You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai kwalbar, bai sauke ba har sai da ya shanye ta tas, har yana suɗar baki-bakinta. Ya ajje ƙasa, yana mai kallon yadda Bobby ke sakin murmushin jin daɗi.


Tun daga wannan lokacin ne Sans ya ƙware a harkar, har ma ya nemi ya zarce Bobby. Suka ɓaci kuma da mugun son mata, da neman mata. Har a gida ake kawo musu matan. Yax da Esien ne suka koma tuƙin napep, duk don su ringa kawo ma su Sans mata suna musu fyaɗe. Idan sun yi fyaɗen kuma sai su sa su kai su can su yar, duk sadda suka farfaɗo su nemi hanyar tsira.


Da wani yammaci ne, daidai irin ƙarfe shida na yamma, babban titin ring road babu kowa a kai, babu giccin ko babur bare mota.





Bobby na tukin mota sai Sans kujerar zaman banza. A tsayin wannan lokacin kam sosai Sans ya ji sauƙi. Baki ɗaya ya ma daina hawa kujera, saboda kyakkyawar kula da ya ringa samu daga wurin wannan nurse ɗin da ke asibitin Turai.


Man motarsu ne ya ƙare, hakan ya sa Bobby yai yai ya tada motar amma ta ƙi tashi.


"Oh Gosh! Guy man motar nan fa ya ƙare."


Cikin takaici Sans ya ce,


"Damn it! A tsakiyar dajin nan da babu giccin kowa ne mai zai mana haka?"


"Ka dai gani ai."


"Guy wats the solutuon?"


"Don't really know abokina. Sai dai ko in kira Yax ya ɗauko jarka ya siyo ya kawo mana. Idan ba haka ba za mu shekara a nan, ba tare da kowa ya gitta ba. Kuma ga shi Saleem ya ce zuwa magrib za ka koma. Likitan ƙashin ya zo. Duk da dai ka samu sauƙi sosai, amma dai yana da kyau a ƙara tabbatar da lafiyarka."


"Haka ne. Just give him a call to. Allah sa akwai kuÉ—i a hannunshi."


"Ameen."


Bobby ya faɗa, haɗe da zaro wayarshi daga jikin chaji yana mai ƙoƙarin kiran Yax ɗin.


Kusan mintina arba'in suka É—auka a wurin, kafin Yax ya iso, suka fita da nufin zuba mai a motar.


Wani mahaukaci ne suka gani yana tinkaro inda suke, hakan ya sa suka firgita su duka, suna ƙoƙarin guduwa saboda yadda yake ƙara tinkaro su.


Duhu ya fara a daidai lokacin, sai hasken wayoyinsu da suka dalle mahaukacin, wanda ya iso daf da su.


Ido buɗe suke ƙare mishi kallo su duka ukun, kallon yadda kamanninsa suka zo ɗaya da Sans, babu ko bambanci.


Sake kallon Sans suka yi Bobby da Yax, sannan suka sake dalle mahaukacin, don su sake tabbatarwa. Shi kanshi Sans ɗin mamaki yake. Tunda yake a rayuwarsa bai taɓa ganin tsananin kama irin wannan ba.


***


Misalin ƙarfe sha biyu na dare ne Mama na zaune falo ta ji sallamar mace. Amsa sallamar ta yi tare da ba ta izinin shigowa cikin falon.


Bayan ta zauna ne suka gaisa, duk da cewa Mama ba ta san matar ba, amma hakan bai hana ta sakar mata fuska ba.


"Ya su Maryama? Ko ana makaranta?"


"Maryama na É—aki. Maryama!"


Mama ta ƙwala mata kira.


Da hanzari Maryama ta share hawayen nata, sannan ta fito cikin wani taku a nutse, da mutuwar jiki a tattare da ita.


Murmushi ta saki a lokaci guda ganin wacce ta zo É—in, zaune bisa kujera.


Bayan ta ƙarisa shigowa ɗakin ta zauna ƙasan matar, haɗe da faɗin,


"Umma ashe ke ce."


Ta saki sassanyan murmushi.


"Ni ce fa da kaina Maryama. Kin gan ni da rana tsaka ko? Ya na same ku?"


"Lafiya lau Umma."


