You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

3⃣8⃣


Follow me on wattpad: PrincessAmrah


***


"Yauwa, gwara da Allah Ya jeho ku a daidai wannan lokacin."


Ta faɗa tana mai sauke ajiyar zuciya, da yaƙinin tabbas mutanen uku da ke gabanta za su saurare ta, sannan kuma za su yarda da ita.


"Baiwar Allah! lafiya? Me ke tafe da ke? Wurin wa ki ka zo?"


Duka Momy ce ta fuskance ta haɗe da zaƙulo wannan kalaman daga ƙasan maƙoshinta, tana mai mamakin budurwar, ga ta dai da cikar zati, kyakkyawa bakin gwargwado, sai dai yanda kanta yake cike da kitson gashin doki, ga ta da hujen hanci har biyu, ko wane ta maƙala masa barima. A bisa goshinta an yi tsattsage an rubuta tafkekeiyar H. Laɓɓanta baƙi ƙirin, wanda da alama su ɗin ma caccake su ta yi. Fatar nan tata ta ji bleaching bakin gwargwado.


"Uhm..."


Ta faɗa tana mai haɗiyar yawu da ƙyar. Kallon da Momy ke watsa mata kaɗai ya isa ya karyar mata da guiwa, ta tabbata da ƙyar idan bayin Allah'n za su saurare ta.


"Dama...uhm...ɗan ku, Annur ne, yana can Maraɗi yanzu haka na baro shi, ya haukace tuƙuru, sannan kuma zuciyarsa ba ta da lafiyar kirki, likita ma ya ce za ta iya bugawa a ko wane lokaci."


Kallon mamaki suka watsa mata su duka ukun, ba su kaÉ—ai ba, har mai gadin ma kallonta yake sake da baki.


"Ku yarda da ni, wallahi da gaske nake maku. Ni da kaina ma zan kai ku har MaraÉ—i, har asibitin da yake kwance."


Tana direwa nan ta share ƙwallarta, tana jiran sauraren martaninsu, shin za su yarda da ita?


"Ina tababa a wannan bayanan naki. Na ma rasa gane inda suka dosa. Ko awanni shida ba a yi ba mun yi waya da Annur, kuma lafiya lau yake. Ban kuma san maganar da kike yi ba."


Mamaki ya gama mamaye zuciyarta, ta ma rasa abin faɗi. Me ake nufi da ita kenan? Da gaske har awanni shida da suka shuɗe Annur lafiyarsa ƙalau? Ko dai ba su yarda da ita ba ne?


Guje wa zargi ya sa Momy umurtar Islam cewa ta ɗauko mata wayarta a ɗaki. Babu ɓata lokaci kuwa ta nufi ɗakin, sai ga ta da wayar Momy a hannu ta miƙa mata.


"Ba zan yi saurin gwasilarki, ko kuma ƙaryata ki ba. Dole sai na bincika, sannan in samu abin faɗi."


Ta latsa lambar Annur, haÉ—e da kara wayar a kunnenta.


Shiru Annur ba É—auki wayar ba, har ta tsinke, Momy ta sake kiransa. Sau huÉ—u tana kiransa amma bai É—auka ba, hakan ya fara karyar mata da zuciya, hankalinta ya fara tashi, ta fara tunanin gasgata baiwar Allah'r.


"Ya salaam! Annur dan Allah pick my call. Kar ka bari zancen yarinyar nan ya zama gaskiya. Hauka? Ciwon zuciya? Kai a'a, wallahi ba dai Annur É—ina ba."


Tana faÉ—in hakan tana sake kiran Annur amma shiru bai É—auka ba.


A karo na ba adadi da take kiransa ya É—auka, a lokacin tana daf da tsinkewa, Bobby ya tashe sa daga barcin yamman da ya koma, ko salla bai yi ba.


Da muryar barci ya ce,


"Hello Momy."


Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke. Ta dafe ƙirjinta da hannunta na hagu, tana jin yanda wani irin sanyi ke sauka a cikin zuciyarta.


"Momy talk to me. Is there any problem?"


"No...no, Annur. Kana ina ne?"


Bayan ya sosa sumarsa ya ce,


"Momy ina gidan su Farouk Sardauna. Tun 5pm da na tashi aiki sai na yo nan kawai, saboda na jima ban gaishe da Maminsa ba."


