You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka buÉ—e mana fuskokin namu, suka shigar da mu wani babban gida. A nan muka ga jerin mata birjik, wasunsu a cikin damuwa, wasu kuwa hankalinsu kwance suke hidimar gabansu.


A wannan gidan muka ci gaba da zama, har tsawon wata É—aya. Kwatsam cikin wani dare aka kawo ma Æ´an ta'addar hari, sojoji da gwamnati ta turo, kuma suka gano daji da gidan da muke.


Wannan sojojin ne suka fitar da mu, suka dawo da mu a cikin garin Maiduguri, cewa daga nan kowa ta nemo asalin gidansu ta koma.


A nan tashin hankalina ya sake ninkuwa. Tuna ƙarar bomb ɗin da ya tashi a kangon da Aunty suke, da kuma fitar Yaya Salman bai dawo ba, ga uwa uba wayar ƙarshe da Yaya Salman ya yi da Abbu, ya ji sautin bindiga. Na ɗora hannuna a ka, na rasa uwar ubana. Damuwa ta bi ta dunƙule a cikin zuciyata.


A nan inda nake tsaye na ji an taɓa ni, na juyo don ganin mai taɓa nin, sai na ga wata budurwa wacce ba za ta wuce sa'ar haihuwata ba.


"Ki yi haƙuri kin ji. Dukkan tsanani yana tare da sauƙi."


Ta faÉ—a cikin sassanyar muryarta. Na ce,


"Ban san sadda nawa sauƙin zai zo ba."


Ta murmusa,


"Duk daren daÉ—ewa zai zo gare ki."


"Ina fatar hakan."


Na faÉ—a cike da damuwa.


"Zama a nan bai kamace ki ba a matsayinki na Æ´a mace. Ki zo mu je gidanmu."


Ban musa mata ba, saboda ko yawan magana ba na so. Na bi bayanta. Gaban wata danƙareriyar mota muka isa, aka buɗe mata baya, ta shiga haɗe da ba ni izinin shiga ni ma.


Bayan mun isa gidansu ta sa na yi wanka, ta kawo min kayanta na saka. Ko da na gama shiryawa an jera min tarkacen abinci a gabana. Na yi mamakin yadda cikin daren nan aka iya haɗa liyafar abinci kamar wannan. Kaɗan na ci na ce na ƙoshi. Na kwanta barci. Nan fa damuwa ta sake ninkuwa, na nemi barci na rasa. Sai kuka da tunanin rayuwata da nake yi.


A gidan su Ummi na ci gaba da rayuwa har tsawon watanni biyu, sannan ta ce min hutunta ya ƙare ita kam, za ta koma makaranta. A nan kuma hankalina ya kuma tashi. Na ce da ita zan koma Bama in binciki dangi da iyayena, ta ce ina, ai har yanzu akwai sauran tashin hankali a garin. Na kartake cewa sai na je, ta haɗa ni da mahaifanta. Da yake mutanen kirki ne, suka lallaɓa ni kan cewa in haƙura har a samu kwanciyar hankali a garin, duk da dai da sauƙi ba kamar da ba. Kalamansu masu daɗi suka siye min zuciya na haƙura. Kuma suka ce idan ina ga kamar zaman gidan ba zai min daɗi babu Ummi ba, sai in bi ta makaranta.


Tare aka mana siyayyar dawowa duk da ni ba ɗaliba ba ce. A nan Al-Qalam University. Tare muka ci gaba da rayuwa, a lokacin da na cika watanni uku a garin ne Allah ya haɗa ni da Alhaji Marwan, har muka fara soyayya da shi. Sadda hutun first semester ya ƙare na su Ummi, muka koma gida hutu, na gabatar da Alhaji Marwan a matsayin wanda zan aura. Abii ya ce ya zo ya same shi su yi magana, tunda dai har na amince zan aure shi.


Kin ji yadda komai ya faru. Kuma tun daga wannan lokacin muka koma Bama tare da Ummi da iyayenta da kuma Alhaji Marwan, muka tarar iyayena babu su, sai dai wasu daga cikin danginmu, wanda suka ɓuya. Amma mafi rinjaye duk an karkashe su basa raye.


