You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taɓa zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_


Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


7⃣3⃣


Wattpad: PrincessAmrah


***


Dukkansu babu wanda ya san sadda ƴan sandan suka tafi. Momy ce ta lallaɓa ta musu alama kan su tafi ɗin. Cike da mamaki Dady ke kallon yadda Annur da Sans suka kasa rabuwa da junansu. Hanan da Janan sai murmushi suke saki, duk da cewa su ɗin ma suna al'ajabin wannan tsananin kama da take tsakanin Annur da Sans.


Uncle Marwan ne ya ce,


"Duka sai mu rankaya cikin gida, zan mana bayanin duk yadda abubuwan suka kasance."


Yawu ta haɗiya da ƙarfi Momy. Cikin ƙarfin hali ta matso magana, ta ce,


"Alhaji Marwan kana nufin dama can ka san inda Annur ɗina yake? Me ya sa za ka ɓoye mana?"


Ya yi murmushi.


"Duka wannan tambayoyi ne da zan amsa mana su idan mun samu wuri mun zauna. Ga kuma Dr. A tsaye."


Ya isa ga Dr. Hamdan yana murmushi.


"Ashe dama nan za ka yo Dr."


Dr. Hamdan ya murmusa.


"Shi ne mutumin da na faÉ—a maka na zo wurinsa É—in. Da alama ma dai kun san juna."


Dady ya ce,


"Young Dr. Ana ma maganar sanin juna ni da Marwana? Ƙanina ne uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya."


Da mamaki Dr. Hamdan ya kuma sakin murmushi.


"Allah mai iko! Kuma fa daga gidansa nake yanzu mai kawai na biya na shawo. Ai ni ban ma sani ba."


"Mu shiga daga ciki ko?"


Dady ya faɗa cikin murmushin ƙarfin hali.


Sai a sannan Annur da Sans suka saki juna. Yamaira ta riƙe musu hannuwa su duka biyun bayan ta saki hannun Yesmeen. Maryama kuma ta kama wa Yesmeen ɗin hannu, tana jin tsananin daɗi a duniyarta. Duk wata fargaba da damuwa da take a cikinta sai ta neme ta ta rasa.


Sun kama hanyar babban falon gidan kenan Dr. Islam ta iso. Da sauri ta taddo su, saboda tunda Baban Abdul ya faɗa mata Momy na neman ƴan sanda hankalinta ya tashi. Tana asibiti ne ta duba wasu patients shi ya sa tun ɗazu ba ta zo ba. Ba ta ga fuskokin kowa ba sai Maryama da ta waigo tana kallon ta. Murmushi suka sakar wa juna, duk da yake cewa Islam mamakin mutanen da ta gani a gabanta take yi. Jira ta yi har ta ƙariso kusa da ita. Suka gaisa cikin sakin fuska sannan suka isa cikin falon.


Take mamaki ya kama Islam ganin mai irin fuskar Annur har guda biyu sun zauna kusa da juna. Sai ta saki wayar hannunta ido buÉ—e ta kasa zama sai bin su da kallo take yi. Babu wanda ya mata bayani, har sai da ta jiyo muryar Momy cikin kuka ta ce,


"Alhaji Marwana ka mana bayanin abin da yake faruwa, don Allah. Ka sa hankalina ya daɗa tashi, gabana ya ƙi ya daina faɗuwa."


Alhaji Marwan ya yi gyaran murya.


"Zan fara da yi mana wata ƴar guntuwar nasiha, game da ɗaukar ƙaddara kyakkyawa da mummuna. Duk abin da ka ga Allah ya tsara ga bayinSa to ka ɗauka cewa dole sai ya faru da su ɗin, duk dabararsu kuwa. Sannan sau da dama abin da ba ka tunanin faruwarsa sai ya faru. Abin da kake da tabbacin zai faru kuwa sai ka ga bai faru ɗin ba. Ina so ku ɗauka cewa dama can Allah ya ƙaddara cewa za ku raini Annur tun yarintarsa har ya girma, sannan kuma a ƙarshe ku samu labarin cewa ba ɗanku ba ne na asali, ba ku ne kuka haife shi ba."


