inda zan fara ba, addua ce kawai daidai da ke. Allah ya saka miki da alkhairi Fiddou. Kamar yadda kika taimake ni ke ma Allah ya taimaka miki har ƙarshen rayuwarki. Allah ya dauwamar da farin-ciki a rayuwar aurenku. Allah ya ba ku zuria mai albarka."


Mahmouda ya amsa da,


"Amin. Ai babu komai Annur."


Ruwa ta kawo musu suka sha sannan suka miƙe cewa za su tafi gidan su Hadiza. Bankwana suka musu sannan suka kama hanyar gidan na su Hadiza.


Tare suka fita daga motar, Hadiza na gaba suna biye da ita har suka shiga cikin gidan.


Yayanta suka nemi ganawa da shi. Bayan sun gaisa Annur ya masa bayanin abin da ke tafe da su. Karara ya nuna jin daɗinsa. Saboda yawon ta-zubar ɗin da Hadizar ta yi a baya, amma cikin ikon Allah dama ta nadama ta dawo har ta yi istibra'i, mijin auren ake nema. Don haka duk sadda suka shirya kawai su zo a ɗaura aure, babu buƙatar ɓata lokaci tunda dai ba aure ba ne za a yi kamar irin na ƴan mata.


Annur ya ji daɗi sosai, ya ce insha Allahu iyayensu za su zo bai ɗaya a ɗaura auren a tafi da amarya. Godiya suka masa sosai sannan suka miƙe. Hadizar ta raka su har mota ita da yayanta, suka tafi suna jinjina halin karamci irin na mutanen.


*


Doya da ƙwai take soyawa, amma ji take zuciyarta na tashi, kamar ba ta son warin ta. Famar doɗe hanci ta kama yi, amma sai tsananta abin ke yi. Annur da ke daidai shigowa kitchen ɗin ya ce,


"Baby lafiyarki kike famar doÉ—ar hanci?"


Ba ta buÉ—e hancin ba ta ce,


"Wallahi ƙamshin doyar ne ba na so."


"To fa! Ko zazzaɓin ne har yanzu?"


"Na ji sauƙin zazzaɓin Baby. Da shirin tafiya lecture ma nake yi wai nan. Tashin zuciya ce kawai nake ji, kuma ƙamshin ne da ba na so..."


Tun ba ta rufe baki ba ta ji amai ya taso mata. Da gudu ta isa wurin sink ta hau kwara amai. Ba wani abun kirki ba ne ba a cikin dama. Guntun doughnut ne da yoghurt da ta yi sammakon sha, saboda yunwar da ta tashi da ita.


Da hanzari ya isa gare ta yana mata sannu. Take daga yin amai duk sai ta galabaita. Ya kamota ya riƙo bisa jikinsa. Yana ƙara ce mata sannu wani aman na zuwa, a jikinsa ta ci gaba da kwara shi. Bai ji ƙyama ba ko kaɗan, sai ma tausaya mata da ya yi sosai, ya hau yi mata sannu.


Ƙauri ya ji alamar doyar ta soye har man ma ya gama yin baƙi. Ga kuma Maryama a jikinsa. Da sauri ya ɗauke ta ɗaf, ɗayan hannunsa ya sa ya kashe gas ɗin sannan ya nufi toilet ɗin ɗakinsa da ita.


Rigar jikinta ya cire mata, ya wawwanke mata baki da wuyanta sosai da sabulu sannan ya É—auro mata towel ya kwantar da ita bisa gadon sa. Banda sannu babu abin da yake mata. Tausayinta yake yi sosai, yana ji kamar ciwon ya dawo a jikinsa.


Kayan nata ya É—auka ya fita da su can corridor ya jefa a washing machine ya wanke sannan ya cire rigarsa ma ya wanke.


Dawowa ya yi ya fiddo mata rigarsa long sleeve ya saka mata. Sannan ya ɗauko wani skirt nata na English wears ya saka mata yana yi yana ce mata sannu. Jin wayarsa ya yi tana ƙara. Da sauri ya duba mai kiran ya ga Salman ne.


"Ango lafiya dai ko?"


Ya faÉ—a cikin muryar gajiya.


"Lafiya ƙalau Annur. Wani aiki ne ya taso a Office yanzun nan Mu'azzam ya kira ni. Ya ce min kuma kai ma ba ka je ba."


Annur ya ce,


"Wallahi na yi shirin tahowa to kuma Maryam jikin babu daÉ—i. Asibiti ma zan kai ta yanzu.