Maryama ta juya ga Mama, ta ce,


"Mama ita ce Umman Amrah. Dama na faÉ—a miki za ta zo ai."


Faraa sosai a fuskar Mama ta ce,


"Allah sarki! Ai ban gane ki ba."


Umma ta ce,


"Haka ne. Ko ranar walimarsu ba mu samu damar gaisawa ba. Yau ai ga ni na zo har gida."


"Mun kuwa ji daɗi ƙwarai da gaske."


Mama ta fada. Ta kalli Maryama ta ce,


"Maryama kawo mata drink ko. Abinci ma na daf da sauka ai."


Bayan Maryana ta miƙe ta ce,


"Ehh Mama. Miya ce kawai ba ta ƙarisa dahuwa ba. Bara na kawo drink ɗin."


Ta doshi hanyar Kitchen, tana mai jin wata nutsuwa sosai a tattare da ita. Damuwar da take ciki na É—an raguwa, duk da dai akwai ta É—in fanjam a cikin zuciyarta.


Lemon five alive na roba ta sako guda biyu a plate, sannan ta É—ora cup a kai, ta nufi dawowa falon.


Fira ta tarar Mama da Umma suna yi, tamkar dama can sun san junansu.


A gaban Umma ta ajje, sannan ta koma kan kujera ta zauna, tare da faÉ—in,


"Umma don Allah ki sha lemu kafin a gama abinci."


ÆŠaukar lemun ta yi Umma, ta fasa ta zuba kaÉ—an a kofi ta sha. Bayan ta shanye ne ta ce,


"Ina Annur É—in yake?"


"Yana can É—akin. Mu je ko?"


Maryama da Mama suka miƙe, Umma ma ta miƙe.


Sai da ta fara rufo ƙofar falon don kar a bar shi haka babu kowa, sannan suka nufi ɗakin da Modu yake, Maryama a gaba sai su Umma biye da ita.


A zaune suka same shi, yana ta faman jeren alphabets, sai ha haÉ—a sunan Amrah da Maryama ta koya mishi, sannan ya haÉ—a sunanshi, sai kuma na Maryama a gaba.


Kallonshi Umma ke yi cike da mamaki. Tabbas babu ko tantama Annur ne wannan. Real Annur, na Amrah.


Ido buɗe suka ƙarisa shigowa cikin ɗakin, suna kallonshi.


Ganinsu da ya yi ne ya sa Modu murmusawa, yana faÉ—in,


"Maryama kin gani na iya? Kalla ki ga. Ga Amrah, ga Annur, ga ki."


Ya saki murmushi yana gwada musu jeren da ya yi.


Idonshi bai ankare da Umma ba har sai sadda Maryama ta mishi nuni da ita. Take gabanshi ya hau faÉ—uwa, ya ringa nuna ta da yatsa, bakinsa ya gaza furta komai.


'Hakan na nufin ya gane Umman Amrah kenan?' Maryama ta tambayi kanta. Da alama ana samun nasara, ana samun ci gaba sosai. Tunda ga shi har ya fara tunowa da wasu abubuwa na rayuwarshi. Ya fara tunowa da wasu mutanen da suka dangance shi.


"Ka san ta ne?"


Maryama ta gaggauta tambayarshi, tana ƙura masa dukkanin idanuwanta.


"Ni ma ban sani ba. Kin san ni?"


Ya tambayi Umma.


"Ƙwarai da gaske kuwa Annur, na san ka, farin sani ma kuwa. Ni ce Umma, Umman Amrah. Ka tuna ni?"


Dafe goshinsa ya yi alamar tunani, kafin ya ce,


"Idan kin san ni to ni ma na san ki."


Ya saki dariya har da tafa hannuwa.


Dariyar suka yi su É—in ma. Amma dai duk da haka akwai alamun ya É—an tuna ta, ko ma dai yaya ne.


Sun jima a É—akin Umma na masa firar Amrah, da surkulle da sokana dai yake É—an amsa mata, wasu abubuwan kuma idan ya yi tamkar mai hankali, sai dai kuma a take sai sako shirme, wanda zai tabbatar da cewa shi É—in mahaukaci ne ba mai hankalin ba.


