You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba halan? Walle in dai baka zo ba mun cire ka daga sahun danginmu, mun yafe ka, tun da har ka gagara ka zo ka sallaci mahaifiyarka, dama tun ranta bai fita ba tacce a kirawo ka kui bankwana, babu irin kiran da ban yi ma ba amma kaƙƙi zuwa, daga ƙarshe ma sai kab bar ɗaukar kiran nawa, har Allah Ya karɓi rayuwarta, kuma bayan mutuwar tata ma ka ƙi zuwa. Babu komi Mahmouda, mun gode."


Kawai ta tsinke wayar da wani irin kuka.


Dafe kansa ya yi, wayar tasa ma sakinta ya yi ƙasa, yana jin yanda zuciyarsa ta masa nauyi sosai, kamar ba zata iya ɗaukar baƙin cikin da yake ƙunsa mata ba.


"Ka yi shiru giÉ—e, ka biya kuÉ—i ko ana samu a ceto rayuwar wancan bawan Allah tun bai mace ba."


Masifaffen likitan ya faÉ—a a karo na uku da yake ma Mahmouda magana bai ma san yana yi ba.


"Ina zan je in biya halan?"


Ya samu da ƙyar ya fiddo maganar, bayan ƴan daƙiƙu da ya yi shiru yana sauraren likitan.


"Tahi can, zaka ga hanyar Pharmacy ceniya, ka tai can ka biya kuÉ—É—i, zasu baka rasiÉ—i sai ka kawo can a cike masa katinsa, sannan ko ina duba shi."


Tafiya ya yi inda likitan ya kwatanta masa, bayan ya biya kuɗin ya dawo medical record, ya basu reciept sannan aka cike masa katinsa. A wurin suna sai da ya tambayi Fiddou, ta ce kawai a saka masa Modu Najibou, sannan aka miƙa katin ofishin likita, aka tafi da Modu da har yanzu ko motsi baya yi.


A cikin zuciyar Mahmouda kuwa tir kawai yake da hali irin na wannan likitan, ko kaɗan bashi da kirki bare ya roƙi alfarmar tafiya wurin jana'izar mahaifiyarsa.


Ganin kaMar akwai sassauci a fuskar Ƴan sandan ya sa ya faƊa masu komai, a ƙarshe ya nemi alfarmar zai je ya halarci jana'izar mamansa da ta rasu.


Daga farko basu amince ba, sai daga baya suka tausaya masa, suka yanke hukuncin É—aya daga cikinsu zai bi Mahmouda, idan an gama su dawo tare, har sai an ga yanda hali ya nuna ga wanda aka kaÉ—e É—in.


Sefa ya zaro daga aljihunsa wanda bai ko tsaya ƙirgawa ba, a hankali ya tako har inda Fiddou take, yana kallon yanda idanuwanta ke zubda ƙwalla, wanda hakan ya tabbatar masa da cewa lallai wannan mutumin da ya banke yana da matuƙar muhimmanci a rayuwar Fiddou, musamman ma da ya ga zallar tashin hankali a cikin ƙwayar idonta.


Kuɗin ya miƙa mata, fuskarsa babu walwala ko kaɗan a tattare da ita.


"Mi zan yi da su halan?"


Ta jefo masa tambaya ba tare da ta karɓi kuɗin ba.


"Zan tai in dawo, Mammata ta rasu za a yi jana'izarta yanzu, shi ne zan tai, kuɗin ga kuma ko akwai abin da za a buƙata nashi kahin in dawo."


Jiki babu ƙwari ta ɗaga hannuwanta da take jin sun mata nauyi ƙwarai ta karɓi kuɗin, ba tare da ko kallonshi ta yi ba. Saboda a zahirin gaskiya wata irin tsanarshi take ji a zuciyarta, a ganinta kaman duk abin da ya faru da Modu SHI NE SILA, dan haka bata jin akwai sauran wani abu da zai yi ya burge ta.


"Allah Ya bashi lahiya, sai na dawo giÉ—e."


Bata ce masa ko uffan ba, haka kuma bata sake kallonsa ba har ya ɓace ma ganinta, ta sake fashewa da wani kukan.