"Subhanallahi! Me ya same ta?"


"Zazzaɓi ne dai take ta fama da shi kusan five days back, to yanzu dai abun ya yi worst, ba ta da wani ƙarfi sosai."


"Ya salaam! Gaskiya ka gaggauta kai ta asibiti. Bari in kira Mu'azzan É—in a tsayar da aikin har zuwa gobe idan Allah ya kai mu. Allah ya kyauta ya ba ta lafiya."


"Ameen Salman. Ka gaishe da Hadizar."


"Za ta ji."


Ya faÉ—a haÉ—e da tsinke wayar.


Mukullin motarsa ya ɗauka ya je ya buɗe ta ya sa mai gadi ya buɗe masa gate, sannan ya koma ya cicciɓo ta. Wayarsa da tata ya ɗauko sannan ya datse ƙofar bayan ya kwantar da ita a kujerar gaba.


K-Dara Specialist Clinic suka nufa. Sai da aka fara buÉ—e mata kati sannan aka tura ta layin ganin likita. Har a lokacin tana kwance a jikinsa, sannu yake ta yi mata. Ana zuwa kansu ya kama ta suka shiga. Likitan ya nemi sanin abin da ke damun ta Annur ya masa bayani.


Takarda ya basu cewa a je a yo awon fitsari da na jini. Ganin yadda jikin nata ya galabaita sosai ya sa ya ce dole za a ba ta gado a saka mata drip don walwalarta ta saitu. Nurses ya kira suka kai ta É—aki, amenity aka kama mata Annur ya biya, aka yi mata duk gwaje-gwajen da suka kamata.


Sai a sannan ya kira gida ya sanar wa Momy, sannan ya kira gidan su Maryama ma ya faɗa ma Mama. Yana gama waya da Mama Salman ya kira ya ji ya jikin? Ya ce da shi ma an kwantar da ita. Fatar samun sauƙi ya mata sannan ya ce anjima za su zo da amaryarsa Hadiza.


Bayan duk results sun kammalu likitan ya nemi ganinshi. A nan ya masa albishir da cewa Maryama na É—auke da juna biyu na wata guda da sati É—aya. Hamdala ya yi ga Allah cike da farin-ciki ya baro Office É—in.


A hanya ya ci karo da Dady da Momy sun zo duk a ruÉ—e. Ganin sa da suka yi yana murmushi duk sai suka yi turus suna kallon shi. Momy ta ce,


"Ta ji sauƙi kenan ma."


"Ehh alhmdulillah! Mu je na kai ku É—akin."


Suka bi bayanshi har zuwa amenity room 4.


A kwance suka same ta an rufe ta da blanket da ya aro a ɗaki na kusa da na Maryama. Cikin ruɗewa Momy ta tattaɓa jikin Maryama da aka liƙa wa drip tana barcin wahala.


"Allah sarki! Sannu Maryama. Me yake damun ta ne Annur?"


Sosa ƙeyarsa ya yi haɗe da sakin murmushi. Bin shi da kallo suka yi. Dady ya yi murmushin shi ma.


"Ah to da alama dai jika muka samu. To Allah ya raba lafiya."


Sai ma yanzu ta ƙara kallon Maryama sosai ta ga fayau ɗin da ta yi. Ta kamo hannunta ta riƙe.


"Ashe dai jika ne ke wahalar min da ƴa. To Allah ya sauƙaƙa ya rangwanta miki."


Ta ƙarisa rufe ta da blanket ɗin.


Ya sosa kansa ya ce,


"Momy to tunda kun zo bara in samu komawa gida in harhaÉ—o abubuwa. Ko bargon nan aro shi na yi wancan É—akin."


Momy ta ce,


"To shi kenan. Sai ka ɗauko kafet ɗin sallah ma. Daga nan ka biyo da flask na ruwan zafi da kayan tea. Ga shi ko girki ban ƙarisa ba na baro gidan."


Dady ya ce,


"Kin dai kashe ko?"


"Na kashe."


Ta ba shi amsa.


"Ok to da kyau. Mun yi waya da Nadrah ai ta ce wai Hanan da Janan dai sun ce nan za su dawo baki É—aya. Da suka koma É—in nan duk sai suka ji daban. Kuma babansu ya bar su."


Annur ya ce,


"Ah to masha Allahu. Ni fa dama har zan ce ya kamata Momy ta samu mai aiki haka nan. Wai ina ma asalin waccan É—in?"