Miƙewa Umma ta yi, ta ce,


"Bari in ƙoƙarta tafiya, lokacin dawowar Mallam gida ya kusa. Kar ya dawo bai same ni ba."


Mama ta ce,


"Aikam Umman Amrah babu inda za ki tafi sai kin ci abinci. Ai ina jin ma ba zai rasa ƙarisa dahuwa ba. Maryama je ki bincika."


Suka fita É—akin a tare.


Sai da Umman Amrah ta ci abinci ta yi sallar la'asar sannan ta tafi. Da godiya suka rabu da Maryama, tana mai tsananin jin daɗin kalaman Umman Amrah, na cewa za ta rinƙa zuwa akai akai, har zuwa lokacin da zai samu lafiya ya koma asalin gidansu.


Da yamma Mama da Maryama suna zaune a falo, bayan Muhammad ma ya dawo daga Islamiyya yana ta musu zuba, wayar Mama ta ɗauki ƙara. Daga jikin chaji Muhammad ya ciro ya miƙo mata, ta duba ta ga Abba ne ke kiranta.


Da sallama ta É—auki wayar, sai dai a maimakon ta ji Abba ya amsa sallamar, akasin haka ta samu. Cike da masifa ya ce,


"Na turo Mallam Ya'u yanzu yanzun nan ya zo ya É—auko ku. Ku zama cikin shiri, zai kawo ku gidan Yaya Imrana ne. Ina nufin har da Maryama."


Bai jira ya gama sauraren tambayar da Mama ke masa ta lafiya? Ba, kawai ya datse wayarshi.


Cike da mamaki ta kalli Maryama, fuskarta na nuna zallar damuwa, ta ce,


"Wai mu shirya yanzu Mallam Ya'u zai zo ya tafi da mu gidan Yaya Imrana. Allah dai Ya sa lafiya."


"Ameen."


Maryama ta faɗa baki ɗaya jikinta babu ƙwari. Miƙewa ta yi babu kuzari ta nufi ɗakinta, ta ɗauko dogon hijabinta ta saka, sannan ta zauna da wayarta a hannu, tunani da fargaba sun taso ta gaba, tana son sanin haƙiƙanin dalilin wannan kiran na gaggawa da aka musu.


Bayan kamar mintina sha biyar sai ga Mallam Ya'u ya iso. Da sallama ya shigo ya sanar musu cewa su fito su tafi. Haka suka mimmiƙe jiki babu ƙwari, shi kanshi Muhammad fargabar abin da zai iya faruwa ce ta ɗarsu a zuciyarsa. Fatan samun nasara kawai yake, har suka isa gaban motar.


Muhammad ne a gaba, sai Maryama da Mama a bayan motar, bayan sun tabbatar ma mai gadi cewa ya kula da Annur da ke ciki, ba za su kulle ba gudun samuwar wata matsalar.


Da isarsu aka buɗe musu babban gate ɗin gidan. Gida ne babba mai matuƙar girma, wanda ke ƙunshe da parts kusan guda biyar.


Bayan sun faka motar ne suka firfito, dreba kawai suka bari a ciki, su kuma suka ƙarisa part ɗin kawu Imrana, da hasashen a can za su samu Abba.


A babban falon suka yi sallama. Ɗaki ne mai girma, wanda ya ƙawatu da kayan alatu. Sanyin AC duk ya gama garwaye ɗakin, ga wani irin ni'imtaccen ƙamshi da ke tashi ta kowacce kusurwa.


Tsit ɗin da suka samu a ɗakin ne ya matuƙar ƙara razana su. Ga Abba da Kawu Imrana jere bisa 3 seater, sai Deedah zaune a ƙasa, ya sunkuyar da kansa.


Kawu Imrana ne ya amsa sallamar, haɗe da sakar musu murmushi, yana mai basu izinin ƙarisowa ciki.


A ƙasa Maryama da Muhammad suka jera, suka gaishe da kawun nasu, yayin da Mama ta zauna can nesa da su, bisa 1 seater.


"Sannunku da zuwa Hajiya."


Kawu Imrana ya ce da Mama, a lokacin da take gaishe shi.


"Yauwa Yaya. Allah dai ya sa lafiya, mun ji kiran gaggawa..."