Daga Dady har Momy sai suka miƙe tsaye idanuwansu a buɗe suna bin Uncle Marwan da kallo.


"Yaya Iqra ku koma ku zauna. Yanzun nan zan warware muku zare da abawa."


Dady ne ya koma ya zauna, amma Momy ta gagara zama, Islam ma ta yi tsaye har yanzu ba ta daina mamaki ba.


"Annur ba É—anku ba ne. Duk ma yadda za a yi to tabbas ba shi ne ainahin É—anku ba. Ta yiwu a asibitin da aka haife shi ne aka samu matsala aka sauya muku shi. Amma tabbas É—an uwan Salman ne ga shi nan, É—an uwan tagwaicinsa. Sannan kuma Yaya ga Yamaira matata ga ta."


Ya nuna musu Yamairah da ta sunkuyar da kanta ƙasa tana kuka.


"Kar ka faÉ—a mana magana son ranka Alhaji Marwan. Ni na haifi Annur da kaina fa. Ta ya za ka ce wai ba shi ne É—ana ba? Wace hujja gare ka ta cewa an sauya min shi ne?"


"Ba ni da hujjar da zan yi proving zancen nan a yanzu, har sai mun je asibiti an yi gwajin DNA. Amma ina so na miki wata tambaya."


Bai jira ta kuma cewa komai ba ya ci gaba,


"Kin taɓa ganin mutane masu tsantsar kama irin ta Annur da Sans kuma suka kasance ba identical twince ba? Sadda kika haifi Annur ƴan biyu kika haifa aka ce miki kin rasa ɗaya? Salman da Yamaira ƴan Borno ne. A Borno State ke ma kika haihu. Bakya tunanin duk abin da na faɗa zai iya zama possible? I want you to think well, Hajiya Suhaila. Kafin mu je asibiti a muku DNA test."


Dady ya ɗan fara gasgata zancen Alhaji Marwan. Sai ya dafe kansa yana kuka sosai, tamkar ba namiji ba. Shi dama can haka yake da zuciya mai rauni, ƙaramin abu ma sai ya saka shi zubda ƙwallarsa. Bai gama tunani ba ya ji muryar Dr. Hamdan ya ce,


"Yanzu the best solution is that, a yi DNA test ɗin kamar yadda Alhaji Marwana ya faɗa. After that, idan za ku iya to tabbas za ku koma asibitin da aka haifi Annur. Akwai records na komai da ya faru in dai ba za ku iya manta date ɗin haihuwarsa ba. A lokacin har sunan nurse ɗin da ta karɓi haihuwarsa ma ana rubutawa. Sai ku zanta da ita. Ta yiwu a daidai lokacin da aka haife shi an haifi twince, sai aka musanya guda ɗin da ɗan da kuka haifa, aka damƙa muku Annur."


Cikin kuka Yamairah ta ce,


"Babu ko tantama abin da ya faru kenan. Mahaifiyarmu ta faÉ—a mana cewa Æ´an biyu ne ta haifi Yaya Salman, amma É—ayan ya rasu a take."


Sai Momy ta ƙwalalo ido haɗe da zubewa ƙasa rijif. Lokacin da ta haihu ta tuna. Shereefa da ta haihu aka ce mata ɗayan ya rasu. Cikin kuka ta ce,


"Ya sunan mahaifiyar taku?"


Yamaira ta ce,


"Sunanta Shereefah."


Momy ta dafe zuciyarta. Tana ganin yiuwar abin da a tunanin ta ba zai taɓa yiuwa ba. Kafin ta ce komai, Alhaji Marwan ya ce su taso su biyar; Dady, Momy, Annur, Sans da kuma Yamairah su tafi asibiti yanzun nan a yi ta ta ƙare. Yana so ya fitar da su Momy daga wasi-wasi.


Dr. Hamdan ma ya miƙe cewa zai koma Kano yau. Amma Dady ya roƙe shi alfarmar ya jira su dawo. Ko gaisawar kirki ma ba su samu sun yi ba saboda wannan tashin hankalin.