Sosai Abii ya yi bincike game da Alhaji Marwan, tamkar Æ´arsa da ya haifa haka ya yi É—awainiya da ni, ya aurar da ni ga Alhaji Marwan. Ga shi har da tukuicin Yesmeen, wacce na saka ma sunan mahaifiyata, Shereefah."


Cike da mamaki Maryama ke kallon ta. Tausayinta take ji sosai, sai dai tsabar al'ajabi da labarin ya gama ba ta.


Da ƙyar ta samu ta tattaro magana ta haɗa, ta ce,


"To amma bara na miki wata tambaya Maman Yesmeen. Yaya Salman É—in naku Æ´an biyu ne asalinsa ko kuwa dai shi kaÉ—ai ne aka haifa?"


Yamaira ta ce,


"Aunty ta faÉ—a mana wai twince ne, amma wancan É—in ana haihuwarsa ya rasu..."


Tun ba ta rufe baki ba Maryama ta miƙe tsaye. Sai yanzu hasashen nata ya tabbata. Kanta ta dafe, tana jin tunani kala da kala a cikin zuciyarta. Ta ma rasa abun yi, ganin komai take tamkar a mafarki.


"Ta faru ta ƙare! An yi wa mai dame ɗaya sata."


Ta furta tana fifita da tafukan hannayenta duka biyun, saboda wani irin gumi da ta ji yana tsattsafo mata.


"Kenan dai Yah Noor ba su Momy ne suka haife shi ba?"


Shi kanshi Alhaji Marwan zancen da yake kenan a zuciyarsa. Ya cire hular kansa yana fifita da ita.


Dawowa ta yi ta zauna Maryama. Cikin kuka ta ce ma Yamaira,


"Wannan ba shi ne ainahin Salman yayanki ba..."


"Don't tell me rubbish! Ta ya za ki ce min wai ba yayana ba ne, bayan kuma ina a cikin hankalina?"


"Duba shi da kyau Yamaira. Na tabbatar da dole koma ƙaƙa ne akwai abin da za a iya samu bambanci nasu. Sannan kuma wannan ma ba shi da hankali fa."


Yunƙurin miƙewa zaune ta yi ta kasa. Maryama ta taimaka mata ta tashi zaunen, ta zuba ma Annur idanuwa.


Da ƙyar ta iya gano wata tawada da take a fuskar Salman wacce ta nema ta rasa a fuskar Annur. Ta jima tun suna yara tana masa zancen tawadar, har wata rana yake ce mata da yana da yadda zai yi ya cire ya ba ta ita da ya yi, sai dai kuma babu hali. Ba kowa ba ne zai iya kula da ita, saboda ta kusa da wuyansa take, ita ma saboda tun suna yara ne ya sa ta iya fahimta. Yanzu kuwa ta darara idonta sosai babu ita. Sannan kuma kamar fuskar wannan ɗin ta fi walwala fiye da ta Salman. Duk da ba wai dariya ya yi ba, amma daga yanayin yadda yake za a iya sanin cewa mutum ne shi mai faraa fiye da Salman.


"Na tabbata a shirun nan da kika yi kin gano bambancinsu, ko da kuwa kaÉ—an ne."


Kai ta É—aga mata cike da mamaki. Kafin ta buÉ—i baki ta ma Maryama tambaya ita ta riga ta yin magana.


"Kenan dai Æ´an biyu ne..."


"Amma kuma ai aunty ta ce mana gudan ya rasu."


"Duk ma dai yadda za a yi Æ´an biyu ne Yamairah. Salman É—in ku shi ne Sans. Ko?"


"Ehh. Aunty ta saka masa wannan sunan, saboda É—an fari ne. Please yana ina yanzu?"


"Yana gidan su wannan..."


Ta gwada mata Annur da hannu.


"Gidan su yayan Uncle Marwan."


Ta ƙwalalo ido.


Kai Alhaji Marwan ya jinjina mata.


"Ku faÉ—aÉ—a min maganar."


Ajiyar zuciya Maryama ta sauke. Ta labarta mata kaf abin da ta sani, tun daga farko har ƙarshe.