Tun ba ta rufe bakinta ba Abba ya fara masifa,


"Ina fa lafiya. Ƙaramar yarinya kamar Maryama tana neman miyar da mu wasu shashashu, wanda ba su san abin da suke ba. Wato ita har ta yi ƙamarin da babu kunya za ta nunar da ba ta son Ahmadu ko? To wallahi ba ta isa ba! Ke ba ki isa ki baɗa mana ƙasa a idanuwa ba. Yaran yanzu sam! Ba ku san arziƙi ba."


Da hannu Kawu Imrana ya dakatar da shi, yana murmushin dattako ya ce,


"Ya isa haka Balarabe. Ba a haka ai. Ni yanzu duka ba wannan ne dalilin da ya sa na tara ku ba. So nake na ji bayani daga bakin Maryama."


Ya juya ya fuskance ta, ya ce,


"Ƴata kina son Ahmad ko bakya son shi? Ko kaɗan ba na so ki ji kunya ko kuma nauyin faɗi, feel free and tell me, babu wanda ya isa ya miki auren dole. An wuce wannan zamanin ai tunin duniya. Dama tun farko na ji daga bakin Ahmad ɗin ne, kuma shi da kanshi ya faɗa min irin shaƙuwar da take tsakaninku. Ki faɗa min gaskiya, tun daga cikin zuciyarki."


Kuka ne ya kufce ma Maryama, ta sadda kanta ƙasa, tana mai rasa dukkanin nutsuwarta. Ta ma rasa me za ta faɗa. Shin ta yaya za ta iya buɗe bakinta a gaban Kawu Imrana da kuma shi kanshi Deedah ɗin ta ce wai ba ta son shi? Abu dai da kamar wuya. Ba ma za ta taɓa iya wannan ta'asar ba. Ita ba ma ta san ta ya akai har zancen ya fito ba, cewa wai ba ta son Deedah.


Cikin kwantar da hankali Kawu ya ce,


"Ba na so ki cuci kanki ƴata. Wallahi na miki alƙawari zaɓinki za ki aura. Ƙin amincewa da auren Ahmad kuwa ba zai taɓa shafar dangantakarmu ba. Da a ce sai an yi a zo zumunci ya ɓaci, ai gwara tun wuri a tarbi abun."


Cikin ƙarfin hali take son shanye kukanta. Ta saka dukkanin hannayenta tana sharewa hawayen, sai dai kuma wasu sabbi ne ke saukowa.


Satar kallon Deedah ta yi, ta ga yadda ya baza dukkanin idanuwansa yana kallonta, yana mai son jin me za ta faÉ—a.


Da shessheÆ´a ta fara magana,


"Kawu, Abba, ku gafarce ni, ba na son a ce na zama silar ɓacin ranku. Amma wallahi ko kaɗan ban taɓa son Yaya Deedah da aure ba. Irin soyayyar da nake ma Hammad ƙanina ga shi nan, irinta nake ma Yaya Deedah. Ku yi haƙuri don Allah, amma a bar kowa da zaɓinsa."


Cikin zafin nama Abba ya taso da niyyar ya wanka mata mari, sai dai Kawu ya riga shi isa gare ta, ya san zuciyar ɗan uwanshi, ya san cewa dukan nata zai yi dama. Riƙe masa hannuwa ya yi, ya ce


"A kan me za ka dake ta? Don kawai ta faÉ—i ra'ayinta? Kar mu yi haka da kai Balarabe. Ko akwai wanda ya yi maka dole a sadda za ka yi aure? Babu. Haka ni ma babu wanda ya min dole. Matana uku a halin yanzu, babu wacce aka haÉ—a ni da ita, ko kuma aka mana auren dole. Duka auren soyayya ne. Saboda haka Æ´ata ma ban ga wanda zai mata dole ba. Wanda duk take so shi zan aura mata."


Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke Maryama. Tana jin wani irin daɗi a cikin zuciyarta. Damuwarta na ragewa, saboda jin kalaman Kawu. Sai dai kuma so ɗaya da ta haɗa ido da Abbanta ba ta sake marmarin kallonshi ba. Tsantsar jin haushinta da yake kawai ta iya hangowa a cikin ƙwayar idanuwansa.