Momy ta yi murmushi.


"Salman ya korar min da kaf masu aiki."


"Bari in je to Momy."


Ya tafi.


Da dare ɗakin ya cika da ƴan dubiya. Salman ma ya ɗauko amaryarsa Hadiza da kwanansu huɗu da aure yau. Baba da Mama ma sun zo tare da Hammad. Momy dama ba ta tafi ba tana nan. Sai ga Islam da mai gidanta sun zo Abdul-Ahad biye da su. Jiddah ma ba a bar ta a baya ba. Deedah ya kawo ta, saura sati biyu bikinsu. Suna nan sai ga Uncle Marwan ma da Yamaira wacce ƙaramin ciki ya fara bayyana a jikinta.


Kwananta biyu a asibitin aka sallame ta tare da ba su shawarwarin yadda za su kula da cikin sosai. Sannan kuma aka faÉ—a mata sadda za ta fara zuwa awo.


A mota shagwaɓa kawai Maryama ke sakar masa. Abu kaɗan ta kama ƙuhin kuka. Shi kuwa sai famar rarrasar ta yake yi har suka isa gida.


Cikin kwanaki biyu Maryama ta fara samun sauƙi. Annur abu kadan ya tambaye ta me ya faru? Me take so? Idan ma wurin aiki ya je to suna tare a waya, saboda ba ta koma School ba Dr. Ya ce ta bari har ta ƙara warwarewa.


Duk hidindimun bikin Jiddah babu wanda aka bar Maryama da Annur a baya. Tare suka rinƙa zuwa events ɗin ciki kuwa har da dinner. Ranar ɗaurin aure aka shafa fatiha, Jiddah ta zama amaryar Deedah, kowa ya shaida hakan. Da yamma aka ɗauki amarya aka kai ta tafkeken gidanta da ke Batagarawa lowcost, kasantuwar Deedah ya samu lecturing a jamiar Umaru Musa nan cikin garin Katsina.


Har da Maryama aka saka ango É—aki. Ta ma amarya nasiha sosai ta mata gyare-gyaren gida, misalin goma da rabi Annur ya zo ya É—auke ta.


Haka suka ci gaba da rainon cikinta kuma tana zuwa makaranta abin ta.


Ranar wata laraba da yamma naƙuda ta kama Maryama. Dama Hanan da Janan sun dawo, Hanan aka kawo mata tana kwana tare da ita. Janan kuma tana gida tare da Momy. Annur ba ya gida a lokacin. A ruɗe Hanan ta ɗauki wayarta ta kira Annur ta sanar da shi halin da ake ciki. Cikin kiɗima ya ce da ita yana hanya dama. Ta harhaɗa komai kafin ya iso.


Baby wardrobe ta buÉ—e a É—akin Maryama ta fiddo kaya uni-sex guda huÉ—u da overrole guda biyu, tunda dama duk an faÉ—a musu twince ne a cikin Maryama.


A kit ta haÉ—o da diaper da duk wani abu da za a nema. Tana gamawa Annur na isowa. Yadda ya ga halin da Maryama take ciki duk sai ya daÉ—a tausaya mata. Kamar ya mata kuka ya ji, ya kinkime ta ya kai mota, Hanan ma ta shiga motar suka kama hanyar asibiti.


Sai da suka isa sannan Hanan ta kira Momy ta sanar mata. Annur kuma ya kira gidan su Maryama ya faÉ—a.


Bayan an shiga labour room da ita su Momy suka iso. Mama ma suka iso a ruÉ—e suka haÉ—e da su Momy. Dukkansu bakin labour room É—in suka tsaitsaya suna jiran tsammani. Annur kam tagumi ya yi da dukka hannuwansa, har hawaye na zirara daga idonshi.


Ta jima tana naƙuda, kusan awa huɗu tana abu ɗaya har duhu ya fara, sannan ta haifi namiji. A take kuma ta kama wata sabuwar naƙudar. A nan ba ta wani sha wahala sosai ba sai ga ƴa mace ta haifa.


Hamdala ta saki bayan fitowar yarinyar. Da sauri É—aya daga cikin nurses É—in ta fita waje. momy da Mama har rige-rigen tambayarta suke.


"Congratulations! Ta haifi twince mace da namiji yanzu za a kimtsa su duka har da uwar. Tana cikin lafiya ita da yaranta."