Ta É—ora hannunta a ka,


"Yaushe Yaya Salman ya zama riƙaƙƙen mashayi? Yaushe ya zama mazinaci ban sani ba? Ba halinsa ba ne, wallahi ƙaddara ce ta miyar da shi haka. Yaya Salman ɗina mutum ne mai tsoron Allah. Mutum ne mai ilimin addini, da sanin hukunce-hukuncensa."


Ta kuma sakin wani kukan.


"Ni yanzu mamakin da nake yi, ta yaya Annur ya dawo hannun su Yaya IA? Ina nasu É—an da suka haifa yake?"


"Ni kaina ina son sanin hakan. Amma kam alamu sun tabbatar cewa Yah Noor ba É—an su Momy ba ne. Twin brother É—in Salman ne, yaya ga Yamairah."


"Tirƙashi!"


Alhaji Marwan ya ambata a fili.


*


Ƙarfe biyu da rabi Hanan ta gama haɗa komai ta jera a dining. Ta nufi ɗaki ta samu Janan ta yi wankanta ta cancaɗa kwalliya, ta saka doguwar rigar roba amma ba mai bin jiki ba. Ta tasa waya a gabanta tana ta famar yin selfie.


Hanan ta gyaÉ—a kai.


"Sannu da aiki Hajiya Janan."


Ta kanne ido haÉ—e da karkace baki ta É—auki wani hoton, sannan ta ce,


"Yauwa ke dai Æ´ar albarka..."


Ta sake karkace baki ta É—auki hoton. Hanan ta yi dariya sannan ta nufi toilet ta yi wanka.


Tana fitowa ta kimtsa cikin riga da skirt na atamfa da Momy ta siya mata. Saboda ita kam tana son native dresses, duk da cewa ba a ƙasar Hausa suka tashi ba. Ta feshe jikinta da turare sannan ta fice daga ɗakin.


Fira suka yi da Mony sama-sama har aka fara kiran la'asar Momy ta je ta gabatar da tata. Tana dawowa suka jin horn alamar su Dady sun iso. Aikuwa ihu Hanan ta yi haÉ—e da ficewa a guje domin tararsu. Janan ma daga É—akin ta fito tana yin video ta snap chart har ta kusa kai ma Momy karo sanann ta farga.


"Idan ba ki ajje wayar nan ba sai na faffalla miki mari."


"Tuba nake ranki ya daÉ—e."


Ta É—ora wayar bisa hannun kujera sannan ta bi bayan momy suka fice waje.


Sosai suka yi farin-ciki ganin yadda Sans ya warware kamar bai taɓa jin ciwo ba. Kwana ashirin ba wasa ba. Suka rankaya zuwa falo.


Ya jiki suka hau yi masa yana amsa musu da walwala. Kafin suka rankaya zuwa dining table É—insu mai kujeru shida, suka jera. Hanan ce ta yi serving É—insu, cike da farin-ciki da jin daÉ—i suke cin abincin, Janan na ta famar surkullenta da ta saba.


Sai da duk suka ƙoshi sannan suka watse. Momy ta buƙaci ganawa da Sans domin ta masa nasiha.


Bedroom ɗinta suka nufa. Nan ta hau yi masa faɗa cikin ruwan sanyi take tafasa shi. Ta masa nasihu masu ratsa zukata, sannan a ƙarshe ta masa addua, haɗe da ba shi izinin tashi ya tafi zuwa ɗakinsa.


Wanka ya watsa sannan ya É—auro alwalla. Bayan ya gama sallah bai sauka daga bisa kafet ba sai da ya yi istighfari sosai, yana mai tsananin nadama. Sai dai fa damuwar nan É—aya tana nan addabe da zuciyarsa. Tararrabin ranar da asirinsa zai tonu yake.