"Yanzu Yaya goyon bayan wannan shashashar yarinyar za ka yi? To ni dai sam! Ba da yawuna ba. Ahmad Deedah na ce ta aura, ba kowa ba."


Murmushi ya yi Kawu. Ya dafa kafaÉ—ar É—an uwanshi, yana faÉ—in,


"Ashe dai har yanzu baƙar zuciyar nan da na san ka da ita tana nan. Sai yaushe ne za ka san ka girma Balarabe? Ka rufa wa kanka asiri ka rage wannan halin, ko kaɗan ba hanyar ɓullewa ba ce."


GyaÉ—a kansa ya yi, ya ce,


"To idan ba ki auri Deedah ba uban wa za ki aura? Na ce uban waye wanda kike so?"


Bakinta kyarma yake, ta gaza furta komai, hankalinta na daÉ—a tashi. Kallon Mama take tana neman taimakonta, tana son jingina a jikinta ko za ta É—an samu nutsuwa, amma ina, Mama ma harararta ta yi, tana mai tsananin jin haushinta.


Hammad ne ya riƙe mata hannun dama, yana mai ɗaga mata kai alamar ba ta ƙwarin guiwa, haɗe da sakar mata ɓoyayyen murmushi, wanda a tsakaninsu kawai za su san ya yi shi.


"Wallahi kin ji na rantse aure zan miki. Ko ki fiddo miji nan da sati biyu ko kuma in nemo duk wanda nake so in haÉ—a ki da shi. Wanda bai yi sharar masallaci ba ai ya yi ta kasuwa."


Tsananta duka kawai gabanta ke yi. Wani irin raÉ—aÉ—i take ji a cikin zuciyarta. Sauyi kawai take gani daga wurin Abbanta. Me ya sa zai mata haka? Shin kanta farau irin haka?


"Da ke nake magana!"


Ya zaro mata idanuwa, ya ma ƙi sauraren Kawu da ke dakatar da shi.


"Ka yi haƙuri Yaya. Amma na riga da na rantse. Wallahi aure zan mata, cikin kwanakin nan ba ma da nisa ba. Ba dai ni za ta kunyata ba? Kar ma ka yi ƙoƙarin dakatar da ni. Don Allah."


"What are you still doing Bala? Kana É—aukar aure kamar wani abun wasa. Ta ya za ka ce aure za ka mata, babu wani binciken kirki?"


"Ita ta ja komai Yaya. Don haka ke nake sauraro. Waye shi, kuma É—an gidan waye? Ban damu da wadata ko rashinta ba. Ke nake sauraro!"


A iya wannan lokacin kam tsoro ya gama mamaye dukkanin gaɓoɓin jikinta. Yana zagaya duk jini da jijiyoyinta.


Kallon da yake mata ne ya sa ta ƙoƙarta tattaro magana, ba tare da ta san me take faɗi ba, ta ce,


"Annur nake so!"


***


*You know what? 4k words na muku yau. The most longest page since after Sallah. Fatan kun ji daÉ—inshi sosai.*


*Readers, ya kuke ganin wannan al'amarin? Shin Abba ya kyauta kuwa wannan gaggawa da ya saka a auren Maryama? Zai amince da zaɓinta, duk dayake cewa Annur ɗin mahaukaci ne? Ta ya auren mahaukaci da mai lafiya zai yiwu? Idan har ya amince ɗin ma, a haka za ai aure babu danginshi ko ɗaya? Kodai za su miyarshi gida ne sannan a yi auren?*


*Amsoshin tambayoyin suna ga alƙalamin marubuciyar, sannu a hankali za ta warware mana dukkan tambayoyin.*


*Mutanena masu mutunci kuna ina? Kun ga dai na karkata na rubuto muku dogon shafi mai mutunci. Fatan kuma za ku karkata hannayenku zuwa ga ƴar tauraruwar nan domin ku kankaro min mutunci ni ma.😘😀*


*Ghosties kuma masu kama da cartoons, ku ci gaba da laɓe. Insha Allahu wayoyinku hucking za su rinƙa yi muku daga yanzu.😏*


Thanks all


Pinky durling💞
RAZ 2
[9/8, 12:49 AM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_




Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*




5⃣8⃣




Wattpad: Princess Amrah


***


"Wurin Amrah nake so ku kai ni. Kullum sai na sha fama da Dadyna da Momyna kan cewa su kai ni inda Amrah, amma sai su ce da ni wai Amrah ta mutu, ba zan sake ganinta ba. Ni kuwa ta kufto na gudo ba tare da sun sani ba. Ai za ku taimaka min ko?"