"Ok, are you okay?"


Ta sake tambayarsa cike da damuwa.


"Am very okay Mom. Allah dai Ya sa lafiya."


Murmushi ta ƙirƙiro ta ce,


"Babu komai Annur. Please ka dawo gida mana, I need to see you, tun jiya rabon da na saka ka a idona."




"Ok Mom. Zan dawo yanzu insha Allah."


"Sai ka dawo."


Tana gama faÉ—in haka ta tsinke wayar, tana bin Hadiza da kallo.


Shiru ya biyo baya a tsakaninsu. Hadiza na mamaki sosai, saboda a hands free momy ta saka wayar, duk suna jin abin da yake faruwa.


Sosai jikin Hadiza ke rawa, mamaki tsantsa a cikin zuciyarta. Ta ya hakan za ta faru? Wannan wane irin plan ne Annur yake yi? Me ya sa zai ma kansa ƙaryar ciwo? Idan kuma da gaske ne bai da lafiya, me ya sa zai ɓoye wa iyayensa?


Ba ta samo amsoshin wannan tambayoyin ba ta ji Momy na faÉ—in,


"Yarinya da alama dai ɓatar hanya kika yi. Ƙila kuma wani Annur ɗin ne daban, amma dai ba nawa ba. Tunda ga shi a gabanki mun yi waya lafiyarsa ƙalau. Idan ma wani makirci ne kika ƙulla, to haƙarki ba ta cimma ruwa ba. Idan kuma ke ƴar damfara ce, sai ki ƙara gaba, domin kuwa a nan dai ba ki yi nasara ba."


Kuka sosai Hadiza ke yi. Ta ma rasa abin da za ta faÉ—a. Ba ta san me za ta ce su yarda da ita ba. Ita dai ta san shi ne ta gani. Tabbas Annur ne wannan marar lafiyar, domin kuwa ko Qur'ani za a ba ta ta rantse tsaf za ta rantse É—in.


Cikin muryar kuka ta ce,


"Ku yarda da..."


"Please get out from here. Mu ba sa'anninki ba ne da za ki tsaya kina neman yi mana wasa da hankali. Gwara ki taka da ƙafafuwanki ki bar gidan nan, tun ba a fitar da ke ba."


Islam ce ta yi wannan maganar cike da masifa, ita dama in dai wurin tsiwa ne to tana gaba gaba, ta iya rashin mutunci sosai ba kaÉ—an ba.


Shessheƙa take yi sosai, jikinta na rawa, kanta na sara mata, tana jin zuciyarta na mata zafi sosai da kalaman Islam. In dai masifa ce ita ɗin ma ta iya. Ta iya rashin mutuncin ita ma. Babu abin da Islam za ta gwada mata, domin kuwa ita ɗin kwarkwararriyar ƴar bariki ce. Ta zauna da wanda suka zarce Islam masifa, haka kuma ta san raddin mayar wa irinsu. Sai dai kuma a yanda zuciyarta ta yi rauni, take tsantsar tausayin halin da ta baro Annur a ciki, ko kaɗan ba ta jin za ta iya biye wa Islam su yi musayar kalamai. Ko ba komai ita ɗin ta haɗa jini da Annur, Annur ɗin da take ma soyayyar da ba ta taɓa yi wa wani ɗa namiji ita ba. A haka jiki saɓule ta miƙe, ta fuskanci Momy, da rawar murya ta ce,


"Ku gafarce ni idan shigowar da na yi gidanku ta ɓata muku rai. Na muku alƙawari hakan ba za ta sake faruwa ba."


Ta jawo haɓar gyalenta ta share hawaye.


"In da a ce ko kaɗan kina da alamun kamala da zan iya ɗaukar maganarki. Sai dai kuma yanayinki kawai ya isa ya tabbatar da rashin ingancin duk wata kalma da za ta fito daga bakinki. Bara na baki shawara saboda gaba; duk inda za ki je ki yi irin wannan ƙaryar, to ki saka kayan mutunci. Wannan gashin dokin da kika sa ki tabbatar kin ɓoye shi. Ki ɗaura ɗankwalin da zai rufe miki goshinki. Hakan ne kawai zai iya saka wa a yarda da ke."