Tana nan zaune a reception ta ji muryar waccan nurse É—in tana mata magana,


"GiÉ—e kin taho nan kin yi zaune, mi da baki matsa inda likita ba halan? GiÉ—e ya tashi kuma bai san kowa ba. Gashi can likita ya gama kula da shi har ma an kai shi É—akin maza an kwantarshi."


Tashi Fiddou ta yi a saɓule ta share hawayenta, duk irin rashin natsuwa na Fiddou amma ta koma kamar ba ita ba, tafiya ma a hankali take yinta, haka magana ma a natse kamar dai ba ita ba.


"Wane ne É—akinsa halan giÉ—e?"


"Mu tai in kai ki."


Bin bayan nurse É—in ta yi shima É—ayan É—an sandan ya bi su, suna isa male ward ta ce,


"Ku shiga, gadon da zai kallo ku shi ne an na giÉ—e."


Shiga ciki suka yi bayan nurse ɗin ta tafi. Tun daga nesa ta hango shi an maƙala masa ledar jini, da alama jininsa ya fita sosai, dama kuma bata yi mamaki ba, la'akari da yanda kayanshi suka yi kace kace da jini, kamar an yanka wata dabba an goge da kayan nashi.


Da kuka ta ƙarisa zama kusa da shi, tana gyaɗa kai tana faɗin,


"Sannu Modu, sannu sannu. Wallahi laihina ne duka wanga, laihina ne da ban zo na kawo ma abinci da wuri ba, na san yunwa ce ta ishe ka ka nemi ƙetaro titi ka biɗo ni, shine wagga ta'asa ta hwaru. Allah Ya baka lahiya Modu."


A hankali ya fara buɗe idanuwan nasa, da ƙarfi ya ƙarisa buɗe su, yana tunanin a inda yake, da kuma halin da yake ciki.


"Modu..."


Ta faÉ—a da murmushi mai haÉ—e da ruwan hawaye.


Murmushi shi ɗin ma sakar mata, kafin ya fara yunƙurin tashi zaune.


Miƙewa ta yi da sauri ta ce,


"A'a hwa Modu, halan baka ga baka da lahiya ba? Koma ka kwanta ka jiya? Ka natsu dan Allah dai."


Bai koma ya kwanta ɗin ba sai kallonta da yake yana murmushi irin na taɓaɓɓi , yana ɗan zaro idanuwansa.


"Walle giÉ—e ina hwasawa, ina hwasa kai ka inda take."


Yana jin ta faÉ—i haka ya koma ya kwanta, yana É—an gyaÉ—a mata fuska alamar kar ta fasa, ruwan hawaye na zirara daga idanuwansa, murmushin da yake kuma bai kau ba.


"Yauwa ko kai hwa. Ka bari har likita ya gama duba ka sannan ko mi zaka yi sai ka yi abinka. Ka ga yanzu baka da lahiya ne, jininka ya fita sosai sai da aka siya wani shi ne ake ƙara ma."


Murmushin fuskarsa ya faÉ—aÉ—a, bai É—auke kallonsa daga Fiddou ba ya ce,


"Ni bani son wannan jinin, ku bar ni da nawa wanda ke gudanya da..."


Bai ƙarisa maganar ba ta kalle shi ta ɓata fuska,


"Wai Modu me yake damunka ne? Na hwaÉ—i ma jininka ya hita da yawa hwa, mi da ba zaka yi shiru hakan nan ba halan?"


Shirun kuwa ya yi ganin kamar ranta ya ɓaci. Ya runtse idanuwansa alamun baccin ƙarya yake, sai kyarma idanuwan ke yi, hawaye kuma bai daina fita daga cikinsu ba.


Suna cikin haka sai ga wata nurse ɗin ta daban ta zo, hannunta riƙe da kwando mai ƙunshe da allurai da magunguna.


"GiÉ—e hala wanga ne Modu?"


Ta ce da Fiddou tana kallonta.


Kai kawai ta É—aga mata.


Matsawa ta yi inda yake, tana yi tana magana,


"Hala har yanzu bai hwarka ba?"


"Ido nai biyu ai ko yanzu. Modu!"


Ta kira sunansa yanda zai ji.