Dariyar yaƙe yake, amma kuma ruwan hawaye na sauka a bisa kumcinsa. Sai famar sauke ajiyar zuciya yake.


Sosai suke mamakin wannan mahaukaci. Muryarsa da duk yanayinsa iri É—aya ne da Sans, ba su da bambanci. To waye wannan?


Kuka ya fasa mai ƙarfi.


"Don Allah ku ma kar ku ce min Amrah ta mutu. Kar ku ce ba zan sake ganinta ba. Wallahi Amrah nake so! Ita nake ƙauna, da ita nake da burin ci gaba da rayuwata."


Ya dafe kansa, tamkar wani mai cikakken hankali.


"Ina ne gidanku, kuma su waye iyayenka?"


Sans ya yi ƙarfin halin tambayarsa, duk da mamaki da ya gama garwaye dukkan saƙon da ke cikin zuciyarsa.


"Ban sani ba ni ma. Dady da Momy su ne iyayena. Amma ban san su ba, ban san gidanmu ba."


"To kar ka damu. Za mu kai ka inda Amrah. Za ka bi mu dai ko?"


Kansa ya ɗaga da sauri, har yana cin tuntuɓen magana, ya ce,


"Zan bi ku. Ku kai ni wurin Amrah, na tabbata ita ma tana can tana jira na mu yi aure."


Mamakin abin da Sans É—in ya faÉ—a ne ya wanzu a zuciyar Bobby. Ya kalli abokin nashi yana son yin magana, amma ya É—aga masa hannu, alamar kar ya ce komai.


"Kamar yadda kuke mamaki to ni ma haka nake yi. Kamar yadda ba ku san shi ba ni ɗin ma haka ban san shi ba. Haka kawai jikina yake ba ni something will happen, alkhairi ba sharri ba. Ku duba yanayin fatarsa, alamun ya ji hutu kenan. Da kuma suturar da take jikinsa, duk da kasantuwarsa mahaukaci, amma tsadaddu ne. Don haka na yanke hukuncin mu tafi da shi. Kuma koda ma a ce ba haka ba, abu ne mai matuƙar mamaki, mutum ya haɗu da mai kamanni sak irin nashi, ko kaɗan babu bambanci. Ba na jin zan iya tafiya in bar shi, har sai na gama bincike a kansa."


Jinjina kansa ya yi Bobby. Ya ce,


"Good thinking. To amma yanzu ya za mu yi da shi? Tunda ba gida za mu nufa ba."


"Wannan mai sauƙi ne. Yax ya tafi da shi a kan mashin. Mu kuma sai mu hanzarta tafiya asibitin."


"Amma kamar da wahala fa mahaukaci ya hau mashin ba tare da mai kula da shi ba. Kuma inda na san da haka da sai in ce ya zo da napep ai. Ko kana ga babu komai?"


Sans ya ce,


"Gaskiya ka faÉ—a kai ma. To ko za ku tafi da motar can gida ni sai in tafi asibiti a mashin É—in? Na ga ai ba daÉ—ewa zan yi ba."


Bobby ya ce,


"Ƙafarka fa. Za ka iya tuƙin mashin babu matsala?"


"Babu matsala Guy. Idan ma akwai, I'll give you a call."


Bobby ya ce,


"To shi kenan abokina. Bari mu wuce."


"A kula da shi sosai Guy. A ba shi abinci ya ci. A masa duk dabarar da ta dace kafin in dawo. Idan ka ji ni shiru ka kira ni."


Da haka suka rabu, su Bobby suka juya baya domin komawa gidan gonarsu, yayin da Sans ya haye bisa mashin ya kama hanyar shiga cikin gari.


*


Waya yake cike da ƙunci da damuwa. Jikinsa har karkarwa yake, yana faɗin,


"Inspector ban san sadda ya fita ba. Ba ni kaɗai ba, dukkan ƴan gidan ma babu wanda ya kula da fitarsa. Tun sadda ya kamu da ciwon nan yake attempting guduwa ake kama shi, daga ƙarshe ma aka fidda masa ɗaki guda haɗe da ɗaure shi, aka kuma datse ɗakin.