Islam na gama faɗin haka ta kama hanyar barin wurin. Saboda kallonta ma kawai ƙara rura wutar tsanarta take a zuciyarta. A ganinta ba ta da babbar maƙiyya sama da Hadiza; ta nemi ɗaura masifu da bala'i ga yayanta. To miye amfanin tsayawa ta ci gaba da kallonta?


"Malam Ya'u a tabbatar ta fita, sannan a kulle gida."


Momy ta faÉ—a haÉ—e da bin bayan Islam, suka nufi falo.


Maryama kawai aka bari tsaye wurin tana karantar Hadiza. Psycologist ce ita, ta yanayin mutum ma kawai za ta iya fahimtar wani abu game da shi.


"Baiwar Allah zo ki fice cikin ruwan sanyi, tun ban É—auko sandata ta shaÉ—i na zabga miki ita a gadon bayanki ba."


Dakatar da shi Maryama ta yi da hannunta. Ta sake matsowa daf da Hadiza. Ta ce,


"Zan iya yin magana da ke?"


Ajiyar zuciya ta sauke Hadiza. Ta ji daÉ—i da Allah Ya sa mutum É—aya na da hankalin da har ta nemi yin magana da ita.


Kanta ta É—aga alamar ehh. Ta ci gaba da kallon Maryama, tana tsananin mamakin irin kallon da take bin ta da shi.


"Hajiya da kanta ta ce a kore ta. Dan haka ki yi haƙuri, duk wata magana da za ki yi da ita ba dai a nan ba, dan bana so na rasa aikina."


"Damn it!"


Maryama ta faÉ—a tana jin haushin mai gadin da ke magana iya gaskiyarsa.


"Ba ni lambar wayarki, zan neme ki mu yi magana."


Babu musu kuwa Hadiza ta fara karanto ma Maryama lambarta. Babu waya ma a hannunta, ta baro ta cikin gida. Sai dai a kanta ta haddace lambar. Bayan ta gama karanto mata ta maimaita har sau biyu, ta tabbatar daidai ne sannan ta bar wurin, Hadiza ma ta fita daga gidan.




Ko da ta koma cikin falo ta tayar Momy da Islam na firar abin da ya faru. Mamakin wannan baiwar Allah'r kawai suke. Ko miye dalilinta na laƙaba wa Annur ɗinsu manya manyan ciwuka?


Zama ta yi jiki babu ƙwari. Zuciyarta na karanto mata abubuwa da dama, wanda ta gagara sanin haƙiƙaninsu. Ƙoƙarin kawar da tunaninta take amma ta kasa, wuri ɗaya kawai ta tsurawa ido tun da ta zauna.


Dr. Islam ce ta ce,


"Da alama dai Maryama kina da raunanniyar zuciya. Yanzu É—an abin da ya faru ne har yanayinki ya sauya?"


Murmushi ta ƙirƙiro Maryama, ta ce,


"Kawai dai na yi mamakinta ne. Haka kawai babu dalili sai ta zo ta kawo zancen ƙarya? Ba ta tunanin a lokacin da za ta zo ɗin Annur yana gida? Kuma wace riba za ta ci idan ta aikata hakan?"


Cikin halin ko in kula Momy ta ce,


"Ni fa na fi ganinta a ƴar damfara ce. Kun san yanzu da dabara suke aikin nasu. Ƙila kuma ƴar fashi da makami ce ta zo dan ta ga sirrin gidan."


"Allah Ya fi ta kuwa. Babu abin da za ta iya yi mana wallahi."


Islam ta faɗa cikin ɓacin rai.


Daga haka har aka yi sallar magrib. Annur ya kira Momy cewa sai bayan ishai zai dawo, saboda zai yi meeting da wani company da suke son a ƙera masu ƙananan notina.


Sosai hakan ya yi wa Maryama daÉ—i. Dama ba ta so ta haÉ—u da shi, ko dan kar ya santa ta dalilin Dr. Islam.


Bayan sallar ishai suka ma Momy bankwana, Islam da kanta ta nufi kai su gida. A mota sai fira suke, tana nuna mata jin daÉ—in ziyarar da suka kawo musu.


"Yanzu kuma sai yaushe, Muhammad?"


Islam ta faÉ—a cikin fara'a.


"Sai kuma gobe za mu dawo."