Idonsa guda ɗaya kawai ya buɗe, shi ɗin ma ba duka ba, ya ɗan ƙwanyarasa a fuskar Fiddou kaɗan, sannan ya sake rufewa yana murmushi.


"Modu likita ta hwa zata baka magani. Mi da kake satar kallo na halan?"


Dariya ta so ta ɗan ƙwace wa nurse ɗin da kuma wancan ɗan sandan da ke tsaye yana kallonsu. Yanayin na su Fiddou akwai ban dariya.


Allura ta haɗa nurse ɗin kafin ta fara tunanin ta yanda zata fara, dan ta ga alamar taɓaɓɓe ne ba kansa ɗaya ba.


"GiÉ—e halan ya zan yi da wannan Modu?"


Ta juyo ga Fiddou tana tambayarta.


"Kuma walle Modu bashi son allura. Akwai sanda yai yi wani ciwo an sha daga da shi kahin a yi allurar nan. Amma na san yanda zan yi da shi."


Ta faÉ—a haÉ—e da mayar da kallonta ga Modu da murmushi.


"Modu ka ƙi buɗe idanuwanka ko? Walle idan baka buɗe su ba ba zan kai ka inda take ba, sai dai ko kukan jini zaka yi ka yi."


Da saurinsa ya buɗe idanuwan yana ware su a kanta, ya washe baki wanda dariyarsa kawai zaka kalla ta tabbatar maka cewa mahaukaci ne. Banda ƙazantar da ke jikin tufafinsa, da kuma sumar da ta gama mamaye kaf ilahirin fuskarsa, ta bisa kai kuwa dama ta yi tsawo har ta gaji, da alama dai ya jima bai yi aski ba.


"Mi zan yi ya yarda a yi?"


Nurse É—in ta faÉ—a a tsorace, dan bata so wani abu ya same ta, kuma da alama dai baya son allurar, dan yanda ta ga yana binta da kallo ita da allurar tata, gudunta ma kar ya mammake ta.


Magana ta mata ƙasa ƙasa yanda Modu ba zai ji ba, kafin a hankali Nurse ta murmusa, ta kalli Modu ta ce,


"Kana so na kai ka wurin Amrah?"


Da sauri ya fizge ƙarin jinin da ake masa, ya diro daga bisa gadon, duk da ciwukan da ke jikinsa basu hana shi kuzari ba, yana kuka yana dariya da furucin,


"Dan Allah ki kai ni wurinta, wallahi *AMRAH NAKE SO!"*


How are y'all? I hope y're all fine.


How was this chapter? Kun ji ta daban ko? Ina fatan dai kuna gane maganar ta 'yan Nijar...lol😁


What do you expect? Who is that mahaukaci mai fadin AMRAH NAKE SO? I think he is the lover of Amrah, irin sosai da sosai din nan. Which Amrah? The writer of AMRAH NAKE SO? No. Her namesy from HOUSE OF NOVELS? I don't think so. To wace Amrah ce wannan? Ba dai wacce ta mutu ba ko?😳


Na hakura da jero expectations din nan nawa dai. Na bar ma marubuciyar ta warware min komai. Da haka nake son kuma masu karatu ku bar marubuciyar, ita zata bayyana maku komai.


Many regards to the readers of this book, especially those that reads and votes, not the ghosts, ehen🙄


Pinky durling
RAZ 2
[8/30, 3:47 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)


Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


3⃣0⃣




Saurin dakatar da shi ta yi da faÉ—in,


"Koma ka kwanta in dai kana so na kai ka wurin Amrah. Ka kuma natsu na maka allurag ga ko kuma in hwasa."


Duk da baya son allurar amma a haka ya haƙura ya koma bisa gadon ya kwanta. Jikinsa sai karkarwa yake har ta samu da hikima ta soka masa allurar, tana yi tana faɗin,


"In dai yana son zuwa wurin masoyiyarsa Amrah to bana so ko motsi ya yi har sai na ƙare yin alluragga."


Da haka har ta samu da zare allurar daga jikinsa.


Tana gamawa kuwa ya fara ƙoƙarin saukowa daga bisa gadon, fuskarsa da murmushi yana faɗin,


"Ki kai ni wurinta. Dan Allah ki kai ni na ga Amrata."