***


*To mutanena...an zo wurin fa. Wasu sun ce wai bakin Amrah ya gwanance da faɗin an zo wurin😀 to ba bakinta ba ne. Alƙalamin ne ya saba da faɗar an zo wurin, kuma saboda an zo ɗin ne ya sa yake rubutawa...lol🤣*


*Me za ku ce game da wannan shafin?*


*Na warware muku sirrin auren Yamaira da Alhaji Marwan? Kun ga ta yadda rayuwarta ta dawo Katsina? Kun ga yadda ta kuɓuta daga hannun ƴan ta'adda?*
*Idan har kun gani da gaske kuma kun gode, I need more comments here.*


*Ita kuma ƙawata Janan da ta ɗauki diary, ta kuma rantse sai ta karanta, ko ya abun zai kaya?*
*Da gaske ina son Janan, ina ma dai za ta yi ƙawance da ni🤣😀*


*Tafiyar tamu tana ta gangara. Sannu a hankali alƙalamin ya kusa sauka. Insha Allahu.*


*Masu mutunci sannunku da aiki, sannunku da jimirin kankaro shi. Aikinku na kyau. Keep it up durlings.*


Thanks all.


Pinky durling💞
RAZ 2
[9/24, 11:51 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taɓa zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_




Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*




7⃣0⃣


Wattpad: PrincessAmrah


***


Sai da ta sha ruwa sannan Alhaji Marwan ya ce da ita ta tashi su tafi, cewa gobe za su sake dawowa su É—auki Maryama da Annur É—in, sai su gana da Dr. Hamdan a gidansa.


Har gaban motarsu Maryama ta raka su, sannan ta dawo dafe da kanta, har yanzu al'ajabi bai kau daga zuciyarta ba. Tunanin yadda rayuwar Annur ta dawo a gidan su Momy kawai take, da kuma yadda aka yi aka ce wai Annur ɗin ya mutu a lokacin da aka haife sa. Ajiyar zuciya ta sauke, sannan ta ce da Annur ya tashi su nufi sallah, saboda tuni aka kira magrib ɗin. Tashi ya yi suka tafi jiki babu ƙwari, shi kanshi kallo guda za ka masa ka tabbatar cewa ba ya cikin walwalarsa.


*


A hankali ta leƙa fuskar Hanan, ta tabbatar da ta yi barci sannan ta ɗaga pillow ɗinta ta jawo diary ɗin Sans. Buɗewa ta fara yi, anan ta ga head line na Bama da kuma exact day na ranar da ƴan ta'adda suka fara kawo musu hari. Tun daga harbin da ya ji an ma Abbunsu, izuwa fitarsu daga gida, suka zauna a kango, har tafiyarshi zuwa siyar da wayarsa bai bari ba. Duk abin da ya faru a wannan ranar har komawarsa Maiduguri da motarsu da ta lalace a hanya, dawowarsu bayan ya siyo musu, harbin ƙafarsa da aka yi abinci duk ya rubuta.


Ta dafe kanta cikin mamaki. Tunani ta fara yi kodai ba na Uncle Noor É—insu ba ne? Sai dai kuma hotonsa da ta gani a next page ya tabbatar mata da cewa nasa ne. Amma kuma a ina ya samu suna Salman (Sans)? Tambayar da ta gaggauta yi wa kanta kenan. Ba ta kai ga samun amsarta ba ta buÉ—o shafin gaba. Nan kuma duk abin da ya faru washe gari ne a rubuce. Mutanen da suka zo suka tsotse man motarsa suka tafi da shi Maiduguri, kai shi asibiti da suka yi, zaman da ya yi a can har ranar da aka sallame shi.


A wannan gaɓar hawaye sosai Janan ke yi, mamaki bai gushe daga saman fuskarta ba. Ta sake buɗo wani shafin, sai ta ga hoton Sans ɗin wanda yake a cikin yanayi na damuwa. Daga ƙasa an rubuta


"Tun daga lokacin da na zama gurgu na tsani kaina, na tsani komai nawa. Kamar yadda fuskata babu annuri a wannan hoton, to haka na kasance tun sadda aka naƙasa min ƙafa."


Ta matse ƙwallarta, haɗe da buɗo next page. A nan kuma tafiyarsa ce daga Maiduguri har zuwa Katsina. Ƙalubalen da ya fuskanta a tafiyar, da kuma bawan Allah'n da ya haɗu da shi a mota wanda har ya saya masa abinci. Isowarsa tasha da fizge masa kuɗin da aka yi sadda yake kan keken guragunsa.