Dariya suka saka daga Islam É—in har Maryama. Dafe da baki Maryama ta ce,


"Lallai ma Hammad a gaishe ka. Yo da wannan mu tsaya mu kwana mana."


Caraf Muhammad ya ce,


"Ai sai da na ce miki mu tsaya mu kwana kika ƙi. Gaskiya Maman Abdul mu koma, ban gaji da wasa da Abdul ba, ga shi kuma ya yi barci ko bankwana ba mu yi ba."


"Allah Ya toni asirinki Maryama. Ashe dai kwana ɗan bawan Allah Ya so yi kika ƙeƙashe ko?"


Dariya ta yi Maryama, ta ce,


"Yanzu dan Allah Muhammad idan muka tsaya muka kwana, Mama fa? Duk yinin yau fa ba mu zaune tare ba. Good Friday guda amma ba mu gida."


Baki tunzure ya ce,


"Amma Yaya Maryama ba ga Easter Monday nan ba. Ai za mu zauna a gida mu huta."


Ka yi haƙuri to. Yanzu dai mun riga da mun taho, sai kuma wani lokacin idan Allah Ya kai mu."


"To." Kawai ya faÉ—a cikin kumburi, wanda har Islam sai da ta murmusa.


"Aunty Islam ai za ki zo walimar saukar mu ko?"


"Me zai hana? In dai kin tuna min idan lokacin ya zo, insha Allahu za mu zo, har Momy ma."


"Zan kuwa tuna miki da yardar Allah. Ai an kusa ma. Ba zai wuce kwana goma ba. Amma dai idan ya rage kamar kwanaki uku zan kira na sanar da ke."


A daidai isowarsu ƙofar gida Islam ta ce,


"To Allah Ya nuna mana."


Ta ce da Muhammad,


"Hammad in ga hannunka."


Miƙa mata hannun ya yi ta karɓa, kuɗi ta cusa masa a ciki haɗe da faɗin,


"Kar ka buÉ—e har sai ka shiga gida. Ka gaishe min da Mama. Dare ya yi ai da na shigo mun gaisa."


Bankwana suka yi cike da ƙaunar juna suka rabu.


***


Tun daga lolacin da Hadiza ta bar gidan su Annur ba ta daina mamaki ba. Tana matuƙar son sanin ainahin abin da yake faruwa. Me Annur yake ɓoyewa ne haka? Ko dai wani ne wai ba shi ba? A zahirin gaskiya ita dai ta san Annur ne ta gani, ko tantama babu. Wane dalili ne zai sa ya zaɓi hauka a matsayin wani ƙulli na shi? Ta tabbatar kuma da shi ne Momy ta yi waya, saboda a handsfree ta saka, ta ji muryarsa.


Dafe kanta ta yi a karo na barkatai, tana tunanin mafita. Latsa kiransa ta yi, cikin sa'a kuwa ya É—auka a wanaan karon.


"Babe..."


Ya furta cikin sanyin murya.


So take ta gwada shi, ta ga iya gudun ruwansa. Hakan ya sa ta ce,


"My A...ina kewarka sosai. Lafiya dai ka daina É—aukar kira na?"


Da murmushi ya ce,


"Ayyuka ne suka sha kaina da yawa. Amma yanzu komai ya daidaita. Kin dawo kenan?"


A zuciyarsa kuwa dariya yake mata. Tunda ya ga ta kira sa da lambar Nigeria ya tabbatar cewa ta dawo, lokacin kwasar rabonsa ya yi.


"My A ka san wani abu?"


Ta faÉ—a cikin kakkausar muryarta, wadda ainahinta ba haka take ba, tsabar gwanancewa da bariki ne kawai ya komar da ita haka.


"Sai kin faÉ—a babe."


"Wani na gani mai kama da kai a Maraɗi, idan har ba mutum ya san ka sosai ba ba zai iya banbance ku ba. Ni kaina da ƙyar..."


Dakatar da ita ya yi da faÉ—in,


"Share kawai."


Yana son ɓatar da zancen.


Jin haka ya sa ta ƙara shiga wasi-wasi. Me ya sa daga fara magana zai dakatar da ita? Da alama ya san komai. Tabbas wani ƙullin ne, sai dai ita kanta ba ta san ainahin me yake nufi da hakan ba.


Kawar da maganar ta yi ta hanyar jawo wani zancen na daban. Shi kuwa babban burinsa kawai su haÉ—u, domin ya kwashi abin da yake muradi.