Annur daga nesa ya ji maganar, aikam sajdatushhukri ya yi, yana jin farin-ciki lulluɓe da zuciyarsa. Isowar Salman da Hadiza kenan su ma suna ji suka yi hamdala ga Allah.


Take suka yita kiran ƴan uwa da abokan arziƙi ana sanar da su haihuwar. A nan suka kwana, Hanan da Mama suka kwana tare da Maryama. Mama sai fama take da ita a kan ta shayar da yaran amma turo bakinta kawai take yi wai zafi. Haka dai suka yita fama har gari ya waye.


Annur ya zo da kayan kalaci da ya karɓo daga wurin Momy. Suna cikin karyawa ma aka ba su sallama. Bayan sun gama duka suka rankaya suka koma gidansu da suka koma watanni biyar da suka gabata.


A cikin kwanakin nan shida kafin suna kullum gidan cike yake da ƴan barka. Babu wanda ba ya yaba kyawun yaran. Ga su dai jarirai amma hakan bai hana kyawunsu bayyana ba. Jidda da ta zo da ƙaramin cikinta sai famar kallon yaran take yi, ba ta ma so a karɓe su.


Daren suna da dare Annur ya nemi ganawa da Maryama a part É—insa. Bayan ta zo ya ce,


"Uwar biyu dai."


Ta sakar masa murmushi.


"Kai kuma uban biyu."


Ya shafi fuskarta.


"Na ji dai. Dama ce miki zan yi an siyo komai da kika rubuta. Maganar sunan yaran, nake neman shawararki."


"Ban gane ba."


"Ina nufin wai sunan da za a saka musu. Miye raayinki? Tun ranar da aka haife su na so na musu huÉ—uba, to kuma su dama can da sunayensu, Hassan da Usaina, amma dai daga bayan nan na ji shaawar mu musu suna kawai."


Ta sakar masa murmushi.


"Macen dai na yi mata suna."


"Namijin fa?"


"Na bar maka zaɓi."


Ta ba shi amsa hannunsa riƙe da nata.


"To wane suna kika yi mata?"


Kallon cikin ƙwayar idonsa ta yi, ta ce,


"Amrah..."


Tun ba ta rufe baki ba ya jawo ta a jikinsa cike da farin-ciki.


"Sosai raayinmu ke tafiya a tare Maryama. Haka nake fatar ɗorewarmu, komai namu ya ci gaba da tafiya tare, soyayyarmu ta ci gaba da bunƙasa. Allah kuma ya raya mana yaranmu."


Ta janye jikinta daga nasa.


"Dady kar kuma a wuce gona da iri. Jego dai nake yi."


"Ba za a wuce ba uwar biyu. Ba ki tambaye ni sunan da na zaɓa wa namijin ba"


"Sai ka faÉ—a Dady."


Ya É—an lumshe idanuwansa.


"Farouk na zaɓa masa. Na tabbata su Momy za su ji daɗi sosai. Kuma hakan ne kawai zan yi na kwatanta kyautatawarsu a gare mu. Allah dai ya sa ya miki."


"Ko bai min ba ya min Dady, bare ma kuma ya yi É—in. Allah ya raya mana little Farouk da little Amrah. Allah ya albarkaci rayuwarsu."


"Amin ya Rabb. Sai ki tafi ko kar a neme ki."


Ta miƙe ta masa bankwana sannan ta tafi.


Haka sunan ya kasance cike da farin-ciki. An ci an sha, an kuma yi nishaÉ—i. Fiddou da Mahmouda ma ba a bar su a baya ba sai da suka zo. Aunty Saddiqa ma ta zo da yaranta. Aunty Nadrah ce kawai ba ta samu zuwa ba daga Cyprus. Yamairah ma ta zo da jinjirinta mai suna Kamal. Sunan ya tara mutane sosai. Kowa ya saka ma Farouk da Amrah albarka. Sai dare sannan aka warwatse.


*


GyaÉ—a kanta ta yi cike da takaici, ta ce,


"Wai Farouk me ya sa kake da jan faɗa ne? Tun ɗazu Saddam ke kawo min ƙararka sai ka ce sharri yake yi maka. Kuma dai ga shi Amrah ta tabbatar min da kai ne ke tsokanar tasa. Ba ka jin kunya ƙaninka fa ne kuma saboda kai ya zo hutu gidan nan. Haba Farouk!"


Kunnuwansa ya kama tun kafin ya matso inda take.


"Am sorry Ammi. Ba zan ƙara ba."


Ta masa murmushi.