Rasa yanda zata yi da shi ta yi. Kwandon ta É—auka ta yi tsaye tana tunanin mafita. Jin muryar Fiddou ta yi ta ce,


"Sai ka yi bacci ka tashi sannan zata kai ka. Yanzu ka kwanta ka huta kahin a jima."


Komawar kuwa ya yi ya kwanta, yana wani irin yaƙe, haƙoransa da suka gama rinewa suka bayyana.


GyaÉ—a kai kawai nurse ta yi cike da tausayi ta bar wurin. Dama allurar da ta masa har da ta bacci ta zuba a ciki. Take bacci ya É—auke sa sai sauke ajiyar zuciya yake.


KATSINA, NIGERIA.


"Maryama, wato dai ba zaki faɗa min damuwarki ba ko? Yanzu kina ga kaman kina da wacce ta fi ni ne? Kina da wacce zaki tinkara da damuwarki wadda ta fi ni? Idan na shiga wata damuwa, zaki ji daɗi ki tambaye ni matsala ta na ƙi faɗa miki? Haba Maryama! Ya kamata fa ki san ke ba yarinya ba ce, kin wuce lokacin da zaki ringa ɓoye min damuwarki. Aikin Muhammad ne wannan ba naki ba Maryama."


Ajiyar zucuya Maryama ta sauke. Tana tunanin ta faÉ—a mata gaskiya ko kuwa dai kawai ta faÉ—a mata yanda suka yi da Jiddah? Shawara ta yanke kawai cewa kar ta faÉ—a mata gaskiya, saboda abin da Jiddah ta faÉ—a tsaf zai iya faruwa.


"Mama, na samu labarin wata baiwar Allah ne, labarin da ya matuƙar razana ni, ya zauna min a zuciya, nake jin tausayin baiwar Allah'r har cikin zuciyata."


Cikin matsuwa da son jin zancen Mama ta ce,


"Ehen, mabuƙata ne, a taimaka masu?"


"Ko kaÉ—an Mama, ba haka ba ne. Amrah ce..."


Ta kwashe komai ta faɗa wa Mama, sai dai ta ɓoye mata taimakon Annur da take son yi.


Zafafan hawaye ne suka ringa fita daga ƙwayar idon Mama. Tana jin yanda tausayin Amrah ke ratsa duk ilahirin zuciyarta. Take jin tsananin bugawa da zuciyarta ke yi. Wace irin yarinya ce wannan? Wace irin mace ce mai tattare da halayen kirki? Dama akwai irinta a wanann zamanin? Ashe akwai masu kyawawan hali irin Amrah?


"Wannan ita ce damuwata Mama. Dalilin da ya sa kika gan ni cikin damuwa ke nan. Na rasa yanda zan yi da tausayin Amrah. Rayuwarta da mutuwarta duka abin tausayi ne. Akwai manyan darussa a cikin labarin Amrah, wanda saurarensu kawai wani babban ilimi ne."


"Dole ne zaki shiga damuwa Maryama. Dole hankalinki ya tashi. Ina miki fatan kasancewa da irin halayen Amrah, ko da ba duka ba. Idan har kika kasance haka kuwa zan daÉ—a alfahari da ke, zan ninka gatan da nake gwada miki, zan ci gaba da tutiya da ke a duk inda zan shiga."


Rungumar Mamanta ta yi, cikin kuka ta ce,


"Ina alfahari da ke Mamana. Insha Allahu zan ci gaba da kwatanta halayen Amrah. Zan zamto abar alfahari a gare ki, kamar yanda Maman Amrah ke alfahari da Amrah, tun tana raye har bayan mutuwarta."


Murmushi Mama ta saki a fuskarta, tana jin yanda soyayyar ƴarta ke shiga a duk gaɓoɓinta, ƙaunarta take ji ta ko wane saƙo na zuciyarta.


Suna cikin haka Muhammad ya shigo, School bag ɗinsa ya jefar a ƙasa yana mai ƙirƙiro kuka ya ce,


"Mama yau ma..."


Bai ƙarisa ba Maryama ta dafe kanta haɗe da faɗin,


"Problem boy. Yau ma me?"


"Yaya Maryama ban fa yi masa komai ba ya daken."