A shafin gaba kuma haɗuwarsa da Farouk Sardauna ne. Silar haɗuwar tasu da kuma taimaka masa da ya yi ya kai shi gidan gonarsu. Ta sake buɗo wani shafin, sai ta ga hoton Bobby wanda ya saki kyakkyawan murmushi a ciki, daga ƙasa an rubuta,


"He always smiles. He helped me, and never forget him in my mind. Ina fatar ranar da Allah zai kawo min hanyar da zan rama taimakon da ya yi min, ko da kwatankwacin wanda ya min É—in ne."


Ta buÉ—o wani shafin. Date da time ne duka a rubuce na ranar da ya fara shan kayan maye. Ya rubuta,


"Ba na so, amma damuwa da ta yi min yawa ta sa na fara. Na kuma ji daɗin hakan, saboda ban ƙara shiga cikin damuwar rashin dangina ba tun daga sadda na zama drug abuser."


ShessheÆ´ar kukanta ce ta tada Hanan. Cikin magagin barci ta yi firgigit ta buÉ—e idanuwanta.


"Janan whats wrong with you? Why are you crying?"


Ta yi saurin ɓoye diary ɗin, ta share ƙwallarta.


"Its nothing."


Ta ƙirƙiro murmushi. Zaune ta miƙe Hanan. Ta ce,


"There must be something wrong, Janan. Ke É—in nan da ba kya kuka, amma look at your face, tears sun gama wanke cheeks É—in ki. Janan kina da wacce ta fi ni ne?"


Ta gyaÉ—a kanta.


"To me ya sa za ki ɓoye min damuwarki? Mene ne kike ɓoyo da wancan hannun?"


Ƙarfafa kukan nata ta yi Janan, ta ce,


"Hanan akwai damuwa fa, damuwa mai girma. Uncle Noor..."


Ta kwashe duk abin da ta karanta ta sanar da ita, tare suka ci gaba da jimamin cikin kuka, sannan suka ci gaba da karantawa.


Abin da ke gaba rubuce shi ne haɗuwarsu da Annur mahaukaci a daji, da kuma ɗaukarsa suka miyar zuwa gidan gonarsu. Tafiyarsa ya haɗu da foster da ake cigiyarsa, sauya kayan Annur zuwa jikinsa, aske gashin kansa zuwa irin na kan Annur, yadda aka yi ya dawo gidan lokacin da Bobby ya kawo shi. Duk babu abin da ya ɓoye a diary ɗin.


Kallon junansu suka yi, sun kasa tsayar da hawayensu. Mamaki bai gushe daga zuƙata da fuskokinsu ba. Hanan ta yi sauri ta buɗo shafin gaba.


Aikin da boka ya musu ne a farkon shafin, yadda aka jiyar da hankalin kowa, aka kasa ganin ko ɗison bambancinsa da Annur, da canjin aikinsa a kamfanin Dady daga mai zane zuwa ga CEO, rabuwa da abokan ainahin Annur, shaƙuwarsa da Bobby kaf sai da ya zana.


"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!"


Hanan ta faÉ—a hannunta a ka.


"Why did you do this? Me ya sa za ka yaudari su Dady? A ina ka kai mana Uncle Noor É—inmu?"


Kalaman da ke fitowa daga bakin Janan kenan cikin kuka. Suka sake buÉ—e wani shafin.


Haɗuwarsa da Maryama ne a jiki, ranar da daga kallo ɗaya ya fara ƙaunarta, faɗan da Dady ya masa a kan fara rugujewar company saboda sakacinsa, zuwansa wurin boka ya masa faɗa a kan true love, aikin da aka masa aka cire masa ƙaunar Maryama, duka ya rubuta.


Shafin gaba kuma damuwar da ya fara shiga lokacin da Farouk Sardauna ya fara ciwo ne. Farkon zuwansu likita da kuma gargaÉ—in da aka musu game da smoking. Tsanantar ciwon Bobby, da kuma damuwar da suka shiga sosai na ciwon nashi.


Next page hotonshi ne ya dafe goshinsa yana kuka sosai, a ƙasa ya rubuta


"Unforgetable day, the night that my best ever friend gone, and gone forever"


Da date da komai na ranar, ya kuma rubuta irin raÉ—aÉ—in da zuciyarsa ta shiga.


Suka sake buɗe wani shafin, alƙawarin da ya ɗauka na daina smoking da duk wani mugun hali ne a ciki.