Zaman kuwa ya yi, Maryama da Isam sai kallon-kallo suke, sun kasa cewa ko uffan.


Zaman tsit ne ya biyo ɗakin, sai ɓuruntun Hanan da ke girki a kitchen. Yesmeen kuwa ta yi barci tun ɗazu tunda ba da ita suka tafi ba. Dr. Hamdan latsar wayarsa kawai yake yi, sai ya ɗan nisa ya ce musu sannu.


A asibiti kuwa, bayan an gama duka aka tabbatar wa su Momy cewa Annur ba jininsu ba ne, amma shi, Salman da kuma Yamairah jini ɗaya ne. Hakan ya daɗa tayar musu da hankali. Momy kamar zuciyarta za ta buga haka take ji. Ta rasa yadda aka yi hakan ta kasance. Wane irin daƙiƙanci da rashin hankali ne zai saka ma'aikaciyar asibiti tafka irin wannan babban kuskuren?


A cikin mota kuka kawai Momy ke yi. Dady kuwa kukan zuci yake yi, wanda ya fi na hawaye ciwo. Alhaji Marwan da ke tuƙi ne ke ta tausarsu.


"Shi ya sa kafin na tinkare ku da maganar, sai da na muku nasiha saboda na tabbata sai haka ta faru. Na sani, cewa babu daɗi, kuma dole za ku damu. Amma dole ku daure, ku miƙa komai ga Allah, sannan kuma ku miyar da komai ba komai ba..."


Bai rufe baki ba Annur ya ce,


"Kuma hakan ba wai yana nufin zan bar su Momy ba ne. Ko da a ce iyayena suna raye, na tabbata su kansu ba za su taɓa raba ni da su Momy ba. Raba ni da su kuwa tamkar raba ni da numfashina ne. Sun min abin da ba zan taɓa mantawa da su ba. Matar da ta shayar da ni, ta raine ni irin rainon da mahaifiya ke yi ga ɗan da ta haifa, har kuna tunanin akwai ranar da zan iya butulce ma su Momy? Har abada!"


Nannauyar ajiyar zuciya Momy ta sauke, duk da haka dai hawaye na zuba bisa kumcinta.


Sans bai ce komai ba. Sai jinjina lamarin kawai yake yi. A ranshi yake tunanin ashe ɗan uwansa na jini ne ya wulaƙantar da rayuwarsa. Ashe dai da rabon zai sake haɗuwa da jininsa. Ga shi Allah ya haɗa shi da mutum har biyu, ko ma uku. Tunda dai Yamairah ma kanta ta ajje ƴa, kenan ita ma ta shiga sahun jininsu. Bai san sadda ya saki murmushi ba, murmushin da har sai da ya bayyana.


A haka suka ƙarisa gida mai gadi ya buɗe musu gate suka shiga ciki da motarsu. Dukkansu jiki a saɓule suke banda Sans da Yamairah. Su kam daɗi ne ya turnuƙe zukatansu.


A falo suka yi branching, yanayin fuskokinsu kawai ya sa duk Æ´an É—akin suka gasgata cewa DNA É—in bai zo daidai da na su Momy ba.


Hannu Dady ya miƙa wa Dr. Hamdan haɗe da sakin murmushin ƙarfin hali.


"Dr. Mun bar ku da jira."


"Babu komai ai. Ga shi har na yi sallah ma."


"To masha Allahu. Abu dai ya tabbata Dr. Ashe Annur ba jininmu ba ne."


Ya goge ƙwallar da ta zubo masa a daidai nan. Haɗe da dakatawa saboda nauyin maganar da ya ji.


Dr. Hamdan ya ce,


"Kar ka damu Oga. Haƙuri za ka yi, haka Allah ya tsara muku tun asali. Yanzu ka ga wani al'amari na Allah, inda za ka san cewa komai rubutacce ne, yaushe rabo na da kai? Shekara da shekaru muka rabu, ko a waya ba mu tare. Amma cikin iko da hikimar Allah, kamar wasa na gan ka a Facebook an sako min kai a People You May Know. Ina ganin sunan na ji daɗi sosai, ban gama tabbatar da kai ɗin ba ne har sai sadda muka yi magana da kai. To ka ɗauka cewa wannan ɗin ma dama can rubutacce ne."