Ya faɗa fuskarsa a daƙune, kamar ta ce zata masa wani abu ne.


"Kullum haka kake fa Muhammad. Ban san me ya sa ba sam ba ka ci sunan nan ba. Asalin mai sunan haƙurarren bawa ne, mai kyawawan halaye. Amma kai kam ko kwatantawa ma baka yi, na rasa dalili."


Zama ya yi a bakin gado bakinsa tunzure yana faÉ—in,


"Ai dama Yaya Maryama ban taɓa ji kin yabe ni ba, komai sai dai ki ce bani da gaskiya."


Dafa kafaɗarsa ta yi murmushi ƙunshe a fuskarta ta ce,


"Amma ai ka san bani da kamarka ko? To duk abin da zaka ga ina maka ƙauna ce ta ja haka. Ko so kake kawai ko yaushe na yita goyon bayanka, bayan kuma ba gaskiya ba ne?"


Janye hannunta ya yi daga kafaÉ—arsa ya ce,


"Ni dai ban yarda ba. Daga ke har Mama da Abba kuna nuna min banbanci. Ko kaÉ—an bakwa gwada min soyayyar da ta dace."


Zaro idanuwanta ta yi cike da mamakin kalaman fa suke fitowa daga bakin Muhammad,


"Wace irin magana ce kake haka, Muhammad? Kana da hankali kuwa?"


Tashi Mama ta yi ta gyaÉ—a kanta, ta kalli Maryama da faÉ—in,


"Ki fahimtar da shi Maryama. Na kula dai wani abu ne ya ɓata masa rai tun asali. Idan kun gama ki rako shi akwai kyautar da na ajje masa ta musamman."


Murmushi ta saki Maryama, ta ce,


"Mama zaki bar ni da rigimammen yaron nan ke nan. Iyaka na zazzane yaro idan zai min shegantaka."


A daidai fitar Mama ta ce,


"Kun fi kusa ai."


Ta ƙarisa ficewa daga ɗakin.


Juyowa ta yi ga Muhammad da fara'a ta ce,


"In banda abunka Muhammad, kai kaɗai ke nan namiji a gidan nan, ta ya kake tunanin ba zamu ƙaunace ka ba? Duk abin da ka ga muna maka fa muna son ka kasance na gari ne. Ko hausawa sun ce ka so naka duniya ta ƙi sa, ka ƙi naka kuma duniya ta so shi. Idan muka bayyana soyayyarmu a gare ka, baka tsammanin wani abu zai je ya dawo? Abin da mutanen yanzu suka kasa fahimta kenan. Yana ɗaya daga cikin abubuwan da suke taɓarɓarar da tarbiyyar yaran zamani, wato nuna masu soyayya da gata, a kasa nusar da su abin da ya dace da su. Komai suka kawo kawai daidai ne. Muhammad so kake ka zama sangartaccen yaro?"


Sai a sannan ya fara saukowa, cikin sanyin murya ya ce,


"Amma Yaya Maryama ko yau fa mantawa aka yi da ni a makaranta, ba a je an ɗauko ni ba. Kuma na shigo gida, baku damu da sanin wa ya kawo ni gida ba. Duk ƙaunar ce wannan?"


Dafe kai ta yi Maryama, tana jin haushin kanta na mantawa da ɗauko Muhammad da suka yi. Sai yanzu ta tuna Abba ya kirata a waya ya sanar mata ba zai samu ɗauko Muhammad ɗin ba, kuma drebansa ya tafi ƙauyensu yau.




Cike da damuwa ta ce,


"Yi haƙuri Hammad ɗina, ko kaɗan kar ka ga laifin Abba da Mama. Laifin nawa ne, saboda Abba ya sanar min na biya na ɗauko ka idan na tashi, sai kuma na ji bana jin daɗi ban je lecture ɗin ba. Ka gafarta min ka ji ƙanina?"


Da dan murmushi shimfiÉ—e a saman fuskarsa ya ce,


"Babu komai, Yaya Maryama komai ya wuce."


"Yauwa ƙanina abin alfaharina. To ya aka yi ka dawo? Ka hawo mashin ne?"