Ta yadda dai muke zargin fitarsa, wata ƙila ko sadda aka kai mishi abincinsa na rana ne wanda ya kai mishin ya manta bai rufe ƙofar ba. Tunda dama idan an kai mishi abincin kwance shi ake yi, har sai ya cinye sannan a koma a ɗaure shi, amma sai an datse ɗakin. To kuma bayan ya gama cin abincin ne aka tarar ba ya nan.


Inspector don Allah a taimaka mana, wallahi daga ni har mahaifiyarsa hankalinmu a tashe yake. Ba mu san inda Annur zai faÉ—a ba. Ba mu san a rayuwar da zai afka ma ba."


Sai a nan ya ci burki. Yana sauraron abin da inspector É—in ke ce mishi.


"Ka cire damuwa daga ranka Pharm IA. Insha Allahu Annur zai bayyana. Za mu same shi a yau É—in nan."


"Ina fatar hakan Inspector. Allah Ya bayyana shi. Na gode ƙwarai. Sai na ji ka."


Ya tsinke wayar daga nan, yana mai juyawa ya fuskanci Matarshi da ke ta famar kuka riris, ya ce,


"Ki yi haƙuri ki daina kuka. Da yardar Allah zai bayyana, cikin ƙoshin lafiya."


Shessheƙar kuka take, ta ce,


"Allah tabbatar mana."


HaÉ—e da share hawayenta, tana sharewa wani na daÉ—a saukowa.


Da yamman aka barbaza ƴan sanda domin neman Annur. Duk wasu tituna da ke cikin garin Katsina sai da aka watsa ƴan sanda. Daji daji haka suka rinƙa shiga. Saboda kuɗi ne masu mugun yawa Pharm IA ya tura musu.


*


Gudu yake sosai Sans, sai dai ya taka burki, a daidai isar shi wani check point, inda tun daga nesa ya hangi faskeken hoto irin nashi, sai dai ba shi É—in ba ne.


Akwai layin motoci da mashina a gabanshi, saboda daidai junction ne. Hakan ya ba shi damar karanto rubutun da ke manne jikin hoton, cewa ana neman Annur Iqra Al-Hussein, mahaukaci ne, za a gan shi da kaya kala kaza, ya fita ne da misalin ƙarfe uku na rana.


Hasken traffic ne ya dalle rubutun, har Sans ya kai ƙarshe a karanta shi. Mamaki yake sosai, take zuciyarsa ta kitsa mishi abin da zai yi. Ba dai mahaukaci ba ne? Na san abun yi.


Ya lallaɓa ya yi kwana, ya bi one-way har sai da ya isa u-turn, sannan ya ci gaba da zura gudunshi, da nufin komawa gidan gona.


***


Cikin mamaki Abba ya kalli Maryama, bakinsa na rawa ya ce,


"Wane Annur É—in kike magana? Kar dai ki ce min wannan mahaukacin."


Kai kawai ta É—aga ma Abba, tana zubda hawaye sosai.


Ita kanta Mama sai da ta sha mamaki. Deedah ma kallonta yake ƙyam, yana nazartar yanayinta. Bai san komai da ke wakana game da Annur ba, kawai dai ya san cewa Annur ya zama riƙaƙƙen ɗan iska; manemin mata kuma mashayi. Amma don me Maryama za ta zaɓi wannan tuƙururun ɗan iska a matsayin abokin rayuwarta na har abada? Dama dalilin da ya sa ta taɓa tambayarsa Annur kenan? Gyaɗa kansa ya yi, yana jin ba zai iya yin shiru ba, dole ya yi magana a wannan gaɓar.


"Abba ku gafarce ni, zan É—an yi magana."


Ya juya ya kalli Maryama, ya ce,


"Maryama ki rufawa kanki asiri, ba wai don kishi ko wani abu ba. Ba kuma ina miki buƙulun auren wanda kike so ba ne. Amma fa bai cancanke ki ba. Annur ba ya sahun mazajen da ya kamata a ce kin aura. Me ya

Please Login or Register in order to submit comment