Suna cikin fira kiran Maryama ya ringa shigowa a wayarta. Duk da ba ta san lambar ba, haka kawai ta ji tana son datse wayar da Annur, domin ta ɗauki kiran lambar, wata ƙila kasuwa ce ta yi.




*


**


Na gaishe da Yayana Ibrahim Lawal Zaria. Ina matuƙar jin daɗin kulawarka a gare ni, da wanann littafin. Fatan kana isar da saƙon gaisuwa ta ga takwarata Amrah.


Gaisuwa ta musamman ga Zulaihat Rano. Haƙiƙa ke ta daban ce, kin zarce su. Ina yin ki, ina ƙaunarki fi sabilillah.


Rerbeeart_sk Zarah_bb ZulayheartRano89 khadeeja_Candy lamtana Kamala-Minna Soyayya fi sabilillah.


Ban san ƙyashin da ke hana masu karatu danna alamar tauraron nan ba. danna shi na daɗa ƙarfafa min guiwa ta hanyar yi maku posting a kan lokaci. Yin biris haɗe da wuce shi kuwa harzuƙa zuciyata yake, in ji kamar na ringa ɗaukar tsawon mako guda ba tare da na yi posting ba 😂


RAZ 2
[8/30, 3:51 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *


🅰MRAH NAKE SO!* ♥


(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)


Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_


3⃣9⃣


Wattpad me @ PrincessAmrah


***


Sallama ta yi mata Maryama. Muryarta sanyaye, tana mai jin daÉ—in É—aukar kiranta da Hadiza ta yi, dan a tunaninta ma ko ba daidai ta hardace lambar ba.


Amsa sallamar ta yi Hadiza. Tana son gasgata muryar, saboda tun É—azu take tsumayen kiran Maryama.


"Fatan kina lafiya. Sunana Maryama..."


Ba ta ƙarisa maganar ba Hadiza ta tare ta da,


"Wadda muka haÉ—u gidan su Annur?"


"Exactly."


Maryama ta furta a hankali.


Gaisawa suka yi sama sama, kafin Maryama ta ce,


"Ina son sanin haƙiƙanin abin da kika faɗa ɗazu ne. Dan Allah ba na so ki min ƙarya. Ki faɗa min iya gaskiyar abin da kika sani. Please!"


Ta ƙarashe maganar da muryar magiya.


"Ban san taƙamaimai me zan faɗa miki ba Maryam. Ni kaina a rikice nake, baki ɗaya kaina ya ƙulle. Da gaske nake, wallahi da gaske nake na ga Annur a Maraɗi. Amma abin da ya rikitar da ni, yanzu haka na yi waya da Annur, alamun lafiyarsa ƙalau, kuma na fara masa maganar na ga mai kama da shi, ya nemi shashantar da maganar."


Dafe kanta ta yi Maryama. Cikin tausasshen lafazi ta fara ajje kalamanta, tana mai tsananin son Hadiza ta fahimce ta, tare da ba ta iyakar amsar da ta sani.


"Hadiza...please ya kike da Annur? Ke ɗin wacece? Ƴar wane gari ce? Me ya kai ki Maraɗu da har kika ga no mai kama da Annur?"


A daburce ta ce,


"Ba mai kama da shi na gani ba, wallahi shi na gani. Ko za a yanka ni ba zan daina faÉ—ar Annur na gani ba."


Ajiyar zuciya ta sauke Maryama, ta ce,


"Na ji, na yarda Annur ne kika gani ba mai kama da shi ba. Ki ba ni sauran amsoshin tambayar da na miki."


Ko kaÉ—an ba ta son zancen. Abun kunya ne gare ta ta iya buÉ—ar bakinta ta ce ita karuwa ba ce. Karuwar Annur, wacce ta gudo daga garinsu kawai saboda zaman kanta.


"Are you with me?"


Maryama ta tambayi Hadiza, jin ta yi shiru, kuma tana jin saukar numfashinta, alamun dai tana saurarenta kenan.


"Uhm...na san shi ne...yana so na."


"Dadiron ki ne?"


Ta tsinkayo muryar Maryama ta mata wannan tambayar, cikin halin ko in kula.