Bayan ya miƙe tsaye yana ƙoƙarin cire neck tie ɗin uniform ɗinsa ya ce,


"Maman Abdul ce ta É—auko mu tare, ita ta kawo ni har gida."


Miƙewar ita ma ta yi Maryama, ta ce,


"Wacece kuma Maman Abdul? Ban taɓa jin sunan a bakinka ba."


"Wani yaro ne ɗan Nursery 2. Yana yawan zuwa wurin abokina Khalid ne, a nan na san shi har muka shaƙu. Muna mutunci sosai da yaron. To dama wani lokaci idan mamanshi ta zo ɗaukarsa kafin a zo ɗaukana ina zuwa in gaishe ta, har ta ce zata tafi da ni, ni kuma sai in faɗa mata za a zo a ɗauke ni. To yau kuma sai bata zo ɗaukarsa da wuri ba, ni ɗin ma kuma haka. Muna ta jira sai gata ta zo, ganin duk ɗalibai sun watse ya sa ta ce kawai na zo mu tafi ta sauke ni. Dalilin da ya sa bata je ɗaukarsa ba wai ta shiga yin surgery ne, da yake likita ce. Har ma ta ce min zata zo har gida ta gaishe da Mamana, saboda yanda nake kula da yaronta."


Jinjina kai Maryama ta yi, ta ce,


"Ka dai ringa kula sosai da irin wannan abubuwan. Yaushe ta ce zata zo?"


"Ni dai ta ce min wai zuwa anjima zasu zo, tun da dai ta ga gidan yanzu."


"To shi ke nan, Allah Ya kawo ta lafiya."


Daga nan ta fice daga É—akin ta koma falo.


***


Zaune yake ya zabga uban tagumi, kwalaben syrup ne jere a gabansa, ga wata irin sigari babba, irin marar warin nan da turawa suka fi amfani da ita.


Damuwa ce shimfiɗe cikin zuciyarsa, wanda har fuskarsa ta gagara ɓoye hakan.


Bai ko tsaya yin diluting ba, kwalbar kawai ya É—aga ya kai bakinsa, bai sauke ba har sai da ya shanye tas, ko É—is bai rage ba.


Ajje kwalbar ya yi sannan ya kai sigarin a bakinsa, yana yi yana gyaɗa fuskarsa, cike da ƙunci da baƙin ciki.


"Kar dai maganar boka ce ke neman tabbata. True love É—in da na faÉ—a ne ke neman kawo min cikas ko kuwa? Ta ya Dady da kansa zai hau ni da faÉ—a, saboda abin da ba yau aka fara yinsa ba? Yau na fara jawo hasara a kamfani? Akwai matsala!"


Ya sake fasa wata kwalbar syrup ɗin ya kaita bakinsa. Bayan ya shanye duka ya ajje, yana neman kai sigari a bakinsa ya ji wayarsa na ƙara.


ÆŠauka ya yi ya kara a kunne, cikin muryarsa da ta fara canzawa ya ce,


"Hello babe!"


A ɗayan ɓangaren aka amsa da,


"Akwai damuwa my A. Babu kuÉ—i hannuna kuma ina da matsaloli da dama. Ya za a yi?"


Wata budurwa ce ta yi maganar, wacce yanayin maganarta kawai zai tabbatar wa mutum cewa ita É—in ma irinsa ce.


"Babe ya kike so a yi?"


Ya furta yana lumshe idanuwansa.


"My A. ka turo min kawai, ko akwai matsala ne?"


Canza wa wayar muhalli ya yi, daga gefen hagu ya mayar gefen dama, ya matse ta da kafaɗarsa sannan ya ƙoƙarta da hannun da sigarin take ya buɗe wata kwalbar syrup ɗin.


"My A. Na ji ka yi shiru, da alama dai akwai damuwa."


"Babu damuwar komai. Ina up ne."


Dariya ta tulle da ita kafin ta ce,


"Har ma sai ka faÉ—a? Voice É—inka kawai ya tabbatar min da hakan."


"Na sani ai. Ina zamu haÉ—u?"


Sai da ta É—an yi shiru kaÉ—an, kafin ta ce,


"Dole sai mun haÉ—u zaka bani? Me zai hana ka min mobile transfer kawai?"