"Babu abin da ya fi damu na irin wulaƙancin da na ma Salman. Na ci mutuncinsa, na ci zarafinsa a kan ɗan uwansa. Ashe ni ban sani ba haukan banza nake, a kan ɗan uwansa ne nake masifar, ɗan uwanshi gudan jininsa..."


Yaimaira ta gaggauta dakatar da Momy.


"Ki daina faɗar haka please. Yadda kika ɗauki Yaya Annur to a yanzun ma haka nake fatar ki ci gaba da ɗaukarsa. Na tabbatar da shi ɗin ma a nashi ɓangaren haka ne. Tunda dai mun rasa iyayenmu, kuma ko suna rayen ma wane irin butulu ne shi da zai bar ku bayan rayuwar da ya yi a tare da ku?"


Sai a sannan Islam ta yi magana.


"Lallai maganar Uncle Marwan gaskiya ce. Cewa so da dama abin da ba ka taɓa tsammani ba yana faruwa. Ga shi nan dai, tunda muke a rayuwarmu ba mu taɓa kawo wa rayukanmu ba cewa Yah Noor ba shi ne ainahin ɗan su Momy ba."


"To ina É—an namu yake?"


Momy ta tambaya cikin kuka. Ta ji muryar Dady ya ce,


"Ina tunanin shi ne ya rasu."


Cikin takaici Momy ta kalli Dady.


"Ba na tunanin É—anmu yana raye, kamar shi ne ya rasu sai aka macanza shi a matsayin É—an uwan tagwaicin Salman."


Ta dafe kanta. Kuka sosai ke sake zo mata. Tana jin takaicin rayuwarta. Komai ganinsa take tamkar a mafarki. Kamar za a bubbuga ta ta tashi daga barcin da take yi.


Dr. Hamdan suka ji ya ce,


"Kamar yadda na faɗa muku a farko, daurewa za ku yi ku shirya ku tafi Maiduguri. FMC ɗin tasu an dawo da ita nan cikin Maiduguri, da ma'aikatan nasu da duk wasu records da ke akwai, duk da dai ba na tunanin har yanzu za a iya samun nurse ɗin da ta karɓi haihuwar tasu tana aiki ba ta yi retire ba. Amma dai sanin nata yana da amfani, nemanta kuma ba zai yi wahala ba."


Alhaji Marwan ya ce,


"Wannan gaskiya ne. Kuma abin da ya kamata a yi kenan, wata ƙila ba za a rasa wani labari daga gare ta ba."


Dady ya ce,


"To gobe idan Allah ya kai mu sai mu tafi. Hausawa suka ce da zafi-zafi kan daki ƙarfe. Mu yi komai kan lokaci, ta yadda za mu gama a kan lokaci."


"Haka ne. Pharm IA ni bari in kama hanya, yanzu insha Allahu."


Hanan da ke daidai isowa wurin ta ce,


"Uncle an fa gama abinci ta ya za ka tafi ba tare da ka ci ba? Ga shi can a dining na jera."


Da fara'a ya ce,


"ÆŠebo ki kawo min a nan kawai in ci."


Ta koma dining É—in. Faten dankalin turawa da kaza ne ta zubo masa a plate, ta sako fork da spoon sannan ta kawo masa. Drink ta kawo masa ta dire a gabansa sannan ta juya ta tafi.


"Wai ni kam Maryama, ban ma tambaye ki lafiyar ango ba. Wannan tashin hankali bai bar ni ba."


Kallon juna Maryama da Annur suka yi suka sakar ma junansu murmushi. Sannan ta ja hannunta suka wuce ɗaki. A can ta labarta mata duk abubuwan da suka faru tun daga farko har ƙarshe. Islam ta fasa kuka.