"Yauwa yarona. Allah ya maka albarka ka ji. Zo ka É—aukar min Baby Hoodah in shiga toilet in dawo."


Yarinyar Æ´ar kimanin watanni biyar ya É—auka. Kusan faÉ—uwa suka yi Maryama ta ce,


"Farouk bi min Æ´a a hankali ni dai."


"To Ammi."


Ya faÉ—a bayan sun fita daga É—akin.


Amrah ta yi zaune wuri guda tana duba wani littafi a hannunta. Muryar Saddam ta ji ya ce,


"Yaya Amrah me kike yi?"


Ta sakar masa murmushi.


"Saddam ina duba karatun da aka mana ne a islamiyya jiya, huruf ne. Idan na gama gwanancewa anjima sai in koya wa Farouk."


Saddam ya ce,


"Kin ji daÉ—inki ke kam Yaya Amrah."


"Kai ma za ka ji ai, musamman ma dai idan ka dage ka yi karatu sosai. Dady da Ammi sun sha ba mu labarin Amrah, asalin wacce aka saka min sunanta. Mace ce da ta zama abar alfahari har bayan rasuwarta. Har yau har gobe tarihinta na nan rubuce a ƙasar nan. Ina son zama kamar ita."


Farouk da ya iso kusa da su yana rirrigar Baby Hoodah ya ce,


"Ni ma ina miki fatar kasancewa kamar ta Amrah. Insha Allahu za ki zama ɗin, har ma ki zarce ta. Allah ya ba mu ikon riƙo da addininsa, ko kaɗan kar mu zama masu saɓa wa koyarwar ma'aiki SAW."


Annur da ke tsaye yana saurararsu duk sai ya ji yaran sun daÉ—a shiga ransa. Wayo tamkar ba Æ´an shekara bakwai ba. Kansa kawai ya gyaÉ—a bayan ya daÉ—a yin godiya ga Allah da ya albarkace shi da yaran Æ´an biyu, da kuma Hoodah mai sunan Momy Suhailah Æ´ar watanni biyar.


Ya samu Maryama ta fito daga toilet tana duba wasu takardu. Ji ta yi ya riƙo ta ta baya.


"Dady ba dai har ka dawo ba."


"Na dawo Ammi. Meeting muka yi da wasu baƙi. Sun ɗauke ni contract ne, zan musu wasu zane-zane tsawon watanni uku. Za su ba ni naira miliyan goma."


"Alhamdulillahi!"


Ta faÉ—a bayan ta rungumo shi.


"Allah ya ƙara buɗi na alkhairi Dady."


"Amin ya Allah. Salman sun dawo fa. Kin ji motsin su?"


"Ikon Allah! Wallahi ban ji ba. Kuma Hadiza ba ta kira ni ba. Allah dai ya sa sun yi nasara."


Shiru ya yi kafin ya ce,


"Ba su yi ba Maryam. Wai likitan ya ce bai ga wata matsala a tattare da duka biyun su ba. Lokacin haihuwar ne dai kawai bai yi ba. Daga can ma suka wuce saudiyya suka sake yin addua."


"Ehh Hadiza ta ce min dama Saudiyya suka wuce. To Allah dai ya kawo musu mai albarka."


"Amin. Saddam dai ya saba sosai da su Farouk."


"Wallahi fa. Ko É—azu Jiddar ta kira ni wai ya Saddam dai ba ya mana kuka ko? Na ce da ita ko kaÉ—an. Don ma dai Farouk na tsokanarsa ne. Amma dai na masa nasiha insha Allahu ba zai kuma ba."


"To madalla. Fiddou ma wai ta sake haihuwa. Gama wayata da Mahmoud kenan na shigo gidan ma."


Ta zaro ido.


"Lallai Fiddou. Haihuwa ta uku fa kenan. To Allah ya raya mata su bisa sunnah."


"Ameen ya Allah. Ya ce wai ni aka yi wa takwara. Annur."


Ta ji daÉ—i sosai.


"Aikuwa Dady dole mu daure mu je barka sannan kuma mu koma suna. Sun yi ƙoƙari sosai wallahi."


"Allah da gaske sun yi ƙoƙari?"


Ta É—aga kanta.


"To sai ke ma ki min ƙoƙari yanzu, ki saukar min da gajiyar nan."


Harara ta maka masa.


"Su kuma yaran da ke waje mu yi yaya da su?"


Ya taɓe bakinsa.


"Ke ni fa

Please Login or Register in order to submit comment