Suka kalli juna cikin kuka sosai, duk da sun ji haushinsa daga farko, amma a nan sai suka fara tausaya masa. Bai kyauta ba abin da ya yi, amma idan aka yi la'akari da jalalar rayuwa da ya gani a baya, dole a ji tausayinsa. Suka sake buÉ—e wani.


Alƙawarin Bobby da ya so cikawa ne a jiki, sai dai hakan bai samu ba, ya haƙura da Maryama har abada.


Shafi na biyun ƙarshe suka buɗe, hoton shi ya duƙar da kansa ƙasa, ya rubuta,


"Hukuncin ƙarshe da zuciyata ta yanke min."


Suka buɗo shafin ƙarshe, wanda ya rubuta,


"I've decided to kill myself. Na so na taushi zuciyata, amma abun ya gagara. A lokacin da nake yin wannan rubutun, kuka nake sosai, na yi shi ne musamman domin duk wanda ya yi farko a karatun diary ɗin nan ya tabbatar cewa ba haka kawai Salman ya so kashe kansa ba. Rayuwar ce ta juye masa baki ɗaya. Farin-ciki ya ƙaurace masa. Ina roƙon duk wanda ya fara karanta diary ɗin nan, ya samu Dady da Momy cikin nutsuwa, kar ya tayar musu da hankali, sannan ya ba su su karanta. Idan kuma a cikin Dady ko Momy ne suka fara karantawar, ina mai roƙon gafararku, ku gafarta min na basajar da na muku, na zauna da ku a matsayin ɗanku da kuka haifa. Na gode ƙwarai da tarayyata da ku, ku ɗin mutanen kirki ne, wanda samun kamarsu a daidai wannan lokacin zai yi matuƙar wahala. Ɗan ku Annur yana raye, sai dai an masa kurciya, da ko ni kaina ban san inda yake ba yanzu haka. Please forgive me, once again."


Ya saka full stop a daidai nan.


Rungumar junansu suka yi su duka biyun, kuka sosai suke yi, suna matuƙar jin daɗi da Allah ya sa Sans ɗin bai mutu ba. Duk da abin da ya aikata, suna son shi a hakan, matsayi da darajarsa kuma suna nan a cikin zuƙatansu.


Rufe diary É—in Janan ta yi, babba ne kamar girman photo album, sannan ta ajje a gefenta.


"Duk da kuskuren da ka tafka ka ba ni tausayi."


Hanan ta faÉ—a. Janan ta ce,


"Mu bari har da safe sannan mu kai ma su Momy su karanta ko?"


Hanan ta ce,


"Janan tunda dai bai mutu ba mu yi haƙuri mu binne maganar nan, ba mu san kalar hukuncin da su Dady za su ɗaukar masa ba. Kin ga ya ce idan aka kore shi daga nan bai san inda rayuwarsa za ta faɗa ba.


"Dole za a faɗa musu, Hanan. Idan har muka yi shiru to Allah zai iya kama mu da laifin yaudara. Na san halin Dady, kamar yadda na san halin Momy. Na tabbatar cewa ba za su ƙi shi ba. Za su masa uzuri, sannan kuma za su tashi tsaye neman Uncle Noor."


Hanan ta yi shiru, kafin ta ce,


"You are right Janan. But ni dai I can't tell them. Wallahi ba zan iya sanar da su ba, don ban san halin za su shiga ba bayan sun ji."


"Ni zan sanar musu, yanzu ma ba sai gari ya waye ba."


Hanan ta riƙo ta,


"Janan me kike shirin aikatawa a cikin daren nan? So kike yi ki hana su barci?"


"Hanan please let me tell them. Da safe kuma idan ya shigo ta yaya zan iya faÉ—a musu a gabanshi?"


Shiru Hanan ta yi kawai ta koma ta kwanta. Damuwa lulluɓe da zuciyarta, zullumi da fargaba take tsananin ji.


Ta sauka daga bisa gadon, haÉ—e da nufar É—akin Dady.


Knocking ta yi a hankali ta ji shiru, hakan ya sa ta ƙara yi.


"Waye?"


Ta ji muryar Dadyn ya faÉ—a.


"Janan ce Dady."


"Lafiya?"