Cikin yanayin slow ya ce,


"Da wasa kike babe, kin san bana fitar da kuÉ—ina a haka nan. Dole na fanshe a jikinki."


"Amma my A. Na ga ka hau up da yawa, ba zaka iya yin komai ba. Gashi kuma ni a matse nake da kuÉ—in, zamu je wani biki ne MaraÉ—i. Gobe da sassafe zamu tafi."


Cikin halin ko in kula ya ce,


"Zan miki transfer na 50k yanzu. Amma ki sani, zan fanshe ko ba yanzu ba."


"Babu komai."


Ta faÉ—a haÉ—e da tsinke wayar tana dariya.


Yana kashewa ya yi searching account number É—inta, ya tura mata kuÉ—in. Shi kuma ya ci gaba da shan kayan mayensa, wanda suka mantar da shi duk damuwar da yake ciki, damuwar da dady'nsa ya saka shi.


Me zaku iya cewa masu karatu? Shin kun hango wani abu a cikin chapter'n nan kuwa? Idan kun hango, menene? Feel free and tell me your expectation. Ni dai na ce bana tunanin komai, what of you?


Na gode kwarai da addu'o'inku. Alhamdulillah! Na ji sauki sosai. Mura dai ce har yanzu voice dina ya gagara komawa daidai. Ku ci gaba da yi min addu'a, ina matukar jin dadin hakan.


Na kokarta yi maku 2k words duk da rashin jin dadin jikina. Don farin cikinku kawai masoyana.


Basman mai sanyinta ina yinki over, ina farin cikin kasancewarki a duniyata, ke din ta daban ce, ba zan gajiya da yi miki fatan alkhairi ba.


Aunty Maijidda Musa kina ina? Hakkun kina faranta min rai. Amrah na kaunarki irin totally din nan, fatan kin san da hakan.


RAZ NOVELLA 1&2 Ina kaunarku fi sabilillah! Kaunar taku a jinin jikina take, ina alfahari da ku, ina kuma yaba maku da comments a kan wannan littafin. Hakan na dad'a kara min kwarin guiwa sosai da sosai. Kun san ina kaunarku kuwa?


Sauran groups da nake ciki duk ina yinku. Ina matukar kaunarku, ina jin dadin kokarinku na yada wannan littafin har ya zagaya inda ban taba tsammani ba.


My dear Kdeey kaunarki a kahon zuciyana take, kin sani kuwa?


Kar dai na cika ku da surutu, sai mun hadu a next page idan Rabbissamawati wal'ard ya nuna mana.


Pinky durling
RAZ 2


[8/30, 3:47 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!* ♥


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)


Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


31


Buɗe idanuwansa ya yi ya sauke su a bisa fuskar Fiddou da ta tsura masa nata idanuwan tana kallonsa ko ƙaƙƙautawa babu.


Da ƙarfi ya fizge ƙarin ruwan da aka dasa masa yanzu, babu wata wata ya diro daga bisa gadon, yana kallon Fiddou da murmushi a saman ƙazamtacciyar fuskarsa mai cike da suma babu kyawun gani.


Murmushin yaƙe ta mayar masa, tana ƙoƙarin miƙewa tsaye da faɗin,


"Ina zaka tai ne Modu? GiÉ—e koma ka kwanta do Allah de."


Kai ya gyaɗa mata alamar ba zai koma ba yana ƙoƙarin ci gaba da tafiya da ɗangyasasshiyar ƙafarsa, ƙafar wandonsa ɗaya ta gama yayyagewa, tun daga ƙasa har kusan rabin wandon.


Saurin shan gabansa ta yi tana faÉ—in,


"Modu walle in dai kattai ba zan kai ka inda Amrah ba. Idan kuma baka so in kai ka ton ka tahi."


Duƙewa ya yi a daidai inda yake, ya saki kuka da sauti mai ƙarfi, wanda ya karaɗe asibitin, yana bada wani echo sound har inda babu mutane yana amsawa.


A rikice ta duƙa ita ma, ganin halin da yake ciki ba ƙaramin firgita ta ya yi ba, a tunaninta ko wani abun ne na daban ya same sa.


Mutane ne da dama suka tasan ma É—akin,

Please Login or Register in order to submit comment