Tunda take ba ta taɓa jin haushin kasancewarta wacce za a iya ambato da wannan kalmar ba sai yau. Me ya sa ba ta zama wacce za ta iya bayyana ko ita wacece ba a duk inda za ta tsinci kanta? Me ya sa take rayuwar da ita kanta take jin kunyar bayyanar da kanta a irin rayuwar gaban wasu mutanen? Haka kawai take jin ƙwarjinin Maryama. Ta rasa dalilin da ya sa take ganin darajarta, sam! Ba ta jin za ta iya yi mata ƙarya. Kuma a dukkanin yanayin Maryama idan aka mata ƙarya sai ta gane.


Da ƙyar ta iya bultso magana daga bakinta. Laɓɓanta na lugude ta ce,


"Ehh...abokina ne, yana biya min buƙatata, ni ma kuma ina biya masa ta sa. Ni ƴar Nijar ce, karuwanci ya gudo da ni daga ƙasarmu. Maraɗi ne garimmu, can ne asalina. Na je wurin wani biki ne na dangimmu, har Allah Ya sa na ga Annur ɗin a can."


"Biki...?"


Maryama ta ambata tana mai ci gaba da,


"Bayan kin gudo kin kama zaman kan ki ne kuma har kika iya komawa wurin wani biki? Kenan hakan ba zai iya zama wani abu ba a gare ki?"


"Tabbas! Hakan ba komai ba ne."


"Anyways, lets back to our business. To ke yanzu ta wace fuska kika kalli abun? A tunaninki tabbas Annur ne kika gani? Idan shi ne, me kike tunanin ya sa ya aikata hakan?"


"Abin da na kasa ganowa kenan. Zuciyata ta kasa tantance min gaskiyar wannan lamarin. Na kasa fitar da abun daga zuciyata. Wallahi a yanayin da na samu Annur abin a tausaya masa ne, abun ya zauna a zuciyarka ne."


"Shi kenan to. Yanzu idan na nemi taimako daga gare ki, za ki iya taimaka min?"


"Me zai hana?"


Hadiza ta gaggauta tambayar Maryama.


"Yauwa to. Ba zan so na zo inda kike ba gaskiya, saboda hakan zai iya zubar da kima ta a idon jama'a, ba za a iya gane dalilina na zuwan ba. Ya kenan?"


Shiru ta yi Hadiza tana nazari, dan ba ta san amsar da za ta ba ma Maryama ba.


"Uuhm..."


Maryama ta ambata.


"Ya kike so a yi?"


"Ko za mu yi mahaÉ—a?"


"Idan hakan kike so ya yi. Sai ki faÉ—a min inda za mu haÉ—u É—in ina jira."


Za ta kashe kenan Maryama ta ce,


"Wait, a minute please...dan Allah kar ki sanar ma kowa wannan maganar. Ina so ta zama sirri a tsakanimmu, ko Annur É—in kar ki faÉ—a ma wa."


"Ba zan faɗa ma kowa ba na miki alƙawari."


Bankwana suka yi daga nan suka kashe wayoyinsu.


Latsa kiran Jiddah ta yi Maryama. Babu ɓata lokaci kuwa Jiddah ta ɗauka. Bayan sun gaisa ne ta kwashe komai ta sanar da Jiddah, har wayar da suka yi da Hadiza yanzu.


"Am totally confused. Baki ɗaya kaina ya ƙulle, na kasa hango komai Jiddah. What can you say? Please hint me, little, Jiddah!"


Kanta ta gyaÉ—a kamar tana gaban Maryama ne, ta ce,


"Akwai ɗaure kai sosai lamarin. Me ye zai kai Annur Maraɗi cikin awoyin da ba su wuce shida ba? Me zai sa ya ga Hadiza a Maraɗi, kuma ya ƙi nuna ya santa, bayan kuma dadironsa ce? A tunanina ko kaɗan ba zai ɓoye mata kanshi ba, saboda ya san ta san komai game da shi. Ta gama sanin sirrinshi tunda har ya kasance ma'aboci aikata zina da ita."


Shiru Maryama ta yi na tsawon lokaci, kafin ta iya zaƙulo magana daga bakinta, ta ce,


"Ko kaɗan tunanina bai ba ni cewa Annur ne ta gani ba. Saboda a yanda ta siffanta shi, babu yanda za a yi cikin ƙanƙanin lokaci ya yi wanann ɓadda-kamar. Kuma ma idan ɓadda-kama zai yi, sai in ga ai a nan Nigeria zai yi ta. Ban ga dalilin da zai sa ya tafi Nijar ba."