Ya ce bayan ya buɗe mata ƙofar ido a buɗe. Diary ɗin hannunta ya kalla.


"Me ya faru?"


"Dady akwai matsala."


Ta share hawayen da ya kuma sauko mata. Ya kunna wutar É—akin sannan ya kama hannunta zuwa bakin gado. Motsinsu ya sa Momy ta buÉ—e idanuwanta, tana ganinsu ta gaggauta murtsukar idanuwan haÉ—e da tashi zaune tana tambayarsu abin da yake faruwa.


"Ni ma kaina ban sani ba Suhaila. Shigowarta kenan É—akin tana kuka."


"Subhanallahi! Janan ba ki da lafiya ne?"


Ta gyaÉ—a kanta.


"Whats your problem? Where is Hanan?"


"Tana É—aki."


Ta miƙo ma Dady diary ɗin.


"Dady I want you to please read this. Amma don Allah ba na so ku tashi hankalinku. Shi al'amarin Allah duk inda kake ba ka tsallake shi. Ku ɗauka a zukatanku cewa wannan ƙaddararku ce, kuma dole sai ta faru da ku."


Cikin mamaki da kiÉ—ima Momy ta ce,


"What are you saying, Janan? Me ke a cikin littafin?"


"Ku karanta Momy. And calm down, idan ba ki nutsu wurin karatun ba ba lallai ki fahimci wabi abu ba."


Ta miƙe da kuka ta bar ɗakin haɗe da jawo ƙofar ta rufe.


*


WASHE GARI


Da sassafe ta tashi kamar kullum, ta nufi kitchen. Dankali ta fere ta yanka sannan ta tsane a kwando ta barbaɗa gishiri. Ta ɗora mai a kasko bayan ya yi zafi ta zuba dankalin. Tarugu da albasa ta yi grating sannan ta yayyanka hanta ƙanana-ƙanana. Ta zuba hantar a pan da ruwa kaɗan, ta saka kayan ƙamshi da albasa da maggi. Bayan ta dahu da zuba mai kaɗan a ciki ta soya sama-sama, ta juye tarugun a ciki ta hau suya. Ba wani soyuwa sosai ta yi ba ta zuba maggi da curry, sannan ta fasa ƙwai guda ɗaya a ciki ta hau juyawa. Bayan ta soyu ta juye a ƙaramin bowl, sannan ta kwashe dankalin saboda wuta kaɗan ta saka dana don kar ya soyu da wuri har sai ta gama sauce ɗin. Plate mai ɗan faɗi ta juye dankalin a ciki, ta nemi foil paper ta lulluɓe shi da bowl na sauce ɗin sannan ta kwasa ta kai dining. Electric water flask ta jawo daga jikin socket ta ɗora a table ɗin. Ta buɗe dining carbinate ta haɗo komai sannan ta nufi ɗaki.


Ta samu Annur har ya gama shiryawa cikin ƙananan kayan da ta ajje masa. Sai famar zuba ƙamshi ɗakin yake yi, ya yi zaune ya ƙura wa wuri ɗaya ido. Magana ta masa har sau biyu bai ji ba. Ta tafa hannu a daidai fuskarsa ya zabura.


"Mi amor."


Ta É—an cunno bakinta bayan ta zauna kusa da shi.


"Ka sha kyau sosai."


Ya yi murmushi.


"Tunanin me kake?"


Dariya kawai ya sakar mata, ya yaƙe duka bakin nasa.


"Anyways, lets go and have a break fast."


Ta ɗora tafukan hannayenta, shi ma ya ɗora nashi a kan nata. Tare suka nufi dining area ɗin. Dama ta yi wankanta, ta saka ƙananan kaya riga da wando amma rigar mai ɗan tsayi ta kai guiwa. Bayan sun zauna ta hau ba shi a baki, sannan ita ma ta ba kanta. Da haka har suka ƙoshi.


Saƙale da hannu suka dawo falo. Ta kunna kallo sannan ta nufi bedroom ta ɗauko wayarta. Tana dubawa ta ga missed call na Dr. Hamdan Ramat. Ta iso falon daidai sadda take latsa kiransa tana Allah-Allah ya ɗauka.

Please Login or Register in order to submit comment