"Haƙiƙa Amrah haske ce, haka mahaifiyarta ma. Tun ina yarinya ni da Aunty Saddiqa muka ɗora wa Amrah da iyayenta karan tsana. Muka tsane su kasantuwarsu talakawa. Sai ga su ta dalilin Mahaifiyar Amrah komai ya bayyana. Yes, ita ce sila. Saboda inda ba ta ba ki labari ba da komai bai faru ba. Da a haka za a yita zama cikin duhu ba tare da su Momy sun gano cewa Yah Noor ba ɗansu ba ne. Sannan ke Maryama."


Ta rungomo Maryama, ta ce,


"Tabbas ke jaruma ce. Mace ce ta kirki wacce ta san me take yi. Allah ne kaɗai zai iya biyanki abin da kika aikata. Har kika iya daurewa kika auri mahaukaci, wanda ko ni nan ba zan iya ba. Insha Allahu zan je har gidan su Amrah in roƙi mahaifiyarta gafara, a kan abubuwan da na aikata mata ita da Amrah."


Maryama ta yi murmushi cike da jin daÉ—i, ta ce,


"Za kuma ta yafe miki. Na san halin Umma sosai, a wurinta Amrah ta gado kyawawan halaye."


Sai bayan sallar la'asar sannan Dr. Hamdan ya tafi. Sun masa godiya sosai, har Maryama ma sai da ta masa. Ta yi mamakin mutumin, yadda Dr. Sandra ta mata bayanin matsayinsa da kuma iliminsa, amma a haka yake da irin wannan sakin fuskar.


Annur da Sans kam sai suka kasa rabuwa. Daidai da sallah tare suka je masallaci. Labari kawai suke yi. Sans na daÉ—a neman gafararsa bisa ga abin da ya aikata masa. Sai a yanzu ma yake jin duk yadda abun ya faru. Murmushi kawai ya saki yana jin daÉ—i, saboda a ganinsa hakan ma alkhairi ne, tunda har ya gano Æ´an uwansa na jini wanda bai san da su ba. Sannan kuma ya gane cewa iyayensa basa raye, ko ba komai zai musu addua.


A falo suka samu Momy da Dady zaune. Fuskar Momy duk ta kumbure tsabar kuka. Duk ba ta da walwala sosai. A gabanta suka zauna a tare. Ta tsura musu idanuwa tana kallo. Sai yanzu take daÉ—a tabbatar da tsantsar kamannin da ke tsakaninsu. Bambancinsu ba wani mai yawa ba ne. Sai wanda ya ajje hankalinsa sosai sannan zai fahimta.


"Momy murmushi fa ya kamata a ce mun same ki kina yi a daidai wannan lokacin. Ga yaranki sun ƙaru, sun zama ƴan biyu. Sannan kuma ga ƙanwarsu Yamaira. Ai idan ni ne ke dariya zan ta yi inta famar wagar baki."


Dady ya yi dariya sosai.


"Yo Annur idan taita wagar baki kuma ai sai a kai ta psychiatry a ce ba ta da lafiya."


Sans ya ce,


"A'a fa Dady. Murna ce kawai."


Ba su bar wurin ba har sai da suka ga sun saka ta dariya sosai. Dady ya ce da Annur ya je ya ce ma Maryama ta fito su tafi har an fara kiran magrib. Annur ya ce a dai bari har su yi sallah sannan su tafi.


A É—aki kuwa Hanan da Janan sai famar zaulayar Maryama suke. Wai yau za ta amarce, saboda sun mata, wacce tun ga bikin ta so yi mata ita amma sai ba ta samu damar komawa washe garin bikin ba, saboda zuwan su Hanan.






"Tunda dai komai ya bayyana, na tabbata a yau komai zai kammama."


Harararta ta yi cikin wasa,


"Ke don Allah Aunty Islam."


"Yo ai gaskiya ce Maryam. Da gaske sai kin dage, don yayan can nawa da alama gwarzon namiji ne."


Ta yi saurin doÉ—e kunnuwanta.


"Ai ba na ma jin ki ni kam."


"Ke dai kika sani. Na tabbata a zuciyarki kina nan kina ta shi min albarka. Amma don iyayi sai wani rufar kunnuwa kike..."