Murmushin takaici ta yi Jiddah, ta ce,


"Ba abun mamaki ba ne dan ta ce shi ne a Maraɗi. Ai kin ga Annur ya taɓa samun taɓin ƙwakwalwa, kuma wanda ya samu matsalar hauka, a kowane lokaci ya kan iya tasar masa. Ta yiu ya taso masa ɗin ne bayan ya je can, tunda mutum kamar Annur dama ba za a raba shi da shiga cikin Nijar ba."


"Jiddah na fara tunanin wani abu. Na yarda da kalaman Hadiza ɗari bisa ɗari. Na fara zargin ƙila dai mai kama da shi ne ta gani. Kin san fa akwai irin haka."


"Haka ne tabbas. Amma yanzu ga shawara É—aya."


"Ina jin ki Jiddah...Allah Ya sa mai ɓullewa ce."


Jiddah ta ce,


"Kawai ki ma Bobby maganar kai tsaye cewa Annur ya ce yana son ki. Tunda yana yawaita faɗar zai iya ja da duk wanda ya nemi raba ki da shi, a ganina zai iya tona asirin Annur, in ma da wata ƙullalliya da yake ƙullawa ne"


"Good idea."


Maryama ta furta cikin murya mai nunar da ta ji daÉ—i.


Bankwana suka yi da juna, Maryama ta kashe wayar, tana jin sassauci a cikin zuciyarta.


***


Daga gefensa take zaune, butsu butsu ta ɗaga kanta ta dube shi, cikin tausayi da ƙara jin soyayyarsa a cikin zuciyarta.


"Amrah..."


Ya furta a cikin baccinsa wahaltacce da Dr. Huzaif ya narka masa allurar barci sannan ya samu ya yi.


A hanzarce ta miƙe tsaye tare da isa dab da gadon. Tsura masa idanuwa ta yi, kyam ta ke kallon fuskarsa. Kyakkyawa ne sosai. Hancinsa a tsaye yake siriri, bakinsa ɗan ƙarami wanda ya gama farfashewa, duk ya bi ya lalace tsabar wahala.


GyaÉ—a kanta ta yi ta gaggauta dawowa a cikin hayyacinta. Tunanin banza take a ganinta, tunda dai ga shi a kwance yana fama da kansa, me zai sa ita ta zurfafa a begensa?


"Amrah...Amrah nake so!"


Ta sake jin Modu ya ambata duk a cikin barcinsa da yake yi na wahala.


"Modu nice ag gabanka hwa. BuÉ—e idanuwanka ka gani Fiddou ce hwa ba Amrah ba."


Bai ma san tana yi ba, sai a hankali ta jawo abin rufa ta rufe shi cike da tausayi, ta kama hanyar komawa zamanta za ta zauna.


Jin sallamarsa ta yi ya shigo, hannunshi da leda babba, ya ƙarisa shigowa cikin ɗakin.


Da fara'arta ta amsa masa sallama, ta fasa zaman har sai da ya iso inda take.


"Sannu Fiddou! Ya giɗe yaƙ ƙara ji da jiki?"


"Da sauƙi dai."


Ta furta haÉ—e da gyaÉ—a kanta, hawaye na neman fara kwaranya daga idanuwanta.


"Ya isa giÉ—e ba kuka nat tambaye ki ba. Insha Allahu yana samun lahiya ba da jimawag ga ba. Kuma na tabbata likita zai ba shi kula yanda yak kamata. Ki kwantar da hankalinki."


Shiru ta yi da kukan, sai dai kuma hawaye bai daina fita ba. Tausayinsa take ji. Ko kaɗan ba za ta taɓa iya jurewa ba, ba za ta iya yarda da maganar Dr. Huzaif ba.


"Mahmouda ba na tunanin Modu zai warke. Likita da kai nai yac ce giɗe ga shi yana cikin yanayin matsala. Ka gan shi nan hwa barcin wahala ne yake. Ciwo yad dame shi, likita yai yi mai allurar barci. Yanzu kana ganin wanda zai warkewa ne ba zai taɓa

Please Login or Register in order to submit comment