Ba ta rufe baki ba wayarya ta yi ringing. Baban Abdul ne ke kira hakan ya sa ta gaggauta ɗauka. Ce mata ya yi ga shi nan a falo ta fito su tafi da sauri, saboda sai sun biya ta gidan iyayensa sun ɗauko Abdul da aka kai tun safe yini, kasantuwar har yanzu hutunsu bai ƙare ba.


Tashi ta yi Maryama ma ta bi bayanta. Daga rakiyar su Islam sai Annur ya ce ita ma ta fito su wuce.


Bayan ta ɗauko hijabinta sai da Dady ya musu nasiha sosai sannan ya ba shi makullin Corolla LE ɗinsa cewa ya mallaka masa ita. Tunda asalin tashin ita ce a hannun Sans, ba kuma za a iya karɓarta daga gare shi ba.


Ta yi mamakin yadda ya iya gane gidan nasu babu ko ɓata lokaci, amma sai da suka fara biyawa ya musu siyayya. Suna isa gida mai gadi ya buɗe musu gate bayan ya tabbatar cewa su ne. Suka shiga ya faka a madaidaicin parking space ɗin gidan.


Maƙale da juna suka iso bakin ƙofar. Faɗi take ya sake ta ta fiddo key daga jikarta amma ya ƙi sakinta. Da dabara ta samu ta fiddo ta miƙa masa. Kasa buɗewa ya yi dole sai da ta karɓa ta buɗe ɗin, suka ƙarisa ciki.


Sallar isha'i ya fara jan su suka yi. Sannan ya ce da ita ta tashi su yi nafila, irin wacce amarya da ango ke yi. Tun a nan jikinta ya yi sanyi, sai ta ƙara tabbatar da zancen Dr. Islam, cewa ba zai ɗaga mata ƙafa ba yau. Tana so, tabbas. Saboda babu macen da za ta zauna tare da namiji a matsayin mijinta na tsawon wannan lokacin, kuma a ce ko yaya ne ba ta ji sha'awarsa ba.


"ÆŠauko plate a juye kazar nan. Ina jin yunwa."


Ta harare shi.


"Sai fa da Hanan ta ce maka ta kawo abinci ta yi tuwon semo da ɗanyar kuɓewa ka ce a'a. Shi ne kuma za ka ce wai kana jin yunwa?"


Ya kama hannuwanta duka biyun ya saka a nashi.


"Da gaske ina jin yunwa Maryam..."


Ji ta yi wata irin kasala ta wanzu a jikinta. Yadda ya kira sunan nata dole jikinta ya yi sanyi, ga kuma yadda yake wasa da ƴan yatsunta, duk sai ta fara rasa nutsuwarta. Da ƙyar ta iya saita kanta. Ta ce,


"Ina zuwa."


Ta yi saurin zare hannuwanta daga cikin nashi. Ba ta jima ba sai ga ta ta dawo da plate sai cups guda biyu. Naman kazar ta juye a ciki, sannan ta zuzzuba musu lemukan a cups É—in. Tana gamawa kuma sai ta yi shiru, ta saita idanuwanta a wuri guda tana kallo. Ganin haka ya sa Annur kamo ta ta dawo a jikinsa.


"Tunanin me Mi_amor ke yi?"


Samun kanta yi da jin kunyarsa. Ta rufe fuskarta tana murmushi.


"Kawai na tuno wasu lokuta ne, da nake mana irin wannan zuba abincin, nake baka a baki da nufin ba ka da lafiya. Wai ashe dai ɗan bawan Allah'n nan kallo na yake ƙyar, lafiyarsa ƙalau."


Ya haÉ—a fuskarsu tana gogar juna.


"Ba kodayaushe ne nake da lafiya ba, kamar yadda na faɗa. Abun yakan kaɗo min ne. Tun daga ranar da Umma ta zo ne dai ban ƙara jin ciwon ba."


"To na ji. Ka ce kana jin yunwa kuma ka tsaya zuba surutu."


Ya janye fuskar tasa sannan ya taɓe baki.


"Yunwar fa ba wata ta a zo a gani ba ce. Ko kalamanki kawai na ci gaba da saurara zan iya jin cikina ya cika."


Dukan wasa ta kai masa.


"Lallai ma mutumin nan. Dama ba yunwar kake ji ba."


Ta ɗauko plate ɗin. A hankali suka rinƙa feeding junansu, suna yi suna kora lemu mai sanyi har suka ƙoshi. Kwashe kayan duka ta yi ta kai kitchen, sannan ta dawo ta fesa freshner, a take ɗakin ya gauraye da ƙamshi.


"Yah Noor na bar ka lafiya. Ni zan kwanta."


Ta doshi hanyar barin ɗakin. Ai ko bakin ƙofa ba ta isa ba ta ji shi ya damƙo ta. Bai ce mata komai ba sai ji ta yi ya ɗauke ta ɗaf kamar wata jinjira. Ta rinƙa mutsu-mutsu tana faɗin ya sauke ta amma ya yi kamar bai ji ta ba. Sai a tsakiyar gado ya dire ta.


"Yarinya kin ma isa? Kin san irin dauriyar da na rinƙa yi a baya ina kwanciya da ke a gadon nan ba tare da wani abu ya haɗa mu ba? To yau duk sai na fanshe dauriyar da na yi a baya"


Sai ta samu kanta da faÉ—uwar gaba.


"Yah Noor please..."


Bai ko jira ta ƙarisa zancen ba ya haɗa bakinsa da nata. A take lamurran suka fara sauyawa. Soyayya yake gwada mata wacce ya jima yana wa Amrarsa tanadinta. Shi kanshi ya yi mamakin kansa, bai taɓa tsammanin akwai macen da zai damƙa wa dukkanin soyayyarsa ba, sai ga shi a yau ya samu wannan tabbacin.


Tun tana noƙewa har ta miƙa masa ragama tare da ba shi haɗin kai.


Da asubah ya kunna side lamp. Kyakkyawar fuskarta ya ƙura wa idanuwa. Lallausan gashin kanta duk ya barbazu bisa fuskarta. Barci take yi sosai ga hawaye da ya bushe a fuskarta. Sai ya saki murmushi haɗe da dafa goshinta.


"Allah ya yi miki albarka Maryam. Allah ya biya miki dukkanin buƙatunki. Na ba ki amanar rayuwata Maryama. Duk da cewa Amrah na nan a cikin zuciyata, kamar rubutun da aka zana a jikin dutse, wanda babu gogewa a gare shi. Hakan ba zai taɓa saka ni daina ƙaunarki ba. Kalmar Amrah nake so ba za ki sake jin ta a bakina ba, har abada! Daga yanzu sai dai kin rinƙa ji na ce MARYAMA NAKE SO!"


Ya sauke hannunshi daga dafewar goshin da ya mata. Sannan ya nufi toilet ya yi wanka ya É—auro alwalla.


***


*Masu kuka ina fatar kuka ya ƙare😀. Yanzu kam na tabbata babu sauran ɓacin rai. Sai dai zuwa Maiduguri da su Dady za su yi, ko za su dace? Amsar na a shafin gaba, wanda daga shi sai na ƙarshe insha Allah.*


*Finally, the long awaited day has come. Annur da kansa ya furta Maryama yake so. Ya haƙura da faɗin Amrah yake so, har ƙarshen rayuwarsa. Wa da wa suka ji daɗi? In ga hannuwanku sama...lol.*


*Masu kirana, masu turo min saƙon waya duk ina godiya. Allah ya saka muku da alkhairi ya bar zumunci.*


Thanks all.


Pinky durling💞
RAZ 2
[9/28, 8:47 PM] Princess Amrah✍🏻💞: *🅰MRAH NAKE SO!♥*


_(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi)_


Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (Sickler)


Na Amrah A Mashi
(Princess Amrah)
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


7⃣4⃣


Wattpad: PrincessAmrah


***


A bisa stool ta zauna tana shafa mai.

Please Login or Register in order to submit comment